Header Ads
Showing 90001 words to 93000 words out of 287659 words

Chapter 31 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1803

Ads at the middle of Article

tayi, Juyawa tayi tare da komawa cikin toilet area ɗin, A bakin ƙopar toilet ɗin da yake aciki ta tsaya tare da kai hannu ta ruƙe handle ɗinta, Zurfin tunani ta shiga yi akan yadda zata samu Ta 6alle ƙopar, sam babu wani makami dazata yi amfani da shi, ƴan dabaru ta shiga yi na yadda zata 6alle ƙopar, Allah ne ya taimake Cikin sa'a, Sakatar ta saki, Ƙopar ta buɗe batare da tasha wahala ba, ajiyar zuciya ta sauke tare da tura ƙopa ta shiga ciki tana faman wurwurga idanuwanta, tun abakin kopar tayi arba da wandonshi yashe a ƙasa, ras! Taji gabanta ya faɗi, cigaba da tafiya tayi tana bin ƙasan da kallo, rigarshi ta gani a ƙasa itama ya yi wurgi da shi, tsayawa tayi a tsaye cike da fargabar halin da zata yi tozali dashi,

Yana acan Gefen tukunyar fulawar nan, anan ya zauna, daga inda take tana iya hangen fuskarshi, wuyanshi har zuwa ƙirjin shi, sai kuma ƙafafuwanshi daya zuro dasu ta ƙasa,
Ya lumshe idanuwanshi sai nishi yake yi tamkar wanda yasha gudu,

Muryarta na kerma ta ambaci sunanshi"DANISH"

buɗe idanuwanshi ya ɗanyi Sunyi jawur dasu daga gani yana acikin mawuyacin hali, jikin shi duk zufa ta wanke shi kamar wanda aka tsamo daga cikin kogon ruwa

Ta wutsiyar idonshi yake kallonta, juyawa tayi da sauri ta ɗauko mashi rigarshi da wandonshi,

Matsawa ta ɗanyi nesa da shi, yadda bazata iya ganin tsiraicin shi ba
Cikin sanyi murya tace"bansan me yake damunka ba, amma ina zargin kaina akan halin da ka ke ciki, dan Allah ka yafe mun ka yi haƙuri," har lokacin bai motsa lips ɗinsa ba, balle ta yi tsammanin zaiyi magana magana,

Miƙa mashi kayan shi tayi"dan Allah ka mayar da kayan ka, bazan so ƴan uwanka su ganka a haka ba, hankalin su ba a kwance ya ke ba, duk sun damu dakai"

Wurga mashi kayan tayi a saman fuskarshi suka sauka,
"Dan Allah ka sanya kayan ka," ta kuma maimaita mashi, cikin sigar lallashi,
Gani tayi ya runtse idanuwan shi sosai, ya ciccije soft lips ɗinshi duk ya fasa su, wata irin gigitacciyar ƙara ya saki,
Afirgice angel ke kallonshi, Su Batool dake acan cikin ɗakin Jin sautin ƙarar Danish Yasa suka Watso a guje, kafin su ƙaraso angel ta yi saurin juyawa zuwa bakin ƙopar ta datse ta,

Tana jiyo sautin bugun ƙopar da suke yi suna ambaton Sunan danish, tayi masu hakanne don bazata so sugan shi tsirara babu kaya ba,
Kafin ta dawo inda yake, tuni Yayi watsi da kayanshi data wurgo mashi, kwance ƙasa ta hangoshi sai burgima yake yi wannan karan hada hawaye akan fuskar shi lamarin ya yi matuƙar ɗaure mata kai, tana so ta taimaka mashi amma tana jin tsoron kallon tsiraicin shi
Rufe idanuwanta ta yi, amma bata rufe su sosai ba, tana gani biji biji a ahaka ta lalla6awa ta cigaba da tafiya zuwa inda yake kwance ta lalubo Wandonshi, ta soma kiciniyar mayar mashi a jikin shi, daƙyar ta samu ta zura mashi, Ajiyar zuciya ta saki tare da buɗe idanuwanta akan fuskarshi,

Sai faman nishi yake yi, idanuwanshi suna arufe, long eye lashes ɗin shi duk sun jiƙe,
calmly ta furta sunanshi"Danish are u ok"
Jin muryar angel acikin kewayan yasa suka gane cewa tana a ciki, sunyi mamaki yadda akai ta buɗe kopar, nan fa suka shiga kwala mata kira suna fadin ta bude masu ƙopa

Ɗaga murya ta yi tare da ce Masu Bazata buɗe ƙofar ba, saboda sun ƙala mata sharrin cewa itace silar jefa shi cikin halin da yake Ciki, don haka idan har sunga ta buɗe masu ƙopa, danish ya samu sauƙi ne"

Bugun ƙopar haris yake yi tamkar zai 6alleta" Bazaki zo ki buɗe mana ƙopar ba? a harzuƙe tace"Bazan buɗe ba,"
Sassauta murya haris ya yi"pls angel ki buɗe mana ƙopa, nasan bakya son danish kada kice zaki ƙarasa shi,"

Girgiza kai ta ɗanyi cike da jin takaicin maganar haris,

Tafin hannunta takai saman fuskar Danish ta shafa a hankali tare da ambaton sunanshi"Danish"

Dogon numfashi taga yaja gami dasauke ajiyar zuciya, yana so ya buɗe idanuwanshi amma ya kasa, sai lumshewa eyes ɗin nashi suke,

"Danish pls try to open ur eyes,"

Sama sama numfashinsa ke fita da hucin zafi, hannayenta ta sanya tare da tallabo kanshi ta ɗaura saman laps ɗinta,
Shafa gefen fuskarshi taci gaba dayi, yayin da ta soma karanto addu'o'i acikin zuciyarta, tana ɗan tottofa mashi saman fuskarshi,

Ba'a ɗauki tsawon lokaci ba, ya fara dawowa cikin hayyacin shi,

Lokacin dare ya fara yi, su biyu acikin toilet, ya yin da su batool ke zazzaune bakin ƙopar shiga toilet ɗin, sun galabaita har sun gaji da bugun ƙopar suna yi mata magiya akan ta bude masu, suga a wani hali ɗan uwansu yake ciki, wasu har sun fara gyangyaɗin bacci,
Itama angel ɗin baccin ta soma ji a cikin idanuwanta,
A lokacin da bata yi tsammani ba, taji ya ruƙo hannunta a cikin nashi sosai ya damƙe mata hannu, firgigit tayi tana kallon shi,
Lumshe idanuwanshi suke bai kaiga ƙarasa rufe su ba, He was calmly looking at her face without blinking his eyes,

Furta sunanshi tayi"danish" muryar shi so cool ya ambaci sunanta "angel" for the first time da danish ya ta6a ambaton sunanta,

"Are u ok,"? Ta kuma tambayarshi, bai amsa mata ba, ƙoƙarin miƙewa zaune yayi amma jikin nashi yaƙi bashi haɗin kai, da sauri ta taimaka mashi wurin tallabo shi ya miƙe zaune, tare da kwantar da kanshi saman kafadarta, still numfashin shi da huci yake fita, tana jin shi saman fatar wuyanta, saitin inda dogon hancin ya shafa,


*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*



Sam bata ji komai ba, daya kwantar da kanshi saman kafadarta, sai taji tamkar ɗan uwanta ne na jini, ƙurawa sumar kanshi ido tayi, doguwa har saman bayan shi, kamar ta sanya hannu ta shafa sumar haka zuciyarta ke raya mata,

'Pls angel open the door for us, mun ƙagara mu ga ɗan uwanmu," muryar hannah ce take yi mata magiya,
Hannu tasa ta dafa kafaɗar shi"danish suna son ganin ka, mu koma ɗaki," kusan minti biyar da yin maganar, ya ɗan dago da kan shi, still jikin shi ba kwari kerma yake yi,

Rarrafawa tayi ta ruƙo rigarshi ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a ya zurata ajikin shi, Sai da ta taimaka ma shi wurin ruƙo shi tukunna ya samu ya miƙe, a haka suka soma tafiya har suka ƙaraso bakin ƙofar ta buɗe ta fito da shi, gaba ɗaya suka miƙe tsaye zasu rungumo shi,

Da sauri batool ta ware hannayenta wurin kare shi"Jikin shi ba ƙwari, danish yana buƙatar hutu," A jiyar zuciya kowa ya sauke, wuce wa angel ta yi Cikin ɗakin, Su Batool suka Bi bayan su, ya rurruƙeta ji yake kamar zai faɗi ƙasa, wani irin jiri jiri yake gani a Cikin idanuwanshi, a saman gadonshi ta tsaya tare da taimaka mashi ya kwanta sama,

"Sannu danish, Allah ya baka lafiya," batool ce ta yi maganar, su haris ma duk su kayi mashi ya jiki, sam ya kasa amsa masu amma duk yana jinsu,

Sunyi tsaitsaye cirko ciko a gefen da gefen gadonshi, hasken ɗakin ya yi duhu, alamar dare yayi lokacin bacci ne, da sauri Javed yaje gaban table ya kunna masu sauran fitilun, ɗakin yayi haske ya ɗauko ɗaya daga Cikin fitilun ya ajiye ta daga gefen gadon Danish,

Motsin buɗe ƙofa suka jiyo, da sauri kowannan su Ya juyo yana jiran ganin wanene zai 6ullo daga saman benan

Biyu ne daga Cikin Giants dake kawo masu abinci, Abun mamaki ɗaya daga Cikin su hannun shi na ɗauke da wooden tray, samanshi an rufe da jan ƙyalle, da alama kayan abinci ne, ɗayan Giant ɗin kuma Syringe ne a hannun shi, already an zuba ruwan allurar a ciki,

Me ruƙe da syringe ɗin ne ya yi masu nuni da hannunshi su matsa su basu wuri, da sauri suka ja baya, me ruƙe da tray ɗin ya sauke shi ƙasa gefen gadon danish, Kafin ya matsa zuwa saman gadon, wata irin zabura danish ya yi, ya daddafe kanshi yana faɗin baya so kada su matso kusa da shi, ya dinga ambaton sunayen su haris yana faɗin ba zasu taimake shi ba? Suna ganin za'a cutar da shi,

Tsananin tsauyin shi ne ya kama su batool, idanuwan kowannan su ya ciko tab da kwalla,

Ruƙe shi sosai Giant ɗin ya yi, shi kuma ɗayan Ya daddage ya caka mashi allurar a wuyanshi, nan take jikin shi ya saki, ya sulale saman katifar idanuwanshi a rufe,

Sakin shi su ka yi, a tare suka juya cikin takun nan nasu, suka fuce daga cikin ɗakin,

Fitar su keda wuya Su hannah suka yi mashi rumfa suna ambaton Sunanshi, danish danish

Haris yace subar shi ya huta zai ji sauƙi tunda anyi mashi allura,

Angel tace"Wai kun yadda allurar magani ce su kayi ma shi? Meyasa danish yake kuka yana faɗin bayaso sai kace ƙaramin yaro? Kuma har yana faɗin mu taimake shi, u ave to think about it, ni sam ban yarda da waɗannam mutanan ba, Allah kaɗai yasan me su kayi ma shi"

Yatsina fuska deeja tayi cike da jin haushin angel ta soma magana"babu abunda su ka yi ma shi, tun da muke dasu basu ta6a cutar da wani daga cikin mu, koma meye kece kike da alhakin ciwon da.......' Bata kai ƙarshen maganarta ba, sakamakon naushin da angel ta sakar mata a saman fuskarta, tsabar raɗadi yasa Deeja ta dafe kuncinta,

"Ni kika buga"? Harara angel ta jefa mata"kaɗan kika gani, in har kika ci gaba da faɗin cewa ni ce silar da danish yake a wannan halin saina zubar maki da haƙoran gaba, wawuya kawai, don kinga kwanakin nan nayi sanyi shiyasa har kika samu damar gaya mun magana"

Ganin sun harzuƙa yasa javed yin saurin shiga tsakaninsu, cikin sanyin mirya yace" kodan saboda danish, kuyi haƙuri kuyi shiru," jinjina kai deeja ta yi"na ƙyale ki a yanzu, amma wlh saina rama naushin da ki kayi mun" Tsoki angel taja"duk lokacin da kika shirya nima a shirye nake, mai rabon shan duka,"

Daga haka su ka yi shiru, Can Haris ya hango parveen zuƙunne gaban Kayan abincin da aka kawo, sai faman shinshina su take yi, hannu yakai tare da ruƙo wuyan rigarta, ya ɗago da ita tsaye ta maƙe wuya

"Abincin Mara lafiya ne, Kada ma mutun ya sanya rai," harara parveen ta ɗan jafe mashi"Amma ae muna jin yunwa sosai, wannan dama ce a gare mu, kuzo kawai mu zauna muci mu ƙoshi, in yaso sai mu rage mashi kaɗan, bama lallai ya iya cin abincin ba"

Wani kallo Hannah tayi mata" ke fa dama indai kan abinci ne, Ba imani kika cika ba, Kinsan dai sau ɗaya ake kawo mana abinci, wannan kuma da kika ga an kawo na danish ne, ina ma laifin kice idan yaci ya ƙoshi ya rage sai muci kingin"?

Murmushin yaƙe parveen ta saki"Ae naga bacci yake yi, zamuyi ta jiran shi ne har saiya farka yaci ya rage tukunna muci"? ta yi tambayar tana ƙyafƙyafta ido, yadda tayi ba ƙaramin dariya ya basu ba,

Mubeen yace"Ni kaina yunwa nake ji, Don ba yadda zanyi ne Allah," yana rufe baki naufal yace"ae ba kai kaɗai ba, ina ɗazu ɗinnan da muka dinga bugun ƙopa, to anan duka abincin da muka ci ya zube,"

Murmushi haris ya ɗan saki tare da cewa"duk bala'in ku dai bazaku ta6a abincin ɗan uwana ba, har saiya ci ya rage" dariya su kayi gaba ɗayansu, da alama suna farin cikin dawowar ɗan uwansu,

Dare fa ya yi sosai, yakamata kowa yaje ya kwanta, acewar yasmin, juyawa su kayi kowa ya nufi gadonshi, Banda mutun ɗaya Parveen ta yi tsaye agaban gadon danish

Dawowa Haris ya yi tare da kai hannu ya ruƙo wuyan rigarta" muje ki kwanta" bubbuga ƙafa ta yi tare da cewa"Mara lafiya ne fa shi, taya zamu barshi shi kaɗai, Ni inaso Inyi jinyarshi ne",

"Saboda shi kaɗai ne a ɗakin ko"? Ya yi tambayar yana kallonta, shiru tayi tana faman tur6une fuska,

"Oya muje ki kwanta, sarkin wayau" ya ambaci hakan tare da janta, sai da yakai ta har saman gadonta, tukunna shima ya wuce nashi gadon ya kwanta,

Gaba ɗaya sun kasa runtsawa, bakomai suke jira ba, face farfaɗowar Danish,

"Kinyi bacci"? Muryar haris ce, yana daga kwance yayi maganar yana kallon Parveen dake a kwance saman gadon ta dake a kusa da nashi
"Taya zan iya bacci da ƙamshin abinci a hanci na," dariya haris yayi,

"Amma Haris baka ganin abincin zai iya lalace wa, tunda shi danish ba'asan lokacin da zai farka ba,"

"Calm down ur mind, tun da ki ka ga sun ajiye abincin nan, sunsan zai farka ne, Giants ne fa Sunsan me suke yi," sun jima suna tattaunawa, da haris before bacci yayi awon gaba da parveen,

Tsakiyar dare lokacin rabi da kwatarsu sunyi bacci, banda mutun ukun, Angel data ɗaurawa kanta alhakin ciwon danish, sai kuma Haris da yake na hannun damarshi, bayan su sai Batool, kowannansu yana kwance sunyi likimo tamkar masu yin bacci,

Ashe zuƙunne bata ƙare ba Kamar daga sama su ka ji danish ya fasa gigitacciyar ƙara mai matuƙar firgitarwa, farfaɗowarshi kenan, ya ta shi da wani sabon Ciwon, a matuƙar gigice angel ta yaye bargonta haris da batool duk suka cire bargunansu, hatta masu bacci sai da suka farka sakamakon Ƙarar danish data karaɗe Cikin ɗakin,

Gaba ɗaya hankalin su yae matuƙar tashi, ganin Danish Zaune saman gadonshi sai ƙara yake saki, ya daddafe kanshi da dukkan hannayenshi, tamkar wanda ake cikin zare ranshi saboda tsabar yarda yake fitar da sautin ƙarar har wani jijjiga muscles ɗin Jikin shi ke yi,

Durowa su ka yi daga saman gadajensu, jikinsu har kerma yake yi wurin tunkarar shi, Haris ne ya hau saman gadon, Javed da Mubeen hada naufal da sauran Ƴan matan duk Suna a tsaitsaye fuskokinsu da alamun ruɗu,

"Danish meya faru? meke damunka? dan Allah kayi mana bayani, " magana suke yi mashi amma sam baya sauraronsu ihu kawai yake yi, shi kaɗai yasan Raɗaɗin da yake ji bawan Allah,

"Bari naje na kira tsohuwa" Acewar Batool, juyawa ta yi da niyar taje ƙopar ɗakin tsohuwa, Angel tayi wuff ta ruƙo hannunta, tsayawa tayi tare da waigo wa ta kalli hannun angel da ta ruƙe ta, suka haɗa ido da juna"Ki jira akwai abunda nake so, in jaraba yi mashi idan bai ji sauƙi ba sai kije ki faɗa mata,". Rai a6ace haris yace"don me zaki hana ta zuwa ta kira ta? So kike mu rasa ɗan uwanmu? Baki ga halin da yake Ciki bane? Yana rufe baki Deeja tace"Da alama so take ta ƙarasa kashe shi, dama ni ban yarda da ita ba, ko me take da shi da zata iya taimakon shi?

angel bata tsaya sauraronsu ba. Kota kansu bata bi ba, batool ta kuma kallo tare da cewa"Ku bani dama," jinjina kai batool ta yi tare da kallon su haris tace"Tun da ta nemi alfarma, mu barta ta jaraba, amma kuma komai ya biyo baya, ke kija tun da kin hana a kira tsohuwa" gyaɗa kai angel ta yi, tare da matsawa ta haye saman gadon danish, ya kakkame Jikinshi sai kerma yake yi, yana sakin ihu ga zufa duk ta wanke jikin shi, duk da weather ɗin prison mai sanyi ce,

Miƙa hannu ta yi da niyar ta ruƙo shi, Ya buge hannun nata alamar baiso, duk yabi ya birkice masu,

Ganin yaƙi bata damar ruƙe shi yasa haris jan dogon tsoki tare da cewa"U just wanna waste our time, pls batool go and call her" tafiya batool ta soma yi ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa,

Rufe ido angel tayi, Cikin sanyin murya mai tattare da natsuwa da cikar kamala, ta soma raira qira'ar karatun alqur'ani mai girma,

Gaba ɗaya suka bita da kallo, sam basu san me take karantawa ba, amma tunda suke basu ta6a jin sautin abu mai daɗi ba, irin wanda angel take Rairawa ba, hatta batool dake ƙokarin kwankwasa ƙopar ɗakin tsohuwa, tana fara jiyo sautin karatun da angel keyi nan take ta dakata, tamkar an dasa mata aya, da matuƙar mamaki ta juyo tana kallon inda suke.

Bakomai yafi ɗaure masu kai ba, Fa ce yadda danish ya yi shiru, yadaina ihun da yake yi, kuma jikin shi ya daina yin kerma,

A hankali angel ta buɗe idanuwanta, ta ɗaurasu akan fuskar Danish still bai buɗe idanuwanshi ba, matasawa ta ƙarayi kusa dashi sosai, ta sanya hannayenta biyu tare da ruƙo doguwar sumar kanshi, ta tattare ta zuwa bayanshi, moving lips ɗinta ta yi xuwa saitin kunnanshi na dama, sosai taci gaba da raira mashi karatun har cikin kanshi yake jin wani irin baƙon yanayi mara misaltuwa, zuciyarshi tayi sanyi, kasala ta baibaye shi,
,
Haƙiƙa Angel tabar ƴan kallo, Su haris sun saki baki kamar lehen sakarai sai kallonta suke yi, ta kawo masu wani baƙon abu da basu ta6a ji ba,

He slowly wrapped his arms around her waist and squeezed her tightly tamkar zai shige cikinta, sai faman nishi yake yi yana fitar da numfashi da sauri da sauri, tana jin zafin jikin shi sosai ajikin nata, saboda matsewar da suka yi ajikin juna, tana jin yadda heart ɗinsa ke beating

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads