Showing 72001 words to 75000 words out of 149432 words
Chapter 25 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
ba,to Bari kiji abunda kike Kira iskanci shi aka kawo ki kiyi,nace iskanacin kika zo yi,kuma badi kiji wallahi indai baki fita a idona ba sai nayi maganinki,baki zuwa Islamiyya ne?ko kuma ba'a fad'a maki hakkin miji akan matarsa ba?"
"An fad'a Mana."
"Oho an ma fad'a maku kin sani amma kike take sani?ki gwammaci ki kwana cikin tsinuwar mala'ikun Allah?"
duk tunanin Gwaggo ta d'auka cewa Inteesar da Muhdeen suna mu'amalar auratayya ne gajiya da rashin sabo ya sa Inteesar gudowa ta barshi,don haka ta cigaba da cewa
"Haka Zaki dinga hak'uri da yanayin mijinki,a haka zaki saba kema ki zama jaruma irinsa ki daina gudowa nan kada nima tsinuwar taking ta shafe ni."
Ba tare da ta ce komai ba ta mik'e jin zancen Gwaggo ba na k'are bane, kuma gashi har an tayar da sallah a masallaci,bata tsaya yin wanka ba ta d'auro alwala ta fito,kallonta Gwaggo tayi ta ce,
"Banga kinyi wankan janaba ba,ana sallah da najasa ne?"
Inteesar dai shiru ta yi bata ce komai ba, k'ok'arin d'aukar hijabinta kawai take,sai jin muryar Gwaggo ta sake ji tana cewa
"To ko a can d'akin nasa kika yi wankan tsark?"
Nanma bata ce komai ba,har zata tada sallah sannan ta juyo ta kalli Gwaggo ta ce
"Gwaggo ki tashi fa kiyi sallah lokaci na tafiya."
Daga nan ta tada sallah yayin da Gwaggo ta shiga toilet don d'oro alwala.
Koda ya dawo daga masallaci d'akinsa ya koma ya kwanta ya cigaba da barcinsa.
Bayan Inteesar ta gama azkar da karatun al qur'ani kamar yadda ta saba fara gyaran gidan ta yi sai dai ba kamar na wahalar da Muhdeen ya dinga sata ba,yanzun idan ta gyara falo da d'akinta da toilet sai kitchen,sai kuma falon Sumayya da d'akin Muhdeen,bayan ta kammala gyara ko Ina ne ya rage d'akin Muhdeen,tana ta tsoro da zullumin shiga d'akin tuna abunda ya mata a daren jiya gabanta ne ya shiga fad'uwa tana tsoron shiga har ta kai hannu da zummar bad'e k'ofar sai ta fasa ta juya ta nufi kitchen dan d'aura masu breakfast,
Ruwan shayi ta dafa da yaji kayan k'amshi sai Dankalin turawa da plantain ta soya da k'wai,bayan ta kammala ne ta jera su dinning table sannan ta nufi d'akinta ba kowa a d'akin don Gwaggo ta dawo falo tana kallon T.V, magana ta dingayi a zuciyarta ita kad'ai tana cewa
"Sai dai yau d'akinsa ya zauna hakanan ba gyara, don bazan shiga d'akin ba idan yana ciki,salon ya je yayi mani fyad'e ya cuceni tunda ba k'aunata yake ba,gara idan naje na auri mai sona nakai masa budurcina amma bazan ta'ba bari wani mugu ya rabani da shi lokaci guda ba."
Haka ta yi ta surutanta ita kad'ai,wanka ta shiga bayan ta fito ne ta shafa man shawanta Mai k'amshi na wajen Hajiya Bilkisu mai gyaran Amare,riga da siket ta saka na atamfa ya zauna mata cif a jikinta inda ya k'ara bayyana kyakkyawar surar jikinta da kyawun dirinta.
Wani turare da bata ta'ba amfani da shi ba ta d'auko ta shafa son turaren yana da wani sirri na musamman shiyasa ma Hajiya Bilkisu ta sanar da ita cewa idan har zata fita daga gida kada ta shafa turarenta sai dai idan tana cikin gida ne,bayan ta shafa turaren ne ta fito ta zo falo inda ta tarar da Gwaggo,
"Barka da hutawa Gwaggo"
"Ke ni ba wani barka wallahi,haka gidan naku yake?"
"Me ya faru Gwaggo?"
"Tambayar me ya faru kike 'yar albarka ?meye ma bai faru ba?to Ni ban saba da haka ba,ace mutum bazai ci abinci sassafe ba sai k'arfe goma?so kike ki kashe ni da yunwa ko?to wallahi bazan iya ba matuk'ar haka zaki dinga yi to zan kira waya a turo direba ya d'auke ni,ko a gidan Fatima koda ba zata karya da wuri ba sassafe zata kawo mani nawa har d'aki,wata rana ma kece kike kawo mani,amma daga yin aurenki zaki koyi mugun hali na barin bak'o da yunwa to kika sake mani haka zan bar gidan nan."
Da sauri Inteesar ta durk'usa tana rok'on Gwaggo akan tayi hak'uri,kada ta tafi don idan ta tafi farin ciki ya k'are mata a gidan.
"Tuba nake Gwaggo ki gafarceni bazan sake ba insha Allah."
"To shikenan naji,yunwa nake ji kije d'akin mijinki ki Kira shi yazo muyi karin kumallo a tare."
Gabanta ne ya fad'i Jin abunda Gwaggo ta ke cewa,don haka ta ce
"Gwaggo kamar barci yake,mu barshi idan ya tashi sai ya ci nasa."
"A'a kedai kije ki Kira shi,kawai."
Ba yadda ta iya ranta baiso ba ta nufi d'akinsa,tura k'ofar ta yi tare da sallama,kwance ya ke kan gado idanunsa a lumshe kamar mai barci amma ba barcin yake ba,ganin kamar yana barci yasa ta k'araso d'akin cikin sand'a, waige-waige ta dingayi tana tunanin ina ya ajiye mata wayarta da amshe a hannunta.
Shi kuma tunda ta shigo k'amshin turaren Hajiya Bilkisu ya fara aiki,don turaren na musamman ne mai d'auke da wani sirri wanda idan mace ta shafa turaren namiji ya shak'a kamshinsa sai shauk'i ya kamashi,to kuwa tunda Muhdeen ya ji k'amshin turaren nan gaba d'aya ya rasa nutsuwarsa ji yake kamar ya rungumeta
Rasa ina ya aje wayar ta yi har ta nufi closet zata duba sai ta fasa duk yana kallonta, side drawer ta duba takaddu ne kawai zagayawa ta yi d'aya 'bangaren da ta janyo side drawer na jikin gado na sama kasancewar tayi kusa da shi sosai k'amshin turaren ya k'ara hautsina shi, sunkuyawar da tayi ne ya fincikota ta fad'o jikinsa,had'a ta yayi da k'irjinsa ya fara kissing nata ta ko ina,jikinsa sai rawa suke idanunsa sun fara janaza kala zuwa ja tun tana k'ok'arin k'watar kanta har ta kasa don abun nasa na yau yafi na jiya yamutse ta ya dingayi ta ko ina kuma son ransa a haka suka kwashe mintuna talatin,ganin yana neman wuce gona da iri ne kuma ta kasa k'watar kanta don bai bata wannan damar ba yasa ta sakar masa kuka,sakinta ta yi tare da maida numfashi,gashin kanta duk sun yamutse,d'an kwalinta ta d'auka ta nufi hanyar fita har ta kai bakin k'ofa ta tsaya ta goge hawayenta sannan ta jiyo ta kalleshi tare da harararsa ta ce
"Wallahi sai Allah ya saka mani abunda ka yi Mani."
Mi'kewa taga ya yi ta fita a guje,dariya ya yi tare da cewa
"matsoraciya ai da kin tsaya"
Fita shima ya yi don bai gaisa da Gwaggo ba.
Gwaggo na zaune a falo ta had'a tagumi daga cewa Inteesar ta kira Muhdeen shikenan ba ita ba shi fiye da rabin awa, Inteesar gaba d'aya kunya ce ta kamata ganin yadda duk kayan jikinta suka yamutse haka ma gashin kanta,ba yadda za'ayi ta shiga d'akinta ba tare da Gwaggo ta ganta ba,kuma ita gaskiya tana jin kunyar Gwaggo ta ganta a haka don sai ta zargi want abu, tsaye ta yi a jikin k'ofar da zata sada ta da falonta inda Gwaggon ta ke,ji ta yi kawai an rik'e hannunta ana janta zuwa falon,juyawa tayi da sauri ta kalle shi,kafin ta yi magana ne har ya janyota sun shigo falon,ido Gwaggo ta zuba masu daga shi har ita,kallo d'aya ta ma Inteesar ta fahimci komai don haka kauda kanta kawai ta yi kunya duk ya ishi Inteesar amma shikam ko a jikinsa,gaida Gwaggo ta yi tare da cewa
"Ina kwana Gwaggo?"
"Ina wuni zaka ce mani ba ina kwana ba,k'arfe nawa yanzun ku shige d'aki kaida matarka Kuna ta jarabarka a d'aki kun banzatar dani ko?kuma kafi kowa sanin cewa bana iya zama da yunwa ciwona zai tashi ko."
Kallon Gwaggon ya yi ya kalli Inteesar ya ce
"Gwaggo dama bakiyi breakfast ba?"
"Lokacin da na tura matarka ta kira mani kai bata fad'a maka ba?"
"A'a Gwaggo bata fad'a mani ba"
Kallon Inteesar Gwaggo ta yi tare da cewa
"To da na aike ki baki fad'a ba ko?kika rik'e shi a d'aki kika k'i fad'a masa ko?ke ga jarababbiya uwar son miji,kinje kinyi muk'us a d'aki kin samu abunda kike so ni yunwa ta kase ni ko?indai ke buk'atarki ta biya ni ko oho ko?'yar yarinya dake sai jaraba,to ba sai ki mani Kora da hali ba kinbarni da yunwa ba tafiya ta zanyi kuje can ku k'arata
*KUYI HAKURI DA WANNAN*
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, Idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page 4️⃣5️⃣
"'yar yarinya dake sai jaraba,to ba sai kin mani kora da hali kin barni da yunwa ba,tafiya ta zanyi kuje can ku k'arata."
Tsabar takaici yasa Inteesar sakin kuka ta fad'a jikin Gwaggo ta kasa magana sai kuka kawai take, rik'e ta Gwaggo tayi ta rungumeta tana cewa
"To me aka maki na kuka tsabar sangarta ne ko kuma me?dan na fad'i gaskiya shine zaki saka ni gaba kina mani kuka haba 'yar albarka me kuma zaki zauna kina ma kuka?ya isa hakanan."
Ta k'arasa maganar tana shafa bayanta alamaun rarrashi.
"Bana son kukanki wallahi ki daina mana kada ki tayar mani da gankali."
'Dagowa ta yi tare da goge hawayenta ta ce,
"To kada ki tafi ki zauna da ni,idan kika tafi nima bazan zauna a gidan nan ba."
Kallonta kawai Gwaggo ta yi tare janyeta daga jikinta,ta shi tayi ta janyo hannun Inteesar ta mik'ar da ita tsaye.
"Taso muje mu ci abinci."
Binta ta yi ba tare da ta ce komai ba,shima bayansu ya bi yana kallon ikon Allah daga magana sai kuka.
Kwanci ta shi ba a wurin Allah,a haka har Gwaggo ta cika sati biyu a cikin gidan,kullun tana mak'ale jikin Gwaggo,shi kuma Muhdeen na zuwa Asibiti idan ya tafi da safe sai yamma ya ke dawowa,wani lokacin yakan je gidansu ya gaida Mummy da Dady,Mufida ma ta zo da k'awayensu Saliha da wasila sunzo gidan Inteesar,har ya wannan lokacin Muhdeen bai ba Inteesar wayarta ta ba.
Kwance take a saman cinyar Gwaggo suna fira, Mufida ce ta shigo.
"Assalamu alaikum"
Mi'kewa Inteesar ta yi da fara'arta ta rungume Mufida, Mufida ce ta gaida Gwaggo sannan ta juya ta kalli Inteesar ta ce,
"Wai me ya samu wayarki ne?"
Ta'be baki Inteesar ta yi tare da cewa
"Ba abunda ya same ta"
"Mummy na ta kiranki bata shiga, the same thing."
"Waya ta tana wajen yaya."
Kallon mamaki tayi Mata
"Me wayarki yake yi a wajensa?"
"Kar'bewa yayi wai bazai bani ba."
"Me ya faru haka da zafi da zai kar'be maki waya?"
Shiru Inteesar tayi tana nazari don bata jin zata iya sanar da kowa halin zaman da suke yi da Muhdeen,duk da cewar Mufida k'awarta ce amma ai kuma k'anwa ce a gurin Muhdeen,don haka ta ce,
"Mubaar maganar kawai"
"Me kuma kike 'boye mani Inteesar?mufa aminan juna ne bana 'boye maki komai kema baki 'boye mani,amma tunda kika yi aure kika fara mani 'boye-'boye."
Dariya ta yi tare da kallon Mufida.
"To ai kema kinsani akwai Banbanci tsakanin matar aure da wacce ba matar aure,kuma ai duk mace ta gari bata fitar da sirrin gidanta."
Ta'be baki Mufida ta yi tare da cewa
"To mace ta gari,idan miji na gari na ciki kije ki sanar da shi Mahaifiyar k'awarki Wasila ta rasu."
Dafe k'irji Inteesar tayi tare de cewa
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,Yaushe ta rasu?"
"Jiya"
Salatin Inteesar ne yasa hankalin Gwaggo ta dawo gare su,don ta yi nisa waje kallon T.V
"Allah sarki Allah ya jik'anta da rahama."
Gaba d'ayansu suka amsa, Mufida ce ta kalli Gwaggo ta ce
"Dama can gidan rasuwar zanje,na kira Inteesar a waya na sanar da ita amma ban same ta ba,shine na ce bari na biyo ko zata samu zuwa."
Kallonta Gwaggo tayi tare da cewa
"Gashi mijinki baya gidan bare ki nemi izininsa ki bita ku tafi."
Marairaice fuska tayi
"Gwaggo ki barni na tafi idan ya dawo sai a sanar dashi."
Girgiza kai Gwaggo tayi tare da cewa
"Ba nice na ajiye ki ba,ba kuma zama na kike ba,saboda haka ki kirashi a waya ki nemi izininsa,idan ya amince sai ku tafi."
Shiru Inteesar ta yi tana tunanin ta ina ma zata fara,dan ita ko kashe ta ma za'ayi bata san lamabar wayarsa ba,Mufida ce ta ce,
"Yauwa bari na kira maki shi da waya ta,idan ya barki sai muntafi."
Murmushi kawai ta yi a zuciyarta tana addu'ar Allah yasa ya amince ya barta.
Mufida ce ta lalubo lambar wayarsa ta kira amma switch off,sau biyar Mufida na kiransa amma the same thing,kallon Inteesar ta yi tare da cewa
"Duka lombobinsa fa a kashe,basa shika Wallahi."
Dafe kai Inteesar ta yi tare da cewa
"To yanzun meye mafita?"
"Bari to na gwada kiran layin yaya Jabeer nasan dukkansu yanzun suna Asibiti dukkansu."
Lamabar Jabeer ta lalubo ta danna masa kira.
Jabeer dake zaune a office d'insa yana duba patient,wayarsa ce take ruri bai kula ba har ta katse,sai da aka sake kira ne ya d'aga tare da cewa
"Mufida ya akayi ne ya mutanen gidan?"
"Yaya Jabeer dama layin yaya Muhdeen ne a kashe,kuma Inteesar ke son magana da shi."
"Okay lafiya dai ko?don ya shiga tiyata ne yanzu."
Kai ta jinjina
" Okya ba damuwa Allah ya bada sa'ar aiki,idan ya fito ka sanar da shi."
"Insha Allah zan sanar da shi."
Daga nan ya katse kiran ya cigaba da abinda ya keyi.
Bayan sun gama magana ne Mufida ta juya ta kalli Inteesar ta ce,
"Gaskiya zan tafi,don mijinki yana d'akin tiyata ,idan ya fito na ce yaya Jabeer ya sanar dashi kinga may be ya kira lambar Gwaggo ya ji dalilin kiransa,yanzun kinsan wayar Gwaggo kinsan bata ajiye waya fili sai cikin kaya ayi ta kira bata sani ba,kinga idan ya Kira sai ki sanar dashi idan ya barki kindai san gidan sai mu had'u a can, amma fa ba dad'ewa zanyi ba zan tafi kitso."
Daga nan ta mik'e tare da musu sallama ta tafi.
Baya awa biyu ne sai ga wayar Gwaggo ta fara ringing,dubawa tayi tare da d'aga kaiwa a kunne.
"Assalamu Alaikum"
Muhdeen da ke zaune a office d'insa ya fara magana
"Barka da gida Gwaggo."
Washe baki tayi tare da cewa
"Muhammadu ya aiki?"
"Alhamdulillah,naji ance kuna nema na ne."
"Eh matarka ce wai mahaifiyar k'awarta Allah ya mata rasuwa,shine Mufida ta biyo mata su tafi tare."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Allah ya jik'anta,ina ita Mufida take?"
"A'a itakam Mufida kam ina zata tsaya jiran matarka,kai da aka ce kana can kana farke cikin cikin mutane ne zata tsaya jiranta?"
"Mufida ta tafi kenan?"
"Eh sai dai ita matar taka ce ake jiran ka fito ka bata izini ta tafi."
"To ban bada izinin ba."
"Ban gane baka bata izini ba,gaisuwar mutuwa ce fa zata."
"Gwaggo ta tsaya tayi masu addu'a a gida,ita k'awar kuma ta kira ta a waya tayi mata ta'aziyya."
Girgiza kai Gwaggo tayi kamar yana ganinta ta ce,
"Haba Muhammadu, Mahaifiyar k'awarta aka ce ta rasu,kuma k'awa ce ta sosai ko lokacin bikinku ta yi k'ok'ari har nan gidan ma ta zo sannan sai ka hanata zuwa?bai kamata ba."
Shiru yayi na d'an lokaci kafin ya ce
"Shikenan ta sanar da Ishaq Direba ya kaita tayi ta'aziyya ya dawo da ita."
"Yauwa da'n albarka,Allah ya dawo mani da Kai lafiya."
"Ameen ya Allah"
Daga nan ta katse kiran ta kalli Inteesar ta ce
"Ina fatan kinji duk maganar da mukayi."
Kai ta jinjina lamar eh,sannan ta ce
"Nagode Gwaggo bari na d'auko hijabi na na kira Ishaq mu tafi."
"Amma fa kar ki dad'e"
"Insha Allah Gwaggo bazan dad'e ba."
Daga nan ta shiga d'akinta,ba jimawa ta fito rik'e da hijabinta tana sakawa,ta rik'e handbag d'inta ta fice.
A harabar gidan da k'ara ta ke tambayar mai gadi ko ina Ishaq,inda mai gadin ya shaida mata cewa yanzun nan aka kirasa a waya 'yarsa ba lafiya shine ya tafi gidan
Jin hakan yasa ta ce da mai gadin Allah ya bata lafiya,daga nan ta fita zuwa bakin titi ta tsaida mai keke napep ta shiga zuwa gidansu wasila.
Har k'ofar gidansu Wasila mai adaidata sahun ya ajiye ta,bayan ta shiga ne ta gaida mutanen sa ke cikin gidan tayi masu ta'aziya sannan ta nufi falon gidan nan ma cike yake da mata masu kar'bar gaisuwa,bayan ta gaishe su tare da masu ta'aziyya ne ta nufi d'akin Wasila,nan ta samu K'awayensu wad'anda suka gama school tare dasu a d'akin,nan dai suka gaisa ta tayiwa Wasila ta'aziyya da addu'o'i,zama tayi suka cigaba da kar'bar gaisuwa.
Suna nan har aka kira sallar la'asar,nan wasu suka dinga tashi dan gabatar da sallah,dama koda Inteesar bata ga Mufida a gidan ba batayi mamaki ba dan dama Mufida ta ce ba zata dad'e ba zata tari wajen kitso ne.
Bayan ta idar da sallah ne tayi masu sallama dan tafiya gida, kasancewar akwai d'an tazara zuwa bakin titi yasa ta fara tafiya dan neman abun hawa.
Wata jar mota ce ta tsaya a gabanta tare da yi mata horn,ko kallon motar ba tayi ba ballantana tasa waye a ciki,tafiya ta cigaba da yi shima matuk'in motar ya dinga binta a hankali yana danna horn,ganin abin nasa ne taga yayi yawa yasa ta juya ta kalli motar,ba kowa bane illa Usman sai murmushi ya ke sakar mata,da mamaki ta kalle shi tare da furta sunansa
"Usman"
Zaune yake a mazaunin Direba yayin da k'anwasa Khadija ke zaune a gefensa,itama murmushi ta sakarwa Inteesar tare da cewa
"Lallai yaya na yayi gaskiya,muna cikin tafiya ya hangoki ya ke sanar dani cewa kece nace ya za'ayi ya sani tunda baiga fuskarki ba?ya ce to bari mu k'arasa na tabbatar,ashe kuwa kece."
Murmushi Inteesar ta sakar mata tare da cewa
"Nice Khadija da ace ba tare da Usman na ganki ba wallahi bazan gane ki ba."
"Saboda kinsan had'uwa ta dake lokacin da na samu accident ne ina asibiti,tun lokacin bamu sake had'uwa ba."
"Ni kuma duk inda na ganki zan gane ki,saboda pics d'inki da ke wayar yaya na."
Da mamaki Inteesar ta kalli Usma
"Ina ka samu pics d'ina awai wad'anda na d'auke ki a asibiti ba tare da saninki ba da wad'anda na d'auke ki a k'ofar gidanku ranar da na je akan magani zan Kai maki."
Jinjina kai Inteesar ta yi ba tare da ta ce komai ba,jin muryarsa ta yi yana cewa
"Daga ina zuwa Ina?"
"Daga gidan rasuwa zuwa gida"
"To ki shigo nan gaba kad'an zan aje Khadija sai