Showing 27001 words to 30000 words out of 149432 words
Chapter 10 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
haka haka ?"
Murmushi tayi tare da kallon ledar hannun Mufida tana fad'in,
"Har kin amso muna d'inkin ankon bikin ne?"
"Wannan bashine amsar tambayar da na maki ba, cewa nayi meke damunki idan kuma yanzun mun Fara 'boyewa junan mu sirri ne to shikenan"
Murmushi tayi tare da dafa kafadarta tace,
"Haba aike ma kinsan ba abunda muke 'boyewa junan mu ba sirrina da baki sani ba haka ma ba naki wanda bansani ba,wani al'amari ne ya d'an sani cikin tunanin da kikaga ina yi."
Bata labarin yadda sukayi da Usman tayi har zuwan Muhdeen da yadda Umma bataji dad'in ganin kayan nan ba,duk sai da ta sanar da Mudida.Mufida kam janyo ledojin tayi ta bud'e ta ciro chocolate cake da Biscuit ta Fara ci tana ci tana magana.
"To waishi Usman d'in meye nufin shi akanki kodai ya fad'a ne."
Ta k'arasa maganar tana dariya,dukan wasa Inteesar takai mata tare da cewa,
"Ni yanzun buri na bai wuce nacigaba da karatuna ba gsky dan kwata- kwata bana ma mafarkin aure yanzu. "
Caraf Mufida tace,
"Yauwa kin ma tuno Mani da labarin da nake son baki,Albishirin ki".
Da sauri Inteesar tace goro tana murmushi Don tunanin ta labarin da zai sanyata farin ciki ne,Mufida tace ,
"Wallahi nayi matarkin auren ki amma yayana kika aura".
Take far'ar fuskar Inteesar ta d'auke.
"Wani yayan ki na aura?"
Kallonta mufida tayi ganin yadda ta sauya lokaci guda tace,
"Ina da wani yayan da ya wuce Yaya Muhdeen ne?"
Fuskar Inteesar ta kalla taga annurin fuskar ta d'auke cikin mamaki tace,
"Meye kuma na 'bata rai dan kawai nace nayi mafarkin kin auri Yaya na? kuma Koda na fad'awa Mummy tace itama duk lokacin da zatayi mafarki da matar Yaya Muhdeen ke take gani a mafarkinta "
Ta'be baki Inteesar tayi tace,
"Kodayake mafarki ba gaskiya bace k'arya ce, Amma ko a mafarki naga wannan mugun yayan naki na farka sai nayi sadaka."
Sake baki Mufida tayi tana kallonta damamaki abun ya d'an Sosa ranta Amma sai ta share tacigaba da shan chocolate,zuwa jimawa kad'an ta kalli Inteesar tace,
"Wai ke yayana kikeyiwa k'iyayya har haka?mutumin da Mata suke neman sa da kud'in su,aike wallahi idan ma kika samu miki irin Yaya Muhdeen abun alfahari ne a gurin ki.Domin shi miji ne na nunawa sa'a,wasu ma da suke masa kallon balarabe wad'anda basusan asalin sa ba,domin ya had'u ta ko'ina koke da kike ganin ke wata kyakkyawa ce baki Kai Yaya na ba,har kike wani neman tsari dashi,shi wannan Usman d'in da kike kulawa ko kwatakwacin kyawu da had'uwar Yaya na baikai ba.
Inteesar ta ta'be baki tace,
"Ni kyau baidameni ba Hajiya yaje yayi ta fama da kyawun nasa 'yan matan da suke ribibin sa suje suyi tayi,ke nifa bana son namiji kyakkyawa "
Mufida ce tayi wata dariyar raining hankali.
"Eh dole kice baki son namiji kyakkyawa tunda baice yana sonki ba"
"Taya Mai zaice yana sona mutumin da ya tsane ni a rayuwa baya k'aunar gani na nima ba Wanda na tsana sama dashi a rayuwa"
"Inteesar yaushe kika koyi yiwa mutum sharri? Yaya Muhdeen d'inne ya tsane ki me yayi maki na tsana?"
Murmushin yak'e tayi ta kalli Mufida tace,
"Ba Zaki Gane bane,tunda ba a gaban kowa yakeyi ba sai yaga ba idon mutane yakemun cin kashin da yakeyi,kuma ko na fad'a maki yanzun ma ba Zaki yadda ba.Amma zan fad'a maki Abu d'aya saboda Yaya Muhdeen na d'auke k'afata da zuwa gidan ku,Amma kukayi bina keda Gwaggo har kuka gaji,Amma yanzun tunda ya kusa aure da zaran yayi aure ya tare da matarsa a sabon gidan sa zaku cigaba da ganina a gidan KU,Amma gaskiya yayan ki ya azabtar dani a baya bana k'aunar ma mu had'a inuwa d'aya dashi."
Allah sarki bansan meye ya maki ba,kuma baki fad'a Mani ba Amma inaji a jikina kece matar da Yaya na zaiyi rayuwa da ita.
*KUYI HAKURI DA WANNAN KILA KUJINI ANJIMA*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
( Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa.
Page2️⃣1️⃣
"Allah sarki bansan meye yayi maki ba,kuma baki fad'a Mani ba amma inaji a jikina kece matar da yayan mu zaiyi rayuwa da ita.
Wani kallo ta watsawa Mufida ba tare da ta sake cewa komai ba ta kanyo ledar da Mufida ta shigo da ita,kayan ta fito dasu wad'anda suka Kai d'inki ranar da Usman ya kad'e ta da mota,duka d'inkin iri d'aya akayi masu tun daga Kan atamfa da material da less d'in duk dinkunan iri d'aya akayi masu, tundaga Kan ankon yinin biki har zuwa na dinner da lunching.harda wani shadda da Mummy ta siye masu su biyu kawai zasuyi ankon , Inteesar taji dad'in ganin kayan sosai tsabar farin ciki rungume Mufida tayi tana godiya.Mufida ta kalle ta tare da zame jikinta daga nata tace,
"Nidai sake ni don naga alamar k'arfi ya ishe ki,kuma da kike mani godiya ai ba nice zakiyi wa godiya ba, Mummy ce,don ita ta siye Mana kayan kuma kuma ta biya kud'in d'inkin.Kuma tace tasa akawo mana gyalulluka da takalma jakka wad'anda zasu shiga da kayan."
Murmushi Inteesar tayi tana fad'in ,
"To sai dai kece zaki saka gyale,amma banda ni don kinsan cewa Hijab nake sakawa."
Ta janyo less d'in purple colour ne wanda yake da ratsin milk colour tana fad'in,
"Kinga Hijab d'in da Mummy ta siye mani last month Milk colour ne dama ban ta'ba Sanya shi ba,kinga zai shiga da less d'in."
Harara Mufida ta watsa mata.
"Wane irin Hijab kuma?kinsan Allah ba Hijab d'in da zaki saka gyale zamu saka iri d'aya,duk da nasan baki saba ba amma lokacin bikin nan kam dole kiyi hak'uri .Don Wallahi so nake komai namu ba ban banci komai ya kasance iri d'aya zamu saka,Don so nake mu kece raini a bikin nan.Sannan kuma gsky dole ki koma gidanmu da zama har a gama sabgar bikin nan."
Da sauri Inteesar ta kalleta da niyyar bud'ar baki tayi magana,amma sai taga Mufida ta had'e fuska ta ajiye Mata kayan ta nufi hanyar fita.
Tana jin sanda Mufida ke yiwa Umma magiya akan tabar Inteesar tayi kwana biyu a gidansu kuma Umma ta amince da hakan. cikin farin ciki Mufida tabar gidan.
'Bangaren Muhdeen kuwa Shima sai shirye-shirye yakeyi da abokan sa,dama babban abokinsa d'an uwan sa ne jabir sai kuma abokan su guda biyu Salisu da Bilyaminu,suna ta sabgogin bikin abokin nasu ba kama hannun yaro. Yau ne suka shirya inda zasu had'u da k'awayen Amarya ,don suji abubuwan da suke buk'ata na hidimar biki.
Su Hajiya Gwaggo kuwa,gatanan dai ba yabo ba fallasa,ita bata farin ciki da auren kuma bata bak'in ciki.Yayinda bak'i da suka zo daga garuruwa musamman mutanen garin Kontagora da Abuja duk sun iso,k'anwar Dady wato Hajiya Maryam tazo da 'ya'yanta tagwayen'yan mata Azeeza da Azeema suma bazasu wuce sa'annin Mufida da Inteesar ba Asiya ma tazo don bikin yayi dai-dai da hutunta .Hajiya saudat matar Alhaji Adam wato mahaifiyar Jabeer ma ta iso da suran dangi da suke garuruwa duk sun iso.
Mufida ce ta janyo tagwayen k'anwar Dady Azeema da Azeeza suka nufi gidansu Inteesar,dama tunda suka iso suke tambayarta ina Inteesar,don sun saba ganin Pic d'inta idan Mifida ta d'ora a status ko a dp don akasari tare suke d'aukar photo,suna kuma k'aunar Inteesar har cikin ransu.
'Bangaren amarya kuwa nan ma shiri sukeyi ba kama hannun yaro, k'awayen ta kuwa sai santin ango sukeyi duk da yawancin su basu ta'ba ganin Muhdeen a zahiri ba sai photo da suke ganin sa, k'awayenta biyu ne kawai suka San Muhdeen a zahiri Jummy da shila, kasancewar sune manyan k'awayenta kuma akasari suna yawan zuwa gidansu Sumayya wata rana su tarar da Muhdeen yazo suna tare,wata rana kuma shine zaizo ya tarar dasu sunso wurinta.
Koda Su Mufida da Azeema da Azeeza suka k'arasa gidansu Inteesar sun tarar da ita ta gama wanke kwanukan wanke-wanke ta shiga dasu kichen d'insu dake tsakar gidan tana fitowa suka had'a ido,sallama suka shigo cikin gidan, Inteesar ta amsa masu tare da tunanin ina tasan wad'annan Tagwayen masu matuk'ar kama da juna,take ta tuna cewa a wayar Mufida ce take ganin pic d'in Tagwayen.Murmushi suka sakar Mata yayinda itama ta mayar masu da marttanin Murmushin tace,
"Oyoyo manayan bak'i ne mukayi yau a gidan namu haka?"
rungume ta sukayi Azeema ta rungumeta ta ta gabanta yayinda Azeeza ta rungumeta ta bayanta tamkar ba yau suka fara ganinta ba.Lokaci d'aya suka saketa fuskokinsu d'auke da murmushi, Azeema tace,
"Inteesar mun same ku lafiya?"
Cikin farin ciki da jindad'in ganin su ta bata amsa.
"Lapiya qalau wallahi,sai dai bansan dawa nake magana cikinku ba Azeeza ce ko Azeema?"
Murmushi Mufida tayi kafin ta bata amsar cewa
"Kina magana ne da Azeema"
"Ayyah Masha Allah sannu da zuwa Azeema"
Ta maida dubanta ga Azeeza wacce ke karanta message a wayar ta.
"Sannu da zuwa Azeeza fatan kun iso lafiya?"
"Lafiya lau wallahi Inteesar,ai muna d'an hutawa kad'an mukazo don muganki"
"Aiba Wai saboda ganin ta kad'ai mukazo ba,munzo d'aukarta ne yau zamu tafi da ita gidanmu can zatayi ta kwana sai bayan biki sannan zata dawo gidansu"
Murmushi Azeema da Azeeza suka sake tare da cewa
" hakan yayi"
Inteesar ta fara magana tana fad'in
"Ba inda zanje yau sai dai gobe idan za'ayi lunching sai ku biyo tanan mutafi"
Harararta Mufida tayi sama da kasa.
"Ai baki isa ba,dama na nemi izinin Umma tun wancan ranar,kuma ta amince muje sai bayan biki ki dawo,bayan haka jiya da na shigo na k'ara tuntu'bar ta da maganar tace ba komai har Abba ma ta sanar dashi.Don haka ki tattaro muna d'inkunan bikin mu kizo mu tafi.
Shiru Inteesar tayi tana nazari don ba haka taso ba,don kwata-kwata batayi niyar komawa gidan ba,saboda alwashin do da taci Kan cewa ba zata je gidan ba sai bayan Muhdeen yabar gidan,amma yanzun kam ba yadda zatayi don Mufida ta d'aure ta da jijiyoyin jikinta.Mufida ce taja hannun Azeema da Azeeza.
"Kuzo mu shiga mu gaida Umma"
Binta sukayi harda Inteesar,bakunan su d'auke da sallama,bayan ta amsa masu ne suka shiga,tana kwance kan gadonta dama duk maganar da sukeyi a tsakar gidan a cikin kunnenta yake,zama sukayi kan tabarmar suka gaishe ta cikin girmamawa.Ta amsa masu fuskarta a sake Mufida ta fara magana tana fad'in.
"Umma wad'annan 'yan uwa na ne,yaran k'anwar Dady ce,'yan biyu ne Azeema da Azeeza"
"To Masha Allah,kunzo lafiya ya hanya?"
Dukkan su biyu suka amsa da
"Alhamdulillah"
"Umma dama munzo zamu tafi da Inteesar"
Cewar Mufida yayin da take kallon fuskar Umma,
"Badamuwa ku tafi Allah yasa a watse taro lafiya yasanya alkhairi"
Ameen suk amsa yayinda Inteesar tayiwa mahifiyarta sallama suka mik'e suka nufi hanyar fita su duka. 'Dakin Inteesar suka shiga inda ta kwaso d'imkunan bikin zata d'aiki kayan sawarta Mufida ta hana Wai tayi amfani da nata,daga nan suka nufi gidansu Mufida.
A yammacin ranar bayan suk sunyi wanka sun canza kayan jikin su, Azeema da Azeeza wani material pink colour suka saka riga da siket, yayinda Mufida ta saka doguwar Riga na atamafa, Inteesar kuwa rigar Mufida ta abya ta saka Green wanda Muhdeen ya siyo ma Mufida a Dubai lokacin da suka je siyen kayan lefe,kayan sun burgeshi Matuka amma Sumayya tace bata son kayan,hakan ne yasa ya siyewa K'annen sa Mummy ta raba masu kayan su uku Asiya,Mufida,da kuma Inteesar.Suna zaune akan gado suna suna fira ne Inteesar ta mik'e ta bud'e fridge din d'akin ganin ba ruwa sai lemuka ne yasa Kai tsaye ta fita d'akin Don zuwa kitchen ta d'auko ruwan da zata sha.Dai-dai tana k'ok'arin shiga kitchen d'in Dai-dai Muhdeen ya shigo zai wuce part d'insa Yana rik'e da waya a kunnensa Koda yaga Inteesar zata shiga kitchen a tunananin sa Mufida ce,hakan yasa ya janyo hannunta ba tare da ya kalleta ba yace,
"Yauwa Muje ki gyara Mani part d'ina,duk da ba wani iya gyara kikayi ba yafi babu,zanyi manaji hakanan"
Bai kalli fuskarta ba yaja hannunta suka nufi part d'insa ,sai da suka shiga falon ya saki hannunta yana cewa,
"Ki fara gyara falon"
Daga nan ya wuce cikin bedroom d'insa,binsa tayi da kallon mamaki.
Daga nan sai ta fara k'ok'arin gyaran falon,cikin k'ank'anen lokaci ta gama gyara falon fess ta kunna turaren wuta take falon ya d'auki k'amshi.Dai-dai lokacin ya fito har wannan lokacin ya fito hannunsa rik'ke da waya yana danne-danne a wayar kallon falon yayi sannan ya maida idonsa akan wayar yace,
"Dama kin iya gyara waje iskancine kesa idan an sakaki bakiyi dakyau sai yau da kikaga damako?To shiga ciki ki gyara bedroom d'in"
Har yakai K'arshen maganar bai d'aga ido ya kalleta ba.kwatsam sai yaji saukar muryarta a kunnensa sa tana cewa,
"Nikam wallahi bazan shiga ba"
Da sauri ya d'ago Kai yana kallonta da mamaki,domin shi a zatosa Mufidace ganin kayan da ya siyo Mata a Dubai ne a jikin Inteesar yasa yayi tunanin Mufida ce a she ba ita bace Inteesar ce tasa kayan Mufida.Had'e fuska yayi yana cewa
"Kee ubanwa ya kawoki d'akina?"
Kallon mamaki take masa don gani take ya raina mata hankali.
"Tukunna ma dai ba kince idan na sake ganinki a gidan nan duk abunda naga dama nayi maki ba?ke ga mara kunya fitsararriya ko?to yau zakiga kuwa abunda zanyi maki"
Gaban Inteesar ne ya fad'i ganin ya nufota gadan-gadan fuskar nan a murtuk'e ba sassauci a tare da shi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
( Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa.
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.
Page2️⃣2️⃣
Gaban Inteesar ne ya fad'i ganin ya nufota gadan-gadan fuskar nan a murtuk'e ba sassauci a tare da shi.
Tattare k'asar rigarta tayi da nufin guduwa,kunsan abu ga dogon mutum ai taku biyu yayi ya isa gare ta, kafin ta ankare ganinsa kawai tayi a gabanta yayi mata dirar mikiya.Hannayenta duka biyu yasa ya murd'e mata hannayenta tare da maidasu baya,hakan yasa ta bud'e baki ta saki k'arar azaba da sauri yasa hannunsa d'aya ya toshe mata bakii, yayin da d'aya hannun yana rik'e hannayenta da ya murd'e.Girgiza kai kawai take yi na azaba yayinda Idanuwanta suke tsiyayar da hawaye.girgiza kai taci gaba da yi idanunta na cigaba da zubar da hawaye.Girgiza masa Kai tacigaba da yi amma ko a jikinsa baiji tausayinta ba.
Suna cikin wannan halin ne Jabeer ya turo k'ofar falon ya shigo,turus ya tsaya yana kallon Muhdeen cikin tsananin mamaki ya ce
"Meye haka?wanna wani irin rashin imani ne?"
K'arasawa yayi ya cire hannun Muhdeen daga rik'on da yayi wa Inteesar.yana sakinta ta zube a wurin ta samu damar fitar da kukan zucin da takey.Jabeer harara ya watsa masa .
"Yanzun meye kake aikatawa haka? Zaka kama 'yar mutane kana azabtar da ita akan meye?"
"Ba azabtar da ita nayi ba tarbiya nake koya mata."
"Eh k'warai kuwa tarbiyya kake koya mata irin tarbiyuar da kake koyawa Asiya da Mufida,idan Asiya da Mufida sukayiwa laifi haka kake ladabtar dasu?"
Ya k'arasa maganar yayin da yake kallon Muhdeen.
"Ai idan sune basasu yi mani irin abunda yarinyar nan tayi Mani ba ballantana har na d'auki irin wannan hukuncin akan su."
Girgiza kai Jabeer yayi tare da ce wa,
"Duk da bansan me tayi maka ba kuma nansan alak'ar dake tsakanin ku ba,amma da dukkan alamu yarinyar nan bata da rashin tarbiyya ko rashin kunya.Ni nasan halinka fa idan ka d'aurawa mutum karan tsana,wata kila ka kure ta ne shiyasa har takaiga tayi maka haka."
Don't tell me that,how dare you gaban yarinya kana gaya mun maganganu tare da bani laifi?salon ta k'ara raina ni ko?."
Ba tare da Jabeer ya sake wata magana ba ya durk'usa gaban Inteesar dake ta k'ok'arin mik'ar da hannayen ta amma ta kasa,har lokacin kuka take,cikin tausayawa ya kalleta ya ce,
"Sannu ko?"
Kai ta gyad'a masa alamun yauwa ba tare da ta yi magana ba.
"Cikin tausasawa ya ce,
"Me kikayi masa ne?"
Cikin muryar kuk ta fara magana.
"Nidai haka nan kawai ya tsaneni banyi masa laifin komai ba, shiyasa ma nace bazan sake zuwa gidan nan ba sai yayi aure yabar gidan su Mufida suka matsa nazo."
Cikin tausasawa ya girgiza kai.
"Kenan ke k'awar Mufida ce?"
Kai ta jinjina masa alamar eh,da ya ke shi Jabeer baisan Inteesar ba kasancewar duk lokacin da yake zuwa bayan sallar isaha'i ne,kuma lokacin Inteesar ta riga tabar gidan.
"To amma me kikazo yi a d'akin sa?"
"Shi ne ya janyoni wai nazo nayi masa gyaran falo"
Kai Jabeer ya jinjina.
"Okay.yanzun ki tashi ki tafi,sannan ina mai matuk'ar baki hak'uri a madadinsa"
Tashi ta yi dak'yar ta dafa hannayen ta mik'e tsaye, ta nufi hanyar fita ta fice Jabeer yabi ta da kallon tausayi.Gwaggo ne ke zaune a falo su day wasu Mata k'awayen Mummy su uku,ganin Inteesar ta fito daga part d'in Muhdeen idanunta sunyi ja alamun kuka yasa ta mik'e dakyar,ta nufi Inteesar ta ce,
"Subhanallahi 'yar albarka me ya same ki?me kikayi je yi d'akin Muhammadu?me yayi maki? "
Murmushin k'arfin hali tayi tare da ce wa,
"Bakomai Gwaggo kada ki damu"
Ta k'arasa maganar tana mai nufar k'ofar kitchen,bayan ta shiga kitchen d'in fridge ta nufa ta d'auko goran robar ruwa tare da tsiyayawa a kofi tasha.Sai da ta k'ara koge fuskar ta inda hawaye ya gangaro da bayan yatsunta sannan ta nufi da'akin Mufida.
Da sallama d'auke a bakinta ta shiga,kallo d'aya Mufida tayi mata da sauri ta mi'ke ta isa gare ta tare da dafa kafad'arta.
"Inteesar lafiya kuwa me ya same ki naga idon ki alamun kinsha kuke?"
Murmushin k'arfin hali tayi tana kallon Mufida ta ce,
"Kada ki damu kaina ne ke Mani ciwo yanzun zan d'an kwanta,idan na tashi zuwa anjima zai sake ni"
Azeeza ce ta ce.
Ikon Allah daga fitar ki zuwa kisha ruwa shiru baki dawo ba sai yanzun kika shigo kanki na ciwo.Dama kina kukan ciwo ne kamar k'aramar yarinya?"
Ta k'arasa maganar cikin yanyin zolaya.Azeema ce ta d'aura da ce wa.
Ni da