Header Ads
Showing 45001 words to 48000 words out of 287659 words

Chapter 16 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1774

Ads at the middle of Article

damu, Bazan faɗa ma shi cewa ke kika kawo mun giyar ba, Zance ni na fita na siyo ta, hakan yayi maki" jinjina kai ajumma tayi kafin ta ruƙe handle ɗin ƙopar ta fuce,
Zama Hajiya adama tayi a gefen katafaren gadonta, takai hannu ta Ɗauki kwalbar Soju Ta cire mufin, Abaki ta kwafata Cikin ƙanƙanin Lokaci ta shanye duka, wani irin biji biji tafara gani a cikin idanuwanta, Ajiye kwalbar tayi, tare da kai hannu ta ƙara ɗaukar wata kwalbar ta shanye duka, sauke kwalbar tayi saman table, Ta yunƙura zata miƙe duniyar ta soma juya mata, sha tara sha takwas ta dinga gani acikin idanuwanta, wani irin nauyi Jikinta yayi mata, Tangal tangal ta soma yi tana tafiya ta nufi hoton dake manne jikin bangon ɗakinsu, Ta curo hoton ta ƙura mashi ido tana kallon shi, har wani girgiza kai take yi,
Can dai ta rushe da wata irin mahaukaciyar dariya tamkar zararra, muryarta ashaƙe ta soma magana"Duniya juyi juyi, wohoho Kai ya ɗau zafi, In ban da ta6ara da ɗamsil basira Ta ya za'ace mutun ya 6ace tun 1960 Amma An gaza gano inda yake? Ƴan sandan nan basu san ciwon kansu ba, Gashin Hammata ma yafi su Amfani, Nayi fushi Allah Ni da kaina zan nemo abuna ahe, Ku zuba ido ku gani yanzun nan zan gano su,' takai ƙarshen maganar tare da ajiye hoton ƙasa, tattare Zanin leshin jikinta tayi, ta zuƙunna ƙasa tana rarrafe, Saƙo da lungu na ɗakin ta shiga Bi tana sambatu Tana faɗin"Gasu Can sun 6oye, kamo su nan kamaso Sunan, Zo nan ɗan ɗana Uzairu Yaron mamansa, kaima zo Tajuddeen ɗina, Kai na manta da Angela ta Yarinyata zonan in raira maki waƙa, Wacece Kumatu Angel ce kumatu, kumatutu kumatu, kumatutun mama, kumatutun baba......" tana raira waƙar tana kuka, zama tayi tare da cewa"Yauwa, Ga abinci Nan Shekaran jiya na girka maku shi, nasan kuna jin yunwa, banda wawaso, duk wanda ka samu rabon ka ne,," gaba ɗaya ta haukace ita kaɗai take ta sambatu, giya takai mata karo, ita fa ala dole su take gani acikin idanuwanta, tana magana tana sakin gyatsa,
Yunƙurawa tayi ta miƙe tsaye tana faɗin"Zan Binciko ku duk inda kuka 6oye ja'iran yaran, harni zan girka maku abinci ku ƙi ci? Kai tajo hada cewa ba daɗi? Ni da ku ne" hannu tasa ta zuge zip ɗin rigarta, Ta cire rigar tare da yin wurgi da ita ƙasa, Ta warware zanin shima ta jefar da shi ƙasa, ya rage daga ita sai undy, Ƴar duma duma da ita, ga uban tumbi, wurgi tayi da kallabi leshin kanta, Ta koma mahaukaciyar ƙarfi da yaji, dambe ta shiga yi ita kaɗai, sai da ta Tarwatsa komai na ɗakin, da sunan tana neman Su Uzairu, itace har cikin toilet, gaban toilet seat taje tana leƙawa, Hankali Ya gushe,
A karshe ta zube ƙasa tana birgima tana faɗin"Ya Allah kota sama ne, A jeho mini su, Nasan kasan inda su ke, tunda kai kana ganin komai, ko karkashin ƙasa mutun ya 6oye......."
Ta jima tana sambatu, kafin Allah ya kawo bacci ya yi awon gaba da ita, Lokacin da Uncle abdallah ya shigo Cikin gidan, Jikinshi sanye Cikin Suit sun zauna ma shi,
Tun a palour suka yi kici6us da Ajumma, Sam ba ta yi tsammanin Aranar zasu dawo ba, A tsorace ta gaishe dashi muryarta na kerma, Kota kanta bai bi, kaitsaye ya nufi bedroom ɗinsu Ya tura ƙopar ya shiga, tun daga kan Kayan Hajiya adama data tube ya fara Cin karo da su yashe a ƙasan tiles, Ko'ina na ɗakin ta hargitsa shi, tsayar da idanuwan shi yayi akan hajiya adama da ke kwance ƙasa ta baje sai sharar bacci take yi hada minshari, Ga kwalaban Soju ɗin da tasha nan Ajiye saman table,
"YA SALAM" rai a6ace ya ambaci hakan, kutsa kai yae cikin ɗakin A ƙasa yayi toxali da hotonsu Uzair, wanda hajiya adama ta jefar ƙasa, zuƙunnawa yayi tare dakai hannu ya ɗauki hoton nasu yana kallo,
Nan take ya gane dalilin shan giyar nata, in har zata cigaba da kallon hotonsu uzair, to kuwa bazata ta6a daina shaye shaye ba, ba irin faɗan da baiyi mata ba akan tadaina amma taƙiya,
Takawa yayi zuwa jikin bangon ya liƙa hoton, kafin Ya nufi inda take a kwance ya zuƙunna, ya jima yana kallonta, hannu yakai saman ƙafarta yaɗan bubbuga, Shiru bata farka ba, Sai da yayi dagaske Sannan Ta buɗe idanuwanta waɗanda sukayi jawur dasu, Tana kallon shi,
"Get up, Ina son magana da ke" da alama har yanzu wine ɗin bata sake ta ba, daƙyar ta lalla6a ta miƙe zaune tana faman yin hamma,
"Waya kawo wannan abun Cikin gidan nan"? Ya yi tambayar yana nuna kwalaban Soju ɗin da ta sha, fuskar shi a murtuke,
"Ni na kawo su, don su ɗebe mini kewa,"
"Narasa gane meke damunki? Meyasa kullum burinki ki 6atamun rai? Kin manta sharuɗɗan da dr park ya gindaya maki akan lafiyarki? Kina tunanin shan wine ɗin da kike yi shi ne mafita agare ki? Yakai ƙarshen maganar yana kallonta,
Sai faman lumshe ido take yi,"magana fa nake yi maki? Harara ta wurga mashi"To Ubana Alhaji Adamu, Zaka fara faɗan naka ko? nasan bai wuci kace haramin bane shan giya, Zan illata lafiyata, bayan shi sai kuma me"? A harzuƙe tayi maganar tana kallon shi, har saida gabanshi ya faɗi ras! Saboda yadda ta rufe ido tana gaya mashi magana, lallai har yanzu bata dawo Cikin hayyacin ta ba,
Sassauta muryarshi yae, Cikin sigar lallashi yace"Allah ya huci zuciyarki, ni ba faɗa nace zanyi maki ba, Amma dan Allah kidaina shaye shayen nan baida amfani, idan damuwa ce tayi maki yawa Ki ɗauko qur'ani ki karanta mana"
"Ka yanke shawara game da komawarmu nigeria? nifa na lura kamar baka damu da 6acewarsu ba, harkokin kasuwancinka kawai kasa agaba, Nikaɗai ce nasanya damuwa akansu, almost 2 years ban ta6a ganin ka tashi tsakar dare kayi Nafila a kansu ba,
Jinjina kanshi yae"Adama kenan, Ae duk cikakken musulmi wanda yayi imani da Allah, ya kuma yi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, Bazai ta6a zama ya ƙuntata kan shi ba don Allah ya jarabce shi, Nasan cewa aduk inda suke Allah yana atare dasu, Kuma inayi masu addu'a, wannan ma ya wadatar ba dole saina tashi tsakar dare ba, bansani ba ko so kike in ajiye harkokin kasuwancina, In sanya damuwa araina a ƙarshe Nima in koma ɗan giya,' hannu tasa ta dafe gefen kanta, hawaye masu ɗumi suka soma shararowa mata,
Ruƙo hannayenta ya yi Cikin nashi"Ki faɗamun kome kike so zanyi maki, Amma dan Allah kidaina shaye shayen nan kodan saboda lafiyarki, bana so kema in rasa ki kamar yadda narasa iyaye na, da kuma ya'yana," cikin shessheƙar kuka tace"Mu koma Nigeri, Nagaji da zama a ƙasar nan, ƙwara idan ina acan zanfi samun kwanciyar hankali,"
"Shikenan, Zanyi abunda kike so amma ki ɗan bani lokaci, In kammala wani aiki da nake yi, da zarar na gama zamu koma can ɗin kamar yadda kikeso,"
Gyaɗa kai tayi"wannan karan idan har baka Cika min alƙawarina ba, sai dai kawai kaji labarin Na tafi,"
"In sha Allah hakan bazata faruwa," sosai ya kwantar mata da hankalinta, Har ya samu Ta shiga toilet tayi wanka ta canza kaya, Da kanshi ya gyara masu ɗakin, ya tattara kwalaban Soju ɗin ya fita yaje ya jefar dasu, Sannan hankalin shi ya kwanta,

*UAE*

Haɗaɗdiyar Daular Larabawa

Abu dhabi,

Alhaji Ubaid ne zaune A cikin Hamshaƙin falon gidansa, Wanda yaji Hadaddun furniture tsadaddun gaske, ga wani sanyin A.c dake ratsa sassan Jikin mutun,
Ya ɗau wankan Shadda, Ya hakimce saman 3 seater, Hannun shi na ruƙe da jarida, A gaban shi table ne mai ɗauke da mug na coffee,
Ya natsu yana Karanta Jaridar, kamar daga sama yaji An fisgeta, kafin ya ɗago ya kalli wanda ya kwaci jaridar daga hannun shi, tuni tayi tearing ɗinta into pieces,
Bakowa bace face Laila, Mahaifiyar Benazir, doguwar balarabiya tasha wankan Abaya launin royal blue, yalwataccen gashin kanta har tsakiyar bayanta, Ƙafafunta na sanye da High heels,
Zuba mata ido yayi batare daya ce mata ƙala ba,
"Idan har zaka cigaba da kallon waɗannan gantalallun Ni kuma bazan gaji da yage duk wata jarida da zaka kawo A cikin gidan nan ba, tunda na lura bakasan ciwon kanka ba, Menene alaƙarka da su? Ga ƴarka ta cikin ka da ta 6ata shekara da shekaru Baka damu da ita ba, sai wasu can rainon talauci," rai a6ace takai ƙarshen maganar, tare da juyawa ta nufi bedroom ɗinta, Sai gata ta dawo hannunta ruƙe da newspaper me ɗauke da sunan khaleej times, ta wurga mashi saman fuskar shi"Ita ce jaridar dana amince maka ka karanta, tun da karantun jaridar ya zamar maka dole"
Hannu yasa ya janye jaridar daga saman fuskar shi, still idonshi na akan fuskarta,
"Mutanan da kika kira da gantalallu, Sunfi ki daraja da ƙima a idona, dake da ƴar taki, Saboda bakusan ciwon kanku ba, in banda rashin ɗa'a, da rashin sanin darajar miji har kin isa Ina karanta abu kinzo ki fisge ki yayyaga, Haka aka koya maki tarbiya a gidan ku,"?
Wuri ta samu saman Sofa ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, batare da tace mashi ƙala ba,
Sai da ta mula tasha iska tukunna tace"bansan meke damunka, duk kabi ka sanya damuwa kan wasu kucakai, ga wadda take jinin ka, Amma sam Baka damu da ita ba,"
Murmushin takaici yasaki kafin yace" Benzir don son ranta ta gudu kuma tana a raye tunda har ta iya ta turo mun saƙo a duk lokacin da taga dama, Su kuwa waɗannan bayin Allahn, Rana ɗaya aka neme su aka rasa, Har yau babu labari a kansu, taya bazan damu da su ba? Jikata ɗaya da nake da ita kwallin kwal, Narasa ta, ƙaramar yarinyar da bata mallaki hankalin ta ba, Wayasan a wani hali suke ciki"?
Ta6e baki Laila tayi"Laifinsu ne ae, kasan ƴan jarida da kafiya, ga shegen naci da bin ƙwaƙƙwafi, acan wurin neman labari suka tsokano abunda yafi ƙarfinsu gayanan ae yanzu wa gari ya waya,"? Yadda tayi maganar ko ajikinta,
Girgiza kai Alhaji ubaid yayi yayin da yake kallonta"Hada jikarki fa a cikinsu,"
"Jikarka dai, Ni ban haɗa komai da su ba, Auran benzir da yaron nan ƙaddara ce, kai ka sani nesa ba kusa ba, benazir tafi ƙarfin shi, Ni nayi tunanin ma ɗan Abdallan ne shima ashe ɗan wani faƙirin mutunne dake zaune a karkara....." rai a6ace Alhaji ubaid ya dakatar da ita"Cin mutuncin ya isa haka, Kuma ki iya bakin ki, mutumin da kike kira fakiri a yanzu haka baya a raye ya riga mu gidan gaskiya, ke wai baki tsoron Allah? Mace har mace ba kyan hali, silar ki ga shi nan duk narasa ya'yana saboda gur6ata masu tarbiyar da kike yi,"
Murmushi tasaki tana kallon shi,"Nifa komai zaka faɗi akaina bazan ta6a jin haushi ba, Ga Coffee ɗinka nan Yana huce wa yakamata ka sha" tayi maganar tana nuna mashi Mug ɗin dake ajiye saman table,
Banza yayi da ita batare daya furta mata komai ba,
Kashe murya tayi tare da cewa"Habibi fushi ka ke da Nooril ƙalbin taka"? Dariya taga ya saki kamar wani zautacce, mamaki ya kamata, ta ƙura mashi ido tana kallon shi,
Wayar shi dake ajiye saman sofa hand ta soma ringing,
Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar tare da miƙe wa, still da dariya akan fuskarshi ya fuce daga Cikin gidan,
Girgiza kai lailah tayi"ɗan siyasa kenan, Jibi yadda ya mayar dani shashasha, Ina tunanin na harzuƙa shi ga shi nan ya fuce yana yi mun dariya wato nice mahaukaciyar, Allah ya kyauta, Ni ya dawo ma muyi magana ta fahimta, Tunda ciwon ƙafar ta shi yayi sauƙi, zan tunzura shi ya nemi takarar shugaban ƙasa, Wannan shi ne burin da nake da shi,' takai ƙarshen maganar tare da kwalawa mai aikinta Zainab kira, da sauri ta fito daga Cikin kitchen ta nufe ta, Balarabiya ce a ƙalla takai shekara arba'en, jikinta na sanye da kayan aiki,
Cikin harshen labaraci tace"ki sanar ma Sauran maids ɗin Gobe A shirya Abinci kala kala na gargajiya dana zamani, Dr Shureim zai kawo mana ziyara daga egypt"
Jinjina kai zainab tayi cikin ladabi ta amsa mata da"Toh, in sha Allah za'a shirya komai, Allah ya kawo shi lafiya,"
Laila ta amsa mata "ameen"
Bayan fitar Alhaji Ubaid, A entry hall na gidan ya tsaya ya amsa Kiran da akayi ma shi daga gida Nigeria, Yana waya idonshi na akan Masu aikin gidanshi, dake ta aikace aikacansu,
"Ka kwantar da hankalin ka, Lokaci kawai nake jira, Ina nan ina shirye shirye dawowa Nigeria, Siyasa fa yanzu muka sanya ƙafa ba gudu baja da baya, Namiji da jarumta aka sanshi bada ragwanci ba, Wannan karan babbar kujera nake hari, Zanyi duk iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin Na siye zuciyar Dattijon nan, Kona samu ya sanya mun albarka Cikin lamurrana,"
On the other hand muryar Babban mutumin Da yake waya da shi ce ta soma bayyana" Da kamar wuya fa, kasan halin shi Kaifi ɗaya ne, wani irin bauɗaɗɗan mutunne abunda ya yi niya shi yake aiwatarwa, Amma zamu yi kokarin shawo kanshi, Ko dan muyi nasara akan abunda muke son Cimmawa, yanzu dai dawowarka Nigeria shiya fi komai mahimmanci,"
"zan dawo In sha Allah, Kodan saboda Yaran nan da suka 6ace, Sunan ina zaune ne a Ƙasar nan amma tunanina gaba ɗaya yana a nigeria, nadamu da su," fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yakai ƙarshen maganar, abokin nashi da suke waya yace"Wai har yansu babu labarin su? Ae ni da naji shiru nayi tunanin an same su ne," muryarshi da alamun mamaki
"kusan shekara biyu fa kenan babu su babu alamarsu, Ni tsorona ma kada ace abokan hamayyata ne suka Farmake su, kasan mutanan nan ba imani ne da su ba, Komai zasu iya aikatawa indai akan siyasar su ce,"
Jajanta ma shi abokin na shi ya yi, da ga haka su kayi ma Juna Sallama, Har ya juya zai koma Cikin falon, Yaji ƙarar shigowar mota, juyawa yayi yana kallon Motar da ta shigo, Danƙareriya mota mai numfashi, da alama Baki ya yi,
Bodyguard ne Ya fita daga Driver seat na motar, Ya zagaya ya buɗe mashi mota, Wata irin dariya Alhaji ubaid ya saki lokacin da yayi tozali da Alhaji badamasi, Mataimakinsa Lokacin da yana gomna a jihar jos, da sauri ya nufe shi yana faɗin"Marhaban bika Mutumina, Irin wannan zuwan bazata haka, Yaushe ka shigo ƙasar" Alhaji badamasi sai faman washe baki yake yi, yayi shigar larabawa, Ga wani ƙamshi dake fita a jikinshi,
Rungume juna su kayi kamar zasu haɗiye juna, A tsaitsaye suka fara gaisawa kafin Suka Nufi Cikin garden ɗin gidan, A waya ya kira lailah yace Ayi ma mai aiki magana ta kawo masu kayan marmari su sha, A garden a kayi masu Shimfiɗa Saman Lallausar darduma suka zauna domin tattaunawa a tsakanin su,

Shin Ya rayuwar Angel ta kasance bayan An sace ta Cikin Mota?

Sambatu take ta faman yi, Cikin fitar hayyaci, tarasa gane inda take, Ko'ina duhu, babu haske ko misƙala Zarratin, jikinta yayi mata wani irin nauyi tamkar an ɗaura mata dutse a samanta, Ko yatsan ta ta gaza ɗagawa, Wani baƙon yanayi da bata ta6a jin kanta acikin shi ba, ga zafi ta ko'ina, numfashin ta kanshi daƙyar take fitar dashi, atakure take jin kanta, tun tana kukan a bayyana har ta koma tanayin na zuci, Cikin disasshiyar muryarta ta soma ambaton duk wata addu'a da tazo bakin ta,
Tsawon mintuna talatin kenan, tana acikin wannan yanayin ta haɗa uban gumi, duk ta cicci je la66an ta sun faffashe, Saboda ƙuncin da take Ciki, takaici ya isheta, ta kuma rushewa da kuka tana faɗin"Wai ba kowa ne a kusa, Ku faɗamun ina ne nan! Wayyo Allah na! Danejo! daddy Can you hear me! its me ur angel, pls if u are hearing my voice, Answer me, Am really scared of being alone in this darkness......" cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar,
Wani irin raɗaɗi maƙoshin keyi mata hada ƙaiƙayi,Tana Cikin buƙatar ruwa, throat ɗinta ya bushe ƙamas,
Ƙoƙin motsa lips ɗinta tayi da niyar ta ƙara magana, Ba zato ba tsammani, haske ya soma bayyana Acikin wurin da take, nan take ta dakata da yin kuka biji biji ta fara gani kafin idanuwan nata su ka washe ta ƙura ido tana Kallon Ceiling ɗin da take fuskanta,
Dogon Ginin dutse ne mai matuƙar Girma da faɗi da tsayi, Ceilling ɗin Yayi uban soro daga inda take daƙyar ta ke iya hango ƙarshen shi, wasu fitilu ne jere can saman ceilling ɗin, hasken su ne ya gauraye Cikin ɗakin da ta ke, sauke idanuwanta tayi tare da yin ƙoƙarin miƙewa zaune, don ta samu damar ƙarewa baƙon wurin kallo,
tamkar hostel na kwanan ɗalibai haka wurin ya ke, daga 6angaren da take kwance 6angaren yamma ne tana fuskantar gabas akwai jerin gada je da a ka yi su da Metal(ƙarfe) A ƙalla sun kai goma sha biyar, single bed ne na mutun ɗaya kowane gado yana da lallausar mattress a saman shi, tare da matashin kai (pillow) da kuma duvet, launin farare, a ɗaya daga Cikin gadajen ANGEL take a zaune, tana bin kowace kusurwa ta ɗakin da kallo, akwai wasu kujeru da a kayi su da

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads