Showing 237001 words to 240000 words out of 287659 words
Chapter 80 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
daurewa kawai take yi,
"Zan faɗa maki Angel, amma kiyi min alƙawarin, ba zaki sanya damuwa aranki ba....."
jinjina kai Angel ta yi tare da cewa
"Nayi maki alƙawari" numfasawa deeja tayi Cikin ƙanƙanin lokaci ta labarta mata dukkan abunda ya faru, tun daga kan zuwan tsohuwa Zafreen, har izuwa sandar data ɗaura mata asaman ƙirjinta da kuma abunda ya faru bayan tafiyar zafreen!" Lamarin yayi matuƙar girgizata, Hankalinta yai mugun tashi, zuciyarta har wani tafarfasa take yi tamkar zata 6allo daga ƙirjinta saboda tsabar bugun da take yi, Idanuwanta sun kaɗa launinsu ya ciza sosai.
Hannu biyu tasa ta dafe kanta, muryarta na kerma ta shiga ambaton
"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un!
Duk addu'ar da tazo bakinta karanto ta ta ke yi cikin fitar hayyacin duk don ta samu ta tsayar da zuciyarta daga tafarfasar da take yi mata, ta kuma samu sassaucin raɗaɗin da take ji, idan ba haka ba, ita kanta bazata Iya sarrafa ta ba, zata ƙara yunƙurin kashe kanta ne, kamar yarda ta yi ɗazu.
Deeja sai tausarta ta ke yi tana bata baki akan su yi haƙuri, su lallashi junansu, tun da basu da yadda zasuyi, a ƙalla sun ɗauki kusan minatuna talatin, zuƙunne a ƙasa suna jimami, a ƙarshe ma sai suka rungume junansu, hakan da su ka yi ba ƙaramin sanyaya musu zuciyarsu ya yi ba.
Raba jikin su su kayi daga na juna, idanuwansu sunyi luhu luhu da su,
"Angel yakamata muje mu kwanta, mu yi bacci muma, inyaso gobe da safe idan su azeeza suka farko, sai mu ƙara duba jikin su, wlh na tausaya musu sosai, Musamman Jamima da ta rasa haƙorinta ɗaya......"
Muryar Angel ce ta katse ta"babu komai akwai Allah, akwai kuma mutuwa da hisabi, ae Allah ba azzalumin bawansa bane, Yana ji yana gani, a sannu zai bi mana haƙƙin mu, naji zafin tafiya da aka yi dasu haris, saboda rashin imani da tausayi hada majnoon suka tafi ƙaramin yaron da ba cikakken hankali ne dashi ba, Allah kaɗai yasan ina zasu kai su, me zasu yi masu, Hmmmmm, in sha Allah bazan gaji dayi musu addu'a ba, Allah ya kare su aduk inda zasu kasance, duk runtsi duk wuya idan suna da rabon ƙara shan ruwa aduniya, duk irin azabtarwar da zasu yi masu, zasu rayu ne! Bansani ba zamu ƙara haɗuwa da su ko kuwa shikenan silar rabuwar mu kenan........" ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta, hakan yasa ta kasa ƙarasa maganar, ta ɗan dakata tana mayar da nunfashi, kafin ta samu ta dai dai ta maganarta,
"Zan yi mana addu'a dukkan mu idan mutuwa sauƙi ce agare mu, Allah ya ɗauki ran mu mu huta, don banga amfanin irin wannan rayuwar da mu ke yi ba, Da farko na yi mana kwaɗayin mu samu ƙopar da zamu gudu daga cikin kurkukun nan ko dan ku ɗanɗani rayuwar ƴanci, amma yanzu na zauna nayi wani tunani, Rayuwar tamu gaba ɗaya atare da kurkukun ƙaddara take, saboda ko mun samu hanyar tsira zasu cigaba da bibiyar mu ne, saboda waɗanda suka sadaukar damu na jinin mu ne! Suna atare da mu, ba zama arasa samun wasu daga Cikin su ba acikin kurkukun ƙaddarar nan! Duniyar nan acike take da ruɗani, wai har na jinin ka ne zai sadaukar da kai? mahaifi ko mahaifiya! Ko wani danginka! Idan har hakane kuwa banga abunso ga rayuwar duniyar nan ba! Saboda babu gaskiya acikinta, halaka ce tsantsa, son zuciya da kwaɗayin abun duniya yasa mutane sun rufe idonsu suna aikata abunda suka ga dama, sun manta cewa dukkan mai rai mamaci ne, zamu yi kwanciyar ƙabari, sannan za'a tada mu domin yin hisabi, Ga duk mai hankali yasan cewa rayuwar duniyar nan bakomai bace, Duk wani abu daka mallaka da zarar ka mutu zaka rasa shi! dukansu kaf ba wanda za'a rufe ka da su acikin ƙabarinka, Iya halinka ne kawai zai cece ka, to wai su irin waɗannan mutanan makafi ne? Ko kuwa kurame ne? Abun da zai ba ka mamaki mafi rinjayen su, Sun sani su ke ta ke sanin, ko dabba tafisu tunani mai kyau, zuciya ta bushe, sun mayar da zalunci hanyar cin abincin su, duniya kawai suka sa gaba, Anata sharholiya an manta da mutuwa.......wa'iya zubillah! Ya Allah ka karemu daga fadawa hannun irin waɗannan azzaluman mutanan, Ya Allah ka shiga tsakanin mugu dana gari......"
Ruƙo hannunta Deeja tayi acikin nata"Angel, Bana so kiyi mana fatan mutuwa, saboda inaso mu samu hanyar tsira kodan mu tona asirin azzaluman mutanan da su ka cutar da rayuwar mu, ke da kan ki kika faɗa mana cewa kada mu fidda rai da rahamar ubangiji duk runtsi duk wuya, Angel idan muka mutu ki tuna bamu kaɗai bane akwai sauran ƴan uwan mu dayawa acikin kurkukun nan, bayan su akwai waɗanda ake shirin kawowa cikin sa, Idan har aka cigaba da aikata zaluncin nan har yaushe ne zai tsaya? Daga ni har ke babu wanda yasan tun lokacin da aka gina kurkukun ƙaddara, Dukan mu mun tsinci kan mu ne acikin sa ne......." hawaye ta ko'ina kan fuskarta taci gaba da cewa"Inaso mu kafa tarihi, agidan kurkukun ƙaddara, duk da nasan ba lallai bane mu rayu gaba ɗayan mu ba, amma raina yana bani cewar wasu zasu iya ku6uta, daga ciki har dake Angel nake sanyawa ran fita" dakatawa ta yi da yin maganar idonta akan fuskar Angel da ke kallonta, ajiyar zuciya ta sauke tare da cigaba da yin maganar
"Tarihin da nake so mu kafa shine mu kawo ƙarshen Mugayen shuwagabannin Gidan kurkukun ƙaddara, Mu tabbatar asirinsu ya tonu, inaso inga ranar da za'a rugurguza ginin nan ya dagargaje ya zamana babu shi adoron duniyar nan, zan roƙi Allah yabamu ikon aiwatar da hakan! Domin kuwa saida iznin shi ne komai zai wakana......."
tun da Deeja ta soma magana Angel ta tsareta da ido, tsantsar mamaki ne ya kamata, yanayin yadda Deeja take yin maganar da ƙwarin gwiwarta, ya yi matuƙar ɗaure mata kai, zuciyar imani ta shige ta, yayin da ita take ƙoƙarin sarewa ta fidda rai da fita sai gashi Deeja tana ƙarfafa musu gwiwa, ko a mafarki bata ta6a tunanin Deeja zata iya tsara kalami irin haka ba, Tabbas ta samu wani ƙwarin gwiwar awurinta, nan take taji cewa zata Cigaba da nema masu hanyar fita, kodan su cimma burinsu na kawo ƙarshen kurkukun ƙaddara!!
"Zamu iya Angel in sha Allah"! Fuskar Angel ɗauke da murmushi ta ɗan jinjina kanta tare da cewa"Kin faɗi gaskiya, zamu Iya bi'iznillahi, mune zamu kawo ƙarshen KURKUKUN ƘADDARA"!
Da alama su Deeja sun manta cewa duk abunda su ke tattaunawa a tsakanin su, Jami'an Gidan kurkukun ƙaddara suna kallon su
Sun ɗauki tsawon lokaci zaune a ƙasa suna ɗaukarwa junansu alƙawari, har saida dare ya tsala tukunna, Suka miƙe atare jiki duk ba ƙwari, hannunsu ruƙe dana juna suka nufi gadajen su parveen.
ɗaya bayan ɗaya Angel take binsu da kallo, tsananin tausayin su ne ya kamata ganin irin illar da ta yi masu, babban abunda ta ke ji ma fargaba kada su farka da safe su tuhume ta akan abunda ba laifinta bane, tuna wannan yasa hawaye suka wanke mata fuskarta, Deeja sai tausarta take yi daƙyar ta samu ta shawo kanta, Bayan ta gama kallon su tabi su da addu'a, tana tottofa musu saman bargunansu.
Sallama su ka yiwa juna ita da Deeja, akan idonta deeja ta nufi gadonta ta kwanta.
wuce wa tayi zuwa gadon Jamimah, A hankali ta haye tare da kwantawa gefenta, tasa hannu ta janyota jikinta, ta rungumeta sosai, saboda tsananin tsauyinta da take ji, baiwar Allah bata ji ba, bata gani ba, ta cire mata haƙori ɗaya, dole taji ba daɗi, ga azeeza da ta gurjewa yatsun hannayenta, kowa dai da irin tabon da tabar mashi, taji tsanar tsohuwa zafreeen fiye da tunanin me tunani saboda itace silar komai!
ta kwana da tunanin abubuwan da su ka faru awannan ranar, Bakomai yafi tsaya mata arai ba, face yarda aka goge kowani jini na jikinsu da wanda ya zuba a ɗakin su, aka kuma maida su saman gadajen su, wannan abun ya yi matuƙar ɗaure mata kai tun lokacin da Deeja ta sanar da ita, Shin wanene yayi musu hakan❗❓
Deeja ta sanar da ita cewa Tajiyo takun takalmin mutun acikin ɗakinsu tsoro da firgici ne su ka hana ta buɗe ido taga wanene har saida baccin ya yi awon gaba da ita........ (Nima kuma nayi awon gaba da alƙalamina)
💋PRISONERS💋
A washe garin ranar babu wanda ya farka daga cikin su, tun jiya su ke ta sharar baccin su, jamimah ce ta fara mutsu mutsun buɗe idanuwanta gaba ɗaya atakure ta ke A jikin Angel ta matse ta kamar zata mayar ita cikin cikinta, hada zufa a jikinta, shessheƙar ku ka ta soma yi tana ta faman ƙoƙarin janye jikin ta daga na wanda ya rungumeta ko ta samu ta miƙe.
sautin kukanta ne ya farkar da Angel a hankali ta buɗe idanuwanta waɗanda su ka kumbura, muryar jamimah ce ta janyo hankalin ta
"ni asake ni, wai wanene ya matse ni,"
Da sauri Angel ta zame hannayenta da ga jikin Jamima, ta yi zumbur ta miƙe zaune, ɗagowa jamimah ta yi fuskarta jawur da ita ƴan kumatun sun yi suntum da su, Suna haɗa ido da Angel, ta zazzaro idanuwanta waje jikinta ya hau kerma a gigice ta duro daga saman gadon tare da ɗaura hannayenta sama ta fashe da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali.
Lamarin yayi matuƙar girgiza Angel tasan bai wuci a bun da ya faru jiya bane yasa ta tsorata da ita, Jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Saukowa tai daga saman gadonta tana tunkarar jamima tare da miƙa mata hannu muryarta na ɗan rawa tace"Jamima nice fa Angel ɗin ki, meyasa kike gudu na"? Girgiza kai ta dinga ki bakinta ƙumshe da kuka ta shiga faɗin"Ni ba Angel ɗita bace, Saboda baki son mu, Jiya kamar zaki kashe ni, kika cire min haƙorina,' ta yi maganar tare da zura yatsanta ɗaya cikin bakinta don taji idan dagaske ba haƙorin, rushewa ta kuma yi na wani sabon kukan jin gi6in da ke a bakinta, Tuni hawaye sun wanke fuskar Angel, tsananin tausayinta ne ya kamata.
"Bana son ki Angel! i hate you! I don't want to see you, because you're not human, you're a genie!"
Cikin shessheƙar ku ka Jamimah ta furta maganar, yayin da ta ke ƙoƙarin ja da baya ganin Angel na tunkaro ta, A jikin bango Jamima ta manne tana girgiza mata kai, alamar karta kuskura tazo wurin ta, zuciyar Angel ba ƙaramar karaya ta yi ba, ta rasa ina zata tsoma ranta ne taji daɗi, a gaban jamimah ta zuƙunna saman gwiwowinta, ba tare da ta iya furta komai ba.
Duk wannan abun da ke faruwa akan kunnuwan masu bacci waɗanda tuni sun jima da farkawa tun lokacin da Jamima ta rushe da kuka, Sautin ya daki dodon kunnuwan su, Tashin su kenan, hankalinsu gaba ɗaya akan Jamima da Angel, Azeeza ce ta soma shessheƙar kuka tana zaune saman gadonta, idanuwanta akan yatsun hannayenta da su ka jigata, duk sun faffashe sai sai babu ɗigon jini ko raɗaɗi, muryar ta adisashe ta ke yin magana.
"Na gaza yarda da abunda idanuwana su ka nuna min, bazan zargi Angel ba, amma meyasa ta take min yatsun hannuna? Meyasa ta buge mu? Laifin me mu ka mata"? Sosai ta fashe da matsanancin ku ka, Hakan ba ƙaramin rikita Angel yai ba, tana fama da jamimah ga su Azeeza sun ɗauka su ma.
Idanuwan kowannan su acike yake tab da ƙwalla, zuciyoyin su ba ƙaramin karaya su ka yi ba, Muryar Hanna tamkar zata fashe da kuka tace"Duk irin haƙurin da nake baki Angel baki saurareni ba, har cewa nayi ki haɗa da bugun da za ki yi ma jamimah ki yi min amma shine kika ƙi saurarena, ki ka haɗamu duka ni da ita, kika buga mu ƙasa har saida haƙorinta ya cire, ko ita baki tausaya mawa ba, ita da ta ke ƙarama"
Gaba ɗaya suna neman zautar da ita, sam ta kasa juyawa ta kallesu saboda nauyin haɗa ido da su ta ke ji, still bata motsa ba, tana a zuƙunne gaban Jamima dake ta shessheƙar kuka, Abun ya ta6a zuciyoyin su, sun kasa fahimtar cewa ba yin kanta bane, dama zai yi wuya su fahimci hakan, kawai sun yi imani da abunda idanuwansu suka nuna musu ne.
"Da yanzu na mutu babu ni babu ƙara cin abinci, mu fa biyu Angel ta haɗa dani da hibba ta buga mu ga ƙasa, hakan bai isheta ba, sai da ta taɗiye ƙafar rubina ta kife ƙasa tukunna hankalinta ya kwanta.........." parveen bata ƙarasa maganar ba saboda kukan daya ciyota, Angel taga haza, Zuciyarta sai tafarfasa ta ke yi, ta runtse idanuwanta sosai, tana sauraron kowannan su
"Har yanzu ƙuguna ba dai dai ya ke ba, ni banma san ya akai na dawo saman gado ba, Angel taso naƙasa min rayuwa" Acewar Sarah, tana magana tana dafe qugunta da hannu ɗaya........
Eve da ke ta matse ƙwalla ido jawur tace"Haka muma ta haɗa kawunan mu nida Yasmin Ta buga mu jikin bango, daga nan ma ni ban ƙara sanin meya faru ba" Sai da ta kammala sauraron kowan nan su, gwiwowinta duk sun sage, har wani jiri ta ke gani acikin idanuwanta, sunan Allah take ta ambato acikin bakinta, a daddafe ta samu ta miƙe tsaye tare da juyawa tana fuskantar su.
A Yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri saman fuskarta, sai faman jinjina kanta ta ke yi tana kallonsu da rinannun idanuwanta, babu wanda ya motsa daga saman gadon shi, duk suna a zaune suna kallonta, Kamar yarda idanuwan ta ke fitar da hawaye haka suma nasu ke tsiyaya, magana ta ke so ta yi amma ta kasa, wani irin raɗaɗi ta ke ji acan cikin zuciyarta, ga maƙoshinta da ke a bushe sai ƙaiƙayi ya ke mata.
"Kun yarda cewa ANGEL zata iya cutar da ku!"? Muryar Deeja ce ta janyo hankalin su zuwa ga dubanta, ta yi masu tambayar ne a yayin da ta ke saukowa daga saman gadonta, Tafiya take yi kamar babu wadataccen jini a jikinta, a tsakiyar ɗakin nasu ta tsaya tana bin faces ɗinsu da kallo, ta ɗaura da cewa"Tambayar ku na ke yi, ba ku bani amsa ba, jiya da abun ya faru me ya zo maku acikin ran ku"?
Azeeza ce ta fara yin magana acikin su"ni dai nasan Angel baza ta ta6a iya cutar da wani acikin mu ba, amma narasa gane meyasa ta yi mana hakan"? tai tambayar tana kallon Deeja,
Kamar yarda azeeza ta ce, suma sauran duk haka su ka ce, sun san bazata Iya cutar dasu ba, Angel koda wani ta gani zai cutar dasu bazata ƙyale shi ba, balle kuma ace ita da kanta ne ta yi musu hakan, abunda ya sanya musu kokwanto ya ruɗar dasu shine taya akai ta yi musu Jahilin bugun nan da kanta kuma da hannayenta!
Juyawa Deeja ta yi ta fuskanci Angel da ke atsaye kamar an dasa mata aya, Jikinta sai kerma yake yi.
"Ba laifin ta ba ne, kuma ba yin kanta bane, bakowa bane Ya jawo hakan fa ce muguwar matar nan, tsohuwa Zafreen! Itace silar komai, Idan har ba za ku manta ba, akan idon ku ta ɗaura mata sanda saman ƙirjinta, ni dama tun a lokacin raina ya bani cewar wani mugun abun ne za ta yi mata, dama tace bamu ta6a gabza faɗa a tsakanin mu ba, kuma wai a dokar prison ba'a amince ma kowani prisoner yaji daɗin rayuwar shi ba, Allah ya isa tsakanin mu da tsohuwa Zafreen, wlh ban ta6a danasanin tafiyar Tsohuwa Tamira ba irin na jiya, Mun yi babban rashi, ƙwara ita da daɗi da ba daɗi wani lokacin tana yi mana mutunci in taso"
Babu wanda jikin shi bai yi sanyi ba, yanzu sun fahimci cewa Ba yin kanta bane, dama basu yarda cewa zata iya yi musu hakan ba, Angel ɗin da take matuƙar ƙaunar su, in dai a kansu ne har ranta zata iya badawa don ta fanshe su, Ni shaida ce akan hakan!
Atare suka hada baki wurin bata haƙuri, tace masu basu ne ya kamata su bata haƙuri ba, duk da ba yin kanta bane, Ita ya dace ace ta basu haƙuri tun da da ita a ka yi amfani wurin cutar da su, don haka tana me neman yafiya agare su, su yi hakuri su yafe mata, kuma in sha Allah hakan ba zata ƙara faruwa ba, ita kanta ta yi mamakin yarda akai Sihirin tsohuwa Zafreen Ya kama jikinta, duk da shi sirihi gaskiya ne, kuma babu wanda yafi ƙarfin ya shiga jikin shi sai wanda Allah ya tsare! Shiyasa ake so bawa ya kasance mai neman tsari awurin ubangiji, ba dole sai abu ya risƙe ka ba, kace zaka fara roƙon Allah, a'a a koda yaushe ka kasance cikin neman tsari daga gare shi, addu'ar nan itace takobin mumini, after that azhkar na safe dana marece, mutun ya dage da yin shi ba fashi, da wuya kaga wanda ke yin azhkar mummunan abu ya faru dashi ba tare da Allah ya tsare shi ba!, Allah dai yasa mu dace.
Bayan Angel ta nemi yafiyar su Hankalin kowannan su ya kwanta banda mutun ɗaya, Jamima itafa har ga Allah tsoron Angel ta ke ji,
Abun ka ga yaro Ta ƙame jikin bango sai kuka take yi musu tana faɗin itafa bata son ganin Angel, cos she's a genie ba mutun bace, ba zata zauna a ɗaki ɗaya da ita ba, sai dai su rufe ta a cikin toilet, idan an kawo abinci su dinga kai mata acan tana ci, idan har ba su yi hakan ba, ita zata koma da yin rayuwa acikin toilet ɗinne, Abu kamar wasa ta sanya musu rigima, babu wanda bai lallashe ta ba acikin su akan ta yi haƙuri amma taƙiya, ƴar tahalikar nan har bayani su ka yi mata yadda zata fahinci cewa ba laifin Angel bane amma tace musu tasan me ta ke yi, su daina ganinta ƴar ƙarama kar take kallon su, Har ita za su yi ma wayau, so su ke ta zauna tare