Showing 6001 words to 9000 words out of 287659 words
Chapter 3 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
sunji haushin Abunda Matarshi tayi, dama tun fil azal basu so ya auri bare ba, sun so ace cikin dangi ya samu mata ya aura, don ba yadda zasuyi ne ƙaddara ta riga fata,
A 6angaren Taj kuwa yaso ace uncle abdallah ƙanin mahaifinshi, yana nan a ka yi sunan sai dai kash, tunda jimawa sukayi tafiya zuwa South korea, da ya ke acen kasuwancinshi yafi ƙarfi, duk da haka Sunyi waya dashi, Har video call suka kira shi don ya nuna masu babynsu, aikuwa sunsha ruwan mamakin ganin kyakkyawar ɗiyar tajuddeen, Don ita Hajiya Adama matar Uncle din, cewa tayi da zarar sun dawo nigeria zata ɗauke ɗiyarta, saboda ta raineta ko alokacin Taj bai sanar da su game da Abunda ya faru tsakaninshi da benazir ba, don baiso ya tashi hankalinsu ya bari ne sai Sun dawo tukunna Suji komai,
Alhamdulillah An kammala taron suna Lafiya, ƴan uwa da abokanan arziki sunci sun sha sun shaida Zuwan *UNAISA* duniya, aranar Tajuddeen kamar yayi hauka saboda tsabar farin ciki, domin kuwa ya samu alheri sosai awurin abokananshi, da kuma masoyanshi don hada key ɗin mota ya samu, ga kuma kayayyakin da suka dinga haɗawa ƴarsa, manya manyan akwatina na kayan baby, shi kanshi ya samu kyautar shaddoji a daren ranar sunan Tare da Uzair suka shiga ɗakinshi suna ƙirga kyaututtukan daya samu, A kalla ya samu kuɗi Sama da 3m, baya ga kayayyakin da ya samu har hawaye saida taj ya zubar, dama shanun da aka yanka ranar sunan bai ƙarasa biyan kuɗinshi ba, bashinsa yaci har uzair na gargaɗin shi akan karya ɗauki abunda yafi ƙarfinshi Ya siya masu rago kawai ya wadatar, Amma yace ina ƴar shi tafi ƙarfin rago sai dai sa.sai gashi Allah Ya rufa mashi asiri,
Sai da su Deeje sukayi Wata ɗaya Cuf tukunna suka shirya komawa Buzaye, Sunyi tunanin taj zai bar masu yarinyar ne su tafi da ita can ƙauyansu buzaye kafin Ya samu matar aure, Amma ina koda Su ka zo mashi da maganar tafiya da babynshi, Sai ya juya masu ƙeya, alamar bazai bayar ba,don dole suka haƙura, dama deejen ce ta matsa su tafi da ita,amma mahaifiyarshi Yahanasu sam bata ayyana hakan aranta ba, musamman da ta ga yadda Inna kuluwa ƙanwar baba maigadi take kula da ita Sai hankalinta ya kwanta,
Ba ƙaramin alheri taj yayi masu ba lokacin da zasu tafi, kusan abunda ya samu ya kasa uku, ya basu kashi ɗaya,Kashi ɗaya kuma yaba Uzair amininsa, Amma yaƙi kar6a saima ya ƙara mashi sunyi rabuwar arziƙi da iyayenshi Sunata sanya mashi albarka har kwalla saidaya zubar bayan tafiyarsu Allah sarki rayuwa kenan
A 6angaren inna kuluwa kuwa babyn Tana samun kyakkyawan kulawa a wurinta, duk da ba'a tare suke yini ba kuma ba a tare suke kwana ba, saboda taj da kullum yana manne da ita, sai dai fa duk lokacin da tafara tsala kukan yunwa, dakan shi yake daukar ta yakai ma inna kulu aɗakinta, Yaƙi yarda yabar mata Yarinyar Saboda ya mutu akan sonta, kona seconds baisan rabuwa da ita zuwa aikine kawai yayi mashi cikas, ba ƙaramin abu ke rabashi da babynshi ba, ko aiki yaje yana dawowa jiki na rawa ya ke zuwa ɗakin inna kuluwa ya ɗauketa, idan dare yayi kuwa dama atare da ita yake kwana, Saman kirjinshi yake kwantar da ita Su sha baccinsu,
A daren ranar wata Alhamis ne Yana zaune saman Sofa Yana danne danne acikin Laptop ɗinshi, Ya jiyo sautin dirar motoci a lokacin angel tana a hannun inna kulu, bai kaiga zuwa ya ɗaukota ba, Yana jira ya kammala aikinsa ne kafin ya Amsota don su kwanta,
Zugudum yayi yana jiran ganin wanene Ya kawo mashi ziyara a irin wannan Lokacin Kusan ƙarfe 9 na dare,
Daga wajen Falon yaji anyi mashi sallama, muryar babban mutum,
Da sauri ya kalli agogon dake manne a bango, kusan ƙarfe tara na dare, duk a tunaninshi uzairne don bai ɗauki murya ba,
hakan yasa shi ɗan ɗaga murya tare da cewa"Come In"
Turo ƙopar akayi, a hankali Ya shigo bakin shi ɗauke da sallama,
Da mamaki akan fuskar taj yake kallonshi,
Babban mutunne yana sanye Cikin kaya na mutunci na hausawa, Shadda tare da malun malun mutun mai cikar kamala,
fuskarshi ɗauke da murmushi,
Bakowa bane face Alhaji Ubaid Mahaifin Benazir Kaka Ga Angel,
Fuskar taj ɗauke da murmushi ya miƙe tsaye Yana kallonshi, kowannan su da abunda yake saƙawa aranshi,
"Taj nasan ban kyauta ba, wlh naji kunyar haɗa ido dakai," cikin sanyin murya yayi maganar, da sauri uzair ya qarasa inda yake a tsaye, ya miƙa mashi hannnu don su gaisa,girgiza kai yayi tare da cewa,
"Bana jin zan iya haɗa hannu dakai don bancancanta ba"
Tausayinshi ne ya kama Uzair, cikin sanyin murya yace"kada ka sanya damuwa aranka komai ya wuce,"
Damuwace ƙarara akan fuskarshi"ɗane ka haifeshi baka haifi halinshi ba,"
Murmushi taj ya ɗan saki, kafin ya ruƙo hannunshi zuwa cikin Falon, Suka zauna saman Sofa suna fuskantar Juna,
"Baba yaushe kuka dawo ƙasar bansani ba? ya kuma Jikin naku"?
"Jiya muka dawo, Jiki yayi kyau Alhamdulillah,wlh taj naso nazo tun lokacin da ka kirani waya ka sanar dani rashin Hankalin da benazir tayi maka, Naji takaicin abun nan ƙiris Ya rage in kwashe mata albarka" yakai ƙarshen maganar fuskarshi duk a hautsine, bawan Allah da alama Yaji jiki, tun lokacin da Taj ya haɗu da benazir kafin auransu mahaifinta baya qasar saboda lalurar da ya ke fama da ita, Na ciwon ƙafa mai raɗaɗin gaske,
Alhaji ubaid tsohon gomna ne, bai jima da hawa mulkin ba, Shekara ɗaya kacal Lalurar ta sameshi,Ba ƙaramar wahala yaci ba, Don kowa yayi tunanin bazai rayu ba kullum Ciwon nashi ba sauƙi,ƙara gaba yakeyi,Gashi mutane suna matuƙar sonshi,Yana da farin Jini sosai, adalin shugaba ne mutumin kirki Mai son talakawa, Ga kyautata masu dayawa suna tunanin Abokan hamayyarsa ne suka Yi mashi Asiri, wanda hakan yasa shi ajiye shugabancin, kuma tun daga lokacin zama Nigeria ya gagares hi,da zarar yabar ƙasar Sai yaji sauƙi, da zarar ya dawo sai ciwon nashi ya dawo sabo,tun daga nan ne yabar ƙasar gaba ɗaya tare da Iyalinshi ya koma Dubai da zama, benazir kaɗai Ya bari anan saboda auran da tayi,
"Allah ya ƙara Lafiya, Allah kuma ya kare ku daga sharrin makiya da mahassada,"
"Ameen ameen tajo, ae ina ganin saƙon gaisuwarka da kake turamun kullum ta waya, Inajin dadi sosai," shiru suka ɗanyi kafin Alhaji ubaid yaci gaba da magana"Abu biyu ya kawoni wurinka, Na farko ina mai baka hakuri game da abunda Benazir ta aikata mata, yanzu haka maganar da nake yi maka, Na yafeta acikin zuri'ata Saboda bata jin maganata, tafi karfina......"tunkan yakai ƙarshen maganar, taj yayi saurin katse mashi hanzarinshi"kada ayi haka baba, Ayi mata uziri, dukkan mu nan babu wanda yasan dalilin dayasa benazir ta gudu tabar jaririyar ta, Kowa yasan tsakanin Uwa da ɗanta akwai soyayya mai karfi, Ni nasan ba hakanan benazir ta tafi ba, Dole akwai wani abu da yayi silar tafiyarta,
Girgiza kai Alhaji ubaid yayi"bakasan halinta ba ne, ni da na haifeta ni nasan halin kayana, Tagagari kowa, halinta sak dana jatumarta,dama ƙaddara ce tasa na aurota,
Murmushi taj ya ɗan saki"Adaiyi hakuri baba,".
"Bazan bari ayi 6arna ina kallo ba, Benazir so take tajamun zagi a idon jama'a, tana so ta zubarmun da mutuncina da kuma ƙimata,sai kace ita ta haifi kanta? Babban abunda yafi damuna, bansan a ina take rayuwa ba,Gaba ɗaya ta kashe layinkan wayarta, nasa A binciko mun ita amma an nemeta ƙasa ko sama babu, Ita kaɗai tasan uwa duniyar data shiga,"dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana mayar da numfashi,
Mu haɗu a Next Page, yanzu wasan ya fara gaba ɗaya book one Introduction ne wannan story ɗin cakwakiyar dake acikin shi, is hardly to make a prediction about what wll happen next😂 ...................
*Boss Bature ✍️
Taj kuwa tuni jikin shi yayi san yi, duk da ba su yi zaman lafiya da benazir ba, hakan bai sauya komai ba na daga son da yake Yi mata, Yana jinta sosai acikin ranshi, kusan tun ranar da ta gudu, kullum sai ya jaraba kira layin ta da daddare ko Allah zaisa ta buɗe shi, Amma kullum a kashe yake samun shi,
Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mashi tunaninshi"Ka sawwaƙe mata kawai, da ta je tayi ta aikata zunubi da auran ka akanta, don nasan ba dawowa zata yi ba,"
Girgiza kai taj yayi "baba bazan Iya ba, zan jira ta ne har ranar da Allah zai dawo mun da ita nasan zata dawo ne duk mun daran daɗewa"
Gyaɗa kai Alhaji ubaid yayi"Abunda nake fata kenan Yanzu ina jikar tawa take ne? Inaso na ganta,'
"Tana hannun Inna kulu, Ƙanwar matar maigadina ce, itace ke shayar da ita"
"Allah sarki Amma naji daɗi sosai, ka ɗauko mun Jikata na ganta kafin na tafi da yake bani kadai nazo ba akwai escorts dina dake awaje suna jirana"
Amsa ma shi ya yi da toh, kafin ya miƙe da sauri Ya nufi corridor ɗin da zata sada shi da ɗakin inna kuluwa Lokacin daya ƙarasa a kwance ya samu inna kuluwa tana bacci angel kuma na kwance gefen ta an sanya mata kayan sanyi ajikinta, sai faman tsotar yatsanta take yi, Murmu shi ya saki tare da kai hannu ya ɗauketa Ya fito da ita,
Ƙarasa wa yayi tare da miƙa ma alhaji ubaid ita Wani irin farin Ciki ne akan fuskar shi "Tabarakallahu ahsanul khalikin Taj kaga ikon Allah, Yarinya ƴar kyakkyawa sai kace rainon turai wannan idan ta girma ae zata iya ciyo mana gasar miss world,
Murmushi taj ya saki yana kallonshi addu'o'i ya shiga karanto wa yana tofa mata Taj na amsa ma shi da ameen ameen har ya kammala yi mata addu'ar, Fira sosai su ka yi da surukin nashi, har lokacin Angel na a hannunshi Sai da ya ta shi tafiya ne tukunna ya miƙa ma Taj ita
"In sha Allah zan dinga zuwa akai akai ina duba jikata, Yanzu ka tura mun account number dinka In sha Allah zakaga saƙona"
"Ngde ssae Allah ya kiyaye hanya, idan Anji wani labari game da benazir dan Allah a sanar min"
"Kada ka damu suriki na, duk inda take nasan tana sane da ƴarta da ta bari, kodan saboda ita zata dawo ne"
Har wajen da su ka yi parking na motocin su guda uku, Taj ya rako shi da sauri wani bodyguard Ya buɗe mashi mota ya shiga A jere motocin suka fuce,
Fitar su ke da Wuya, ba zato ba tsammani Sai ga alert na Miliyan 20 ya shigo wayarshi, Ya yi farin Ciki sosai da kuɗinnan dama yana ta tunanin yadda zai tafiyar da rayuwar shi da kuma rayuwar ƴar shi, ga kuma Iyayen shi da yake taimakama wa ga kuma albashin baba mai gadi, Salary ɗin shi basu isa ya dunga ɗaukar duk wani responsibilities nasu, A ranar yayi kwanan farin Ciki,
Bayan Wani Lokaci
Alamu sun nuna cewa Angel ba ƙaramar fitinanniya bace, don tun bayan wata ɗaya da aka haifeta, Taj ya yi ban kwana da yin Bacci cikin kwanciyar hankali, Saboda tsabar kukan ta, da ya ke a ɗaki ɗaya ya ke kwana da ita saboda tsabar son da ya ke yi mata, Kona seconds baison rabuwa da ita,sai suna bacci Idan ta tsala ihu tamkar wadda za'a zare ranta, har asibiti ya mayar da ita don aduba Lafiyarta, Still binci ke ya nuna tana da ƙoshin Lafiya,
Inna kuluwa kuwa da ke shayar da ita lokacin da ta fara Haƙora biyu agaba, Ba ƙaramar azaba take sha ba gartsa mata Cizo take Yi,baiwar Allah Ba ta ta6a sanar da taj halin da ake ciki ba, kullum sai tayi zazza6i duk da tana samun kulawa a wurinshi, Duk wani nauyi nasu ya ɗauke masu shi, Hatta Abincin da take ci wanda ke gina lafiyar jikinta Aneelarh ce ta rubuta masu komai, taj ya siya mata
Lokacin da baby ta fara rarrafe A wata na shida, Tayi 6arna kamar zata haukata masu gidan, da rarrafe take 6aro da kaya su zube kasa ta kacaccalasu akwai ranar da Ta samu wasu mahimman takaddu na Taj, Ta kekketasu into pieces, Ranar Har zazza6i yayi saboda muhimmancinsu kuma idan tayi 6arna taga ya zabga tagumi Yana kallonta Sai ta 6a6aka dariya kamar babban mutun haka sautin dariyarta yake, a lokacin da takai shekara ɗaya da rabi,
Da kanta ta daina shan nono, hakan yasa inna kuluwa ta yaye ta, a washe garin ranar da ta yaye ta, ta sanar da taj maganar komawarta ƙauyen su, ya yi mamakin jin zata tafi duk da irin rayuwar hutun da take yi agidan, Ba don yaso ba ya sallameta, kuma Yayi mata alheri sosai baiwar Allah ita kanta ba don taso ba, tabar gidan sai don zargin wani abu da take yi, Game da Ƴarshi to fah
Bayan tafiyarta kamar an ƙarama yarinyar rashin ji, har tsoro take ba taj saboda ƙarfin halinta, a kwai wani lokaci da ta addabe shi da 6arna, Sai ya dinga ɗaurata Saman Freezer dake ajiye A falo, sam ba ta so Yana ɗaura ta a sama, tun tana mashi kuka a karshe Sai gashi Idan ya daura ta da zarar Ya bar wurin sai ta faɗo kasa, Taci gaba da 6arna Abun Ya ɗaure mashi kai Yarinya sai kace aljana ranar da ta ƙure shi Keji yasa akayi mashi mai girma hada mukullin rufewa Ya sakata acikin kejin Yasa mukulli Ya rufe A tsakar falo ya ajiyeta, shi kuma Ya koma saman Sofa ya kwanta yana kallonta ranta Ya 6aci sosai tun tana gwarancin ta har takai ga fashe mashi da kuka, tausayinta Ya kamashi har baisan lokacin daya fiddo da ita daga cikin kejin ba, Ya rungumeta yana lallashin ta har ya samu tayi bacci, A daren ranar daga zuwa Yin sallar isha'e, Ya dawo ya taras Ta 6alla mashi Laptop dinshi da yake aiki da ita, idanuwan shi sukayi jawur ga shi bai iya koda yi mata tsawa ne balle aje ga bugu, A fusace ya ɗauke ta ya nufi gidan su aneelerh da ita ya kai ma Su, Yace ya basu kyauta su ruƙe ta awurin su,ba ƙaramin farin Ciki su ka yi ba, hannu biyu suka kar6eta ashe xaune bata ƙare ba A tunanin shi Ya samu hutu Daren Ranar bayan yayi wanka ya zura kayan baccin shi Ya kwanta cike da farin Cikin Yau zaiyi bacci hada minshari,
Wuraren ƙarfe 12:30 na dare, Can Cikin bacci Ya dinga Jin mutsu mutsun mutun ajikinshi, hakan yasa shi farkawa daga bacci, Yakai hannu ya kunna fitilar gefen gadon,
Kamar ance Ya dago karaf idanuwan shi suka sauka akan baby Angel dake kwance ajikin shi ta ƙanƙameshi, wani irin tsoro ne Ya ziyarci zuciyarshi, a firgice Yake kallonta Har wani murmu shi take sakar mashi, yarinyar da bazata wuce shekara 3 aduniya ba, Abun yayi mugun ɗaure mashi kai taya akai har ta yi wayon da zata iya Kamo hanya daga gidan Taj dake a jikin gidan shi ta dawo gida ƙarfe 12 da rabi na dare batare da jin tsoro ba,
Jiki a sanyaye Ya shiga yi mata addu'a yana tofa mata asaman kanta, Wai koda shaidanun aljanune suka shafe ta, sae faman lumshe ido takeyi alamar bacci zata Yi,
Babu yadda ya iya haka ya ƙanƙame ta a kirjinshi Yana shafa sumar kanta, Sae gashi bacci Ya ɗauketa bada jima wa ba shima bacci Yayi awon gaba dashi.
Wuraren Sallar asuba, Uzair da aneelarh suka buga uban sammako, Hankalinsu atashe Yarinya ta 6ace, Duk sun ruɗe Suna shiga falon Gidan Suka ci karo da Taj tare da Angel zaune saman Dining Chairs Hannun shi ruƙe da Kofin tea yana bata abaki tana sha,
A ruɗe suka kalli Juna, saboda tsabar mamaki kafin ma Taj yayi masu bayani Uxair Ya rufe shi da faɗa yana cewa 'Don me zaije Ya ɗauki yarinya batare daya faɗa masu ba, Yasa duk sun tashi hankalinsu,'sai da ya Kammala zazzaga mashi masifa,
Tukunna Taj yace"Wlh bani na daukota ba,dakanta ta dawo,
A sukwane Aneelarh tace"Wai dagske ita tadawo da kanta"?
Kafin taj ya basu amsa angel tariga shi cewa"Eh da ƙafafuna na dawo, kuma ma baba maigadi bashi ya buɗe mun ƙopa ba, ni na buɗe dakaina" tana magana tana cije le6e kamar ƴar daba,
Tashin hankalin da ba'a sama shi date! cike da tsantsar mamaki suke kallonta, Taya akai har ta iya buɗe ƙopar da ake rufewa da key?
Girgiza kai Taj yay "Lamarin Baby sai addu'a, Ina kwance jiya wuraren karfe sha biyu da rabi na dare naji motsin mutun ajikina a she itace ta dawo Ba ƙaramin tsorata Nayi ba"
Tabbas sun fara zargin Yarinyar tana da aljanu shiru kawai sukayi batare da sun sanar ma Taj abunda suke hasashe ba,
A daren Ranar Alhaji Ubaid Ya ƙara kawo masu ziraya, Kamar yadda ya saba duk in yana ƙasar sai ya zo, kuma duk in yazo sai ya kashe ma angel kuɗi kamar hauka kafin ya tafi,
A washe garin ranar da safe Ba zato ba tsammani Sai ga text message an tura mashi da baƙuwar Number, Benazir ce tayi saƙon Bakomai ta rubuta ba face Tana neman Saki a wurin Taj, kuma kada yayi tunanin zata dawo ta tafi kenan har abada abunda yasa ya yi farin Ciki da saƙon sanin cewa tana araye, Hakan ba ƙaramin kwantar mashi da hankali yayi ba, Har bibiyar Number da ta tura saƙon yayi amma a kashe ya sameta, Yaji takaici sosai tun yana sa ran dawowar benazir cikin rayuwar shi harya fidda rai, ba don yaso ba ya tura mata da text ta number yasan wata rana dole ta buɗe ta gani, Saki ɗaya yayi mata acikin saƙon daya rubuta mata....,......
A ranar Uncle abdallah ya dawo Nigeria, Uzair ne da kan shi ya ɗaukosu a Airport zuwa gidansu, tsabar farin Ciki a wurinsu bakinsu kasa rufuwa ya yi musamman Taj, hajiya adama tayi murnar ganin su Cikin ƙoshin lafiya Ranar yini tayi da angel awurinta, tun dawowar su Angel awurun su take kwana, Bakomai yafi ba Taj mamaki ba face irin yadda yarinyar take natsuwa agaban mutane, Amma idan shi da itane