Showing 243001 words to 246000 words out of 287659 words
Chapter 82 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
ta yi dab da ita, ta ɗan zuƙunna saman ƙafafuwanta, tare da ɗaura hannayenta biyu saman kafaɗar jamima ta juyo da ita, suna facing ɗin juna
Sassauta muryarta tayi Cikin sigar lallashi tace"its okey my little sis, stop crying, bakisan cewa hawayenki, tsada ne dasu ba, " zumbura mata ƙaramin bakinta ta yi, fuskarnan a tur6une, har wani hura hanci ta ke yi, shafa gefen fuskarta Angel ta yi da hannunta,
"Ƴar kyakkyawa da ke kamar Azeeza ta, idan muka fita daga cikin kurkukun nan, zamuje gidan daddyna, akwai suturar sanyawata da daddyna ya siya min tun ina ƴar ƙarama, nasan zasu yi maki, bayan haka ina da kayan wasa, irinsu teddy nasan baki san su ba, hada piano ɗina, duk zan baki su, sannan in sanya ki makaranta, kema ki yi karatu, kamar yarda sauran yara su ke yi, ko baki so" ta6e baki tayi don ita bata fahimci zancenta ba, amma taji an ambaci kayan wasa, Ɗaga mata gira tai"ina so," mirmushi Angel ta saki"amma fa sai mun shirya," hura hanci ta yi, tare da cewa "Ae mun shirya" dariya Angel ta saki, Tare da janyota jikinta, ta rungumeta sosai, kafin ta raba jikin su.
Wanka ta yi mata a cikin toilet ɗin, ta kuma wanke mata gashin kanta, bayan ta gama ta goyota saman bayanta,
Suna shiga cikin ɗakin, su parveen suka dinga sowa suna tafa musu hannu, Ganin sun shirya da juna, ba ƙaramin daɗi su ka ji ba, A saman gadonta ta zaunar da ita, ta ɗauko comb ta sharce mata sumar kanta, bayan ta gama, Kalaba ta yi mata guda biyu, sun sauko gefe da gefen kafaɗarta, ta zura mata ribbon ɗinta jikin wutsiyar kalaba ɗaya, ba ƙaramin kyau ta yi ba.
Lokacin da marece ya nutsa kingin abincin su na safe da su ka ajiye, Hannah ta ɗauko musu, asaman dining carpet ɗinsu suka zazzauna, Suna ci saboda gatanci abaki Angel ta dinga ba jamimah, ran azeeza ya 6aci musamman da ta dinga yi mata gwalo, yarinyar ta rainata, kishi ya rufeta, ganin yadda azeeza ke ɗaure fuskarta, yasa Angel ta koma tana basu abincin su biyu ita da Jamima, idan ta basu abaki su ka ci, itama sai taci, a haka har suka kammala.
Saman gadajensu suka haye tare da kwantawa, a ƙasa Angel ta shimfiɗa bargonta, su uku suka kwanta asaman shimfiɗar, ita da Jamima da Azeeza, sarakan kishi, duk abunda jamimah tayi sai azeeza tayi, suna a kwance saman shimfiɗar, jamima ta rungume Angel, itama azeeza ta baya ta rungumeta, sai dariya take yi, abin ba ƙaramin nishaɗi yake sanyata ba.
Ba su kwanta da niyar yin bacci ba, saboda Angel ta hanasu yin baccin marece, saboda su samu damar tashi tsakar dare su dinga yin addu'o'insu, wani irin bacci ne mai daɗi ya ɗauke su, hada masu yin min shari irinsu parveen aci ci mala ikun tauna.
Dare yana gab da yi, aka buɗe ƙopar ɗakin su, sautin bai farkar dasu daga bacci ba, A hankali Giant ɗin ke saukowa saman staircases, kafaɗarshi ɗauke da mutun, daga gani macace duba da irin shape ɗin ƙafafuwanta, uban gashin kanta ya sauko ta bayanshi inda kanta yake, ya lullu6e fuskarta, Ƴar rigar dake a jikinta guntuwa ce launin ja, daƙyar ta rufe mazannanta, hakan ya bayyana suffar fararen cinyoyinta, kamar ka ta6a jini ya ɗigo, Yanayin tafiyar Giant ɗin da ya ɗauko ta, ta banbanta da ta sauran Giants da suka saba zuwa kawo musu abinci, akwai natsuwa da kamala atattare da shi, jikinshi gaba ɗaya a rufe yake da baƙaƙen kaya, baka ganin koda yatsan hannun shi ne, bai nufi ko ina ba, sai saman gadon da ke ɗauke da no 3 a saman shi ya kwantar da ita a hankali, tare da janyo duvet ɗin dake a saman mattress ɗin Ya lullu6e mata jikinta dashi, a hankali yake ja da baya batare da ya juya ba, kamar yana kallon su, Har sai daya kai bakin benan tukunna ya juya da sauri ya haura benan ya fuce daga cikin ɗakin.......nima kuma na ajiye alƙalamina🤟
💋PRISONERS💋
A hankali yake ja da baya batare da ya juya ba, kamar yana kallon su, Har sai da ya kai bakin benan tukunna ya juya da sauri ya haura benan ya fuce daga cikin ɗakin.
Ko sautin rufe ƙopar bai farkar da su ba, kamar matattu, yaushe rabon da su yi irin wannan baccin su kansu sun manta, tsawon lokaci babu wanda ya farka, har dare ya yi, Hasken ceilling ya ɗauke, Na floor lamps ya kunna kan shi.
Azeeza ce ta fara yin motsi zata farka, hannunta dafe da mararta, wani irin azababben fitsari ne ya matse ta, da kasala a jikinta ta yunƙura ta miƙe zaune saman shimfiɗarsu, idanuwanta biji biji bata iya ganin komai.
muryarta cikin shessheƙar kuka ta soma magana tana laluban Jikin Angel.
"Angel ki tashi ki raka ni toilet, fitsari ni ke ji ya matse ni sosai....pls Angel ki tashi kada in yi shi a wando,"
Ko motsi Angel ba ta yi ba, balle har ta sa ran za ta farka.
Jamimah ce ta jiyo muryar Azeeza da ke ta yin kuka, farkawarta kenan, ta zame jikinta daga na Angel, ta miƙe zaune tana mutsustsuka idanuwanta da yatsun hannayenta, fuskarta a ɗaure babu annuri.
Ƙura ido ta yi a kan fuskar azeeza Dake ta kerma tana kuka, Muryarta da alamun bacci bai isheta ta ambaci sunanta"Azeeza...' tana jin muryar jamimah tai saurin katse kukan nata tare da cewa"Jamimah fitsari nake ji, dan Allah ki taimaka ki raka ni toilet, ya matse ni" baki asake Jamimah ke kallonta,
"Toilet dinne saina raka ki? Ke baki iya zuwa? Ko tsoro kike ji ne"? ta yi tambayar tana binta da kallon rainin wayau.
Jamimah ba ta san cewa azeeza na fama da lalurar rashin gani ba, Muryarta na rawa tace"Jamimah bana gani, idan dare yayi, makauniyace ni...."
Ta6e baki jamima tayi mata tare da cewa"ƙarya ne, Ni zaki raina ma wayau? Idan da gaske baki gani to ya akai da rana kike gani? Nafa san me nake yi,"
Takaici ne ya ishi azeeza duk yadda taso ta fahimtar da jamima taƙi yarda cewa bata gani, hakan yasa ta miƙe a makance ta soma tafiya tana laluban hanya, jamimah sai kallon bayanta ta ke yi, abun ya ɗaure mata kai ganin yadda ta ke ta sanya hannu tana laluban hanya, cikin rashin sa'a Azeeza ta nufi bango gadan gadan duk a tunaninta ta ƙaraso bakin ƙopar shiga sashen toilet ɗin ne, ta daddage zata buga kanta, Jamimah ta kware murya tare da cewa"Bango ne fa ba ƙopa fa",
Ta yi maganar tare da miƙewa da gudu ta nufi in da Azeeza ta ke a tsaye jiki na kerma don ba ƙaramin firgita ta yi ba, da taji muryar jamimah tana faɗa mata cewa bango ne ba ƙopa ba.
ba ta yi tsammanin zata taimaka mata ba, sai jin hannunta ta yi a cikin nata, ta ruƙo ta tare da jan ta zuwa cikin sashen, kafin su ƙarasa toilet ɗin tuni ta fara sakin fitsarin a wando, Suna shiga ciki ta zame wandon jikinta, da sauri jamimah ta kawar da kanta gefe don kada taga tsiraicinta, bayan ta gama yin fitsarin, ta yi tsarki kafin ta maida wandon jikinta, ta kira sunan jamimah, ta taimaka mata a daddafe su ka nufi ƙopar fita.
"Amma dai idon ki a rufe ya ke lokacin da nake cikin yin fitsarin ko? Azeeza ce tai maganar, murmushi jamimah ta saki tare da cewa"naga komai, daga yanzu sai ki daina raina min wayau kina kira na ƴar yarinya, nima ae kina min wanka, kuma kina ganin nawa"
Shiru Azeeza ta yi ba tare da ta tanka mata ba.
A lokacin sun fito daga sashen toilet din
"Amma wai dagaske baki gani da daddare? To ya akai kike gani da rana? yamutsa fuska azeeza tai"ko nace maki eh, ba yarda za ki yi dani ba, ki bari idan Angel ta farka daga bacci ki tambaye ki ji, " ta amsa mata da toh.
A lokacin sun shiga cikin ɗakin nasu, har zasu nufi shimfiɗar da Angel ta yi musu, ba zato ba tsammani idanuwan Jamimah suka sauka akan Gado mai ɗauke da no 3, dakatawa ta yi da yin tafiyar, ta ƙurawa gadon ido ta hango mutun naɗe cikin bargo, tunani ta shiga yi wanene saman gadon? Saboda a iya saninta tunda aka kwashe mazan cikin su, babu mai kwana saman tsaffin gadajen su sai Angel! Ita kaɗaice ta ke kwana saman gadon Danish, da sauri jamimah ta juya ta kalli ɗayan 6angaren don taga ko wani daga cikin su Hibba ne Ya dawo saman gadon ya kwanta, sai dai ko da tabi gadajen su da kallo kowannan su yana nan,'
A firgice ta wurga eye balls ɗin ta kan shimfidar Angel don ta tabbatar idan Angel ɗin tana nan, lamarin ya yi matuƙar razana ta ganin Angel baje saman bargo sai sharar baccin ta ke yi.
Azeeza da ta gaji da tsayuwa jin taƙi motsawa su tafi, muryarta a kasalance tace"Jamimah! Ke fa nake jira naji kin dakata da tafiya, Me kike yi ne, dan Allah ki kaina saman shimfiɗarmu in kwanta,"
Hankalin Jamimah ba ƙaramin tashi yai ba, muryarta atsorace ta furta"Azeeza Genie a ɗakin mu, saman gado no 3" ta yi maganar tana zazzare idanuwanta.
duk da Azeeza bata iya gani hakan bai hanata zare idanuwanta ba, zuciyarta ta yi wani irin bugu tamkar zata faso kirjinta, Azeeza sarkin tsoro,
"Innallahi wa'inna ilaihirraji'un! Jamimah ki faɗa min gaskiya, ko dai ƙarya kike yi min, wani irin genie kuma a cikin ɗakin mu, ki dai duba da kyau,"
jamimah tace" kin san Allah dagaske na ke maki, kamar mutun ne saman gadon, kuma na dudduba su hibba mun cika mu goma sha ɗaya, na saman gadon shine cikon na sha biyu."
Girgiza kai azeeza tai jiki nata 6ari tace"jamimah bargo ne da pillow ba mutun ba, ni dai mu je mu kwanta, " ta yi maganar tana ƙoƙarin jan hannunta, duk tabi ta tsorata kanta.
"Ni dai sai naje na duba gadon inga wanene, ke ki ke je ki kwanta"
Ran Azeeza ba ƙaramin 6aci yai ba, zuƙunnawa ta yi ƙasa tana rarrafawa don ta gano inda shimfiɗar Angel ta ke.
A hankali jamimah ke tafiya tana tunkarar gadon, ga tsoro tana ji amma ta nace sai taga wanene, tana ƙarasawa bakin gadon, ta ɗan dakata, tare da miƙa hannunta yatsunta nata yin kerma ta ruƙo bargon, wani irin tsorone ya ziyarci zuciyarta, a hankali ta yaye bargo, a gigice ta runtse idanuwanta ta daddage ta fasa wata irin firgitacciyar ƙara wadda ta yi silar farkawar masu yin bacci.
A matuƙar ruɗe Azeeza ta faɗa saman jikin Angel da ke kwance, Allah yaso ta isa ga shimfiɗar da kuwa zuciyarta ta buga silar ƙarar da jamimah ta fasa.
Bakomai ne ya tsoratar da ita ba face Sumar kan matashiyar dake akwance saman gadon, dama can a tsoroce take shiyasa bata iya tantance gashine ko ba gashi ba, ita dai taga abu kamar hauka, Mai uban yawan gaske ya nanannaɗe, idanuwanta ne suka dinga nuna nata kamar gashin yana motsi, aiko ta rushe da kuka da gudun gaske tabar bakin gadon har tana tuntu6e garin gudu, hankalin su Deeja ba ƙaramin tashi yai ba, ganin yadda jamimah ta furgice tana kuka, bata nufi ko'ina ba, sai saman jikin Angel ta faɗa mata, suka ƙanƙameta ita da azeeza, sun tada mata hankali, ko motsi sun hana tayi tun da tafarka, duk sunbi sun furgice.
Babu wanda ya lura da abunda ya tsoratar dasu.
"Me ke faruwa ne? Wanene ke yi mana kwaratsi a cikin ɗaki"? Parveen ce ta yi maganar fuskarta a yamutse, deeja tace"Jamimah ce, bansan me suke ma ihu ba" ta yi maganar tare da saukowa daga saman gadonta, tare da nufar shimfiɗar Angel.
Su yasmin duk suna zazzaune saman gadonsu basu motsa ba, idanuwansu akansu Jamimah.
Zuƙunnawa Deeja ta yi agabansu tare da ambaton sunayensu
"Jamimah! Azeeza! Lafiya ku ke yin ku ka? Wani abu ya faru ne"? Bakin Angel ya mutun, takasa magana, saboda faɗuwar da gabanta ke yi.
Cikin shessheƙar kuka Jamima tace"Ge..nie a ɗakin mu, ga ta can kwance saman gado number 3"
Jin ta ambaci bed no 3 yasa kowan nan su yin saurin kai idanuwan shi kan gadon, ganin kamar mutun ne yasa su ka soma kallon junan su, a ƙoƙarin su na su gano wanene acikin su yaje ya kwanta gadon, Ɗaya bayan ɗaya suka dinga saukowa daga saman gadajen su, tun daga kan Eve yasmin hibba hannah rubina, Sarah, kaf ɗinsu, A tsananin tsoroce su ke ƙarewa gadon kallo sai faman zazzare idanuwansu su ke yi.
"dagaske mutunce kwance saman gadon batul ɗin mu"! Jin wannan maganar da Parveen ta yi ne yasa Angel ware idanuwanta, ta sanya hannu tare da janye su Azeeza daga Jikinta.
Ta yunƙura ta miƙe jikinta na rawa ta nufi gadon Itama Deeja tabi bayanta, Ya rage saura azeeza da jamimah, sun fi kowa tsorata, rungume juna su ka yi kamar zasu haɗe jikinsu ya zama ɗaya.
A kewaye da gadon suka tsaitsaya curko curko, suna ƙare mata kallo, farat ɗaya Angel ta gane wacece muryarta na rawa ta ambaci sunanta da ƙarfi
* "BATOOL!" *
Ras! Gaban kowan nan su Ya faɗi, a ruɗe su ke kallonta, Basu tabbatar cewa ita bace, har sai da Angel ta hau saman gadon, Jiki na rawa ta sanya hannayenta biyu ta yaye sumar kanta gefe ɗaya, kyakkyawar fuskar batul ta bayyana, zazzare idanuwansu waje su ka yi, abun ne da basu tsammace shi ba, ba zaka iya tantance yanayin da su ke a ciki ba, suna so su yi farin ciki sai dai suna fargabar ace batul ɗinsu wani abu ya same ta, tun daga kan fuskarta su ka shaida hakan, kamar an ninka hasken fatarta, dama fara ce sol kamar Angel ko tabo babu a jikinta, hatta gwiwar ƙafarta jawur ta ke, ta canza masu sosai ta rame kamar an ɗibi naman jikinta, brownish lips ɗinta sun ciza sun bushe ƙamas, hankalinta a kwance ta ke fitar da numfashi sai dai kamar a firgice ta ke.
Halin da suka shiga furta shi 6ata baki ne, Zuciyoyin su sun karaya, Jiki yayi la'asar, Idanuwan kowannansu hawaye ne kwance a cikin su.
Muryar Angel cikin shessheƙar kuka ta furta"Ya Allah kasa ba mafarki na ke yi ba, Batul ɗina ce ta koma haka? Waye ya dawo mana da ita? Ta ina ta shigo? Dama dagaske ne abunda Gabriel ya faɗa min na cewa yaga matashiyar yarinya tana gudu asaman third floor! Batul ɗina ce kenan! ' Zuciyarta a hautsine ta yi maganar, ita kanta batasan ta furta hakan ba. yayin da idanuwanta ke akan jikin batul.
Hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskarta, ta ɗaura hannayenta biyu saman kafaɗunta, ta ɗago da ita, tare da kwantar da ita saman ƙirjinta, nan take taji wani irin yanayi mara misaltuwa ya ratsa jikinta, hakan ya ƙara tabbatar mata da cewa Batul ɗinta ce babu tantama, cikin rauni na murya ta shiga faɗin"wlh itace! Batul ɗin mu ce aka dawo mana da ita, tsawon wata uku, till today ashe da rabon zamu sake yin tozali da ƴar uwar mu! Alhamdulillah ya Allah bazan iya misalta farin cikin da nake a ciki ba........" Sosai ta fashe da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, suma sauran ƴan uwan nasu suka kama yin kukan farin ciki.
A gefe da gefen gadonta kowannan su Ya zauna, wasu ma saman gadon suka haye, kamar sun samu tv suna kuka suna kallon ƴar uwarsu dake a kwance jikin Angel, don tunda ta ƙanƙameta bata saketa ba, sosai ta yi tighting ɗinta a jikinta kamar zata mayar da ita cikin cikinta, Allah sarki tsohuwar zuma, Gaba ɗaya sautin shesshekar kukansu Ya karaɗe cikin ɗakin, bakomai yasa su yin kukan nan ba face tsabar farin cikin da su ke aciki, sai dai duk da hakan akwai fargaba acan ƙasan zuciyoyin su, saboda ba su san me aka yi mata ba, na tsawon lokacin da ta ɗauka a hannun su.
suna matuƙar jin fargabar abunda zasu ji daga gare ta, wani abu da ya ƙara tada masu hankali, Taƙi farkawa, duk wannan koke koken da su ke yi baisa ta buɗe idanuwanta ba, Azeeza dake rungume da jamimah tun da taji muryar Angel tana ambaton sunan Batul, tabi ta ruɗe ta shiga laluban hanyar da zata kai ta gare su, sai dai takasa, sai rarrafe ta ke yi a tsakiyar ɗakin tana ambaton sunan batul.
Jamimah ce ta taso itama tuni ta daina yin kukan jin cewa ƴar uwar su ce ba Aljanna, sai taji hankalin ta ya kwanta, tafiya tayi zuwa inda azeeza ta ke a zuƙunne ta ruƙo hannunta ta miƙar da ita, tare da yi mata jagora zuwa gaban gadon batul inda su Angel su ke a zazzaune, da taimakon Hannah ta samu ta haye gadon bayan sun matsa mata hanya, muryarta da zumuɗin ta ke faɗin ina batul ɗin ta ke ne? Dagaske itace aka dawo musu da ita?
fuskarta sharkaf da hawaye ta ke yi masu tambayar.
Makanta ba ta yi ba, idanuwanta akansu Angel saidai bata iya ganin su, ganin yadda take ta sharar ƙwalla tana ambaton sunan batul, Yasa deeja ta ruƙo hannunta ta ɗaura shi saman sumar kan batul data cika bayanta.
shafa gashin ta dinga yi da hannunta, muryar hanna a sanyaye tace mata"azeeza bacci ta ke yi, bata farka ba, tana rungume ne a jikin Angel ne" koda hanna ta yi mata magana, bata haƙura da laluban jikinta ba, har saida ta ɗaura hancinta a saman bayan batul, ta tabbatar da cewa ita ɗinta ce, tukunna hankalinta ya kwanta, farin ciki ya cika zuciyarta, sai zabga murmushi ta ke yi, Angel fa taƙi basu damar su rungumi ƴar uwarsu, tunda ta ƙanƙameta a jikinta taƙi sakinta, yadda kasan uwa da ƴarta, hannayenta biyu daddafe da bayanta, ko lokacin da azeeza take shasshafa sumar kan batul duk tana ji, sai dai bata motsa ba, gani take kamar in ta saketa za'a ƙara rabata da ita ne, Angel na matuƙar ƙaunar batul, fiye da tunanin mai tunani, irin ƙaunar da ta ke yi mata bata da banbanci