Header Ads
Showing 120001 words to 123000 words out of 149432 words

Chapter 41 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1361

Ads at the middle of Article

kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan duk abu d'aya ne, sannan idan har kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group, don ko kinshiga idan baki comments zan fitar da ke ne.




*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.




*SANARWA*


Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.




*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*


Page6️⃣7️⃣


"Wace ce matarka? Inteesar kake nufi? to ai naga ita wacce kake Kira matarka bata ma san kanayi ba, isaka ne ke wahalar da mai kayan Kara."


Muhdeen ne ya fusata ya shak'o wuyar rigar Usman ya ce,


"Ka iya bakinka ka san kuma da wa kake magana, idan baka fita daga harkarta ba zan d'auki mummunar mataki akanta."


Dai-dai lokacin Abban Inteesar ya k'araso K'ofar gidan, ganinsu a hakanan yasa ya k'araso wajensu da sauri


"Subhanallahi Muhammad me ke faruwa ne?"


Sakin wuyar Usman yayi tare da hankad'a shi gefe yana huci kamar wani mayunwacin zaki, Usman ne ya durk'usa ya gaida Abba.


"Ina wuni Abba?"


"Lafiya lau me ke faruwa ne?"


Shiru suka yi ba wanda yayi magana, sai da ya sake tambayarsu a karo na biyu sannan Usman ya ce,


"Dama nazo wajen Inteesar ne muna tsaye muna magana da ita, daga zuwansa ya fara mata fad'..."


Abba ya katse sa da cewa


"Yaushe Inteesar tazo gidan? kuma ka meye alak'arka da ita?"


'Dan sunkuyar da kansa k'asa yayi tare da cewa


" Abba aurenta nake son nayi?"


Kallon mamaki Abba yayi masa ya ce,


"Bawan Allah kai musulmi ne?"


"Eh ni musulmi ne Abba."


"Kasan haramun ne ka nemi matar aure?"


Da sauri Usman ya kalle shi tare da cewa


"Matar aure?"


"Bata fad'a maka bane?"


Gaba d'aya jikinsa ne yayi sanyi, amma sai ya daure ya ce,


"Bansan cewa tana da aure ba Abba, bata fad'a mani ba."


"Tun yaushe kake tare da ita?"


"Baka gane ni bane Abba? nine Usman wanda na muka ta'ba samun accident da Inteesar kimanin watanni hud'u da suka wuce."


Sai a lokacin Abba ya tuna Usman ya ce


"Allah sarki, sai yanzun na tuna, amma ya akayi kasan tana nan ko kuma kuna waya da ita ne?"


"A'a Abba bamu waya da ita na dad'e ko na kira wayarta bata d'agawa wani lokacin bata shiga ko na kira a kashe."


To Inteesar tayi aure akwai igiyar aure akanta, wannan da ka gani shine mijinta, kallon Muhdeen yayi tare da sakin murmushi ya ce,


"Dan Allah kayi hak'uri ka gadarce ni rashin sani ne ya kawo haka, ina maku fatan alkhairi a rayuwar aurenku."


Abba ya ce


" Masha Allah, Allah ya baka wata macen auren tagari"


Sallama ya masu ya bud'e murfin motarsa ya shiga ya bar wajen, Abba ne ya kalli Muhdeen ya ce,


"Dan Allah kayi hak'uri Muhammad"


"Bakomai Abba."


Kai Abba ya jinjina tare da cewa


"Mu shiga ciki ko? ka tsaya kana tsaye a waje."


Shiga cikin gidan sukayi Abba na gaba Muhdeen na binsa a baya, da sallama suka shiga Inteesar da Umma na zaune a tabarma, Umma ce ta ce,


"Muhammad sannu da zuwa"


"Yauwa sannu Umma"


Durk'usawa yayi k'asa ya gaida Umma


"Umma ina wuni"


"Lafiya lau Muhammad bya aiki?"


"Aiki Alhamdulillah"


Zama yayi akan tabarma da Umma ta shimfid'a masa, Abba ne ya kalli Inteesar dake gaishe sa


"Abba ina wuni?"


"Lafiya lau, waye yazo wajenki a waje?"


Shiru tayi ta kasa magana, tsawa ya daka mata wanda yasa ta firgita ta matsa kusa da Muhdeen


"Kinsan cewa kina da aure zaki tsaya kina magana da wani saurayi, kinci arzikin ya sanar da ni gaskiya baku waya amma da yazo shine kika tsaya da shi baki sanar da shi cewa ke matar aure bace?"


"Abba ina k'ok'ari na sanar da shi ne sai ga yaya yazo."


Salati Umma ta saka tare da cewa


"Dama ba mijinki bane yazo? ai na d'auka shine yazo shiysa na barki kika fita."


Abba ne ya ce,


"Daga yau kada ki sake kula shi duk da shima naga Alamar yana da sanin yakamata, kuma nayi masa bayanin kinyi aure ya bawa mijinki hak'uri, kada na sake jin makamancin wannan abun ya faru idan kuma ba haka ba zakiyi mamanki na."


Idanunta cike da k'walla ta ce,


"Abba kayi hak'uri"


"Bani zaki ba hak'uri ba mijinki zaki nemi yafiyarsa, tashi ku tafi."


"Abba mu tafi ina"


"Ina ne gidanku? Kina da wani gidan da yafi gidan mijinki ne a yanzun?"


"Abba ba tare muka zo ba kuma ni sai anjima zan..."


Kafin takai k'arshen maganar da tayi niyyar yi ne ya d'aga mata hannu


"Tashi kibi mijinki"


Wani bak'in ciki da takaici ne suka lullu'be ta, yayi da shi kuma zuciyarsa fara tas murna kamar ya zuba ruwa k'asa yasha, tashi yayi tare d masu sallama da godiya ya nufi hanyar fita yana jiran fitowarta, sallama tayi harda kukanta basu kula ta ba haka ta mik'e ta nufi hanyar fita Abba na binta a baya.


Yana tsaye jikin motarsa yana ganin fitowarsu baisan lokacin da murmushi ya su'buce masa ba, kwana tayi don komawa gidansu Mummy taji muryar Abbanta na cewa


"Ina zakije?"


Haka yasa ta dawo don tuna maganar Mummy da suka ce kada ta sanar da Abbanta da Ummanta matsalar da ta faru, hakan yasa tayi shiru ta shiga motar ganin yana bud'e mata murfin motar, shiga tayi inda Abba ya k'ara bashi hak'uri ya nuna masa bakomai, Abba ya koma gida yayin da Inteesar ta d'ora kanta a saman cinyarata tana ta sakin kuka, tada motar yayi yabar layain, jin sautin kukanta yake har cikin ransa, amma shi baiga abun kuka ba, shi fa ta masa laifi baiyi kuka ba sai ita, saboda tasabar jin dad'i.


Ganin tsawon lokaci suna tafiya ne kuma tasan gidan su day na Mummy ba nisa yasa ta d'aga kai taga ina suke, gabanta ne ya fad'i ganin wani hanya daban Wanda bata san da ita ba , da sauri ta kalle shi ganin ya tamke fuska ya fito mata a asalin Muhdeen d'insa yasa taji tsoronsa ya dawo mata sabo, d'aurawa tayi ta ce


"Yaya ina zaka kaini? wallahi su Mummy zasu neme ni basu ganeni ba."


Kamar kurma haka ya k'yaleta kamar baiji ta ba, sau uku tana magana ya share ta


"Nidai gaskiya ka mayar Dani gida dan bazan koma gidanka ba."


Nan ma shiru bata ankara ba taga yayi parking a k'ofar gidan wani tangamemen gida, horn yayi mai gadi ne ya fito ya ga Muhdeen sanna ya bud'e masa gate ya shiga yayi parking, mai gadin ya k'araso yana gaishe sa ya amsa tare da tambayarsa ya aiki, Nima ya gaishe ni amma duk rashin son magana da na ke na amsa, tsaye nayi ina k'arewa gidan kallo kamar wata bak'auya, ta shagala da kallon k'ayataccen gidan, ta mance da wai fushi take da shi, sai jin muryarsa tayi yana cewa


"Idan kin gama sai kizo mu shiga ciki."


Kunya ce ta kamata ta had'e fuska ta ce


"Ba inda zan shiga."


Ganin yana tattare hannun rigaraa ya sa ta ce


"Me zakayi"?


"Zan d'auke ki ne."


Da sauri tayi gaba yana binta a baya tsayawa tayi daf da k'ofar yayin da shi kuma ya bud'e k'ofar ya shiga, tsayawa tayi ta coge ya kalle ta ya ce,


"Ba zaki shigo bane? tura baki tayi tare d cewa


"Ba inda zan ahiga har sai ka mayar dani gida."


Baice da ita komai ba ya shige ciki abinsa, ya barta nan tsaye a wajen.


Babban Babban falo ne mai d'auke da sofa sa set biyu na royal, waoyinsa ya ajiye Kan center table dake falon,. kai tsaye bedroom ya wuce ya inda ya fad'a toilet yayi wanka ya ya feshe jikinsa da turare mai dad'in k'amshi.


Fitowa yayi sanye da kananun kaya a jikinsa, riga red color da wanda 3 quarter black , yayi masifar kyau yana tafe cikin takunsa na k'asaita da tafiyarsa irin na lafiyayyun maza, k'irarsa da cikar zatinsa irin na cikakken namiji suka bayyana, k'amshin turarensa ne suka fara sanar da ita ya k'araso, juyawa ta kalle shi k'wayar idonsa ta kalla da sauri ta janye idonta ganin wani irin kwarjini da yayi mata, bata ankare ba sai ji tayi ya d'auke ta cak kamar jaririya, wutsil wutsil ta fara yi amma rikon da yayi mata ba na wasa bane.


Har cikin bedroom d'insa ya shiga da ita bai dire ta ko ina ba sai cikin toilet a bahon wanka dake cike da ruwa, ganin yadda ya saka ta tsamo-tsamo cikin ruwa gata ta jike sharkaf da ruwa, hakan yasa ta fashe da kuka bata San me zata cewa su Mummy da Gwaggo ba, kuka ta cigaba da yi tana cewa,


"Ni ka kaini gida"


"Wane gida zan kaiki? ai wannan shine gidanki."


"Nikam ba gida na bane nan "


"To naji ba gidanki bane bari nayi maki wanka sai ma tafi ? amma idan baki tsaya nayi maki wanka b a to muna na. gidan."


"Ya zanyi da kayana da suka jike?"


"Kada ki damu akwia sababbin kaya a gidan nan zan baki ki saka."


Make kafada tayi


"Ban yarda ba su Gwaggo zasuyi mani fad'a"


Bai saurare ta ba ya fara cire mata rigar jikinta, bayan ya saura daga ita sai bra and pant ne ya rik'e bra d'in tare da rufe k'irjinta, 'balle bra d'in yayi dukiyar fulaninta suka bayyana cirko -cirko kamr su tsire idanunsa, cije le'b'bensa yayi tare da zare mata pant d'in, sabulun wanka ya d'eba yana sawa a hannunsa yana murza mata a jikinta duk da ta fahimci cewa bawai wanka zaiyi mata ba kawai yana so ne ya luguiguita ta Dan yadda ya dinga mata wasa da bra d'inta yana shafasu da sunan wanka, ganin abun nasa yayi yawa ne yasa ta saka masa kuka.


Sannan ya d'aurayota ya d'aura mata towel, ita kuma kunya ce ke damunta ta da takaici,bayan ya nad'e ta cikin towel d'in ya sungumenta kamar jaririya sai gaban dressing mirror zai sha fa mata ta ce bata so, don haka ya dire ta a tsakiyar gadon shim ya kwanta tare da janyo masu bargo ya lullu'be su.


"Baby nayi missing naki sosai."


Kuka ta saka ta ce


"Wallahi nikam bazan yarda ba sai ka..."kafin takai k'arshen maganar ta ya had'e bakinsu waje d'aya ya fara tsotson la'b'banta kamar ya samu sweet, hannunsa na kan bra d'in ta yana murza su.


Nan fa ta nuna masa bata San zancenba sam ta fara k'ok'arin k'watar kanta.








*Daga alk'alamin*


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan






*Don k'arin bayani*


09065327995


Love you oll😘😍




Comments &shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CIdxYmFSO83KRgWbm5FJ2a








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






Idan kinsan cewa kina cikin group na Inteesar to kada kiyi joining wannan, wancan ya cika ne yasa na bud'e wannan duk abu d'aya ne, sannan idan har kinsan cewa ba zakiyi comments ba kada ki shigar mani group don ko kinshiga idan baki comments zan fitar da ke ne.




*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.




*SANARWA*


Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.




*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*


Page6️⃣8️⃣


Nan ta nuna masa bata San zancen ba sam, fara k'ok'arin k'watar kanta, amma ina bai bata wanna damar ba nan fa ya fara zaucewa, wayarsa ce ta fara ruri bai kula ba ya cigaba da abunda yake yayin da Inteesar kuma sai kuka take, hankad'e sa tayi zata gudu cikin zafin nama ya janyo ta yayin da wayarsa ta sake d'aukar wani ruri, tsuki yayi ya janyo wayar da niyyar kasheta gaba d'aya, amma suna Dadynsa ya gani zaro ido waje yayi ta kalli Inteesar sannan ya d'aga wayar tare da k'arawa a kunne, tun kafin yayi magana ya ji muryar Dady na cewa


"Muhammad ina kake?"


Cikin sark'ewar murya ya ce,


"Ina gida Dady?"


"Ina inteesar take?"


"Tana tare da ni"


"Na baka mintuna goma yanzun ka kawo mani Inteesar ko nayi mummunar 'bata maka rai."


Bai jira cewarsa ba ya katse kiran, Inteesar da ke rungume a jikinsa tana jin duk maganar da Dady yayi ne ta saki murmushi ta ce


"Thank you so much Dady"


Zuba mata ido yayi ganin yadda take murmushi ga hawaye a idanunta, jefa mata tambaya yayi


"Me yasa kika tsane ni ne haka kuma yaushe wannan k'iyayyar da kike Mani zai fita daga rayuwarki?"


Kamar bata ji me ya ce ba towel d'in da ya nad'o ta ciki ta d'aura tare da cewa


"Ka jik'a mani kaya na kuma mintuna goma aka baka ya zamuyi kenan?"


Bai ce ta ita komai ba ya ya sauka daga daga Kan gadon ya nufi wurin closet dake cikin bedroom d'insa ya ciro mata wata Abaya purple colour da mayafinta ya bata, kallonsa tayi ta kalli sabuwar Abyar da ya bata ta saka tayi gaba yana binta a baya har suka fito ya rufe k'ofar, mai gadi yayi masu sallama ko amsawa baiyi ba hannu kawai ya d'aga masa, kallo d'aya zakayi masa kaga yana cikin damuwa, mai gadin ne ya k'araso wajen motar ya ce,


"Yalla'bai lafiya dai ko?"


Kallonsa Muhdeen yayi tare da cewa


"Me ka gani Mallam Musa?"


"Naga ka shiga cikin jin dad'i da annuri amma yanzun naga kana cikin damuwa, shine na ce ko wani abun ne ya faru?"


"Bakomai kada ka damu"


Kud'i ya d'ebo masu yawa ya mik'a masa, ya kar'ba yana godiya sanna yaja mota suka bar gidan .


A can gida kuwa bayan Direban Dady yayi parking ne ya fito ya bud'e murfin baya Dady ya fito, yana shiga ya tarar da su duka a falo, ya kalli Mummy ya ce


"Ina Inteesar take?"


Gwaggo ce ta kalle shi ta ce,


",Meye haka Sani zaka shigowa mutane ko sallama."


"Kiyi hak'uri Gwaggo ina dawowa ne na had'u da mahaifin Inteesar yake sanar dani cewa yanzun Muhdeen da Inteesar suka tafi sunzo gaida Ummanta."


Gwaggo ta dafe k'irjj ta ce


"Me nake shirin ji haka? ta yaya akayi hakan ta faru?"


Girgiza kai Dady yayi tare da cewa


"Ban sani ba gaskiya, dan ko da ya sanar dani cewa sunzo gaishe da Umma, yanzun suka tafi bazan masa wata tambaya ba tunda basu san halin da ake ciki ba."


"To ina suke yanzun?"


"Na kira sa na tambaye shi ya sanar dani wai suna gidansa."


Salati Gwaggo ta saka tana tafa hannu yayin da Dady ya cigaba magana.


"Na sanar da shi nan da mintuna goma ya dawo da ita, nasan yanzun suna hanya."


Suna nan tsaye sai suka ji sallamarsu, gaba d'aya suka juya suka amsa sallamar tare da zuba masu ido, Gwaggo ce ta k'ara bude idanunta da kyau taga kayan da suka tafi da su ba shine a jikinsu ba, Inteesar atamfa ta fita da shi yanzun kuma gata da abaya shi kuma ya fita da manyan kanta yanzun gashi da k'ananun kaya, tafa hannu tayi ta ce,


"Wato ke bansan wace irin yarinya bace, mu zaki rainawa hankali? dama kun shirya da shi akan zaku haɗu yasa kika mana k'arya ko? ai ba akai can ba badai namiji bane gaki nan gashi ranar da zai ƙuntata maki sai kinji duk duniya ba wanda ya tsane ki sama da shi, wacce ma suka same ta da wahala ya ta ƙare da namiji ballanta ke da ya ganki a sama, ana neman k'watar maki 'yanci baki ganewa ba, tunda haka kika zaɓa mun zuba maki ido kije ki tattaro kayanki kizo kibi mijinki ku tafi Allah ya kawo ƙazantar ɗaki."


Kuka ta fashe da shi tana cewa


"Wallahi Gwaggo ba yadda kike tunani bane, Abba na ne ya tilasta mani binsa shine na ce ya kawo Ni gidanku amma ya wuce da Ni can wani gida, ba yadda na iya ku fahimce Ni."


Muhdeen ne ya durƙusa a kan gwuiwowinsa cikin ƙasƙantar da kai ya ce,


"Gwaggo, Dady Mummy nasan nayi kuskure a baya wallahi nayi nadamar abinda na aikata a yanzun son Inteesar nekeyi har cikin zuciyata, dan Allah ku bani dama na gyara kuskure ne a karo na farko, insha Allahu ba zakuyi danasanin ƙin amincewa da ni ba, kuyi haƙuri ku mance da abinda ya wuce a baya, insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba, wallahi yanzun soyayyar da nake mata ni kaina bansan iya adadinsa ba kuma bansan yaushe ne na kamu da sonta ba, a yanzun ji nake bazan iya rayuwa ba ita ba."


Zuba masa ido sukayi ganin hawaye a idanunsa tabbas kuka yake, kuma ya kamu da sonta ne ko shakka babu don sun hango soyayyar da yake mata a cikin zuciyarsa, Dady ne yayi murmushi tare da cewa


"To me yasa a baya ka dinga ƙuntatawa rayuwarta bayan kasan cewa kana sonta? ai masoyi kyautata masa ake tare da faranta ransa ."


"Dady dan Allah ku daina tuna Baya insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba, nidai ku bani dama ba zakuyi dana sani ba."


Gwaggo ce tayi tsuki tare da cewa dana sani na nawa kuma? ai nice mai da na sani da naje da ƙafa ta har gurin ubanta na nema maka aurenta ba tare da sanin ka ba, kai dai kawai daga sama ka same ta, lokacin da na yi maka gata na aura maka ita madadin kayi farin ciki da godiya a gare Ni sai harara ta ka dinga yi da jin haushi na, sannan ka dinga wahalar da baiwar Allah da azabtar da ita akan laifin da ba ita tayi maka shi ba, ba ita ta ganka tace tana so ba, ballantana ka ɗora mata ƙaran tsana bata da laifin komai, Gara kai an sanar da kai a ranar da za'a ɗaura maka auren ita kuma ba wanda ya sanar da ita sai bayan auren ta sani, haka tayi haƙuri ta jure bata taɓa kawo ƙarar kayi mata wani abu ba, Dan dai na firar da suke yi da Mufida ta sanar da ita, har take roƙon ta kada ta faɗawa kowa Mufida ta nuna ba zata iya ba sai ta faɗa, da haryanzun kana nan kana cutar ita, baka san kana sonta ba sai da aka ɗauko ta zuwa nan, sannan ga wannan ifirituwar matarka tana neman kashe ta, ai idan muka bari yarinya nan ta koma gidanka ganin bayanta za'ayi, dan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads