Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 287659 words

Chapter 14 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1773

Ads at the middle of Article

su kadai suke rayuwar su a daji,_

Family din danejo basu dayawa, Saboda yawancinsu ba'a wuri ɗaya suke ba, Kowa Ya kama gabansa, Kaɗan ne suka rage, Ita dai takasance marainiyace, Iyayenta sun rasu tun kafin ta mallaki hankalinta, kuma ita kaɗai suka haifa, ta taso A hannun ƙanwar mahaifiyarta wadda suke kira da inna wuro, ƴa'ƴanta huɗu bawuro shine babban ɗanta,Yana da mata Ɗaya Haulatu, ɗansu ɗaya wanda suke kira da cubaɗo, bayan shi sai Adda itace ta biyu, sai gidaɗo sai kuma ƙanwarsu hasiya, Kakanninsu duk sun rasu, Ɗaya kaɗai ya rage masu na 6angaren Mahaifiyarsu, sukaɗai suke rayuwarsu a wuri ɗaya.

Yinin ranar Danejo bata motsa ba, ta kasa ta tsare sai Yarinyar ta farka, saboda ta ƙwallafa rai akanta sosai, tunkafin ma tafarka tasan wacece ita, Allah ya jarabceta da son yarinyar,

Tun tana sa ran zata farka, har dare ya yi bata farka ba, har sun fara fidda rai, Su uku ne acikin bukkar, Danejo da kuma Hasiya, suna ta zaman jiran tafarka har bacci ya yi awon gaba da su.


Tsakar dare lokacin kowa Yayi bacci Cikin ƴar bukkarsa, ta soma mutsu mutsun buɗe idanuwanta, ƙoƙarin motsa Jikinta tayi sai dai ina sam takasa,tamkar an ɗaureta da igiyoyi haka take ji, ga wani irin zafi da take ji ajikinta, sautin muryarta sam baya fita, Can ƙasan maƙo shi take sambatu,
"Daddy mu koma gida, tsoro nake ji,"tun sautin baya fita harya fara fita da ƙarfi, da iya ƙarfinta na ƙarshe Ta yaye bargunan da suka lullu6a mata, buɗe idanuwanta tayi sosai tana kallon Bukkar, Wasu jerin kwaryoyi tagani a jere, da wani akwatin karfe da sauran tarkacensu na fulanin daji, Wurga eyes dinta tayi akan Fitilar kwan dake Ajiye a ƙasa wadda ta haskaka Cikin bukkar, kafin takai idanuwanta kansu Danejo dake ta bacci daga zauna suna gadinta,

Wani irin tsorone Ya ziyarci zuciyarta, hankalinta ya tashi matuƙa, ganin baƙin fuskoki, Ga kuma wani wuri mai kama da A kurkukin kaji, rushewa tayi da matsanacin kuka, a firgice Danejo da hasiya suka farka jin sautin kukan Mutun, Tsareta da ido su ka yi suna kallonta kamar yadda take kallon su, Cikin harshen fulatanci suka soma ƙoƙarin rarrashinta, Ta wawware masu gray eyes ɗinta, jin suna yi mata gwaranci,
Cigaba da kuka tayi tana faɗi"Daddy! wayyo Allah na!! Ina daddyna ya ke!! Su wanene ku! A ina nake ne!!" miƙewa Ta yi da ƙyar saboda ba isasshiyar lafiya gare ta ba, Jikinta sai kerma yake yi, Ga uwar zufa data wanke mata jikin nata, ganin tana ƙokarin neman hanyar fita daga Cikin bukkar yasa suka miƙe da sauri Suka nufe ta zasu ruƙeta, watsawa ta yi da gudu tana bin jikin bukkar a ƙokarinta nata gano hanyar da zata fuce, su kuwa sun dage sai haƙuri suke bata"kiyi hakuri ki zauna baki da lafiya, muma mutane ne kamar ke kada kiji tsoron mu baza mu cutar dake ba" tunda suka soma magana take ta faman zazzare masu idanuwanta, saboda bata fahimtar yaren da su ke yi mata magana da shi, ballantana kuma harta fahimci cewa lallashin da suke Yi mata,

"Wayyo Allah daddyna, Ni ku maida ni wurin daddyna, Inaso nagan shi," sosai take Yi masu kuka, mai tsiwar gaske, gaba daya sautin kukan nata ya karaɗe kunnuwan duk wani mai yin Bacci acikin bukkokin,

Kukanta Ya ishesu, ɗaya bayan ɗaya suka soma fitowa daga cikin bukkokinsu, kowa yana ta faman Yin hamma, A haka suka nufi bukkarsu danejo, inda suke Ji yo sautin kukan nata.

Inna wuro ce ta shigo ciki, tare da su haulatu, gaba daya suka ɗaura idanuwansu Kan ANGEL, dake ta kuka, tambayar su Danejo su ka yi meke faruwa?Suma su ka ce basu sani ba, ta tashi tana ta kuka, kuma su basu san harshen da take yi masu magana da shi ba" adaren ranar babu wanda ya runtsa Cikinsu, taruwa sukayi akanta sunata aikin lallashi, ta burkuce masu sam bata fahimtarsu, kamar yadda suma basu fahimtarta, sunan Daddynta kawai take kira,

Koya rayuwar Angel zata kasance acikin fulanin daji? Yarinyar da ta taso Cikin kulawa da soyayyar mahaifinta, batasan rashi ba, batasan maraici ba, Ta saba da rayuwar gatanci sai abunda takeso daddynta yake yi mata, Yau gata a ƙurmin daji, Cikin fulanin daji mutanan da basu Jin harshen hausa Sai fulatanci, ita kuma bata Jin fulatanci daga hausa sai turanci, Sai kuma larabcin data koya a makarantar islamiyar da take zuwa, Taya zata Iya jure zama dasu? Abincinsu yanayin rayuwarsu sam ta banbanta da ta mutanan dake rayuwa Cikin gari,

Kafin safiya tayi Angel ta galabaita sosai, Idanuwanta sun kunbura saboda rashin bacci da kuma kukan data sha, sun ƙanƙance, jijiyoyin wuyanta duk sun firfito rudu ruɗu jikin fatarta, le6enta ya faffashe hada busasshen jini, ga wani irin zazza6i na tashin hankali daya rufarmata, a ƙarshe yanke jiki tayi ta faɗi asume, Jinya ta koma sabuwa, magunguna suka shiga haɗa mata nagargajiya ƴan dabarunsu da ba'a rasa ba, Hada wasu ganyayyaki suka jiƙa mata acikin gora, suna bata tasha, Allah ya haɗa jininsu da ita, musamman Danejo kullum A tare da ita take kwana, Ba ƙaramin tausayinta suke Ji ba, Saboda ko magana bata Iya furtawa, Jikinta yayi tsauri sosai, Babu sauƙi tamkar zata rasa ranta, ga shi ko a bincinsu bata Iya ci, Furace kaɗai itama ɗin sai sun ɗura mata abaki tukunna take wucewa ta makoshinta daƙyar, angel ta wahala sosai, ta rame ta bushe ta ƙanjame tayi duhu tamkar ba yarinyar nan mai ƙiriniya ba,

Kusan Wata Uku ta yi Acikin wannan mawuyacin halin, kafin Allah ya kawo mata sauƙi, tafara buɗe baki tayi magana, Sai dai subi ta da ido don basu fahimtar me take cewa, kullum saita yi masu sambatu akan su nemo mata daddynta, daga baya da ta fahimci basu gane yaren da take yi masu, Saita Zuƙunna ta sanya yatsanta a kasar wurin da ruwa ya jiƙa,ta soma Zana fuskar mutun Asaman ƙasar, data kammala zanen ta kirasu tana nuna masu zanen, Suka zuba ido suna kallon jagwalgwalon zanan fuskar da ta zana, Kallon juna su ka yi Alamar basu fahimta ba, fashewa tayi da matsanancin ku ka, Ta watsa da gudu Tabar wurin bukkokinsu, Suma suka bi bayanta a guje, suna ƙokarin kamota gudun kada wata muguwar dabbar daji ta halakar da ita,
Cikin ƙurmin dajin ta nutsa, har tazo inda wannan ruwan Yake inda Taj ya jefa ta ciki, Juyo wa Tayi tare da kallonsu, sai faman haki suke yi sun sha uban gudu, da hannu ta dinga nuna masu cikin ruwan Saboda ta gane cewa a nan ne inda daddyn ta Yazo da ita Ya wurgata ciki,

Duk yadda taso ta fahimtar dasu, Sam sun gaza fahimta, dunƙule hannayenta tayi tare da murzasu, tana kwatanta masu a cikin mota suka zo dajin, Nan ma still basu gane me take nufi ba, Zuƙunnawa tayi agaban ruwan, ta rushe da matsanancin kuka, duk jikinsu yayi sanyi,

