Showing 57001 words to 60000 words out of 149432 words
Chapter 20 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
inda ta fara magana kanta a akasa.
"Nace amm dama Wai dama ummm"
Tsuki yayi tare da daka Mata tsawa
"Ke! dalla gafara can,idan zakiyi magana kiyi kin tsaya kina mun munafurci a nan."
Kanta a sunkuye k'irjinta sai dukan uku-uku yake ta fara magana.
"Dama cewa zanyi kullun zan dinga share da goge falo da kitchen safe da yamma kamar yadda ka ce nayi,sai kuma d'aki guda takwas da kace suma safe da yamma naga yanzun d'akuna uku ake amfani dasu sauran biyar d'in ba'a komai dasu,kuma suna kulle ba datti suke yi ba kuma kace suma safe da yamma shine na ce a dinga barinsu sai ranar juma'a sai na dinga bud'esu ina share su."
Gajeren murmushi ya yi
"Dani dake waye mai gidan?"
"Kai ne"
"Dani dake waye mai ikon fad'a aji?"
"Kai ne"
Dani dake wa ya ajiye wani?"
"Kinga kuwa magana ta ce sama da taki,kije ki gama duk aiyukan da na saka ki kafin kizo kiyi breakfast."
Daga nan ya nufi bedroom d'insa ya barta nan tsaye cike da tausayin kanta.
Haka Inteesar ta cigaba da rayuwa a cikin gidan Muhdeen cikin aikin wahala gashi dai ba aikin da gidan ko d'akunan ke buk'ata amma haka zai ce sai tayi shi,koda duka d'akunan da ba'a amfani dasu gasu fes ba datti ko kad'an amma daboda tsabar mugunta irin na Muhdeen sai ya ce ta goge su ga manyan falo biyu da kitchen guda biyu zata gyara dinning zata goge table da kujerun dinning area d'in,idan ta tashi tun asuba tayi sallah ta fara aikin gidannan tayi wanka ba ita zata samu sararin breakfast ba sai K'arfe biyu na rana.
Gwaggo ce zaune a falo tana sababi wai tunda aka Kai Inteesar gidan Muhdeen ba wanda ya je ya duba halin da suke ciki,ita fa zata je gidan ta zauna tayi sati d'aya,dama yau ne suka cika sati d'aya da tarewa.
Mufida ce ta fito daga kitchen d'auke da basket zata kaiwa su Inteesar abinci,kallonta Gwaggo tayi tare da cewa.
"Ke dama yaune zaki kai abincin k'arshe gidan Inteesar ko?"
Kai Mufida ta jinjina alamun eh
"Hakane Gwaggo daga yau shikenan"
"To idan kinje ki sanar da 'yar albarka cewa rana yata yau zanzo gidan sai nayi wata d'aya zan dawo."
Kallon mamaki Mummy ta bita da shi
"Har wata d'aya Gwaggo?"
"Eh haka nace ko akwai wanda Zai hanani ne?"
Girgiza Kai Mummy tayi
"A Gwaggo ba wanda zai hana ki ai."
"Ato idan ma akwai ne inji bayani."
Murmushi Mufuda tayi
"Yauwa Mummy na mance ban fad'a maki ban tambaye ki ba, Inteesar ta ce tabar wayarta a gidan nan a d'akin Yaya na duba ban gani ba."
Dafe goshi Mummy tayi tare da cewa yauwa namanta ne wlh yana d'akina,tun ranar da suka tafi washe gari na ganshi na d'auka tare da kashe wayan gaba d'aya,ki duba cikin side drawer na ki d'auka ki kai mata."
Ajiye basket d'in tayi tare da nufar d'akin Mummy ba jimawa ta fito da wayar a hannunta,sallama tayi masu ta nufi k'ofar fita,inda Gwaggo ta jaddada mata cewa ta shaidawa Muhdeen zata zo ranar juma'a.
Inteesar na kwance a saman bed d'inta tana barcin wahala,don gaba d'aya a gajiye take Don aikin da take yi yayi mata yawa,jikinta ma ciwo yake mata, ga hawayen da ya bushe a kumatunta da dukkan alamu kuka tayi har barci ya d'auketa.
Lokacin da Direban Mummy ya shigo gidan tare da Mufida lokacin ne kuma Muhdeen ya fito daga cikin gidan,sanye yake da farar shadda tsadadda da ba'kar hula a kansa sai bak'in takalmi da ya sakaba k'aramin kyau yayi ba,kwarjininsa ya k'ara bayyana Ishaq Direbansa ne ke bud'e masa murfin gaban motar, ganin Mufida yasa ya dakata ido ya zuba mata a tare suka sakarwa juna murmushi.
"My lovely bros barka da rana"
Fad'awa jikinsa tayi tare da cewa
"Kayi kyau sosai,ina lovely friend tana ciki"
"My lovely sis tana ciki"
"Okya me take yi?"
Ta'be baki yayi ya ce,
"Ki shiga ki gani mana,ni masallaci zanje sauri nake lokaci yayi."
"Okay ayi juma'a lafiya,ki gaida mutanen gidan."
"A'a Yaya ai wannan karon yini zanyi sai dare zan tafi."
d'an jim yayi yana nazari kafin ya ce,
"Ba Zaki koma gida ki taya Mummy aiki ba?"
"Na fad'a masu sai dare zan dawo,sannan ma Gwaggo ta ce na sanar da ku cewa next week zata zo sai ta yi 1 month sannan zata tafi."
Sai da Muhdeen ya d'an razana da jin zancen zuwan Gwaggo,Amma sai ya dake ya ce,
"To me zaisa tazo ta yi har wata d'aya a nan?ina laifin ta yini ta koma?"
Murmushi Mufida ta yi
"To ina laifi Dan tazo ta yi wata d'aya?kar ka mance cewa Gwaggo na k'aunar Inteesar fiye da tunaninka,bata son 'bacin ranta ko kad'an,ina tunanin zuwanta bai rasa nasaba da k'aunar da take mata da kuma k'aunar da take maka,kasan duk cikin jikokinta ta fi sonka."
Jinjina Kai yayi tare da cewa
" shikenan ki shiga ciki."
Nufar cikin gidan tayi yayinda shi kuma ya shiga cikin motarsa,tunani yake idan Gwaggo tazo gidan nan akwai matsala babba.
Koda Mufida ta shiga ba kowa a falon,hakan yasa Kai tsaye ta nufi d'akin Inteesar,sallama tayi sau uku bata ji an amsa ba hakan yasa ta tura k'ofar d'akin ta shiga,kwance ta same ta ta k'udundune waje guda alamun a takure take,ga hawayen da suka biye fuskarta sun bushe,idonta ma a kumbure alamar ta ci kuka,ido Mufida ta zuba mata ganin yadda ta d'an rame gashi tana barcin amma bata daina ajiyar zuciya ba, hannunta takai ta ta'ba gefen fuskarta a firgice Inteesar ta farka tana zare ido,ganin Mufida ce bata san lokacin da hawaye suka cika mata ido ba yayinda Mufida ta rungumeta.
Daga alk'amin✍️
Zainab Andullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll😍😘
Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne Mai kashe auren wawa.
*SADAUKARWA*
Wannan shafin sadaukarwa ce ga duk matar da ta fuskanci k'alubalen aure da uk'ubarsa ta kuma jure,hak'ika ba wata damuwa da zata d'ore har abada komai loaci ne wata rana sai labari.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page3️⃣8️⃣
Ido Mufida ta zuba mata ganin yadda ta d'an rame gashi tana barcin amma bata daina ajiyar zuciya ba, hannunta takai ta gefen fuskarta a firgice Inteesar ta farka tana zare ido, ganin Mufida ce bata san lokacin da hawaye suka cika mata ido ba yayin da Mufida ta rungumeta.
"Inteesar lafiya kuwa? me ya ke faruwa dake ne?"
Sunkuyar da kanta tayi tare da goge k'wallan da suka cika mata ido.
"Bakomai Mufida me kika gani?"
"Gani nayi duk kinbi kin rame daga ganinki baki cikin jin dad'i."
"Hasashenki ne haka,amma nikam ba abunda ke damuna."
Girgiza kai Mufida tayi cikin rashin yarda da zancenta ta ce,
"Kardai ace har kun fara samun sa'bani da Yaya tun yanzun,ai yakamata ne ace kuna cin amarci ba Wai daga aure an fara samun sa'bani ba,duk da ance zaman aure 'dan hak'uri ne amma yayi wuri da yawa."
"Karki damu Mufida ba komai ba wani sa'anin da muka samu,haka zaman namu yake tun fil'azal."
Da mamaki Mufida ke kallonta.
"Ban gane be Inteesar cewa fa kika yi haka zaman naku yake tun fil'azal."
Murmushin yak'e Inteesar tayi
"Ba haka nake nufi ba,ina nufin haka zaman aure yake tun fil'azal,wato d'an hak'uri ne haka abun yake a ko ina."
Jinjina Kai Mufida tayi
"To wai shin ma me ya had'aku kece mai laifi ko shi?"
Ganin yanayin Inteesar ya d'an canza yasa Mufida yin murmushi tare da dafa kafad'arta.
"Sorry k'awata mubar maganar."
Zama suka yi dab da juna ido Mufida ta zuba mata tana kallonta,kuma tana nazari a cikin zuciyarta,ita dai a iya saninta duk yarinyar da tayi aure sai taga ta canza ta k'ara kyawu da shek'i har k'iba yarinya takan k'ara,idan kuma ba mai kikin k'iba bace sai ta d'an murmure,Amma ita Kam Inteesar sai ramewa tayi gaba d'aya ta fita hayyacinta,amma sai ta bar hakan akan cewa kila dan Inteesar bata son Muhdeen ne auren had'i akayi masu,hakan yasa bata kwantar da hankalinta ba,iska mai d'umi ta furzar daga cikin bakinta,kafin ta fara magana.
"Nasan bakya son Yayana aka aura maki shi,dan Allah kiyi hak'uri ki kar'beshi a matsayin mijinki,ki cire damuwar da take ranki,bakiga shima ya d'auki k'addararsa ba ya rungume ki a matsayin matarsa ba? Wallahi ya burgeni yadda naga yana nuna damuwarsa akanki,ranar washe garin ranar aurenku da nazo kawo maki breakfast kin tuna yadda yadda dinga ji dake?Wai kada na wahalar masa dake nabi a hankali ni a tunani na fa da naji ya ce haka na d'auka ko a daren farkon kun kashe arna ne kin wahala yasa naji ya ce haka."
Ta k'arasa maganar cikin sigar tsokana, Inteesar bata ce mata komai ba tana da ta sauraronta,inda Mufida ta cigaba da cewa.
"Kamar yadda nake jin labari wai hakane a daren farko?"
"Labarin me kuma?"
"Wai idan mijinki ya kusance ki akwai zafi?"
Kallonta Inteesar tayi tare da cewa,
"Me yasa kika mani wannan tambayar?"
"Saboda naga ke kika riga aure cikin k'awayenmu kuma ke kad'ai zan iya tambaya"
"Nima ban sani ba,ki Bari idan kikayi auren zaki sani."
Da mamaki Mufida ta kalleta
"Kamar ya baki sani ba bayan aranar da nazo kawo maku breakfast daga d'akin kika fito da alama tare kuka kwana a d'akinsa."
Dafe goshi Inteesar tayi cikin k'osawa da zancen ta ce,
"Kai Mufida ban sani ba ki na sani bazan fad'a maki ba,domin Allah ya tsinewa matar dake fallasa sirrin shimfid'a aurensu a wajen wani."
Dariya Mufida tayi tare da cewa
"Hakane fa mallama Inteesar."
"Yauwa na mance ban fad'a maki ba Gwaggo ta ce zata zo gidan nan tayi maku kwanaki d'ai-d'ai har talatin."
Wani uba tsalle Inteesar tayi cikin farin ciki da jin dad'in da ta dad'e Bata yi shi ba ta tsinci kanta,don ko ba komai idan Gwaggo tazo tasan zata d'an ji dad'i a ranta k'uncinta zai ragu na tsawon kwanakin da Gwaggo zatayi a gidan.
"Ikon Allah wannan shine Allah d'aya gari banban,ke kina farin cikin da zuwan da Gwaggo zata yi yayinda shi kuma mijinki yana bak'in cikin zuwan da zatayi."
Da mamaki Inteesar ke dubanta
"Kamar ya bak'in ciki?"
"Ki rufa mani asiri kar fa ki fad'awa mijinki,na fad'i hakane kawai dan naga likacin da na fad'a masa yanayinsa ya canza zuwa rashin jin dad'i yayinda ke kuma yanayinki ya canza zuwa jin dad'in zuwanta."
Ta'be baki Inteesar tayi yayinda a zuciyarta take ayyana cewa Muhdeen bazai ta'ba jindad'i Gwaggo ta zo gidan nan ba, mi'kewa Inteesar tayi tana cewa.
"Kinga bari na tashi nayi wanka na d'auro alwala lokacin sallah yayi."
"Okay je ki fito nikam Allah ya yafe mani."
Dariya Inteesar tayi ta shiga toilet d'in.
Da misalin k'arfe biyar na yammacin ranar motarsa ta cinno Kai cikin gidan,bayan Direbansa yayi parking ya fito tun kafin ya bud'e masa tuni ya bud'e ya fito da kansa,kai tsaye cikin gidan ya nufa.
A fall ya tarar dasu Inteesar sanye take da riga da siket na atmafa,d'inkin kuwa ya zauna mata ya kar'bi jikinta ba wani makeup tayi ba powder ta shafa sai lipsglow da ta shafa,dogon gashin kanta ta k'udundune shi a cikin d'an kwalinta, Mufida na zaune a gefenta inda take mik'a mata wayarta da ta taho mata dashi,kar'bar wayar tayi cikin jin dad'i ko ba komai ta rage kewa da kad'aicin da take fama da shi.
"Assalamu Alaikum"
Gaban Inteesar ne ya fad'i sakamokon jin muryarsa da tayi,tunawa da tayi cewar ashe fa yau batayi aikin yammacin da yasa ta dingayi ba,zuwan Mufida ne ya mantar da ita, Mufida ce ta amsa masa sallamar.
"Wa'alaika salam"
Kallon ta yayi yana sakar mata murmushi.
"my little one baki tafi ba har yanzun kina nan?"
"Sai zuwa 8 ne direba zaizo d'aukana dama mun kawo maku abincin amarci na k'arshe don kafin na tafi gidan nan sai naci girkin amarya na farko a cikin gidan mijinta."
Murmushi yayi tare da kallon Inteesar
"Amarya baki ga angonki ya dawo bane ko d'an oyoyon nan babu?"
'Daga kanta tayi ta kalleshi da mamaki amma sai taga ya sakar mata murmushi, sunkuyar da kanta tayi ba tare da ta ce komai ba,mamakinsa kawai take wato idan su kad'aine a gida sai ya dinga gallaza mata ya k'untatawa rayuwarta amma idan akwai wani a wurin sai ya dinga nuna mata kulawa,wato fuska biyu ne dashi,tana cikin wannan tunanin bata ankara ba sai ji tayi ya zauna kusa da ita tare da rik'o hannunsa cikin nata,da sauri ta kalleshi sakamakon wani irin shock da taji a rayuwarta wannan ne karo na farko da d'a namiji ya ta'ba ri'ke hannunta ita duk hankalinta a tashe yake sakamakon aiki da bata yi ba Bata San hukuncin da zai d'auka a kanta ba,cikin tsoronsa da take ji ta fara magana.
"Dan Allah kayi hak'uri na mance ne yau ban..."
Kafin ta k'arasa maganar da zata fad'a yayi saurin d'aura yatsarsa a saman le'benta tare da furta kalmar.
"Shhhh"
Murmushi ya sakar mata tare da cewa.
"Kada ki damu dan baki tashi kin tarbe ni ba ba komai,nasan kinyi bak'uwa ne shiyasa kika mance dani."
Kallon Mufida yayi da ta zuba masa ido.
"Sister bari na na d'an shiga ciki na watsa ruwa,sai dai fa kiyi hak'uri zamu barki ke kad'ai."
"Bakomai tunda nazo gidan sabbin aure ai dole nayi hak'uri."
Hannun Inteesar yaja suka nufi d'akinsa ita dai Mufida ido ta bisu dashi,tana murmushi har suka 'bacewa ganinta shi kuma bai saki hannun Inteesar ba sai da suka shiga d'akin sannan ya sakar mata hannu,tare da watsa mata mugun kallo wanda sai da hanjin cikinta suka kad'a.
"Wato saboda ki had'ani da dangina yasa kika fara magana a gaban Mufida ko?saboda ta fahimci halin da muke ciki take ta fad'awa Mummy da Gwaggo ko?"
Kai ta girgiza kanta a sunkuyar da kanta k'asa ta fara magana
"Kayi hak'uri na d'auka zaka mani fad'a dan bany..."
Tsawa ya daka mata
Dalla rufe mani baki mai zubin munafukai,kiyi ta sunkuyar da kai kamar munafuka,duk wanda yazo gidan nan kika kuskura kika nuna cewa akwai matsala a cikin zamantakewar auren mu ko kuma a kika bar wata k'ofa da wani zai gane yanayin zamanmu sai na lahira yafi ki jindad'i kinsan ni ba sai wani ya baki labari na ba sai dai kina wani labarina,ki shiga kitchen ki samu abunda Zaki girka."
Daga nan Nan ya nufi toilet ita kuma ta nufi k'ofar fita.
Kitchen ta nufa inda inda ta dafa masu jallop d'in shinkafa da yaji kayan lambu da busashshen kifi kasancewar akwai komai na girki a kitchen d'in,Koda aka Kira sallar magrib ta gama girkin.
A dinning table ta ajiye abincin da abun sha,falo tazo ta tarar da Mufida da Muhdeen suna fira,sanye yake cikin k'ananun kaya bak'in wando ta jan riga, murmushi tayi ta kalli Mufida.
"To bisimillah Mufida ga abinci can."
"Okay sannu da aiki matar Yaya"
Mik'ewa Muhdeen yayi
"Ni zan tafi masallaci sai na dawo."
Mufida da Inteesar suka had'a baki wajen fad'in
"A dawo lafiya"
Daga nan ya fice, Inteesar ma kuwa d'aki ta koma ta sake yin wanka,ta shirya doguwar riga na material tayi sallar magarib bata tashi ba sai da tayi sallar isha'i,ta yi addu'a sannan ta cire hijabin ta d'aura d'an kwalin material d'in ta fesa turare ta nufi k'ofar fita.
Fitowarta ya yi dai-dai da shigwarsa k'amshin turarenta ne ya daki hancinsa,dubansa ya Kai wajenta ganin tayi kyau sosai ga k'amshin turarenta ya tafi dashi,kauda kansa ya yi daga kallonta.d'akinsa zai nufa, Mufida ta ce "
Yaya kai muke jira fa muci abinci fa,ba yadda yadda ita dole ya dawo wajen inda ya zauna a d'aya daga cikin kujerun dinning d'in,kusan a tare da Mufida suka zauna,inda Mufda ta yi zuba ma Yayanta sannan ta zubawa Inteesar,itama ta zuba nata ta zuzzuba masu lemo da ruwa a cup sannan suka fara ci.
"Ummm ummm Inteesar gaskiya nayi kewar dadd'ad'an girkinki mai dad'i,kinsan ke ta musamman ce."
Sai faman santi take shi kuma Muhdeen yana binta da ido komai ta ce ya ce eh hakane,shima kansa ya ji dad'in girkin don ya ci sosai.
Suna gama cin abincin ne duk da ita Inteesar ba wani ci tayi ba,suna gamawa ne wayar Mufida ta yi k'ara ganin number direban Mummy ne ya sa ta mi'kawa.
"Ni zan tafi anzo d'auka ta."
Inteesar sai taji na dad'i akan tafiyar Mufida Amma ba yadda ta iya.hakan yasa ta ta aika mata da sak'on gaisuwa wajen su Mummy.
Bayan tarfyar Mufida Muhdeen na koma d'aki wayarsa tayi ringing,ganin mummy ce yasa ya d'auka da sauri.
"Hello Mummy barka da dare"
Daga can 'bangaren Mummy ta ce,
"Yauwa son da kazo d'azun na manta ban fad'a maka ba,duk abunda kake yi ka tabbatar gobe ka je gidan iyayen matarka ka gaishesu."
Ransa baiso ba amma ba yadda yadda ita dolensa ya je.
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
Maman Ihsan
Don karin bayani
09065327995
Love u oll😍😘
Comment & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
Maman Ihsan
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
Wannan kagaggen labari ne,banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba,idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba,arashi ne Mai kashe auren wawa.
*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Page3️⃣9️⃣
"Yauwa son na manta ban fad'a maka ba duk abunda kake yi ka tabbatar ka tabbatar gobe ka je gidan iyayen matarka ka gaishesu."
Ransa baiso ba amma ba yadda yadda iya dolensa ya je.
Inteesar bayan ta gama shirinta na kwanciya barci sai ta d'auki wayarta ta kunnah,kamar jira ake tana kunna wayar sai ga kiran Usaman ya shigo wayar.k'walla ne suka cika mata ido ganin ga shi yana kuranta ta d'auka ne ko kada ta d'auka,tunawa tayi da irin k'aunar da yake nuna mata da yawan murmushinsa a gareta,tunani ta shiga yi Anya ko Usaman yasan ta yi aure kuwa?kai bazai sani ba saboda duk lokacin da zai zo wajenta a gidansu bata ta'ba yarda yazo zuwansa biyu kuma shima na farkon sai da ya yi mata k'aryar magani zai kawo mata,zuwansa na biyu kuma ta sanar dashi ya dakata da zuwa sai nan gaba saboda Abbanta baya bari,daga nan kuma