Showing 141001 words to 144000 words out of 287659 words
Chapter 48 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
cikin shessheƙar kuka tace"its me angle, am back, Giant ne ya dawo dani, na same ku kuna bacci, bana so na tashi kowa shiyasa nazo wurinki, saboda akwai abunda nake son faɗa miki," Tun da angel taji haka, Sai ta yaye bargon dake a jikinta, Ta kalli fuskar deeja da kyau, Gaba ɗaya ta zabge Duk ta bushe, janyota tayi zuwa jikinta ta rungumeta sosai, kamar zata maida ta cikin cikinta, Tayi matuƙar yin kewarta, Sun ɗauki tsawon lokaci, Kafin angel ta raba jikinta daga na deeja tace"Ki faɗa mini menene? Deeja tace"za'a iya jin mu idan muka Yi magana anan, amma zan shiga toitet, sai ki biyo ni" angel ta amsa mata da toh, Miƙewa deeja ta yi jiki duk ba ƙwari ta shige toilet, angel ta miƙe ta bi bayanta, bayan sun shiga, deeja ta sanya jamlock ta datse ƙopar, ta juyo suka fuskanci juna ita da angel,
"Faɗa mini menene kikeson Gaya mini? Duk na ƙagara inji" Cikin shessheƙar kuka deeja tace"Angel yanzu na ƙara yarda da maganarki na cewa ana cutar da rayuwar mu, wani iko na angel, Duk da bakomai zan iya tunawa ba, Amma lokacin da giant ya tafi dani, ina Cikin hayyacina, Inata karanta addu'ar nan da kika koya mana acikin zuciyata, Har yakai ni wani part inda wasu jerin daƙuna suke, Bayan ya shiga dani ɗaya daga cikin su, duhu ya mamaye idanuwana, ban iya ganin komai sai dai biji biji nake gani, Har lokacin ban fita hayyaci na ba, Sai dai bana iya gani da kyau, Naga mutun shida wanda ba baƙaƙen kaya bane ajikinsu kalar na giants, naga launin Ja a ƙugunsu, angel daga nan ne na fita hayyacina, bansan me akayi mani ba, Sai dai naji ajikina an cutar da rayuwata, nayi kukan mutuwa, Na azabtu iya azabtuwa, " Deeja nakai karshen maganarta, Ta zube saman gwiwowinta, tare da fashewa da matsanancin kuka, kamar ranta zai fita, Hankalin angel yayi matuƙar tashi, duk da bata ji me mutun shiddan nan suka Yi mata ba, amma tana ji aranta cewa Lalata suke yi dasu, idan har zata iya tunawa, can lokacin baya,Ta ta6a yunƙurin guduwa daga islamiya zata je gida, Tazo giftawa ta ofishin head master ɗinsu, Tajiyo shessheƙar kuka, da kuma maganganun mutane, duk da ƙarancin shekarunta a time ɗin tana dab da shiga 11 years, Har zata wuce ta la6e ta kasa kunne tana sauraronsu, ɗaya daga Cikin ɗaliban makarantar ne aka samu wani malami yayi ma fyaɗe ya kuma cigaba da lalata da yarinyar da bazata wuci shekara sha bakwai ba batare da sanin kowa ba, idan tazo islamiya aka tashi sai ya ɗauketa saman mashine ɗinshi zuwa gidanshi da ya gina da niyar yin aure, amma sai ya 6uge dakai yara yana 6ata musu rayuwa tare da yi musu barazana, Mahafiyar yarinyar ce ta fara lura da canzawarta, Bata iya tafiya ƙafafuwanta sun gwame, ga yawan yin amai, da su ka kaita asibiti likita ya tabbatar musu cewa ƴarsu Cikine da ita, iyayen yarinyar sun shiga damuwa, bayan sun baro asibiti sun dawo gida, mahaifiyar yarinyar ta ɗauko wuƙa ta ɗaura akan wuyan yarinyar tayi mata barazana akan ta faɗa musu wa yake yin lalata da ita har ta samu ciki, in ba haka ba zata kashe ta, atsananin tsorace yarinyar ta faɗa musu cewa malaninsu ne na islamiya, Koda jin haka sai suka tasa ƙeyarta gaba suka zo makarantar don su tabbatar da abunda ta faɗa musu, A lokacin angel bata fahimci komai ba, amma ta naɗi komai a acikin kanta, sai yanzu da Deeja ke faɗa mata wannan maganar ta soma tariyo abunda ya faru da ɗalibar nan ta makarantar islamiyarsu, duk da bata da tabbaci akan hakan amma tana zargin Suma lalatar ake yi dasu, ' Zuƙunnawa ta yi agaban deeja, Ta sanya hannayenta biyu ta rungumota ajikinta, Lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, itama deejan kuka take yi sosai, ta ƙanƙame angel da hannayenta, Abun da ciwo idan har ya tabbata cewa lalata ake yi dasu saboda rashin imani kuma a lokacin da suke Yi jinin al'ada, 😭😭😭
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Sun ɗauki tsawon lokaci rungume da juna suna ta kuka, Sai da suka yi mai isar su tukunna kowa Ya yi shiru, ba tare da sun raba jikinsu daga na juna ba, Muryar deeja a disashe tace"Na gaji da irin wannan rayuwar angel, bazan iya jure ganin ƴan uwana suna shan wahala ba, tun da ba yanzu suka fara ba, zasu ci gaba da zuwa suna ɗaukar mu ne ɗaya bayan ɗaya har sai sun ƙarar damu, nayi tunanin cewa gata ne ake nuna mana acikin kurkukun nan ashe ba haka bane, tsohuwa ta yi mana ƙarya da tace mana gidan marayu ne, za'a gatanta rayuwarmu, ta yaudare mu ta cuce mu, ba zamu ta6a yafe ma duk wanda yayi silar sadaukar damu zuwa cikin kurkukun nan ba......."
katse maganar ta yi, batare da ta kaiga ƙarasa ta ba, saboda wani irin ƙululun baƙin ciki da ya tokare mata maƙoshinta, Sai lokacin angel ta iya buɗe baki tace"Dama ni nasani tun farkon zuwana kurkukun nan na gane cewa Ba orphanage home bane, Tun daga kan sunanshi, shiyasa nayi ta ƙoƙarin in fahimtar daku, saboda ni nayi rayuwar ƴanci da hankalina da wayau na, sihirin tsohuwa tamira bai yi tasiri a Jikina ba, shiyasa Tunina bai gushe ba, dama taya za'ae Gidan marayu ya kasance Kurkuku? Kuma ba shige ba fuce, Abinci sau ɗaya arana! Uniform kala ɗaya, sai dai idan munyi wanka mu cire mu wanke mu maida a jikin mu? Ga shi babu wani mai kula damu, Rayuwa muke yi kara zube, wlh ko dabbobin dake garari acikin daji sun fi mu ƴan ci, koba komai zasu yawata inda suke so, Kai ni da irin rayuwar nan ma ƙwara mutuwa, saboda ɗaci ne da ita, rayuwar kulle, babu wanda zaiso ya kasance cikin irin wannan makauniyar rayuwar, Ai ko maƙiyi na bazan yi ma fatan shigarta ba....." Sai lokacin angel ta raba jikinta daga na deeja, Idanuwan kowannan su ya yi jawur saboda tsabar kukan da suka sha, Cikin karyayyiyar murya deeja tace"Ni bana Jin ma zanyi tsawaicin kwana, Gani nake kamar nice gawar fari acikin mu...." kafin ta karasa maganar angel ta yi saurin sanya tafin hannunta ta toshe mata baki, tana girgira kai, Hawaye na bin fuskarta tace"in sha Allah ba ke bace gawar fari, wlh bana Yi mana fatan mu rasa rayuwar mu acikin kurkukun nan, ina matuƙar so inga kuma kunyi rayuwa kamar kowa, Idan ma mutuwar ce na ƙwammace ni in fara yinta, saboda bazan Juri rashin wani acikin ku ba, bakisan yarda nake jinku ba, akan ku bana jin tausayin kaina, saboda ku ne abun tausayi" Daƙyar takai ƙarshen maganarta, hawayen deeja duk sun wanke hannunta data rufe mata baki dashi,
"Kowani ɗan adam da irin tashi ƙaddarar rayuwar, kowani bawa da irin ƙalubalan da yake fuskanta acikin rayuwarshi, Allah yana jarabtar bayin shi ba dan baya sonsu ba, face don ya jaraba imaninsu, babu wanda zaice maka 100% yana rayuwa Cikin jin daɗi, dole akwai ranakun farin ciki da kuma na baƙin Ciki, wani farkon rayuwarshi Jin daɗi ne, tsakiyar rayuwarshi wahala ce har zuwa ƙarshenta, wani kuma da farko zai ci baƙar wahala amma daga ƙarshe sai kaga Ya samu farin Ciki, Akwai wanda kuma Kaf rayuwar shi tun daga zuwanshi duniya Allah zai fara jarabtar shi, har zuwa ƙarshen rayuwar shi bazai ta6a jin daɗin duniya ba, zai fuskanci ƙalubale iri iri wanda idan Baida ƙarfin imani da tawakkali zai fidda rai da rahamar ubangiji ne, Zaiyi tunanin cewa ko Allah baiso na ne? At end har yakai ga tunanin salwantar da rayuwarshi don ya huta, wanda yin hakan kuma zai ƙara Jefa kanshi Cikin matsala ne, Kazo duniya a wahalce kuma ka koma a matsayin zero duka kayi asara, Amma idan kayi haƙuri ka miƙa lamurranka ga Allah subhana'hu wata'ala Koda baka ji daɗi anan ba, acan ana kyautata zaton zaka dace, akwai wanda kuma bai ta6a shan wahalar duniya ba, gatanci ta ko'ina, wahalarta kaɗan ya sani, in kaga 6acin ranshi to wani Ya rasa na kusa dashi, aduk halin da bawa ya tsinci kanshi Ya kasance mai godiyar Allah, Kafi wani, wani yafi ka, yanzu kamar rayuwar waɗannan bayin Allah, tunda suka zo duniya A garƙame suke kamar dabbobi, An tauye musu duk wani haƙƙinsu na rayuwa, basu son komai game da jin daɗin duniya ba, sun yi rayuwa acikin duhun jahilci, Basu son iyayensu ba, Basu son danginsu ba, su kansu basu Su wanene su ba, Haba jama'a, wannan rashin imanin har ina? A haka ake so su mutu su fuskanci mahaliccinsu, ai ƙwara wanda ke rayuwa acikin mutane yana fuskantar jarabawar rayuwa, Amma akwai imani azuciyarshi, Atlease Ya tsira da wannan idan yayi tawakkali, amma waɗannan bayin Allahn fa? Ba don zuwan angel acikin rayuwarsu ba da shikenan An kashe su da ransu an gama dasu, yakamata mu ƙara jin tsoron Allah acikin zukatanmu, mu kasance masu tawakkali, kuma mu kasance masu godiya ga Allah aduk halin da muka tsinci kanmu, tun da bamu rasa komai na rayuwa ba, ka kwana ka tashi da ranka da lafiyarka, ka je inda kake so, Ka ci mai kyau kasha mai kyau, ka sanya sutura mai kyau, kana a tare da iyayen ka ko babu su akwai danginka, kai idan ma babu dangin naka Allah Yana atare dakai, Zaka Iya rayuwa ko babu su, da daɗi da ba daɗi, Allah ya baka rai da lafiya, Amma sai kaga bawa yana Ƙorafi don ya rasa wani abu ƙalilan, ko angaza biya mashi buƙatarshi, dayawa gajan haƙuri kesa wasu harsu fara neman duniya ido rufe, Allah dai yasa mu dace, Shiyasa ake so mutun ya dinga ziyarta asibitoci da wuraren da faƙiran talakawa suke yin rayuwa, Kodan ya ƙara imani, Allah dai ya tsare mu ya kare mu daga faɗawa tarkon halaka, kada amanta adunga taya ƴan uwan mu addu'a waɗanda ke a hannun kidnappers da kuma ƴan boko haram, da matsafa, muna roƙon Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifar da muke fama da ita a ƙasarmu badan halin mu ba, Alfarmar Annabi muhammad (SAW) addu'a takobin mumini ce da ita ne kaɗai zamu Iya yaƙar su, tun da mu bamu da yadda zamuyi, waɗanda keda ikon Yin sun gaza, saboda rayuwar mu bata da mahimmanci awurinsu, takansu suke yi, wanda nayi imanin da ace yau hada ƴa'ƴansu aka ɗauka da anga tashin hankali, cikin ƴan awanni sai sun san yadda zasuyi an dawo musu dasu, Akwai dai ranar ƙin dillaci, ranar da dukiya ko ya'ya ko wani muƙami na duniya bazai amfane su da komai ba, A ranar zasu shaida cewa ALLAH ƊAYA NE.
A hankali angel ta zame hannunta daga saman bakin deeja,
"Deeja kodai in taimaka maki ki yi wanka? Naji jikin ki wani iri, daga gani baki jin daɗin shi" girgiza kai deeja tayi"a'a, bazan Iya yin wanka da ruwan sanyi ba, Jikina zai ƙara tsauri, ki barni kawai ahaka, " tsananin tausayinta ne ya ƙara kama angel.
"To Mu je mu kwanta, ko kin samu ki yi bacci ki huta" shiru deeja ta ɗan yi batare data amsa mata ba, har sai da angel ta ƙara maimaita mata, tukunna ta buɗe baki tace"bazan iya tashi ba, ki kije ki tada su daga bacci, ki faɗa musu cewa an dawo dani, su zo mu gaisa," maganar deeja ta yi matuƙar girgiza angel sai taga kamar bankwana ne take so ta yi dasu, muryarta na kerma tace"amma meyasa? Idan baki iya tafiya ne, ni sai in ɗauke ki abayana in kai ki cikin ɗakin ki kwanta, In yaso gobe da safe sai ku gaisa da su" idanuwan deeja a marairaice take kallon fuskar angel, da wata irin raunatacciyar murya tace"dan Allah ki kira mini su in gansu, kada na mutu batare da nayi tozali da ƴan uwana ba," girgiza kai angel tayi cikin shessheƙar kuka tace"In..sha.. Allah ba zaki mutu ba, har sai mun fita daga cikin kurkukun nan, Na roƙe ki ki daina Yi mini maganar mutuwa, kina karya mini zuciyata, Kinsa Jikina duk ya yi sanyi" hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskar deeja, idanuwanta sunyi jawur sosai, la66anta na kerma tace"dan Allah ki kira mini su mu gaisa, inaso inga ƴan uwana."
Juya mata baya angel ta yi tare da cewa"Ki hau in kai ki cikin ɗakin, Sai in tada maki su ku yi magana" fashewa deeja tayi da kuka tana faɗin"bana ce maki bazan Iya miƙewa ba, Kije ki kira mini su ko so kike saina mutu ne batare da nayi bankwana dasu ba"? Yanayin da tayi maganar yayi matuƙar girgiza angel, Hatta muryar deeja ta canza sosai, a ƙarshe ta sassauta muryarta tana yi mata magiya akan ta kira mata su, Muryar angel na rawa tace"shikenan ki jira dan Allah, yanzu zanje in tada su daga bacci kinji," Aruɗe ta yi maganar, ta miƙe da sauri tana tafiya tana waiwayon deeja, fargabarta kada ta mutu kafin ta dawo daga kiran nasu, bayan ta cire jamlock ɗin ƙopar da gudun gaske ta faɗo Cikin ɗakin har kusan tuntu6e ta yi, tun kafin ta ƙarasa cikin ɗakin ta dinga kwala musu kira, Haris danish, naufal hanna hibba batool yasmin ku tashi an dawo da deeja, da alama sunyi nauyin bacci babu wanda ya motsa, gaban gadajensu taje tana bubbuga ƙafafuwansu tare da cire musu bargunan da suka lullu6a dasu, Wannan karan muryarta da sauti mai ƙarfi take kwala musu kira, a matuƙar firgice kowannansu ya farka Yana faman Yin hama, Ba ta bari sun wartsake ba, tace musu"ku tashi muje toilet, deeja tana aciki, An dawo da ita, amma bata da ƙoshin lafiya, ita ce tace in kira mata ku, tana son ganinku" Jiki na rawa suka sauko daga saman gadajensu, Haris yafi kowa zumuɗi, shine agaba sai naufal da mubeen da danish, tare da javed, Matan kuma batool ce agaba sai su hanna hibba eve da su Parveen, Mutun ɗaya ce bata sauko daga saman gadonta ba, Azeeza amma ta farka tana ta kuka tana faɗin ita ba wanda zai kai ta wurin deeja, saboda anga bata da ido, har angel ta juya zata bi bayansu Batool sai kuma ta fasa jin muryar azeeza da sauri taje bakin gadonta ta ruƙo hannunta, tare da taimaka mata ta sauko daga saman gadonta, suka nufi toilet section ɗinsu, lokacin da kowannansu ya hallara acikin toilet ɗin da deeja take, hankalinsu Yayi matuƙar tashi, Ganin yadda jikinta ke ta kerma, wata irin zufa ce ke tsastsafo mata a jikinta, gaba ɗaya ta jiƙe sharkaf, a sukwane suka zuƙunna gabanta suka kewayeta, suna ambaton sunanta, hannu biyu haris ya sanya tare da tallabo fuskarta, daƙyar take iya buɗe idanuwanta da suka rune tana kallonsu, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin azabar da take ji ajikinta, muryar haris a ruɗe ya ambaci sunanta"deeja! ke ce kika koma haka? me ke damunki? kina iya ganinmu"? jinjina ma shi kai ta yi alamar eh, Azeeza dake ta kuka tana faɗin su nuna mata deeja, angel ta zuƙunnar da ita agaban deeja, Ta haɗa hannun azeeza dana deeja, Sosai deeja ta ƙanƙame hannun azeeza dake acikin nata, Cikin sanyin murya ta ambaci sunanta"Azeeza"! Amsa mata tayi"na'am, deeja ashe an dawo mana dake muna ta bacci bamu sani ba, Mun yi missing ɗinki sosai, " shafa fuskar azeeza ta yi da hannunta, nan take azeeza ta ɗan zabura tana faɗin"Zafi hannunki deeja, baki da lafiya ko"? Bata amsa mata ba, sai dai binsu da take yi da kallo, matsawa batool ta yi daga gefenta ta ɗaura hannunta saman wuyan deeja, da sauri ta zame shi, jin wani irin zafi na fitar hayyaci, hankalin ta ya yi matukar tashi tace"Yakamata mu kira tsohuwa ta duba jikinta, kwata kwata babu alamun lafiya atattare da ita" haris yace"me tsohuwa zata Iya yi mata? Ai kawai ku taimaka mata ta watsa ruwa ajikinta, zata ji sauƙi," girgiza kai batool ta yi tare da cewa"bazaka gane ba, kwara a kira ta, tun da ita tafi mu sanin meke damunta" Angel ta lura dasu kowa yana tofa albarkacin bakin shi, amma banda Danish tunda suka shigo ya zuƙunna na ɗan wani lokaci sai kuma taga ya miƙe ya jingina bayanshi jikin bangon da deeja take a zukunne, ya goya hannayen shi saman ƙirjinshi, ya ɗaga kanshi sama idanuwanshi na fuskantar ceilling, tsabar haushin shi ne ya kamata, shi da yake amatsayin babba acikinsu yaƙi buɗe baki ya yi magana, Koda lallashin deeja ne yayi duba da irin halin da take aciki,'
"Ko da ace kun kira tsohuwa, ba abunda zata Iya yi mini, nidai tunda na gan ku Alhamdulillah hakan ma ya wadatar" Deeja ce ta yi maganar, Hanna tace"pls ki tashi mu koma ɗaki ki kwanta," kallon hanna deeja ta yi, ƙarfin hali kawai take yi wurin yi musu magana"Ae bazan iya miƙewa ba, ƙafafuwana sun ruƙe," Juya mata baya haris yai tare da cewa"ki hau in goya ki, mu shiga" nan ma tace mishi bazata Iya motsawa ba,' lamarin yayi matuƙar girgiza su, jikinsu yayi mugun yin sanyi, Rubina tace"nidai zanje na kira tsohuwa ne" tana kai karshen maganarta, da sauri ta juya ta buɗe kopar toilet ɗin ta fuce, gudu gudu sauri sauri ta ƙarasa bakin ƙopar ɗakin tsohuwa, Tasa hannu ta kwankwasa ƙopar, kusan sau uku tana yin knocking, kafin ta samu tsohuwa ta buɗe mata ƙopar ɗakin, fitowa daga Ciki tayi hannunta ruƙe da sanda, ta ɗago da ido tana kallon rubina, Muryarta na rawa tace"dan Allah kizo ki taimaka mana an dawo da deeja amma jikinta babu sauƙi, ko iya miƙewa bata Yi," duƙar dakai ƙasa tsohuwa ta ɗanyi batare da tace komai ba, "dan Allah ki taimaka badan halinmu ba, kada mu rasa ƴar uwarmu," kafin tsohuwa ta ɗago da kanta sai ga su Javed da hibba hada yasmin sun fito daga Cikin sashen toilet dinsu, Hankalinsu duk atashe, ɗaya bayan ɗaya tsohuwa take binsu da kallo, Gaba ɗaya suka haɗa baki wurin yi mata