Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 287659 words

Chapter 6 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1767

Ads at the middle of Article

saman Gadon da gudu ta nufi toilet ta shige taja ƙopar ta rufe,

A hanzarce Ya sauko daga saman godon cike da fargabar karta kashe kanta, tura ƙopar yayi ya ji tayi Locking dinta,

Bubbuga ƙopar ya shiga yi yana ambaton sunanta"My angel am sorry, kada hakan Ya ta6a zuciyarki, kinsan ina sonki, banason zubar hawayen ki"

Daga Cikin toilet ɗin yajiyo muryarta Cikin shesshekar kuka tana faɗin"I hate my self daddy, cikin toilet aka haife ni, kuma ta gudu tabar ni saboda bata sona......"
Runtse idanuwan shi Yayi tare da ɗan Cizon lips ɗinshi Calmly ya kira sunanta"Angel pls forget about it, Tunda kina da ni don me zaki damu kanki? Ni ne mom dinki kuma daddyn ki,
Zuƙunnawa Yayi agaban ƙopar, yana ji aran shi cewa tana zaune a gaban ƙopar, tsit ya ji ta daina kukan
"Pls say something to me, ko naji sanyi acikin zuciyata"
Shiru bata tanka mashi ba,
"Ki buɗa mun ƙopar"
Sai Lokacin yajiyo muryarta can ƙasa ƙasa"daddy inaso na mutu, kodan saboda nadaina 6ata maka rai"
Cikin matsananciyar damuwa Yace"idan kika mutu angel shi ne zan shiga Damuwa wadda zatayi silar mutuwata nima, saboda kece Oxygen ɗin da nake shaƙa,"

Yakai ƙarshen maganar tare da kwantar da kanshi jikin door ɗin, don Yaji daɗin Jin muryarta

"I made a mistake daddy, I won't hurt you anymore,"

Saboda tsabar Mamakin Jin abunda tace har saida Ya ɗan dago da kanshi, yana kwalkwale kunnanshi wai koda Ya samu matsalar hearing ne,
"I love u daddy" ya kuma Jin ta furta mashi aruɗe yace"Repeat it pls"
"I love u daddy"
"sake maimaita mun naji"fuskar shi ɗauke da murmushi Ya yi maganar,
Sake maimaitawa ta yi kamar yarda ya nuna yana son ta yi ma shi,

"I love U daddy, Bani da tamkarka a duniyar nan"
Wani irin ihu ya saki, Irin wanda Ƴan kwallo ke yi idan sunci nasara akan wasan su,

A ƙagare Yace"Come out pls, ina so naji ɗumin ki a jikina"

Yana jiyo alamun tana buɗe ƙopar kamar jira yake yi, tana ƙarasa buɗe wa Ya janyo ta Jikin shi yayi hugging ɗinta very tight, hannun shi na acikin sumarta, Wani irin farin Ciki ne Ya lullu6e shi kamar wanda a ka yi ma Albishir da gidan Aljanna,' dole Taj ya yi farin ciki cos this is the first time da angel Ta fara furta mashi kalmar tana son shi a mtsayina mahaifinta, Ya ji tausayinta sosai, bai ta6a tunanin akwai lagwanta ba sai yau, da ta ji cewa mahaifiyar ta ta gudu ta barta, Jikinta ya yi sanyi, da yasan da haka da tuni ya faɗa mata, da duk wannan abun bai faru ba,
daukarta Yayi asaman bayanshi, yakaita Cikin motarshi, atare da ita suka je masallaci, Ya barta acikin mota, Bayan ya kammala sallar, ya dawo Ya shiga motar yayi driving ɗinsu zuwa Restaurant, komai take so shiyasa aka kawo masu, sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Suka dawo gida, A palour suka zauna saman Sofa tana rungume ajikin shi, Suna kallon tashar Mbs 3, dama best channel ɗinta ce saboda suna sanya Cartoon, tafi sha'awar kallon Cartoon da kuma zombie,

Tuni bacci ya dauketa ajikinshi, asaman kafaɗar shi ya ɗauke ta Ya nufi bedroom dinsu, don ya kwantar da ita, a hankali Ya tura kopar ɗakin Ya shige, A saman gado Ya kwantar da ita, Sai da ya fara daukar wayar shi dake ajiye agaban mirror, Tukunna Ya haye saman gadon ya janyo ta a jikinshi, Yana shafa sumar kanta, cikin magagin bacci ya ji tana fadin"I luv u daddy" murmushi ya ɗan saki, Tare da manna mata kiss a gefen fuskarta
"Luv u too My own daughter"

Number Uzair Ya kira, tana fara ringing Uzair ya ɗauka,
"Aminina Yanzu nake shirin zuwa duba jikin ka"
"Na hutasshe ka ba sai kazo ba, Jiki ya yi sauƙi Alhamdulillah"
"Naji labarin abun kunyar da kaso ka aikata na kashe ƴarka, Ae ni har na yi shirin zuwa ɗaukar rahoto"
Fashewa Taj yayi da dariya"Ta
6atamin raine, ni kaina bansan nayi wannan yunkurin ba,"
"Yanzu Ina virus ɗin taka take"?a cewar uzair, don tun ranar da ta Sa ƴan sanda su ka kama su akan ƙazafin da ta yi masu na cewa su ƴan yankar kai ne, tun daga ranar Yake kiran ta da Virus,
Murmushi Taj yayi, tare da kai hannu ya shafa sumar kan angel, Virus ta yi bacci, Mutumina ka ta ya ni farin Ciki,"
Uzair yace"Meya faru"?
Nan Taj ya kwashe duk abunda Ya faru tsakanin shi da angel ya sanar mashi,"
Yana jiyo sautin dariyar farin cikin da uzair Yake yi,
"Ja'irar taji ƙamshin mutuwa, Allah yasa ƙarshen wahalarmu ce tazo, Amma fa nayi farin Ciki,

"Ameen mutumina"
Shiru suka ɗanyi,yana so ya tambaye shi aneelerh amma ya kasa,
"Muyi video call mana"acewar uzair,
Batare da musu ba suka canza Kiran zuwa Video call, A kwance uzair yake saman katafaren gadonsu, ya dan tada kan shi saman pillow, jikin shi na sanye da kayan Bacci,
"Show me her face" murmushi taj ya yi tare da haska mashi fuskar angel, ta sa ki baki da hanci tana ta sharar bacci,
Dariya uzair yayi"waya ga mashasha, wannan ae itace Laca sera jibi yadda ta saki la66a, a haka zata zama surukar mu,"
Fuskar Uzair ɗauke da murmu shi yace"cin mutuncin ya isa haka aminina, kai ka sani Wlh angel koda kuɗin mutun saida rabon shi, koda rabon shi sai in Allah ya nufa"
Jinjina kai Uzair Yayi tare da ɗan yatsina fuska yace"Virus ɗin"?
Taj na ƙoƙarin buɗe baki ya mayar mashi da martani, adai dai Lokacin Aneelerh ta fito daga Cikin toilet, Chest ɗinta ɗaure da farin towel iya guiwarta ya tsaya, Ta cikin Screen ɗin wayar uzair, Taj Ya hangota yanayin kwanciyar da uzair yayi ya juya ma Toilet ɗin ɗakin shi baya, wanda hakan yasa har Taj ya iya hango fitowarta,

Baisan ya a kai ba Ya tsinci kanshi da satar kallonta, Ya bar uzair sai faman zuba yake yi kamar kanyar da bata da daɗi, gaban mirror ta tsaya tana tsane sumar kanta da towel,

"Me kake tunani ne"? a firgice taj Ya mayar da hankalinshi kan Uzair, muryar shi na inda inda yace"Bakomai zan kwanta mutumina, Sae Allah yakaimu," da sauri ya yi rejecting kiran tunkafin ma uzair ya yi mashi sallama,

Lumshe idanuwan shi ya yi zuciyar shi a cunkushe, duk yadda yaso Ya hana kan shi tunanin abunda ya faru tsakanin shi da aneelerh abun ya faskara, daƙyar ya samu bacci yayi awon gaba da shi,

Tun daga wannan Ranar Angel bata ƙara 6ata mashi rai ba, koda yaushe suna manne da juna wata irin shaƙuwace a tsakanin su, mutu ka raba takalmin kaza, tabbas Angel taba kowa mamaki, irin yadda take son mahaifinta, tarairayarshi take yi, biyayya take yi mashi sau da ƙafa, Xaman Lafiya ya wanzu a tsakanin su.

A hankali ya tura ƙopar falon ya shigo Ciki, dawowar shi ke nan daga masallaci, ya ɗan tsaya sauraron wa'azi, jikin shi na a sanye da jallabiya ash colour, da sauri ya nufi bedroom ɗinsa, Da sallama a bakin shi ya shiga, tunkafin ya ƙarasa shiga ya same ta a kwance tsakiyar gado tana ta sharar baccin ta hada minshari, Agogo ya kalla shida ta kusa, ƙarasa shiga Cikin bedroom ɗin ya yi a gefen gadon ya zauna, tare da ɗan juyo wa yana kallonta, tayi ɗai ɗai a saman gadon, Kayan baccin da ya sanya mata jiya sune a jikinta riga da wando blue sky, curly hair ɗinta duk ya cukurkuɗe ya nannaɗe,

a Hankali ya sanya hannu tare da jan hancin ta, yatsina fuska tayi tare da juyar da kanta gefe batare data farka ba,
"Wake up My lovely daughter" Cikin kunne yayi mata raɗa,
Buɗe gray eyes ɗinta ta ɗanyi slowly tana kallon fuskar shi biji biji,
"Nauyin bacci ko? Oya wake up, kada muyi late, ki tashi inyi maki wanka, in girka maki abinci mu ci mu ƙoshi, kafin na sauke ki a school ni kuma na wuce wurin aikina

Jin tayi shiru ba ta ce komai ba, yasa shi fara Yi mata cakulkulo, lokaci guda ta 6a66ake da dariya, white teeth ɗinta kamar gonar auduga, saboda tsabar kyau, kai kace wani abinci bai ta6a giftawa ta cikinsu ba saboda hasken su,


Sosai ya sanya ta nishaɗi, a ƙarshe Ya ɗauke ta saman kafadar shi Ya nufi toilet da ita, almost 15 mins Ya fito da ita Goye saman bayan shi, Ya ɗaura mata towel ajikinta,

A saman mirror chair ya zaunar da ita, Hair dryer Ya ɗauko acikin drawern dake ɗauke da madubin, Ya jonata ajikin Socket,Nan take Iska ta soma busowa buuuuu, runtse ido tayi tana dariya mirmishi ya saki ganin yadda ta ɗan zabura, zura hannun shi ɗaya yayi acikin sumar kanta yana cakuɗata sosai ya busar mata da gashin, Bayan Ya kammala ya kashe dryer din, ya mayar da ita inda ya ɗaukota, ya kuma ɗauko Comb,Ya shiga sharce mata gashin, Sai faman sakin murmushi take yi, A duk lokacin da taga daddynta yana yi mata hidima kamar sarauniya ba ƙaramin daɗi ta ke ji ba, har tunani take yi anya kuwa akwai yaron daya fita samun gatanci?


ta cikin mirror taj ke kallonta, ganin ta ƙurawa madubin ido da alama wani abu ta ke tunani, Man gashin ta Ya ɗauko Ya shiga shafa mata, Bayan ya kammala Ya ɗauki ribbom ɗinta da ke a jiye gaban mirror din, Hannu yasa yana ƙokarin tattara gashin kanta, Abun mamaki daga ya haɗa zai ɗaure saiya watse, Yawan gashi ne da ita ga tsayi, don a yanzu gashin ta ya kai mid back ɗinta, sai da taj yayi da gaske tukunna Ya samu ya ɗaure mata shi,

"Daddy ni da kai wa ya fi kyau" ta yi tambayar tana sakar ma mirmishi
Dungurin kanta yayi"Kinfi kowa sani ae" ya yi maganar tare da juyawa ya nufi closet ɗinsu, Hannu yasa ya buɗe murfin, Jerin kayan sawan shi ne da kayanta, Uniform ɗinta Ya ɗauko mata riga fara sai mini skirt red colour, Abaya fara ƴar short, a yanzu angel tana a class 5 saboda ƙoƙarinta, ga wayau da Allah ya yi mata uwa dila agari,

bayan ya kammala sanya mata uniform ɗin Ya feshe mata Jikinta da turare, Ya zaunar da ita gefen gado"Am coming now" ya ambaci hakan tare da juyawa Ya fuce daga ɗakin, jim kaɗan Ya dawo hannunshi ɗauke da Food basket ɗinta, madara ce me sanyi Acikin roba, tare da slide bread ya sanya mata aciki,Sai ƙaramar kula mai ɗauke da chips,
Ajiye mata yayi a gefen gadon, Shaf shaf ya shige toilet Yayi wanka, Ya fito sanye da short, zuba mashi ido ta yi tana kallon shi,.
Harara ya ɗan jefa mata"Zansa kaya"
ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tayi, tamkar bata ji me yace ba,
Gyaran murya yayi mata"Can't u hear me? Ki koma Falo inaso zan shirya".
Maƙe mashi kafaɗa tayi cikin shagwa6a tace"Amma ae ni har wanka ka ke yi mun, kuma kana ganina ba kaya, Amma ni kullum sai ka kore ni in zaka sanya kaya'

Tashin Sense, zaro ido waje ya yi yana kallon ta Cike da mamaki, Ya ma rasa gane wai me take nufi, sai lokacin ya gane kuskuran sa na rashin ɗaukar mai aikin da zata dinga kular ma shi da ita da wankan da yake mata har wannan lokacin,

"Angel don't waste my time, Oya hold ur basket, ki jira ni a falo,"
Ganin ya ɗaure fuska ba wasa Yasa ta sauko daga saman gadon tana tur6une fuska takai hannu ta sungumi basket ɗinta ta fuce falo, Saman sofa ta zauna tana Cika tana batsewa, Bayan ya kammala shiryawa cikin suit, Ya fito daga ɗakin Ya nufe ta, Hannunta ya kama suka fito daga falon,

Baba maigadi ya samu, A harabar ajiye motocinshi, Yana goge ma shi motar da zai fita da ita,

Tunkafin su ƙarasa baba maigadi ke ta faman washe ma angel baki, ita kuwa ta tsuke fuska, Dama aduk lokacin data ɗauki wanka ta san ta yi kyau, Daƙyar ta ke ma mutane magana,

Suna ƙarasowa bakin motar, Baba maigadi Ya miƙa mashi hannu suka soma gaisawa, kafin Ya kalli angel"Ƴan mata makaranta za'a tafi"?
Ɗaga mashi kai tayi alamar eh"
"Allah ya bada sa'a Angelata"maƙe mashi kafaɗa ta yi"Ni ta daddy ce"dariya su ka yi gaba ɗayansu,

Taj yace"Bari mu wuce kada mu makara" baba maigadi yace "Allah ya tsare adawo lpy" ya amsa ma shi da ameen kafin ya buɗe mata motar ta shiga ciki, ya zagaya ta left hand, ya buɗe ya zauna a driver seat,


A tsanake Yayi ma motar key, tare da karya kwana Ya nufi gate ɗin, da sauri baba mai gadi Ya riga shi ƙarasawa Ya buɗe mashi gate ɗin, Ya fuce daga gidan,

A hankali yake driving, Ta wutsiyar idonshi ya kalleta, Ta natsu ta kame kanta,
"Karfa kiyi mun bacci mun kusa ƙarasawa"
"Ba bacci nake ba,Ina tunani ne"
"Daddy wlh ni banaso mu rabu, dama ka dinga tafiya dani wurin aikin ku"
Murmushi ya ɗan saki"Karatun naki fa"?y ayi mgnr yayin da yake ƙokarin juya sitiyarin moyar don ya kwarya kwana,
Shiru bata amsa mashi ba,
"Ni inaso ki yi karatu angel, sai da ilmi ita kanta rayuwa ta ke yin kyau, ko bakyason nan gaba ki zama wani abu da mutane za su yi alfahari dake"?

"Inaso" ta amshi amsa a takaice,
"To faɗamun me kikeso ki zama"?
Da buɗar bakin ta sai cewa tayi"house wife" ae baisan lokacin daya tuntsire da dariya ba, zuba ma shi ido ta yi tana kallonshi, fuskarta babu alamun wasa don ita dagaske ta yi maganar,
"Daddy why are u laughing? did i say something wrong"?
Girgiza kai yayi"a'a,May be u did'nt understand my question, Ina nufin wani aiki ki ke son Yi idan kika girma, a aikin gomnati? ya yi tambayar adai dai lokacin daya ƙaraso bakin gate ɗin makarantar, Ya danna hon Mai gadi Ya buɗe mashi gate Ya shiga da motar Cikin school ɗin, A parking space ɗinsu Ya tsayar da motar,

Fitowa yayi tare da zagayawa Ya buɗe mata murfin motar "baki amsa mun tambayata ba"?
Ɗagowa tayi suka haɗa ido da shi
"Daddy my answer is the same, I wanna be a house wife" Sakin baki yayi galala yana kallonta, Ya rasa taya ya akai tafara tunanin zama house wife, dududu fa primary school ta ke,
Gudun kada ya makarar da ita,Yasa shi yin shiru bai ƙara tanka mata ba, Ɗauko mata food basket ɗinta ya yi kafin ya ruƙe hannunta suka nufi Cikin makarantar, kamar kullum har Cikin class ɗin su Ya kai ta, English teacher ɗinsu ya taras a jin Mrs favour,Cikin harshen turanci suka gaisa da shi, ya damƙa mata angel kafin Ya fito daga class ɗinsu Ya nufi motar shi, Zuciyar shi a cunkushe duk ya rasa sukuni, tunani ya shiga yi taya za'ae ya canza mata ra'ayinta na zama matar aure? don wannan ba ƙaramar matsala bace agare shi, ƴar ƙaramar yarinya tana tunanin zama matar aure,

Karasa shige wa Cikin motar yayi a tsanake Yayi mata key, Ya nufi gate ɗin makarantar mai gadi ya buɗe mashi ya fuce,

Harya haura saman titi, Hankalin shi na akan Kalaman angel, shi da yake da burin ta zama babbar ma'aikaciyar gomnati, ashe ita sam Ba wannan bane agaban ta, A ƙarshe dai ya yanke shawarar idan ya ta shi daga aiki ya ɗaukota suka koma gida, Zai zaunar da ita ya yi mata karatun ta natsu, Ko ya samu ya canza mata ra'ayinta,


Wuraren ƙarfe biyu na rana, Ya tashi daga aiki,Sai daya fara zuwa masallaci Yayi sallah cikin jam'i, tukunna Ya nufi school ɗinsu, Lokacin daya karasa makarantar, tunkafin ya fito daga cikin motar, maigadi ya sanar dashi cewa Dr tazo ta dauketa,

Ba ƙaramin daɗi yaji ba, kaitsaye 6atare da 6ata lokaci ba, yaci gaba da da driving, har ya ƙarasa Gida Tun a bakin gate ya tambayi baba maigadi ko aneelerh ta kawo angel, Yace mashi a'a, hakan na nufin tana a gidan su,


Bayan ya ajiye motar Ya nufi Cikin gidan, Bedroom ɗinsa ya shiga, Shaf shaf Ya rage kayan Jikin shi Ya fada toilet don ya yi wanka, ko yaji daɗin jikin shi,


Adai dai wannan Lokacin Aneelerh ta shigo Cikin gidan, ɗauke da angel da alama ta yi bacci, lokacin da ta shigo falo tana ta kwala sallama ba'a amsa mata ba, kawai sai ranta ya bata cewar ko bai kaiga dawowa gidan bane, don bata lura da motar shi da ke ajiye ba, hakan yasa ta nufi bedroom ɗin shi kai tsaye, ta tura ƙopar kafin tasa kai Cikin ɗakin, Asaman gadon shi ta kwantar da angel, short gown ce ajikinta daga gani hada wanka aneelerh tayi mata ta kuma canza mata kayanta,ranƙwafawa ta ɗanyi daga tsaye tana shafa sumar kanta,


Jin motsin ƙopa yasa Aneelerh tayi saurin ɗagowa tare da juyawa bayanta don taga wanene, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Taj dake fitowa daga Cikin toilet,daga shi sai short a jikin shi,

Burki yaci lokacin da yayi arba da ita, duk tabi ta ruɗe a gigice ta watsa da gudu zata fuce daga ɗakin, Unfortunately ta take rigarta dake jan ƙasa, gaba ɗaya ta tafi zata kife kasa da hanzari Taj Yayi ƙwaƙƙwaran Taku Ya ruƙota, ta dawo jikinshi tana faman sauke ajiyar zuciya, taji tsoran faɗuwa ƙasa don ba ƙaramin buguwa za ta yi ba.

Sam ta manta Jikin wa take, ta ƙaƙameshi sosai, har sai da ya ɗanyi gyaran murya tukunna ta dawo hayyacinta, ta yi saurin raba jikinta daga na shi, duk kunya ta rufe kowannan su,

Daƙyar ya iya buɗe baki yayi mata magana
"Sai ka ce kin ga dodo, kawai daga gani na kin zabura zaki gudu, yanzu da kinji ciwo fa? so kike uzair Yasa a ɗaure ni ko"?
Murmushi ta ɗan saki ba tare da ta ce uffan ba, idanuwanta na akan yatsun hannunta,
"Thank u so much aneelerh, kina ɗawainiya da angel ɗina, tamkar mahaifiyarta, naso ace benazir tana da kyakkyawan hali irin

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads