Showing 9001 words to 12000 words out of 149432 words
Chapter 4 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
karasa maganar
Dady ya tattaro dukkan hankain sa ya maida Kan muhdeen sannan yace,
"Kayi magana Mana Muhammad Ina Jin ka."
Sunkuyar da Kai Muhdeen yayi tare da Fara magana.
"Dma akwai yarinyar da muka dai-daita da ita ne,shine ta kirani Wai mahaifin ta yace na turo magabata na suyi magana."
Cikin Jin dadi Dady ya furta
"Kai Masha Allah,naji dadin Jin wannan maganar daga bakin ka.don dama buri na kenan naga auren ku."
Juyawa yayi ya kalli Mummy tare da cewa.
"Bakiji abunda danki ya fada ba?"
Jinjina Kai tayi tare da cewa
"Naji,Amma ka tambaye sa ya tarbiyya yarinyar take?tana da dabi'u masu kyau da addini? Idan ba mantawa nayi ba akwai ranar da Asiya ta nuna mani photon yarinyar a wayar sa,kuma gaskiya nikam bat..."
Abba ne yayi saurin cewa
"A'a kada kice komai tunda baki taba ganin ta ba, photo kawai bazaisa ki fassara 'yar mutane ta wace siga ba.baki da hujja,kedai kawai fatan alkhairi zakiyi masu tunda suna son juna."
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa
"Shikenan.Allah ya tabbatar Muna da alkhairi."
Ameen Abba yace
Sannan ya kalli muhdeen da ya sunkuyar dakai kasa yace
"Ita yarinyar 'yar gidan waye kuma a Ina suke?"
Cikin Jin dadi yace,
"Dady suna zaune ne agarin Abuja sunan mahaifin ta Alh. Tanimu Dan kasuwa ne,kasuwancin Gwal-gwalai yakeyi daga kasar dubai.amma dai yanxun haka suna zaune a London ita da iyayen nata.sai dai ta sanar dani ta hanyar text message Wai gobe zasu dawo Nigeria."
Kai Abba ya jinjina alamun gamsuwa Sanan yace,
"Zanyi bincike akai,idan yaso sai na Kira Yaya Adam da minina Alh.kabir sai muyi abunda ya dace."
Haka kuwa akayi a cikin sati daya aka saka ranar Auren Muhdeen da sumayya nan da watanni biyu masu zuwa.farin ciki a wurin masoyan guda biyu baya misaltuwa,domin abunda suke buri kenan.
Wata ranar Asabar ne Muhdeen ya sanar da Mummy cewar zai kawo Mata sSumayya ta gaishe a.mummy taji dadin hakan sosai.
Da misalin karfe biyar na yamma sumayya ta gama Shirin ta tsaf da kananun Kaya tasaka saboda dasu ta Saba, mom din ta ce tace ta cire su saboda gidan surukanta zataje tayi shiga na mutunci,zasufi ganin mutuncin ta.dakyar ta yarda ta saka wasu matsatstsun Riga da siket na leshi sun matse ta sosai kamar zatayi numfashi su yage,wayar ta ne tayi ringing Jin ringing din wayar yasa ta sakin murmushi,domin tasan waye ke kiranta ringing d'in sa na musamman ne tasa masada sauri ta daga wayar.
"Hello sweet ganinan fitowa"
Muhdeen dake zaune a motar say Yana jiran ditowar ta ne ya ce,
"Please Baby kiyi shigar mutunci da Kamala,na hanaki saka irin kayayyakin da kike sawa kinki ji ko?"
Tura baki tayi tace,
"To ni fa kasan dasu nasaba."
Muhdeen ya ce,
"Ai zance ya kusan karewa da zaran mumyi aure manyan Kaya da manyan hijabai Zaki dinga sakawa,idan kinda kananun Kaya sai dai idan ni zakiyiwa kwalliya"
Murmushi tayi sannan ta ce
"Ganinan fitowa gashin attached din da akayi Mata Kari ta sake shi baya,tayi daurin Dan kwalin nan da ake cewa ture kaga tsiya,siririn mayafi ta rataya shi a gefen kafad'arta ta tare da rataya handbag dama tayi kwalliya fuska tun daga Kan powder har janbaki ta fesa turarurruka kala uku tasa takalmin ta mai tsini ta dauki wayoyin ta ta rike a hannu.ta nufi kofar fita.Afalo ta samu mahaifiyar ta,sallama tayi Mata ta fice.
A cikin mota ta same shi Yana jiranta,bude murfin motar tayi ta shiga ido ya zuba mata yana kallon ta sai sakin murmushi takeyi ta jujjuya ido takeyi tare da cewa.
"Baby ya kaga shigar manyan kayan nawa?yayi ko?"
Zuba Mata ido yayi tare da cewa
"Ba laifi"
Zuba masa ido tayi
"Cewa zakayi ba laifi? Bayan Kai da mummy ne kuka ce nasa kayan mutunci Amma ki ka Yana Mani?"
Murmushi yayi tare da cewa
"Sorry my Baby kinyi kyau Amma kike kisaka Koda irin 'dan abayar nan ne da mayafi da mata ke sakawa"
Kallon mamaki tayi masa tace,
"Tab wlh bazan iya kayan wahala ba duk nauyi ya dameni ga zari ba yanda isaka zai shiga ."
Jinjina Kai yayi
Taci gaba da cewa
"Ni bana ma da abayar ballantana nasaka."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Ba damuwa zamu siya a hanya sai ki saka mu karasa gidan"
"Yakamata ka gane zansha wahala idan na saka"
Yace,
"Shikenan mu tafi"
Baiso haka ba amma ba yadda yadda iya,baiso hakan ba.
Horn sukayi Mai gadi ya wangale masu kofa suka fita,basu same ki Ina ba sai gidan su Muhdeen.Bayan yayi horn mai gadin gidan ya bude masa kofa ne ya shiga yayi parking.
Atare suka bud'e marfin motar suka fito,Tana tafiya cikin takunta na yanga har suka karasa falo,ba kowa sai Mufida dake zaune a Kan kujera ,ganin su ne yasa ta mike cikin farin ciki ta ce
"Sannu da zuwa Aunty Sumayya oyoyo matar Yayan mu"
Sumayya ma murmushi tayi tare da cewa
"Yauwa Mufida ya karatu
"Alhamdulillah"
Kasancewar Sumayya tasan kowa a gidan Muhdeen ya tura Mata photon su tun daga kan Dady da Mummy da Asiya da Mufida duk tasansu a photo.
Inteesar ce ta fito daga dakin Mummy sanye da Hijab ganin Inteesar sai da gaban Sumayya ya fad'i
Inteesar cikin fara'a ta kalle su tare da cewa
"Sannu da zuwa,Ina wuni?"
Yamutse fuska Sumayya tayi tare da cewa
"Wace ce wannan?"
Mufida tace kamar 'yar uwa take a wurin mu kullun Muna nan gidan a tare sunanta Inteesar"
Sumayya ta Kare Mata kallo ganin irin kyawun da Allah ya mata,gata kamar wata balarabiya Fara ce doguwa mai dara-daran idanu,ga hancin ta dogo sai dan karamin pink lips din ta duk da ta saka hijab Amma Ana ganin yala-yalan gashin kanta da ya kwanta luf a goshin ta
take sai taji tsanar Inteesar a cikin zuciyar ta.
Dai-dai lokacin Mummy ta k'araso falon,turus ta tsaya tana karewa summaya kallo,
Cikin wani irin murya ta ce
"Son wannan ce matar da zaka aura?"
Muhdeen ya zamo daga Kan kujera ya durkusa akan center carpet din falon
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love you oll😘😍Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman ihsa)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin Rubuta ta Shi Dan cinzarafi ga kowa ba.idan suna ko hali yazo daya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe Auren Wawa
Page0️⃣9️⃣
Muhdeen ya zamo daga Kan kujera,ya durkusa akan center carpet din falon.cikin far gaba ya ce
"Mummy itace, na kawo ta ta gaishe ki."
Jinjina Kai mummy tayi tana karewa Summaya kallo,gani tayi sam bata dace da Rayuwar Dan ta ba,dan daga gani bata samu tarbiyya mai kyau ba do daga gida ba,kallon Karin gashin da akayi mata ne ya zubo har tsakiyar bayan ta ga uban make up har yayi yawa,suturar jikin ta ya bayyana surorin jikin ta a bayyane, girgiza Kai tayi ta karaso ta zauna kan kujera.
Muhdeen idon sa nakan mahaifiyar sa yana karantar yanayin ta.
Sumayya daga yanda take zaune Kan kujera ta gaida mummy ta ce,
"Barka da fitowa mummy"
Cikin sakin fuska Mummy ta ce,
"Yauwa sannu da zuwa"
Sumayya ce daga yanda take zaune Kan kujera ta Kara da cewa,
"Ina wuni Mummy"
Ba yabo ba fallasa
Mummy ta amsa Mata da,
"Lapiya qalau Sumayya,ya mutanen gidan?"
Amsawa tayi da duk suna lafiya
Dai-dai lokacin ne Inteesar da Mufida suka loda Mata kayan ciye-ciye da lemu da ruwa a gaban ta.
Shidai Muhdeen yana zaune a kasa saman carpet,don dama shi idan iyayen say suna zaune a kujera shi yana k'asa a zaune.koda kuwa daga baya suka zo suka tarar da shi akan kujera da zaran su zauna zai sauka kasa.Haka ma sauran kannen sa, Inteesar ma dabi'ar ta ce wannan tun fil'azal.
Sumayya ruwa kawai tasha Wanda mufida ta kawo tata,kayan ciye-ciyen da Inteesar ta kawo mata kuwa ko kallon su batayi ba ballantana ta taba.
don haka kawai sai taji kishin yarinyar musamman yanda taga Allah yayi mata sura Mai kyau gata Tana zaune a gidan su Muhdeen,kuma tasan dole zai dinga yawan ganin ta.sai tsanar Inteesar ya sake nunkuwa a cikin zuciyar summaya,don tasan tafita komai,abu d'aya zata fita dashi shinec tsayi Don sumayya doguwa ce tafi Inteesar tsayi.bayan nan ba abunda zata n mata,ko hasken fata ma idan Kika kalli Inteesar da sumayya zaki ga Sumayyar ta fita hasken fata.don ita tana karawa da mai maisa hasken fata shiyasa farin nata ya zarce na inteesar.amma da badon mai ba Inteesar tafita hasken fata
Ido ta zubawa Inteesar sai taji k'irjin ta na dukan uku-uku,ta juya ta kalli Muhdeen dake zaune kasa saman carpet tace,
"Baby mu tafi ko"?
Kallon juna sukayi mufida da Inteesar yayinda mufida dariyar da take 'boyewa ne ya kufce mata.
Ganin kowa ita yake kallo yasa taja hannun Inteesar suka shige dakin ta da sauri.
Mummy ce ta kalli sumayya ta ce,
"Tun yanzun gashi komai baki ci ba?"
Yamutse fuska Sumayya tayi yayinda ta kalli kayan ciye-ciyen da Inteesar ta ajiye Mata tare da cewa
"Mummy am okay"
Mummy ce ta Mike tare da cewa
"Ina zuwa"
Kai tsaye dakin ta ta nufa,ba jimawa ta fito dauke da Leda a hannun ta.d'an kunne da sarka ce sai Turarruka a ciki.
Karasawa tayi ta mikawa Summaya karba tayi tare da yin godiya mata sallama suka fita ita da muhdeen
Mummy k'arasawa tayi d'akinta zuciyar ta cike da sake-sake ,tana ganin Sam batayi sa'ar suruka ba,ta dad'e tunanin hakan lokutan da take ganin pics d'in ta da Mufida ta nuna mata wasu ka ganta ba dankwali sai tulun Karin gashin wasu ba suturu. Kirki gasu nan dai da sauran su.
Tumawa tayi da maganar da Dady yayi mata na cewar tayi masu fatan alkhairi kawai kada tayi tunanin komai,hakan yasa a cikin xuciyar ta tace Allah ya Sanya alkhairi.
A bangaren Muhdeen da Sumayya kuwa suna tafiya a mota ne sumayyay ta kalle shi tare da cewa,
"Baby na Wai meye alakarku da yarinyar nan ne?"
Ba tare da ya kalle ta ba idanun sa nakan tuk'in da yakeyi ya ce ,
"Wata yarinya kenan?"
Yamutse fuska tayi ta ce,
"Wadda suka shiga daki da Mufida,Mai sanye da Hijabin nan Mana"
"Okay Inteesar kike nufi ko?"
"Eh"
Ta amsa masa a takaice
Dan Jim yayi kafin yace
"Bamu da wata dangantaka ta jini da ita"
Gaban ta ne ya tsananta bugawa,ta kalle shi tare da cewa
"To zaman me takeyi a gidan ku?"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Nima kaina ba son zaman yarinyar nan nakeyi ba,hakanan kawai naji na tsane ta a cikin zuciya ta,wallahi bana kaunar zaman ta agidan nan.ke intakaice maki Zaki zance ban taba Jin tsanar wani mahaluki a duniyar nan kamar yadda na tsani ganin yarinyar nan ba.
Sumayya wani irin murmushi tayi wanda sai da hak'oranta suka bayyana,cikin jin dad'in kalaman sa ta ce
"Ai da kasa an Kore ta a gidan"
Da sauri ya kalle ta tare da cewa
"Ke! Kinsan yadda Mummy take k'aunar yarinyar Nan kuwa?To bari kiji zata iya 'batawa dani akan yarinyar nan,don ba k'aramin son ta takeyi ba wallahi,ke ba ma ita ba hatta Dady da Mufida suna matakar son ta nida Asiya ce kawai bamu k'aunarta don ma yanzun Asiya bata k'asar tana can kasar Turkey tana karatu."
Shiru tayi tana sauraron sa kafin daga bisani tace,
"To ya akayi tazo gidan?"
Muhdeen ya ce
"Mummy ce zata fita unguwa Direbanta yad'an kad'e ta, mummy ta bita gidan su a bayan layin mu daga nan dai ta janyo yariyar a jikin ta,da taso iyayen yarinyar su bata ita taci gaba da zama a hannunta gaba d'aya,so sai iyayen suka ce a'a ita kad'ai Allah ya basu bazasu iya rabuwa da ita ba.amma fa kwana ne kad'ai batayi a gidan amma nan take ko wane lokaci."
Juyawa yayi yana kallonta kafin ya maida hankain sa Kan tukyin da yakeyi sannan ya ce,
"Wai me yasa kika damu da sanin ko wace ce it's?"
Girgiza Kai tayi tare da cewa ,
"Bakomai ,kawai dai na tambayar ne dan naganta kuma bansan ta cikin 'yan gidan kuba."
Daga ita har shi ba wanda ya cewa kowa komai har suka karasa gidan su Sumayya sallam su kayi inda ya shaida Mata gobe zai shigo.sannan yaja motar
yabar gidan
Ranar monaday da misalin karfe tara na safe Yana zaune a office din sa yana duba mara sa lapiya, yayin da yake ma wani dattijo tambayoyi yana bashi amsa shi kuma yana rubutu a file d'in da ke gaban sa ne jabeer ne ya turo kofar office din ya shigo,don dama shi kadai ne yake shigo masa office Kai tsaye.zama yayi Kan sofa din dake cikin office din ya zauna,bayan ya sallami dattijon tare da sanar dashi inda zaije ya mik'a file din.
Karasowa yayi ya zauna kusa da Jabir tare da mik'awa Jabeer hannu
Murmushi jabeer yayi ya ce
"Angon Sumayya mai jiran gado, har ka Fara kamshin angonci tun yanzun."
Kallon shi Muhdeen yayi tare da cewa
"Ai kallon ka kawai nakeyi duk yadda muke dakai banida aminin da ya wuce ka kuma dan uwa a gare Ni dan wan mahaifina amma ace tunda sumayya suka dawo garin nan baka taba zuwa kun gaisa ba har tambayar ka tayi."
Rik'e baki Jabber yayi yana dariya yace afuwan aboki yau zamuje tare inasha Allah.
yauwa na manta ban fad'a maka ba wannan rigimammitar tsohuwar na kira ta jiya tana ta zagin ka ashe dama baka kiranta ka gaishe ta?tana matsayin mahaifiyar Dadyn ka?"
Tabe baki baki Muhdeen yayi tare da cewa
"Mahifiyar Dady kace ai ba mahifiya ta ba,matar da duk mutum yayi waya da ita sai ta 'bata masa Rai shiyasa na daina Kiran ta."
Dariya yayi tare da cewa
"Ai ciwon Kai Kam yaxun zaka Fara don tace jibi tace zata so,kuma kasan idan tazo gidan Dadyn ka take sauka."
Had'e fuska yayi tare da cewa
"Dama duk cikin jikokin ta tafi saka mani ido wallahi."
Jabeer ne yace
"Ko kuma tafi kowa kaunar ka ba don wallahi tafi sonka fiye da kowa a cikin jikokin ta."
Fira suka 'dana taba kafin ya tashi ya koma office din sa.
Bayan kwana biyu kuwa sai
Gwaggo ta baro garin Kontagora ta iso garin Minna tun ana bikin Muhdeen da Sumayya saura wata biyu tazo.murna a wurin Mummy da Mufida ba'a magana.
Waya ta d'auka ta Kira mu6hdeen tace kada ya dawo gidan nan ba tare da yazo mata da amaryar da zai aura yau d'innan idan ba haka ba ko ruwa bazata bari yasha a gidan nan ba.
Sanin rigimamar Gwaggo ne yasa baida wani zabi dole ya Kira Sumayya yace ta shirya zaizo ya dauke ta ta gaishe da kakar sa da tazo.
Misalin karfe biyar na yamma Mummy ce zaune a falo yayin da Mufida ke zaune Kan carpet,Gwaggo ta shiga ta watsa ruwa.
INTEESAR ce ta turo k'ofar karamin gate din gidan ta shigo gaisawa tayi da Mallam Ibrahim mai gadi sannan ta shige cikin gidan.
Bakin ta d'auke da sallama ta shiga falon durk'usawa tayi har k'asa ta gaida Mummy sannan ta kalli Mufida ta ce,
"Yauwa Mufida Ina Gwaggon take?kinsan ban ta'ba ganin ta ba,wallahi na k'osa na ganta ba."
Mummy ce tayi murmushi tare da cewa,
"Karki damu Inteesar yanzun zata fito Zaki ganta"
Dai-dai lokacin ne Muhdeen ya shigo da sallama sumayya na biye dashi a baya suka karaso yayin da Muhdeen ya zauna a k'asan carpet ganin Mummy akan kujera, s6umayya ta zauna kan 1 seater dake facing din mummy gaida mummy tayi ba yabo ba fallasa ta amsa Mata,
Mufida ta nufi d'akin da Gwaggon take sauka ta sanar da ita cewa Muhdeen ya shigo da matar da zai aura.
Da sauri Gwaggo ta nufi falon 'dan kwalinta a hannun ta take fad'in
"Ina kishiyar tawa take inga da mai tafini da ya tsallake ya tafi wurin ta"
Idon ta ne ya sauka akan Inteesar dake zaune a carpet Muhdeen na gefen ta 'dan nesa da ita.
Washe baki tayi tana fad'in
" masha Allah wannan had'in yayi ai daga ganin zaren ma kalan yadin ne,gata kyakkyawa kamar shi jikan nawa."
Dan Bata lura da Sumayya dake zaune Kan kujera ba.durkusawa tayi ta kamo ha'bar Inteesar tana cewa
"Kai kyakkywar kishiya ta dole nayi kishi dake."
Gaba d6aya falon tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah.Sumayya Kam ta cika da bak'in ciki tayi fam,idon ta ne yakai kan Sumayya dake Kan kujera wani kallo shek'ek'e take mata sannan ta nuna Sumayya tabce,
"Ina kuka samo wannan Mai zubin karuwai?"
Muhdeen ne ya ce
"Haba Gwaggon ki dinga tsayawa kina tabbatar da abu kafin ki fad'a mana,matar da zan aura kike cewa karuwa?"
Ware idanun ta tayi tare da nuna sumayya sannan tace,
"Kana nufin wannan zaka kawo a cikin zuri'ar mu? a matsayin uwar 'ya'yan ka?Haba Muhammadu to nikam bada yawu na ba."
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Don k'arin bayani
09065327995
Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi (Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_
*Alk'alaminmu 'yancinmu*
*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*
Wannan kagaggen labari ne ban rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo daya to ku gafarceni ba da niyyar yin hakan nayi ba, arashi ne mai kashe auren wawa.
Page1️⃣0️⃣
Cikin daurewar fuska ya kalli Gwaggo ya ce,
"To ni ita na gani nake so, kuma bazan canza ra'ay ina akanta ba".
Hannu Gwaggo tasa ta rike baki cikin mamaki ta ce,
"Allah buwayi Gagara misali, oh ni yau naga abunda ya ishe ni, to bari ka ji ko Uban da ya haife ka bai isa idan nace a'a yace mun Eh ba, ballantana kai dansa".
Murmushi Mai cike da takaici Muhdeen yayi sannan ya kalli Gwaggo yace,
"To ai Dama Dady bazai tsallake maganar ki ba saboda ke kika haifesa, "Amma ni kama bak...
Tsawar da Mummy ta daka masa ne yasa ya fasa karasa abunda yayi niyyar fada.
Cikin bacin Rai Mummy tace,
"Kanka daya kuwa? Gwaggon kake fadawa haka, wani irin rashin hankali ne wannan?"
Gwaggo ce tace
"Kyale shi Fatima idan bai ci mun mutunci ba ai bai isa ba".
Sai kuma ta fashe da kuka tana murzar idanu da d'an kwalinta tana fadin
"Yanzu D'an nan ni za ka yi wa cin mutunci a bainar jama'a? Ni ka wulakanta ka nunawa duniya ban isa da kai ba? Dan na hana ka bai kamata ka aure karuwa ba ko?"
Muhdeen