Babu yadda angel ta iya adole ta haƙura taci gaba da rayuwa acikin fulanin daji, tun bata saba ba da su ba, har ta fara sakin jiki da su, Bata da abincin daya wuce fura da nono, da kuma Gasassar masara, Sai kuma nama idan sunyi farauta, shigarta ta koma ta fulanin daji, Danejo ce tayi mata kyautar kayanta, Wanda tun tana yarinya kayan suke ajiye cikin akwatin ƙarfenta, Zuwan Angel Cikin rayuwarsu Ta fiddo da kayan, Ta bata su ta sanya,

Duk rana ta Allah sai angel da danejo sunje Bakin ruwan nan, Kullum ne wani lokacin har dare suke kaiwa abakin ruwan, atare suke fita kiwon shanu, hatta tatsar nono sai da danejo ta koya mata, da wasu abubuwan nasu na fulanin dajin, baiwar Allah ba yadda za ta yi don dole take rayuwa a cikinsu, Allah ne kaɗai yasan halin da Zuciyarta take aciki, a kullum idan suka kwanta suna Bacci, tare da su danejo da hasiya, bata iya runtsawa, Zama take yi tsakar dare, tadinga kukan zuci tana roƙon Allah yasa daddynta yana A raye, ta karaya sosai, wani sashe na zuciyarta yana raya mata cewar Waɗannan mutanan da suka Biyo su suna harbin motarsu sun kashe mata daddynta, amma kuma har cikin ranta tana jin cewa Yana A raye, taya zata tabbar da hakan? Ita dai bata ga gawar mahaifinta ba, balle tashai da yabar duniya, A ƙalla Angel tayi shekara Biyu A hannun fulanin dajin nan, A lokacin Tafara Jin fulatanci sama sama saboda xama da tayi da su,
duk da sabon da tayi da su hakan bai sa ta fasa ƙudirinta na guduwa daga Cikin dajin ba, duk don saboda taje neman Mahaifinta, abunka ga Yaro ga kuruciya, zuciyarta saita dinga raya mata cewa ta gudu taje gidan su, zata samu mahaifinta agida.

A ranar data shirya guduwa daga Cikin dajin, Sai da tabari kowa Ya yi bacci, batare da jin tsoro ba ta fito daga Cikin bukkar, Ko'ina duhu kasancewar darene sosai, Cikin sanɗa take tafiya Tana nufar cikin dajin, duk in taji kukan shanayensu saita firgita, gani take kamar zasu farka daga bacci ne su hana ta guduwa

Ganin tayi nisa daga inda bukkokinsu suke, ta soma tunanin wace hanya zata bi don ta fita daga cikin dajin, ga duhu ko'ina, sai ɗan hasken farin watan da ba'a rasa ba, tana cikin wannan tunanin ta jiyo muryar mutun a bayanta, A firgice ta juya don taga wanene, Hasken fitila tagani amma ba ta iya tantance wanda ya biyota ba, duk da taso ta ɗauki murya,

Tattare zanin jikinta tayi na kayan fulanin da suka bata sune sanye ajikinta, ta watsa aguje cikin dajin tamkar zata tashi sama, tana gudu tana tuntu6e wani lokacin har faɗuwa kasa take yi a haka za ta daure ta miƙe taciga ba da gudu tana waiwayan mutumin daya biyo ta, ganin shi ma yana gudu, nan fa ta ƙara gudun nata, tsawon lokaci suna wannan ƴar guje-gujen cikin dajin ita da mutumin daya biyo ta har Allah Ya kawo ta bakin titi a galabaice ta haye saman titin, wani irin jirine ya soma ɗibar ta. Ta fara tangal tangal za ta faɗi ƙasa, a haka ta jure taciga ba da gudu, ba zato ba tsammani sai ga wata zungureriyar mota baka ta yi parking a inda take a tsaye, A slow murfin motar ya zuge,

Zuro Hannu aka yi daga cikin motar aka ɗauke ta, murfin motar ya koma ya zuge da kanshi, da gudu motar ta miƙi titin.

A daidai wannan lokacin Danejo ta faɗo saman titin a galabaice hannunta riƙe da ƴar filita. Ashe ita ce ta biyo Angel, don ta ga lokacin da za ta gudu daga Cikin bukkarsu.

Waro ido waje ta yi ganin dankareriyar motar da ta ɗauki Angel, tunda take a rayuwarta wannan ne karo na farko da ta fara yin tozali Mota, Tsoro duk ya cika ta, hankalinta ya yi matuƙar tashi, ganin an raba ta da Angel. A gefen titin ta tsugunna tana kuka tamkar ranta zai fita. Wannan shi ne silar rabuwar Angel da Fulanin Daji.
A nan gefen titin Danejo ta yanke jiki ta faɗi a sume, a washe garin ranar ƴan uwanta suka farka daga barci, ba su ga Angel da Danejo ba, hankalinsu ya tashi gabaɗaya suka bazama cikin dajin neman su. Har Allah Ya sa Su Bawuro suka tarar da ita a gefen titi ita kadai a kwance ba numfashi, lamarin ya yi matuƙar girgiza su, tunda suke da Danejo ba ta ta6a yin nisan kiwo irin na yau ba, sun yi mamakin ganin ta ita kaɗai ba tare da Angel ba.


Bayan komawarsu cikin rigarsu, Suka yayyafa ma danejo ruwa ta farfaɗo, fashewa ta yi da matsanancin kuka tana faɗa masu yadda suka rabu da Angel. Duk jikinsu ya yi mugun sanyi, kowa bai ji daɗin lamarin ba, sai dai ba su da yadda za su yi. Da ma tsintacciya ce duk da sun yi sabo da ita, zuwan Angel cikinsu ba ƙaramin farinciki ta samar masu ba. Sun ji takaici da baƙin cikin ɗauke tan da aka yi, to ya za su yi? Allah Ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan.

Da daɗi da ba daɗi haka Danejo ta ci gaba da rayuwa cikin ƙunci da takaicin rashin Angel, ta rame ta ƙanjame tamkar ba Bafullatanar nan ba mai yawan fara'a mai son yin rawa, yanzu ta koma salihar ƙarfi da yaji. Kullum cikin yin zazza6i take, kuma kullum tana akan hanyar zuwa bakin ruwan nan inda suke yawan zuwa ita da Angel su zauna. Kafin tafiyar Angel ta ba su labarin mahaifinta daya gudo da ita cikin daji, a lokacin ta fara jin Harshensu na Fulatanci, ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar da su.

*ANEELERH*


Kwance take saman haɗaɗɗen gadonta na gidan su, A gefenta ƙaramin yaronta ne wanda bai wuci shekara ɗaya da ƴan watanni, Jikin shi na a sanye da overall pink colour, Kyakkyawan yaro rainon madara, fari tass kamannin shi sak na mahaifiyar shi, tamkar ta yi kakin shi, kan shi a cike yake da kwantacciyar suma mai laushin gaske, mommyn ta shi dake kwance gefen shi tana ta sharar bacci Rigar bacci ce a jikinta launin sky blue,

Wata irin zufa ce ta soma wanke mata fuskarta, ta ko'ina zufar take tsastsafo mata, rurruƙe bedsheet ɗin tayi da hannayenta da ke ta kerma, sambatu ta soma yi tana ambaton sunan ANGEL, still idanuwanta suna a rufe da alama mafarki take yi, Cikin shesshekar kuka take faɗin"Angel meyasa nake ganin cikin mawuyacin hali? Waya ta6amun ke? Angel kiyi magana meyasa ki ke kuka? Dan Allah ki faɗamun angel," Ciccije lips ɗinta take yi sosai take ƙara sautin kukan nata,
A dai dai lokacin mami ta fito daga ɗakinsu, itama kayan baccin ne a jikinta doguwar riga, sai hamma take yi da alama daga bacci ta farka, ɗakin Aneelerh ta nufa tunkafin ta shiga ta soma jiyo sautin muryarta, ta cikin ɗakin tana kuka,
Da sauri mami ta faɗa cikin ɗakin babu wadataccen haske sun kashe Kwan ɗakin kafin su kwanta, bedside lamp ce kaɗai take a kunne ta ɗan haskaka ɗakin,
Ƙarasawa tayi daga gefen gadonta, takai hannu tana ɗan bubbuga shoulder ɗinta"Aneelerh! Aneelerh! Lafiyar ki kuwa? Kike ta ku ka"? Muryar mami ce ta farkar da ita, lokaci ɗaya ta zabura zata sauko daga saman gadon, damƙo damtsen hannunta mami tayi'ke lafiya? Bakya ji ina magana"?
"Mami ki barni in tafi, tana buƙatar taimako na," la66anta na kerma tayi maganar,
Fuskar mami da alamun ruɗi tace"wai wacece kike magana akai"? Juyowa tayi suna kallon juna, idanuwanta sunyi jawur tace"ANGEL "
Sakin hannunta mami ta yi ta dafa kafaɗunta, cikin natsuwa ta soma magana" ki kwantar da hankalin ki, ki faɗamun meya faru da angel, kinyi mafarki ne akanta"?
Jinjina kai tayi cikin shessheƙar kuka tace"Mommy, I had a really scary nightmare about angel, tana a cikin mawuyacin hali, yanayin da nake ganin angel abun ya ta6a zuciyata......" takai ƙarshen maganar hawaye na bin fuskarta
Shiru mami ta yi idonta akan fuskar aneelerh, Kafin tace"addu'a yakamata ki yi,"
Cikin disasshiyar miryarta, ta ambaci "أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ وَمِنْ شَرِّ هَذِهِ الرُّؤْيَا"
Kusa sau uku tana ambaton addu'ar,
"Aneelerh mafarki ba gaskiya bane, Shaiɗan ne kawai yake son rikitar dake" girgixa kai aneelerh tayi"mami wannan mafarkin ya wuce a ce shaiɗan ne, ba yau ne rana ta farko da nafara yin shi ba mami, kuma a duk lokacin da zanyi shi, angel nake gani ita kaɗai tana kuka jikinta sanye da yagaggun kaya kamar Almajira,"
"A kowani lokaci, ki ka yi mummunan mafarki akan angel, you should pray for her, alama ce da ke nuna cewa tana buƙatar addu'ar ki, duk da ki nayi saiki ninka akan wadda kike yi masu, muma kuma in sha Allah zamu dage" miryar abie ce, sam basu ji alamar shigowar shi ba, a tare suka Kai idanuwansu kan shi,
A tsaye yake bakin ƙopar ɗakin jallabiya ce a jikin shi, yayi shirin zuwa masallacin domin yin sallar asubahi da ake ta kira,
Tafiya yaci gaba da yi cikin ɗakin yana nufar su,
"Wipe ur tears aneelerh, bana so na sake ganin hawayen ki, " cikin sanyin murya ta amsa mashi da "toh"
"That's good, Jiya munyi waya da uncle abdallah" ya dakata da maganar, a ƙagare suke kallon shi, sun ƙosa su ji mai zaice,
"Yayi mun magana akan BABY JUNAID, nasan aneelerh bazata ji daɗin maganar ba, shiyasa tun jiya ban sanar maki ba," tunkafin ma yakai ƙarshen maganar aneelerh ta ɗaure fuskarta walwalarta gaba ɗaya ta ɗauke,
Ita kanta mami yanayinta ya canza, don tunkafin ma ya ƙarasa sunsan inda zancen nashi ya dosa,
"Suna so A basu shi, ya koma hannun su da zama, da zarar kin yaye shi,.....' girgiza kai aneelerh ta shiga yi tana faɗin"Haba abie, idan aka raba ni da shi ya ake so inyi da raina? Yaron nan fa shi nake gani inji daɗi araina, ina kallon shi amatsayin kyautar Allah, inaji araina Allah yabani shi ne saboda rashin da na....." ƙasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da ya ciyota, da sauri ta kifa kanta saman pillow,
Dariya sosai abie ya yi, ganin yadda ta harzuƙa jin za'a rabata da gudan jininta,
Kallon juna su kayi shi da mami, "meyasa? Kana ganin halin da take ciki, kuma ka ke son ƙara tayar mata da hankali, dagaske ka ke ko wasa? Nasan ka da son zolaya"
Bai bata amsa ba, Ya juya ya nufi ƙopar fita yana faɗin"Idan na dawo daga masallaci zamu yi magana" daga haka ya fuce daga cikin ɗakin,
Shafa bayan aneeleeh mami tayi"ke ki kwantar da hankalin ki, ae wlh ba wanda ya isa ya raba ki da ɗanki, Sai Allah nasan aikin hajiya adama ne, ita zata tunzura shi akan su ɗauko yaro, in banda ma abunsu ae yaron bai kai shekarun da zasu ɗauke shi ba, koda kuwa an yaye shi, nifa ko ya cika shekarun da

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads