Showing 15001 words to 18000 words out of 149432 words
Chapter 6 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
Allah ya Aiko ka mugu kawai Mai bakar zuciya akan yawu zaka kama 'yar mutane zaka illata.wannan irin mari ai sai ka kurmantawa mutane 'ya ta zama musaka.
Gwaggo ne ta janyo Inteesar daga jikin Mummy ta rungume ta a jikin ta Tana Dan bubbuga bayan ta.Hatta Mufida sai da taji kamar zatayi kuka ganin yanda fuskar Inteesar din ta canja.
Gwaggo ta dago fuskar ta tare da janyo ta suka nufi kofar falo suna tafiya Tana fadin,
"Kiyi Hakuri kinji yarinyar arziki wannan muguntar da ya maki Allah zai bi maki hakkin ki akan sa, Mufida ce tabi bayan su daga Mummy sai Muhdeen a wajen,zuba masa ido tayi tace,"
"Gsky son ka 'bata Mani Rai sosai akan wannan Hukuncin da ka yanke akan Inteesar ta watsa maka Miyau haba Hukuncin naka yayi tsauri da yawa Don yarinyar Nan bazata ta'ba watsa maka yuwun bakin ta da sanin ta ba na tabbatar Bata lura dakai bane.yanzu idan Asiya ko Mufida ne suka watsa maka yuwun bakin su a bisa kuskure Hukuncin da zaka dauka kenan akan su?"
Girgiza Kai yayi Yana fadin,
To Mummy so fa jini na ne ta Yaya Zaki hada su day wannan kucak..."
Tsawar da ta daka masa ne yasa yayi shiru.
"Kai! Kai ka fita a idanuna na fada mak,Yadda na dauki Inteesar haka na dauki Asiya da Mufida bana nuna masu Banbanci,haka ma mahaifin KU ya dauke ta komai tare yake masu sai abunda baza'a rasa ba,Hatta Mufida irin shakuwar da sukayi da Inteesar basuyi shi da 'yar uwar ta Asiya ba.kaima haka nake so daga gare ka ka dauke ta kamar kanwa CE a gare ka"
Daga Nan tasa Kai ta shige falon Shima bayan ta yabi .
Gwaggo na zaune akan kujera ta daura Kan Inteesar akan cinyar ta, mufida na zaune tayi tagumi ta zubawa Inteesar ido ganin yanda sawun yatsun yayan nata akan fuskar Inteesar gefen dama da hagu sunyi jajir.
Mummy ta nufi dakin ta Muhdeen ma part din sa ya nufa nufa yayin da Gwaggo tabisa da harara Tana cewa,
"Gaka fari Amma zuciyar ka bakakirin Ga kyawun sura Amma ba kyawun Halayya"
Baibi ta kanta ba ya nufi dakin sa ransa a bace.mummy ce ta karaso falon Hannunta dauke da magani fridge ta nufa ta dauko robar ruwa ta zauna ta balle maganin ba bawa Inteesar tare da Goran ruwa,ba musu ta karba ta hadiye.Ba jimawa bacci ya dauke ta ganin haka yasa mummy tace ma Asiya ta biyo ta kitchen suyi aikin tare.bayan tadiyar su ne Gwaggo ta nufi dakin ta Tana cewa,
"Dan bakin ciki yarinya tazo tayi Mani girkin ta Mai dadi ya Hana ta da muguntar sa"
Muhdeen Yana shiga dakin sa you nufi toilet dinsa kayan ya cire yayi wanka da sabulu Mai kamshi da turaren wanka,ya shirya cikin kananun Kaya jar Riga da bakin wando,Kai tsaye yabar part din sa ya nufi falon ba kowa sai Inteesar dake bacci,Goran ruwa ya bude ya Dan yayyafa Mata ruwa a fuska,a firgice ta farka zatayi masa kuka Dan tsoron sa take ji,daura yatsar sa yayi a bakin sa alamun tayi shiru.
"Shhhshhh"
Hannayen ta ta saka ta toshe bakin ta Tana kokarin hadiye kukan,sannan yace,
"Ki biyoni daki na"
Da sauri ta Ware dara-daran idanun ta Tana kallonsa cikin tsoro da mamaki Tana girgiza masa Kai,daure fuska yayi ba Alamar rahama,da hannu yayi Mata nuni da ta biyo shi.
Haka ta Mike ba musu Tana gaba Yana binta a baya har suka karasa part din sa cogewa tayi a bakin kofar dakin Tana tsoron shiga sanin cewa ba kowa a dakin kuma Ummanta ta Hana ta ke'bewa tare da namijin da ba muharramin ta ba.
Ganin Bata da niyyar shiga ya watsa Mata harara tare da cewa,
"Ba Zaki shiga ba?"
Kai ta girgiza cikin rawar murya tace,
"Ummana ta hanani ke'bewa da namiji mu biyu idan ba kowa"
Dariyar raining hankali yayi Mata yana Kare Mata kallo yace ,
"Dalla shiga uban me zanyi dake ko ina neman Mata bazan bazan taba iya hada jiki da kucaka irin ki ba ke har kinkai macen da Zan kalla naji wani Abu akan ki?"
Tsaki yaja sannan yace,
"Shiga muje"
Ba musu tabi bayan sa har toilet suka shiga,kayan da ya cire Wanda ta watsawa Miyau ya nuna Mata yace,
Kindan kudin shaddar Nan da kika 'bata kuwa?kinsan nawa na siye ta?kinsan anko mukayi nida Mai sumy kuwa?kinsan yau ne na Fara saka ta da niyar zuwa wurin masoyiya ta kuwa?kinsan zamuje yawan sha'katawa zamuje muyi photo da kayan Nan kuwa?"
Cikin rawar murya tace ,
"Kayi hakuri"
Tabe baki yayi Yana cewa,
"Wannan kayan sun fita a Raina bazan iya saka su ba,yunusa Mai bawa fulawa ruwa zanba su,yanzun ki Duka ki wanke su tas ki fita ki shanya su a Rana,kiyi gadin su sai sun bushe kafin kizo ki goge sau"
*YAWAN COMMENT DIN KU YAWAN READ MORE*🤷♀️Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Wannan kirkirerren labari ne banyi tunanin Rubuta ta shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to kuyi Hakuri bada niyyar yin Hakan nayi ba, arashi ne Mai kashe Auren Wawa.
Page 1️⃣3️⃣
"Yanzun ki d'auki kayan nan ki je ki wanke su tas ki fita kije ki shanya su a rana, kiyi gadin su sai sun bushe karin kizo ki goge su"
Karasawa tayi gaban washing machine Don dake cikin tangamemen Toilet din, ganin hakan yasa shi dakatar da ita cikin tsawa ya ce,
"Keee"
Da sauri ta juyo ta kalleshi,
"Ina kike kokarin zuwa? Hannun ki zaki sa ki wanke su ba warshing machine za ki yi amfani dashi ba"
Yana kallon ta har ta gama wanke kayan da ba datti ne dasu ba,ta d'auraye kumfar sabulun ta fito, ganinan zata bi ta hanyar babban falon gidan ya dakatar da ita. ya nuna wata kofar da bata san da ita ba,koface wacce take cikin part din sa wanda idan kabi direct zai sadaka da garden din gidan.cikin bada umarni ya ce,
"Idan kika shanya kayan a garden din ki jira su bushe kafin ki kawo su ki goge su, sannan wannan kofar da kika gani ita zakibi ki dawo"
Yana gama fad'ar haka ya koma ciki, direct babban falo ya nufa zaman sa keda wuya sai ga Gwaggo ta karaso falon, ganin babu Inteesar yasa ta Fara waige-waigen neman ta ganin Bata Nan yasa ta Harare shi tare da fadin
"Kai ina Inteesar take ne? Nan na barta ita kadai?"
Ko kallon ta bai yi ba ya cigaba da danna wayarsa.
Cikin daga murya ta ce,
"Tambayar ka nake, ina yarinyar da kaci zalinta take?"
Still shiru ya mata kamar bai ji ta ba don dama akufule yake da ita yadda a gaban Inteesar ta dinga zagin say Wai salon ta Raina shi, a hasale ta sake tamayarsa a karo na uku sannan ya ce,
"Ajiyar ta kika bani ko zaman gadinta na ke yi?"
A hasale ta ce,
"Haka kace ko?yanzun tsabar balagar rashin kunyar taka takai ka kalli tsabar ido na ka fada mani haka?" Ina mahaifiyar Uban ka? Nina haifi wanda yayi sanadiyar zuwan ka duniya da har ya d'an banza Mai suffar sadaka yalla, dama ance wanda kafi so shi yafi kuntata maka, duk cikin jikokina nafi kaunar ka da son ka Amma kafi kuntatamani da bakanta mani rai.
Tunda kace ban Isa ba to bari na Kira mahaifiyar ka ai ita na isa da ita"
Daga murya tayi Tana kwalawa Mummy kira
"Fatima! Fatima!! Fatima!!!"
Da sauri Mummy ta fito daga kitchen d'in da sauri jin yadda Gwaggo ki kwala mata kira tasan ba na lapiya bane,bayan ta karaso ta kalle ta cikin girmamawa ta ce,
"Gwaggo lafiya kuwa?"
Kallaon ta Gwaggo tayi ta ce,
"Ina fa lafiya banga baiwar Allah da nasa aka kirata tun daga gidansu tazo wannan bakin mugun yayi mata dukan kawo ruwa, nan ba barta wance"
Ta nuna kujera mai zaman mutum uku
"Shine yanzun na dawo ban ganta ba, ina tambaye sa Ina take yana fada mani maganar banza, amma yanzun tunda ke uwarsa ce zai fada maki"
Kallonsa Mummy tayi na dan lokaci tana karantar yanayinsa ta ce,
"Son ina yarinyar nan take?"
Kallon ta yayi cikin kwabe fuska ya ce,
"Mummy nima yanzun na fito daga d'aki banga kowa anan ba, wata kila ta shiga dakin Mufida ta kwanta"
Mummy ta kalli hijabin Inteesar tare da wayarta akan kujera yasa ta kalli Gwaggo ta ce,
"Kin ga Hijabin Inteesar da wayarta ba inda taje ina ganin ta shiga ta kwanta ne"
K'ai Gwaggo ta gyada ya yin da Mummy ta koma cikin kitchen d'in, Gwaggo ta ci je lebe tare da ce wa,
"Wayyo ciwon kafata ta soma yi mun ciwo"
Ta karasa maganar da 'kyar ta zauna Kan kujera tana kallon Muhdeen da kallo daya ya Mata ya dauke kansa ta ce,
"To yauwa d'an albarka dama magunguna na sun Kare ka taimakawa tsohuwar nan mana"
Kamar bai ji ta ba haka yayi mata shiru
"Magana nake maka shalele na"
Dariya ce taso kufce masa amma sai ya dake tare da cewa,
"To waye kuma shalelen naki a yau?"
"Kai mana d'an Albarka likita bokan turai, ai ba ni da shalele bayan kai"
Murmushi yayi
"Ada ne nake shalelen ki, amma yanzun bani ba ne waccen yarinyar mai kama da Aljana ita ce shalelen ki yanzun, don na lura zaki iya batawa dani in dai akanta ne"
Ya Karasa maganar ba tare da ya kalle ta ba, rike baki Gwaggo tayi tare da ce wa,
"Waya fada maka ba kaine shalele na ba? Ka ta'ba ganin inda aka canzawa tuwo suna?"
Dariyar raining wayo yayi mata sannan ya ce,
"Ana ki canzawa tuwo suna sai dai idan bai kwana ba, amma idan ya kwana ya zama d'umame"
Gwaggo ta kalle shi
"Shalele na ka manta cewa da tsohuwar zuma ake magani?"
Murmushi yayi tare da ce wa,
"Sanin da ki ka yi na cewa da tsohuwar zuma ake magani Amma yanzun anayi da sabuwa Dan neman karin sinadari"
Kallon mamaki tayi masa
"Wai kai komai aka fada maka sai ka samu amsar maidawa? to naji don Allah ka kawo mani irin magungunan da saka aika mani dasu nasa da na shafawa"
"Babu wani maganin da zan baki wannan karon allaura za ni yi maki"
Kallonsa tayi da sauri ta ce,
"Ai me za ka yi mani?"
Mi'kewa yayi tare da bar mata falon.
Bangaren Inteesar kuwa tana nan zaune ta tasa kayan a gaba tana jiran bushewar su, kasancewar akwai Rana har sun kusa bushewa, magana takeyi a fili.
"Insha Allah na bar masa gidansu kenan, lokaci yayi da zan nisance su tunda har tsanar da yayi Mani yakai haka, dama dole tasa nake zuwa gidan su bawai son kaina ba ne, mahaifiyarsa ce take sani zuwa sshe lokacin da mahaifiyar sa taje ta samu Umma da maganar cewa na dawo gidanta gaba d'aya da zama Umma da Abba suka Hana Ashe da sun amince da na kad'e a hannun sa in banda su da suke matsa Mani aiba killin zan zo ba, ko ban zo ba zasu kirani a waya ne wai dan Allah nazo wata Rana Mufida ce zata zo tace wai Mummy tace nazo.amma yanzun duk abunda zai faru ya faru ya faru zan dauke kafa ta a gidan nan, ki zuwa school din da nake shiryawa da wuri na biyowa Mufida zan daina shiryawa da wuri ne har sai na tabbatar sun bar gida sannan na fito mu had'u a hanya, duk da cewar Mummy, Dady, Gwaggo, ga kuma Mufida da muka shaku ba za su so hakan da zanyi ba Amma shine mafita a gareni.Yaya Muhdeen kayi hakuri na kusa bar maka gidan ka zuba ruwa kasa kasha, mugu a gaban mutane baya nunamin hantara da kyara Amma da zaran ba idon kuwa kare ma narishi daraja a idonsa"
Tana ta magana ita ka dai kamar tanayi da wani ga zazabi naso rufe ta ga azababben ciwon Kai da yasa ta gaba,Tana Nan zaune kayan suka bushe ta kwaso su tabi ta yanda ta fito,har Bedroom din sa ta wuce ta fara goge kayan.
Can fall kuwa bayan angama girki Anjera a Dinning table kowa ya hallara Mummy, Muhdeen da Gwaggo ya yin da Dady ne kadai baya nan.Mufida ce ta fito cikin tashin hankali tana fadin
"Mummy gaba daya na duba ko Ina banga Inteesar ba Ina ta shiga?"
Dai-dai lokacin Inteesar ta fito daga part din Muhdeen dafe da kanta, jin alamar tohuwar mutum yasa suka waiga dukkan su sauka zuba mata ido suna kallonta da mamaki, ya yin da Mummy tayi saurin mikewa ta rike hannunta cikin mamaki tace,
"Daga ina kika fito?Mai ya kaiki part d'in son?"
Mummy ta kara rungume ta tana fad'in
"Subhanallahi jiki yayi zafi, zazza'bi ne ya rufe ta"
Janyo hannunta tayi suka karasa dinning room dinta zaunar da ita kan kujerar dake kusa da ita.Ba yadda Mummy batayi ba akan Inteesar taci abinci taki da kyar tasha lemon da Mummy ta tsiyaya mata a cup, Mummy ta kalli Muhdeen ta ce,
"Son"
D'agowa yayi ya kalleta tare da cewa,
"Na'am"
"Ka d'auko kayan aikin ka sannan ka dauki Inteesar a motarka ka kaita gida kayi Mata treatment din da ya dace kafin ka dawo,sannan kafin KU nufi gidan su ka biya ka siye mata fruit saboda bata ci abinci ba"
Cikin bada umarni tayi maganar, kallonta yayi ganin yanayin fuskar ta ba sauki yasa yace,
"To Mummy yadda kika ce haka za'a yi"
Kallonta ta maida ga Inteesar ta ce,
"Inteesar ga yayanki zai kaiki gida yayi maki abunda ya dace kafin nima na zo"
Kai Inteesar ta gyada ba ya yin da gabanta ya ci gaba da fad'uwa.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Wannan kirkirerren labari ne banyi tunanin Rubuta ta shi Dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM*
Page1️⃣4️⃣
Kai Inteesar ta gyd'a yayin da gabanta gaba da fad'uwa.
"Uhm wannan marukan da tasha ba dole tayi rashin lapiya ba? Yanzun haka ba Wanda ya ta'ba Mata wannan Marin,ko uwar ta ubanta nasan bazasu yiwa wannan nitsatsiyar yarinya Marin nan ba Amma Rana tsaka wani katon banza ya more ta."
Gwaggo ce tayi maganar yayin da karasa bayan Inteesar Tana shafa kyakkywar fuskar Inteesar.
Muhdeen ko kallonta baiyi ba yayinda ya Mike ya nafi part dinsa fuskar Nan a muturke.Mufida ce to janyo hannun Inteesar tare da cewa,
"Muje na rakaki mota,idan na dawo daga gidan Yaya Jabeer matar sa Bata da lapiya ne zamuje da Mummy mu gaishe ta,idan muka dawo zan biyo gidan naku Allah ya baki lapiya"
Inteesar tace ,
"Ameen "
yayin da suka nufi hanyar fita,Kai tsaye parking lot suka nufa Inda Mufida ta bude Mata murfin gidan gabar motar.kai Inteesar ta girgiza tare da cewa,
"Baya zan zauna"
Ba musu Mufida ta bude Mata bayan motar ta ahiga,zamanta keda wuya sai ga shi Shima ya karaso hannun sa rike da akwatin magunguna,murfin motar ya bude yashiga ganin Bata gefen sa yasa Kai idon sa baya,ganin ta dukunkune yasa yace Mata.
"Niba direbanki bane ki tashi ki dawo gaba"
Mufida ce tace
"Ya Ina ga kamar zatafi yin Balanced a baya tunda nac... "
Had'iye sauran maganar tayi ganin irin kallon da yake Mata ne yasa tayi shiru.bude bayan motar tayi ta kama hannun Inteesar Dan ta taimaka ta fito,a hankali ta fito da taimakon Mufida Dan har jiri take ji Yana neman dauke ta.Bayan ta zauna gaban motar ne ya figi motar suka bar gidan.
Sai da ya biya ya siye Mata fruits kamar yadda umma ta Umarce shi.Tundaga Kan lemo,kankana,Apple, Abarba inibi da ayaba sannan ya kama hanyar gidan su Inteesar din kasancewar yasan gidan ya ta'ba Kai Mummy.
Dai-dai lokacin da ya Isa kofar gidan ya juya ya kalli Inteesar,ganin idon ta a lumshe kamar Mai bacci.Dai -dai lokacin ne kuma Kira Sumayya ya shigo wayar Video call ne.daga Kiran yayi ganinta sanye da shaddar da suka shirya sawa sunyi anko su tafi uawan shakatawa.lumshe kyawawan idanun sa yayi tare da bude su yace,
"Mai Baby kinyi kyau sosai"
Murmushi tayi tare da cewa,
"Thanks Amma ya bangan ka da naka a jikin Ka ba?kayi lettin zuwa waje na yakamata ace minti talatin da suka wuce ka iso Amma shiru"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace,
"Ki bani minti talatin zan karaso yanzun Nan insha Allah"
Turn baki tayi sannan tace,
"Kana Ina ne yanzun?"
"Ina kofar gidan su Inteesar"
Rasss Gaban ta ya dadi tace,
"Wace Inteesar"
Saita secreen din wayar yayi dai dai yanda Inteesar ke zaune gefen sa idonta alumshe.
Take Sumayya Gaban Sumayya ya Fadi ganin Inteesar a cikin motar Muhdeen yayin da ita Tana can Tana jiran sa Amma shi Yana can wurin wannan yarinyar.
Take taji wasu zafafan Hawayen kishi suna kwaranya a idanun ta muryar kuka tace,
"Nagode da abunda kayi Mani "
Tana kokarin kashe wayar ne yayi saurin cewa,
"Kinga dakata ki saurare Ni nayi maki bayanin abunda ya daru"
"Want bayanin zakayi Mani?cewa Inteesar tafi Ni mahimmanci a wirin ka ne da yasa ka shanyani kusan awa d'aya Ina jiranka yayin da Kai kake can wajenta"
"Kinga ki tsaya nayi maki bayanin yadda akayi"
Kara fashewa tayi da kuka,Don dama Tana da zafin kishi Bata tsaya sauraren sa ba ta katse kiran.
Juyawa yayi ya kalli Inteesar da ta lumshe ido kamar Mai bacci yayinda duk Tana Jin maganar da suke.
"Fita"
Ya fada Mata a takaice,yayin da Shima ya fito ya rufe marfin motar.da'kyar ta iya bude marfin motar ta fito jiri ne ya d'ebe ta tayi luuu zata fad'i. a guje Muhdeen ya Karasa gare ta ya tare ta ta fad'a jikin sa.
Cikin wata iriyar kasalar da ta dorar masa lokaci guda yace,
"Kiyi a hankali"
Same jikinta tayi ta jingina da motar saboda ganin takeyi komai na jujjuya Mata.
Karasawa yayi bakin kofar gidan tare da yin sallama,Yana Nan tsaye Umma ta fito sanye da Hijab.zubawa kyakkywan saurayin Mai kwarjini da haiba ido, Muhdeen kyautatawa ne ajin farko dogo ne fari fuskar sa zagaye da kwantaccen saje da yayi luf a fuskar sa Gashin kansa ma haka yake kamar ba na bakin fata ba ga madaidaitan idanun