Showing 279001 words to 282000 words out of 287659 words
Chapter 94 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
da miƙewa ta dinga gudu zufa na bin jikinta har sai da Allah ya bata nasarar kaiwa ga Second Floor, Ta ƙarfi ta buga tsalle ta haye sama tana faman Haki, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, Ƴan hanjin Cikinta sai kaɗawa su ke Yi, A hankali ta yunƙura ta miƙe tsaye tare da juyawa tana kallon benan, Wani abun mamaki Gaba ɗaya ya daina motsawa sauke ajiyar zuciya ta yi, Angel da kasada taci gaba da tafiya Saman hawa na biyu, Sai faman baza ido ta ke yi tana ƙarewa ginin kallo, tsarin shi yadda kasan Ƴan hanjin Cikin mutun saboda kwana kwanar da ke gare shi, A dai dai Bakin wani corridor taci burki tana leƙa Ciki, Ɗakuna ta hango A jere Kusan guda Huɗu biyu suna fuskantar biyu, Ƙofofin su a rufe su ke sai dai bata da tabbacin Ko an sanya masu Kuba.
"Ya Allah ka tsare ni daga sharrin duk wani abun cutarwa, Ya Allah ka haɗa ni da abunda nazo nemo Cikin sauƙi ba tare da nasha wahala ba," acikin zuciyar ta take ambaton hakan, ɗaga kafarta tayi tare da nufar Ƙofofin, Hannu ta kai ta ɗan ta6a Jikin ƙofar farko ba zato ba tsammani taji ƙofar tana lilo alamar a buɗe ta ke, Sai da ta fara karanta addu'ar neman tsari ba tare da Jin tsoro ba, ta faɗa Ɗaya daga Cikin ƙofofin, wurga ƙafar ta ke da wuya wani uban wari ya daki hancin ta, Idanuwan ta a zazzare ta ke ƙare ma Ɗakin Kallo, tamkar Igiyar Shanya ce kewaye A cikin shi ta kowane 6angare, babban abunda yayi mugun ɗaga mata hankali Gangar Jikin Matasan Ƴan mata ta gani da maza Wanda basu haura shekarun su Batul ba, zindir babu kaya a jikin su, An ɗaure wuyan su sagale Jikin Igiyoyin nan kamar kayan wanki da alama Sun gama amfani dasu, wasu An cire nonuwan su,wasu kuma an cire gaban su,Wasu Idanuwan su aka kwalkwale Yayin da wasu kayan Cikin su aka wawake, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!
Wata irin narkakkiyar zufa ce ta wanke ko'ina na jikinta da ke ta yin kerma kamar wadda ake kada ma mazari, duk ta bi ta furgice ganin komai ta ke yi tamkar a mafarki, Hannayen ta daddafe da kanta cikin fitar hayyaci ta fito daga Cikin ɗakin, Maimakon tayi reverse ta koma Inda ta fito sai ta ƙara gaba saboda gushewar da hankalin ta yayi, A gigice Ta fito daga ɗakin Wani irin jiri take gani a cikin idanuwan ta, Hannunta dafe da ƙirjinta Zuciyar ta sai tashi take yi ga wani irin zazza6i da ya lullu6eta.
A bakin Ƙofar ɗaki na biyu ta faɗa tana faman haki, Karaf idanuwan ta suka sauka Akan Giants da ke gudanar da aikin su na Theatre, gadaje ne sunfi talatin Cikin Ɗakin mai faɗin gaske, kowani gado Yana ɗauke da mutun kwance saman shi, Sun fafe cikin su suna ɗibar kayan cikin nasu tare da ɗaura su saman table ɗin da ke a gefen su, A matuƙar razane ta juya tana neman hanyar da zata bi ta Fitar da ita daga Cikin Corridor ɗin, Allah Yaso basu lura da ita ba babu wanda Ya ganta don gaba daya hankulan su na akan aikin da suke kuma basu zaton wata matsala , Watsawa ta yi da gudu Ita kanta batasan inda take tunkara ba Sunan Allah kaɗai ta ke iya ambato a cikin bakinta, adaidai saitin wata ƙopa ta soma jin Wata kakkausar murya tana magana da wani irin gur6ataccen yare mara daɗin ji, A hautsine takai idonta Ƙofar Dogon labule ne launin Ja ya rufe ta, Yatsun hannunta na kerma ta ɗan yaye labulan.
Babban ɗaki ne mai girman gaske kamar palour, komai Na cikin shi Red & black Colour ne, bangon ɗakin Zanunnukan kan ƙwarangwal ne dana kunama, da na wasu halittu masu dogon harshe Da zaƙo zaƙon akaifu irin na shaiɗanu, Zanen su ne ta ko'ina gwanin ban tsoro, Mutane ta gani a jere sunkai su Talatin Kowannan su na sanye Cikin Jajayen dogayen riguna masu huluna, hannuwan su ruƙe da ƙoƙuna masu ɗauke da jini, daga tsakiyar su wasu tiƙa tiƙan mutane ne kusan su Shidda, Yadda kasan Irin malaman Majami'u na ƙasar India, Tumbur babu Kaya ajikin su, Sae dai wani ƙaramin Jan ƙyalle da su ka ɗaure ƙugunan su dashi, ga wani uban tumbi da suka tara, Jikin su bulbul ansha Jini An ƙoshi, Jan fentin da ke saman fuskokin su Ya rufe ainihin Suffar su sun koma kamar dodonni, Sun kewaye wani Dodon tsafi dake a zaune saman armchair, Wata irin halitta mai matuk'ar muni miyau sai zalalowa yake yi daga bakin shi, Zir Jikin shi babu kaya sai uwar yanar da ta nannaɗe gangar Jikin shi tayi mashi tamkar sutura.
A kowace kusurwa ta cikin ɗakin jajayen ƙwaryoyi ne a jere an rufe su da faifai, Ga wasu ƙananun Yara da basu haura 7 years ba mata zuƙunne saman gwiwowin su babu kaya a jikin su, gabansu ca6a ca6a da jini, daga gani amfani aka yi dasu.
Wani ikon Allah duk tashin hankalin da idanuwanta su ka yi tozali dashi baisa ta kurma ihu ba saida taga waɗannan yaran ƙananu tukunna sautin muryar ta ya dawo har ta ƙware Baki zata Kurma Ihu ba zato ba tsammani taji saukar hannun mutun saman bakinta, sosai Ya toshe mata baki! Batasan wanene ba hakan yasa ta zazzare idanuwan ta waɗanda su ka kaɗa su ka yi jawur dasu, tsoro da firgici ne acikin ƙwayar idonta
💋PRISONERS💋
Gaba ɗaya taji an ɗauke ta, Batasan Ina aka dosa da ita ba saboda suman da tayi. Tsawon mintuna, Kafin taji saukar ruwa saman fuskarta wanda ya yi silar farfaɗowar ta, Sambatu ta soma yi tana ambaton Danish nifa danish ɗina nazo nema, wlh bada niyar leƙen asiri na fito ba, ni banga komai ba, dan Allah a maidani Cikin ƴan uwana, Kada acutar dani, tsautsayi da ƙaddara ne suka fito dani, kuma bazan Ƙara ba......." kamar daga sama taji an ambaci sunanta da wata irin murya mai sanyin gaske daga ji mamallakinta ba ƙaramin mutun ba ne.
"UNAISERH ZAHEER TAJUDDEN"! kai tsaye kiran Ya daki dodon kunnanta, idanuwan ta dake a cike tab da ƙwalla sun mata nauyi ta buɗe tana Kallon saman ceiling ɗin da ta ke fuskanta, Fitilu ta gani guda Ukku suna Lilo, Sune suka haskaka cikin ɗakin da take a kwance saman fata mai gashi gashi a jikinta, gaban ta na faɗuwa ta zabura ta miƙe zaune tana faman bin ko'ina na ɗakin da kallo A ƙoƙarinta nata ga wanene ke yi mata magana.
"Ina a bayanki!" Jin hakan yasa ta yunƙura ta miƙe tare da juyawa tana kallon shi, Giant ne Sanye cikin shigar su ta baƙaƙen Kaya ya goya hannayen shi saman faffaɗan ƙirjin shi, Waro ido waje ta yi Kafin ta zabura ta watsa da gudu da niyyar ta nemi ƙofar da zata gudu, Sai dai har ta gama kewaye ɗakin babu ƙopa, A jikin bango ta manne kamar zata shige mashi idonta akan shi yayin da yake tunkarota, ta dinga girgiza mashi kai muryarta A dabarbarce ta ke yi mashi magana
"Wlh kada ka kuskura ka ta6a ni, idan ba haka ba zan ƙona ka da ayar Allah, Mugaye kawai ai ni bansan na fito daga inda aka killace mu ba, kuma ni Danish Na fito nema ba wani abu ba....." a gigice ta ke yi mashi magana, Gani ta ke kamar zai rikiɗa ya koma wannan halittar da Unaizah ta bata labari, tuni hawaye sun wanke fuskar ta, Har ta fara tunanin yadda zata koma Idan Ya kusance ta kamar dai yadda aka yiwa unaizah ta mutu.
Duk haukan nan da ta ke yi bai tanka mata ba, Yayi tsaye a gabanta Kamar yana ƙare mata kallo ne.
"La'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" A saman jikin shi ta dinga tottofa mashi addu'ar da ta ke karantowa.
Hakan yasa shi Sakin dariya sautin ya karaɗe Cikin ɗakin da su ke a ciki, A matuƙar ruɗe take kallon Giant ɗin Jin yana dariya, ita dai a iya saninta Giant basa magana balle har suyi dariya, bakomai Ya faɗo mata a cikin ranta ba fa ce Giant ɗin da ya taimaki Batul ya dawo da ita cikin su, nan take ranta ya fara raya mata cewa ko dai shine!? Tun daga ƙasa har sama take kallon shi, Muryarta na rawa tace "wah...nene kai"? A tsanake ya soma magana "ɗan adam ne ni, sai dai mun banbanta da juna saboda ni Giant ne ba cikakken mutun ba" Mamaki ne ƙarara akan fuskar Angel.
"Ki kwantar da hankalin ki, ni bamai cutarwa bane, Mai taimako ne, kada ki yi tsammanin nima mugu ne kamar sauran," wannan maganar da yayi ce tasa hankalin ta ya ɗan kwanta, har cikin ranta taji ta yarda dashi sai dai ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba, taya akai Ya kawota nan, Sannan Yake yi mata magana? Anya kuwa Giant ne? Ko dai ɗan leƙen asiri ne Ya shigo masu kurkukun......."
"Ba ɗan leƙen asiri bane, nima Ma'aikaci ne na gidan kurkukun ƙaddara kamar yarda na faɗa maki Am A Giant! " ya ƙara jaddada mata maganar shi, Aruɗe ta kalle shi jin ya bata amsar tambayar da ta ke acikin zancen zucinta.
"Wanene kai? Meyasa ka kawo ni nan? Kuma meyasa kake magana bayan ni a iya sanina Giant basa magana"
Juya mata Baya yayi taku ɗaya zuwa uku Kafin Ya dawo gare ta, rumfa yayi mata Da faffaɗan ƙirjin shi Duk tabi tasha Jinin Jikinta
"Tambaya ta farko, sunana SALSABEEL! Tambaya ta biyu na kawo ki ɗakin nan ne saboda in isar da saƙona! Tambaya ta ƙarshe Giant Suna magana ba kurame bane, A tsakanin su da prisoners ne ke basa magana, Idan kika natsu zan fayyace maki komai, ki bani haɗin kai saboda bani da isasshen lokacin da zan 6ata, Mintuna talatin suka rage man kafin garkuwar sautin dana sanya ta karye," Jinjina kai Angel tayi alamar gamsuwa da bayanin shi.
"Da ace tuntuni mun haɗu da juna, da baku kai tsawon lokacin nan a gidan kurkukun nan ba, " Sakin Jiki ta yi jin abunda yace, har ta buɗe baki zatayi magana Ya dakatar da ita
"Kada ki katse ni, Idan na kammala magana daga bisani za ki Iya jera min tambayoyin ki idan lokaci bai ƙure mana ba" jinjina mashi kai tayi alamar taji maganar shi.
"Ni da mahaifiyata bamu da burin daya wuce mu kawo ƙarshen Zuluncin da ake aikatawa agidan kurkukun nan, Dukkan mu bada son ran mu muka kasance ma'aikata A cikin shi ba, mun miƙa wuya ne saboda fansar da mu ke so mu ɗauka da kuma kawo ƙarshen Matsafan dake a cikinsa, Mun jima da wannan ƙudurin acikin zuciyoyin mu sai dai ƙarfin mu bai kai mu iya ja da Shuwagabannin dake mulkar kurkukun ƙaddara ba, Saboda shaiɗanun mutane ne masu haɗarin gaske Mai iya ja dasu Sai Allah ba dai mutun ba" Angel ta natsu tana sauraron shi, ko motsi bata yi, Har yanzu bata fahimci kan zancen shi ba, gashi ya hana ta tambaye shi.
Cigaba da magana yayi "Nasan har yanzu baki fahimci inda zancena ya dosa ba, " dafe bangon da ta jingina dashi yayi da tafin hannun shi,
"Tun kafin zuwan ki kurkukun nan munsan komai dangane da rayuwar ki! kaifin basirar ki da hankalin ki shiyasa muka kwaɗaitu da son zuwan ki tun da labari yazo gare mu na cewa kece ƙaddarar Prison! ," gaba ɗaya Ya gama ruɗar da ita, Duk tabi ta kakkame Jikinta.
"Ma'anar hakan shine ke kaɗaice zaki iya tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara! Kamar yadda yazo mana a allon tsafin mu, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mana ba nida mahaifiyata TSOHUWA TAMIRA!!!!" ƙara zare idanuwan ta tayi akan mask ɗin da ya 6oye ainihin fuskarshi, Al'ajabi ne ya kamata Jin ya ambaci sunan tsohuwa tamira a matsayin mahafiyar shi!
"Ƙaddara kala Biyu ce, Mai kyau da mara kyau, A hasashen matsafa Idan suka killace ki a hannun su zaki zamar masu kyakkyawar ƙaddara, Amma idan suka bar ki a cikin Jama'a kina yawo shine zaki zamar masu ƙaddara mara kyau......." Kasa haƙura ta yi hakan yasa ta katse mashi maganar shi da cewa "Taya akai na zama ƙaddarar su"? Ta jefa mashi tambayar tana kallon shi da zararrun idanu.
"Kin manta me na faɗa maki?" Ko da ya ke halin ki ne Iya tambaya kamar ƴar jarida shiyasa kika gaza haƙura har saida kika katse mini magana ta" muryarta a dabarbarce tace "Bazan ƙara ba"
Gyaɗa kai Ya yi kafin ya ɗaura da cewa "rayuwarku tana a cikin haɗari mai munin gaske, musamman ɗan uwanki Danish"! Gabanta ne ya faɗi jin ya ambaci sunan Abun ƙaunar ta.
"Kasancewar shi garkuwar kurkukun ƙaddara, Matsafa sun ƙwallafa rai akan shi, Saboda shi ɗin tamkar wata nasara ce agare su, idan dashi baza a ta6a Iya rushe Ginin kurkukun ƙaddara ba, su kansu matsafan baza a iya cin nasara akan su ba, shiyasa suka bashi babban matsayi Na Prison Shield! A halin yanzu da na ke yi maki Magana, Ɗan uwanki Danish Ba cikakken Mutun bane, He's a dangerous Giant! Sun riga da sun bashi horon zama Giant duk wani zunubi da kika sani mai girma a duniyar nan na rashin imani da tausayi sun koya mashi, sun riga sun yi Transforming ɗin shi into a Giant, Horo Ne wanda ba mutane zalla suke basu shi ba harda baƙaƙen shaiɗanun aljanu, Harshe na bazai Iya furta maki abubuwan da su ka yi mashi ba da kuma wanda su ka sashi ya aikata kafin su tabbatar da komawar shi Giant........" Bai ƙarasa maganar ba ganin ta sulale daga jikin bangon zuwa ƙasa, zuciyarta ba ƙaramin karaya tayi ba, idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla, bakomai take hangowa ba face fuskar Danish ɗinta! Yanzu shikenan Sun canza shi zuwa Giant, Sun 6ata mashi rayuwar shi sun gur6ata mashi tunanin shi.
Zuƙunnawa Salsabeel Yayi agabanta Saman ƙafafuwan shi,
"Lokaci Yana tafiya, agurguje Zan faɗa maki yadda za ku Yi don ku gano ƙofar nan da zata fitar daku daga Cikin kurkukun nan, shine abu mafi muhimmanci agare ku!
Cikin shessheƙar kuka tace mashi "Idan dagaske ne Zaku iya taimaka mana mu fita zanji dadi sosai, sai dai Ni bazan Iya barin kurkukun nan ba tare da Danish ba, Dole in tafi dashi, in ba haka ba, Ni zan tsaya in yaso sauran ƴan uwan mu su ku6uta," sosai ta fashe mashi da kuka.
"Ni kaina bazan bari ku tafi ba tare da Danish ba! Domin kuwa shi ba iya garkuwar kurkuku bane, Ku kanku garkuwa ne agare ku! Fita prison ba abu bane mai sauƙi, Shi kaɗai ne zai Iya taimaka maku don ku gudu cikin sauƙi, dalilin da yasa nace haka saboda ginin kurkukun nan a cikin ƙurmin Daji ya ke, Idan har Allah yasa kuka samu damar fita zaku faɗa cikin Daji ne mai hatsarin gaske mai ɗauke da mugayen namun dawa, Sannan tafiya ce wadda ƙafa bazata ta6a iya yin ta ba, amma in dai Garkuwa Yana a tare daku bazai bari wata dabba ta cutar daku ba, Koda kuwa Zaki ne ko Kura zai Iya rikiɗa ya koma irin suffar su don yayi faɗa dasu harma yayi nasara akan su......." dakatawa ya ɗanyi da yin jawabin, Itama Angel tuni ta dakata da yin kukan tana kallon shi, Zuciyarta cike da mamaki haɗi da rudanin maganganun shi, Kuma daga gani ba ƙaramin mutun bane.
"Bana so ku ƙara Wata ɗaya a gidan kurkukun nan saboda muna gab da shiga watan da za'a gabatar da Black Night, taro ne na matsafan duniya da zasu halarta a gidan kurkukun nan daga ƙasashe daban daban zasu zo, ranar gwada rashin Imani, ranar zubda jinin prisoners, Idan muka bari ranar ta riske ku a cikin kurkukun nan, bana tunanin ɗaya daga Cikin ku zai Rayu! Dalilin da yasa suka daina zuwa ɗaukar ku saboda sun dakatar maku da Jinin al'adar ku na mata saboda tanadin da su ke yima wannan ranar, tsawon watannin da kuka ɗauka ba ku yi Jini ba, a ranar zasu yi maku sihirin da zaisa ya dawo maku gadan gadan don su gwada rashin imani akan ku......" Hankalin Angel ba ƙaramin tashi yayi ba, Idanuwanta azazzare ta ke kallon mask ɗin fuskar shi, tsigar jikin ta duk ta tashi haiƙam jin abunda yace,
"Lokaci Yana ƙure mini, Yanzu Zaki Iya yi mini duk wata tambaya dake a cikin zuciyar ki" Numfasawa tayi kafin ta soma jera mashi tambayoyi akan abubuwan da suka cunkushe mata kwakwalwar ta.
"Ka ce mini kai ɗan tsohuwa Tamira ne! Dama tana da ɗa? Da farko ta ta6a faɗin cewa da ace ta ta6a yin aure da tuni ta yi jika dani, daga bisani kuma ta gaya min cewa Itama prisoner ce kamar mu tun tana ƙarama aka kawota gidan kurkukun ƙaddarar harta girma ta yi aure harta haifi ya'ya da jikoki, kaina ya ɗaure, Kuma meyasa ku ke son ɗaukar Fansa? Sannan taya za'ai mu iya ganin ƙofar da zata fitar damu daga Cikin kurkukun, Bayan haka inaso insan ta yadda zamu taimaki ɗan uwanmu Danish Ya dawo Cikin hayyacin shi, menene dililin dayasa ake kira na da Ƙaddarar Kurkuku? Itama ƴar uwata Batul Akwai sunan da aka sanya mata a bayan rigarta Heart beat of prison, na jima inason sanin meyasa aka banbanta mana uniform ɗinmu dana sauran Ƴan uwanmu? Suwane ne keda gidan kurkukun nan? Waye ya sadaukar dani?" tun da ta fara jera mashi tambayoyi bai katse ta ba, har sai da takai ƙarshe tukunna ya soma magana a tsanake.
"Kamar yarda na faɗa maki da farko haka zan maimaita maki a yanzu, Ni ɗa ne ga tsohuwa Tamira! Ni kaɗai ne ɗa da ta haifa, wata'ƙil ta gaya maku hakan ne gudun kada asirinta ya toni a fahimci cewa Kamar tana son kusan wani abu dangane da rayuwar ta ne, wanda Yin hakan Babban matsala ce agare ta, Shiyasa ta ke yi maku ƙarya a kalamanta, Dalilin daya sa muke son ɗaukar fansa Saboda mahaifi na da su ka yi silar mutuwar shi, Babban malami ne wanda duniya tasan da zaman shi ana kiran shi da Habibullah, Yana ɗaya daga cikin manyan