Showing 147001 words to 149432 words out of 149432 words
Chapter 50 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
lokacin sallah yayi.
Koda aka idar da sallar magrib bai bar masallacin ba sai da akayi sallar isha'i sannan ya bar masallacin.
Kai tsaye office ɗin Dr Abdulkarim ya nufa, amma bayanan, dan haka sai ya zauna saman sofa da ke cikin office ɗin yana jiran shigiwarsa.
Da misalin karfe tara na dare ne Dr Abdulkarim ya shigo office ɗin fuskarsa ɗauke da damuwa, ganin Yarima zaune a office ɗin ya ce,
"Allah ya taimaki Prince."
Zuba masa ido yayi tare da cewa
"Ya jikinta?"
Girgiza kai yayi tare da cewa
"Ya kake da yarinyar ne?"
"Tsintar yarinyar nayi a gefen hanya, maybe accident tayi."
"Kana nufin baka san daga inda take ba?"
Ataƙaice ya ce,
"Bansan komai game da ita ba."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Da sauri y kalle shi cikin fargaba tare da cewa
"Don't tell me that she's dead."
Girgiza kai yayi tare da cewa
"She is alive, amma gaskiya tayi loosing memory nata."
A firgice ya kalle Dr Abdulkarim
"What?"
"Sai dai kayi haƙuri amma gaskiya ta rasa tunaninta."
"Kana nufin ka ce mani ta mance wace ce ita?"
Dr Abdulkarim ya gyaɗa masa kai alamar eh
"Kana nufin ta mance sunanta iyayenta komai da ya shafi rayuwarta ta mance ?ba abunda ta sani yanzun?"
Jinjina Dr Abdulkarim yayi tare da cewa
"Kaina kasan wannan ba sai na fada maka ba, duk abinda ya faru da ita a baya ta manta sai dai ta gina sabuwar rayuwa, a halin yanzun ƙwaƙwalwarta ta koma kamar na jaririn da aka haifa yau."
Dafe goshinsa yayi cikin damuwa ya ce,
"To ko mu fitar da ita ƙasar waje ne ko Allah zaisa a dace?"
Murmushi yayi tare da cewa
"Ko ina zaka kaita abunda zasu faɗa kenan."
"To ba wata shawa da kake ganin idan anyi amfani da ita za'a dace?"
"Gaskiya babu sai dai idan Allah yasa ta ziyarci wuraren da ta taɓa sani a rayuwarta, ko kuma ta haɗu da mutanen da ta sansu a baya kafin faruwar hakan to tayiwu tunaninta ya dawo."
"Ya salam, toyanzun ya zanyi da ita?'
"Shawarar da zan baka shine ka Kaita gidan marayu"
Girgiza kai Yarima yayi tare da cewa
"Hakan ba mai yiwuwa bane, zan tafi da ita can."
"Ina zaka tafi da ita?
"Yola"
Daga nan bai sake magana ba
Kishingiɗa yayi tare da cewa
"Allahu ya bata lafiya."
Yadda Muhdeen yaga rana haka yaga dare gaba ɗaya bai iya rintsawa ba, dan ko gidan Sumayya bai je ba, a gidan Inteesar ya kwana gaba ɗaya hankalinsa ya tashi ba alamar barci ma zai iya ɗaukarsa.
Ɓangaren Gwaggo da Mummy hankainsu ya tashi sosai, suna ta addu'ar Allah yasa duk inda suke suna lafiya Allah ya bayyana ta
Karfe huɗu na asuba Muhdeen ya shiga toilet ya watsa ruwa tare da yin alwala yazo yayi nafila da addu'ar duk inda suke Allah yasa suna lafiya ya kareshi tare da bayyanar da su.
Ƙarfe shida na safe Muhdeen da Jabeer suka shirya dan zuwa Gombe, Jabeer ne yayi driving ɗin su bayan sunyi sallama da su Mummy ne suka kama hanya, Muhdeen bai ma sanar da Sumayya zancen tafiyar ba, dan ya ji tana cewa zata bishi kuma ba zaiso tafiya da ita a wannan yanayin da suke ciki ba, dan haka bai sanar da ita ba daga shi sai Jabeer suka kama hanyar zuwa Gombe.
*Saura 1 page book 1 ya ƙare, idan har kina buƙatar cigaba da karanta littafin Inteesar to zaki biya ₦300 kacal ta wannan account ɗin* *2242538358 Zainab Abdullahi U B A nagode*
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*_Albishir! Albishir!! Albishir!!!_*
*_Jama'ar Annabi inayi muku Albishir da cewa nakawo muku wannan shahararre Kuma ingantaccen gida, gidan da suka darje suka rairaye suke kawo Muku kayiyyaki masu dankaren kyau da Kuma inganci abisa farashi dai dai da Aljihun ku_*
*_Hajiyata, kanwata, Aunty na, kinaso kisamu kaya Wadanda ba kamarasu? Kayanda idan kika shirya kika fito kizama abin kallo a wurin Yan uwanki?_*
*_dama wadanda zasu ganki ahanya?_*
*_sbd yadda Zaki fita daban da saura?_*
*_Kinaso Idan kikayi shiri arinka tambayanki a ina kika saye wannan kayan?_*
*_Zakije gidan biki ko gidan suna Amma kina tunanin kayan dazaki saka saboda kiyi fita ta Alfarma ta kece raini?_*
```ARZUQLANA GALLERY```
*_sunkawo muku duk Wani abu Wanda zakuna bukata kama daga:_*
```Laces
Atampha
Shadda
Abayas
Materials
Gyale
Takalma
Jaka
Kayan Kitchen
Bangles n jewelries```
*And many more*
```GIDAN KYAU, GIDAN QUALITY, GIDAN SAUKI, GIDAN KWALISA, DA ADO```
*_Wani abin sedai kunbiyomu zaku Gani da idanunku_*
*_sunayin kasuwancinsu bisa gaskia da Amana, ba cuta ba cutarwa_*
*_koda bakida kudin Siya Muna gayyatarki dan ki tallata kema kisamu naki_*
*_Yar uwa kasance a gidan, da abaki labari gwanda ki bayar_*
https://chat.whatsapp.com/FRJAnQZXm0t7rAroZWlMnQ
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a giji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.
*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*
Page8️⃣0️⃣
Jabeer me yayi driving nasu bayan sunyi sallama da su Mummy da Gwaggo, Muhdeen bai sanar da Sumayya zancen tafiyar ba dan ya ji tana cewa zata bishi, kuma bazai so tafiya da ita ba a wannan yanayin da suke ciki, dan haka bai sanar da ita ba daga shi sai Jabeer suka kama hanyar zuwa Gombe.
Bayan ya dawo daga masallaci yana kishingiɗe a ɗakin Dr Abdulkarim, yayin da Dr Abdulkarim yake daga gefensa.
Wayarsa ce ta fara ruri, ko kallon wayar baiyi ba ballantana yayi niyyar ɗauka, har ta katse bai ɗaga ba, kallonsa Dr Abdulkarim yayi tare da cewa
"Wayar ma sai kaga dama kake ɗagawa?"
Bai ce da Abdulkarim komai ba kuma bai ɗaga wayar, har sai da aka kira wayar sau uku sannan ya ɗaga.
Gimbiya Anisa ce ta kira shi video call, kara wayar yayi a gabansa ya ajiye ta, tare da zubawa wayar idanunsa.
Zaune take ta ɗaura ƙafa daya kan ɗaya, yana sanye da alkyabba irin ta 'ya'yan sarakai, masu mata hidima na zagaye da ita, yayinda wata take ƙara gyara mata hullar alkyabbar, ɗaya wata tana durƙushe a gabanta tana bata fruit a baki, tana taunawa cikin yana kamar bata son ci.
Murmushi ta sakarwa Yarima Areef tare da cewa
"Barka da safiya my prince, fatan ka tashi lafiya."
"Alhamdulillah"
"Yarimana tun jiya nake jiran dawowarka na ji shiru, sai kuma nake jin labari wajen Fulani cewa ka tsaya ne saboda wata yarinya, gaskiya ba girmanka bane wannan, duk da nasan cewa kai mutum ne mai taimako da tausayi, amma hakan bai dace ba kana ɗan sarki guda ka tare a asibiti kawai dan ka tsinci yarinya a gefen titi."
"Ni waye da nafi ƙarfin taimako, ba wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda yafi shi tsoronsa, shi Allah baya duba zuwa ga surar jikinmu da dukiyarmu sai dai yana duba ne zuwa ga zuciyoyinmu da ayyukanmu."
Shiru kawai tayi ya zuba ma pink lips ɗinsa da ke matukar burge ta ido, inda ya cigaba da cewa
"Ina nan tare da ita, har sai ta farka sannan zamu taho da ita."
A zabure ta miƙe tsaye tare da cewa
"Ku tafi ina."
"Masarautarmu kina da matsala da hakan ne?"
"Komawa tayi ta zauna, ba tare da ta sake magana ba, ta ce,
"Yanzun yaushe zaka dawo na ganka?"
"Maybe gobe ko jibi insha Allahu."
Datsar tufa tayi tare da cewa
"Gaskiya bazan iya haƙurin zuwa jibi ban ganka ba, idan har ba zaka samu dawowa yau ko gobe gaskiya sai dai kaga na zo nan."
"Kizo ina wai?"
"Gombe"
"Koda wasa kada kiyi Wannan gangancin, ba hali na sanyi tafiya na kwana biyu ki ce zaki biyo NI?"
Dariya tayi tare da cewa
"Ai a hakan ma nayi ƙoƙarin n daure dan naga ba aure mukayi ba, amma idan mukayi aure su inda zaka je ƙafata ƙafarka, Allah dai ya kaimu ranar aurenmu.
Ta ƙarasa magana tana murmushi.
Kallonta yayi tare da cewa
"Bissalam"
Daga nan ya katse wayar, Dr Abdulkarim ne ya kalle shi tare da cewa
"Gimbiya Anisa na masifar sonka sosai, gashi kun dace da juna dukanku jinin sarauta ne gaba da baya, Allah ya kaimu ranar aurenku"
"Ka daina tunanin cewa zan auri Gimbiya Anisa, dan gaskiya bata da ce da irin macen da make da burin aure ba, tana da gadara ta taƙama, tana da sin mulki da sarauta, Ni kuma duk Waɗan nan abubuwa basu dame ni ba, kullun maganarta zata zama matar sarki, wai nine sarkin gobe, yayin da Ni kuma bana son sarautar nan."
Jinjina kai Abdulkarim yayi tare da cewa
"Sarauta kam ko kana so ko baka so dole ka karɓe shi, dan mahaifinsa bashi da wani burin da ya wuce yaga ka gaji kujerar sarauyarsa. domin kai ne mafi mafi soyuwa a gare shi."
Daga nan ya mike tare da cewa
"Pls muje mu duba yarinyar nan mana."
"kada ka damu nurse zasu yi mata duk abinda ya dace."
Daga nan ya miƙa shima Dr Abdulkarim ɗin tashi yayi yabi bayansa
Masu tsaron Yarima Areef ne suka take masa baya, dakata yayi na tare da ya kalle su na ya daga masu hannu dakatarwa., sanin me yake nufi me yasa suka koma inda suka tsaya, dan dama sun saba da wannan idan suka fita yakan dakatar da su,amma idan a masarautarsu ne bai hana su dan ya laura mai Martaba baya son yana dakatar da su.
Koda suka iso Gombe basu sha wahalar gane gidan ba, dan haka, autar su Umma ne yayi masu jagora, har cikin gidan
Da sallama suka shiga gidan, inda suka gaida da kowa na gidan tare da tambayarsu ya mai jiki, aka masu jagora har ɗakin kakan Inteesar suka gaishe ta tare da yi mata ya jiki.
Bayan an kawo masu abinci da ruwa ne Jabeer ne kawai ya iya shan ruwan, amma Muhdeen ko kallon ruwan baiyi ba burinsa kawai yaga Inteesar.
Koda suka shiga ɗakin da aka kwantar da ita, har lokacin tana kwance idanunta a lumshe, ƙarasawa Yarima yayi kusa da gadon tare da zuba masa ido.
A hankali ta buɗe idanunta ta sauke su akan na Yarima, kallon juna suka dingayi na na lokaci, kafin ta cire ƙwayar idanunta daga nasa, ta maida su ga sauran nursess guda uku da ke ɗakin.
Yarima ya kalle ta tare da cewa
"Sannu ya jikinki?"
Shiru kawai tayi tare da zuba masa ido, ya ƙara cefa mata wata tambaya ya ce
"Ya jikinki?
Nan ma shiru tayi ba tare da ta ce komai ba,
Kallon Dr Abdulkarim Yarima yayi tare da cewa
"Wuni ɗaya da kwana ɗaya tana kwance ba abunda ta ci, yakamata a nemo mata
Abinci.
Murmushi Abdulkarim yayi tare da cewa
"Kada ka damu an je kawo mata."
Kallonta Yarima yayi tare da cewa
"Zaki iya tashi ki shiga toilet ki wanke baki?"
Kallonsa tayi kamar mai kiyon magana ta ce,
"Toilet baki?"
Dr Abdulkarim ya kalli daya daga cikin nursess ɗin ya ce,
Ta raka ta ta nuna mata yadda zatayi, dan haka ta ja hannun Inteesar suka nufi toilet, sabon brush ta ɗauko tasa tooth paste ta miƙawa Inteesar, sannan ya sake saka wani a wani brush ɗin, ta ƙara da jikin tap tana riƙe da hannun Inteesar, ta dinga nunawa Inteesar yadda ake yi ta hanyar yiwa kanta, haka kuwa akayi duk yadda tayi sai Inteesar ta yi itama.
Har suka kammala suka fito, dai-dai lokcin da aka kawo mata kofin tea, aka bata ta shanye tass.
A ranar nan sai da Muhdeen da Inteesar suka dinga zagaye Gombe, suka kai report police station aka tabbatar masu akwai motar da tayi accident jiya amm mutanen da ke cikin motar sun ƙone kurkusa hankali tashe Muhdeen ya ce sune amma baya tunanin sune, kuma aka sana cikin tamabaya ne ko akwai wadanda sukayi accident, jagorancin autar su Umma da Mallam Habu, nan dai suka gano motar da Inteesar yayi hatsari, hankalin Muhdeen yayi matuƙar tashi ganin motarsa da Inteesar suka tafi da ita ta koma, ya tsaya yayi mutuwar tsaye sai jin muryar Mallam Habu na cewa
"Innalillahi wa'inna ilaihir, duk sun ƙone ƙurmus."
Ji sukayi tim Muhdeen ya daɗi wajen sumamme, a guje Jabeer ya ƙarasa gare shi tare da ɗago shi yana kiran sunansa.
Autan su Umma ne ya kalli Malam Habu ya ce,
"Haba mallam Habu ba haka ake magana ba, ta yaya zaka ce sun ƙone kurmus? ba wanda ya mutu a cikin motar nan, dan banga alamar ƙashin mutum a cikin motar ba."
Jabeer ya ɗauko robar ruwa a mota ya yayyafawa Muhdeen a karo na uku ya farfaɗo, koda ya farfaɗo kuka ya ke yana cewa
"Kada ka ce mani Inteesar ta rasu, dan idan ta tafi nima zan bita ne."
Autar su Umma ne ya dafa kafad'arsa tare da cewa
"Ka kwantar da hanklinka, ba alamar mutum ya ƙone a cikin motar nan, dan haka muje asibitoci mu duba ko Allah zaisa an samu waɗanda suka ceci rayuwarsu, suka kaisu asibitin, daƙyar suka lallaɓa shi ya shiga mota inda suka dinga zagaye asibitoci sun tambayar ko an kawo wasu mace da namiji da sukayi accident, ko ina sukayi tamabaya za'a ce masu ba nan bane.
Yarima ne ya tara jama'arsa inda yake sanar da su cewa da zaran an idar da sallar la'asar zasu kama hanya komawa Yola, dan ya ce daga masallacin zasu tafi.
Inteesar kuwa an shirya ta cikin Abaya blue tayi kyau sosai, Yarima ne yasa da Galadima dai Dr Abdulkarim suka cikin ɗakin da take, yayin da Yarima ke hanta da magana yana murmushi, yayin da Galadima kuwa zuciyarsa baƙa sai kallon Yarima yake yana kwafa a cikin zuciyarsa.
Haka su Muhdeen suka dinga zagaye asibitoci amma shiru basu da ce ba, inda Jabeer ya kalli Mallam Habu ya ce,
"Ba wani asibitin da kuka sani na kuɗi ko na gwamnatin?"
"Jinjina kai kawai Mallam Habu yayi tare da cewa
"Gaskiya waɗannan kawai na sani."
Autar su Umma ne ya ce
"Akwai dai wani asibitin kaɗai sanya taga bamu je can ba."
Jabeer ya ce wa
"Ina ne?"
"Autarsu Umma ya ce can ne ta farkon shigowa gari, shine ma yakamta mun fara zuwa, dan yafi kusa da inda maka baro wajen accident ɗin."
Kiran sallar la'asar akayi wanda Mallam Babu ya ce
"Bari suyi sallar la'asar sai su tafi can Asibitin Dr Abdulkarim ko can aka kai su, da wannan tunanin sukayi sallah suka tafi masallaci dan yin sallar la'asar sai su je asibitin Dr Abdulkarim.
Acan ɓangaren Yarima kuwa yada an ajiye komi da zasu tafi da shi a cikin mota, yayin da suke jiran a idar da sallar la'asar suja motocinsu ya ɗaga zuwa Yola.
*Shin ya kuke gani Muhdeen zasu ƙara so asibitin nan su haɗu da Inteesar?;idan sun koma da ita ashirin Sumayya ya tonu ya makomarta a wajen Muhdeen? Wani irin hukunci zai ɗauka akanta?shin ina direban da ya ɗauki Inteesar yake? Bashir zai faɗa wa Muhdeen kamar yadda yayi wa Ikirarari? idan kuma Yarima ya tafi da ita Yola ya rayuwarta zata kasance a cikin gidan sarauta?kunsan dai gidan sarauta da makirci waye Yarima Areef wace ce gimbiya Anisa?meye makomar Sumayya*?
*Dan cigaba da karanta littafin Inteesar book 2 ki biya kuɗinki naira ɗari uku kacal # 300 ɗan jin ƙarahen labarin, zaki tura kuɗi ki ta wannan account ɗin* 2242538358 *Zainab Abdullahi U B A bank sai ki turo shaidar biya ta wannan lambar 09065327995*
*Don neman ƙarin bayani*
09065327995
Love you oll😍😘
Love you oll😍😘