Header Ads
Showing 66001 words to 69000 words out of 287659 words

Chapter 23 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1779

Ads at the middle of Article

nuna Deeja da hannu"Zoki wuce, Ki jira idan ya gama ki shiga" maƙe kafaɗa deeja tayi"babu inda zanja, meye naki aciki?
Wata irin gigitacciyar tsawa angel ta daka mata, Saboda tsabar ruɗi a firgice danish Ya koma Cikin toilet din,"
Da gudu Sauran Ƴan uwansu dake acikin ɗakin suka faɗo Toilet area ɗin, Haris da su aziza,
"Meke faruwa ne"? Javed ne yae tambayar, Batool tace"Nima bansani ba, ranta ya 6aci ne saboda na faɗa mata cewa idan uziri ya kama mu kuma babu wuri mutun biyu suna shiga toilet ɗaya shine take fushi,"
Harara haris ya watsa mata tare da cewa"To ke meye naki aciki da har zaki nuna 6acin ranki akai"?
Matsawa angel tayi Saitin inda haris yake a tsaye, Kafin ta soma magana atsanake,
"Saboda hakan bai dace ba, Koda kuwa Namiji da namiji ne su shiga toilet ɗaya balle kuma Mace da namiji, bazan bari ana aikata 6arna batare dana hana ba, don haka daga rana irin ta yau, idan har na ƙara kama mutun biyu acikin toilet ɗaya, Saina Karanta ma shi charman dudu Cikin shi ya kumbura ya mutu kowa ya huta"

Jin wannan maganar ta angel yasa hankalin kowannansu ya tashi, musamman deeeja tuni idanuwanta sun cicciko tan da ƙwalla,

"Ya kike so muyi idan uziri ya kama mu, a lokaci ɗaya"? Hanna ce tayi mata tambayar,
"Sai ku matse koma menene ku ke ji, idan na ciki suka kammala suka fito sai mutun ya shiga"
"Ammaaaa......."kasa ƙarasa maganar haris yayi ganin tana nannaɗe hannun rigarta alamar za ta yi dambe,
"Abi Umarni na azauna lafiya, Shine kawai idan kuma mutun yace zaiyi mun gardama, yasan me zai biyo baya,"

Gaba ɗaya duk suka sha jinin jikinsu, juyawa tayi tare da kallon deeja"Ke kuma Munafuka, zoki wuce ki jira idan ya kammala ki shiga, ni dama sam ban yarda dake ba, da wasu idanuwanki tubarkalla kamar na kwartan mazuru, idan shi yana da ta6in hankali ai ke da hankalinki, Sullu6iyo kawai, zaki wuce kosaina Zubar maki da haƙoran gaba"? Jiki na rawa deeja ta ƙarasa fitowa daga cikin toilet ɗin Taja ƙopar ta rufe,

Kallon sauran ta yi"Kowa Ya kama harkar gabansa, kuma Allah yasa wani yayi gulmata acikin ku, Aljanata kamila zata faɗa mun ne, daga nan ni kuma zan tofa ma mutun charman dudu" takai ƙarshen maganarta tare da sa kai ta wuce su tamkar damisa, Ta nufi Cikin ɗakin sai da ta shiga ta zauna gefen gadonta, Taci gaba da tiƙar dariya, can kuma ta dakata da yin dariyar hawaye suka soma shararowa daga cikin idanuwanta,
Hannu biyu tasa ta dafe kanta, wani irin tsananin tausayinsu take ji, har cikin ranta take jin tsananin sonsu da ƙaunarsu, a halin yanzu babu wanda bata so acikinsu, saboda tausayinsu da take ji, ashirye take data taimaka masu wurin gyara rayuwarsu,

Jin motsin shigowar su Cikin ɗakin Yasa ta yi saurin share hawayen dake akan fuskarta, ta kishingiɗa saman gadonta,

A jere suka shigo kowa sai satar kallon Angel yake yi, cike da jin tsoronta, Ko zama ba suyi ba, Giants suka turo ƙopa suka shigo Hannunsu ruƙe da kayan breakfast ɗinsu, ba ƙaramin daɗi angel taji ba dama daren Jiya da wata irin matsiyaciyar yunwa ta kwana,

Bayan sun ajiye Masu farantan, kamar kullum Jiki na rawa suka Nufi saman Carpet ɗin kowa yayi zaman Cin tuwo, Suka zagaye trays ɗin,
Sai da duk suka hallara, Hada danish wanda tunda ya zauna Jikin shi keta kerma sam babu natsuwa attare da shi, Gaba ɗaya tsawar da angel ta daka masu ɗazu ta gama gigita shi,
Tun da suka fara Cin abinci, Wurin ya yi tsit baka jin sautin komai saina taunar abincin da suke yi, ganin nata ya kusa ƙarewa yasa ta fara tsantsani, can data lura danish ba wani cin abuncin yake yi ba, tsakurarsa kawai yake yi kamar baisan ci, da yake suna Fuskantar Juna, ta faki idon sauran ƴan uwan nasu, tayi musayar plate dana danish, ko da taga yana kallonta, saita zazzare mashi ido don kar yace zai anshe kayan shi,' lamarin yayi matuƙar ɗaure ma shi kai, yana ji yana gani tayi mashi musayar plate, ta ajiye ma shi nata data kusa Cunye, na shi kuwa a cike yake da abinci, bai dai ce komai ba, Yaci gaba da cin nata abincin data tura mashi,

Bayan sun kammala, Giants suka tafi da kayan abincin, Ganin Kowa ya nufi gado zai kwanta yasa tayi saurin cewa"Ku dakata" Tsayawa su ka yi tare da juyowa suna kallonta,
"From now on, when you finish eating food, no one will lie down and sleep, you have to exercise, doka ta ce duk wanda yaƙi bi kuma yasan me zai biyo baya,'
Natsuwa su kayi suna sauraronta, Haris ne yai kokarin cewa"Saboda me"?
"Saboda lalacin ku yayi yawa, idan kuna motsa Jiki zaku yi ƙarfi, "
"So kike kiyi iko damu"? Kafin ta bashi amsa aziza tayi saurin cewa"pls haris kayi shiru, kada ta karanta mana charman dudu, nidai zanyi abunda kike so angel,"
Murmushin gefen fuska angel tasaki tare da kallon su batool tace"what about u guys? Zaku yi ko kuwa"? Har suna haɗa baki wurin cewa"eh zamuyi komai kikeso" Kallon haris tayi"kaima dole kayi idan har kana son zaman lafiya, idan ba hakan ba ta kanka zan fara aiwatar da aikina, tare da aljanata kamila,"
Haɗe girarsa yai fuska a tur6une yace"Ae bance bazan yi ba"
Ƙumshe dariya tayi abakinta, daƙyar ta samu ta basar da dariyar, ta ɗaure fuska tana hura hanci,
"Sister ya ake yi toh baki faɗa mana yadda zamu motsa jikin ba"

"U will start running from wall to wall, untill i command you to stop, Idan aka kammala sai ayi Jumping,"

Amsa mata su ka yi da toh, jikin bango suka koma suka tsaya a jere, Kowa ya naɗe hannun rigarshi,
Komawa tayi daga bakin gadonta, ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, Cike da bada Umarni Tace"Idan Na ƙirga uku Sai ku fara" su ka amsa mata"Toh"

"1,2,3, Oya start" Da gudun gaske suka tafi Bayin Allah, Idan suka kai karshen bango sai su dawo sai su koma, har saida su ka yi kusan sau talatin tukunna ta basu hutu, zuƙunnawa su kayi a ƙasa, zufa ta ko'ina ajikinsu, Musamman danish kamar an tsamo shi daga Cikin ruwa, sae nishi suke yi,
"Lokacin yin jumping ya yi, Maza kowa ya miƙe afara tsalle sau talatin kowa zaiyi duk wanda ya kammala sai yaje toilet ya watsa ruwa," amsa mata su ka yi da toh, ta tsaresu da ido har saida kowa ya kammala tsallan nashi, sannan ta ƙyale su tace kowa ya watsa ruwa azo ayi fira,
Anan ta zauna tana jiransu, Bayan sun kammala, Jiki amace suka dawo cikin ɗakin Kowa Ya zauna saman gadon shi,
"Yau kin bamu wahala sister, amma naji daɗin Jiki na" batool ce ta yi maganar, Haris da deeeja sunfi kowa Jin haushin angel, saboda ta sanyasu aikin wahala, danish kuwa tuni bacci ya yi awon gaba da shi, sam basu saba da wahala ba,

Kallon su ta yi ɗaya bayan ɗaya tun daga kan danish dake bacci har zuwa sauran dake ta faman yin gyangyaɗi,

Gyaran murya ta yi masu gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kanta,
" Jiya kamar Kunyi mun wata tambaya ko'? har suna haɗa baki wurin cewa"tambaya akan me kanan"? Ta gefe ta kalle su "Kun manta? Ku tuna kun tambaye ni wani abu jiya,"
"Eh, muna so Ki bamu labarin rayuwarki," azeeza ce ta yi maganar,
"Gobe zan baku labarin rayuwata, Yau inaso Mu tattauna dangane da addini ne, Kallon juna su ka yi kafin suka dawo da hankalinsu kanta,
"Addini kuma? Menene ma'anar hakan"? Da ruɗi akan fuskar hibba ta yi mata tambayar,
Tana kokarin buɗe baki taci gaba da magana, Danish dake bacci ya kwatsa wata irin razananniyar Ƙara mai firgitarwa, " gaba ɗaya Hankalinsu Ya koma kanshi,
A zubure ya miƙe zaune Ya sanya hannayenshi Biyu ya daddafe kanshi, yaci gaba da fasa gigitacciyar ƙara, Da gudun gaske su haris suka sauko daga saman gadajensu. suka nufi gadon danish, Kowa ya shiga Lallashin shi suna bashi baki,
Angel kuwa sakin baki tayi tana kallon ikon Allah. lokaci ɗaya ranta ya bata cewar tabbas Danish ba shi kaɗai bane, Meyasa sai lokacin da take ƙoƙarin yin magana kan addini zai farka yana fasa masu ƙara? Da alama anyi hakan ne don a ɗauke masu hankalinsu daga kanta, gashi yanzu gaba ɗaya sun rasa samun natsuwa sun duƙufa suna lallashin shi,
Wani irin wahalallan murmushi angel tasaki tana kallon ikon Allah, wato da tsiya dai sai an dakatar da ita, jiya an kwaɗe mata kai da sanda yau kuma ta 6angaren danish aka biyo mata,
"Danish Pls can u talk to me? kana ganin fuskokin mu? Meya faru dakai? Atare suke jefa mashi tambayoyin nan, Angel ta kasa kunne tana sauraronsu,
"Danish ka yi mun magana meke damunka? haris ne yae tambayar yana shafa dogon wuyanshi, Sae faman kerma jikin shi yake yi, ga wata irin zufa dake tsastsafowa daga Cikin sumar kanshi, ya runtse idanuwanshi sosai, duk ya ciccije lips ɗinsa,

Zurfin tunani ta shiga yi, shin wata hanya zata 6ullo masu, tun da nan an toshe ta, sai yanzu ta ƙara yarda cewa akwai wata maƙarƙashiya, bakomai take tunawa ba face Wani American film da ta ta6a kallo na Magicians, a gidan aunty aneelerh, A cikin Film ɗin matsafa ne suke canza ma mutun tunaninshi su sarrafa shi, ko su sanya mashi tsafi a jikin shi, ko kuma suyi amfani da shi,' Jiya daga za ta yi magana an kwaɗe mata kai, kuma bata ga kowa ba, hakanan ta ke zargin tsohuwace kuma ga dukkan alamu zarginta ya tabbata tsohuwarce, sanan meyasa Basa son duk wani abu daya shafi Addini? A lokacin da ta kalli film ɗin ta ɗan shiga ruɗu harta tambayi aneelerh,
"Su matsafan ba'a iya yin maganinsu"? aneelerh tace"Allah shi ne maganinsu, idan yaso duk wannan 6acewar da suke yi sai kiga an kama su har an ɗauki mataki kansu, shiyasa ake so mutun ya kiyaye kuma ya dage da neman tsari awurin Allah, saboda su mutanene masu hatsarin gaske, ta kowace hanya zasu iya 6ullo maka," aneelerh tayi mata bayani akansu sosai, Natsuwa tayi tana bin ko'ina na ɗakinsu da kallo, tana ji acan ƙasan Zuciyarta kamar ta manta da wani abu, wanda ta gaza tunawa acikin kwakwalwarta, Aranta tana ji kamar ta ta6a kasance acikin gidan kurkukun ƙaddara, tsayar da idanuwanta ta yi akan red carpet ɗin da suke zama Su ci abinci kanshi, tunawa tayi da maganar aneelerh a inda tace"ɗaya daga Cikin alamomin matsafa, shi ne launin Ja, suna sanya jajayen kaya ko kuma A gidansu suna yawan amfani da jan abu kamar labule haka da sauransu,
Jinjina kai angel tayi tare da cewa"Tsohuwa tana sanya jajayen kayan, Kuma carpet ɗin ɗakin mu Shima ja ne, kuma duk in aka kawo mana abinci, a saman trays ɗin ana sanya janƙyalle a rufe shi, Menene ma'anar launin jan nan na gidan kurkukun ƙaddara? su Giants suna sanya Baƙaƙen kaya shima launin baƙi bako da yaushe yake kasancewa abu mai kyau ba, dole nayi kokari wurin gano ma'anar waɗannan kalolin guda biyu Black and Red, kuma dole Nayi bincike akan lalurar dake damun danish domin kuwa wannan ciwon nashi Ba Misophonia bace, Kirkirarta a ka yi domin shi kawai,

Hankalin angel fa yaƙi kwanciya, Saima ƙara ta shi da yake yi, Babban abunda take ji ma tsoro, Abunda take hasashe ya zamo gaskiya, saboda taji ance matsafa idan suka ɗauki mutun suna amfani da shi ne, Ko su cire sassan jikinshi, Ko su ɗibi jinin jikin shi, idan kuwa har hakane, To kuwa bata ga ta zama ba, duk da tana kokwanto akan hakan saboda su Batool sun faɗa mata cewa ba'a ta6a cutar da su ba, Kuma suna samun abinci, Matsafa ina suka ga lokacin ba mutun abinci, da zarar sun kamo shi kashe shi suke yi bayan sun gama kwashe amfanin jikin shi,

Duk ba wannan ba, tambayoyi da yawa da take neman amsarsu WACECE TSOHUWA? SU WANENE GIANTS DAKE ZUWA KAWO MA SU ABINCI? A INA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA YAKE? TA FARA HASASHEN GIDAN KURKUKUN BA'A CIKIN NIGERIA YAKE BA, ZAIYI WUYA MA ACE ACIKIN GARI YAKE, SHIN SU KAƊAI NE ACIKIN GIDAN KURKUKUN KO KUWA AKWAI WASU MUTANAN? MEYASA AKA HANASU SHIGA CIKIN SHI"?

ta yi zurfi a cikin tunaninta muryar batool ta katse ta da cewa"Angel har yanzu baki yi bacci ba"! Firgigit tayi tare da kallon batool dake a zaune gefen gadonta hannun ruƙe da fitila, tsananin mamaki ne ya kamata, ganin duk sunyi bacci, ita kaɗaice zaune saman gadonta, batasan tsawon lokacin da ta ɗauka ba, Sai da batool ta fargar da ita, ashe dare ya yi har sun kwanta, ita a yadda tabarsu suna akan danish dake ta fasa ƙara, Yanzu ga danish ɗin nan kwance cikin bargonshi sai bacci yake yi, su azeeza ma duk sun kwanta,
"Yansu na farka zan shiga toilet shine na hango ki a zaune, nayi mamaki" murmushin yaƙe angel ta sakar mata tare da cewa"Bana jin bacci ne, ya jikin danish"?
"Ya ji sauƙi, baki ga ma har yayi bacci ba" tayi maganar tana haska gadon danish ,
Gyaɗa kai angel tayi"Nima yanzu zan kwanta, kije ki shiga toilet ɗin,"
Batool tace"ae har na shiga na fito, zan wuce ne na lura dake a zaune"
Shiru angel ta ɗanyi, ganin kamar tana acikin damuwa yasa batool tace,"Baki da lafiya ne? Ko wani abu na damunki"?
da sauri angel tace"bakomai, kawai ina tunanin rayuwar duniya ne"
"Yau da kika samu motsa jiki, ga6o6in jikina sai ciwo suke yi mun, amma yanzu dana ta shi daga bacci sai naji daɗin jiki na,"
Angel tace"idan kuka saba kullum zaku ji dadin jikin ku, zai saki sosai ba'a son mutun daga yaci abinci ya kwanta, anfi son kadan motsa jikinka, "bayani tayi mata dangane da amfanin motsa jiki, batool tace"Daga yanzu duk in muka ci, abinci zamu dinga yi, bari naje na kwanta" tana kokarin miƙewa angel ta yi saurin ruƙo hannunta, kallonta batool tayi tare da cewa"Lafiya"?
"So nake na tambaye ki, A gidan kurkukun nan Ana kiwon kaji ne"? Cikin rashin fahimtar zancanta, batool tace"Kiwon Kaji kuma? Meye ma'anar hakan"
Dafe kai angel tayi"Ina Nufin kaji da ake kawo mana muna ci kusan kullum, Ana kiwonsu ne a gidan nan ne? Still batool bata fahimci zancenta ba, ta dai san kaza da ake kawo masu a soye suci, amma batasan ma'anar kiwon ba,
"Shikenan tunda baki sani, Amma kin ta6a shiga cikin kurkukun nan? Naga ranar da aka kawo ni, Ni kaɗai nafarka acikin ɗakin nan, Ku kuma daga waje kuka shigo Ciki, Ina kuka je ne"? Ta yi tambayar tana kallonta"
"Bazan iya tuna komai ba," cike da takaici angel tace"Komai baki sani ba ke, to faɗa mun a gidan kurkukun nan ku kaɗai ne kuke rayuwa a cikinsa"?

Girgiza kai tayi"A'a bamu kaɗai bane, Kinga wannan numbobin na bayan rigunan mu, akwai me 400," waro ido waje angel tayi muryarta har shaƙewa take yi wurun cewa"Are u serious"? Ɗaga mata kai batool tayi alamar Eh, taci gaba da cewa"idan zan iya tunawa kafin zuwanki, Munyi rayuwa acikin wasu Prisoners ɗin waɗanda Ke rayuwa a killace cikin kurkukun nan, bamu kaɗai bane, muna da yawa," mamaki ƙarara akan fuskar angel ta kuma cewa"Amma ku meyasa aka ware ku daga Cikinsu"? Batool tace"nima bansani ba,"
"Yanzu faɗa mun, duk wani abu da kika sani game da kurkukun nan,"
"Bansan komai ba"
"Ke dai ki tuna" shiru batool tayi tana kokarin tunano abunda ta sani, tsawon lokaci kafin ta soma magana
"Idan aka ɗauki mutun ba'a dawo wa da shi, idan muka tambayi tsohuwa ina ƴan uwanmu suke waɗanda aka ɗauka daga Cikinmu, sai tace mana mu kwantar da hankalin mu, Suna nan cikin ƙoshin lafiya wata rana zasu da....." bata kai karshen maganarba, ta miƙe da sauri ta dauki fitilarta, ko kallon angel ba ta yi ba ta wuce saman gadonta ta kwanta,
Zuba mata ido angel tayi Cike da mamakin yadda ta miƙe zumbur ta tafi batare da ta ƙarasa maganarta ba, kodai itama an zungureta ne? Ta yi tambayar a cikin Zuciyarta,

Kafin ta yi Shirin kwanciya, kamar kullum ta ɗaga hannayenta sama tana yi masu addu'o'i, Hada daddynta kullum ne bata mantawa da shi, Yana acikin ranta..........🥺

*ANEELERH*

Mami ce zaune gefen gadonta har ta yi shirin kwanciya, jikinta na sanye da Sleeping gown, ta ƙura wa screen ɗin wayarta ido,
fitowa abie Yayi daga Cikin toilet yana gyara wuyan jallabiyar jikin shi,
gyaran murya yayi mata ta ɗago tana kallon shi, fuskarta da alamun damuwa tace"Ina ta kiran aneelerh bata ɗaga ba, "
"Bansan meyasa kika tashi hankalin ki ba, sai kace wadda ta tafi wata uwa duniya,"
"Dole na damuwa, saboda ni bata faɗamun cewa a can xata kwana ba, kuma na kira layin Uncle bash ɗin tana ta ringing bai ɗaga ba, itama dr Aisha na kira layinta bata ɗaga ba, idan acan zata kwana ae yakamata su kira su sanar dani,"
Murmushi abie ya saki"Na lura ba ƙaramin ji kike da ƴar nan taki ba, Ko da yake nasan saboda wa kika hana idonki bacci,"
"Bai wuci kace saboda baby junaid ba, ae dole na damu da jika na, shi kaɗai fa nake da shi kwallin kwal an tafin mu da shi, sai da nace tabarmun shi a wurina, amma ta kafe akan saita je can da shi,"
"In banda abunki, taya

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads