Showing 111001 words to 114000 words out of 149432 words
Chapter 38 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
faranti da aka jera foodflask a ciki, tana fitowa daga kitchen d'in ta nufo falo dai-dai lokacin da Muhdeen ke shigowa ya juya falon ya maida k'ofar ya rufe, tana ganinsa tayi saurin komawa cikin kitchen d'in da sauri ba tare da ya ganta ba, jin motsi hanyar kitchen yasa ya kalli wajen amma baiga kowa ba.
Mummy dake cikin kitchen ganin Inteesar ta dawo da sauri yasa ta ce,
"Lafiya kuwa me ya faru?"
A hankali tayi magana ta ce
"Yaya ne ya dawo"
Da sauri Mummy ta nufi hanyar fita kitchen d'in, tana fita kenan sai gashi yana k'ok'arin shigowa kitchen din, tsayawa tayi ta kalle shi fuska a tamke ta ce,
"Lafiya?"
Cikin karaya yayi magana yana cewa
"Mummy na shiga uku wallahi Inteesar bata gidan iyayenta, ku taimaka mani na samota ta ina zan fara, nemanta ban san mutanen da take mu'amala da su ba, ban san k'awayensu ba, suk da cewar jiya nasa Mufida ta Kira duk wasu k'awayensu amma sunce bata nan, Mummy yanzun ba wanda ya kamata ya taimkaa mani a cikin wannan halin sai Mufida tasan mutanen da Inteesar ta sani k'awaye da dangi da 'yan uwa, dan haka tazo mu tafi..."
Tun kafin takai k'arshen maganar da zaiyi yaji Mummy na cewa
"Kuje ina? kuma tare da wace ce? badai Mufida ta ba kamar yadda bata san mai ya had'a ku har Inteesar ta bar gida ba haka zalika ba zaka saka ta cikin zancen nemanta ba, kaje can ka k'arata duk inda 'yarsu ta shiga ka je ka nemo masu ita."
Da mamaki ya ke binta da kallo don kwata-kwata baiyi tunanin jin makamancin wannan zancen daga gareta ba cikin kwantar da muryar ya fara magana
"Mummy yanzun ke da bakinki kike fad'in haka? idan da wani ne ya fad'a mani abunda kika fad'a zan k'aryata shi, amma ni naji da kunne na."
"Ka ji ka k'ara ji duk inda 'yar mutane ta shiga ka je ka nemo masu 'yarsu, duk yadda akayi akwai wani abunda kayi mata Wanda yasa dole ta fita ta bar maka gidanka, amma ba banza ba haka nan kawai ba zata fita ba an d'auki amanar 'yar mutane an baka kana ta gallaza mata har ya kai ga ta bar maka gidanka, Dan haka zama bai ganka ba ka tafi duk inda take a fad'in garin nan ka nemo masu 'yarsu."
"Mummy ba gallazawa ne yasa ta bar gidan ba, domin da gallazawa ne da tuni ta bar gidan a lokacin da nake gallaza mata, amma ba yanzun ba da bana gallaza mata ta bar gidan duk yadda akayi akwai wani 'boyayyen al'marin wanda bansan da shi ba."
Ta'be baki Mummy tayi tare da cewa
"Sai ka tafi ka nemo ta koma mene ne Kaine sanadi."
Zuba mata Ido yayi yana kallonta ya kasa gane dalilin da yasa suka yi biris da lmaarin nan shiru yayi na d'an lokaci kafin ya nufi k'ofara fita ya fice.
Yana driving ne ya ciro wayarsa tare da lalunar wayar Salisu, bugu biyu ya d'aga bai jira yayi magana na ya ce,
"Kana ina ne Salisu?"
Salisu ya bashi amsa da cewa
"Yanzun gani k'ofar gida ina shirin fita."
"Dan Allah ka jira ni a k'ofar gidan naku, gani nan zuwa yanzun nan insha Allah."
Daga nan ya katse wayar tare da maida hankalinsa ga driving din da yake yi.
Koda ya k'arasa k'ofar gidaan Salisu ya same sa yana jiransa, Salisu me ya k'araso ya bud'e murfin motar Muhdeen ya shiga ciki, hannu ya mik'a masa suka gaisa kafin ya ce,
"Mutumi na lafiya kake kuwa? naga kayi wani zuru-zauru?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce,
Ba dole kaga na rame ba?Salisu ina cikin tashin hankali?wallahi akwai damuwa sosai a tattare da ni, banga Inteesar ba tun jiya da safe rabo na da ita, tunda aka kira ni da sassafe a Asibiti akayi mani kiran gaggawa na tafi na barta tana barci, koda na dawo gida da rana banganta ba, abu kamar wasa har yau ba ita ba labarinta."
"Inalillahi wa'inna ilaihi raji'un,kunyi fad'a da ita ne? yasa ta tafi ta barka?sannan yakamata ka je gidan iyayenta dan ba zata wuce can ba."
"Salisu bata gidan iyayenta kuma bata gidan iyayae na, nasa Mufida ta kira dukkan k'awayensu ta tambaye su ko ta je can, nan ma sun tabbatar da cewa bata gidansu, duk inda yakamata ace ta je bata nan."
"Kuma bansan inda ta shiga ba, kuma ni fargabar da nake kada ya kasance ta fad'a mugun hannu, idan wani abu ya same ta bazan iya jurewa ba."
Ajiyar zuciya Salisu yayi tare da cewa
"To yanzun neye mafita?"
"Ko zamuje police station ne da gidan redo ko Allah zaisa a dace."
Take Muhdeen yayiwa motar key suka tafi police station, sukayi report daga nan suka nufi gidan redio ,bayan sunbar gidan redio ne suna tafiya akan hanyarsu ne yayi parking a gefen hanya, Salisu ya kalle sa ya ce,
"Lafiya ka tsaya ko akwai wata matsalar ne?"
Girgiza kansa yayi cikin yanayi na damuwa da yake ciki ne ya kalle shi ya ce,
"Wane lafiya kuma zaka tambaye ni? bayan kasan halin da nake ciki ai ba lafiya, har sai ranar da naga mata ta sannan hankali na zai kwanta."
"Kada ka damu ka kwantar da hankalinka addu'a ce kawai mafita a gare ka, duk abunda yayi tsanani sauk'i na zuwa, insha Allah zamu same ta cikin k'oshin lafiya Allah zai bayyana muna ita aduk inda take, nasan yadda kake ji a zuciyarka amma amma ka daure kayi ta addu'a har Allah ya bayyana mata."
Murmushi Muhdeen yayi tare da cewa
"Naji dad'in kalamanka Salisu har cikin raina, hak'ik'a tunda wannan abun ya faru ba wanda ya ta'ba fad'a mani magana mai dad'i kwatankwacin wanda ka fad'a mani, ba wanda ya nuna damuwarsa akan lamari na sai kai, hatta aminina Jabeer bai damu da halin da nake ciki ba, babbar abunda zai baka mamaki ma Mummy da Dady cewa sukayi wai na nemo ta duk inda ta ke."
Haka Salisu yayi ta bashi baki yana kwantar masa da hankali, sai da ya tabbatar ya d'an saki ransa kafin suka cigaba da tafiya, sauke shi yayi a k'ofar gida inda ya ajiyae shi kafin yaja motarsa ya nufi gidansa.
Koda ya shiga ba kowa a falo don ko motsin Sumayya bai ji ba, da alama bata gidan ta fita kenan, kai tsaye d'akinsa ya nufa, lokacin k'arfe d'aya na rana komai baici ba bai sha ba, rabonsa da abinci tun jiya da yasha yoghurt bai sake saka ko da ruwa a cikinsa ba, gashi wani masifaffen yunwa yake ji na addabarsa amma baya jin zai iya cin abincin duk da yunwar da ta addabe shi, toilet ya shiga yayi wanka ya fito ya saka kaya ya nufi masallaci, bayan an idar da sallah ne yayi addu'a sosai akan Allah ya bayyana masa Inteesar.
Daga masallaci gida ya dawo a falo ya d'an kishingid'a, ba abuda yake tunani sai Inteesar, tuna yadda ya dinga wahalar da ita da azabtar da ita tun kafin aurensu har ya zuwa bayan aurensu, ya tuna irin biyayyar da take masa duk k'untatawa da yake mata bata ta'ba tsallake maganarsa ba, duk abunda ya umarce ta da tayi sai tayi shi koda hakan zai zama bak'in cikinta ne, zata yi masa indai zai faranta ransa, bata damu da halin da zata shiga ba.
Nadama ce ta kama sa tare da danasanin abunda yayi mata a baya, tabbasa da zai ganata yanzun zai gyara kura kuransa ne, ya nuna mata kulawa da k'aunar da yake mata, yana nan zaune ya shagala da tunani bai ankara ba sai jin Kiran sallar la'asar yayi, mik'ewa yayi ya d'auro alwala ya nufi masallaci, kuma har lokacin baici komai ba a cikinsa, bayan idar da sallar ne ya d'auki motarsa ya koma gidan iyayensa.
Da sallama ya shiga falon Mummy ce zaune a falo, amsa sallama tayi masa tare da kallonsa, ganin yadda ya rame cikin k'ank'anin lokaci yiyi zuru-zauru kamar ba shi ba, mamaki ne ya kamata ganin ramar da yayi, a tunaninta baya son Inteesar kamar yadda ta sani, amma yanzun ganin yadda ya koma ne yasa ta shakku akan abunda ta sani, domin kuwa don idan baya sonta bai kamata a ce ya shiga damuwa har haka ba, kenan yana sonta? to me yasa ya wulak'anta ta alhalin ya damu da ita har haka, uwa uwa ce duk da tana fushi da shi amma bata ji dad'in ganinsa haka ba.
K'arasowa yayi ya durk'usa a gabanta
"Ina wuni Mummy?"
Ba yabo ba fallasa ta amsa masa
"Lafiya lau"
Zama yayi a saman center carpet dake falon, daga shi har Mummy ba wanda yayi magana, ganinsa tayi da alamar yunwa a tattare da shi, dan haka ta kalle shi ta ce,
"Ka zo ka ci abinci"
Bata jira cewarsa ba ta nufi dinning area, bin bayanta yayi duk da ba jin cin abincin yake ba amma yaji dad'i, ganin Mummy wannan karon ta d'an kula da shi, zama yayi a d'aya daga cikin dinning d'in tayi serving d'insa, white rice and stew ne da ya ji naman kaza, kunun aya da ta zuba masa a cup ya fara sha, take gabansa ya fad'i, don tabbas idan har Inteesar tayi masa kunun aya haka yake jin d'and'anonsa, abincin ya d'eba da cokali yakai bakinsa ya tauna a zabure ya mik'a tsaye, kallonsa Mummy tayi tare da cewa
"Lafiya kuwa?"
"Mummy ina take?"
Da mamaki ta kalle shi ta ce,
"Wake nen?"
"Mummy Inteesar tana gidan nan, me yasa aka mani haka?"
"Waye ya ce maka tana gidan nan?"
"Mummy ba wanda ya fad'i mani amma tana gidan nan, don wannan abincin da na ci tabbas ita ta dafa shi, wannan kunun aya ma ita ce ta had'a shi, tunda na d'and'ana abincin nan nasan ita ta girka shi wannan d'and'anon girkinta ne, nasan d'and'anon girkinta nasan naki wallahi Umma ita ce ta girka shi, kuma tana cikin gidan nan."
Mik'ewa yayi ya nufi falo yana k'wala mata kira da k'arfi
"INTEESAR! INTEESAR!! INTEESAR!!!"
Inteesar dake zaune a akan sallaya sanye da hijab, tunda ta idar da sallar la'asar bata tashi ba ta zauna tana azkar, gabanta ne ya fad'i jin muryarsa yana k'wala mata Kira yasa gabanta ya fad'i ta furta kalmar
"Inalillahi wa'inna ilaihi raji'un"
Dama ita kad'ai ce a d'akin Mufida ta fita Mummy ta aike ta gidan Aunty Abla, Gwaggo dake d'akinta ta fito tana cewa
"Wannan kuma haukar me yake mana a gida ne? Kazo kana d'agawa mutane murya ."
Ranasa a 'bace yake kallon Gwaggo, yana shirin bata amsa ne sai idonsa ya sauka akan dady dake saukowa, kallon fusakar Dadyn yayi a murtuk'e ya ce,
"Muhammad fitar mani a gida."
Da ya ke kallon Dady jin kalmar bakinsa, bud'e baki yayi da niyyar magana Dady ya d'aga masa hannu alamun dakatarwa ya ce,
"Get out in my house"
Yadda yayi maganaar a tsawa ce, da ganin irin 'bacin ran da ya gani a fuskar Dady yasa ya nufi hanyar fita.
A harabar gidan ya had'u da Mufida da suka dawo da Direb, ganinsa ta tasan akwai damuwa, da har zai wuce sai ya tamabaye ta
"Da Inteesar tazo gidan nan mai ta sanar da su Dady da Mummy ne?"
"Nima ban sani ba"
"Kada kiyi mani k'arya ki sanar da ni gaskiya, me ke faruwa da kowa ya d'auki zafi da ni."
"Yaya ai dole kowa ya d'auki zafi da kai, da badon Allah yasa munje gidanka ba kuma Allah yasa tana da sauran numfashi ai da wani zancen ake ba wannan ba."
Kallon rashin fahimta yake mata kafin ya sake tambayarta
"Kamar ya please ki sanar dani abunda ya shige Mani duhu."
Ajiyar zuciya ta sauke sanan ta bashi labarin yadda suka tafi gidansa ita da Mummy, suka tarar da Inteesar kwance bata numfashi, kanta na fitar da jini, ta kuma tabbatar masa da cewa Sumayya ce tayi yunk'urin kashe Inteesar, take idanunsa suka kad'a zuwa ja jikinsa gar rawa yake, ya. nufi motarsa cikin k'unar rai da fusata ya shiga motarsa, key yayi mata ya dinga danna horn sai da kiwa ya firgita da yadda ya dinga horn, Mallam Ibrahim mai gadi ya wangale masa gate ya fita a guje zuciyarsana masa zugi, Mallam Ibrahim ya kalli bayan motar ya ce,
"Allah dai ya kiyaye hanya amma wannan tuk'in akwai hatsari a cikinsa."
*DAGA ALK'ALAMIN*✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*Don k'arin bayani*
09065327995
Love you oll😍😘
Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*SANARWA*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page6️⃣4️⃣
"Allah dai ya kiyaye hanya, amma wannan tuk'in akwai hatsari a cikinsa.
Driving yake kamar zai tashi sama, gaba d'aya Allah kawai ne zai kaishi gida lafiya, gudu kawai yake akan titi kamar zai tashi sama.
Sumayya kuwa tana cikin bedroom d'inta zaune saman gado, waya ne kare a kunnenta, tana magana tana cewa
"Ba haka bane shila har yanzun mutumin a sama yake, tunda waccan 'yar matsiyata aka rasa inda take gaba d'aya hankalinsa na kanta, ko damuwa dani baya yi, ina naga sakin fuska a wajensa daga na fad'i magana akanta kinga yadda ya hauni da fad'a kamar zai cinye ni d'anya?"
Banko k'ofara d'akin yayi da k'arfi, a firgice ta mik'e tsaye tana kallonsa ganin fuskarsa ba alamun rahama be yasa zuciyarta tsinkewa, ganin yadda yanayinsa da fuskarsa suka canza ne yasa ta fara ja baya, cikin k'arfin hali ta bud'e baki ta fara magana
"Baby lafiya kuw..."
Kafin ta kai k'arshen zancenta taji ya sauke mata tagwayen maruka biyu a kumatunta, d'ayan kumatun ma haka ya sake sauke mata tagwayen maruka biyu, jiri ne ya fara d'ibanta, don tunda take a rayuwarta ba'a ta'ba marinta ba sai yau, yau d'in ma maruka hud'u lokaci guda, k'eyarta ya rik'e ya buga goshinta a bango take sai goshinta ya fashe jini ya fara fita, wuyanta ya shak'e wajen mak'ogoronta ya rike take ta fara kakari idanunta suka fito waje miyau ya fara dalala daga bakinta, cikin kakkausar murya ya fara magana.
"Zaki kashe ta ko? to kafin ki kashe ta ni zan fara kashe ki, a kin had'ani da iyaye na suna fushi dani duk ta sanadiyarki, baiwar Allah da bata maki laifin komai ba kike neman kashe ta, dama Gwaggo ta fad'a mani cewa ke ba matar aure bace amma na dinga k'alubalantarta, amma gashi naga gaskiyarta a yanzun."
Jifa da ita yayi gefe sannan ya nufi hanyar fita yana huci, ita kuma yanda yayi jifa da ita ta zube wajen ko numfashi bata yi.
A can gidansu Mummy kuwa bayan fitarsa ne da Dady ya kalli Mummy ya ce,
"Waye ya sanar da shi cewa tana gidan nan?"
Mummy ce ta kalle shi tare da cewa
"Ba wanda ya fad'a masa , daga ya ci abinci shine fa ya ce wai ita ta dafa abincin nan wannan d'and'anon girkinta ne, daga nan ya dinga k'wala mata kira."
Shiru Dady yayi yana nazari, tabbas ya gane cewa Inteesar ce ta dafa masu abincin, don shi dama haka ya ke tun yana yaro indai ya d'and'ana abincin da ba mahaifiyasa ce ta dafa ba ya sani, yana ganewa Dan a lokacin Dadynsa har yana mamakinsa sai yanzunn ya ke tunowa da wani abun, wato har girkin Inteesar ma yana ganewa, gajeren murmushi Dady yayi tare da komawa ciki, Mummy ce ta kalle Gwaggo ta ce,
"Lamarin nan fa ya fara d'aure mani kai."
Dariya irin ta su ta manya Gwaggo tayi tare da cewa
"Ba abunda ke d'aure mani kai a lamarin su, ki zuba ido kawai kada ki ce komai."
Da misalin k'arfe takwas na dare ne Sumayya ta soma tari a hankali, dak'yar ya iya tashi zaune saboda tana rik'e da mak'ogoronta da ke mata zafi, goshinta dake mata rad'ad'i ta kai hannu ta shafo shi,jin yadda ya fashe ya kumbura ga jini da ta shafo, kuka ta sake da shi mai cike da tsantsar bak'in ciki da takaici, jikinta gaba d'aya ji tayi yana mata ciwo, dak'yar ta lalla'ba ta shiga toilet, tana kuka tana wanka har ta gasa jikinta, har zuwa wannan lokacin mak'oshinta na mata ciwa ga goshinta sai zugi yake mata, raki da son jiki bai bari ta gasa wurin ba.
Haka ta ta fito ta zube a Kan gado, don dama sallah bai dame ta ba ko da kafiyarta ballantana yanzun da ba lafiyar,kuka ta cigaba da yi, wayarta ta kalla inda ta fad'i k'asa lokacin da Muhdeen ya mare ta, tashi tayi ta d'auko wayar tare da lalubo number Dad dinta, sau uku tana jaraba Kira amma bai shiga ba, kuma ba zata iya kiran Mum d'inta ta sanar da ita ba, dan tunda ta lura Mum ta daina goyon bayanta ta daina sanar da ita halin da take ciki, kwanciya tayi a kan gadon har barci ya d'auke ta.
A 'bangaren Muhdeen kuwa shima haka ta kasance a gare shi, ya kwana cikin bak'in cikin abunda Sumayya ta aikata, wanda a dalilin haka kowa na fushi da shi, duk da cewar shima da nasa laifin amma nata ya janyo wannan matsalar har aka kawo wannan matakin, dan shi yanzun yayi niyyar gyara zamantakewarsa da matarsa, ya mantar da ita rayuwarsu na baya.
A haka dai bai samu isashshen barci ba har k'arfe hud'u na asuba, toilet ya shiga yayi wanka ya nufi masallaci.
Daga masallaci ya zauna yayi azkar da karatun al'qur'ani mai girma, sai k'arfe bakwai sannan ya dawo gidan, yana tafiya yana tunanin yadda zai fuskanci Dady da Mummy da Gwaggo akan Inteesar, amma ko ba komai ya samu sassauci a cikin zuciyarsa, kaso hamsin ciki d'ari na damuwar da yake ciki ya ragu, domin yanzun yasan cewa Inteesar bata mugun hannu, duk da dai akwai babban aiki a gabansa.
A falo ya had'u da Sumayya tana zaune kan kujera tana cin snacks da yogurt, don dama aikinta kenan tunda bata iya girki ba sai dai tayi ta fama da kayan su biscuits cake da sauransu, tana zaune tana tsaka da cin snacks ne ya shigo, sai da gabanta ya fad'i dan