Header Ads
Showing 126001 words to 129000 words out of 287659 words

Chapter 43 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1782

Ads at the middle of Article

tsohuwa dake A tsakiyar ɗakinsu Hannunta ruƙe da sanda haris ne agabanta Ya ruƙe qugu, Yana mata maganaTamkar zai rufe ta bugu,

"Saboda me zasu yi wurgi da su? Saboda rashin tausayi da mugunta suka jefar dasu, kamar wasu barguna, gasu nan kina gani da idanuwanki ko tashi sun gaza yi saboda raɗaɗin da jikinsu yake Yi musu, wai mu me aka maida mu ne eye? nifa nafara kokwanto akan kowa ma dake atare damu, " Yana magana yana watsa hannayenshi kamar zai buge tsohuwa dama fa shi haris akwai zuciya, Idan ya fusata Ya isa masifa,

Tun da haris Ya soma magana, Tsohuwa ta zazzaro kwarkwararrun idanuwanta waje, Kwayar idon kamar zasu rubzo ƙasa saboda tsabar zaro su da ta yi, Bakomai bane yasa tayin hakan face Mamaki da al'ajabin daya kamata, karo nafarko kenan da aka fara samun wani acikin su Ya ɗaga mata murya, haƙika tayi matuƙar girgixa, sai da yakai karshen maganarshi Ya juya mata ƙeya yana ƙunƙuni,

Ruƙe ha6arta tayi idonta akan keyarshi, Muryarta Na rawa tace"HARISU!! yau ni kake gaya ma magana babu tausasa harshe? A ina ka samu wannan ƙwarin gwiwar? Kamanta matsayina ne awurinku? Wato ina can ina tufka ana nan anayi mini warwara," a wani sukwane Haris Ya juyo Yabi ta da wani irin kallo Yace"Indai akan ƴan uwana ne fiye da haka ma zan Iya fada maki, Wannan matsayin da kike dashi awurin mu kina dab da rasa shi, Saboda Na fara zargin ba ƙaunar mu kike Yi ba," kasa karasa maganar haris yayi idanuwanshi cike tab da kwalla, tsohuwa sai faman gyaɗa kai take Yi kamar wata ƙadangaruwa,

Ganin tana ƙoƙarin juyawa ta koma Cikin dakinta Ne yasa Danish Yin saurin dakatar da ita, ta hanyar yi mata magana" meyasa a koda yaushe muka sanar dake agame da rashin lafiyar ɗaya daga Cikin mu baki nuna damuwarki? jin muryar danish Yasa tayi saurin Juyowa tare da kallonshi, A tsanake Yake tafiya yana tunkarar inda take atsaye, Duk wannan abun dake faru Su azeeza sun natsu suna sauraronsu, a lokacin sun dakata da yin kukan sai dai har yanzu basu iya miƙewa daga kwacen da suke a kasa ba,

A gefen haris Danish Ya tsaya tare da ɗaura hannunshi na hagu saman kafadar haris, still idanuwanshi akan tsohuwa Yana jiran Jin amsar da zata basu, Sai faman zare ƙwalaƙwalan idanuwanta take yi, Da alama zuciyarta ta shiga ruɗani,

Bata gama kiɗima ba, zazzaƙar muryar angel ta ratsa kunnuwanta da cewa"Ki basu amsar tambayarsu mana? Daga anyi magana kaɗan sai ki dogara sanda Ki koma ɗaki, saboda rashin gaskiya, Meyasa kike 6oye mana gaskiya ne? Tun rana ta farko dana tsinci kaina acikin kurkukun nan raina ya bani cewa ba abun arziƙi ake aikatawa acikin shi ba, saboda bai kwanta mini araina ba, Kina yawan yi mana ƙarya, wanda bani kaɗai ba hatta su kansu yanzu sun fara kokwanto akanki, kince mana ana kaisu treatment room domin duba lafiyarsu, to meyasa ake dawo mana dasu a haukace? Maimakon Muga sauƙi ajikinsu saima dai muka ga tashin hankalin akan fuskokinsu, Da jikinsu, mutumin dake yin jinin al'ada meya haɗa shi da ƙaiƙayin gaba? Da kuma gwamewar ƙafafuwa? Uwa uba da fashewar le6e, ga rama, Wannan wani irin treatment ne tsohuwa"! Tayi tambayar tana kallonta, Tsohuwa dai tarasa bakin magana, sai faman gyaɗa kanta take yi,
Angel taci gaba da cewa"Allah dai ba Azzalumin bawansa bane, idan ma cutar mu ku keyi, To ku sani Allah Yana kallonku, Kuma akwai ranar hisabi, ranar da duk wani abu da kuke taƙama dashi aduniyar nan bazai ta6a taimakonku ba......." Angel bata kai ƙarshen maganarta ba, Tsohuwa ta buga sandar hannunta, Cikin nuna 6acin ranta, Da sauri danish ya dafe kanshi da hanneyenshi,

Ranta amatuƙar 6ace tace"Kin manta abunda na faɗa maki? Nifa bakowa bace agidan kurkukun ƙaddarar nan? Don me zaki titsaye ni kina gaya mini magana yadda kika dama? Meyasa bazaki tuhumi Iyayenku da suka sadaukar daku ba sai ni? Da bani da wata alaƙa ta jini da ku? Ga dukkan alamu baki Ji gargaɗin da nayi maki ba, Ina matuƙar Tausayawa rayuwarku! Domin kuwa duk ranar da kika kuskura Kika bari Ƴan uwanki prisoners suka gasgata maganarki akan tawa, to daga wannan ranar ba zaku ƙara Yin tozali da ni ba, Zan barki dasu ne, Kiga idan zaki iya taimakon rayuwarsu," Tsohuwa Nakai karshen maganarta, Ta Juya fuu kamar zata tashi sama Ta nufi dakinta, Ta shige taja kopa ta rufe,

Sai lokacin danish Ya zame hannayenshi daga saman kanshi, Wato a lokacin da tsohuwa ta buga sandar hannunta, basu ƙara fahimtar me take cewa ba, tamkar ta wanke masu tunaninsu na tuhumar da su ke yi mata, ita kanta angel ta lura da hakan, Sai dai ko kaɗan hankalinta bai tashi ba, Domin kuwa tasan dole su cigaba da tuhumarta, da zarar an dawo musu da ƴan uwansu da aka ɗauka,

Kallon juna su kayi ita da danish, Kafin ta ɗauke idonta daga kanshi ta mayar dasu kansu Batool, tafiya tayi zuwa inda take a kwance, Ta zuƙunna tare da kai hannayenta saman kafaɗun batool ta ɗago da ita tare da kwantar da kanta saman kafaɗunta,

"Sister, yanzu Haka zamu zuba ido muna ji muna gani, Ana raba mu da ƴan uwanmu"? Cikin shessheƙar kuka batool ta yi maganar, kafin angel ta bata amsar tambayarta, Naufal ya rigata cewa"Haƙuri zamuyi, Giants sunfi ƙarfin mu, Ni dai na roƙe ku nan gaba kada ku ƙara gigin shiga huruminsu, Ina gargaɗinku, Idan ku ka yi haƙuri za'a dawo mana da su ne, kamar yarda aka dawo mana dasu Parveena,

Mubeen yace"Nima abunda nake so naja musu kunne akai kenan, Mutanan nan ƙarfi ne da su, They are extremely dangerous! Da ace tun farko baku Yi yunƙurin tunkararsu ba da duk hakan bata faru ba, kun riga da kunsan halinsu, Basa ji basa gani, duk wani koke koken da za ku yi musu abanza, ba saurarar ku zasu Yi ba"

Danish yace"pls let it be past, tunda sun riga sun tafi dasu, Koke koken Ya tsaya iya haka, "

Jinjina kai Angel ta yi tare da binsu Azeeza da kallo tace"Ku daure ku tashi, ku je toilet ku wanke fuskokin ku," amsa mata Su ka yi da toh, daƙyar suka iya miƙewa tsaye a daddafe suka Nufi toilet,

"Batool kema kije Ki wanke fuskarki, koma Kiyi wanka" amsa mata tayi da toh, Ta ɗago da kanta daga saman kafaɗar angel, Hannunta adafe da sumar kanta, ta miƙe ta wuce cikin toilet,

Ba Iya wanke fuska Su kayi ba, Hada wanka su Kayi, Time da suka fito, mazan gaba ɗaya sun koma saman gadajensu, Angel ma tana zaune daga gefen gadonta, Kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarshi,

Lokacin da giants suka zo kawo musu abinci, Fushi suka Yi, suka ƙi zuwa su Ci, naufal yace"da rabon muyi ma kanmu asara, domin kuwa su basu san bihim ba, ko ajikinsu, Mu zamu Ji jiki," wannan maganar da naufal yayi ce tasa parveen ta sauko daga saman gadonta, Ta nufi saman dining carpet ta samu wuri ta zauna, Ɗaya bayan ɗaya suma sauran suka sauko daga saman beds ɗinsu, Suka Nufi Carpet ɗin suka zazzauna,

Lafiyayyan abinci aka kawo musu, ba don suna jin daɗinshi ba suke Cin shi, Kamar waɗanda aka Yi ma dole, In ka cire parveen dake ta zuba loma, dama ita bata wasa da abinci,

Abinci take Ci amma hankalinta na akan giants dake a tsaye sun ƙame, Harara ta dinga jefa musu tamkar ƙwayar idonta zata faɗo kasa, ita kaɗai take haukanta domin kuwa babu tabbacin ko suna kallonta, Bayan sun kammala Cin abincin, Sauran daya rage Batool ta 6oye musu shi acikin kwandonsu, saboda su samu wanda zasu Ci da anjima,

Bayan tafiyar giants, Safa da marwa suka shiga Yi acikin ɗakin duk babu daɗi saboda rashin ƴan uwansu, an rairaye su yanzu sun koma su goma sha ɗaya, Babu mutun Huɗu acikinsu, dole suyi maraicin rashinsu atare dasu, ga zullumin da suke Yi da fargabar ko awani hali suke Ciki?

Idan suka gaji da zagaye ɗakin sai su koma saman gadajensu su zauna, a haka har dare ya rutsa dasu, Ɗakin Ya yi duhu, Rubina ce ta kunna musu fitilun Ɗakinsu Haske Ya gauraye ko'ina, Kowa Ya kishingiɗa saman gadonshi,

Ta yi tsammanin sunyi bacci Jin ɗakin Yayi tsit, Juyawa tayi tare da fuskantar gadon danish, idonshi biyu Ya kwantar da kanshi saman pillow,

"Meya hana ka bacci"? Amsa ya bata da cewa"ke zan tambaya, me kike Yi har yanzu baki runtsa ba"? Ta6e baki ta ɗanyi"Damuwace ta hana ni bacci, ina jin duk babu daɗi zuciyata"

Shiru baice mata komai ba, sai dai kallonta da yake yi, kamar yadda itama take kallonshi, Gani yayi ta miƙe ta sauko daga saman gadonta, a bakin gadonshi ta zuƙunna tare da ɗaura hannayenta saman mattress ɗinshi

Da ɗan mamaki yace"lafiya"? Murmushi ta ɗansaki kafin tace"Bakomai kawai ina so Muyi fira ne," mayar mata da martanin murmushin yayi, har dimples ɗin shi ya lotsa,

"Ai ni ban Iya fira ba, in fact ko surutu ban iya ba, sai in ta kama dole," tace" toh ka ƙaddara ta kama dolen ne, tambaya ce nake so In yi maka hope zaka amsa mini" ɗaga mata gira yayi tare da cewa" Am all ears"

Kame kame ta shiga Yi, abun ma sai yaso ya ba shi dariya, hannun shi yakai saman sumar kanta ya ruƙo gashinta tare da cewa"Faɗa mini mana, indai nasan amsa zan baki," tace"Dama nayi mafarki ne, kana da wuƙa, shin dagaske ne"? Da budar bakinshi sai ce mata yayi"you're trying to be smart, tell me the truth waya faɗa maki cewa ina da wuƙa? Nasan ba mafarki ki kayi ba,"

Hararar shi Tayi jin ya ganota, taso tayi mishi wayau,

"Na ta6a tambayar batool, cewa Inaso zanyi amfani da wuƙa, shine take faɗa mini cewa Akwai wadda tsohuwa ta baka lokacin da kace mata kana so ka rage yawan sumar kanka," Wani kallo taga yana binta dashi, Can kuma yace"me zakiyi da ita"? Dariya tayi tare da cewa"bafa kai zan kashe ba, Nasan abunda kake tunani kenan, ni kawai inaso In rage sumar kaina ne, bama ni kadai ba hada batool itama Gashin kanta yayi yawa yana takura mana" tayi maganar tana yamutsa fuska,

Ta6e mata baki yayi"Nima namanta inda na ajiye ta, ko na mayar mata da ita ko ban mayar mata ba, namanta, "

A ƙagare tace"pls ka daure ka tuna, Zata yi mana amfani,"

"Angel idan Kina son In rage maki gashin kanki ne, Ba buƙatar Yin amfani da knife, i can use my nails to cut it for u" zaro ido ta ɗanyi da mamaki tace"taya zaka Iya amfani da akaifa wurin rage yawan gashin kaina, baka ga yawanshi ba ne"

"Idan kin bani dama zan Jaraba" girgiza mashi kai tayi"a'a, Ni dai nafi so Inyi amfani da wuƙar, Idan Allah yasa ka tuna inda ka ajiyeta sai ka ɗauko mini" ta faɗi hakanne saboda ba gashin take so ta rage ba, Wuƙar take buƙata saboda tsaro,

"Its Okey, Kije ki kwanta, duk time dana tuna i will let u know" ya karasa maganar tashi tare da jan bargo ya lullu6e jikinshi har zuwa kanshi, Miƙewa Ta yi tare da juya ta koma saman gadonta ta kwanta, A daren ranar saida ta roƙi Allah Akan Yasa itama ta fara Menstruation kodan saboda giants su ɗauketa sukaita ɗakin nan taga uban me suke aikatawa, Idan Allah yasa Hankalinta bai gushe ba kenan,

Wasa wasa Yau har tsawon One week kenan ba'a dawo dasu Hannah ba, Tun suna sanya damuwa aransu har suka haƙura suna zaman jiran tammani, Tun daga ranar da aka ɗaukesu Kullum sai ta roƙi Allah tsakar dare Akan Ya karesu aduk inda suke, Bayan haka kuma Tana yawan yin addu'ar akan Allah yasa ta fara jinin itama, duk don saboda da taga me ake yi musu,

Yanzu ta kaiga ko tsohuwa basu tambaya dangane da ƴan uwansu, saboda sun fahimci cewa ita ɗin bata da banbanci da totan masara awurinsu, bi ma'ana bata da amfani duk wani magiyar da zasu Yi mata bazata iya Sanyawa adawo masu da ƴan uwansu ba, sai da ta gaya musu ƙarairakinta,

Yau tsawon 3 weeks kenan Suna ta baza ido suga an dawo musu Da ƴan uwansu, Sai acikin satin karshe na watan da suka shiga, Aranar da daddare suna zaune saman carpet Suna fira sun kunna fitilun ɗakinsu, Ba zato ba tsammani sai ga giants Huɗu sun shigo cikin ɗakin nasu Kafaɗunsu Ɗauke dasu Hannah, A wani irin zabure suka miƙe suna kallonsu, wuce wa cikin ɗakin giants su ka yi adai dai bakin gadajensu hannah masu ɗauke da numbobinsu suka kwantar da kowannansu, Atare suka juya suka fuce daga cikin ɗakin,

Azeeza sai tsalleta take Yi tana murna an dawo musu da ƴan uwansu, Su batool kuwa Kallon Kallon suka shiga Yi atsakaninsu, sun rasa gane farin Ciki zasu Yi ko baƙin Ciki? Ga shi dai an dawo musu da ƴan uwansu da suka daɗe suna jimamin rashinsu, Sai dai ga dukkan alamu Basu acikin hayyacinshi, Har ƙwarama lokacin da aka dawo dasu parveen sunyi magana, Amma waɗannan bayin Allahn, Idanuwansu ne kaɗai suke motsi, Numfashin su da hucin zafi yake fita, ƙafafuwansu duk sun tale, Wani abun tashin hankalin ma, Hada Yakushin akaifa asaman wuyansu, fatar wurin tayi jawur, jini ya kwanta, La66ansu sun faffashe, Hankalinsu danish ba ƙaramin tashi yayi ba, Matan kuwa Sun sha kuka kamar ransu zai fita, Angel tace Yanzu babu buƙatar saita yi musu bayani game da cewar cutar dasu ake yi yau dai gashi nan zahiri idanuwansu sun gane masu, Sahun yakushin akaifar dake asaman wuyansu, Haƙiƙa sun yi matuƙar girgiza, hatta mazan saida suka zubar musu da hawaye saboda tsabar tausayinsu daya kama su, daren ranar basu Iya runtsawa ba, A gefen gadajensu Hanna suka zaune suna Jimami, har garin Allah Ya waye, Koda suka je bakin ƙopar ɗakin tsohuwa suka kwankwasa mata, Munafukar bata fito ba, Hakan ya ƙara tabbatar musu da cewa Bata da gaskiya,

Haƙiƙa sunsha wahala wurin Yin jinyarsu Hannah, kamar bazasu Rayu ba, jikinsu yayi tsauri sosai, babu sauƙi saima abunda ya qara gaba, sai da takai ga Komai daga kwance suke yin shi, fitsari kashi, duka dai, a ƙalla sun ɗauki tsawon one month suna yin jinyarsu kafin Allah yasa suka samu sauƙi Jikinsu ya warware, Suka koma kamar yarda suke da, Sai dai babu wani walwala atattare dasu, Suna yawan firgita, Ko kiran sunansu Kayi sai kaga sun ɗan zabura, Idan suna bacci kuma Sun dinga sambatu suna koke koke, Ahaka ahaka dai da taimakon Allah angel Tana yi musu addu'a duk rana ta Allah, Sai gashi sun wartsake, Sun dawo normal, Bayan sunji sauƙi, Sai ga tsohuwa ta shigo ɗakinsu, Wani irin mugun kallo da suka dinga jefa mata, ba arziƙi taja sandarta ta koma Cikin ɗakinta, Angel taso ace su hanna sun Iya tuna abunda ya faru dasu amma sun kasa, kwata kwata basu Iya tuna komai, Da ace sun tuna koda kaɗan ne to kuwa tabbas sauran ƴan uwan nasu zasu Ƙara gasgata maganarta, duk da ayanzun ma ta fara cin nasara saboda kokwanton su Ya ninku akan gidan kurkukun, Sun sha jinin jikinsu, Sun fara tsorata da lamarin, Haris har alƙawari ya ɗauka akan bazai ƙara bari giants su ta6a wani acikin su ba, Sai dai in bayan babu ranshi, danish dai bamu san matsayarshi ba, Shi dai baice komai ba, Iya nuna 6acin ranshi akan fuskarshi ne, Amma su naufal mubeen da javed duk sun ɗauki wannan alƙawarin na hana atafi da ƴan uwansu idan basu da lafiya! Kallonsu kawai angel take Yi domin kuwa tasan babu abunda zasu Iya yi, ba wani ƙarfi gare su ba, balle suce zasu Iya ja da giants, Mutanan da take tunanin Ba cikakkun mutane bane, Ƙarfinsu bana jinsin bil'adama bane,

Bayan komai Ya lafa tsawon Watanni uku wani iko na Allah, cikin matan ba wanda ya ƙara Yin Menstruation, kamar an ɗauke musu da jinin, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma angel ba, Yanzu hakalinsu ya ɗan kwanta,

Ganin sun samu natsuwa yasa Ta fara jan hankalinsu zuwa ga addinin musulunci, Idan dare Yayi bata barinsu Yin bacci, Tarihin annabawa take basu tun daga kan tarihin Annabi Muhammad (SAW) Cikin hikma take Basu tarihin, Kuma ga dukkan alamu ba ƙaramin daɗin shi suke Ji ba, domin kuwa idan ta fara basu tarihin, Ko fitsari mutun ke ji sai kaji yace a jira ya dawo sai acigaba, idan kuwa tace ta gaji abari gobe zata ƙarasa musu kamar su yi mata hauka, Taci wahala sosai Wurin janyo hankalinsu duk da bata ci nasara ba saboda duhun jahilcin dake akansu, Suna Yi mata tambayoyin ƙural da suka fi ƙarfinta musamman haris, Da yace idan har akwai Allah wanda ya halicce su to meyasa bai ta6a zuwa ya kawo musu ziyara ba? Ire iren irin waɗannan tambayoyin sune kesa tana karaya wani lokacin, Ita dai tayi iyakar bakin ƙoƙarinta wurin sanar dasu gaskiya, Sauran kuma tabar ma Allah domin kuwa shi kaɗai ne zai basu ikon musulunta idan yaso, mutun huɗu ne acikinsu ta lura da suna matuƙar son Addinin, Batool, Azeeza da Javed, sai kuma parveen, sauran kuwa kokwanto ne Ya hana su yarda da ita saboda wasu tambayoyin su da ta gaza amsa musu, shi danish bama tasan a wata matsaya yake ba, Yana dai son tarihin annabawan da take basu, Sai dai Babu alamar yana da niyar kar6ar addinin nata, mutun huɗun nan da suka nuna suna da interest sune suka fara kar6ar addinin musulunci acikinsu, Ta biya musu kalmar shahada, Kusan Yini guda suka ɗauka tana ta fama dasu akan su maimaita sun kasa furta ta, Sai cikin dare Wani iko na Allah tana sake biya musu sai gashi sun maimaita lafiya lou batare da inda inda ba, Tayi farin Ciki sosai kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha, Duk da farin Cikin nata ragagge ne tun da sauran basu kar6a ba, Tafi damuwa akan danish saboda tana ji aranta idan har ya kar6i addinin zai taimaka ma sauran ƴan uwan nashi saboda suna jin maganarshi sosai, duk da

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads