Showing 210001 words to 213000 words out of 287659 words
Chapter 71 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
amma yana ji aranshi cewa wani abu yana faruwa badai badai ba, Shi bakomai yafi jimawa ba face ƴar uwar shi Gabriella, maganganun da angel tayi ɗazu akan tasu ƴar uwar sun tsara mishi aranshi.
A ƙalla ya ɗauki kusan minti talatin Yana tunani acikin toilet ɗin ba tare daya ta 6uka komai ba, Sai daga bisani ne ya soma ƙoƙarin cire rigarshi, Kwatsam idanuwanshi suka sauka akan Glass window ɗin nan, A wani slow yake kallonta sai yake ganin kamar glass ɗin jikinta bai zauna dakyau ba, nan take ranshi ya bashi cewar Yaje ya duba ya gani, wata'kil ma ya samu hanyar shiga Cikin kurkukun ko dan yaje ya ɗauko ƴar uwarshi, ba tare da yayi shawara da zuciyarshi ba, Ya fasa cire rigar ya nufi tagar, Yakai hannu ya tatta6a jikin glass ɗin Yaji yana girgiɗi, ya daddage ya zame shi daga jikin tagar ya sauke shi ƙasa, wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyarci, bakomai yake hange ba face fuskar sister ɗinshi.
Rashin sani yafi dare duhu, cike da ƙwarin gwiwa Gabriel ya dura tagar ya faɗo ta cikin wannan hanyar da angel ta tsinci kanta lokacin da ta ta6a durawa, hada saurin shi wurin miƙar hanyar, babu wadataccen haske, amma yana iya gani dakyau, yana kaiwa ƙarshenta, Ya faɗo cikin wannan babban filin mai ɗauke da dogayen benayen nan, A hankali yake ƙarewa ginin kallo, bai ta6a ganin wuri mai matuƙar ruɗarwa ba irin wannan wurin, hakanan ya dinga jin faɗuwar gaba, tun daga kan hauwa na farko har zuwa na biyu, a ƙarshe ya tsayar da idanuwanshi kan hawa na uku, ba zato ba tsammani idanuwanshi suka hango mashi kyakkyawar matashiyar budurwa tana gudun ceton rai saman hawa na uku, fara fat kamar fatalwa, Jikinta sanye da riga ja, wadda bata kai gwiwarta ba, fararen cinyoyinta santala santala, daga gani babu hankali atattare da ita, tana gudu tana waiwayon bayanta, ga uban gashin kanta dake yarfowa harta saman idanuwanta, hakan yasa ta dinga faɗuwa ƙasa tana miƙewa saboda bata ganin gabanta dakyau, wani irin tsorone ya ziyarci zuciyar Gabriel, Ganin tana saukowa daga saman benan mai hawa talatin, Girgiza kanshi ya dinga yi, zufa tako ina saman fuskarshi, Ya rasa gane shin mutunce ita ko aljan, ko kuma fatalwa ce, Idanuwanshi ne suka dinga nuna mashi kamar sister ɗinshi ce, sai dai akwai banbanci sosai, Ƴar uwarshi ba fara bace, kuma bata da tsayin sumar kai da yawa irin na wannan yarinyar, ' A tsorace ya juya zai koma hanyar daya fito, A lokacin harta ƙarasa saukowa saman benan, sai miƙa mishi hannu ta ke Yi, tana magana sautin muryarta sam baya fita, ranshi ne ya bashi cewar Ya juya ya kalle ta, ya ɗan dakata ya waiwayo baya yana kallonta, sai jan ƙafarta take yi, saboda nauyin da tayi mata, Taya zai iya yarda cewa mutunce ita? Bai gama yanke shawara da zuciyarshi ba, yaga ta faɗi ƙasa kanta ya bugu, ' Gaba ɗaya sumar kanta ta rufe mata fuskarta, Tsananin tausayinta ne ya kama gabriel, koma dai aljana ce wannan ba ƙaramin jiki taji ba, sai motsi take yi alamar tana son ɗagowa da kanta amma ta kasa, kuma duk da tana kwance ƙasa hakan baisa ta fasa miƙa mishi hannunta ba, yayi niyar yaje wurinta amma sai yaga Benayen dake awurin sun soma motsi suna yin sama da ƙasa, Ya zazaro ido ganin suna tunkaro shi, aiko da gudu ya juya ya bi ta hanyar daya fito Ko waiwaye babu ya koma bakin tagar nan, Allah ne ya taimake shi bai 6ace hanyar ba, Jiki na kerma ya haura tagar Ya dura Cikin toilet ɗinsu Yana ta haki, Sai da ya samu natsuwa tukunna yakai hannu ya ɗauki glass ɗin daya jingine jikin bango ya maida shi jikin tagar kamar yadda ya ganshi,
Kamar amafarki yake tariyo abubuwan da suka faru Cikin ƙanƙanin lokaci, zuciyarshi cike fal da tunanin matashiyar yarinyar nan daya gani .............."!
💋PRISONERS💋
Ya jima tsaye jikin tagar ba tare daya motsa ba, zuciyarshi na raya mashi akan ya koma ya taimake ta, sai dai tsoro ya hana shi yin hakan, Ajiyar zuciya ya sauke tare nufar cikin toilet ɗin, wankan ma da ya shigo da niyar yi ya fasa, ƙopa kawai ya buɗe ya fito ya shiga ɗakin su.
A zazzaune ya same su saman gadajen su, angel ce kaɗai kwance saman nata gadon da alama bacci ya ɗauke ta, tunda Gabriel ya shigo idanuwanshi na akan kowannan su, damuwace danƙare akan fuskokinsu, In ka cire mutun uku, Majnun da jamima da ke ta yin rawa tsakiyar ɗakin su, yau ta biye mishi suna wasa a tare, duk da a shekaru Majnun ya girmi Jamimah.
bayan su sai Sarah dake yanke akaifar hannunta da nail cutter ɗinsu, tana zaune saman shimfidarta dake a ƙasan gado, don ita tuni ta yafe hawa gado, komai nata a ƙasa take zama ta yi shi, Hankalin ta kwance babu damuwa akan fuskarta, Danish yana daga kishingiɗe saman bed ɗinsa, ya ɗan lumshe eyes ɗinta, sam babu walwala akan fuskar shi, Azeeza tana zaune saman gadon parveen, ta ɗaura kanta saman shoulder dinta, magana su ke yi ƙasa ƙasa a takaninsu, haris da deeja suna fuskantar juna, sun nutsa cikin tattaunarsu duk dai akan Batul ne, idan muka koma 6angaren su Hanna ita da hibba da Yasmin da eve da rubina kowaccensu na kwance saman gadonta, sun yi likimo kamar masu yin bacci, Zuciya ce ba daɗi, dole jiki yai sanyi, yar gida daddy kuwa bacci ta ke yi sai dai ga dukkan alamu babu lafiya ajikinta, kamar zata faɗo daga saman gadonta, a cikin bacci take murza cikinta da hannunta na dama, idanuwanta sun kumbura, ga sahun marin da Danish yai mata gefen fuskarta kamar jini ya kwanta.
Zuciyarshi a hautsine Ya ƙarasa gefen gadon shi ya zauna, Ya rasa wa zai tunkara game da zancen haura war shi taga, so yake ya sami wanda zai faɗa mawa, ko don su je su ɗauko yarinyar nan da ya gani, tabbas yana ji aranshi cewa mutun ce ita ba Aljana ba, shiyasa abun ya tsaya masa aranshi, gani yake kamar bai kyauta mata ba, yanzu da ace sister ɗin shi ce, acikin wannan mawuyacin halin bazai ta6a ƙyale ta ba, duk runtsi duk wuya sai ya taimake ta, but why ya gaza taimakon ita wannan yarinyar, girgiza kai ya ɗanyi kamar wanda aka zunguri bayanshi ya miƙe Ya cigaba da yin zarya cikin ɗakin nasu, Ji ya ke kamar ya je ya faɗa ma Danish sai dai yana matuƙar kokwanto a kan shi, Kuma yana ji aranshi zaiyi wuya ya bashi haɗin kai don su shiga cikin kurkukun.
To waye zai iya faɗa ma zancen nan? Nutsawa yae cikin tunaninshi, nan take zuciyarshi ta Amabaci sunan ANGEL, tunawa yai da lokacin data watsa ma Giants ruwa a jikin su tana zazzaga musu masifa, hakan yasa shi yarda cewa Yarinyar ba ƙaramar jaruma ba ce, bata da tsoro kuma tana da ƙwarin gwiwa, dama tun ranar da aka kawo su ya lura da yadda take tafiyar da rayuwarta da kuma ta ƴan uwanta tamkar itace ta haife su, ta zama jagora acikin su, kuma ya fahimci cewa yarinya ce ita bata kai shekarunsu Hanna ba, amma tafi su wayau da hankali.
Tun da ya fara zarya acikin ɗakin, su parveen su ke ta kallon shi, hatta Danish ya ankara dashi, kamar akwai wani abu dake damun shi, sam bai lura da kallon na shi da suke yi ba, A ƙarshe zuciyarshi ta saƙa mishi cewa
_Ita kaɗai ce zata Iya taimaka maka wurin nemo ƴar uwarka, tun da itama tana neman tasu ƴar uwar da aka ɗauke, Idan ku ka haɗa hannu da ita, za ku iya cimma nasara, don haka karka kuskura ka faɗama kowa, Ita kaɗai zaka sanar mawa_
Muryar Azeeza ce ta katse mishi zancen zucin mashi ta hanyar yi mishi magana
"Ɗan uwa, me ka ke tunani ne? Tun ɗazu na lura da kai sai zarya ka ke yi mana acikin ɗaki, nace anya lafiya kuwa" Murmushin yaƙe ya ƙaƙalo akan fuskarshi tare da juyar da kanshi Ya fuskanci inda azeeza take zaune ita da parveen. Kamar wasu tagwaye
"Ina tunanin rawar da zan koya ma ku ne ko ba ku so"? Ya faɗi hakan ne don kar su yi tunanin wani abun ne na daban ke damunsa.
Har suna haɗa baki wurin cewa"Muna so mana, dama zuciyar mu duk ba daɗi wlh, kwanakin nan mun rasa farin cikin mu"
"Kada ku ta6a bari damuwa ta hana ku jin daɗin rayuwar ku, saboda kowa yana da damar da zai sanya kan shi farin ciki, yawan zama kuna tunanin zai iya haddasa muku matsala, just ku yi abunda ranku ke so, zaku samu farin ciki" acewar Gabriel
Parveen tace"Angel tana koya mana yadda zamu motsa jiki, da karatu sannan tana bamu tarihi da labarin gidan daddynta, har ma ce mata tayi wata rana zata yi ƙoƙari don mu fita daga cikin kurkukun nan........." natsuwa gabriel yai a yayin da yake sauraran maganar parveen, da alama ya ƙara samun wani abu da yake son ji agame da angel, da sauri ya nufi gefen gadon dasu azeeza suke zaune, shima ya zauna.
"Inaso ku bani duk wani labari da angel ta baku agame da rayuwar ta, da kuma abubuwan da ta koya maku" Buɗe ido sosai Danish yai daga can saman gadon shi yake kallon bayan Gabriel dake zaune gefen su parveen, Mamaki ne ya kama shi for what reason Gabriel zai dinga yi musu tambayoyi kan angel! Menene alaƙar shi da ita? Why yake son ji"? Miƙewa zaune Danish yai saman mattress ɗin, ya jingina bayanshi jikin bango, ya tsare su da ido, Tabbas da ace yasan dalilin da yasa gabriel ya tambayi su azeeza su bashi labarin angel da ya dakatar shi.
Parveen ce ta labarta mishi komai game da angel, tun zuwanta kurkukun da irin ɗawainiyar da ta yi masu, har zuwa ranar da aka kawo su Gabriel cikin kurkukun.
Jinjina kai gabriel yai alamar ya gamsu da labarin da parveen ta bashi na angel,
Azeeza tace"mu taso ka koya mana rawar? Idon shi akan fuskarta yace"nafi so mu yi tare da angel, mu bari ta farka," su ka ce mi shi toh, zasu jira ta farka, Miƙewa Gabriel yae daga gefen gadon parveen, yana juyawa suka haɗa ido da Danish, ya ɗaure fuska, ta6e baki Gabriel yae tare da wuce wa Ya nufi nashi gadon ya zauna yana jiran farkawar Angel.
Lokacin da marece ya nutsa, suna zaune, Unaiza tafarka jikinta nata kerma hannayenta dafe da Cikinta, saukowa tai daga saman gadonta, da gudu ta nufi sashen toilet ɗinsu, har wani jiri take gani acikin idanuwanta, bayan ta shiga toilet ɗin agaban magudaji ta zuƙunna tana ƙwara amai, tamkar ƴan hanjin cikin ta zasu zazzago, temperature ɗin jikinta ya yi zafi sosai, tana acikin mawuyacin hali, an rasa me zuwa wurinta ya taimake ta.
Tun daga cikin sashen toilet ɗinsu har izuwa cikin ɗakin su, Sautin kakarin amanta ne Ya karaɗe ko'ina, Ya addabi kunnuwansu, ganin sunƙi motsawa suje su taimake ta, yasa azeeza ta sauko daga saman gadonta, parveen hada cewa"Zuwa za ki yi? Baki ji abunda angel tace mana akanta ba? Salon saita shanye maki jinin ki ko"? abunda suke jima tsoro kenan shiyasa suka ƙi zuwa su taimake ta, shi kuma Danish abunda ya hana shi zuwa wurinta gudun kada yabar ɗakin Gabriel ya samu damar zuwa wurin angel, saboda ya fahimci cewa so yake yayi magana da angel.
"Ai bata da lafiya, ba zata iya shan jini ba, ni dai zanje na taimake ta ne, kada ta mutu" azeeza ce tai maganar tare da kama hanya ta nufi sashen toilet dinsu, Cikin toilet ɗin da take jin sautin shesheƙar kukan Unaiza, ta buɗe ƙoparshi tasa kai ta shiga, A zuƙunne ta same ta, Baiwar Allah taji jiki, Cikinta ya ɗame dama bata ci abincinta ba, jikinta sai kerma yake yi.
Ƙarasawa gabanta Azeeza tayi fuskarta da alamun tausayinta ta zuƙunna suna fuskantar juna, bata ta6a tunanin wani daga cikinsu zaiji tausayinta ba har yazo wurinta sai ga azeeza tazo, daƙyar take kallonta saboda nauyin da idanuwanta su ka yi mata, sunyi luhu luhu da su kamar ƙwayar cikinsu zasu faɗo ƙasa launin idon nata ya ciza, la66anta sun yi suntum, sai nishi take yi tana matse cikinta.
"Sannu sister, baki da lafiya ne"? Bata samu damar amsa mata ba, azeeza ta kuma cewa"Pls talk to me, I wanna help you." Ganin taƙi tanka mata yasa azeeza ta Miƙewa tare da nufar inda bucket ɗinsu yake, ta tarba shi bakin fanfo ta kunna ruwa ya soma sauka acikinsa, Sai da yai rabi ta ja bokitin tana nishi don ba ƙaramin nauyi yayi mata ba, gefen unaiza ta ajiye bokitin, kafin ta karkatar dashi ruwan cikin ya kora aman da tayi dukan shi, Sauran da ya rage, ta taimaka mata wurin wanke fuskarta, ita kanta azeeza sai da gabanta ya faɗi jin irin zafin da jikin unaiza yae, lokacin da ta ke wanke mata fuskar da hannunta, kwata kwata babu ƙoshin lafiya atattare da ita, hada baki ta kuskure mata.
"Mu koma ɗaki, kinji" a wahalce ta ɗago da ido tana kallon azeeza ta ɗan girgiza mata kai, yayin da take cizon lower lip ɗinta, wani irin raɗaɗin azaba take ji.
"Pls ki yi min magana mana, ni inaso na taimake ki ne" runtse ido unaiza tayi na ɗan wani lokaci, azeeza har ta gaji da tsayuwa, ba dan tana jin tausayinta ba da tuni ta jima da komawa dakin su,
Tana so ta yi ma azeeza magana sai dai ta kasa motsa la66anta, jini har ya fara bleeding ta hancinta, ganin hakan yasa hankalin azeeza ya tashi, da gudu ta nufi cikin ɗakin su, a sukwane ta faɗo Ciki, Hankalinsu Naufal ya dawo kanta, muryarta har tana shaƙewa wurin faɗin"Ƴar gidan daddy bata da lafiya, Hancin ta yana bleeding, dan Allah ku zo ku taimake ta" Shiru su ka yi babu wanda ya tanka mata, duk da sun tsorata da jin abunda ta faɗi,
Ran azeeza ba ƙaramin 6aci yae ba, hawaye har sun fara wanke fuskarta, cikin ƙunar rai tace"wai ba zaku zo ku taimake ta ba"? Kamar kurame sai dai suka bi ta da ido, fuskarta a hautsine ta nufi gadon angel, tana bubbuga ƙafarta tana ambaton sunanta
"Angel wake up, ga ƴar gidan daddy can bata da lafiya, ina ta roƙon su akan su zo mu taimake ta amma sun ƙi saurarana"
tana kuka tana magana, Daƙyar ta samu Angel ta farka, tana faman yamutsa fuskarta da tayi jawur, saboda kukan da tasha, A hankali ta tsayar da idanuwanta kan fuskar azeeza dake ta kuka, Muryarta adisashe ta furta"meya faru ne"? Cikin shessheƙar kuka azeeza tace"Ƴar gidan daddy ce, tana acikin toilet bata da lafiya hada jini a hancinta, ina ta roƙonsu akan su zu su taimaketa amma sunƙi su saurare ni"
Ɗaya bayan ɗaya angel tabi kowannansu da kallo, ita Sarah bacci ne ya ɗauketa bayan ta gama yankar akaifar, amma sauran idonsu biyu, lokaci ɗaya ta fahimci dalilin dayasa suka ƙi zuwa su taimake ta, saboda tace musu ita mayyace, zata iya shanye musu jini, duk da ita ta yi hakan ne don ta sanya musu tsoronta acikin zuciyar su, gudun kada ta lalata musu rayuwa.
Saukowa Angel tayi daga saman gadonta, da sauri ta nufi sashen toilet ɗinsu azeeza tabi bayanta, Suna shiga Cikin toilet ɗin da Unaiza take suka same ta kwance ƙasa, idanuwanta sun juye, Hankalin angel ba ƙaramin tashi yai ba, zuƙunnawa tayi agabanta tare da sanya hannayenta biyu ta ruƙo kafaɗunta, ta ɗago da ita zuwa ƙirjinta, ta faɗa, nan take angel taji zafin da ke ajikin unaiza na fitar hayyaci, hatta nunfashinta da hucin zafi yake fita, ta rasa gane wani irin ciwo ne ke damunta, kamar hada zazza6i, raba jikin su tai daga na juna, ta sanya hannu ta tallabo fuskarta, muryarta na kerma tace"Unaiza meke damun ki? Wani irin ciwo ne wannan"? Biji biji ta ke kallon angel, duk da tana acikin mawuyacin hali, sai da tayi mamakin ganinta, don bata ta6a tsammanin wani daga cikinsu zai iya taimaka mata ba, motsi ta soma yi da la66anta, sunan allura ne take faɗa musu wadda ake yi mata agida, idan ciwon ya tashi, sai dai sun gaza fahimtar me take cewa, koda ace ma sun gane, basu da hanyar da zasu iya samo mata allurar,
"Azeeza ɗauko min mayafin nan na kayan mu," ta amsa mata da toh, ɗaki azeeza ta shiga ta ɗauko Cotton scarve ɗinta, ta dawo ta miƙa ma angel bayan ta kar6a, tace ma azeeza ta zauƙunna ta ruƙe unaiza ajikinta, a cikin bokiti Angel ta tsoma mayafin cikin sauran ruwan da azeeza ta kora aman unaiza, sai da ya jiƙa ta matse shi, ta ɗaura shi saman jikin unaiza, ta dinga goga mata shi, ta ko'ina, ta yi mata hakan ne don ta samu relief ɗin zafin jikin ta.
sai nishi take yi tana fitar da numfashi awahalce, duk in ta ɗaura mayafin ajikinta sai ta zabura, alamar bata son ruwan jikin mayafin na ta6a jikin ta, bayan ta kammala, ta miƙe taje bakin igiyar toilet ɗinsu ta shanya Mayafin, Kafin ta dawo ta sanya hannu biyu ta ruƙo unaiza ta miƙar da ita, jikin ta babu ƙwari, dama ba wata ƙibar kirki ke gareta ba, a haka taja ta zuwa cikin ɗakinsu,
Suna shiga ciki, idanuwansu Hanna suka dawo kansu, gadon unaiza angel ta wuce da ita, tare da kwantar da ita sama, ta juya ta nufi akwati nansu, ta buɗe ta ɗauko tissue ta koma saman gadon unaiza.
Dashi tai amfani wurin goge mata sauran jinin dake a hancinta, bayan ta kammala ta nannaɗe wanda ta goge jini da shi ta cusa su acikin wanda ta kuma yagowa, ta miƙa ma azeeza tace taje ta zuba a acikin trash can, ta amsa mata da toh, bayan ta kar6a ta juya ta nufi toilet dinsu, bada jimawa ba, Azeeza ta dawo ɗakin, gefen gadon unaiza ta koma ta zauna, ya kasance su biyu ne akusa da ita, jikinta ya ɗanyi sauƙi, ta ɗaura kanta saman pillow, still bata daina nishi ba, hannayenta na asaman mararta,