Showing 144001 words to 147000 words out of 287659 words
Chapter 49 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
magiya akan tazo ta duba jikin deeja bata da lafiya, duk sun ruɗe bayin Allah, Girgiza kai tsohuwa ta ɗanyi fuskarta babu yabo ba fallasa tace"Ni da bani da amfani awurin ku?me kuma zan Iya yi maku? Ita uwar ta ku bata iya duba mata jikin nata ne"? Duk sun gane akan wa take magana wato angel, hibba tace"pls ki taimaka mana mu dai, ki manta da komai kizo ki duba Jikinta, mun gane kuskuren mu, bazamu ƙara ba" suna kai karshen maganarsu gaba ɗaya suka zube saman gwiwowinsu, suna roƙonta, Da buɗar bakinta sai cewa ta yi"zan iya taimakon ku, bisa sharaɗi ɗaya"! A ƙagare suka tambayeta menene tace"Su je su kira babarsu angel, tazo ta durƙusa agabanta ta roƙe ta, idan har ta yi hakan ita kuma zata duba lafiyar deejan su," da sauri suka miƙe da gudu suka nufi cikin toilet ɗin, a lokacin Deeja tana kwance saman ƙirjin haris, ya ƙanƙameta da hannayenshi, su angel duk suna a kewaye da ita, banda Maji daɗin gado daya ke atsaye kamar gunki, Yadda suka banko ƙopar toilet ɗinne yaja hankalinsu angel zuwa ga kallonsu, a fujajen suka faɗo, kusan atare suka haɗa murya wurin cewa"Ki zo angel, tsohuwa tace zata duba jikin deejan mu, amma dole sai kin durƙusa agabanta kin roƙe ta," Waro ido waje angel ta yi bakinta asake galala take kallonsu, lallai wannan tsohuwar ta ɗauko ta da zafi, taya zata ce saita durƙusa mata sannan zata duba lafiyar deeja? Mamaki ya hana ta motsa, magiya su javed suka dinga yi mata akan tazo suje ta duƙama tsohuwa, ko sun samu ta duba Jikin deeja" kasa tanka musu ta yi, Har saida batool tace"Angel ki taimaka ma rayuwar deeja, dan Allah badan halin mu ba, Kije ki roƙeta, wannan ce kaɗai damar da muke da ita, idan ba haka ba, deeja zata Iya mutuwa ki kalli yadda jikinta keta kerma yana zufa, duk ta fita hayyacinta" Batool na rufe baki azeeza ta fashe da kuka tana faɗin"Dan Allah angel kije kada mu rasa deejan mu, muna son ƴar uwar mu," ɗaya bayan ɗaya angel take kallonsu, a karshen ta tsayar da idanuwanta kan fuskar deeja dake kwance saman kirjin haris, la66anta sai kerma suke Yi, " ganin zata 6ata musu lokaci yasa suka nannaɗe hannuwan rigunansu, batayi wani aune ba, taji sun sunkuceta gaba ɗaya suka cuccu6ota suka juya da ita zuwa cikin ɗakin, tana ta kiciniyar ƙwace kanta amma sunƙi bari ta kubce musu, a haka suka shigo da ita cikin ɗakin, Tsohuwa na ganinsu ta saki wani irin bazawarin murmushi, dama tasan taurin kan angel da kafiyarta baza su ta6a bari ta tako da ƙafafunta zuwa gabanta ba, su javed na ƙarasowa inda tsohuwa take a tsaye suka saki angel ta faɗi ƙasa, Idon tsohuwa na akanta, ɗagowa ta yi fuskarta a hargitse, saboda tsabar masifa ta rufe idanuwanta tana zazzaga masu masifa tana faɗin don me zasu je su ɗauko ta? Ita fa bazata ta6a duƙama wannan tsohuwar najadun ba, mai kafirar zuciya wadda batasan Allah ba, 'ta inda take shiga bata nan take fita ba, Hankalinsu Rubina ya ƙara tashi ganin tana ƙoƙarin 6ata musu lokaci, ga deeja can tana jin jiki ita kuma da suka ɗauko donta taimaka masu gashi tazo tana ƙara Kwafsa musu, Zuƙunnawa su ka yi gaba ɗayansu saman gwiwowinsu suna roƙon angel akan ta taimake su badan su zata yi ba, ta dubi girman Allah ta roƙi tsohuwa taje ta duba lafiyar deejansu, " tsananin tausayinsu ne ya kama angel ganin hada hawaye akan fuskokinsu, saboda tsabar jaraba da jin takaici ta fashe da kuka tana faɗin"wayyo Allah na na shiga uku, yau zan aikata babban zunubi arayuwata, wlh na tsane ki kamar mutuwa ta, bansan ganinki, muguwa azzaluma, mai zuciya irinta kafiran farko, ke daga ganinki kin hada iri da jinsin fir'auna, saboda rashin imani taimakon ne bazaki iya yi mana ba, dole saina roƙe ki....." Bata ƙarasa maganar ba, yasmin ta sanya hannu biyu ta toshe mata baki, Cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah angel kidaina, idan baxaki Iya ceton ran ƴar uwarmu ba, bai kamata kina ƙara fusata tsohuwa ba, so kike ta fasa taimakon mu" A tsiyace angel ta buge hannun yasmin data toshe mata baki dashi, idanuwanta sun yi jawur tamkar garwashin wuta, kallon kallon suka shiga yi ita da tsohuwa,
"Lokaci Yana ƙure maki, idan har kika bari na juya na dogara sandata na koma Cikin ɗakina, To ku fidda rai da zan sake fitowa, wannan ce kaɗai damar da kuke da ita" tsohuwace tayi maganar, fuskarta ɗauke da shu'umin murmushi, mai nuna tsantsar farin Ciki, bata ta6a jin nishaɗi ba irin na yau, a hankali angel ta kawar da idonta daga kan fuskar tsohuwa ta mayar dasu kan fuskokinsu Javed da yasmin da hibba dake a zuƙunne saman gwiwowinsu, fuskarsu sharkaf da hawaye, gyaɗa kai kawai tayi Jiki ba kwari ta maida idonta ga tsohuwa, murya na kerma tace"zan roƙe ki ne bada son raina ba, dan haka kada ki yi tunanin kin ƙasƙantar dani ne, zanyi ne saboda waɗannan bayin Allahn, da kuma ƴar uwata dake acikin mawuyacin hali, Sannan kada ki yi tunanin kece zaki bata lafiya, Allah subhanahu wata'ala shine ya baki ikon yin hakan, domin kuwa saida yardar shi ne komai yake wakana" daƙyar takai karshen maganar ganin tsohuwa na ƙoƙarin juyawa ta koma Cikin ɗakinta, aikuwa da sauri angel ta ɗago ta zuƙunna saman gwiwowinta, Muryarta a disashe tace"Na roƙe ki dan Allah badan Ni ba, kije ki duba lafiyar Deeja" Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta fashe da ita, tamoji tamojin fuskarta har rawa suke yi, saboda tsabar yarda jikinta ke jijjiga, Angel kuwa wani irin ƙululun baƙin Cikine ya Turniƙe zuciyarta, har wani zazza6i taji ajikinta, Kusan atare su javed suka sauke ajiyar zuciya, saboda tsabar mugunta saida tsohuwa tasa angel ta maimaita maganar da tayi kusan sau uku tukunna tace"hakan ya yi mini, haƙiƙa yau na shaida irin ƙaunar da kike yi musu, ke ɗin uwace ta gari agare su, Ina ji araina cewa nan gaba har rayuwarki zaki Iya sadaukarwa akansu, don ba ƙaramin mamaki nayi ba ganin irin yadda kika sauke duk wani girman kai naki da kafiyarki wurin roƙo na akan lafiyar ƴarki deeja, Naji daɗi sosai Albarka zata tabbata akanki, ni kuma yau ta kasance ranar tarihi arayuwata, wato ranar da the most arrogant young lady in the world ta zuƙunna saman gwiwowinta domin ta roƙe ni......"Tsohuwa bata karasa maganarta ba, muryar angel Cikin fushi tace"Kinga surutun ya isa haka, tunda nayi maki abunda kike so, kema saiki biya ni" cike da shaƙiyanci tsohuwa tace"To gimbiya sarautar mata, Ai ko me kike so yau zanyi maki shi" Harara angel ta watsa mata kamar kwayar idanuwanta zasu faɗo kasa,
Juyawa tsohuwa tayi zata koma cikin ɗakinta, muryar javed ta katse ta"deeja fa? Naga zaki koma Cikin ɗaki" batare da ta juyo ta kalle shi ba tace"Ku jira ni yanzu zan fito," Tsayawa su kayi suna jiran ta, Badajimawa ba sai ga tsohuwa ta fito hannunta ɗaya ruƙe da gorar ruwa ta gargajiya, miƙa ma javed tayi"Ruƙe mun nan, Mu je ciki ka nuna mini ita" da sauri javed ya sanya hannu biyu ya kar6i gorar ruwan, Suka shiga gaba tabi bayansu, angel dai bata bi su ba, A nan ƙasa ta kwanta zuciyarta na tafarfasa, Ji take yau ta bata kanta, tun da harta durƙusawa tsohuwa,
Lokacin da suka shiga Cikin toilet ɗin, Tsohuwa ta basu umarnin su fita waje su jirata, haris dai bai yarda da ita ba, ya ƙyaleta ne kawai yaga iya gudun ruwanta, ɗaya bayan ɗaya suka fuce daga Cikin toilet ɗin, kafin javed ya fita sai da ya fara ajiye mata gorar ruwan a kasa, Tukunna yasa kai ya fuce, Cikin ɗakinsu suka koma Kowa zuciyarshi cike da zullumi, daga Cikin toilet ɗin suka soma Jin kukan deeja yadda kasan ana zare ranta, hankalinsu yai matuƙar tashi, gaba ɗaya suka gaza jurewa, Komawa su kayi Cikin sashen toilet, Koda suka je bakin ƙopar toilet ɗin a datse suka same shi, A dole suka zauna ƙasa zaman jiran fitowar tsohuwa, danish dai yana acikin ɗakinsu, bai bi bayansu ba, Saman gadonshi ya koma ya zauna, yana satar kallon angel dake kwance a ƙasa, Yana so yaje ya lallashe ta amma yana tsoron masifarta, don kuwa yau sai Allah, Taci ka ta batse, jira take kawai ta samu wanda zata huce haushinta akanshi,' wannan dalilin ne ya hana shi tunkararta, gudun kada yasha mari,
Yau fa babu bacci, Dare ya koma musu tamkar rana, azeeza ce kaɗai take gyangyaɗin bacci, tana atsakankanin Batool da naufal, ta ɗan ɗaura kanta saman kafadar batool, ga dukkan alamu bacci take so ta yi, Naufal ne ya lura da ita, ruƙo hannunta yayi acikin nashi yace"azeeza tashi muje in raka ki cikin ɗaki ki kwanta, kada ki yi bacci anan" maƙe mashi kafaɗa tayi muryarta adisashe tace"ba yanzu zan kwanta ba, sai na jira an fito da deeja" Haris dake sauraronsu yace"naufal, Kada ka biye mata, pls ka ɗauke ta, ka kaita cikin ɗaki," rigima ta sanya musu, akan ita bazata je ta kwanta ba, sai ta ga deeja" Naufal bai tsaya sauraronta ba, ya sanya hannayenshi biyu ya sa6e ta, kamar wata ƴar baby haka ya ruƙota ya nufi Cikin ɗakin da ita, A saman gadonta ya kwantar da ita, tare da janyo bargonta dake a nannaɗe ya lullu6e mata jikinta, sai gashi ta yi shiru alamar bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya naufal ya sauke sai da ya fara ɗagowa ya kalli danish dake kishingiɗe saman gadonshi, Ya kuma kallon angel dake kwance a ƙasa, Ya ɗan girgiza kai, kafin Ya juya ya nufi Cikin sashen toilet ɗin, Lokacin da naufal ya shiga Ciki, Ya yi dai dai da buɗe ƙopar toilet da tsohuwa ta yi, aikuwa Jikinsu har 6ari yake yi wurin miƙewa tsaye idon kowa akan Ta, fitowa tayi hannunta ruƙe da sanda, Ta ɗago ta kallesu tace"Ina babar taku take Ne"? Suka haɗa baki wurin cewa"Tana acikin ɗaki" tsohuwa tace"Ku je kuce mata ta ɗauko bargo tazo, ta ɗauki diyarta, " amsa mata suka Yi da toh, Batool ce taje cikin ɗakin ta isar da saƙon zuwa ga angel, atare suka dawo hannun angel ruƙe da bargo, fuskarta a kumbure take hararar tsohuwa,
Matsa mata Hanya tsohuwa tayi"Ki shiga Ki lullu6a mata shi ajikinta, ki fito da ita, " batare da ta amsa mata ba ta nufi ƙopar toilet ɗin ta shige Ciki, tsohuwa ta kalli javed tare da cewa"idan sun fito ka ɗauko mini gorar ruwan nan, ka biyo ni da ita" ya amsa mata da toh,'. Har ta fara tafiya ta dan juyo tana kallon fuskokinsu tace"Yakamata kuje ku kwanta, duk da ma naga kamar Lokacin ya ƙure garin ya waye" bata rufe baki ba, sai ga hasken ɗakin su Ya gauraye ko'ina, sun yi matuƙar yin mamaki, maganar tsohuwa ta tabbata, har gari ya waye basu sani ba, Atare suka haɗa baki wurin yi mata godiya, bata amsa musu ba sai cewa tayi"bani yakamata ku yi ma godiya ba, Babarku ce ta cancanci hakan," Fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar, tare da juyawa ta fuce daga cikin sashen toilet ɗin ta nufi dakinta,
Fitar tsohuwa keda wuya, Sai ga angel ta fito hannunta ɗaya talla6e da deeja, da alama hada wanka tsohuwa tayi mata, uniform dinta na sanye a jikinta, Daga sama kuma bargon da angel ta lullu6a mata ne," wani irin farin Ciki ne Ya lullu6esu, Ganin ƴar uwarsu ta wartsake har tana iya taka kafarta, Sai faman sauke ajiyar zuciya suke Yi, wuce wa gaba angel ta yi suka bi bayansu, a bakin gadon deeja suka tsaitsaya, angel ta taimaka mata ta kwantar da ita saman gadonta, muryar deeja na ɗan kerma tace"Sanyi nake ji, ku ƙara mun wasu bargunan akaina, Ko jikina ya yi ɗumi," Da sauri kowannan su ya nufi gadon shi suka ɗauko bargunansu suka lullu6a mata ajikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci bacci ya yi awon gaba da ita, duƙawa angel tayi agaban gadon deeja daga gefe, ta soma karanto addu'o'i tana tottofa mata, bayan ta kammala ta ɗago da idanuwanta ta kalli su Batool dake a kewaye da ita, tace dasu suyi mata addu'a suma, kowa ya ɗan zuƙunno da kanshi saitin gadon, suka karanta abun da taɗan koya musu suka tofa mata, daga bisani haris yace dasu, Su koma su kwanta, ganin jiya basu samu isasshen bacci ba, ba musu suka amsa mashi da toh, kowannan su Ya wuce saman gadon shi, suka kwakkwanta, Ya rage saura haris dake a tsaye sai angel dake zuƙunne agaban gadon deeja, wuri ya samu gefen gadon deeja ya zauna, ba laifi yanzu hankalin shi ya ɗan kwanta, kallon angel yae tare da cewa"Ke fa? Baki jin bacci"? daƙyar ta iya ɗago da ido ta kalle shi, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta, maganganun da deeja ta faɗa mata sune suke ta yi mata yawo a cikin kanta,
"Dake nake magana" muryar haris ce ta kuma katse ta, batare data amsa mashi ba, ta yunƙura ta miƙe ta nufi gadonta, tana isa ta haye sama ta kwanta, koda suka haɗa ido da danish dake kishingiɗe saman gadon shi, harara ta watsa mashi, kafin ta juya mashi baya, lumshe idanuwanshi yayi, zuciyarshi duk ba daɗi, saboda ya gane dalilin dayasa ta harare shi, dole taji haushin shi, saboda rashin ta6uka komai, shi kuma aganinshi indai baida maganin abu to baida amfani ya tsoma baki, shiyasa yake yin shiru, Amma har ga Allah yana matuƙar damuwa dasu, Yana jin tausayin ƴan uwanshi, Yana matuƙar ƙaunarsu fiye da kan shi,
Rabi da kwatarsu tuni bacci Ya yi awon gaba dasu, mutun uku ne suka rage, Haris da tuni ya jima da komawa saman gadonshi, damuwar halin da deeja ke aciki ce ta hana shi runtsawa, Sai kuma Parveen da Yunwa ta addabe ta, ta lafe kwance saman gadonta sai juyi take yi, bayan ita kuma sai Angel wadda babu alamun zata runtsa, ita fa babban abunda ke damunta, irin takurawa rayuwarsu da ake yi, da kuma cutar dasu da ake yi, tana matuƙar jin tsoran tarasa wani acikinsu, tabbas zata ji raɗaɗin da yafi wanda taji a lokacin da ƙaddara ta rabata da daddynta, a yanzu tafi jinsu acikin zuciyarta fiye da kowa ma nata, yanzu bakomai yafi tsaya mata arai ba, face mutun shiddan nan da Deeja ta faɗa mata cewa ta gansu akanta, Shin su wanene su? Uban me suka aikata mata? Kodai su duka suka afka mata a lokaci ɗaya suka lalata rayuwarta? Innallahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma Ajirni fil musibati...... wani irin ɗaci take ji acikin zuciyarta, idanuwanta suka cuccuko tab da ƙwalla, ta tausaya ma rayuwarsu, Idan har suka cigaba da kasancewa acikin kurkukun nan tabbas kuwa wata rana za'a nemi koda gawawwakinsu ne arasa, Ita dai bata fatan tarasa ranta acikinsa, kodan saboda ta gano su wanene suka assasa ƙungiyar da kuma waɗanda suka sadaukar dasu, Wannan alƙawarine ta ɗaukarwa kanta, sai sun ɗanɗani kuɗarsu, sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwarsu ta yi acikin duniyar nan!!! Acikin zancen zucin da take yi, kwata kwata bata sanya tsohuwa aciki ba, duk da itama taji haushin abunda tayi mata ayau, amma ta ajiyeta gefe ɗaya, saboda ba ita bace agabanta, masu ƙungiyar kurkukun ƙaddara sune agabanta, da kuma waɗanda suka yi sacrificing ɗinsu.
Lokacin da giants suka shigo kawo musu abinci, Mutun ɗaya ce ta Iya miƙewa, har zata tada su daga bacci, Haris yace ta ƙyalesu, taje ƙarƙashin gadon batool ta ɗauko kwandon da suke ajiye abinci, ta kwaso musu aciki, idan suka farka zasu Ci, ta amsa mashi da toh, Bayan ta ɗauko food basket ɗin taje gaban jerin farantan da giants suka sauke musu, Ta zuƙunna ta ajiye kwandon gefe, ta sanya hannu ta yaye jan ƙyallen dake akan farantin farko, Steak and onions ne, Yankan nama manya manya sunji albasa da kayan ƙamshi, Hannu tasa ta dinga ɗebowa tana zubawa cikin kwandon, duka ta kwashe, Ta kuma buɗe faranti na biyu dake ɗauke da Snacks tare da madaidaicin bowl Na kayan marmari ta kwashe komai ta ɗaura akan naman, Faranti na ƙarshe Bottles waters ne, Miƙewa tayi tare da sanya hannu biyu ta ɗauke kwandon, Yayi nauyi, A agaban gadonta ta ajiye shi, ta koma domin kwaso robobin ruwa, dake a jere saman faranti na ƙarshe, Ta ruƙo su a hannayenta, Bayan ta kammala giants dake a tsaye suka raƙwafa atare suka ɗauke farantan, Tare da kama hanya suka fuce daga Cikin ɗakin, Zama parveen tayi agaban gadonta, ta ɗago ta kalli haris dake kallonta tace"Ba yanzu zaka Ci ba? Yana daga kwance saman gadonshi, Yace mata"sai sun farka zai ci" tace"Nima in jira sai sun farka"? Ba don taso ba ta faɗi hakan, Girgiza mata kai yai alamar a'a kafin yace"zaki iya ci mana, kici iya cinki, sauran da kika rage sai muci, ae nasan duk haɗamarki ba zaki iya lamushe abincin duka ba, ko rabi ma ba zaki iya tadawa ba" murmushine ya bayyana akan fuskar Parveen, jin abunda yace, bata ƙara tanka mashi ba, takai hannu tana zakulo naman tana turawa abaki, Sai da taci iya cinta, ta haɗa da snacks ɗin duka, har saida cikinta yayi ƙato, tukunna ta dakata da ci tana faman shafa ciki, bottle water ta ɗauka ta buɗe tasha ruwan, Data kammala ta tura kwandon ƙarƙashin gadonta, Haris yace"Salon da anjima idan kinga muna cin namu, kice kema zaki ci," dariya ta ɗanyi har dimple ɗinta na saman chin ɗinta ya lotsa, komawa saman gadonta ta yi tare da hayewa, da niyar itama ta samu baccin ya ɗauke ta,
Basu suka tashi farkawa ba, sai da suka kwashe tsawon awanni suna bacci, daga bisani yunwa ta fara farkar dasu, ɗaya bayan ɗaya, kowa ya miƙe yana hamma, Haris yace suje su wanko bakinsu suzo suci abinci, Suka amsa mashi da toh, Kowa ya nufi toilet, bayan sun kammala wanke fuskokin suka zo suka zazzauna ya dauko