Showing 42001 words to 45000 words out of 149432 words
Chapter 15 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
kai nawa ne ni kad'ai.Idan mafarki nake ya kamata na farka daga wannan mummunar mafarkin da bazai ta'ba faruwa ba."
Ta k'arasa maganar tana marin fuskarta tana alamun ta farka daga mafarkin da take,cikin muryar kuka ta cigaba da magana ta ce,
"Wake up Sumayya ki farka daga mummunar mafarkin da kike, Muhdeen naki ne ke kad'ai har abada ba wace maccen da zata ra'bi abunda kike so.Na San mafarkine Muhdeen bazai iya Maki kishiya ba ya Riga da ya d'aukar maki alk'awarin hakan."
Tana maganar kamar da wata takeyi ba akan kanta ba. Idanunta da suka canza kala suka koma jazir ta zuba masa su ta ce,
"Dan Allah ka sanar dani cewa mafarki nake ba gaskiya bane,sati biyu kenan da aurenmu ba yadda za'ayi kayi Mani kishiya wallahi zuciyata bazata iya jurewa ba."
Ta k'arasa maganar tana mai k'ara sautin kukanta,hannunsa ta rik'e tana cewa
"Please talk to me,mafarki nakeyi ba gaskiya bane ko?"
Cikin tsananin tausayinta da yakeji ya janyota ya rungumeta ya fara magana
"Sumayya ke musulma ce kinyi imani da Allah kin yarda da manzonsa,ina son kiyi tawakkali ga Allah mutum bai Isa ya gujewa k'addararsa duk abin..."
Kafin yakai k'arshen maganar da zai fad'a ya daka masa
"Ya Isa!"
Da mamaki yake kallonta yadda take d'aga masa murya
"Amsa d'aya nake buk'ata daga gareka,an d'aura maka aure ko ba'a d'aura ba?"
Cikin fargabar abunda zai biyo baya ya ce,
"Eh"
Take taji wani k'ululun abu ya tokare mata a k'ahon zuciyarta na bak'in ciki wanda tsawon rayuwarta bata ta'ba shiga bak'in ciki irin na yauba.A guje ta fita daga da'akinsa ta nufi d'akinta ta saka key ta rufe.
'Bangaren Inteesar kuwa duk Bata san abunda ke faruwa ba,kasancewar ranar juma'a ne ba Islamiyya hakan yasa tana idar da sallar Azahar ta d'auki Al-qurani tana karantawa,suratul kahfi take karantawa gashi tun safe take jin gabanta na fad'uwa,hakan yasa a zuciyarta da dinga nanata inalillahi wa'inna ilaihir raji'un.
Abba da Umma ne zaune a tsakar gida,Umma ta rafka uban tagumi cikin damuwa da take ciki ta fara magana.
"Yanzun Mallam ni na rasa dalilin da yasa ka amincwa wad'annan mutanen akan auren Inteesar,wani irin lamari ne wannan lokaci guda azo neman aurenta kuma a kokaci guda a bayar da aurenta sai kace wata kaza.Kuma bamu tuntu'beta ba munji tana son sa ko ba ta son sa shin shima yana son ta?gaskiya ni Ina jin tsoron abunda zaije ya dawo dangane da wannan auren da za'a zo lokaci guda a nema kuma mu bayar ba tare da munyi bincike akai ba kamar muna neman Kai da 'yar mu?"
"Kinga duk wannan maganar ki barshi kawai,aure ne dai an riga da an d'aura shi abu d'aya ne ke mani yawo a cikin k'wak'walwarta shine angon da aka d'aura aurensa sati biyu da ya wuce Mai zaisa ya sake wani auren yanzu?"naga alamun 'bacin rai a idanun Gwaggo lokacin da ta zo neman auren Inteesar,sai dai fargaba na d'aya shine ban sani ba ko shi yaron da aka d'aurawa 'yata aure dashi yana son ta?ban damu akan cewa Inteesar tana son sa ko Bata son sa ba saboda nasan tarbiyar da nayiwa 'yata da kuma biyayyarta a gareni,nasan ko bata son sa zata zauna dashi tayi masa biyayya don nasan 'yata mai biyayya ce kuma tana gudun ta aukata abunda zaisa ta fad'a cikin fushin Allah.Tsoro na d'aya shine idan ya kasance shi baya son ta ya k'untatawa rayuwar ta,wannan shine kad'ai abunda nake fargaba kin gane ko?"
Ya k'arasa maganar idonsa nakan Umma,Kai ta jinjina masa alamar gamsuwa da bayaninsa.
"Bugu da k'ari ba abunda Family d'in Alh.Sani zasu nema a waje na a ce na kasa yi masu shi ko meye shi matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba.Mutanen arziki ne kowa yana yabonsu a unguwar nan kema kanki shaida ce akan k'ok'ari da k'aunar da suke nunawa 'yar taki,Addu'a kawai zamu bita da shi Allah yasa shine mafi alkhairi a rayuwarta.
Umma ta amsa da
"Ameen"
Gidan Muhdeen kuwa tunda Sumayya ta shige d'akinta ta murza key ta rufe sai suratai take kamar wata mahaukaciya.kayan kwallalliyar da suke jere a gaban dressing mirror ne ta Fara wargazawa tana d'aukar su d'aya bayan d'aya tan jifa dasu masu fashewa na fashewa kallon kanta tayi ta cikin mirror d'in hannu ta dunk'ule ta kaiwa mirror naushi take mirrorn ya tarwatse idonta takai ga T.v dake mak'ale a bango a guje ta k'arasa gaban T.v zaro shi tayi ta bugashi a Kan tiles d'in d'akin ya fashe haka komai dake d'akin ta shiga illata shi, hatta pillows da bedsheet sai da ta yi ta cilli dasu durowar kayanta ta bud'e ta dinga d'ebo kayan tana cillosu waje, a k'asa haka ta dingayi bayan ta gama zuar da kayan ta dinga binsu d'aya bayan d'aya ta yayyagasu ko wanne sai ta rabashi gida biyu sannan tayi cilli dashi gefe wad'anda taji sunyi Mata k'arfi a hannu sai ta saka hak'ori tayi masu hanya sannan ta k'arasa yagawa.bayan ta gama ne ta bud'e 'bangaren da akwatunan kayan lefenta suke,nan ma ta zuzzuge zif d'in akwatunan haka ta dinga wurgi da kayayyakin abubuwan fashewa na fashewa wad'anda ba na fashewa ba kuwa ta tattaka su.
'Bangaren Muhdeen kuwa tunda Sumayya ta fita daga d'akinsa ya zauna a bakin gadon gaba d'aya ya rasa mai ke damunsa.don yasan ko yabi Sumayya Dan ya rarrasheta ba sauraransa zatayi ba,hakan yasa ya d'an barta tukunna.Ya rasa me yasa Gwaggo zata yi masa haka zata sa ayi masa aure ba tare da amincewarsa ba,sannan ta rasa wacce zata say aura masa sai Inteesar yarinyar da ya tsana a rayuwar sa ita ce aka aura masa?lallai kuwa Inteesar ta tabka babban kuskure da ta yadda da wannan auren,Don wallahi sai ta d'and'ani kud'arta,daga ranar da ta shigo cikin gidan nan a matsayin matarsa daga ranar zata zatayi ban kwana da farin ciki.Yana cikin zancen zucin nasa ne yaji wani irin k'ara na tarwatsewar abu,cikin tashin hankali ya fito daga cikin d'akinsa ya nufi d'akin Sumayya.
Daga cikin d'akin Sumayya kuwa show glass d'in da aka jera Mata turararruka ne da su kwalaben humra da turararen wuta,lokacin da idonta ya sauka akan show glass d'inne ta nufesa tana k'arasawa ta d'auki k'arfen da da ke ajiye na rataya jakunkuna ,tana d'aukar k'arfen ne ta bugawa show glass ya tarwatse,k'arar show glass d'inne yaja hankalin Muhdeen ya nufo d'akin nata cikin tashin hankali.
Yana tura k'ofar yaji a datse ya shiga buga k'ofar Yana Kiran sunanta Amma Ina Bata ma San tanayi ba sai buge-buge da jefe-jefe takeyi tana Sam batu tayi nan tayi can duk abunda ya tari gabanta jifa dashi take,komai na d'akin ta gama hargiza wa ta fargasa duk abunda ya kasance na fashewa abu biyu ne a d'akin Wanda suke zaune a muhallinsu, durowar zuba kayanta sai gado suma don ba zata iya d'aukarsu bane hatta katifa tayi jifa dashi gefe.
Muhdeen ne koma d'akinsa ya d'auko key yazo ya bud'e k'ofar,ganinta ya yi kamar mahaukaciya duk ta fita hayyacinta ga hannayenta da taji ciwo.Suna had'a ido dashi ta d'aga masa hannu ta ce,
"out of my side"
Cikin tashin hankali ya ce,
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Duk'awa tayi ta d'auki wani dogon fasasshen gilashi ta d'aga ta saita shi dai-dai saitin cikinta cikin d'aga murya ta ce,
"Kafita!"
Had'a hannayensa yayi alamar rok'o ya Fara magana
"Dan Allah ki tsaya ki saurareni,wallahi bada amincewa ta aka d'aura Mani aure da Inteesar ba."
Zaro ido tayi cikin cikin mamaki ta ce,
"Inteesar ka aura?"
Girgiza Kai tayi tana fad'in
"I said out, wallahi idan baka fita ba zan kashe kaina!"
Ta fad'i maganar tana saita tsinin kwalbar a cikinta.
Daga alk'alamin✍️
Maman Ihsan
09065327995
Love u oll😘😍
*MAULUD MUBARAK*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa.
Page3️⃣0️⃣
"I said out,wallahi idan baka fita ba zan kashe kaina!"
Ta fad'i maganar tana saita tsinin kwalbar a cikinta.
Ganin kamar da gaske take yasa ya fita falo gaba d'aya ya rasa me zaiyi.
Wauarsa ya ciro daga cikin aljihu, number Jabeer ya lalubo ya danna masa Kira,bayan Jabeer ya d'aga wayar ne muhdeen ya fara magana yana cewa
"Jabeer don Allah duk abunda kake ka ajiye shi kazo gidana yanzun nan."
bai jira cewarsa ba ya kashe kiran.Safa da marwa yake yana zaman jiran Jabeer.
Jin sallamar Jabeer ne yasa shi sakin ajiyar zuciya,k'arasowa yayi ya rik'e hannun Jabeer ya ce,
"Jabir ina cikin tashin"
Kallonsa Jabeer yayi cikin rashin fahimtar inda zancensa ya dosa ya fara magat
"Wai meke faruwa ne ne?"
"Ai komai ma ya faru"
"Kayi mani bayanin da zan gane inda zancenka ya dosa,ka kirani a waya kana cewa wai da sanina akayi maka aure wani irin aure kuma? dan Allah ka fitar dani haske domin kwata-kwata ban gane inda zancenka ya dosa ba."
Cikin 'bacin ran yanayin da ya ke ciki ya fara magana
"Jabeer aure suka k'ara yi mani,sati biyu da auren mu da my Sumy suka k'ara mani aure,jiya ana idar da sallar juma'a ne aka d'aura aure ba tare da sun nemi izini na ba kawai umarni suka bani inaji Ina gani aka d'aura auren.Jabeer wallahi bana son auren nan ba yadda zanyi ne."
Shiru Jabeer yayi yana nazarin maganar shikam baiji takaicin wannan auren da aka d'aurawa Muhdeen ba,don yasan cewa iyayen nasau sun lura da rashin tarbiyar Sumayya ce shiyasa aka nema masa masa wata matar.A cikin zuciyarsa yaji dad'in zancen don dama ba yadda baiyi dashi ba akan kada ya auri Sumayya amma soyayyarta ta riga da ta rufe masa ido ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Wace ce matar da aka aura maka?"
Cikin takaici ya fad'i sunanta
"INTEESAR"
Gaban Jabeer ya fad'i Jin sunan Inteesar,take yaji wani Abu zuciyarsa har sai da wayar hannunsa ta su'buce masa ta fad'i k'asa.Sunanta ya ambata da k'arfi
"INTEESAR?"
Kai Muhdeen ya jinjina masa alamar eh
Shiru yayi na d'an lokaci kafin ya saki murmushi ya ce,
"Indai Inteesar ce na Taya ka murna samunta a matsayin mata,duk da na fahimci baka son aurenta amma Ina da yak'inin cewa zuwa gaba zakayi alfahari da ita."
Tsuki Muhdeen yayi
"Allah ya kiyaye kaima fa na lura da cewa a 'bangaren su Gwaggo kake."
Gajeren murmushi Jabeer yayi tare da cewa
"Ba zaka gane gata akayi maka ba sai nan gaba."
"Ba wani gata ni ba wannan yasa na kiraka ba,tunda my Sumy taji Ina fad'a maka zancen auren Inteesar har suma tayi Kai a rak'aice dai gata can a d'aki dai fashe-fashe takeyi."
Da mamaki Jabeer ya saki baki yana kallonsa
"Yanzu tana ina Wai?"
Tana d'akinta Kai tsaye suka nufi d'akin,k'wank'wasawa suka dingayi suna bata baki amma ina bata saurare su ba.Haka suka hak'ura inda Jabeer ya nuna masa cewa ya barta zuwa anjima idan ta d'an sauko sai suyi magana.
Daga haka ne Muhdeen yaja Jabeer zuwa d'akinsa inda Muhdeen ya shiga bathroom room don yin wanka inda yabar Jabeer zaune saman sofa yana jiransa.
Daga can d'akin Sumayyay kuwa tunda ta gaji taga bazata iya cigaba da yayyaga kayan ba.Hakan yasa sauran akwatunan kayan lefen auren ta dinga jansu tana kaiwa harabar gidan tana jibgesu,a haka har ta gama jidar kayan lefen auren bayan ta gama jibgasu waje guda ne ta d'aga kai ta hango Mai gadin gidan tare da Zayyanu Direban gidan suna kallonta,harara ta watsa masu tare da yi wa Zayyanu Direban alamun yazo manuniya,gabasa ne ya fad'i ganin ta kirasa don kallon mahaukaciya sukayi mata ganin yadda takeyi tsoro da fargaba ya hana Zayyanu k'arasawa wajenta sai da mai gadin yayi masa da alamar yaje,cikin tsoro ya k'arasa wajenta.magana tayi masa a kausashe ta ce,
"Kaje ka kawo mani fetur yanzun nan."
Da mamaki ya tsaya yana kallonta,
Tsawar da ta daka masa ne yasa yaba r wajen cikin rawar jiki,ba jimawa sai gashi ya dawo da fetur a cikin galan,amsa tayi tare da ce masa ya kawo mata ashana.k'arasawa yayi wajen mai gadin gidan ya amso mata ashana ya kawo mata.
Ga mamakinsu gani sukayi ta bud'e robar fetur d'in ta tsiyaya shi duka a jikin akwatunan kayan lefenta,sanan ta kyasta ashana ta jefa kai tsaye cikin gidan ta koma.
Jabeer dake zaune saman sofa ne ya hango bak'i ta jikin gilashin windows, mi'kewa yayi tare da d'an zuge gilashin window d'in,ganin hayak'in da ya turnik'e gidan ne yasa shi sakin salati dai-dai lokacin da Muhdeen ya fito daga wanka ganin hakan yasa cikin sauri ya saka Jallabiya suka nufi hanyar fita,don sun d'auka gobara ce.
Suna nufar inda suka ga hayak'in na tasowa turus suka tsaya ganin akwatuna da da kaya suna ci da wuta.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Kalmar da Muhdeen ya furta kenan.Jabir ya kalleshi tare da cewa
" ta yaya kuma me hakan yake nufi?"
Ajiyar zuciya Muhdeen ya sauke tare da cewa
"Sumayya ce ta k'ona kayan lefenta "
Cikin mamaki Jabeer ya ce,
"Kana nufin kayan lefen da kuka je Dubai kuka siyo da akwatunan sune ta bankawa wuta?"
Kai Muhdeen ya jinjina masa alamun eh.
"Tirk'ashi
Shine kalmar da Jabeer ya fad'a,sannan ya d'ora da cewa
"Gaskiya duk yadda nake tunananin Sumayya lamarinta ya wuce haka,ta wuce sanin tunanina.wannan ai hauka ne da rashin sanin darajar dukiya.kayan miliyoyin kud'in ne zata bankawa wuta?saboda mahaukacin kishi?
Zuba masa ido Muhdeen yayi,kafin ya d'aura da cewa
"Haka take duk lokacin da aka 'bata mata rai sai tayi asarar duk abunda ya tari gabanta,amma ban ta'ba tunananin cewa zata iya k'ona kayayyakin lefen nen ba,amma hakan Bai rasa nasaba da cewar kishi ne yasa ta k'ona kayan lefen nata."
"Muhdeen zan baka shawara guda d'aya,shawarar kuma ita ce kada ka ajiye Inteesar a cikin gidannan,don idan har ka had'asu gida guda wata rana wannan mahaukaciyar matar taka zata iya kashe Inteesar ko ma ta illata ta,mafita d'aya ce shine ka raba masu gida,ka Kai Inteesar wancan gidan naka."
Wani kallon irin Wanda ke nuna alamar bazaiyuba muhdeen ya watsawa Jabeer.
"Wani gidan ne zan Kai ta? gidan da na gina da sunan Sumayyata ne zan d'auki waccan kucakar yarinyar na ajiye a ciki?."
Da mamaki Jabeer ke binsa da ido jin kalamansa
"Kamar ya?me kakae nufi ne?"
"Kai nifa wallahi ka daina mani maganar yarinyar nan ba itace a gaba na ba,aure dai an d'aura ko to shikenan tunda haka suka so,amma bazan ta'ba kallon wannan kucakar yarinyar a matsayin mata ba.Yanzun kawai ka sanar dani yadda za'ayi na shawo kan Sumayya."
Tsaki Jabeer yayi cikin jin takaicin maganganun da Muhdeen ya fad'a sannan ya ce,
"Wannan matsalarka ce ni inada abunyi,nabar aiki a asibiti sakamakon kiranka so zan koma patient na jira na,kaima ka shirya dawowa bakin aiki don ayyuka sun mani yawa."
Yana Kai K'arshen zancensa sai ya nufi motarsa ya shige,horn yayi Mai gadi ya bud'e masa ya fice yabar muhdeen yana mamakin me yasa duk 'yan uwansa suka juya masa baya akan Sumayya.
Wayarsa ce tayi k'ara sunan Mummy ce ya bayyana a kan fuskar wayar,bayan ya d'aga kiran ne ta shaida masa cewa tana buk'atar ganinsa yanzun a gida.Daga nan ta katse wayar shi kuma ya shiga ciki d'akin Sumayya ya nufa still a kulle k'ofar take hakan yasa ya nufi bedroom d'insa key d'in motarsa ya d'auka ya nufi gidan iyayensa.
Koda ya ya isa gidan horn yayi mai gadin gidan ya lek'o ganin motar Muhdeen ne yasa cikin azama ya bud'e masa gate,bayan yayi parking ya fito ne ma'aikatan gidan suka dinga gaishesa amma ko kallonsu baiyi ba hannu kawai ya d'aga masu don ransa yakai k'ololuwa wajen 'baci.
Gwaggo ce da Mummy a falon suna tattaunawa sai Mufida dake zaune kan center carpet,don Mufida ma Bata San da zancen auren ba sai yau.Kuma Mummy ta kwa'beta cewar kada ta fad'i ma Inteesar zancen auren,su manya zasu San yadda zasu fad'a mata cikin hikima don kada ta tashi hankalinta.
Da sallama ya shigo falon gaba d'ayansu suka amsa masa sallamar, inda ya k'araso ya durk'usa ya gaida Mummy
"Ina wuni Mummy"
Cikin sakin fuska ta amsa masa
"Lafiya lau son ya Sumayya take"
Jim ya d'anyi don bazai iya sanar dasu halin da yake ciki da Sumayya ba,cikin sanyin jiki ya ce,
"Tana lafiya lau Mummy"
Ganin yanayin d'an nata da yanayin maganarsa ta fahimci cewa akwai wata matsala don haka ta d'aura da cewa
"Ka sanar da ita zancen auren ne?"
Kai ya jinjina
"Eh na sanar da ita Mummy"
"Masha Allah ina fatan dai ba wata matsala kuma Sumayyar Bata tashi hankalinta ba,duk da nasan kowace mace ce dole zata shiga damuwa kishi kumallon mata ne."
Bazai iya yi wa mahaifiyarsa k'arya ba,kuma bazai iya sanar da ita halin da suke ciki ba.
Jin muryar Mummy yayi ta cigaba da cewa
"Son don Allah ka rarrasheta,ka kwantar mata hankali sosai please."
Kai kawai ya jinjina ya kalli goggo cikin jin haushin auren da tasa akayi masa ne ya kauda Kai ciki-ciki can k'asan mak'oshi yayi maganar ya ce,
"Ina wuni"
Ta'be baki tayi tare da fashewa da dariya tana fad'in
"Yaro man kaza,wato fushi kake dani ko?to kaci gaba gausuwarka ma bana so d'an k'wal uba mai zubin sadaka yalla,nayi maka gata amma ba godiya ko?zanyi maganinka ne daga Kai har wannan matar taka gata nan kamar busashshen cry fish."
Harara ya galla mata ta ta'be baki tana cewa
"Uwarka ka harara gata nan a zaune d'an k'wal uban yaro."
Dai-dai lokacin Dady ya sakko ya K'araso wajensu.zama yayin da Muhdeen ya ce,
"Dady Ina wuni"
"Lafiya lau,sauri nake dama zan fita nace Mummynka ta Kira Mani Kai,kana jina ko?"
Kai ya jinjina
"Eh Dady"
"Abunda nake son na sanar da Kai shine,zancen tarewar Inteesar a ina zaka ajiyeta ne? gida d'aya da Sumayya ko kuma zaka kaita d'ayan gidanka ne?"
"A'a Dady gida d'aya zasu zauna."
Kai Dady ya jinjina tare da fad'in
" Masha Allah"
"Zancen tarewarta kuma Nan da sati d'aya zata tare."
Kai kawai ya jinjina ba tare da yayi magana ba.
Zancen kayan lefe kuma Ni da kaina zan bada kud'i a had
Kafin yakai k'arshen zancen Gwaggo tayi saurin cewa
"Sani akan me zaka bada kud'in kayan kefe?ai bazai yi wu ba,ita waccan Kai ka bada kud'in kayan lefenta?shi da kansa ya siya,to haka ma Inteesar shi ne da kansa zai siya saboda hakan zaisa ya