Header Ads
Showing 270001 words to 273000 words out of 287659 words

Chapter 91 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1758

Ads at the middle of Article

da bai wadata sosai ba"

Jin motsin shigowar su Yasa ta yi saurin fuskantar su, sai faman murza idanuwansu su ke da yatsun hannayensu, Parveen sai hamma ta ke Yi bakinta hada miyan bacci.

"Sai da nace maki ban da Azeeza meyasa kika tado ta"? rai a6ace ta yi maganar idonta akan Azeeza, da Batul ta ruƙo hannunta

"Bani na tada ta ba, Ina cikin tada su Deeja ta farka tana Jin fitsari shi ne na ruƙo hannunta muka shigo atare" mayar da idanuwanta tayi akansu, Kusan su dukane banda Jamimah ita kaɗaice basu Tada ta ba, tana can ƙudundune Cikin bargo saman shimfiɗar su.

"Wai lafiya aka tayar da mu daga bacci? Ko an kawo abinci ne"? Parveen ce ta yi tambayar fuskarta a yamutse,

Harara Angel ta watsa mata"Halan mafarkin shi ki ke cikin Yi aka tada ki, shiyasa kike tambayar ko an kawo abinci" Kwa6e fuska ta yi ba tare da tace komai ba, Sai faman murza ido su ke yi, fuskokin su a tur6une.

"Hakanan muna yin baccin mu mai daɗi an tada mu," hannah ce ta yi maganar tana murgaɗa ƙaramin bakinta.

Jan hannun Azeeza Batul ta yi zuwa cikin toilet su ka shige.

"Ganin Yadda su ke ta kwa6a magana ransu a6ace saboda an katse masu bacci, har suna cewa ta tsare su da ido, idan ba abunda zata gaya masu zasu koma ɗaki su kwanta ne" Har sun yunƙura zasu Juya muryar batul ta katse masu hanzarinsu da cewa"AN SAMU ƘOPAR DA ZAMU GUDU" A ruɗe Suka dakata da yin tafiyar suna kallonta, tamkar saukar aradu Haka maganar ta dirar masu acikin kunnuwan su, wani irin kallon rainin wayau su ke binta da shi, ƙarasa fitowa ta yi daga Cikin toilet ɗin hannunta ruƙe dana Azeeza.

"Idan ku ka natsu zamu Yi maku bayanin komai" ga dukkan alamu sun shiga ruɗani duba da irin kallon da su ke yi mata.

"Wannan maganar daga jinta a cikin mafarki ake yinta ba'a gaske ba" Hibba ce ta yi maganar, idanuwanta kamar na mashayin giya.

Sarah tace"Nima nafi tunanin mafarki ne mu ke yi, idan har ta tabbata dagaske mu ke ganin batul da ta yi maganar to kuwa tabbas Ganyen da muke ci ya fara zautar da ita, shiyasa ta fara mana sambatu"
Sarah na rufe baki Hannah tace"ni bazan tsaya sauraron wannan shirmen ba, Kun ga tafiyata"

ta yi magnar tare da nufar ƙopa zata fuce da sauri batul ta saki hannun azeeza tai wuff ta ruƙo wuyan rigar Hannah ta janyo ta tare da dawo da ita ta jinginar jikin bango.

Angel ta kasa kunne tana sauraron su, gani ta ke kamar ba za su iya fahimtar su ba koda ace sun faɗa masu, saboda basu ɗauki abun serious ba.

"Kun tasa mu agaba kuna kallo kamar kun samu madubi, idan ba za ku buɗe baki ku yi magana ba, Ni zan koma ɗaki" acewar Rubina.

"Ki yi masu bayani mana ko ni zan yi masu"? Batul ce ta yi ma Angel magana.

Gyaran murya tayi Kafin ta sassauta muryarta ta yadda sautin ba zai fita sosai ba, kamar maiyin gulma, ta soma fayyace masu komai dangane da hasashen da su ke yi akan Kalaman tsohuwa tamira.

Sun natsu suna sauraronta, Yadda suka tattara hankulan su akanta sai ta yi tsammanin ko sun Fahimci inda zancen nata ya dosa ne, sai da ta kai ƙarshen Maganar, kusan atare suka haɗa baki wurin jan tsoki.

"Kawai don ta yi kalami sai asamu ƙofa, sai ka ce ba ku san wacece tsohuwa tamira ba, In banda ma rainin wayau taya za'ace mune makullan buɗe ƙopa? Ƙanzon kure ge ne wannan" Parveen ce ta yi maganar tana hura hanci ita ala dole an 6ata mata rai.

"Da nasan abunda zaku gaya mana kenan Allah da ban farka ba lokacin da batul taje tada ni daga bacci" acewar Eve

"Ni dama kwanakin nan ban yarda da ku ba, Ku biyun nan Batul da Angel, damuwa tasa kun fara zaucewa," Yasmince ta yi maganar , kamar zasu rufe su da duka Kowa Da abunda ya ke furtawa, Mutun Biyu ne a cikin su basu yi magana ba, Deeja da ta jingina kanta Jikin bango ta lumshe idanuwanta sai Azeeza da ke a tsaye bakin ƙofar toilet, Ta kasa kunne tana sauraronsu duk bata ganin su.

"Koda ace baku yarda da maganar mu ba, Inaso ku bamu dama, Mu fara neman ƙofar da ke a cikin ɗakin mu. Idan ba'a ganta ba ni na yarda Ku yi min duk abunda ya dace dani," cikin sanyin murya Angel tayi masu maganar.

"Deeja! Banji kince komai ba? Ke baki faɗi naki ra'ayin ba, dangane da kalaman tsohuwa Tamira,"

Daƙyar deeja ta iya buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci ta ɗaura su kan fuskar Batul da ke Yi mata magana, da buɗar bakin ta sai cewa ta yi"Oh wai da ba mafarki bane? Baki asake Take kallon su, Dafe kai batul tayi da hannu ɗaya"Wai meye haka? Idan har ba ku ɗauki maganar nan serious ba kun bamu haɗin kai tayaya zamu Iya ganin ƙofar...."

Tun kan ta ƙarasa maganar Rubina tace"Ae ba za ku ta6a ganin ƙofa ba, hasashen ku akan kalaman tsohuwa tamira Wasiƙar jaki ce wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, in banda wahalar da kai ta ya tsohuwa Tamira zata Taimake mu? Ku yi amfani da kwakwalwarku mana, koda yake dama ba cikakken hankaline damu ba, " Murmushin takaici Angel tasaki Jin abunda Rubina tace, wato dama basu da cikakken hankali.

Muryar azeeza ce ta janyo hankalin su ga kallonta.

"Ni ina goyan bayan maganarsu Angel, tsohuwa tamira tana son taimakon mu, kafin tabar cikin mu, Ta yi mana abubuwan da zata faranta mana rai wanda ke nuni da za ta yi kewar mu sanna ta faɗa mana cewa tana so wata rana mu tuna da ita acikin rayuwar mu, duk mutumin da ya furta maka wannan kalami dole asamu ƙaunarka da tausayinka acikin zuciyarshi, yakamata muyi nazari sosai, Koda ace bazamu yarda da maganar su Angel ba dangane da hasashen su akan kalaman tsohuwa, Kada muƙi bin maganarsu Mu jaraba duba ko'ina na cikin ɗakin, kafin mu yanke hukunci, Sannan inaso na tuna mana wani abu, kamar yadda Angel ta faɗa mana ba'a ganin wanda ya halicce mu, That mean idan zamu samu taimako daga wurin shi ba kai tsaye zai bayyana ba don ya taimake mu, sai dai Ya haɗa mu da wanda zai taimaka mana, ko ya fahimtar damu ta wata hanyar Kamar dai yadda Angel tayi mafarki da kalaman tsohuwa tamira.........." tun da Azeeza ta soma Yin magana Hankalinsu ya dawo kanta, Ko ƙyafta idanuwan su basa yi, Sun natsu suna sauraronta, Musamman Angel tsabar mamaki yasa ta saki baki tana kallonta, Yarinyar Allah ya yi mata baiwa, Ita takasa fahimtar dasu yadda zasu gane sai gashi kalaman Azeeza sun yi ta'asiri acikin zukatan su.

Nauyayyiyar ajiyar Zuciya kowan nan su ya sauke, sarah tace"yanzu abunda za'ae mu fara neman ƙofar! idan Allah yasa aka same ta sai mu fara tunanin ta yadda zamu tattara makullan buɗeta,"

Atare suka haɗa baki wurin cewa"Haka Ya dace, "
"ita fa azeeza da bata gani? Ko dai in kai ta ɗaki ta kwanta"? Deeja ce ta yi maganar.

Tun kafin Wani ya bata amsa Azeeza ta bubbuga ƙafafuwanta Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"wlh ba in da zan je, dani za'ayi komai kawai don anga bana Iya gani shine za'a ware ni" ganin zata ja masu hayaniya yasa Angel yin saurin kai hannu ta janyota zuwa jikinta, ta rungumeta tana faɗin"Its okey azeezata, Ai dole ma ayi tafiyar nan da ke, kwantar da hankalin ki" ajiyar zuciya azeeza ta sauke tare da sanya hannayenta Biyu ta ƙanƙame Angel.

"Kafin Mu fara bincike, Yakamata Mu fara Yin addu'a akan Allah ya bamu Ikon ganota Cikin sauƙi," Angel ce ta basu shawarar Yin hakan, atare suka ɗaga hannayen su Sama ta dinga jera masu addu'o'i suna amsa mata da ameen, bayan sun kammala Hibba tace"Bafa lallai yakasance ƙofa ta ke nufi ba, A kalamanta, " Batul tace"ae shiyasa zamu fara dubawa, Kunga idan ba'a samu ƙofar ba, sai muyi wani tunanin na daban"


Gyaran Murya Angel ta yi Hankali ya dawo kanta.

"Zamu Raba kan mu wasu zasu shiga toilets, wasu ɗaki, Amma na ɗaki dole su ɗaga gadajen mu, don ina hasashen ƙofar ta sirri ce, ta in da bamu tsammani zamu Iya ganinta, don haka mu sanyawa ran mu cewa har cikin Tukunyar fulawa zamu Iya samunta, kota jikin bango, kota ƙarƙashin gado, kai harma ta inda ruwa ke bi ya wuce, amma fa Wanda zasu duba Ƙarƙashin gadajen mu dole su yi taka tsantsan saboda ana ganin duk wani motsin mu, don haka Na ɗaki mu bari sai gobe zan shirya mana wasan Ƴar 6uya, zamu dinga shigewa da sunan mun 6oye kunga zasu yi tsammanin wasa muke Yi, ba wani abu muke nema ba"

Murmushi su ka saki gaba ɗayan su, kafin daga bisani Batul ta rarrabasu zuwa gida uku, Nan fa suka baza cikin toilets ɗinsu suna neman ƙofar nan, Angel tana ruƙe da hannun Azeeza saboda makantarta, Uban gumi suka haɗa akan fuskokin su, Sun bada himma sosai, wurin neman ƙopar ba inda basu ɗaga ba, hatta tukunyar fulawar da ke a toilet ɗinsu saida batul da Deeja suka haɗa ƙarfi wurin ɗaɗɗagota amma basu ga komai ba, Bangon da aka jingine ta dashi ashafe Ya ke haka ƙasantama Ashafe Yake babu wata ƙofa, Kamar zasu fashe da kuka su ka sauke tunkunyar, furennin cikin ta ma duk sun bushe babu mai lafiya, Ko'ina Ciki da bai na sashen toilet ɗinsu saida suka bincika amma babu ƙopa, A ƙarshe sarah Ta hango masu Tagogin nan da ke a saman ceilling waɗanda tun farkon zuwan Angel ta yi tozali dasu a garƙame da kwaɗo, Kowani toilet akwai tagogin saman ceilling guda biyu, hankalin su gaba ɗaya ya karkata akan tagogin ransu ya gama basu cewar Za'a samu hanyar da zata 6ullar da su wajen kurkukun, Sai dai basu san ta yadda zasu Iya kaiwa gare su ba saboda basu da tsauni tsayin su kuma ba zai kai su ba, hatta Sarah Da tafi su tsawo bazata Iya koda ɗaga hannu ta ta6a jikin su ba, Bayan haka kuma basu da Makullin da zasu Iya buɗe tagogin, daga bisani tunani su ya canza akan Su nemo makullan buɗe tagar, A daren ranar basu koma bacci ba, Saboda Aikin neman makulli, Sunci baƙara wahala ga bacci a idonsu amma Sun nace akan neman makullai, wasa wasa har Gari Ya waye suna aikin neman makulli, A ƙarshe da su ka galabaita, don dole suka haƙura, Ga yunwa suna Ji ga bacci a idanuwansu.

A saman floor na sashen toilets ɗinsu, Kowan nan su Ya samu wuri ya zauna suka fuskanci juna, Sai haki suke Yi kamar waɗanda suka Sha Gudu, Baccin wahala ne Ya ɗauke su mai nauyi, duk sun ɗaɗɗaura kawu nan su saman kafaɗun Junansu, Baka Jin sautin komai saina minsharin su.

Daga cikin ɗakin su muryar Jamimah ce ke ta ƙwala masu kira, babu mai jinta, farkawarta kenan daga bacci, Hankalinta atashe ya ke ganin babu su asaman gadajen su, saukowa ta yi daga saman gadonta, tare da nufar Sashen toilet ɗin su, shigar ta keda wuya ta yi arba dasu zazzaune suna bacci, Mamaki ne ya kama Jamimah, ganin su anan maimakon saman gadajen su, ƙarasa shiga ciki ta yi a yayin da ta ke leƙa fuskokin su don taga Idan baccin gaske su ke yi ko kuwa tsokanar ta su ke Yi, Kallon ƙurulla jamimah take binsu dashi, adai dai saitin fuskar Angel ta tsayar da eye balls dinta, muryar ta ƙasa ƙasa ta furta"My Genie" shiru bata amsa mata ba, da ta fahimce cewa dagaske baccin su ke yi, Sai ta zauna tare da kwantar da kanta saman laps ɗin Angel ta lumshe idanuwanta kamar maiyin bacci, Tsawon Lokaci babu wanda ya farka, Sun saki baki suna bacci.

A firgice Parveen Ta farka tana ambaton"Nagansu wlh nagansu" Sautin muryarta ne Ya farkar dasu Angel a fujajen su ka wawware Idanuwansu masu ɗauke da bacci suna kallon Parveen, Har suna haɗa baki wurin tambayar Ta"Makullan kika gani? a ina su ke"? Yawu ta haɗiya tana faman Zare ido, tare da ƙare masu kallo, Sam babu natsuwa atattare da Ita, Muryarta Ashaƙe tace"Kamar mafarki na yi nagan su a cikin ƙasar tukunyar fulawar nan, Makullan........"

Tun kan ta ƙarasa maganar Zumbur suka mimmiƙe har suna bangaje juna wurin shiga toilet ɗin Saboda tsabar sauri, Jamimah batasan Kan me suke magana ba, binsu kawai ta ke Yi kamar bindi.

A Gaban tukunyar fulawar Su ka zuzzuƙunna, Deeja da batul na ƙoƙarin tsoma hannu cikin ƙasar Angel ta dakatar dasu ta hanyar yi masu magana"Bana so acire furennin nan saboda raine dasu, Ina gudun kada silar cire su su mutu......" Bata kai ƙarshen maganar ba, Deeja ta tari numfashinta"A halin da muke cikin yanzu bamu buƙatar furanni, ganinsu ma ƙara tayar mana da hankali ya ke yi, don haka cire su zamuyi" ba tare da 6ata lokaci ba, Mutun Biyar ne su ka tsoma hannayensu Ciki, duk suka tsige furennin tare da jefar dasu ƙasa.

Hankalin Angel sam ba akwance ya ke ba, Saboda ta yi believing da furannin rai Ne dasu, Ko da su Deeja su ka jefar dasu Ƙasa da sauri ta zuƙunna ta sanya hannu ta ɗauki furen daddynta dana Aunty aneelerh hada ƙaramin furennin nan, Har zata miƙe idonta Ya sauka Akan Dogon furen nan da ganyen shi ya koma baƙi, yanzu ya koma asalin colour din shi, Punch pink Ya ciza sosai, hakanan ta dinga jin gabanta Na faɗuwa, Ayayin da ta ke kallon shi, Kasa miƙewa ta yi har saida ta ɗauke shi ta hada da sauran furennin da ke a hannunta, tukunna taji Hankalinta Ya kwanta.

Fasa ƙara Azeeza Tayi tare da faɗin

"Mun samo shi! Gashi nan Makulli ne" jin muryarta Yasa Angel matsowa kusa dasu, Hankalin kowa Akan hannun Azeeza Ta damƙe wani abu dake a nannaɗe Cikin ƙasa, Wani irin farin Cikine Ya bayyana akan fuskokin su, Tun kafin Ta buɗe masu tafin hannun nata su ga menene.

A hankali Azeeza Ta ware tafin hannunta, Ta soma kakka6e ƙasar da ke nannaɗe da abunda ta damƙo, ko da ta kammala Kakka6e ƙasar jikin shi, Murnar da su ke yi ta koma Ciki, Ashe jijiyar fure ce, tsabar takaici Yasa kowaccen su ta dafe goshin ta da hannu, Ƙululun bakin Ciki Ya tokare masu maƙoshin su, Ji su ke kamar su rufe Azeeza da bugu, don ba ƙaramin sanya rai su ka yi ba, Kamar masu zaman makoki Haka suka zazzauna Cikin toilet ɗin Abun duniya ya ishe su, Jamimah ce kaɗai a tsaye ta ruƙe qugu Tana bin su da kallo.

"Wai ni kun barni aduhu me ake nema ne? Duk kun cire mana furennin mu, Genie Ki fada mini," hada ƴar shagwa6arta

Ɗago da ido Angel ta yi tare da kallonta kafin ta miƙa mata hannu"Zo nan" matsawa ta yi kusa da ita, Ta sanya hannu biyu ta janyota zuwa jikinta

"Yaushe kika farka daga bacci bamu sani ba"? Yatsina fuska ta yi"tun ɗazu na farka ina ta kiran sunayen ku babu wanda ya amsa mini, Sai da nazo sashen toilet tukunna nagan ku kuna bacci, ni kun barni a ɗaki"

Harara Azeeza ta watsa ma Jamimah kafin ta soma kwaikwayon maganarta, salon jan faɗa, Hakan ba ƙaramin dariya ya basu ba.

"Yanzu fa ba lokacin Yin nishaɗi bane, Yakamata Mu nemi mafita, Ni dama tun farko raina bai bani cewar Akwai wasu makullai ba, Mu ɗin dai mune makullan, Ƙofa ce kaɗai zamu gano, Saboda a jawabin da tsohuwa Tamira ta yi mata cewa ta yi Mu ɗauka cewa mu ɗin makullan Wata ƙopa ce guda ɗaya wadda zata sama mana farin ciki, To kunga anan tana nufin we're the keys da zamu buɗe ƙofar" Angel ce ta yi jawabin

"Ni kuma aganina akwai makullan, Ma'anar abunda ta ke nufi, Mu zamu haɗa hannu don mu gano su, Sa'annan waɗannan munafukan tagogin da suka zuba mana ido suna kallon mu, Ina zargin ƙofar tana A cikin su," Deeja ce ta yi maganar, Kowa sai tofa albarkacin bakinsa ya ke yi kamar masu gabatar da shirin wasa ƙwaƙwalwa.

"Ni ma nafi hasashen acikin su ne za'a samu ƙofa, saboda su kaɗai ne hanyoyin da zasu Iya 6ullewa wajen ɗakin nan" Acewar Hibba.

"Ku dakata, Kada Mu ɗaura buri akan waɗannan Tagogin, Har yanzu fa akwai wuraren da bamu Bincika ba, Na farko akwai ƙarƙashin gadajen mu, Da kuma ɗakin tsohuwa Tamira" Yasmin ce ta yi maganar, Rubina tace"Ai babu ta yadda za'ai mu iya buɗe ɗakin Tsohuwa Tamira, tun da mu ke bamu ta6a shiga ɗakin ba, saboda kullum agarƙame ya ke kuma babu makulli ta waje balle muyi tunanin balle shi mu shiga"

Gaddama ce ta 6alle atsakanin su kamar za su yi faɗa kowa Ya kafe akan tashi shawarar, Sai tada jijiyoyin wuya suke Yi, Ko yunwar cikin su basa Ji ga Jikinsu da ke ta tsami saboda rashin wanka, Hayaniyarsu ta cika ko'ina, ganin zasu hargitsa mata lissafine yasa ta dakatar dasu ta hanyar daka masu tsawa, Nan fa kowa yaja bakin shi yai shiru, Hankalinsu ya koma kanta, Miƙewa tayi tsaye kamar malami agaban ɗaliban sa, A tsanake ta soma magana.

"Idan har mu ka rasa natsuwar mu to kuwa ba zamu ta6a Iya gano ƙofar nan ba! Mu kan mu hankalin mu ba a kwance ya ke ba, ta ya ya ku ke tunanin zamu Iya gano ƙofar bayan mun ƙi haɗa kan mu, mu sanya natsuwa wurin bincikota"? Ta jefa masu tambayar tana ƙare masu kallo, duk sunyi ƙuri da idanuwansu,

"Maganarki gaskiya ce Angel, komai yana buƙatar kwanciyar hankali da natsuwa, Yanzu ki faɗa mana me ya kamata mu yi? Tun da kinfi mu kaifin basira"

Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, Jin an wasa ta, Miƙa ma Jamimah furennin dake a hannunta tayi tare da cewa"Ruƙe mini su My little sis" Kar6ar furannin Jamimah ta yi a hannunta.

"Abu na farko da yakamata Mu fara yi shine mu tsaftace jikin mu, ta hakanne zamu Ji daɗin Jikin mu brain ɗinmu ta yi fresh, mu samu natsuwar fara yin bincike na hankali, nasan kafin mu kammala

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads