Header Ads
Showing 105001 words to 108000 words out of 149432 words

Chapter 36 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

1373

Ads at the middle of Article

bani ba kin tashi kin tadiyarki ko a jikinki ko? wato idan ma yunwa ta illata ni ba damuwarki bane ko Fatima? kuma kinsan ina da gyambon ciki bana iya jurar yunwa yanzun nan jiki na sai ya soma rawa ko akwai abunda na tare maki a cikin gidan ne da kika fara gajiya da ni? nan fa gidan d'ana ne ni na haife shi kafin ki ganshi ya aure ki, don haka baza ki hora ni da yunwa ba abincin da d'ana ne yake nemowa."


Girgiza kai Mummy tayi tare da murmushin takaici, don inda sabo ta saba da halin Gwaggo haka take dam, shiyasa hakan bai dame ta ce,


"Don Allah kiyi hak'uri Gwaggo, wallahi nima tafiyar a ba shiri tazo mani dole ce tasa na fita."


"Au dole ne fitar shiysa amma ni ba dole bane bani abinci ko?"


"Allah ya huci zuciyarki Gwaggo, na kammala had'a breakfast sannan na tafi sha'afa nayi ne shiyasa, kuma Gwaggo ai da kika ji shiru da sai ki shiga kitchen ki d'ebi kici ."


"Da nina saba shiga kitchen na d'ibi abincin naci?"


Dady ne ya kalli Gwaggo ya ce,


"Kiyi hak'uri Gwaggo insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba."


Kallon Mummy yayi tare da cewa


"Wai yau sammakon gaida Umman Inteesar kikayi haka?


Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin ta sanar da shi ne ki kada ta sanar da shi? Idan ta sanar da shi dole Gwaggo zata sani kuma Gwaggo ba zata iya bata matsala akan shawara da ta yanke musamman idan akayi la'akari da soyayyar da take yiwa Muhdeen.








Daga alk'alamin✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






Don neman k'arin bayani


09065327995






Love you oll🥰😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)








*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.


Page6️⃣0️⃣


Idan ta sanar dashi dole Gwaggo zata sani, kuma Gwaggo zata iya bata matsala akan shawara da ta yanke, musamman idan akayi la'akari da soyayyar da yiwa Muhdeen.


"Eh Asbiti naje tare da Mufida na barta a can zuwa anjima zata dawo."


Daga nan kitchen ta nufa dan ta kawo masu breakfast nasu, jin muryar Gwaggo tayi tana cewa


"A'a idan saboda mu zaki shiga dawo ki huta, don nariga na cika ciki na ban tsaya jiranki ba nida Sani muka ci."


Daga nan Mummy komawa d'akinta tayi, duk da tana jin yunwar amma ji take ma ba zata iya cin komai ba.




Koda Muhdeen ya shiga d'akin Umma ya samu zaune a bakin gadon, sai Mama Huraira ce a gefenta sai wasu mata guda uku mak'otan Umma da suka zo dubiya.


"Assalamu alaikum"


Gaba d'ayansu suka amsa sallama, ya k'araso ya durk'usa ya gaishe su cikin girmamawa tare da k'ara tambayar Umma da jiki, suka amsa masa da sauk'i.


Dube-dube yake kamar mai neman wani abu, ya kasa magana da dukkan alamu Inteesar bata cikin d'akin, tamabayar kansa yake ko ina take ko tana toilet ki kuma ta fita tayi sallah ne, to ai kuma ga d'akin yau akwai wajen sallah bai cika ba irin na wancan ranar, Mama Huraira ce ta lura kamar akwai abunda take nema ta kalle shi ta ce,


"Muhammad akwai abunda kake nema ne?"


Murmushi yayi tare da cewa


"Bakomai na d'auka Inteesar tazo ne."


Girgiza kai tayi tare da cewa


"Gaskiya yau bata zo ba, ka barta a gida bata nan ne?"


Ya rasa ma ta ian zai fara mata bayani,magana ya fara yana cewa


"Dama munyi zata zo ne, to na d'auka ta iso ne ashe bata zo ba"


Girgiza kai tayi


"Bata zo nan ba gaskiya."


Sallama yayi masu tare da cewa bari ya koma gidan kila bata samu fitowa bane.


Mummy tana zaune kan sallaya tana azkar na yammaci, tana ta rok'awa Inteesar sauk'i a wajen Allah, bayan ta idar ne tana cire hijabin taji ana knocking a k'ofar bedroom nata, tasan Dady baya gida Mufida na asibiti Gwaggo na barci a d'akinta, mamaki ne ya kamata waye zai shigo har bedroom bak'o dai iya karsa falo,bada izinin shigowa tayi ta zubawa k'ofar idanu, ganin Muhdeen ne yasa ta tamke fuska dan ranta ya 'baci idan ta tuna da abunda yayiwa Inteesar.


"Assalamu alaikum"


Wa'alaika salam"


Ya k'araso ya durk'usa k'asa ya gaishe ta


"Ina wuni Mummy?"


"Lafiya lau"


Shiru yayi na tsawon mintuna biyar ba wanda yayi magana, d'agowa tayi ta kalle shi taga ya sunkuyar da kai kuma yana durk'she be zauna ba, kauda kanta tayi tare da cewa


"Ya dai ina fatan dai lafiya?"


"Lafiya lau Mummy, dama na d'auka tazo nan ne?"


Kallonsa tayi tare da cewa


"Wace ce ta zo nan?"


"Inteesar nake nufi."


"Ce maka tayi nan zata zo? to nidai banganta tazo ba, amma ka shiga d'akin kakarku ka tambaye ta ko tazo nan tana d'akinta kafin ta k'araso nan."


Jinjina kai yayi tare da cewa


"To bari naje na gani ko tana can"


Mik'ewa yayi ta bisa da kallo ya fice don zuwa d'akin Gwaggo.


Gwaggo na zaune a bakin gadonta tana cin goro Muhdeen ya shigo d'akin ba tare da yayi mata sallama ba, kaallon mamaki take masa tare da cewa


"Yau naga ja'irin yaro d'akin kafura ka shigo da ba zakayi mani sallama ba? d'an banza mai suffan yahudu da nasara, ko nayi kama da kaba'ira ce da ba zakayi mani sallama ba."


Bai tanka ta ba ita kuma bata fasa fad'a da take ba, kallonta yayi tare da cewa


"Ba wannan ya kawo ni ba, Ina mata ta take?"


Kallonsa take shek'ek'e take kafin ta ce,


"Ka d'auke ta inda ka ajiye ta."


Kauda kanta tayi ta cigaba da taunan goronta, ganin ta share sa ne yasa ya k'ara mata magana yana cewa


"Bata gida kuma bata wajen Ummanta ba inda nake tunanin zata je da ya wuce nan."


"Kai ka fita a Ido na, ka kiyaye ni na fad'a maka dan tsabar ka raina ni idan uwarka ce zaka shiga mata d'aki haka ne? ko kuma zakayi mata magana haka? Bansan inda matarka take ba ko ce maka tayi waje na zara zo da zaka titsiye ni da tambayar inda take? wata kila ma ba nisa tayi ba ta koma gida kazo kana damu na, ka fitar mani a d'aki ko yanzun nan na kira ubanka a waya yazo yayi mani iyaka da kai."


"Ank'i a fata daga d'akin naki"


"Haka ka ce?"


"Eh haka na fad'a kuma haka kika ji."


Wayarta ta ciro daga k'asan filo tana cewa


"Yanzun ubanka zai mani katanga da kai."


Tana shirin kiran wayar Dady bayan ta lalaubo number dak'yar tana kashe ido dan bata gane wayar sosai, tana kara wayar a kunnenta.


Cikin zafin nama ya fisge wayar, tare da sakawa a aljihu ya kalle ta ya ce


"In banda masifa da kika saba da shi daga tambaya ina mata ta sai bak'ar magana?"


"Ka bani waya ta kuma kaje can gida matarka nasan tana gida ba inda zata tafi ba saninka."


Jefa mata wayar yayi sannan ya nufi k'ofar fita, jin muryarta yayi tana cewa


"Ka jefi uwarka Fatima amma ba ni Kulu ba"


Har ya tsaya zai bata amsa ya kuma yi ficewarsa ya barta tana ta masifa ita kad'ai.


A can gida kuwa Sumayya da taji yunwa na neman illata, ta sai ta kira Ishaq Direba ta aike sa yayo mata takeaway, tana zaune tana ci ya turo k'ofa ya shigo, dube-dube yake ganin bata falon ne yasa ya nufi d'akinta nan ma bata nan, kallon Sumayya yayi tare da cewa


"Har yanzun Wai bata dawo ba?"


Ta'be baki tayi tare da cewa


"Dama ka daina wahalar da kanka akan nemanta."


Wani banzan kallo ya mata


"Akan me kika ce haka?"


Gani nayi akan me kake wahalar da kanka bayan ta fita bata sanar da kai ba, ka fita harkarta kawai


"Karki sake mani magana makamancin wannan, ke idan zaki fita sanar dani kike yi? ba gara ma ita da ke ba, nasan dai ba zata ta'ba fita gidan nan ba tare da izini na ba, sai dai idan wani abu daban ne, ke tunda na aure ki dai-dai da rana d'aya baki ta'ba bin magana ta ba, ko kibi abunda nake so bakiyi, kina mani biyayya a matsayi na na mijinki wanda mukayi auren soyayya da ita, ita Inteesar ba auren soyayya muka yi ba, hasali ma na tsane ta bana son ganinta, koda aka aura mani ita haka na dinga wahalar da ita da bautar da ita da ayyukan wahala, bana barin ta huta haka zan dinga wahalar da ita ba tausayawa, hakanayyukan da ba sai tayi ba haka zan saka ta yi bana bari ta huta, amma duk da haka tana kallo na a matsayin mijinta bata ta'ba nuna mani 'bacin ranta ba, kwanakin baya Mahaifiyar k'awarta ta rasu Mufida ta biyo mata su tafi, haka tasa Gwaggo ta Kira waya ta har na bada izini sannan ta tafi, shekaranjiya na same ki d'aki kina shirin zuwa oarty, na nuna maki kada ki tafi, ina da buk'atarki haka kikayi fatali da buk'ata na mijinki kika fita ba tare da izinin mijiki ba, ina cikin halin buk'atar mace kika tadi kika barni, Allah da ikonsa sai ya turo mani ita a dai-dai lokacin da ya dace, gashi bata cikin kwanciyar hankali kuma ga mahaifiyarta kwance ba lafiya, a haka na nuna mata buk'ata ta kuma ba gardama ta amince mani saboda tasan girman hakkin mijinta kan wuyanta tasan laifin bijirwa miji masifa ce, amma ke baki San hakan ba, matar da akan rashin lafiyar Umma bata tafi ba sai da ta nemi izini na sannan ta tafi, wani uzurin kuma zaisa ta fita ba izini na."


Kallon mamaki take masa har ya gama maganarsa, sannan ta ce


"Kana nufin ta ta fini kenan ?"


"Kee Sumayya wallahi ki kiyaye ni, a halin yanzun raina a 'bace yake kada ki tunzura ni, dan idan kika tunzura ni zan aikata abunda daga ni har ke bazai muna dadi ba, Dan haka ki kiyaye ni kafin yanzun nan Kisha mamaki, dan zan aikata abunda daga ni har ke bazai muna dad'i ba, karki manta da wannan."


Daga nan ya fice ya barta zuciyarta na tafarfasa, tana mamakin wai yau ita Muhdeen ke fad'awa haka.


Mummy na zaune a d'akinta tana tunanin halin da Inteesar ke ciki, wayarta ce ta fara ringing ganin Mufida ce tasa ta d'aga ta rawar jiki kafin tayi magana Mufida ta ce,


"Mummy Albishirinki."


Murmushin farin ciki tayi ta ce


"Goro ta farfad'o ne?"


Mufida ta kalli Inteesar dake zaune ta jinjina bayanta da filo ta ce,


"Eh Mummy gata nan zaune wallahi na tambaye ta me ya same ta muka same ta kwance cikin jini da kwalabe, tayi mani shiru bata bani amsa ba, amma idan kika zo kila tayi maki magana, duk maganar da nake mata bata ce komai ba kallona kwai take kamar wata kurma."


Shiru Mummy tayi tana nazari kafin tace,


"Ina Doctor take?"


"Yana office nasa"


"Yasan ta farfad'o?"


"A'a bai sani ba."


"To kiyi sauri ki sanar dashi yanzun nan, nima gani nan zuwa."


Daga nan ta katse kiran ta d'auki mayafinta da handbag ta nufi hanyar fita.








*Daga alk'alamin*✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)




Don k'arin bayani


09065327995






Love you oll😍😘


Comments & shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89








*INTEESAR*




Story & writing by✍️


Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)






*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*






*GARGA'DI*


Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izinina ba.




*SANARWA*


Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarce ni bada niyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.




*SADAUKARWA*


Wannnan shafin naki ne Faty mannir ina jin dad'in comment naki, don haka na sadaukar da wannan shafin a gare ki naki ne, kiyi yadda kike so da shi, sauran members na INTEESAR ma ina godiya da da comments had'i da add'ar da kuke mani Allah yabar k'auna.




*BISIMILLAHI RAHAMANI RAHEEM*


Page6️⃣1️⃣


Daga nan ta katse kiran ta d'auki mayafinta da handbag ta nufi hanyar fita.


Kici'bis suka yi da Dady wanda shigowarsa kenan daga waje, ganin yadda take sauri yasa ya ce,


"Ina kuma zuwa haka?"


Shiru tayi tana nazari kafin ta ce


"Asibiti"


"Waye kuma baida lafiya"


Jim tayi kafin ta ce,


"Inteesar"


A kid'eme ya kalle tare da cewa


"Subhanallahi me ya same ta?"


A juyar zuciya ta sauke


"Alhji dogon labari ne ba lokaci muje kawai."


Kallon k'ofar d'akin Gwaggo yayi tare da cewa


"Ina Gwaggo"


"Tana d'akinta barci take"


Fita sukayi inda ta umarci Direbanta ya kaisu asibitin da Inteesar take, shiga sukayi bayan motar aka jasu zuwa Asibiti.


Zaune take akan gadon marasa lafiya kanta an nad'e shi da bandeji,Mufida na zaune a gefenta Doctor yana tambayarta yadda take ji ko akwai abunda ke damunta, kai kawai ta girgiza alamar ba komai.


Mummy ce ta turo k'ofar ta shigo Dady na biye a bayanta, k'arasawa tayi kusa da Inteesar ta rungume ta hawaye tab a idanunta ta fara magana


"Sannu Daughter ya jikin naki?"


Take hawaye suka dinga ambaliya daga fuskarta kamr an bud'e famfo, Mummy tasa hannayenta tana goge mata hawayen tana cewa


"Ki daina kuka Daughter zaki samu lafiya, insha Allah komai zaizo k'arshe da yardar Allah."


Jabeer ne ya turo k'ofar ya shigo, ganin Inteesar zaune yass ya saki murmushi tare da cewa


"Alhamdulillah"


Kallonta yake yana cewa


"Ashe ta farfad'o"


Dady dai baisan me ya faru ba kuma baisan dalilin kwanciyarta Asibiti ba, kallon Mummy yayi tare da cewa


"Accident ta samu ne?"


Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa


"Sai dai idan mun koma gida muji daga bakinta amma yanzun kam bansani ba."


Kallon Doctor yayi tare da cewa


"Yaushe za'a iya sallamarta?"


"Dama ba wani abu da zamuyi mata tunda ta farfad'o, sai dai ciwon kai da ba'a rasa ba, kuma zamu bata magungunan da zata dinga sha."


Fita yayi tare da sanar dasu yana zuwa


"Inteesar ce ta fashe da kuka tana cewa,


"Mummy dan Allah kada ku mayar dani gidan Yaya wallahi bazan iya jurar zaman gidansa ba."


Ta k'arasa maganar tana mai sake fashewa da wani sabon kukan, rungume ta Mummy tayi tana cewa


"Daina kukan haka nan ba zaki koma gidansa ba kinji? ki kwantar da hankalinki ba zaki koma can ba, haka Mummy ta dinga rarrashinta saosai har tsagaita da kukan da take, shi dai Dady abun ya d'aure masa kai, don baisan me ke faruwa ba, ganin yadda Inteesar ta rikice yasa yayi shiru yana jiran su koma gida.


A cikin mintuna talatin aka sallame su suka koma gida inda Jabeer ma ya bisu.


Da sallama suka shiga cikin falon Gwaggo tana zaune kan kujera tana kallon T.V Africa Tv3 inda suka saka wa'azin Shekh Jabeer Sani mai hula.


Amsa masu sallama tayi tare da zuba masu ido, ganin Inteesar yasa ta mik'a ta sauri tana salati


"Inalillahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga uku ni kuluwa me ya same ki 'yar albarka naga anbi an nannad'e maki kai da bandeji?"


Ba wanda ya iya magana cikinsu k'arasowa sukayi suka zauna yayin da Inteesar ta k'arasa wajen Gwaggo ta zauna a saman center carpet kusa da kujerar da Gwaggo take zaune, kallonta Gwaggo tayi tare da cewa


"Kada dai zargin da nake akanki ya tabbata, mijinki yazo nemanki ya ce baki gida kin fita kada dai a ce hakkinsa ne ya kamaki da kika fita ba tare da saninsa ba kika samu hatsarin mota naga an wani yi maki rawani da bandeji."


"Bayan sun zauna ne Dady ya kalli Mummy ya ce wai me ya same ta kuma ina mijinta?"


Mummy ce ta kalli Mufida ta ce,


"Ki fad'a masu abunda ta sanar da ke."


Gyara zama tayi ta sannan ta basu labarin irin zamantakewar da ke tsakanin Inteesar da Muhdeen da duk wahalhalun da tasha a gidansa a hannunsa da matarsa, komai sai da ta sanar da su kamar yadda Inteesar ta bata labarin komai ba abuda ta 'boye masu, da yadda Inteesar ta nuna cewa subar maganar a sirri kada ta fad'awa kowa.


Gaba d'aya Falon tsit sukayi kamar ruwa ya cinye su, ran kowa ya 'baci sosai da abunda Muhdeen ya aikata, tausayin Inteesar kawai ke cikin zuciyarsu musamman Gwaggo da ita ce sanadiyar had'in auren nasu, gani take ko wane hali Inteesar ta shiga ita ce ta jefa ta ita ce sanadiyar komai.


Dady ne ya kalli Inteesar ya ce,


"Mu a iya saninmu matarsa tana can London bamu san cewa ta dawo ba tana gidan ba, tun yaushe ta dawo k'asar?"


Cikin sanyin muryarta ta ce,


Tun ranar da Gwaggo ta bar gidan, don tafiyar Gwaggo kenan naji yana waya yana cewa zaizo ya d'auke ta, ya ce mani nayi girki na musamman zamuyi bak'uwa sai da tazo naga ashe ita ce."


Gwaggo ce ta fara magana


"Ke kuma da kina shashasha kika zauna yana wahalar dake da bautar dake ko? sannan har wannan matar tasa zata maidake baiwarta kina ji kina gani ko? ta kwanta da miji akan gado suyi abunda zasuyi su shiga toilet suyi wanka su fito, ke zaki shiga ki gyara masu gadon ki wanke masu toilet d'in ko?"


Ta k'arasa maganar cikin k'unar rai, kafin ta cigaba da cewa


"Allah ya wadaran naka ya lalace, Inteesar kin bani kunya, wai bata iya girki ba kece zata bawa umarnin ki dafa mata abunda take so, kiyi mata duk wani aiki, bata aikin komai sai dai ta ci ta Sha ta kwanta ko?"


K'wallar da suka cika mata idanu ne ta goge tare da cewa


"Ni na d'auka zaman aure nakeyi, kuma aure ibada ne, na kudirta cewa duk abunda ya umarce ni nayi zanyi shi ne matuk'ar bai sa'bawa addinin musulunci ba, saboda neman Aljannah ta nakeyi, kuma shine ya umarce ni da nayi mata duk..."


Wani tsawa ta daka nata tare da cewa


"Dalla rufe mani baki, tunda nake baki ta'ba 'bata mani rai irin na yau ba, me matar tasa ta fiki da shi kyawu ko kuma diri? ba abunda zata nuna maki wanda ta fiki da shi, wato shiyasa ranar da zan dawo nan ya dinga farin ciki yana Allah Allah na tafi ashe akwai abunda yake k'ullawa."


Dady ne ya kalli Inteesar ya ce,


"Wannan ciwon na kanki fa ya akayi kika jishi?"


Kuka ne ya k'wace mata nan suka dinga rarrashinta har ta tsagaita ta fara magana


"Ina kwane ina barci ne shine na bud'e Ido na naganta a kaina, da sauri na sauka daga gadon kawai sai naji saukar abu a kaina daga nan bansan komai ba

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads