Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 149432 words

Chapter 7 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1398

Ads at the middle of Article

sa Mai masu kyau da kwarjini.


Durkusawa yayi cikin girmamawa ya gaida Umma.


"Ina wuni Umma?"


"Lapiya qalau"


Ta amsa masa cikin sakin fuska


'Dan Jim yayi Don ya gane cewa Umma Bata sanshiba yasa yace,


"Dama Inteesar ce bataji dad'i ba shine Mummy tace na na kawo ta nayi treating d'inta kafin su karaso"


Jin haka yasa Umma ta fahimci cewa shine Muhdeen din da ake fadi.nuna mata Inteesar da ta jingina da jikin motar yayi tare da cewa,


"Umma jiri takeji shiyasa nayi sallama Don azo a taimaka Mata"


Da sauri Umma ta karasa ta tallabota tare da had'a ta da jikin ta suka nufi cikin gidan.


Acikin d'akin Inteesar din ta kaita yayin da ta koma tare da bawa Muhdeen izinin shigowa.Har dakin tayi masa jagora hannun sa dauke da akwatin magunguna sai ledar fruit din da ya siya Mata.
Tana kwance akan katifar ta ya kalle ta tare da cewa


"Tashi zaune Kisha fruits din kafin nayi maki allura ,Kinga ba komai a cikinki da kikaci"


Shiru tayi masa tare da tura baki Tana kunkuni


.Umma CE to daka Mata tsawa Tana fadin


"Wai lapiyar ki Yana maki magana kinyi banza dashi ba taimakon ki zaiyi ba"


Hawaye ne ya cika Mata ido tace,


"Umaa kiyi hakuri indai taimako ne daga wurin say bana bukata ya tashi kawai ya tafi"


Umma shiru tayi ta zuba Mata idanu Don ita a tunanin ta allura ce bata so shiyasa take fad'in hakan.


Sake magana yayi a karo na biyu yace,


"Dakin daure kinci wani abun ko kadan ne*


Cikin tsiwar da Bata San Tana da ita ba ta Fara magana Tana fad'in


"Dalla mallam ka tashi ka dauki tarkacen ka bana bukatr ganin ka a rayuwa ta,ko a hanya bana fatan sake had'uwa da Kai.Kuma gidan KU bazan sake zuwa ba idan kaga kafata duk wulakancin da kaga dama kayi Mani Ni na jawowa kaina "


Shiru yayi ya zuba Mata ido Yana mamakin yadda har ta iya bud'e baki tayi masa magana gatsai haka...


Bai karasa tunani da yakeyi ba ya sake Jin murayar ta Tana cewa.


"Ka tashi ka fita bana kaunar ganin ka a rayuwa ta,na tsane ka irin tsanar da ba ta'ba yiwa 'Dan Adam shi ba.Ba zaka sake gani na a gidan KU ba ballantana..."


Bata Kai aya ba taji Umma ta daka Mata tsawa Wanda yasa Inteesar fashewa da kuka Tana fad'in


" Umma Don Allah ya fita wlh idan na kalleshi zuciyata tafasa takeyi"


Numfashi taja alamun maganar ma karfin hali
ne,sannan tace,


"Da ace Kaine likitan da zakayi Mani treatment na samu lapiya gara nayi ta zama da ciwo"


Ledan fruits din da ya siyo ta dauko ta watsa masa su a jikin sa.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*








Wannan kagaggen labari ne ban Rubuta shi Dan cin zarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.




*BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM*




Page1️⃣5️⃣




Ledan fruits d'in da ya siyo ta d'auko ta watsa masa su a jikin sa.


Umma da ranta ya gama 'baci ne ta fita waje,ba jimawa sai gata ta shigo da zabgegiyar bulala,ta nufi Inteesar da niyyar za ga Mata bulalar Amma cikin zafin nama Muhdeen ya shiga tsakani Yana ba wa Ummi hak'uri.


"Ka bar ni da ita yanzun nan taji a jikin ta"


Girgiza Kai Muhdeen yayi tare da cewa


"Kiyi Ha'kuri Umma zafin ciwo ne yasa haka"


"Ba wani zafin ciwo da zai sa ta haka?Bata cikin hayyacin ta ne?ka daina kokarin Kare ta "


Ta karasa maganar Tana jifa da bulalar ta fita d'akin ranta a 'bace,Don Bata taba tsammanin Inteesar za ta yi abunda tayi a yanzun ba.
Bayan fitar Ummin ne ya juyo ya kalle Inteesar cikin 'bacin Rai ya soma magana.


"Wace ce ke?me kike dashi ?me kike ta'kama dashi? Kyawu? Ilimi? Daraja?Dukiya ?ko me?"


Haka ya jera Mata wad'annan tambayoyin,ita Kam ko kallon sa ba ta yi ba zuciyar ta cike da fargabar hukuncin da zata d'auka akanta,Don rabon da ta ga irin wannan 'bacin ran a wurin Ummi har ta manta.
Muryar Muhdeen ce ta ji Yana cewa,


"Kalle ni da kyau ni Muhammad Muhdeen na fi karfin wulakanci wallahi,ke har kin Isa ki wulakantani ?ban da yi wa mahaifiya biyayya da ta umarceni nazo nan meye zai kawo ni wajenki. Wallahi kinci arzikin Mai daraja da na baki mamaki wallahi.


Bai sake magana ba Fara had'a Alluran da zai Mata yayi,Tana ganin haka ta Fara kuka ita wallahi Ba ta son Allura magani take so, dariyar mugunta yayi tare da cewa,


"Yauwa na ji dad'in sanin haka kasancewar kina masifar tsoron Allura ,da haka zan yi maganin ki"


Fashewa tayi da kuka Don A Rayuwarta Tana masifar Jin tsoron Allura fiye da komai,cikin muryar kuka da tsoro tace,


"Yaya Don Allah ka yi hakuri wallahi bana son kayi Mani Alluran Nan Don mutuwa zanyi kuma nikad'aice Umma na ta Haifa ka tausayawa Umma na kada ta rasa 'yar ta gudaliya"


Dariya ce ta so su'buce masa Amma sai ya Danne yace,


'karamar mara kunya ba Ni kika gamawa yiwa wula'kancin da Tunda nake a rayuwa ta Ba'a ta'ba yi Mani kwatankwacin sa ba,Don Haka dole na hukunta ki"


Fashewa tayi da kuka sosai Tana ihun Kiran Umma


"Umma ki zo za'a kashe maki 'yarki guda d'aya da Allah ya baki,Umma na kizo wallahi fansa yake da niyyar dauka akaina,Umma kinsan bana son Allura ballanta shi da biyu zaiyi Mani Alluran Nan"


Bai kalle ta ba ya ci gaba da abunda yake yi saida ya gama sannan ya kalle ta yace,


"Ki d'aga rigar ki sama"


Cikin muryar kuka tace,


"Wallahi bazan d'aga ba tunda baka da imani"


Tana fad'ar haka ta Mike cikin rashin 'karfin jiki ha jire dake d'ibarta ta nufi hanyar fita daga d'akin cikin jirin dake d'ibarta tayi luu zata fad'i Don ganin duhu takeyi,cikin zafin nama ya Karasa ya ri'keta da hannu d'aya,yayin da d'aya hannun yayi amfani dashi wajen soka Mata allurar ba tare ya d'aga rigar ba, yayi Mata Allurar.Gigitaccen Kara ta saki tare da sakar masa jiki taci gaba da ihu Tana Kiran Umma a haka ya yi Mata allurai biyu sannan ta kwanta Tana kuka kamar 'karamar yarinya son Sai ta ji zafin Alluran na daban ne,yasha Bambam da Wanda ta Saba ji.nan ya ajiye Mata magunguna ya Rubuta yadda za ta yi amfani dashi ya tattara kayan say ya fito daga d'akin,a tsakar gida ya samu Umma yayi Mata sallama tare da shaida mata gobe zai dawo.Bayan fitarsa Umma ta shiga ta samu Inteesar inda tayi Mata fad'a sosai akan abunda ta yi wa muhdeen,ita dai shiru tayi tare da bawa Umma hak'uri,fad'a ya sake Mata tare da nuna Mata cewa wannan mummunar d'abi'ar Bata son shi, Inteesar din kuwa hakuri kawai take bawa Umma tare Mata al'kawarin ba za ta sake ba.
Lalla'bata umma tayi ta d'aci Abinci kad'a kafin ta kwanta.


Muhdeen kuwa Koda ya 'karasa gida Bai samu sun Umma ba sun tafi gidan jabeer gaida matarsa Maryam da tayi rashin lafiya.
Wanka yayi ya canza Kaya cikin hanzari ya nufi gidan su Sumayya,Bayan yayi horn Mai gadi ya bud'e masa ne ya shige cikin gidan,
Yana zaune a motarsa ya Kira layin Sumayya Yana ta ringing Bata d'aga ba.


Sumayya kuwa Tana zaune a d'akin ta da tayi kaca-kaca dashi ta hargitsa sa gashin attached din da akayi Mata Kari ta barbaza shi kamar mahaukaciya sintiri takeyi a d'akin Tana ta suratai ita kad'ai,duk abunda ya tari gaban ta sai tayi jifa dashi gaba d'aya ta yay bedsheet din gadon tayi jifa dashi pillows din ma gaba d'aya tayi watsi dasu a cikin d'akin kayan makeup dinta duk tayi watsi dasu da turarruka,wad'anda suke cikin kwalabe kuwa duk sun farfashe suk abunda tayi tozali dashi sai ta hargitsa sa,hatta sidedrawer sai da ta d'auke sa tayi jifa dashi,
Dama ita haka take tun Tana yarinya Iyayenta basa tsawatar Mata sai abunda taga dama take yi basu Hana ta.indai ranta yayi masifar 'baci to duk abunda ya tari gabnta sai taga bayansa,hatta T.v dake kunne Yana aiki Tana kallon wani series a tashar zee word idon ta na sauka Kan T.V ta d'auki 'karfen da handbags dinta suke rataye gadan-gadan ta nufi wurin karfen Bayan ta dauki 'karfen Kai tsaye plasma T.Vn ta nufa ta Fara kwalawa T.V 'karfen har sai da taga seecreen d'in T.V ya ragargaje idonta ne suka sauka Kan dressing mirror jifa tayi da 'karfen ta nufi gaban mirror Hannunta tasa ta naushi mirror d'in take ya ragargaje Hannunta sai zubar da jini yake.


Mum d'inta dake ta bubbuga kofar Tana ro'konta ta bud'e dakin kada ta ji wa kanta ciwo Amma Ina Bata ma San tana yi ba,gashi Dad d'inta baya Nan ya tafi kasar Dubai,gaba d'aya mum hankalinta yakai 'kololuwar tashi gashi key din d'akin Sumayyar na jikin kofa ta cikin ballantana ta Nemo spare key ta bud'e


Muhdeen da ke cikin mota ya gaji da Kiran layin Sumayya Yana ta ringing Bata d'auka ba,dama wayar na falo ta bar shi lokacin da ta kirashi video call ta gansa tare Inteesar cikin motarsa a guje ta shige d'akin Tana kuka ta saka key karar fashe -fashe ne yasa Iya Ggaje Mai Mata gyaran d'aki ta nufi d'akin Mum ta sanar da ita cikin tashin hankali Mum ta karaso taji 'kofar a datse duk da sai an 'bata Mata Rai sosai take haka,Mum ta rasa gane meye ya Bata Mata Rai haka,
Idonta ne ya sauka Kan wayar Sumayya dake kawo haske alamun kira,karasawa tayi tare da d'aukar wayar tana subawa ganin Maaoyin 'yarta ne yasa ta d'aga tare da cewa,


"Hello"


Muhdeen Jin muryar Mum yasa yiyi saurin gaishe ta.


"Ina Wuni Mum"


Ajiyar zuciya ta sauke karin ta amsa masa


"Lapiya Qalau"


Ya cigaba da magana


"Mum lafiya Ina ta Kiran Sumayya Bata d'agawa?"


Ajiyar zuciya Mummy ta sauke kafin ta cigaba da magana


"Ba lafiya kam gata cikin d'aki ta rufe kanta Tana ta kuka da fashe-fashe"


Da sauri Muhdeen ya fito daga cikin Motar sa ko rufe murfin baiyi ba a guje ya nufi 'kofar falon


Sumayya dake ta sambatu Tana fad'in


"Ba zai yi ba 'karya ne wallahi Muhdeen nawa ne Ni kad'ai ba wata 'yar matsiyata da zata rabani da shi, Inteesar 'karya kike baki Isa ki ra'bi abunda nake so ba, Muhdeen nawa Ni kad'ai ne",


'kara fashewa tayi da kuka Tana fad'in


"Baby me yasa kayi Mani haka?dama da kake fad'a Mani cewar ka tsani Inteesar baka 'kaunar ganin ta 'karya ka fad'a mani?kai fa ka yi muna d'inki iri d'aya ni da kai kace mu saka yau mu tafi yawan sha'katawa mu sha Ice cream mu yi d'auki pictures,lokacin da ka d'ibar Mani har ya wuce bakazo ba na kiraka kawai sai na ganka da wannan yarinyar 'yar matsiyata zaune a gaban motar ka? Dai-dai lokacin da ya kama ta ace muna tare?Why? Why?zakayi Mani haka?"


Ta 'karasa maganar yayin da ta taka kwalbar turaren da ta fasa,


Jini hannayenta da 'kafafuwar ta ke zuba duk ta 'bata d'akin,Bata damu da jinin dake zuba a jikin ta ba kishi ya rufe Mata idanu.


Daga can falo knocking Muhdeen ya gaji dayi, Don Haka ya Fara dukan 'kofar da kafad'arsa bugu na uku kuwa sai ga kofar Bature ta fad'i 'kasa,Sumayya na tozali da Muhdeen ai ta Fara -waige -waige kwalbar turaren wuta na itace tayi tozali dashi Wanda Bai fashe ba,da sauri ta d'auka tare da saiti dai- goshin muhdeen ta seta kwalbar ta jefa masa a goshin sa.






*ZAKU IYA JINA SHIRU GOBE BAN YI MAKU POSTING BA BANI DA LAPIYA NE KUYI MANI ADDU'A DA BAKUNANKU MASU ALBARKA*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89






*INTEESAR*


Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89




*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi
( Maman Ihsan)




*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*




*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*




Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa.






*BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM*




Page1️⃣6️⃣




Kwalbar ta jefa masa a goshinsa, cikin zafin nama ya goce kwalabar ta daki bangon d'akin ta tarwatse, ganin yadda jini ke zuba a hannayenta da 'kafafuwarta ne ya d'aga hankalin Muhdeen da Mum d'inta, cikin sauri Mum ta karasa tana cewa,


"Haba Sumayya me aka yi maki da zafi haka da har zaki illata kanki?"


Cikin muryar kuka ta soma magana,


"Mum wallahi bazai yuwu ba babu maccen da ta isa ta mallaki abunda na mallaka, domin duk abunda na mallaka nawa ne ni kad'ai babu wacc..."


Mum ce tayi saurin katseta ta hanyar ce mata


"Wai akan wa kike magana ne?"


Muhdeen ne ya cewa Mum su kaita Asibiti ganin yadda jini ke fita daga jikinta, Sumayya sai hararar Muhdeen ta ke yi tare da cewa,


"Me ya kawo ka nan gidan? Ka koma can wajenta tunda ta fini mahimmanci a wurin ka"


Maganar da Sumayya tayi ne yasa Mum gane cewa fushin da Sumayya tayi yana da alaka da Muhdeen, ya yin da Muhdeen ya bud'e baki da niyyar magana ta d'aga masa hannunta dake tsiyayar da jini alamar ya dakata tace,


"Bana bukatar jin komai daga gareka, Get out of my room"


Takarasa maganar tana nuna masa 'kofar fita tana kokarin karasawa garesa da niyyar hankad'a sa waje cikin rashin sa'a ta saki wani gigitaccen 'karan azaba ya yin da tataka wani fasasshen kwalbar turaren da ta fasa, zama tayi a wajen ta kasa tafiya ganin hakan ne yasa Muhdeen ya kalli Mum tare da cewa,


"Mum kada a biye mata mu kaita Asibiti ne kawai, Jin hakan yasa Mum tace,


"Okay bari na d'auko mayafina"


Ta fita ta nufi d'akinta don d'aukar mayafin nata ya yin da Sumayya keta sambatu cikin muryar kuka tana fad'in


"Babu inda zan je ka tafi koma wajen wacce ta fini a wajenka meye damuwar ka dani Auren mu saura wata d'aya da sati uku amma ka barni ka tafi wajen wata banza ka manta dani ina ta zaman jiranka"


Muhdeen zuba Mata ido yayi Yana mamakin want irin mahaukacin kishi ne Sumayya take dashi,dahar zata illata kanta akan abunda bata da tabbas akansa zargi ne kawai,bud'e baki yayi tare da cewa'


"Duk abunda kike tunani ba haka bane,kinyi kuskuren fahimta ce da zakiyi hakurin saurara ta da nayi maki bayanin komai"


Dai-dai lokacin da Mum ta shigo d'akin Tana fad'in kada ya biye Mata su tafi kawai,hakan yasa ya d'auke ta kamar wata jaririya kasancewar Bata iya tafiya sakamakon kwalaben da suka shiga cikin 'kafar ta,sai ihu take Tana Kai masa suka a 'kirjin sa Tana fad'in ya ajiye ta Amma Ina baiko sauraren ta har sai da ya bud'e murfin gaban motar ya direta yayin da Mum ta shigo baya 'ko'karin bud'e murfin motar Sumayya tayi Amma Ina ya riga yayi locked din motar ba Halin ta fita horn yayi Mai gadi ya wangale masa 'kofar gate d'in ya fice a guce.


Iya Gaje Mai gyara masu d'aki ne ta shiga dakin Sumayya Don ta gyara 'barnar da tayi,itama tayi mamaki matu'ka 'barnar da tayi ta yau tafi ta kullum yawa ganin jinin dake malale akan tiles d'in d'akin ne yasa ta jinjina Kai tana ta magana ita kad'ai Tana cewa,


"Kai amma wannan yarinyar anya kanta d'aya kuwa? ace mutum ya dinga yin abu kamar na mahaukata? yarinya Sam bata da tarbiyya da sanin yakamata waye zai shigo d'akin nan yace mai hankali tayi wannan aikin? Tajawa iyayen ta asara,Koda yake su bazasu damu ba ai sun Saba da halin ta kuma su suka d'auka kome taga dama tayi dai-dai ne uwa Babu kwa'bawa uba Babu harara komai tayi sai dai a zuba Mata ido Ina Bata it's komai ba Ana Shirin aurar da ita wallahi Ina tausayawa mijin da zai aure ki."


'Bangaren su Gwaggo kuwa suna Isa 'kofar gidan jabeer kuwa Bayan direban yayi horn Mai gadin ya bu'de masa ya Cinna hancin motar cikin gidan, jabeer dake Shirin fita idonsa ne ya sauka akan kakar tasa mahifiyar Babansa da sauri ya Karasa ya bud'e Mata murfin motar yayi ta jefo kafa kafarta dakyar ta fito rungume ta yayi cikin farin cikin ganin ta yace,


"Uwar gida na sai yau kikaga damar zuwa gidan mijin naki har Ina Shirin zuwa biko"


"Dariya tayi Tana fad'in,


Ai ko kayi biko ba dawowa zanyi ba,Don tunda kayi Mani kishiya ka rage kula dani "


Karasawa yayi gurin Mummy ya gaishe ta cikin girmamawa,ta amsa masa cikin sakin fuska tare da tambayar sa ya Mai jiki,Mufida ma ta gaishe sa daganan suka karasa cikin gidan.


A falo suka zauna,shi kuma ya nufi bedroom d'in maryama a kwance ya same ta kamar yadda barta,ya sanar da ita zuwan su Mummy mi'kewa tayi cikin karfin hali Hannunta ya ri'keta suka nufi hanyar falon,Bayan sun Isa falon ganin idanun su Mummy yasa ta zame Hannunta daga nasa,ta karasa ta du'kusa ta gaishe su tare da zama akan center carpet din falon, Gwaggo Dada ce tace,


"Wannan kishiyar tawa da alamu cikin nan na wahalar dake ko? Uhmm koda yake gwara haka yanzun zaku San irin wahalar da iyayen KU suka Sha akanku ku Kara sanin darajar iyaye ai yanzun ma aka fara wasan"


Jabeer ne da ya 'karaso falon dauke da lemu da ruwa a cikin tray ya ajiye tare da duban Gwaggo yace,


"Waishin dubiya kikazoyi ko kuma kin zo kisamun mata a gaba da maganganun ki need?"


"Ai gaskiya na fad'a mata
Wanda zai hau sama ya taka leda ai baiyi komai ba tukunna, jibi fa yadda take langwa'bewa kamar an tsoma tsumma a cikin ruwa"


Dariya sukayi gaba d'ayan su banda Maryam data kwa'be fuska kamar za ta yi kuka, jabeer ya kalleta yace,


"Kada ki damu Gwaggo haka take da sannu zaki saba da ita"


Umma CE tace,


"Ya jiki Maryam"


Murmushi tayi tare da cewa,


"Da sau'ki Mummy"


"Allah ya 'kara sau'ki"


Cewar Mummy, fira suka d'an ta'ba kafin sukayi masu sallama, Jabir har wajen mota ya rakasu sai da suka fice sannan ya koma cikin gidan.


'Bangaren Muhdeen kuwa suna tafiya a Kan hanyrsu ta zuwa Asibiti Sumayya tayi-tayi ya dakatar da motar

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads