Showing 186001 words to 189000 words out of 287659 words
Chapter 63 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
yake furta su, da alama abun yana hurting ɗinsa.
"Ƙaurace min bashi bane mafita, saboda muna son junanmu, zamu cutar da kanmu ne, gaba bata da amfani, amma in mu ka yi haƙuri da juna, wata rana xamu cimma nasara,"
tana ji aranta cewa waɗannan kalaman saboda ita yake furta su,
Bai ƙara cewa komai ba, tun da yakai ƙarshen maganarshi, Jiki na rawa azeeza da parveen suka nufe shi, atare suka faɗa jikinshi, suna kuka, Hannayenshi biyu ya sanya wurin rungumesu, Jiki asanyaye Deeja da su hanna suka matsa kusa dashi, Suma suka kwanta bayan Su parveen dake rungume ajikinshi, Tsabar farin Ciki ne yasa su haris suka ɗaga hannayensu suna tafa mashi, Hada su naufal da javed and mubeen, atare ƴan matan suka haɗa baki suna faɗin"We luv u so much our elder bro Danish, muna matuƙar ƙaunarka, munsan cewa ba za ka ta6a bari a cutar damu ba, da son ranka, sai don ba yadda xaka yi ne, mu ma mun gane kuskuren mu naƙin fahimtarka......" Sosai Danishi yaji daɗin kalamansu, hada yafiyarshi suka nema akan bugun da su kayi mashi lokacin da aka ɗauki Batool, Yace masu bakomai ya cancanci hakan ne, Ɗaya bayan ɗaya saida yabi kowaccensu, Ya rungumeta ajikin shi, Su parveen an samu abunda ake so, Har wani ƙanƙame shi take yi, kamar zata 6alla wuyanshi da hannayenta, har sai da haris yaja wuyan rigarta, ya janyeta daga jikin Danish Cikin zolaya yake faɗin"Halan Yayi maki kama da Tsokar nama ne? Shiyasa kike ƙoƙarin lashe jikin shi," Gaba ɗaya suka saki dariya, shima Danish ɗin murmushi ne akan fuskarshi, Mubeen ne ya lura da angel data kifa kanta saman pillow, ya ɗaga murya tare da cewa"Jama'a mun manta da Mai girma Angel" yayi maganar yana nunata da hannun shi, haris yace"yawwa ƙwara daka tuna min, Angel ki taso kema ki rungumi ɗan uwanki, kamar yadda kowa yayi, yau muna Cikin nishaɗi,"
da biyu haris yai maganar yasan basu shiri, banza ta yi dasu bata ce komai ba, Azeeza ta ruƙo hannun danish tana faɗin"Pls Muje wurinta ka rungume ta itama," janye hannun shi yai daga ruƙon da azeeza tayi mashi, Saboda ba zuwa zaiyi ba, A sharuɗɗan alƙawarin da suka ɗaukar ma juna, Zai nisance ta, da kuma gujewa haɗa ido, idan har yaje kusa da ita Alƙawarin xai karye,
Atare suka hada baki suna fadin Pls Danish Muje dan Allah, itama mu sanyata farin Ciki, " ganin yaƙi basu haɗin kai yasa suka koma wurin angel suna lallashinta akan ta taso suje itama ta rungumi ɗan uwanta, duk tana jin sautin muryoyinsu acikin kunnuwanta, sai magiya suke yi mata amma taƙi ɗagowa daga kan pillow, ransu ya 6aci, haris yace Tunda mun bisu ta arziƙi sun ƙiya, muyi amfani da ƙarfin mu"
Ya kai ƙarshen maganar yana nannaɗe hannun rigarshi, suma sauran suka nannaɗe nasu hannuwan rigunan, alamar xasu yi dambe, dama ɗabi'arsu ce, naɗe hannun riga, Atare suka tarar ma danish, suka dinga janshi, kamar dutsi sai nishi suke yi, saboda ya toge yaƙi basu haɗin kai, duk yadda yaso su ƙyale shi amma hakan ya faskara, ba zato ba tsammani suka wurga shi saman gadon angel gaba ɗaya ya faɗa saman jikinta, Har wani firgita ta ɗanyi, sai kuma ta lafa,
Su azeeza sai ihu suke Yi suna dariya, Hada tafa musu hannu,
Bawan Allah Fargaba duk ta cika shi, so yake ya ɗaga ta amma yana shakkar su haɗa ido da ita, kusan atare zuciyoyinsu ke bugawa, Tana iya jiyo sautin numfashinsa dake sauka saman fatar kafaɗarta,
"Alƙawari Ya karye tunda Kun hada jiki, Ko ba haka ba guys? Haris ne yae musu tambayar suka haɗa baki wurin cewa"Yeah" sai tiƙar dariya suke yi hankalinsu kwance, kamar waɗanda A ka yi wa Albishir da mukullin fita daga cikin kurkukun ƙaddara,
Ita kanta angel mutuwar kwance ta yi, tun da ya faɗo saman jikinta, ta gaza motsa koda yatsun hannunta ne, sai faman sauke ajiya zuciya take yi, yafi a ƙirga, maimakon taji haushin kwanta mata jiki da yayi saima taji wani irin sanyi mai daɗi yana ratsa zuciyarta, ta yi matuƙar yin kewar shi, almost 1 month Basu shiri da juna, till today da Allah yasa Su haris suka taimaka wurin hankaɗo shi, yanzu aiki ya rage nata wurin ƙoƙarin ganin sun haɗa ido, hakan zai tabbatar da cewa Alƙawarin su ya karye...............💋
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Ƴar ƙara ta saki kamar wadda aka Cixa, a matuƙar ruɗe Danish ya ɗago da kanshi daga saman shoulder ɗinta, sam bai yi tsammanin idanuwanta a buɗe suke ba, saboda ta ɗan lumshe su, tana ganin ya ɗago ta zaro su acikin nashi, har saida yaji gaban shi ya faɗi, Su haris dake kewaye da gadon sai ihu suke yi suna faɗin"Alƙawarin Ya karye, Ya 6alle, Ya ruguje Ya rushe," gwanin ban dariya Sai nishaɗi suke yi abun su, A wani irin yanayi suke kallon juna, ɗaga mashi gira tayi tare da kashe mishi ido ɗaya yadda kasan ƴar duniya tace"Alƙawari Ya karye, Irin wannan kallo haka kamar xaka Lashe ni," lumshe idanuwan shi yae still ya sake opening dinsu slowly on her face, ya rasa dalilin kallon ƙurullan da yake yi mata, ko na second ɗaya baya son ya kawar da eyes ɗinshi daga kallon kyakkyawar fuskantarta.
yana jin wata irin natsuwa mai kwantar da tarzoma acikin zuciya, Dariya haris yae tare da cewa"Danish fa suman kwance yae, Da alama Mun kashe mashi baki, Parveen ɗauko musu Madubi Su kalli fuskarsu atare, Ki haɗo mishi Da Naman kazar shi da bai ci ba, xamu tasa shi gaba sai angel ta bashi abaki Yaci, Ko yana so ko baya ehe" gaba ɗaya suka haɗa baki wurin cewa"Dolen shi ne ma, Idan yasa taurin kai Mu tarar masa, kamar yadda mu ka yi a yanzu," jiki na rawa parveen ta nufi akwatin da madubin yake, A jiye ƙarƙashin table ɗinsu, Nan suka kwantar dasu, ɗaya saman ɗaya, ta janyo akwatin Ta buɗe shi, daga sama Mirror ɗin yake, Ta sanya hannu ta ruƙo handle ɗin shi, da gudu taje ta miƙa ma Haris Ya sanya hannu ya kar6a, kafin Ta juya ta nufi gadon Batool, Allah sarki, Har yanzu a ƙarƙashin gadonta suke Ajiye kingin abincin da suka rage, Zuƙunnawa tae tare da tura hannu ta janyo basket ɗin, maimakon taje ta kai musu, sai da ta fara Kai naman baki ta ɗan 6alla, tukunna ta miƙe da sauri taje ta miƙa ma Haris kwandon, yace da azeeza ta kar6a ta ruƙe, tun da shi madubi ne a hannun shi, Bayan azeeza ta kar6a suka ɗan dakata suna jiran Danish Ya miƙe daga Jikin Angel, sai dai basu ga alamun xai ɗago ba, don ya tsare ta da waɗannan fararen eyes ɗin nashi, sun ƙurawa juna ido, kamar ranar suka fara ganin juna, muryarta ƙasa ƙasa tace"Ka ɗaga ni, na fara jin nauyi," da alama bai ji me tace ba, Xaro mashi gray eyes ɗinta tae gwanin ban tsoro ta kuma cewa"Am talking to u my man, Alƙawari ne dai ya karye, ko kana so ko baka so," Bata yi tsammanin zai tanka mata ba, in a smoky voice ya furta"kin shammace ni," murmushi ne ya bayyana akan face ɗinta,
"Bani na shammace ka ba, sune suka shammace ka, Kuma taimakon ka su ka yi, ko ba haka ba"? Tae maganar tana ɗan jifar shi da harara, martanin mirmishin ya mayar mata, kafin ya daure ya yunƙura ya ɗaga jikinta, ya koma daga gefe ya gyara zaman shi sama mattress din, ya jingina bayan shi jikin bango, Itama ta miƙe ta jera kafaɗa dashi suka xauna, Yayin da suke fuskantar ƴan uwansu, dake a kewaye dasu, Sai murmushi suke sakar musu, musamman azeeza hada wani kashe musu ido.
Matsawa haris yai daga gefen gadon Ya miƙa ma Angel madubin, Tasa hannu ta kar6a, tun kafin ta saita shi saitin fuskar Danish yae saurin shutting eyes ɗinshi, muryar shi tae low wurin furta"Pls angel, ki janye shi bana son ganin shi," sosai ya datse idanuwanshi, naufal yace"Why? Its just a mirror, face ɗin ka zaka gani ba wani abu ba, muna so ne kawai kaga irin kyan da ka yi acikin Sabon Uniform ɗinka, ko ba haka ba guys"? Atare su haɗa baki wurin cewa"Yeah"! Kallon shi Angel tae ganin har jikin shi ya fara kakarwa, Mamaki ya kama su, ko meyasa baisan Kallon madubi, wannan itace tambayar da suke yi ma kansu.
"Idan ma tsoron kallon shi ka ke ji, remember that am with u by ur side, u can hold me,"
jin wannan maganar ta Angel, yasa shi yin saurin xagayo da hannun shi ta bayanta zuwa saman kafaɗarta ta hagu, Ya ɗan kwantar da kanshi saman right shoulder ɗinta, Har ga Allah bai son kallon Mirror, Ba yadda zai yi ne don sun matsa mi shi, kuma a yanzu yana son farin cikin su shiyasa ya amince musu,
Kanga madubin ta yi saitin Fuskarshi tare da cewa"Ka buɗe idanuwanka a hankali," bin umarnin ta yae wurin buɗe eyes ɗinshi slowly ya ware su akan Round mirror ɗin, har wani lumshe su yake yi, Murmushi angel ta saki ganin yana kallonta ta cikin madubin tace"Bani xaka kalla ba, Fuskarka zaka kalla" ta6e mata lips dinshi yae irin an takura shi ɗin nan,
Su haris sai dariya suke tiƙa, sun samu Abun kallo, hada ƙoƙarin zuƙunnawa bakin gadonsu, saboda sun gaji da tsayuwa, duk yadda ta so Danish Ya kalli fuskarshi acikin mirror yaƙiya sai dai ya kalli fuskarta, Javed yace"its okey, Hakan ma ya wadatas, Yanzu A ajiye madubin gefe, Ga chicken leg ɗinsa nan ki bashi ya ci, idan ya kammala da kazar sai ki ba shi fruit ɗin shi" Amsa mashi tae da toh tana murmushi ta miƙa ma parveen madubin ta sanya hannu biyu ta kar6e shi, ta juya ta nufi box ta ajiye shi, ta dawo ta zuƙunna gefen su hanna, Duk fa wannan budurin da suke Yi basu san cewa Dare Yayi ba, don tuni Hasken Fitilun ceilling ɗinsu Ya ɗauke, Na floor lamps ne Ya Haskaka Room ɗin nasu, ba tare da sun ankara ba, Wasu irin fitilune Da zarar duhu yayi da kansu suke kunna kansu, Kamar dai na saman ceiling ɗinsu, banbancin shi ne, da zarar dare yae suke ɗauke wa su kuma na ƙasan sai in duhu yayi suke kunna kansu, Kuma haskensu baida banbanci, da alama babu mai jin bacci acikinsu, sakamakon baccin da suka sha ɗazu da marece, hada ƙarin hakan yasa suka gaza gane cewa Dare ya yi.
Azeeza ce ta miƙa ma Angel Kwandon Tasa hannu biyu ta kar6a ta ɗaura shi saman Laps ɗinta, kafin ta zura hannun ta na dama ta ruƙo cinyar kazar ta ɗago da ita, saitin bakin shi ta kanga mashi ita, Sai gashi Ya xaƙe dai ci ya ke yi su mubeen suna ta yi mishi clapping, sai da ya Cinye rabi Ya janye bakin shi, ta tambaye shi ko ya ƙoshi ne? yace mata eh, zata iya cin sauran, parveen kamar zatai kuka tace mufa,' Dariya angel tae tare da miƙa ma azeeza Naman kazar maimakon parveen tace"Saboda rashin tsoron Allah Parveen Nafa ga wurin da kika yaga, hada sahun haƙoran ki, a jikin cinyar kazar, ko an gaya maki ban lura ba ne," Yatsina fuska parveen tayi, Hada murguɗa baki, Azeexa kuwa ta kar6a cinyar kazar daga hannun Angel, ta ɗan gutsira ta miƙa ma hanna itama ta yaga, ɗaya bayan ɗaya saida kowa Ya Ci naman, A ƙarshe suka miƙa ma parveen Ƙashi, su ka ce Ta gwaigwaye shi, Hada ƴar ƙwallarta saboda tsabar baƙin ciki, kuma hakan baisa taƙi kar6ar ƙashin ba,.
Apples ta curo kusan Uku da suka rage mashi, Yace mata shi ɗaya ya ishe shi, sauran ta basu su ci, tace mashi hada sauran fruit din? Don akwai ayaba guda uku, Yace mata Ta ajiye mashi ayaba ɗaya ta basu sauran su ci, Sai daɗi suke Ji, Ta miƙa ma haris Apples biyu da ayaba Biyu Yasa hannu ya kar6a, Shi ya rarraba musu, tare da miƙa ma kowannan su, suka kar6a suna ci.
Abaki angel taci gaba da bashi apple ɗin yana Ci, sai da ya ci rabi, yasa hannu ya kar6a, Ya koma yana bata abaki tana ci, Ayabar ma shi ya 6are 6awon Ya zura mata a baki, taci kusan rabi kafin ya ƙarasa cinye sauran, bayan sun kammala suka sha ruwan su dake acikin bottle,
Haris ne ya kawar da kwandon Ya maida shi a ma ajiyarsa, Parveen kuma ta kwashe 6awon Ayabar da su ka 6are ta nufi toilet ta zubda su cikin trash can, Daga bisani ne suka gane cewa dare ya nutsa, Angel tace su jira tayi musu addu'a kafin su kwanta, Suka amsa mata da toh, Saukowa tae daga saman gadonta, tabar Danish zaune yana kallonsu, Cikin harshen larabci ta shiga karanto musu addu'o'in tana tottofa masu, suna amsa mata da ameen, bayan ta kammala, Hannah ce ta basu shawarar su Cire sabbin Uniform ɗinsu, Su sanya tsoffin gudun kada su yi squeezing,
In yaso gobe da safe sai su maida sabbin, Angel tace kin kawo shawara mai kyau, daga yanzu old uniforms ɗinmu sun zama sleeping dress ɗinmu, Kowa Ya ji daɗin wannan shawarar, without wasting time suka sauya Kayan jikinsu, Kowa Ya ninke nashi ya tura a cikin akwati, Suka ɗauko Tsaffin suka sanya ajikinsu, daga bisani Kowannan su Ya nufi gadon shi ya kwanta Suka ja bargunansu, in a short time bacci yae awon gaba dasu, ɗakin yae tsit ba ka jin hayaniyar komai, Mutun biyu ya rage angel da Danish, babu alamun zasu runtsa, Ae yau suna cikin farin Ciki,
Ya yi tsammanin zata dawo ta kwanta saman gadonta, sai kuma yaga ta nufi ƙopar shiga sashen toilet dinsu, har sai da ta shige, kafin ya sauko daga saman gadon yabi bayan ta, A bakin ƙopar toilet din ya la6e yana kallonta,
A yayin da take zuƙunne gaban tukunyar flowers din nan, kamar mai ta6in hankali, haka ta zauna tana ba furen Batul labarin abunda Ya faru Yau, hada ƴar ƙwallarta tace"Naso ace kina atare damu, a ka yi wannan shagalin, nasan zaki yi farin ciki sosai, saboda burin ki ne, kiga mun haɗa kan mu, Ina matuƙar ƙaunarki ƴar uwata rabin raina..." kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon hawayen da suka wanke mata fuskarta.
Sam ba ta ji takun tafiyar shi ba, sai dai ta ji shi, a gefenta Ya zuƙunna, ɗagowa ta yi da rinannun idanuwanta suka haɗa ido da juna, a hankali ya cire hannun shi ya ɗaura shi saman sumar kanta, Ya ɗan kwanto da kanta saman shoulder dinshi, cikin sanyin murya ya soma lallashinta, Har ya samu ta ɗan lafa, Da kanshi ya share mata hawayen dake akan fuskarta, a tsanake suke kallon furen batool Ya miƙe tsaye babu lanƙwasa, Red leaves ɗin shi sun bubbuɗe sun cixa launinsu, Haka furen daddynta Yana a tsaye launin shi kore Ya cixa, sai dai wani abun mamaki furen Ya xuƙunna, kamar mutun " aɗan ruɗe tace mashi"me hakan ke nufi? Furen dad ɗina Ya zuƙunna," hannu Danish ya kai tare da shafa ganyen furen yace"Bani da amsar tambayarki, amma A ilmin da nake dashi kan furenni, Daddyn ki, Yana yin wani abu adai dai irin wannan lokacin" bakomai ya faɗo mata arai ba, face Sallah, saboda sanin cewa a lokacin baya daddynta yana yawan Yin nafilfilin dare, duk da bata da tabbacin cewa idan Yana araye, ko kuma Lokacin ƙasar Nigeria da kuma Na kurkukun ƙaddara Ɗaya ne, zai Iyayiyuwa asamu banbanci tunda kurkukun tana hasashen ba acikin ƙasar Nigeria Ya ke ba,"
jin ta yi shiru yasa shi kallonta in a cool voice yace"what are u thinking"? Da sauri tace mashi ba komai, yace mata"muje mu kwanta, idan ma kina so zan goya ki abaya na" murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, har time ɗin ba ta ɗago da kanta daga saman kafaɗar shi ba.
wani irin daɗi take ji, ita fa jin Danish take yi kamar wani sashe na sassan Jikinta, da ke taimaka mata wurin yin numfashi, idan ta haɗa jiki da shi, ba komai take tunawa ba, face Daddynta, Yadda take tumurmusarshi, idan suka kwanta a gado ɗaya, wani lokacin da gangan take ɗaura mashi ƙafafuwanta saman ƙirjin shi, duk don saboda ta takura mishi, a lokacin data addabi rayuwarshi, Allah sarki tajuddeen Namijin Duniya!
Numfasawa ta yi kafin ta Canza akalar tunanin nata zuwa ga Aunty Aneelerh, Bakomai ya fado mata arai ba, face ranar da ta faɗo musu ɗaki babu sallama, Sun fito daga Cikin toilet Kowannan su ɗaure da white towel a ƙugun shi, hankalinsu ya tashi ganin Angel, Uwar gulma da son tsegumi ga tambaya kamar ƴar jarida, A lokacin ita da uzair duk suka sha Jinin jikinsu aka rasa me magana acikinsu, Ita ko ta ruƙe qugu tana binsu da kallon tuhuma. ta ce su fada mata me suke yi acikin toilet su biyu, har suna haɗa baki wurin ce mata, babu abunda suke yi, dama sunga yayi datti ne shine suka shiga suna mopping ɗinshi, wani irin kallo ta jefa musu tace"To meyasa suka fito da ɗan towels a ƙugunsu? Ina kayan su suke"? Saboda tsabar ruɗi uzair yace"ita ce take wanka, ta kira ni don in cuɗa mata bayanta, saboda hannun ta bai kaiwa" Dariya angel tasaki tana fadin"wai ita zasuyi ma wayau, sun ganta ƴar ƙarama, hmm basu san tasan komai ba, tun da sunƙi faɗa mata, zata je ta faɗa ma daddyn ta ne abunda suke aikatawa acikin toilet, tana kai ƙarshen maganar, ta watsa da gudu zata fuce, aikuwa aguje suka bi bayanta, har suna bangaje juna Abakin ƙopar fita bedroom dinsu, ta dinga yi musu yawo da hankali, tana zagaye falon suna bin bayanta, daƙyar suka samu Allah ya taimake su, suka damƙota, Suna faman sauke ajiyar zuciya, a saman sofa suka zaunar da ita, sai tiƙar dariya take yi tana kallonsu, su fa duk a tunaninsu tasan komai game da ma'aurata, tunda sun san halinta, kamar aljana haka take ga shegen wayau, sai da suka tambayeta me zata faɗa ma daddynta, tace musu abunda suka faɗa mata suna yi acikin toilet, ba ƙaramin kwanciya hankalinsu yae ba, ganin