Showing 24001 words to 27000 words out of 149432 words
Chapter 9 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
ne ya shiga gaban motar don baikamata ya barsu su tafi da mutumin da bai sansu ba.
Tafiya kad'an sukayi suka 'karasa wani private hospital dake unguwar, parking yayi tare da fitowa da sauri ya hangi masu wasu ma'aikatan asibitin kiran su yayi sai gasu da hanzari sun d'auko gadon tura marasa lafiya, bayan an kwantar da ita suka wuce da ita ya yin da suka rufa masu baya.
Bayan an shigar da ita d'akin an kwantar da ita bisa gado sai ga doctor da nurses biyu a bayansa, Doctor d'in ne ya umarci su Mufida da su fita su jirasa a waje, fita sukayi Mufida dai har yanzu bata daina kuka ba, saurayin da ya kad'e Inteesar ne ya kalli Mufida yace,
"Ki kwantar da hankalinki ki daina kuka in sha Allah zata samu lafiya"
Kai ta gyada masa ba tare da tayi magana ba, ta nufi kujerun dake wurin ta zauna akan d'aya daga cikin su tare da yin tagumi, Ishaq direban su ne ya kalleta yace,
"To ni bari naje na d'auki mota na tafi na sanar da su Mummy"
Kallaonsa tayi tace,
"To"
Saurayin da ya kad'e Inteesar dai Yana Nan tsaye wayar Sa ya Ciro daga cikin aljihun sa ya lalubo number mahifiyar sa ya shiga Kiran layin.
Wata dittijuwar mata ce Mai kimanin shekaru hamsin tana zaune akan a falon ta, Kan d'aya daga cikin lafiyayyun kujeran dake falon,wayar ta CE to soma ringing dubawa tayi ganin d'anta ne ke Kira yasa ta d'aga da sauri tare da cewa,
"Babana har yanzun baka 'karaso ba?"
Ajiyar zuciya saurayin ya sauke cikin sanyin murya
yace,
"Mummy na samu accident ne"
Zumbur ta mi'ke da sauri Tana fad'in,
"Subhanallahi Babana me ya same ka? Kana Ina ne?"
"Ba abunda ya sameni wata yarinya ce na kad'e da mota na kawota aaibiti"
Cikin damuwa ta furta kalmar,
"Inalillahi wa'inna ilaihir rajiun,wane asibitin kuke"
"Muna nan asibitin Top medical dake tunga"
Bata 'kara cewa komaiba ta ajiye wayar tare da 'kwalawa autar ta Kira.
Khadija! Khadija!!
Da sauri matashiyar budurwar ta fito hannunta d'auke da wayar ta,kafin tayi magama matar tace,
"Kiyi sauri yanzun Nan ki fito zamu tafi asibiti yayanki ne ya kad'eta wata yarinya da mota"
Tana kaiwa 'karshen maganarta ta nufi d'akinta,
Ba jimawa tafito dai-dai lokacin da itama Khadija ta fito rataye da handbag hannunta ri'ke da makullin motarta,suka nufi kofar fita.
Inteesar cikin 'kan'kanin lokaci ta farfad'o, kasancewar ba wani rauni taji sosai ba,buguwa ne da 'kujewa tayi,bayan doctor ya fito ya basu damar shiga su ganta kwance suka sameta, Mufida na ganinta ta saki murmushi a guje ta karasa jikin ta fad'a jikin ta ta rungumeta,ganin yadda Inteesar ke cije le'be yasa Usman wato saurayin da ya kad'e Inteesar yace,
"Ki d'an saketa kamar Tana Jin zafin rungumar da kikayi Mata"
Sakinta Mufida tayi tare da zama gefen gadon Tana murmushin ganin jikin Inteesar d'in da sau'ki, Inteesar ce the d'aga idonta ta kalli Usman suna had'a ido ya sakar Mata wani lallausan murmushi,da sauri ta sunkuyar da kanta kasa,Jin muryarsa tayi yace,
"Sannu ko, ya jikin naki?"
Ba tare da ta d'ago ta kalleshi ba tace,
"Da sau'ki"
Murmushi yayi tare da cewa,
"Allah ya baki lafiya ya kiyaye gaba"
Mufida ce ra amsa da,
"Ameen ya rabbi"
Suna cikin Haka aka turo 'kofar aka turo 'kofar aka shigo d'akin,kusan a tare suka shigo Gwaggo,Mummy,sai Umman Inteesar,suna shigowa sai ga Ammy mahifiyar Usman da 'yarta Khadija ne suka shigo d'akin. Gwaggo ce ta ri'ke hannunta cikin tausayawa tace,
"'Yar Albarka Garin yaya hakan ta faru?nidai nasan kina da nutsuwa ba laifinki bane,yanzun haka tu'kin ganganci ne direban Nan yayi ways sani ma ko d'an shaye-shaye ne yasha ya bugu Yana neman illata maki illata muna ke,in bandama..."
Bata Kai aya ba Mufida ta Kira sunan ta ganin zatayi 'baran 'barama ga Wanda ya kad'e Inteesar a wajen kuma ba mashayi bane yadda Gwaggon ke fad'a,Hasalima Inteesar ce Mai laifin don itace tahau titin dai-dai motar na kawowa,duk da cewa ita ceton rai tajeyi ganin makaho zai hau titin gashi ba idone dashi ba,dayake tsautsayi akanta yake ba'a kad'e makahon ba ita aka kad'e.
Mufida ce tace
"Haba Gwaggo ki daina yanke Hukuncin abunda bakida masaniya akansa,bakisan yadda Abu ya faru ba ki dinga bincike"
Gwaggo ce ta galla Mata harara tare da cewa,
"Dalla rufewa mutane baki magananniya na'ki nayi bincike,kuma duk Wanda ya kad'e Inteesar sai Allah ya..."
Cikin sauri Usaman yace,
"Mama Don Allah kiyi Ha'kuri nice na kad'eta bisa tsautsayi,kuma ba yadda kike tunani bane Allah ne ya 'kaddaro hakan zata faru ba makawa sai ta faru,KU gafarceni Don Allah"
Gaba d'ayan su zuba masa idanu sukayi suna kallonsa.
Mufida ce tace,
"Wani makaho ne yazo yana dogara sanda zai hau titi ganin hakan ne yasa Inteesar ba tare da ta duba titi ba Kai tsaye tahau titin dai-dai motarsa na kawowa"
Gaba d'aya d'akin shiru akayi ana sauraren ta, Gwaggo kuma sai taji kunya saboda su'butar bakin da tayi, kowa sai addu'a da Allah kiyaye gaba,Ammy mahaifiyar Usman CE ta gaishe su tare da gabatar da kanta ta kuma Basu ha'kurin abunda ya faru,suka nuna ba komai .
Sun d'an jima suna fira a tsakaninsu,lokaci-zuwa lokaci duk sanda Inteesar ta d'ago Kai zasu had'a Idanu da Usman kuma sai taga ya Mata murmushi,har ta kosa su tafi,zuwa can Ammyn Usman tayi masu sallama Kan cewa zasu dawo gobe,hakan yasa Usman da Khadija sukayi masu sallama suka tafi.
Mummy ma tayi masu sallama tace zataje tayi girki ta kawo masu Gwaggo kama tace it's zata kwana da Inteesar tayi jinyarta Umma ma tabita suka tafi gida,Don dama Mufida ma tace Nan zata kwana.
Washe gari da sassafe Inteesar na kwance a gadon ta na jinya, Mufida na kwance Kan dogon kujera Mai zaman mutum uku Tana barci,yayinda Gwaggo ke cikin toilet tana brush,Usman ne ya turo 'kofar ya shigo tare da sallama, Inteesar ta juya Kai ta kalleshi murmushi ya sakar Mata tare da 'karasowa ya zauna Kan chair d'in dake gefae gadon ya kalleta yace,
"Ina kwana?"
Tashi zaune tayi tare da sunkuyar da kanta 'kasa tace,
"Ina kwana ?"
Fuskarsa d'uke da murmushi ya amsa Mata tare da cewa,
"Ya jikinki"
"Da sau'ki"
Ta bashi amsa fuskarta a sunkuye,idonsa ne ya sauka akan wayarta yasa ya d'auki wayar tare da tambayarta ce ko na Mufida,don photonsu su biyu ne a Kan wayar kowacce fuskarta d'auke murmushi,Kai ta d'aga masa alamun wayarta ce,ganin Babu pin yasashi saka number sa a cikin wayar yakira layinsa Jin vibration a aljihunsa yasa yasan Kiran ya shiga,ajiye Mata wayar yayi dai-dai lokacin da Gwaggo ta fito Toilet,cikin girmamawa ya gaisheta tare da tambayarta ya Mai jiki tace,
"Jiki kam Alhamdulillah angodewa Allah d'annan yasu Mahaifiyar taka suka koma?"
"Alhamdulillah sunanan zuwa anjima"
"To Allah ya kawosu lafiya"
Kallon Inteesar yayi tare da cewa,
Nima nayi sammakon zuwa ne saboda saboda yanzun haka tafiya zanyi zuwa Abuja, nace bari na biyo na duba jikinta, kafin na tafi, don Doctor ya sanar Dani cewa jibi Za'a sallameta,nazo dubata kafin na tafi,"
Mi'kewa yayi tare da cewa,
"Bari na tafi direba na jirana a waje"
Hannu yasa a aljihunsa,kud'i ya Ciro dubu hamsin ya ajiye masu.
"Gwaggo tace,
Kud'in asibitin ne?"
Murmushi yayi tare da cewa,
"Na biya Kud'in komai na asibiti sallamar KU kawai za'ayi KU tafi"
Washe baki Gwaggo tayi tace
Dakyau yaron kirki,da wasu marasa mutunci ne guduwa zasuyi bayan sun kad'e mutum,Amma Kai kayi abunda ya dace, Uwarka ta iya haihuwa"
Murmushi yayi ya kalli Inteesar yace,
"Zan kiraki a waya Allah ya baki lafiya"
Bata san lokacin da ta maida masa martanin murmushin da yayi mata ba, daga nan sai ya nufi 'kofa ya fice fusakarsa d'auke da murmushi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
( Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa.
Page1️⃣9️⃣
Bata sanan lokacin da ta mayar masa marttanin murmushi da yayi Mata ba,daga nan sai ya nufi 'kofa ya fice fusakar sa d'auke da murmshi.Kallon ta Gwaggo tayi ta ta'be baki sannan tace,
"Shi kuma wannan da yake murmushi dawa yakeyi ne?"
Gyara kwanciyarta tayi ba tare da ta kalli Gwaggo ba,tayi magama can kasan ma'koshi,
"To Ni inama zan san dawa yakeyi,oho masa"
" 'karya kike munafuka har zaki wani ce baki san dawa yake ba?nan nake ta kallon ku Kuna tayiwa juna murmushi kamar wasu masoya,shi kuma ya zuba maki ido yana ta kallonki ko 'kifta ido Babu kamar wani tsohon maybe,to kidai bi sannu a hankali don samarin bana ba tabbas. 'Yan yaudara sunyi yawa musamman ke da kike sumu-sumu nan ba wani wayau ne dake ba".
Tura baki tayi, Gwaggo ta ta'be baki tana cewa,
"In banda ma rashin sanin inda kaknki ke maki ciwo mutumin da ya saka ki cikin wannan halin sai ki dinga masa murmushi kamar wata sakarya?"
Turo 'kofar akayi da sallama,Mummy ce Da direbanta d'auke da basket da suka jero masu Breakfast a ciki,Direban ya a jiye basket tare da gaida Gwaggo,ta amsa masa yayiwa Inteesar ya jiki ya fice daga d'akin.Mummy ta kalli ta dur'kusa ta gaishe ta.
"Gwaggo ina kwana"
"Lafiya qalau,ya naganki ke d'aya ina sanin yake?"
"Yanana Zuwa anjima ka'an,yace na gaishe ku kafin ya 'karaso nima nayi sammakon ne saboda Breakfast da na taho maku dashi"
Jinjina Kai Gwaggo tayi tare da cewa,
"Allah ya kaimu anjiman ya kawo shi lafiya"
"Ameen ya rabbi"
Cewar Mummy da ta kalli Inteesar,sai Inteesar tayi saurin gaida Mummy.
"Ina kwana Mummy?"
Murmushi mummy tayi tare da zama a gefenta ta shafi fuskarta cikin son yarinyar.
"Lapiya qalau 'yata ya jikinki?"
Murmushi tayi tace
"Alhamdulillah naji sau'ki"
"To Masha Allah ga Breakfast ki tashi kici"
"Mummy tea kawai zansha"
Dai-dai lokacin da Mufida ta farka daga barci, mi'kewa tayi ta fad'a jikin Mummy Tana fad'in.
"Morning"
Gwaggo ce ta had'o tea ta kawo ma Inteesar ko bread ma bata kula ba balle ayi maganar Dankali da kwai.A ranar Dady yazo ya gaida Inteesar sannan ya tafi wurin meeting d'in da zaije, Abba da Umma ma duk sunzo,sai wasu 'kawayen Inteesar su biyu wasila da salaha sunzo sun gaishe da Inteesar, suna tsakiyar fira ne wayar Inteesar tayi ringing,ganin number tayi ba suna,d'agawa tayi tare da yin sallama,Jin wata ba'kuwar murya yasa tad'anyi shiru Tana tunanin muryar waye wannan?
Daga can 'bangaren yace
"Ina wuni?ya jikinki?
"Lapiya qalau naji sau'ki"
Murmushi yayi yace
"Masha Allah Allah ya baki lafiya yasa ya zama kaffaran jiki"
Shiru tad'anyi kafin tace,
"Ameen ban gane dawa nake magana ba"
Murmushi yayi yana fad'in
"Usman ne Wanda tsautsayi yasa ya kad'e ki da motar"
Shiru tayi Tana sauraron sa yaci gaba da maganar sa shi kad'ai wani lokacin tace eh idan na cewa A'a ne tace a'a a haka har suka d'auki tsawon mintuna suna waya har ta gaji ta 'kosa sannan yayi Mata sallama.Bayan ta ajiye wayar ne Mufida ta kalleta tare da cewa,
"Wai keda waye tun d'azu kike waya haka?"
Yamutse fuska tayi tare da cewa
"Wanda ya kad'eni da mota ne ya Kira ni?"
"To ina ya samu number ki?"
"Yazo da safe lokacin kina barci"
Ta karasa maganar Tana kwanciya Don ta gaji.
Bayan kwana biyu aka sallame su inda suka koma gida,ana dai ta shirye shiyen biki ta kowanne bangare.
A ranar Usman ya Kira Inteesar Kan cewa zaizo gidan su,ta'ki amincewa da hakan,ya nuna Mata cewa ai yakamata bayan dawowar sa ya sake duba jikin ta bayan an sallame su,ta nuna masa cewa ba komai ta warke.Fahimtar bazata bari yasan gidansu bane yasa yace Mata akwai sauran magungunan da Doctor yace a bata saboda idan batayi amfani dashi ba buguwan da tayi ciwon zai iya tashi kowane lokaci,jin hakan yasa ta bashi address d'in gidan su.
A can gidan Mummy kuwa, Gwaggo tasa Muhdeen a gaba wai me yasa baije asibiti ya gaida Inteesar ba har aka sallame ta.Mummy ma Bata San da hakan ba don ba wuni takeyi a asibiti ba.Nan ta bashi Umarnin cewa yau d'innan yaje har gidan su ya gaishe ta,ransa baiso ba haka ya amince zaije.
Misalin 'karfe biyar na yamma Usman ne a 'kofar gidan su Inteesar,Yana tsaye ya jingina da motarsa yayin da Inteesar ke tsaye sanye da Hijab har 'kasa,kanta sunkuye a 'kasa Tana wasa da yatsun hannun ta.Murmushin nan nasa yayi tare da cewa,
"Wai Kunyata kikeyi har haka ne kin kasa had'a ido da ni?"
Shiru tayi tacigaba da wasa da yatsun hannun ta, dai-dai lokacin da motar Muhdeen ya karaso 'kofar gidan,idanun sa ne suka sauka akan Usman da Inteesar,kallon mamani yake masu Wanda Shima Usman ya lura da hakan Amma sai ya kauda Kai.Muhdeen mamaki yake Wai kamar yarinyar Nan har ta isa aje saurayi ganin irin kallon da Usman ke Mata yana murmshi yasa shi ta'be baki hakanan kawai yaji gabansa ya fad'i yaji tsanar Usman ya d'arsu a cikin zuciyar sa.Bud'e marfin motar yayi ya fito,jin 'karar murfin motar ne yasa Inteesar d'ago ido ta kalleshi caraf suka had'a ido harara ya watsa Mata Wanda yasata sunkuyar da kanta 'kasa,duk akan idon Usman hakan ya faru Amma ya basar,d'ago ido ta sakeyi a karo na biyu suna had'a ido yayi Mata alamar tazo da hannayen sa,kallon ta ta maida ga Usman tace,
"Don Allah ina zuwa"
Kai ya jinjina alamun amincewa,sannan ta 'karasa wajen motar Muhdeen,sallama tayi ya amsa Mata can 'kasan ma'koshi tace,
"Yaya Ina wuni?"
Shiru yayi kamar baiji ba,sai da ta sake maimaitawa nan ma shiru don haka bata sake magana ba dama tasan halin sa.Tsawon 5 minutes baiyi magana ba,ganin baida niyyar magana ga fuskar nan a had'e ba alamun fara'a yasa tace,
"To Yaya sai anjima"
Tana Shirin barin wajen taji yace,
"Kina sauri ki koma wajen saurayin ki ko?karamar yarinya dake Wai har kin iya zance da saurayi,aikin banza Gwaggo ta addabeni Wai nazo na gaida mara lapiya ashe lafiyar ki kalau da na sani ban 'bata lokaci na ba. "
Ya karasa maganar yana watsa Mata kallon banza sannan ya juya ya shiga motarsa yabar wajen,shiru tayi tana tunananin maganar sa a zuciyar ta tace Mai hali bazai ta'ba canzawa ba.
Karasawa tayi wajen Usaman tace,
"Zan shiga gida sai anjima"
Ajiyar zuciya ya sauke ganin yanayinta ya canza cikin 'kan'kanin lokaci,yace
"Naga yanyinki ya canza na janyo maki 'bacin rai ko?bana son na zama silar 'bacin ran kowa,idan wannan shine wanda zai aure ki ko an tsaida magana a tsakanin ku ki Fad'a mani don naga kamar akwai matsala da ya ganni dake"
Bakomai Yayar 'kawata Mufida ne,shine Wanda zaiyi aure next week,d'inkin ankon bikin muka tafi kaiwa har ysautsayi yasa ka kad'e ni da mota "
Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi yace,
"To Masha Allah"
Murfin bayan motar sa ya bud'e ya d'auko manyan ledoji guda biyu ya mi'ka mata yace
" ga magungunan ki nan da nace zan kawo maki"
Kallon ledar tayi da mamaki tace,
"Magungunan ne har leda biyu manya ?"
Baibi ta kanta ba ya figi motarsa yabar wajen yayin da ta shige gida zuciyarta cike da mamakin yawan magungunan.
Muhdeen yana Isa gida ya iske Gwaggo a falo tana ganinsa tace,
"Ina fatan yau kaje ka duba jikin yarinyar nan"
Har zai shige part d'insa ya dakata Ya kalleta
"Wace yarinyar kike cewa ba lafiya?duk kinbi ki dameni banje gaida ita ba yarinyar da naje na sameta ita da saurayi suna firan soyayya..."
Caraf Gwaggo mi'kewa tayi tana fad'a
"A'a kaga nifa banason sharri wace yariyar ne keda saurayi?bana son 'kazafi wallahi.Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi
( Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to KU gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren Wawa.
Page2️⃣0️⃣
"A'a kaga nifa banison sharri,wace yarinyar ce keda saurayi?Bana son 'kazafi wallahi"
Bai tanka Mata ba Kai tsaye ya nufi part d'insa don bazai iya biyewa Gwaggo ba.
Bayan Inteesar ta shiga gida d'auke da ledojin da Usman ya kawo mata ne,Umma ta kalle ta ita da ledan hannunta tace,
"Amso magani nan waje shine kika kwashe mintuna a wajen? Sannan wad'annan ledojin ne na magunguna?"
Zama tayi akan tabarmar tare da ajiye leda,gabanta ne ya fad'i lolacin da ta zazzage d'ayar ledan ganin Turarruka kala-kala da sauran kayan kwalliya kala-kala masu yawa,juyawa tayi ta kalli Umma da ta zubawa kayan ido tana kallon kayan tana kallon Inteesar.
"'Bud'e d'ayar ledan mugani abunda ke ciki"
Jiki a sanyaye ta bud'e d'ayar ledan ta zazzage abunda ke ciki a gefe, nan ma zubawa kayan ido tayi ba kowane magani kayan ciye-ciye ne kawai.Snacks ne da su Biscuits da chocolate da sweet,idanu Ummi ta zuba Mata ba tare da cire idanunta daga gare ta ba.Ganin hakan yasa tayi narau-narau da ido hawaye na tsiyaya daga idanun ta cikin rawar murya tace,
"Umma wallahi bansan abunda ke ciki ba sai yanzun,nidai Kira na yayi a waya yace mani wai doctor ya bayar da magani a bani shine naje ka'ba duk a tunani na magunguna ne a ciki,wallahi bansa cewa abunda ya kawo ba kenan sai yanzun"
Shiru Umma tayi tana nazari kafin daga bisani tace,
"Ya akayi ya samu number wayar ki kuma waye ya nuna masa gidan Nan?. "
Shiru tayi tana kallon fuskar Umma kafin daga bisani ta bata labarin yadda yazo asibitin da yadda yadda d'auki number ta hanyar saka number sa wayar tata ya Kira number sa har ya samu number ta,da yadda yadda zaizo ta hana shi ya nuna Mata cewar magunguna Doctor ya bada a bata hakan yasa ta kwatanta masa gidan su Bata San cewa uzirin sa zai kawo sa ba.
Umma dai shiru tayi kafin tace,
"Wannan ya zama na farko kuma na 'karshe kada na sake ganin irin makamancin wannan da ya faru"
Kai ta jinjina tare da cewa
" insha Allah"
"To madalla kwashi kayan kikai d'akin ki"
Tattara kayan tayi ta nufi d'akinta da su,Umma ma d'akinta ta shige, Inteesar naman zaune ta fa'd'a suniyar tunani sai ga Mufida ta shigo da'akin bakinta d'auke da sallama tana rik'e da leda a hannunta k'arasawa tayi ta zauna gefen Inteesar ta dafa kafadarta,firgigit ta dawo daga suniyar tunananin da ta shiga, Mufida ta kalleta tace,
"Lapiya kuwa? me yake damunki