Header Ads
Showing 69001 words to 72000 words out of 287659 words

Chapter 24 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1800

Ads at the middle of Article

zata tafi tabar maki shi, bayan ba'a yaye shi ba, idan ya yi kuka ya zakiyi da shi"?
"Nima ae macace, Kaima kasan ina da abunda zan bashi" Dariya abie yayi a lokacin ya dawo gefenta ya zauna,
"Yanzu dai ki kwanta kiyi bacci, zuwa gobe da safe, zasu dawo kiga jikanki,"
Ba don taso ba, ta ajiye wayar Suka kwanta bacci atare,

A 6angaren Aneelerh Kuwa, tun Bayan magbrib suka baro gidan Uncle bash, Drivern gidansu Musa ne ke yin driving ɗinta, Tana a zaune Cikin back seat na motar, Jikinta na sanye da Arab gown ta yafa mayafi akanta, Baby junaid na rungume saman kirjinta, Yasha kayan sanyi ajikin shi,

"Ba gida zamuje ba, Gidana nake so ka kaini akwai wasu kaya da zan ɗauka"musa dake driving yace"Amma Ba mu yi da Alhaji cewa zan kaiki gidanki ba,"
"Eh na manta ban faɗa ma shi ba, ka kaini ba matsala," acewar aneelerh,
Shi dai hankalin shi bai kwanta da su je gidan nan ba, ganin dare yayi kuma gidan yana a karkashin Binciken ƴan sanda bai son wani abu ya faru,
"Amm hajiya naga dare yayi yanzu, me xai hana mu bari sai gobe da safe in kaiki gidan'?
ɗaure fuska aneelerh tayi sam batasan gaddama"meyasa ka ke yi mun magana sai kace wata ƙaramar yarinya? Bani nace ka kaini ba? Ae ba jimawa zanyi ba, akwai abunda nake so in dauko ne Ko minti biyar bazan yi acikin gidan ba,'
Muryar shi na inda inda yace"Zan kai ki mana kawai dai naga dare yayi ga kuma yaro ahannunki,'
"Muje kawai nidai" Amsa mata yayi da toh, ya juya sitiyarin motar ya haura saman titin da zai sada shi da unguwarsu Uzair,
Lokacin da suka ƙaraso unguwar tsit babu hayaniya ko gifcin mutun baka gani, kowa ya shige gidanshi, akwai hasken street light ta ko'ina,
A bakin gate ɗin Gidan, Musa yayi parking ɗin motar, ya fito da sauri ya buɗe ma aneelerh murfin motar, Fitowa tayi hannunta rungume da junaid, Key ɗin gidan yana a hannunta, Dama biyu gare su ɗaya na uzair ɗaya nata, wanda ke a hannun jami'an dake bincike na Uzair ne,

"Madam kodai in bi ki mu shiga Ciki"? Kallon shi tayi ganin duk ya tsorata"Motar fa wa zaka barma gadinta"? Muryarshi a sanyaye yace"hakane kuma bari na koma Ciki na jira ki, dan Allah Aunty kiyi sauri" murmushi tasaki jin ya canza mata suna, ya kirata da madam ya kuma kirata da aunty, Maimakon sunan da yake kiranta da shi Hajiya,
Wuce wa ta yi zuwa bakin ƙopar dake a jikin gate ɗin gidan, ta sanya key ta buɗe ta, ta shiga daga Ciki, duk akan idon musa dake a tsaye ya jingina bayan shi jikin motar,

A tsanake take tafiya Cikin Gidan wani irin yanayi take ji atattare da ita, Ko'ina ta shiga bi da kallo, tun daga kan inda suke ajiye motocinsu har zuwa ƙopar shiga falonsu, Bakomai take tunawa ba face rayuwarsu da Uzair, tuni taji hawaye sun wanke mata fuskarta, yau tsawon shekara biyu da watanni kenan, babu su babu alamarsu,
Hasken electric bulbs ne Ya gauraye gidan, tamkar da rana,

Lokacin da tazo bakin ƙopar falon, ta sanya key ta buɗe ƙopar ta shiga daga Ciki, Ko'ina a gyare yadda kasan mutane na rayuwa acikin gidan,

A saman Sofa ta kwantar da baby junaid dake ta bacci, ita kuma ta shige Cikin bedroom ɗinsu, tsayawa tayi tana bin ɗakin nasu da kallo, sai ta dinga ganin kamar fuskar uzair yana sakar mata murmushi,

Girgiza kai kawai ta yi yayin da hawaye ke cigaba da sauka saman fuskarta, Hotonsu na aure dake manne jikin bango ta ƙurawa ido, Sunyi matuƙar yin kyau, kusan minti biyar kafin ta Hau saman gadonsu ta kwanta tana shessheƙar kuka,
Dama babu abunda ya kawota Cikin gidan tazo ne kawai don ta ƙare mashi kallo saboda kewar Mijinta da tayi,,

Bubbuga mattress din ta dinga yi da hannunta tana kuka tana faɗin Wai ina kaje uzair? Meyasa ka tafi kabarni cikin maraicin rashinka, bayan kasan bana iya rayuwa da wani ɗa namiji idan ba kai ba, dan Allah mijina ka dawo gareni wlh ban gaji dakai ba, ina matuƙar ƙaunarka, kazo kaga Babynmu kyakkyawa da shi, so kake ya taso amatsayin maraya wanda bai da uba? Why uzair? Wata amsa kake so na bashi idan ya tambaye ni dangane da Mahaifinsa? Sai sambatu take yi ita kaɗai tana kuka, sam ta manta da Musa driver dake jiranta, ga kuma Yaro da ta bari a palour shi kadai saman Sofa yana bacci,

Kusan awa ɗaya aneeelerh bata motsa ba, wani irin yanayi mara misaltuwa take jin kanta a ciki, sai faman shessheƙar kuka take yi,

Lokaci ɗaya taji mummunar faɗuwar gaba ras! Tamkar ƙirjinta zai dare biyu, bugun zuciyarta ya ƙaru, Jiki na rawa ta sauko daga Saman gadon muryarta na kerma take ambaton sunan Junaid,

Da gudun gaske Ta faɗo Cikin Falon, Tana ɗaura kanta saman Sofa ɗin data kwantar da junaid, taga wayam babu shi sai dai towel ɗin data nannaɗe shi aciki, A ƙasa aka jefar da shi,

Kamar afarmaki take ganin lamarin, Tsabar ruɗi tarasa me zatayi, Tsananin tsoro ne bayyane akan fuskarta, Ƙarasawa tayi gaban sofa ɗin ta sanya hannu tana shafa Saman kujerarar, ta tabbatar cewa an ɗauke Mata Yaronta, tunani tayi kodai Musa ya shigo ya ɗauke shi ne? da gudu ta zabura Ta fito daga cikin falon, Har ta kusa kaiwa Bakin gate ta juyo kukan baby junaid ɗinta, a matuƙar gigice ta juya ta koma Cikin gidan, duk inda ta nufa sai taga babu shi, Rushewa tayi da matsanancin kuka tana faɗin"Innallalahi wa'innna ilaihirraji'un! Wayyo Allah na! dan Allah wanene ya shigo? kada ku cutar mun da yarona na roƙe ku, ku ƙyale mun shi, ' tana Cikin maganar nan tajiyo takun tafiyar mutun a firgice ta juya bayanta, gifcin shi ta gani koma wanene yana a sanye Cikin bakaken Kaya, Fuskar shi tana sanye da face mask, Hannunshi na ruƙe da Baby Junaid, Da gudun gaske Aneeelerh tabi bayanshi, sai dai kafin ta ƙarasa tuni ya 6ace ma ganinta,
Gaba ɗaya ta haukace Jikinta sai tsuma yake yi ga wata uwar zufa data tsastsafo mata, ita ba kanta take ji mawa ba, Ɗanta take jimawa ba, shida bai mallaki hankalin shi ba,
"Dan Allah na roƙe ka ka dawo mun da ɗana, Kome kakeso zan baka, Amma kada ka cutar mun shi, idan ma ni kakeso ka dauke ni ka ƙyale mun shi pls," cikin shessheƙar kuka tayi maganar,

Motsi ta kuma Ji daga can saman stairs ɗin gidan, A hautsine ta ɗaga ido tana kallon mutun dake atsaye, Hannun shi ruƙe da baby junaid, ƙarfin hali hada ɗaura shi saman kafadarshi, yana shafa bayanshi, kuma yaron yayi shiru,

Zuba ma shi ido tayi tana kallon shi batare da ƙyaftawar ido ba, Koma wanene wannan mutumin ba ƙaramin karkarfa bane, Yana da tsayi da kuma faffaɗan Ƙirji, ta ko'ina ya rufe jikin shi, ta yadda mutun bazai iya shaida shi ba,
Muryarta na kerma tace"Dan Allah kada ka cutar mun da shi, kome kakeso zan baka," ta yi maganar tana kallon shi, zufa ta ko'ina saman fuskarta,
Gani take kamar zai jefo shi ta saman bene ne ya faɗo kasa kanshi ya fashe,
Fashewa ta kuma yi da wani sabon Kukan, Tunawa tayi da musa driver da gudu ta juya ta nufi hanyar fita don taje ta sanar da shi abunda ke faru,
Harta ruƙe handle ɗin ƙopar, Muryar mutumin ta ratsa kunnnuwanta,
Cikin harshen Turanci yace"idan kika kuskura kika fita, zan wurgo da shi ƙasa," Ras Taji gabanta ya faɗi, Kamar gunƙi haka ta ƙame, zuciyarta a cunkushe Ta juyo tana kallon shi, Har lokacin Yana a can sama,
Muryarta na kerma tace"Na fasa bazanje ba, wlh bazanje ba, dan Allah ka bani ɗana, wlh nayi maka alƙawari bazan ƙara zuwa gidan ba,"
Dawowa cikin Falon Ta yi, A bakin stairs ɗin ta tsaya, fuskarta jaga jaga da hawaye, Bata ta6a ganin tashin hankali ba irin na yau, Ko wanene wannan mutumin? Taya akai ya shigo Cikin gidan? Bayan makullan gidan Suna a hannun jami'an ƴan sanda? Anya kuwa mutunne kodai ta bango ya ratsa Ya shigo?
"Ka faɗamun ko nawa kakeso zan baka ina da kuɗi, Ni dai kawai burina ka bani Yarona,"
Tana magana tana taka staircases ɗin, a kokarin ta nata haura inda yake,
"Hajiya" Muryar Musa driver ce, A firgice aneelerh ta juya tana kallon musa, Ai koda musa yayi arba da mutumin dake A can saman stairs sanye da bakaken kaya, Nan take jikin shi ya hau yin kerma, Ya shiga ambaton"Ƙalu Innallahi wa'inna ilaihirraji'un hajiya wannan kuma daga ina"?
Cikin muryar kuka aneelerh tace"Nima bansani ba, Daga shiga Cikin ɗaki na dawo na taras ya dauke mun baby junaid ɗina, dan Allah kataimaka ka sanya baki mu bashi haƙuri ya bamu junaid mu tafi mubar masa gidan,"
Kallon shi musa Ya kuma yi"Bawan Allah, Don son da kake ma iyayenka Ka taimaka ka bamu yaron nan, Wlh tsautsayi da ƙaddara ne ya kawo mu Cikin gidan nan, dama saida na gargaɗi hajiya nace mata kada mu zo, Amma ta sanya naci akan sai mun zo yanzu ga irinta nan"
Roƙonshi suka dinga yi ko tanka masu baiyi ba, tamkar baijin me suke cewa, Ya ƙanƙame Yaro a hannunshi sai shafa sumar kanshi yake yi,

"Hajiya wannan mutumin fa, ba bamu yaron nan zaiyi ba, Kizo muyi ta kanmu kawai, Allah zai baki wani ɗan, idan ba haka ba mu duka zamu rasa ranmu,"
"Wlh ba inda Zanje sai ya bani yarona, saboda bakasan ciwon haihuwa ba shiyasa zaka ce mu tafi mubar ma shi yaro a hannu, " rai a6ace takai ƙarshen maganar, Duk yana atsaye yana sauraron su,
Suna Cikin yin maganar nan, gaba ɗaya hasken gidan ya ɗauke, duhu ya mamaye ko'ina,
Aneelerh ta shiga matsanancin tashin hankali, Cikin duhu taci gaba da tattaka matattakalar benan, Tana jiyo muryar musa yana kwala mata kira, amma ina kota kanshi bata bi ba, lokacin da ta ƙarasa hawa benan, Muryarta na rawa take faɗin"Bawan Allah, ka bani yaro na in tafi, nasan kana jina, dan Allah kada ka cutar mun shi," tana magana tana lalube Cikin duhu,
Motsin shi ta dinga Ji acikin kunnuwanta, alamun yana a kusa da ita, Kamar ma zagayeta yake yi, Jikinta sai kerma yake yi, ga wata uwar zufa dake tsastsafo mata, mugun tsoro take ji, amma saboda soyayyar dake a tsakanin uwa da ɗa, ta kasa guduwa ta kwammace komai zai faru ya faru, koda zata rasa ɗanta ne,
Wani irin daddaɗan ƙamshin turare ta soma shaƙa Cikin hancinta, koma wanene wannan Ba 6arawo bane, Kuma ba da niyar mugunta yazo ba, Lamarin ya rikitar da ita,
Cikin sanyin murya tace"Dan Allah ka bani shi in tafi, wlh bazan faɗi ma kowa naga mutun acikin gidan ba,"
Hannunta taji ya ruƙo, ras taji gabanta ya faɗi, ɗaura mata baby junaid yayi asaman ƙirjinta, da sauri ta tallebe shi, ta rungume abunta ajikinta, Natsuwa tayi tana jiran jin ya furta wata magana sai dai baice komai ba,
Lokacin da ta daina jin motsinshi a kusa da ita, a dai dai wannan lokacin hasken Gidan Ya dawo gaba ɗaya ya gauraye ko'ina,
Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da ɗaura idanuwanta kan baby junaid dake ta sharar bacci, saman ƙirjinta,
Ƙara ƙanƙame shi tayi ajikinta, kamar zata mayar dashi Cikin cikinta, Yau da ace ɗan tahalinkin nan ya kashe mata shi, da kuwa har ranta zata iya rasawa,
"Hajiya zamu iya tafiya yanzu"? Musa ne yayi maganar jikinshi sai kerma yake yi, yana daga can down stairs, Harara ta wurga mashi,
"Ka bani key ɗin motar, ka kama gabanka, Sakaran Namiji kawai, hada cewa in bar mashi yarona in Zo mu tafi, ban ta6a ganin ragwon namiji irin ka ba, duk macan da ta aure ka tayi asara, " zuru musa yayi mata da ido,"
Saukowa down stairs tayi tare da miƙa mashi hannu"bani key ɗin motar"
Cikin sanyin murya yace"ayi haƙuri hajiya ruɗu ne ya jawo hakan"
A fadace tace"dalla ni bani key,"
Zaro key ɗin motar yayi daga Cikin aljihun shi ya miƙa mata, tasa hannu ta fusge shi, Cikin fushi ta fuce daga cikin falon,
Da gudu musa yabi bayanta yana lallashinta.
Bayan ta rufe gidan da key ta buɗe mota zata shiga driver seat, da sauri musa Yayi hanzarin cewa"Dan Allah aunty aneelerh kiyi hakuri wlh bana Cikin hayyacina ne, su6ul da baka nayi wurin furta maganar, ban kaiga tace ta ba,"
Daƙyar musa ya samu aneelerh ta haƙura ta miƙa mashi key din motar, ta shiga passenger front seat ta zauna shi kuma ya zauna a driver seat,"
Da gudun gaske ya fusgi motar, kafin su ƙarasa gida saida ta gargaɗe shi akan karya kuskura ya faɗa ma su abie dangane da mutumin da suka gani Cikin gidan, yaja bakin shi yayi shiru tun da bai cutar dasu ba, su ɗauka tamkar mafarki su kayi, Yace mata toh,

Lokacin da suka ƙaraso Cikin gidan, A parking space Musa ya yi parking ɗin motar, ya fito ya zagaya ta other side ɗin ya buɗe ma Aneelerh mota,
Fitowa tayi hannunta rungume da baby junaid, Har lokacin Jikinta kerma yake yi, ta tsorata sosai da wannan tahalikin da ya kai masu farmaki,
Kallon musa tayi shima kallon nata yake yi, harara ta jefa mashi ya sunnar da kan shi ƙasa, Ni zan wuce ciki, "
"To hajiya sai Allah yakaimu, Allah ya kyauta gaba," bata amsa ma shi ba ta nufi Cikin gidan,
Da alama duk sunyi bacci, bata nufi ko'ina ba, Sai Cikin Bedroom ɗinta, a saman gado ta kwantar da junaid, sai baccin shi yake yi hankali kwance,

Rage kayan jikinta ta yi, ta shiga toilet domin yin wanka, after 15 mins ta fito waist ɗinta ɗaure da towel fari,
Walking slowly ta nufi Saman mirror chair ta zauna, tare da ɗaura gwiwar hannunta gaban madubin, ta zabga uban ta gumi,
Zuciyarta a cike take da tunanin mutumin nan, ko wanene shi? Taya akai ya samu damar shiga Cikin gidan dake a garƙame? Kodai bayan shigarsu ciki shima Ya samu damar shiga Cikin gidan? Shin me yaje yi acikin gidan, gaba ɗaya ta burkita ma kanta lissafi, kusan raba dare ta yi azaune tana tunani akan shi, bata iya gano komai ba, a ƙarshe ta miƙe taje gaban closet, ta buɗe ta curo kayan baccinta, Ta sanya su ajikinta,

Komawa saman gadon tayi, ta kwanta tare da janyo junaid ta rungume shi ajikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci bacci yae awon gaba da ita, Ko da gari ya waye Aneelerh bata sanar da kowa game da mutumin da suka gani acikin gidan Uzair ba, ita kanta tarasa gane dalilin dayasa ta kasa buɗe baki ta faɗa masu cewa wani ya shiga gidan, wata'ƙil ta hanyar hakan asamu wata evidence da zata bayyana ainihin meya faru da su tajo, kuma tun daga ranar bata ƙara gigin zuwa gidan ba, gani take kamar mutumin yana bibiyar rayuwarta, kodan kada ta tona ma shi asiri dole ya bibiyeta, shiyasa take tsoran fallasawa,

Back To prison🌷

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah A yau angel ta cika shekara 1 da rabi A gidan KURKUKUN ƘADDARA, tun daga ranar da tayi ma batool tambayoyin nan bata ƙara tambayarta wani abu dangane da gidan kurkukun ba, dalili kuwa shine a duk lokacin da zata tambayi batool game da prison ɗin, Sai wani abu ya faru, wanda zai ɗauke masu hankali, Haka xalika a duk lokacin da ta yi yunƙurin sanar dasu wani abu game da addinin musulunci sai wani abu ya faru wanda zai dakatar da ita, ta ko'ina an toshe mata hanya,

Abu ɗaya ne take kokarin Koyar da su shine yawan ambaton sunan Allah acikin maganarsu, saboda kwata kwata basa furta sunan Allah, zuwan angel cikin rayuwarsu sun fara koyan wasu abubuwan wanda basu iya ba, salon maganarsu ya fara komawa irin na angel, ta zama tamkar malama acikinsu, Idan suka kammala Cin abinci, bata bari su koma bacci, motsa jiki take sanya su suna yi, Ko kuma suyi wasa a tsakaninsu, bakomai yasa suke jin shakkarta ba, face rashin tsoranta, da kuma wannan kalmar ta charman dudu da take yi masu barazana da ita, shiyasa a kullum take Cin galaba a kansu, duk wannan tsawon lokacin da angel ta ɗauka acikin gidan kurkukun ƙaddara, har yau babu jituwa tsakaninta da Haris da kuma mr sound hater wato DANISH, su biyun nan sunƙi yarda da ita, duk da sunfi kowa jin shakkarta, kuma in ta bada umarni dole kowa yabi hada su ɗin,

Zaune suke gaba ɗayansu sun kewaye Kayan abincin da aka kawo masu, giants suna a tsaye sun kasa sun tsare suna jiran su kammala Ci su kwashe Kayan su tafi,
Hanna ce ta ya ye jan kyallen da aka rufe saman trays ɗin, tray na farko fried meat ne, sai faffadan plate me ɗauke da Snacks a tray na ƙarshe kuma jug ɗin ruwa ne, sai kofuna Bayan su kuma sai kwandon dake ɗauke da kayan marmari da ƴar ƙaramar wuƙa, wadda zasu yi amfani da ita su yanka fruits ɗin,
Kowa yakai hannu ya dauki fried meat yana Ci,

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads