Showing 51001 words to 54000 words out of 149432 words
Chapter 18 - INTEESAR Book Complete by Zainab Abdullahi.txt
Dad d'in Sumayya Yana ringing baj d'aga ba, har sau uku.Nan dai ya kwantar wa Muhdeen da hankali,ya ce su tafi masallaci kasancewar lokacin sallar magarib tayi.
*WAIWAYE*
A ranar da Sumayya ta k'ona kayan lefenta bayan ta koma d'aki ta Kira Mum d'inta tana kuka ta sanar da ita komai.Ran Mun nata ta ce ta tattara kayanta ta bar gidan wani irin wulak'anci ne zasu bada auren 'yarsu sati biyu da aure a k'ara mata kishiya?bazai yiwu ba.Ta bata shawarar ta tattara kayanta tabar masa gida kada ma ta je wurin da zai nemota ta tafi Hotel washe gari ta jirgi ta taho.Shiyasa da Muhdeen ya gama zaga gidajen duk Wanda yasan Yana da alak'a da Sumayya bai same ta ba.wannan shine abunda ya faru
Bayan Dady da Muhdeen sun tafi Masallaci basu dawo ba sai da aka Kira sallar isha'i.Suna zaune a Dinning table kafin su fara cin abinci Dady ya k'ara gwada Kiran number Dad d'in Sumayya.A wannan karon ya d'aga.Kasancewar wayar a amsa kuwa take yasa dukkansu Gwaggo da Mummy da Muhdeen suna jiyo muryar Dad d'in Sumayya.
"Me ka kirani a waya ka sanar dani? cewa d'anka ya saki 'yata ko me? Kunsan kuma da matar da zaku aura masa kuka bari ya auri 'yata?to Bari kaji 'yata ba zata zauna da kowace kishiya ba.Tun yaushe tabar gidan da yake baku damu da halin da ta shiga ba shiyasa baku Kira ba sai yanzun ko?
Dady ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa
"Alhamdulillah tunda tana wajenku hankalina a tashe yake da naji mijinta wai baisan Ina take ba,dan Allah ka saurareni nayi maka bayani ba yadda kake tunani bane,nasan ranka ya 'baci amma ka fahimcemu."
Dad d'in Sumayya fad'a ya cigaba dayi
"Babu fahimtar da zanyi maku d'anka ya za'bi d'aya ko 'yata ko wacce kuka aura masa."
Daga Nan ya katse kiran wayar.
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Domin k'arin bayani
09065327995
*INA BARAR ADDU'ARKU DAN ALLAH KUSA K'AWATA A CIKIN ADDU'ARKU TANA CIKIN DAMUWA ALLAH YA YAYE MATA DAMUWARATA YA KAWO MATA FARIN CIKI A CIKIN RAYUWARTA.DA MA DUKKANIN AL'UMMAR MUSULMI*🙏
Love u oll😍😘Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story & writing by✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.
Wannan kagaggen labari ne banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa.
Page3️⃣4️⃣
"Babu fahimtar da zanyi maku d'anka ya za'bi d'aya ko'yata ko wacce kuka aura masu"
Ran Gwaggo ne yayi maaifar 'baci da jin kalaman Dad d'in Sumayya,don haka ta ta mi'kawa Dady hannu alamun ya bata wayar,ba musu ya mik'a Mata kamar yadda ta buk'ata.Kar'ba tayi tare da karawa a kunnenta ta fara magana.
"Waye kai da har zaka ce ya za'ba ko 'yar ka ko matar da ya aura?to bari kaji ninan kakarsa wacce ta haifi ubansa kuma ta aura masa Inteesar nace baka Isa ba kayi kad'an.kai da ka kasa ba 'yarka tarbiyya shine..."
Muhdeen ya k'araso gabanta yana had'e hannaye alamun rok'o,a hankali yake mata magana dan kada Dad d'in Sumayya ya jiyo muryarsa.
"Kinga Gwaggo ya kike neman ki 'bata komai ne?don girman Allah ki rufa mani asiri ki lalla'basu ko zata dawo,idan bata dawo ba wallahi akwai matsala ."
Tsawa ta daka masa
"Dalla can rufe mani baki kada Allah yasa ta dawo mana, idan 'yar tasa wata masifa ce ya jik'ata ya shanye."
Hannu Muhdeen ya d'ora akai ganin Gwaggo ta dagula komai.
Dad d'in Sumayya da Mum d'inta kuwa duk suna jin komai dake faruwa ta cikin wayar.
Gwaggo ta cigaba da magana
"Idan ma za'ba zaiyi sai dai ya za'bi za'bin da nayi ma..."
Mum d'in Sumayya ce ta kar'bi wayar daga hannun Dad ta katse kiran cikin 'bacin rai ta fara magana.
Akan me zasu wulak'anta mana 'ya? to bamu gaji da 'yar mu ba?wani iri wulak'anci ne wannan ace aure ko wata d'aya bai kai ba ace anyi mata kishiya,sannan ta dawo gida basu nemeta ba sai yau basu damu da halin da take ciki ba,sannan cin mutunci ne zai biyo baya?wallahi bazai yiwu ba 'yata ba zata zauna da wannan 'yar matsiyatan ba don bata Kai matsayin da 'yata zatayi kishi da ita ba."
Kai tsaye ta nufi d'akin da Sumayyar take ciki,tura k'ofar tayi ta shiga zaune ta sameta rik'e da wayarta tana kallon photon Muhdeen tana kuka.kar'bar wayar tayi daga hannun Sumayya Wanda hakan yasa ta d'ago Kai da sauri ta kalli Mum fusrkata da kwalla.
"Mum Kinga har yanzun bai biyo ni ba ki?yana can ya tare da wannan matsiyaciyar Inteesar d'in wallahi bazai yuwu ba Muhdeen nawa ne ni kad'ai duk maccen da ta ra'besa sai na kasheta ko kuma na illatata,Bata Isa ta mallaki abunda na mallaka ba."
Haka dai tayi ta surutu a cikin tana jifa da pillows d'in dake saman bed d'in, Mum d'inta ce ta rungumeta tana rarrashinta.
Muhdeen kuwa tsabar tsabar takaici da bak'in cikin abunda Gwaggo tayi ne ya ishe sa.Bayan Mum d'in Sumayya ta katse kiran ne ta kalli Gwaggo cikin jin haushinta ya fara magana.
"Wai Gwaggo meye matsalarki dani ne?duk kinbi ki addabi rayuwata,kin hanani samun nutsuwa a rayuwata wai me nayi maki ne?kullun kika tashi magana Zaki ce wai cikin jikokinki kinfi sona da k'aunata ta,amma a ganina ba Wanda kika tsana kamar ni.Kinbar kowa ya auri matar da yake so ya zauna da ita amma Ni tun ranar da na kawo Sumayyar nan a matsayin matar da zan aura kika fara kushe ta Wai bata da tarbiyya,shin ke Zaki zauna da ita da rashin tarbiyar ta ko kuma Ni zan zauna da ita?na aure ta duk da haka bai isheki ba sati biyu da auren mu kika sa aka d'aura mani aure da wata Wai Inteesar to Bari koji bana so Inteesar Sum..."
Kafin yakai k'arshen zancen Dady ya d'aga hannu zai mare shi ne Gwaggo ta daka masa tsawa
"Kai Sani!!"
Dakatawa yayi daga Marin da yayi niyar masa,don a rayuwa Gwaggo ta tsani abunda zai ta'ba Muhdeen tana k'aunarsa fiye da sauran jikokinta,tun yana yaro take masifar ji da shi Bata k'aunar taga an ta'a mata shi.
"Akan me zaka mare sa Sani?"
"Haba Gwaggo kina Jin yadda yake magana dake kamar ..."
"Ba ruwanka da nu yake bada kai ba ku daina shiga lamarina da Muhammadu."
Dallonsa Dady yayi tare da cewa
"Tashi ka tafi gidanka"
Ba tare da ya ce komai ba ya mik'e ya ya fice,gaba d'aya ya rasa me ke masa k'unci kawai yake ji a zuciyarsa,ga rashin Sumayya ga kuma aurennan na Inteesar dan ko kad'an baya Jin soyayyar Inteesar a cikin zuciyarsa.Yayi da ya sanin maganar nan a gaba Gwaggo gashi ta 'bata masa komai har ran Dady ya 'baci shi da yasa ran Dady zai fahimci halin da suke ciki amma ba haka ba.
'Bangaren Inteesar kuwa tana nan tana shan gyara sosai ciki da waje ake gyarata Hajiya Bilkisu ta daga wajen tsumata,musamman da taji cewa ba auren aoyayya bane baya sonta matarsa yake so hakan yasa ta ninka abunda tayi niyyar mata.magunguna Kam ta shasu naci da na sha ba hali tace a'a sai Aunty Bilki ta titsiyeta tasa ta cinye ko ta shanye ga na gyran fatar da ake mata bilhak'k'i.
Bayan kwana biyu abun Duniya duk ya ishi Muhdeen ya rasa yadda zaiyi, aiki ma cikin kwanciyar hankali ya gagara yinsa,zaune yake a office d'insa ya yanke shawarar zuwa ya samu Jabeer don ya rakasa suje su rok'i Dady kan maganar zauwansa London. Mik'ewa yayi ya rufe office d'in,kai tsaye office d'in Jabeer ya nufa.
Knowkig yayi Jabeer ya bashi izinin shigowa sannan ya shiga,zaune ya same shi yana shan shayi,yana ganin Muhdeen ya sakar masa murmushi yana cewa
"Angon Amare biyu ka tashi lafiya?"
Banza yayi masa kamar baiji shi ba,sau uku yana masa magana kafin ya bud'e baki dakyar ya amsa masa da cewa
"Ka rakani wajen Dady"
Kallon rashin fahimta yayi masa
"Kamar ya na rakaka wajen dady?"
Cikin yanayinsa na rashin son magana ya ce,
"Sumayya ta yi yaji iyayenta sun d'auki zafi,Ina son naje bikonta na bata hak'uri ta dawo."
"To kaje mana wa ya hanaka?au sorry na manta fa Kai har yanzun kamar yaro kake,ba zaka yi Abu Kai tsaye ba sai da izinin su Dady."
Kur'ban shayin yayi ya ajiye kofin kafin ya cigaba cewa
"Yanzun ina Ina zancen Inteesar?"
Tsuki ya ja tare da cewa
"Ni ba wannan nazo ka tambaye ni ba,ban damu da ita ba su Mummy suka ajiyeta Wai sai ranar juma'a zata tare."
"Why not ka bari idan ta tare daga baya sai kaje ka d'auko Sumayya,nifa bana son ka had'asu gida d'aya,don wlh Sumayya ba hankali ne ya isheta ba take ta illata 'yar mutane,Ni wallahi da wannan haukan da tayi ranar kake azar'ba'bin dawo da ita?da nine Kai da sai ta d'and'ani kud'arta sai ta dawo cikin hayyacinta.koda ya ke wanda ya ce zai had'iyi gatari 'bota ake rik'e masa naso ka bari idan Inteesar ta tare kaje kayo bikonta."
Girgiza kai Muhdeen yayi
"I can't"
Murmushi Jabeer yayi
"Any way, let's go"
Mi'kewa sukayi suka fice a tare,a motar Jabeer suka tafi basu tsaya ko ina ba sai gidansu Muhdeen d'in.
Ba kowa a falo hakan yasa Muhdeen ya ji dad'i a ransa,don dama baya son su tarar da Gwaggo a falo.kai tsaye part d'in Dady suka nufa a falo suka tarar da shi da Mummy,da sallama suka shiga Dady da Mummy suka amsa masu bayan sun durk'usa sun gaishe su ne Dady ya kalli Jabeer.
"Jabeer ya iyali?"
"Tana lafiya Dady"
"Masha Allah haka ake so."
Mummy ce ta ce,
Ya jikin Maryam d'in da sauk'i yanzu ko?"
"Eh Alhamdulillah jikin yanzun da sauk'i"
"Madallah Allah ya sauke ta Lafiya."
Gaba d'ayansu suka amsa da Ameen.Dady ya maida dubansa ga Muhdeen ya ce,
"Muhammad ya dai ko akwai wani Abu ne?"
'Dan sunkuyar da Kai k'asa yayi kafin ya fara magana.
"Dady dama ina son zuwa London ne na dawo da Sumayya."
Shiru Dady yayi kafin ya cigaba da cewa
"Muhammad ban hanaka zuwa ka dawo da matarka ba,amma ka d'an k'ara hak'uri Don halin yanzun ita da iyayenta a tunzure suke,ko ka ke yanzun ba zasu saurareka ba ballantana har su fahimci baka da laifi ba.Amma idan suka d'an huce sai aje a samesu,amma ka d'an basu lokaci."
Muhdeen baiso hakan ba amma ba yadda zaiyi.
"To Amma Dady har zuwa yaushe zan k'ara jira."
Ya k'arasa maganar fuskarsa d'uke da damuwa.Yana son ya sake wata maganar ne Jabeer ya d'an bige masa k'afa da nasa cikin dabara.kafin Jabeer d'in ya d'ora da cewa
"To Dady hakan za'ayi insha Alla,Mungode"
Kai ya Dady ya jinjina cikin gamsuwa da maganar Jabeer d'in.
"To shikenan Allah yayi maku albarka."
Amsawa suka yi da Ameen sannan sukayi masu sallama suka tafi.
**********************
Tun washe garin ranar da Sumayya tayi yaji shim Muhdeen yayi yaji da kwana gidan,domin a ranar ne Jabeer ya kirashi dadaddare akan akwai emergency yazo yayiwa wani tiyata.Kasancewar office d'in nasa akwai bedroom a ciki da toilet.idan ya gama abunda zaiyi sai ya shige bedroom d'in ya wuce toilet yayai wanka ua saka kaya ya hau gado ya kwanta,duk da ba cikakken barci yakeyi ba yawan tunanin Sumayya kawai yakeyi.
Gashi yanzun gobe Juma'a ne za'a Kai Inteesar gidansa,gaba d'aya ransa a jagule yake ransa ya gama 'baci kuma ya kudiri niyyar cewa Inteesar sai ta d'and'ani kud'arta,musamman da yanzun haushinta ya ninku a zuciyarsa gani yake ita ce sanadiyar rabuwarsa da farin cikin zuciyarsa Sumayya.Hakan yasa ya k'ara d'aukar d'amarar k'untata mata.koda Jabeer ya ce zai sanar abokansu tarewar Inteesar dan a raka ango d'akin Amarya cewa yayi baya so,dole Jabeer ya hak'ura ya kyaleshi.
Gidan Mummy kuwa ana ta shirin taron jama'a a gidan don gobe juma'ar nezasuyi taron walima da k'arfe hud'u a shida,bayan walimar ne za'a Kai amarya gidanta.Bayan ankai Amarya gidanta ne dadaddare za'ayi dinner,wanda dakyar ya yarda cewa zaije dinner d'in dan sam yak'i yarda ya dage ba inda zashi,sai da Jabeer ya sanar da Mummy ne ita kuma ta bashi umarni sannan ya amince don bashida ikon bijirewa zancen uwa.
Inteesar idan Wanda Bai santa sosai ba ya kalleta bazai gane ta yadda tayi kyau ta k'ara haske fatarta sai walk'iya da sheki yake ga wani k'amshi da jikinta ke fitarwa,idan ta shiga d'aki ta fita sai d'akin nan ya kwana ya kwana yana k'amshi,ko fitsari tayi k'amshi yake fita daga k'asanta sakamakon wani shu'umin turaran da Hajiya Bilkisu kesawa k'ark'ashin wata 'yar kujera Mai hudi-hudi ta zaunar da Inteesar akai.masha Allah duk Wanda ya ganta bazaice 'yar Nigeria bace,zaka d'auka wata ba indiya ce.Aunty Abla ce tazo d'aukarta domin kaita ayi mata zanan lalle da gyaran gashi.
Daga alk'amin✍️
Zainab Abdullahi K.N.T
(Maman Ihsan)
Domin k'arin bayani
09065327995
Love u oll😍😘
Comment and shareFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GXLLwE11VEK6KkBh5sqU89
*INTEESAR*
Story& writing by✍️
Zainab Abdullahi
(Maman Ihsan)
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
*GARGA'DI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce,don haka a guji sarrafa mani shi ta kowace siga.
Wannan kagaggen labari ne, banyi tunanin rubutashi dan cinzarafi ga kowa ba, idan suna ko hali yazo d'aya to a gafarceni bada niyyar yin hakan nayi ba.Arashi ne Mai kashe auren wawa.
Page3️⃣5️⃣
Aunty Abla ce ta zo d'aukarta domin kaita ayi mata zanen lalle da gyaran gashi, Mufida ma ta gayyaci k'awayenta da suka gama secondary School tare, Wasila da Saliha suma sunzo ana ta hidimar bikin dasu, Maganar dinner ma Mummy ta ce a barshi kasancewar Muhdeen ya nuna baiso itama Inteesar d'in da aka tuntu'be ta ta ce walima kawai zata yi, kuma dama ba kowa yasan da bikin ba tunda aure ne da aka yi ba tare da shiri ba, ko dangi na nesa ma Gwaggo ta ce suyi zamansu tunda basu dad'e da komawa bikin Muhdeen da Sumayya ba ga yanzun na Muhdeen da Inteesar ya taso ba shiri, hakan yasa ba wani jama'a sosai Muhdeen ma ko abokansa bai sanar dasu zancen auren ba, Jabeer ne ya sanar da su Bilyaminu amma abokansa da ba garin suke ba da na k'asar waje duk basu sani ba.
Dama Muhdeen ya sa Direbansa Ishaq ya samo masa mai aikace-aikacen cikin gida, hakan yasa ya samo masa wata Mai aiki duk da cewar ba wani aiki ne a gidan ba kuma Muhdeen har yanzun bai dawo cikin gidan ba, idan mai aikin tazo da safe Ishaq zai bud'e mata k'ofa ta shiga falo kawai da kitchen sai dinning area take gyarawa duk d'akunan gidan a rufe suke.
Yau Muhdeen ya kira Ishaq a waya ya sanar masa cewa yasa mai aikin nan ta shiga d'ayan part d'innan ta gyara saboda za'a shiga part d'in, Ishaq ya sanar da ita ta shiga ta gyara falo ta goge da bedroom guda hud'u dake part d'in kamar yadda aka umarce ta tayi to hakan kuwa tayi, bayan gamawarta ba jimawa sai ga wad'anda zasu shirya d'akin sunzo, nan suka Fara sassauke kayan suna shiga dasu ciki nan suka fara had'a kayan, Gaskiya Mummy da Dady sunyi bajinta wajen yiwa Inteesar kayan d'aki, d'akuna guda biyu suka shirya mata aka duk wanda ya kalli gadajen duka biyu sai sun burge mutum komai na kayan d'aki da akewa 'ya mace ba wanda Dady baiyiwa Inteesar ba, Mummy ma tayi mata kayan kitchen masu kyau da tsada komai anjera mata su.
Inteesar sai yamma suka dawo daga gidan gyaran jiki idan kuka ganta kamar ku sace ta saboda tsabar kyawu da tayi, ga kanta yasha gyara dama ita akwai tsayin suma har gadon bayanta, ga suman bak'i wulik Mai shek'i da santsai ballantana ya samu gyara sai shek'i yake, Hannayenta da k'afafunta yasha jan lalle da bak'i, a daren ranar ma Inteesar tasha gyara a wajen Hajiya Balki.
Washe gari ya kama ranar juma'a ranar da Inteesar zata tare a gidan mijinta, tun da safe Aunty Abla ta zo d'aukar Inteesar gidan Hajiya Bilkisu, Hajiya Bilkisu ma ta shirya ta bisu akan cewa itama ta kashe aikinta na yau saboda bikin Inteesar don itama Allah ya jarabceta da k'aunar Inteesar sosai don dama ita tana da kwarjinin jama'a sosai duk wanda ya kalleta sai yaji ta shiga ransa.
A motar Aunty Abla suka tafi sai yaba kyawunta Aunty Abla ke yi tana dad'a godewa k'awarta akan k'ok'arin da tayi wajen gyara Inteesar, Hajiya Bilkisu dariya kawai tayi tare da nuna cewa Inteesar 'yace a wajenta kuma ko bayan auren zata cigaba da kula da ita tamkar 'yarta fira suka dinga yi a tsakaninsu ita dai Inteesar tana bayan motar tayi tagumi zullumi da fargabar wani irin miji Abbanta ya aura mata, da kuma irin zaman da zasu yi.
Ba laifi kuwa gidan ya cika da jama'a musamman 'yan unguwar, an girka abinci kala-kala kowa yaci abunda ransa keso ga soyayyun naman kaji da na sa da aka yanka,'yan matan unguwar ma duk Mufida ta gayyace su, koda aka shigo da Inteesar kai tsaye d'akin Mufida ta nufa don dama duka k'awayensu da wad'anda suka gayyata suna nan cikin d'akin, nan dai suka nuna farin ciki da fatan zaman lafiya mai d'orewa, k'arfe hud'u akayi walima inda aka gayyaci manyan malamai suka zo suka yi wa'azi da jan hankali akan zamantakewa aure da haƙƙin miji akan matarsa da haƙƙin mata akan mikinta, da misalin k'arfe shida na yamma aka tashi walimar inda akayi rabon sallaya da hijabai.
Da misalin k'arfe takwas na dare aka d'auki Inteesar aka Fara kaita gidan mijinta, nan aka dinga yaba had'uwar gidan da kuma had'uwar dakinta, dangin Umma ba k'aramin farin ciki suka yi ba ganin yadda iyayen Muhdeen suka narkar da naira wajen yiwa Inteesar kayan d'aki Mama Huraira ma k'anwar Umma taji dad'in ganin yadda gidan 'yar 'yar uwarta, ba yadda Inteesar bata yi da Mufida akan su ta kwana amma sam Mufida ta ce a'a amma zata zo gobe, lokacin da taga jama'a na tafiya kuka sosai tayi dakyar Aunty Abla da Mama Huraira suka lalla'bata ta hak'ura suka tafi.
Gida ya rage ita kad'ai ce a ciki zama tayi tare da tagumi tana tunanin wace irin rayuwa zata yi