Header Ads
Showing 87001 words to 90000 words out of 149432 words

Chapter 30 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1380

Ads at the middle of Article

Aunty Abla tayi tare da shafa gefen fuskarta ta ce,


"Jiya munyi waya da Mummy ta ce da zaran Gwaggo ta koma zata zo ta duba ki, nasan da Gwaggo bata nan da tuni tazo ta duba ki, kuma Ummanki kinsan tana da kawaici ba lallai tazo yanzun ba kiyi hak'uri Mummy zata zo maybe gobe ko jibi"


Shiru tayi tare da lamo akan cinyar Aunty Abla, shafa fuskar inteesar tayi abun mamaki sa taji sanyin hawaye a hannunta, kasancewar inteesar ta juyar da fuskarta gefe ba Wanda yaga hawayen da ke tsiyaya, lura da haka yasa Aunty Abla sa hannayenta ta goge mata hawayen, sanna ta ja hannunta zuwa d'aki ta ce,


"Taso mu shiga ciki."


Ba musu tabita suka shiga d'akin intesar tare da tura k'ofar, Muhdeen dai binsu da Ido yayi yana zullumin inteesar ta sanar da ita wani abu mara dad'i, Hajiya Bilkisu ma bayansu ta bi.


A Kan gado Aunty Abla ta zaunar da inteesar ita ma ta zauna gefenta, zuba mata Ido tayi na tsawon mintuna biyu tana nazarinta, dai-dai lokacin Hajiya Bilkisu ta shigo d'akin bakinta d'auke da sallama, gaba d'ayansu suka amsa sallamar ta shigo ta zauna saman side drawer, Aunty Abla ta ce,


"Daughter me ke faruwa?"


Sunkuyar da kanta k'asa tayi


"Bakomai Aunty Abla"


Girgiza kai tayi


"Akwai komai ki sanar dani, ba haka kike ba duk kin rame ga idanunki ma alamar kinci kuka,da alama kina cikin damuwa, nasan ba sonki yake ba zai iya musguna maki ba Wanda ya sani, shiyasa nake son ki sanar dani wata kila akwai irin taimakon da zan maki, yana dukanki ne? "


Girgiza kai tayi alamar a'a


"Yana zaginki ko cin zarafinki?"


Nan ma kai ta girgiza alamar a'a


"Akwai wani abu da yake maki Wanda baki so ne"


Shiru tayi ba tare da ta ce komai ba, ganin bata da niyyar magana sai hawaye kawai dake fita daga idanunta yasa Aunty Abla janyo ta jikinta ta rungume ta tare da d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi.


"Nasan kina cikin damuwa sosai duk da cewar ni kamar dangin miji ne a gare ki amma ina son ki d'auke ni matsayin uwa a gare ki, kamar yadda nake jinki kamar 'yar da na haifa a ciki na, kamar yadda ba zaki iya 'boyewa mahaifiyarki damuwarki ba haka nima kada ki 'boye mani yadda na same ki a haka zuciya ta taji ba dad'i, inteesar me ke damunki ya zamantakewarki da Muhdeen yake?"


Goge hawayen fuskarta tayi ta shiga bawa Aunty Abla labarin zamansu tunda daga lokacin da yake bautar da ita da ayyukan da suka fi k'arfinta har zuwan Gwaggo Wanda lokacin ta samu 'yanci har zuwa yanzun da suke tare.


Aunty Abla da Hajiya Bilkisu sun tausaya mata sosai, ajiyar zuciya Hajiya Bilkisu tayi tare da cewa


"Kenan ba wani abunda ya ta'ba shiga a tsakaninmu na auratayya?


Kai ta d'aga mata alamar eh


Murmushi tayi tare da cewa


"Ki k'ara hak'uri akan wanda kikayi a baya, da zaran ya shigo hannunki sai yadda kikayi dashi, saboda Allah ya baki wata irin baiwa wanda mijinki bai san da shi ba, amma da zaran ya San da hakan to wallahi kinfi k'arfin wulak'anci a wajensa, domin samun mace irinki yana da matuk'ar wahala kuma duk namijin da ya same ki kingama mallake zuciyarsa sai yadda kikayi da shi."


Zuba mata ido Aunty Abla tayi kafin ta ce,


"K'awa ta ta k'ara hak'uri zuwa yaushe? sai ta cigaba da zama cikin bak'in ciki da k'unci wanda ba'asan ranar wucewarsa ba?"


"Kada ki damu nan bada dad'ewa komai zai zamo labari, idan kinyi nazari a cikin labarin da ta bayar ai zaki fahimci ya fara sha'awar kusantarta, tunda ya fara kuwa bai wuya zai shiga hannunta sai yadda tayi dashi."


Kallon inteesar tayi tare da cewa


"Duk ranar da ya nemi kusantarki kada ki k'ara guje masa kamar yadda kikayi a baya."


Da sauri ta kalle ta


"Eh hakan zakiyi ba ki da wani za'bi








Daga alk'alamin ✍️


Zainab Abdullah K.N T
(Maman Ihsan)






Don Karin bayani


09065327995




Love you oll😍😘


Comments and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.




*SANARWA*


Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auran wawa.




*BISIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*


Page5️⃣2️⃣




"Duk ranar da ya nemi kusantarki kada ki k'ara guje masa kamar yadda kikayi a baya."


Da sauri ta kalle ta


"Eh hakan za'ayi baki da wani za'bi"


Tura baki tayi tare da cewa


"Shifa ya ce baya sona kuma da zarar matarsa ta dawo gidan nan zai rabu da ni, to kuma mutumin da baya k'auna ta zan bawa kaina? ya raba ni da budurci na fa kenan sannan ya rabu dani."


Ta k'arasa maganar tana sunkuyar da kanta k'asa,


Dariya sukayi dukansu, Aunty Abla ta d'ora da cewa


"Wa ya fad'a maki zai rabu dake?"


"Shine da bakinsa ya fad'a mani fah."


"Ya dai fad'a ne amma bai isa ya rabu da ke ba, domin rabuwa da ke tamakar bijirewa iyayensa yayi, kuma nasan shi yana da biyayya bazai iya bijirewa maganarsu ba, don haka idan kina tunannin zai rabu dake be to ki daina, kisan yadda zakiyi ki mallaki zuciyarsa kawai."


"Nima fa ba sonsa nake ba, jira nake ya rabu dani kawai na koma gidanmu."


Murmushi kawai Aunty Abla tayi tare da cewa


"To kiyi ta addu'a duk abunda yafi zama alkhairi a gare ki Allah ya tabbatar maki da shi."


Daga nan Hajiya Bilkisu ta bud'e jakkarta ta fito da wasu goruna guda uku, ta mik'awa inteesar d'aya kar'bi ki shanye shi nan da kwana uku safe da yamma zaki dinga sha."


Ta d'auko wani goran ta mik'a mata ta ce,


"Wannan rubutun kuma ki shanye shi yanzun nan ki bani goran."


Ba musu ta kar'ba tare da yin Bisimillah ta shanye ta mik'a mata goran, sai ta mik'a mata cikon ta ukun tare da cewa


"Wannan zumar kuma zaki sha cokali d'aya a rana, sai kuma washe gari sau d'aya ake sha a rana saboda yana da k'arfi."


Jakarta ta bud'e ta fito da wani turare ta ce,


"Wannan dai kinsan irinsa na tsugunno ne, na maki amfani da shi lokacin kina gida na."


Ta ciro wasu ta ce


"Wad'annan turarurruka ne da sabulun wanka ki dinga amfani da su kowane lokaci."


Nasiha suka k'ara mata da shawarwari suka k'ara bata hak'uri, sannan sukayi suka tafi, har zata raka su suka ce ta yi zamanta komawa tayi ta kwanta.


A falo suka samu Muhdeen yana waya, ganinsu yasa ya katse kiran tare da cewa


"Aunty har kun fito?"


Hajiya Bilkisu ce tayi masa sallama ta fice, yayin da Aunty Abla ta zuba masa ido ba tare da ta ce komai ba, tunani ya shiga yi ko dai inteesar ta kai k'ararsa ne? bai gama tunani ba ya ji murayar Aunty Abla na cewa


"Son kaji tsoron Allah yarinyar nan inteesar amana ce a wajenka, kamar yadda ba'ayi shawara da kai ba aka d'aura maka aure da ita haka itama, ba'ayi shawara da ita ba aka aura mata kai, hak'uri zakayi da ita ko baka sonta ka kyautata mata ka sauke duk wani hakki nata da Allah ya d'ora maka, kada kaga cewa ita waccan soyayya ce ta had'aku ka fifita ta akan inteesar, Allah yana ji kuma yana ganinka kuma zai tambaye ka, kafa ka tashi a ranar tashin alk'iyama 'barin jikinka yana karkata, ka sani kake sani, bata kowa sai ta baro gidan iyayenta saboda kai kada ka wulak'anta ta."


Daga nan bata sake magana ba tayi ficewarta, don har ga Allah taji zafin abunda yakewa inteesar a baya, musamman da ta tuna cewa farkon aurensu ya dinga wahalar da ita ba tausayawan alhalin bata masa laifin komai ba.


Cikin sanyin jiki ya koma kan kujera ya zaun, yana tunanin maganganun da Aunty Abla ta sanar da shi kuma yasan tabbas bai kyautawa inteesar ba, a d'an zamansa da ita ba wani abu na kyautatawa ko adalci da ya mata, sai musguna mata da wahalar da ita da yayi, kuma yasan tabbas a halin yanzun idan ya ce zai kwatanta adalci a tsakaninsu to za'a samu matsala da Sumayya, domin sai da ya sanar da ita cewa inteesar kamar mai aiki ce aka kawo mata ba kishiya ba kuma ko kallo bata ishe sa ba sannan ta yadda ta dawo, tunda ba abunda ta iya inteesar ce zata dinga mata.


Mik'ewa yayi ya nufi d'akinta, tura k'ofar d'akin yayi ya shiga da sallama, d'agowa tayi da sauri ta kalle shi cike da fargabar me zai biyo baya, ta dai san arziki da alkhairi baya sa ya shigo d'akinta, idan ya shigo to wani muguntar be zai mata, a zuciyarta ta ce, na shiga uku me kuma nayi masa ya biyo ni d'aki na? ko dai aikin wahalar ne zan cigaba tunda Gwaggo ta tafi, sannan wannan ne karo na farko da ya shigo da sallama a d'akinta, cikin sanyin muryarta ta ce,


"Wa'alaika salam"


K'arasowa yayi gabanta ya ce,


"Wace magana kukayi da su Aunty Abla?"


Gabanta ne ya fad'i amma sai ta dake ta ce


"Bakomai"


Zuba mata Ido yayi yana karantarta kafin ya ce,


"Akwai yanayin maganarta ya tabbatar mani da cewa akwai maganar da kika fad'a mata, wato ke baki iya rik'e sirrin gidanki ko?"


"Ba abunda na fad'a mata ta ce,wai na rame ne "


Shiru yayi sannan ya d'ora da cewa


"Mata ta dai ta dawo yau, saboda haka kiyi mata biyayya a matsayinta na uwar gida wacce kika zo kika tarar, dole ki girmama ta,bayan haka kuma ko a shekaru ba tsaranki bace ta girme maki nesa ba kusa ba, sannan kuma ita ta taso daga gidan iyayenta bata aikin komai masu aiki ke mata gyaran d'aki da girki bata komai sai dai ayi mata bata iya ba, kuma ni bana son ace 'yar aiki zata girka abincin da zanci, kuma bana son ace 'yar aiki zata shiga ta gyara mani bedroom, shine nake neman alfarma a wajenki da ki dinga taimaka mata da ayyukan tunda bata iya komai ba, kinga matsayin ya take a gare ki shekarunta talatin ke kuma shekarunki goma Sha takwas kinga ai ta cancanci kiyi mata ko?"


Shiru tayi tana nazari ba tare da ta ce, komai ba, ganin shirun nata yayi yawa ne yasa shi cewa


"Kinsan cewa na tsani shariya ko?"


Ahiyar zuciya ta sauke ta d'ora da cewa


"Zan iya mata gurkin abincin da zata ci kuma na wanke kwanikan da ta ci, amma gaskiya bazan iya zuwa na gyara mata d'aki na wanke toilet ba."


Zuba mata ido yayi kafin ya ce,


"Saboda me? kinfi k'arfin haka ne?to ki kafin a aura mani ke ni nake wannan aikin ballantana ke."


Murmushi tayi ba tare da ta kalle shi ba ta ce,


"Ballantana ni 'yar talaka ko? nasan abunda zaka fad'a kenan, matarka ta gama zagin iyaye na kaima yanzun zaka d'ora daga inda ta tsaya."


Ta k'arasa maganar tana goge k'walla da suka taru mata a ido.


"Ki kika fad'i haka, kuma na gama yanke shawara dan haka umarni na baki dole kiyi."


Daga nan yasa kai ya bar d'akin, a falo ya tarar da Sumayya da alama shi take nema, tana ganinsa ya fito daga d'akin inteesar ta tamke fuska ranta a 'bace ta ce,


"Baby me kaje yi a d'akin wannan kucakar yarinyar?"


"Naje sanar da ita ayyukan da zata yi ne."


Hannunta yaja suka nufi bedroom d'insa.


Haka rayuwa tayi ta tafiya, kullun inteesar idan ta idar da sallar asuba bata kowa ta kwanta, zata fara gyaran gidan idan ta gama ta shiga kitchen da had'a masu breakfast, bayan ta kammala ne lokacin da suka tashi daga barci zata shiga bedroom d'insu ta gyara masu, su kuma su zauna suna breakfast, duk randa zata shiga ta gyarawa Sumayya d'aki zara tarar ko ina a hargitse da kaya hatta kayan jikinta idan ta cire anan zata barsu zube a k'asa, ko kuma a watsa su saman gado.


'Dakun Muhdeen ne dai idan ta shiga bata shan wahalar gyarawa, domin komai a tsari yake yinsa ko kayan datti ne zai zuba a basket dake cikin toilet suke zuba kayan datti, idan mai wanki da guga yazo a had'a masa.


Wata rana bayan inteesar ta gama aikin gidan, har da breakfast ma ta kammala masu,shiru shiru taga basu fito ba kasancewar wani lokacin Muhdeen na zuwa Asibiti da safe yasa tayi tunanin ko ya wuce ne, bayan ta gama gyara masa d'akinsa ne ta nufi d'akin Sumayya don ta gyara mata, tunda wani lokacin ko Sumayya na barci inteesar na shiga ta fara wanke mata toilet d'inta, don haka ta tura k'ofar tare da cewa


"Assalamu al..."


Bata k'arasa yin sallamar ba ta dakata sakamakon abunda ta gani, Sumayya ce daga ita sai Bra da pant tana zaune akan cinyar Muhdeen, yana sanye da boxer kamar zasu shuge jikin junanasu, k'arar k'ofa ne ya dawo da hankalinsu gare ta, kallo d'aya tayi masu ta kauda kanta gefe tare da cewa


"Kungarce ni, na shigo maku a lokacin da bai dace ba."


Daga nan ta fita taja masu k'ofar,Sumayya ce ta kalli Muhdeen ta ce,


"Wannan banzar yariyar jaka haka aka fad'a mata ana shiga d'akin ma'aurata ba neman izini? idan na fita wallahi sai tayi nadama."


Kallonta yayi tare da cewa


"Baki ga ta baki hak'uri ba?"


"Hak'uri da ta bayar bai isa yasa next time kada tayi ba."


"To idan ba hak'uri ba me zaki mata?"


"Dukanta zanyi gobe ba zata sake ba."


"Kada ki ta'ba 'yar mutane kinji na fad'a maki,don banga abun dukanba."


Yana fad'ar haka ya janye ta d'aga k'afarsa, jallabiyarsa ya saka ya nufi d'akinsa, a falo ya hange ta zaune tana kallon T.V kallo d'aya yaui mata ya janye idanunsa daga kallonta.


Da misalin k'arfe goma na dare Sumayya tana zaune gaban dressing mirror tana kwalliya, k'ananun kaya riga da wando ne a jikinta, kayan sun matse ta sosai duk suffar jikinta a bayyanne, bayana ta gama kwalliyar ne ta d'auki mayafinta k'arami ta yafa ta d'auki wayoyinta ta saka a hand bag tana k'ok'ari ta d'auki hand bag sai Muhdeen ya turo k'ofat ya shigo, rungume ta yayi ta baya tare da cewa


"Baby wannan irin kwalliya haka kamar zaki fita?"


Janyo ta yayi bayan ya zauna akan gadon sai ya zaunar da ita akan cinyarsa ya ce


"Duk wannan kwalliyar ni kikayiwa haka?"


Juyo da fuskarta yayi da niyyar sumbatarta sai tayi saurin janye fuskarta ta ce,


"Kai fa wallahi ka cika jaraba nifa nan shirin zuwa party nayi?"


Da sauri ya kalle ta


"Shirin Ina kikayi?"


"Party nace Mana, kaga ma su jumy suna k'ofar gida suna jira na."


Da mamaki yake kallonta ya ce


"Ba zaki je ba saboda ina da buk'atarki."


"Ai dama kai kullun cikin buka'ta kake, ka cika takura,ni kuma wallahi tunda na shirya zuwa party sai naje ."


"Ina mijinki kike fad'awa haka?"


"Ai dole na fad'a maka gaskiya na fad'a, tun kafin ka aure ni ina zuwa, kuma aurenka bazai hanani zuwa ba,don idan nayi niyyar abu sai nayi bana sauraron kowa."


Daga nan ta fice da mamaki ya bita da kallo, mik'ewa yayi ya nufi d'akinsa, don dama shi mai yawan buk'atar mace ne, take mararsa ta fara masa ciwo,Kan gado yayi rub da ciki.


Inteesar kuwa tana d'akinta tayi shirin kwanciya barci, wayarta ta fara ringing dubawa tayi taga Mufida ce da mamaki ta zubawa wayar idanu ta ji gabanta ya fad'i, d'agawa tayi tare da cewa


"Assalamu alaikum, Mufida lafiya kuwa kira da daddaren nan?"


Ajiyar zuciya Mufida tayi tare da cewa


"Amma bakiji abunda ya faru ba ki?"


Cikin tashin hankali ta ce,


"Me ya faru Mufida, dan Allah ki sanar dani mana"


'Dan jima tayi sannan ta ce,


"Inteesar kinsan kuwa Ummanki ba lafiya sosai tana kwance a gadon Asibiti na general hospital."


Gabanta ne ya fad'i rass jefar da wayar tayi duk ta rud'e ta rasa inda zata bi,hijabinta ta janyo ta saka a guje ta nufi hanyar fita har zata fice sai kum ta tuna bata sanar da mijinta ba, don haka ta nufi d'akinsa.


Knocking tayi har sau uku shiru, yana nan yana fama da ciwon mara,jin knocking yasa ya gane inteesar ce don yaji k'arar tashin motar Sumayya, hamdala yayi a zuciyarsa don yasan ya samu mafita, dak'yar ya iya cewa ta shigo, da sallama ta shigo d'akin hangisa tayi yana juye-juye daga gani baida lafiya, a guje ta k'arasa ta ce


"Yaya baka da lafiya ne?"


'Dago rinannun idanunsa da suka rikid'e zuwa ja ya kalleta, gyad'a mata kai kawai yayi.


Cikin tausayawan irin nata ta ce


"Sannu yaya Allah zai baka lafiya kasha magani.?"


"Cikin muryarsa da bata fita sosai ya ce


"Kece maganin"


Bata ji me ya ce ba ta ce,


"Dama nazo ne na nemi izininka zanje Asibiti Umma ta ce bata da lafiya, tana kwance a Asibiti."


Girgiza mata kai yayi


"Dare yayi bai kamata ki fita ke kad'ai ba "


"Cikin muryar kuka ta ce "Yaya dan Allah ka taimaka mani ka kaini naganta ko hankali na zai kwanata"


Da hannu ya mata alama da ta zo kusa da shi, ba musu ta k'arasa hannunta ya rik'e


"Zan taimaka maki na kaiki amma bisa sharad'i"


Da sauri ta ce


"Wane sharad'i Yaya?"


"Nima ina buk'atar taimakonki, idan kika taimaka mani nima zan taimaka maki na kaiki, idan kuma kika k'i to ba zan ta'ba kaiki ba kuma ba zakije b kwata-kwata."


Kuka ta soma tana cewa


"Na amince da kowane sharad'i indai zaka kaini naga Umma na."


Hijabin jikinta ya cire ya janyo ta zuwa jikinsa ya rungume, bakinta da nasa yake k'ok'arin had'awa nan ta soma kicinuyar k'wacew, kallonta yayi tare da cewa


"Cikin sharad'i kike, bijire mani dai-dai yake da rashin zuwanki wajen Ummanki, ko baki son zuwa?"


Kai ta gyad'a masa alamar tana so


"To don haka ki barni nayi abunda zanyi sai mu tafi kinji ko?"


Cikin sanyin muryar kukanta ta ce,


"To na bari?"






Daga alk'alamin✍️


Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)






Don k'arin bayani


09065327995






Love u oll😘😍


Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullah K.N.T
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads