Showing 21001 words to 24000 words out of 149432 words
Chapter 8 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
Bai kulata ba hakan yasa ta dinga juya sitiyarin motar ta kowane 'bangaren, hakan yasa motar ta ku'buce masa ta dinga tangal-tangal akan titi Mum said salati takeyi ta gama tsorata da lamarin 'yarta, Muhdeen sai 'ko'karin 'kwace Hannunta yakeyi amma abin yaci tura ababen hawa sai kaucewa suke suke suna sauka daga Kan titin, tsawar da Mum ta daka mata ne yasa ta cire hannunta tacigaba da kuka, sannan ya samu yayi control d'in motar parking yayi sannan ya fito Yana bawa jama'ar dake gefen titi suka parking Ha'kuri ya basu, wasu basu kulashi ba wasu kuma suna zaginsa wai bai iya tu'ki ba ya d'auki mota ya hau titi zai kashe al'umma, bai ce dasu komai ba ya shiga motar Kai tsaye ya nufi Asibitin sa.
B'angaren su Gwaggo kuwa daga gidan Jabeer Mummy ta Umarci Direban ta yakai su gidansu Inteesar, Kai tsaye gidan ya nufa dasu, bayan sun gaisa da Umma tayi masu jagora zuwa d'akin Inteesar shigarsu yayi dai-dai da farkawar ta daga d'an gajeren barcin da tayi,Yunwa ce ke kwakular cikin ta yasa ta farka, ganin su Gwaggo da Mummy sannan ga 'kawar ta Mufida yasa ta sakin murmushi,Bayan sunyi sallama ta amsa masu ne suka zauna kan tabarmar dake shimfid'e a d'akin ya yin da sai Mufida ce ta haura kan katifar tare ri'ke hannunta cikin tausayawa tace,
"Sorry my besty ya jikin ki?"
Kwa'be fusaka tayi kamar za ta yi kuka sannan tace,
"Wallahi Yayan ki mugu ne ba yadda ban ro'kesa kara yamun allurannan kum..."
Had'iye sauran maganar tayi sakamakon hararar da Umma ta watsa Mata
Murmushi Mummy tayi tare da cewa
" 'Yata kina tsoron Allura ne haka? "
Gyada k'ai tayi tare da sunkuyar da k'ai kasa.
Mummy ce ta cigaba da magana tace,
"To yanzun ya ciwon kan naki?"
"Da sau'ki Mummy tunda na tashi barcin nan naji jikin nawa ya d'an mani sau'ki sosai"
Amsar da tabawa Mummy kenan ba tare da ta d'ago Kai ba, don ta lura tunda tayiwa Muhdeen rashin kunyar Nan Umman ta ta canza Mata fuska.
Gwaggo ce tace "to Allah ya baki lafiya yarinyar kirki"
Inteesar ce ta d'auki jakkar Mufida don tasan Bata rabo da kayan za'ki a cikin jakkar ta hakan yasa ta bud'e jakkar ta Ciro biscuit da chocolate ta Faraci
"Dariya Mufida tayi tare da cewa yanzun haka har yanzun bakici komai ba ko?"
Murmushi tayi tace
"Wallahi bakin nawa ne ba taste shiyasa banci komai ba"
Mummy ce tace
"Amma sai da na fad'awa son cewa ya siye maki fruits a hanya, kenan bai siya ba kenan ko?"
Gabanta ne ya fad'i jin tambayar da Mummy tayi mata, don bazata iya fad'awa Mummy irin wula'kancin da ta yi wa d'anta ba.
Waige-waigen tayi inda ta watsawa Muhdeen fruits d'in a jikin sa,taga an gyra wajen tasan aikin Ummanta ne, sunkuyar da k'ai tayi kafin tace,
"Ya siyo Mummy"
Da yake Mummy bata cika bin Kwakkafi ba yasa tayi shiru, don tasan indai Umarni tabawa d'anta Umarni Yana binta koda bayaso.
Fira suka d'an ta'ba kafin sukayi masu sallama suka tafi, amma Mufida tace bazata tafi yanzun ba sai tayi jinyar Aminiyarta.
'Bangarensu Muhdeen kuwa suna isa asibitinsa kujeran keke na d'aura marasa lapiya aka d'orata akai don bata iya tafiya, bayan an shigar da itane ya Fara aikin cire mata kwalaben da suke shiga kafar sai sannu yake ya jero mata amma sai tayi banza dashi kamar Bata jishi ba, cikin kankanin lokaci ya gama mata dressing Mum d'inta na tsaye akansu bayan ya gama Mata duk abunda yakamata yayi Mata ne ya d'auke su ya mayar dasu gida Bayan ya had'a Mata magunguna duk da ta'ki yarda yayi mata allurar da zai rage mata zogi.
Kai tsaye gida ya nufa yanda ya samu Gwaggo da Mummynsa a falo ya gaishe su, ya juya zai wuce part d'insa part d'insa Mummy ta lura da d'an jinin da ya 'bata masa riga cikin kid'ima tace,
"Son Mai ya faru dakaine?"
Cikin son 'boye Mata yace,
"Ba komai Mummy kawai na gaji ne, zan je na d'an yi wanka na huta"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa,
"karya ba d'abi'ar ka bace kada ka Fara yanzun, nasan yanayin ka idan gajiya ke damunka,hakazalika nasan yanayin ka idan akwai damuwa a tattare dakai,idanunka kad'ai na kalla nasan akwai damuwa a tattare dakai,shin akwai damuwar da d'a zai 'boyewa mahaifiyar sa?"
Shiru yayi cikin sanyin jiki yabasu abunda ya faru Tundaga lokacin da ta ta Umarceni shi yakai Inteesar gida da Kiran da Mufida tayi masa Video calla ta gansa da Inteesar har zuwa haukan da tayi a d'akinta da Wanda tayi suna cikin Motar har suka kusan yin Accident bai 'boye masu komai ba.
Jikin Mummy ne yayi sanyi ta kasa magana, Gwaggo ce ta dinga fad'a tana cewa,
"Ai dama na fad'a maka wannan ba matar auren ka bace, bata dace dakai ba, ashe bayan rashin tarbiyya da take fama dashi harda ta'bin hankali? Yanzun da kwananka sun kare da ta kashe ka, ina fatan dai yanzun zaka rabu da ita ka nemi wacce ta dace dakai"
Juyawa tayi ta kalli Mummy da tayi tagumi sannan tace,
"Fatima"
Mummy ta d'ago ta kalleta tare da cewa,
"Na'am Gwaggo"
Gwaggo ta cigaba da cewa,
"Na san cewa ban isa da d'anki ba ya rainani baya d'aukar maganata da mahimmanci, amma ina mai baki shawara cewa idan har kina son rayuwar d'anki da kwanciyar hankalin sa to ki hana sa auren wannan mahaukaciya tun a waje tayi yun'kurin kashe shi ina ga anyi auran ai sai dai ta da'ba masa wuka tace zata kashe shi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
(Maman ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Wannan Kirkirerren labari ne banyi tunanin Rubuta ta shi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba Arashi ne Mai kashe Auren Wawa
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHEEM*
Page1️⃣7️⃣
"Nasan cewa ban isa da d'anki ba ya rainani baya d'aukar maganata da mahimmanci, amma ina mai baki shawara idan har kina son rayuwar d'anki da kwanciyar hankalinsa to ki hana shi auren wannan mahaukaciya, tun a waje tayi yun'kurin kashe shi ina ga anyi auran? Ai sai dai ta da'ba masa wuka tace zata kashe shi."
Tana kaiwa 'karshen maganarta ta mi'ke ta nufi d'akinta, jikin Mummy ne yayi sanyi, kallan Muhdeen tayi tace,
"Idan ka gama abunda zakayi ka sameni a d'akina"
Bata jira cewarsa ba ta wuce ta nufi d'akinta, jiki a sanyaye shi ma ya nufi part d'insa
Bayan sallar isha'i Mummy tana zaune kan sallaya bayan ta idar da sallah tana Addu'o'i, Muhdeen ne yayi knocking yana jiran ta bashi izinin shigowa, bayan ta idar da addu'a ta bashi izinin shigowa, da sallama d'auke a bakinsa ya shiga bayan ya zauna ya kalleta cikin girmamawa yace,
"Barka da dare Mummy"
"Yauwa"
Ta amsa masa a ta'kaice, shiru ya d'an biyo baya karin ta kalle shi ta Fara magana,
"Muhammad"
Jin yadda ta kira sunansa da Muhammad ne yasa ya tattara gaba d'aya hankalinsa da nutsuwarsa akan ta, don yasan bata cika kiran sunan sa kai tsaye ba sai dai ta Kira sa da son, ta cigaba da magana tace,
"Ba na son nayi maka dole akan abunda nake so nafi son na baku dama ku za'bi za'bin ranku akan koma meye matukar hakan bai sa'bawa addinin musulunci ba, musamman akan magamar aure tunda shi aure ba abu bane na wasa kuma ba ni ce zanyi maka zaman auren ba kai da kanka ne shiyasa nafi son kai da zakayi zaman auren ka neme wacce ka ke so take son ka ba tare da anyiwa ko wannen ku dole ba domin d'orewar zaman lapiya da kwanciyar hankalin ko wannen ku, maganar da Gwaggo tayi fa abun dubawa ne, domin jikina yayi sanyi da lamarin yarinyar nan yakamata kayi nazari sosai akan maganar Gwaggo kuma kayi la'akari sosai akan abunda ya faru, naso ace nitsatsiyar yarinya ka samu mai sanin yakamata mai tarbiyya da ri'ko da addini, ba wai Umarni nake baka akai ba shawara ce idan tayi maka idan kuma har yanzu kana nan akan bakanka to shikenan Allah ya tabbatar muna da alkhairi.
Kai ya jinjina dare da cewa,
"Ameen ya rabbi Mummy nagode, ki tayani da addu'a"
Kai ta jinjina Don ta lura da cewa 'Danta yayi nisa sosai akan Son Sumayya baya jin kira, don ta lura laifinta ma baya son ana fad'a, lura da hakan yasa tace,
"Kullum cikin maku Addu'ar nake Allah ya tabbatar maku da abunda yafi zama alkhairi a gareku"
Amsawa yayi da Ameenn kafin ya mi'ke ya nufi 'kofar fita, ya juyo ya kalli Mummy yace,
"Ina Mufida ne tunda na dawo naga alamar bata gidan nan"
Murmushi Mummy tayi tace,
"Ina kuwa zaka ganta tana can tana jinya"
Kallon ta yayi cikin rashin fahimtan inda maganarta ta dosa yace,
"Jinya kuma Mummy?Yaushe ne ta Fara rashin lapiyar ?"
Dariya Mummy tayi
"Ai ba jinyar kanta takeyi ba,jinyar Aminiyarta ce Inteesar,kasan sha'kuwar dake tsakanin su barci ne kawai yake rabasu"
Shiru yad'anyi na lokaci kafin yace,
"Amma duk da haka dare yayi yanzum yakamata ace ta dawo gida"
Wayar sa ya Ciro daga cikin aljihun jallabiyar daya Sanya a jikinsa, Number Mufida ya lalubo my little sister sunan da yayi serving number ta dashi kenan,Danna Mata Kira yayi tare da Kara wayar a kunnen sa,
Mufida dake zaune Ita da Inteesar suna cin tuwon shinkafa da miyar zogale Wanda Umma ta girka,sai Santi take,Don taji dad'in girkin sosai,ita ko Inteesar dakyar taji loma uku Don Bata Jin dad'in komai,Wayar ta CE tayi ringing yasa ta duba ganin sunan Mai Kiran ne yasata sakin Murmushi,My lovely brother shine sunan da tasa masa ,d'agawa tayi tun kafin tayi magana tajiyo muryasa yana cewa,
"Me kikeyi a gidan mutane dai-dai wannan lokacin?yanzun Nan kidawo gida"
Bai jira cewarta ba ya katse Kira Don Bai Bata damara tayi magana ba,kallon Inteesar tayi cikin sanyin murya tace,
"Kinga Yaya Wai ma dawo gida dare yayi,"
Marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka tace,
"Kinji Yaya Wai na dawo gida yanzun dare yayi"
Da sauri Inteesar ta kalle ta tare da cewa,
"Ba kinyi mani al'kawarin cewa tare Dani Zaki kwana ba?"
Shiru tayi ma 'Danyi kafin ta saki murmushi ta kalli Inteesar cikin jinda tace.
"Na samu Mana mafita cikin sau'ki,Dady zan Kira na sanar dashi cewa zan kwana tare dake bakida lapiya,nasan bazai hanani ba."
Murmushi Inteesar tayi tace,
"Gaskiya Kam nima nasan cewa bazai hanaki kwana a gidanmu ba"
Wayarta ta d'auka tare da lalubo number Dady,bayn ta Kira number ne ta Kara wayar a kunne bugu biyu ya d'aga tare da cewa
" Assalamu Alaikum"
Mufida tayi murmushi tace,
"Wa'alaika Salam Dady Barka da dare ya aiki?"
"Alhamdulillah yanzun ma insha Allah zan kamo hanyar gida"
Ya 'karasa maganar Yana 'ko'karin kashe Kiran,Jin muryarta Tana magana yasashi dakatawa Yana sauraren ta.
"Dady dama Ina son sanar dakai ne Inteesar ce bata da lapiya Ina gidansu zamu kwana tare da ita ne"
Cikin sauri hankali a d'an tashe yace,
"Subhanallahi me yake damunta?bakuje Asibiti bane?"
Murmushi tayi tare da cewa,
"Kada ka damu Dady da sau'ki,Yaya ya dubata ya Mata allura da magunguna"
Ajiyar zuciya ya sauke yace,
"Okay okay ki bata wayar"
Mi'kawa Inteesar wayar tayi,bayan ta ka'bi wayar ta Kara a kunne.
"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaiki Salam Inteesar ya jikin naki da sau'ki ko?"
"Eh Abba da sau'ki Alhamdulillah"
"To Masha Allah, Allah ya baki lapiya yasa ya zama kaffaran jiki,ki maida hankali wajen Shan magani kinji 'yata Allah yayaye maki,saida safe"
Daganan ya kashe Kiran inda ya shiga bayan motar sa direban sa yaja suka kama hanyar gida.
Mufida tayi murmushi tana kallon kawarta tace,
"Allah sarki yanzun gobe Ni kad'ai zan tafi school,gasky zanyi kewarki sosai Allah dai ya baki lapiya,gashi this time muma Shirin kammala secondary d'in mu zamu zama 'yan matar jami'a"
Dariya ta kece dashi Tana fad'in,
"Wai waya ganmu a jami'a shikenan fa mun zama manyan Mata,Koda yake mum wuce yara tunda a yanzun dukan mu kusa almost 18 years,yanzun cikin kasashen waje wata 'kasa kike son muyi karatun mu a can?"
Murmushi Inteesar tayi tare da cewa,
"Waye ubana dazan tafi kasahen waje karatu? niba 'yar kowa ba bazankai kaina inda Allah baikaini ba ko anan Nigeria ma idan nasamu Abba ya..."
Bata Kai 'karshen zancenta ba tayi shiru ganin irin 'bacin ran da tagani a fuskar Mufida,
Cikin rashin fahimtan fushin nata tace,
"Mufida me ya faru Naga kin canza fuska yanzu-yanzu?"
Tura baki Mufda tayi tace,
"Ba dole na 'bata rai ba tunda kin nuna mun cewa nidake ba Abu d'aya bane,har zakice Wai ke 'yar gidan waye da Zaki karatu waje,bayan kinsan duk abunda Dady da Mummy sukayi Mani zasuyi maki"
Murmushi Inteesar tayi tare da fad'in
"Mufida nasan iyayenki ne suka d'auki nauyin karatuna lokacin da mahaifina ya rasa kud'in da zai biya Mani School fee suka d'aura daga inda ya tsaya,yanzun muna Shirin kammalawa,Banda suturu da sauran ababen bu'kata wannan ma kad'ai ya Isa Allah ya saka da alkhairi,yanzun kina maganar zuwa wata 'kasa ace Nima dani?ke Ni Koda zancigaba da karatuna to anan Nigeria ne kuma a Niger state, IBRAHIM BADAMASI BABAN GIDA(I.B.B. LAPAI)
Marairace fuska Mufida tayi tace,
"To muje Al-HIKIMA University na Ilori mana"
Shiru Inteesar tayi batare da tace komai ba.
Gaba d'ayan su suna zaune a dinning room suna dinner Dady, Mummy,Gwaggo,sai Muhdeen,suna zaune kowanen su nacin Abincinsa Amma banda Muhdeen dake jujjuya cokalin ya kasa cin komai,tunanin halin da Sumayya ke ciki yake, Gwaggo ce ta ta'be baki tace,
"Indai tunanine bakama Fara ba yanzun zaka saka 'kafar wando dashi, matu'kar kace wannan mahaukaciya zaka aura,"
Baice Mata komaiba cikin son kawar da zancen yace,
"Mummy Wai har yanzum Mufida bata dawo gida ba?kuma fa har Kiran wayarta nayi nace ta dawo Amma ta kasa dawowa"
Dady ne yayi magana yace,
"Ta kirani ta sanar dani can gidan zata kwana,tayi jinyar Inteesar sai gobe da safe zata dawo tayi Shirin zuwa school, kuma an amince mata"
Shirin Muhdeen yayi Don baiso hakan ba Amma tunda Dady ya amince dole tasa ba yadda za'ayi dole ya hakura sai dai yace,
" In Banda abunta meye na wani kwana a gidan mutane,nifa Sam hankalina baya kwanciya da irin haka"
Gwaggo tayi saurin cewa,
Idan Kai hankalin ka baya kwanciya mu namu Yana kwanciya,tunda tare da Mai cikakken hankali zata kwana,bada Mai cutar kwakwalwa ba ballantana muyi tunanin kada tayi barci mahaukaciyar ta illata muna ita,"
Ta karasa maganar Tana Kai lemu a bakinta, Muhdeen ransa ya 'baci Don yasa magama take fad'a masa a fakaice wato Sumayya ce mahaukaciyar ,Bai gama tunanin da yakeyi ba ya koma jiyo muryarta Tana fad'in,
"Ina tausayawa mijin mahaukaciya"
Take Muhdeen yabar wajen ransa a 'bace don Yana shakkar Dadyn sa ne kada yaha yanayiwa mahifiyar sa rashin kunyar,da badon haka ba da yaayar Mata da amsa.
Kwanci tashi ba wuya a wirin ubangiji,yau su Inteesar da Mufida suka kammala jarabawar su ta kammala secondary School,kuma yau ne ya rage saura sati biyu bikin Muhdeen da sumayya,kuma yaune Muhdeen da Sumayya zasu dawo daga 'kasar Dubai inda sukaje had'a kayan lefen Auren su,don sumayya for ta'ki yadda Wai Muhdeen ko waning nasa ne zai siyo Mata kayan lefe,ta dage dole sai dai suje Dubai ita dashi su siyo kayan lefen acan,haka duk kayan da Muhdeen ya za'bar Mata zatace ita bayyi Mata ba,sai dai ta za'bo wasu kayan daban ,a cewar ta abunda ya burge wani baya burge ta,Koda ta d'auko kaya taga Muhdeen ya yaba kayan zata mayar dashi,akasarij kayan da d'auka duk Basu kwanta masa ba Amma ba yadda zaiyi da ita,Haka suka cika akwatuna goma Sha biyu da kaya hatta sarka da d'an kunne na Gold ita ta za'ba.koda taga ya siyo wasu dogayen rigunan abaya kala daban-daban masu kyau tace Bata son kayan da zasu takura ta,ya nuna Mata cewa 'kannensa ya siyawa Asiya da Mufida Suma ya cika masu Babbar jaka da tsaraba har da Mummy da Gwaggo duk ya masu tsaraba.koda suka dawo yake nuna masu kayan lefe Mummy dai cewa tayi Allah Sanya alkhairi, Gwaggo ne dai tace Allah wadarai da wannan kayan Don Bata ga kayan arziki a wajen ba.
'Bangaren Inteesar kuwa kamar yadda tayi alwashi hakan ne ta kasance, bata sake taka 'kafafuwar ta zuwa Gidan su Muhdeen ba ko kafin su gama Exam idan ta shirya zata tsaya kan hanya ta jira har sai Mufida da direban Mummy yazo tabisu ko Mummy da Gwaggo sun kirata zata kirkiri abinda zata fad'a masu da zai hanata har sun gaji sun kyaleta. Mufice ta kawo Mata Atamfofi da less da material na ankon bikin tace suje wurin tailorn da Mummy ke kai masu d'inki haka kuwa aka yi ta sallami Umma suka wuce wurin Hamza Tailor, bayan sun za'bi irin wanda suke so ne sukayi masa sallama suka tafi, don dama Mummy ce zata tura masa Kud'in,
Har zasu shiga mota inda direba ke jiran su sai Inteesar ta hangi wani makaho ya taho Kan titi da 'yar sandarsa Yana dogarawa ga Mota na zuwa a bayan sa,ba tare da tayi tunanin duna janya ba tahau titin a guje kafin ta ankare bisa tsautsayi sai ji tayi mota ta kad'eta ta Fadi akan titi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
( Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta ta shi dan cin zarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.
Page 1️⃣8️⃣
Ba tare da tayi tunanin duba hanaya ba, kafin ta ankare bisa tsautsayi sai ji tayi mota ta kad'eta ta fad'i kan titin, Mufida dake can gefe ce ta kwalla mata kira.
"INTEESAR!!!"
Ta karaso a guje ya yin da matu'kin motar da ya kad'e Inteesar Shi ma ya karaso direban Mummy sai salati ya ke yi, ya yin da Mufida ke kuka kamar ranta zai fita ganin 'kawarta kwance a sume, rungumeta tayi ya yin da wata mata dake wajen ta d'auko Inteesar d'in ta saka ta bayan motar mutumin da ya kad'eta, jin yana cewa ad'auko ta su tafi asibiti, da sauri Mufida ta shiga bayan motar tare da janyo Inteesar ta rungumeta idonta na zubda hawaye Direban Mummy