Showing 195001 words to 198000 words out of 287659 words
Chapter 66 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
ruwa ko yin wani uziri wannan ƙopar zaku bi, Anan toilets ɗin mu su ke" Yana magana hankalin shi na akan Matashiyar yarinyar nan, dake ta kallon shi tana faman cizon pink lips ɗinta, ran angel idan yai dubu ya 6aci, bakomai yafi ƙona mata rai ba face ganin yadda take kallon Danish tana cizon le6e, tarasa gane me hakan ke nufi, to ko dai halittarta ce ahaka? Ko kuwa wani sabon salon iskancin ne"?
"Bana jin yunwa, I need to take bath, before in kwanta In huta" Ƴar gidan daddy ce tayi maganar tana ƙoƙarin sauke School bag ɗinta, Idon kowa na akanta, Miƙa ma Danish Backpack ɗin tai tare da cewa"Ka ajiye min ita, sannan ka raka ki toilet ɗin, bazan iya ganewa ba" Wani irin kallon harara angel take jefa ma Danish, duk yasha jinin jikin shi, Sam ya kasa kar6ar jakar Unaiza, Sai angel ce ta kar6e jakar tace"Zan ajiye maki ita, sannan zan raka ki toilet ɗin, idan ma kinaso har cuɗa maki baya zan Iya yi" Girgiza kai Unaiza tae tana fadin"No, bana so, ki dai ajiye min back pack ɗin, Shi sai ya raka ni toilet ɗin" mamaki ne ya kama angel, aranta tace"that's impossible, kinzo da bidi'a," Kar6ar jakar tayi daga hannun unaiza taje ta ajiye mata ita gefen donta mai ɗauke da no 16, juyowar da za ta yi, karaf idanuwanta suka sauka akan Unaiza da ke ƙoƙarin cire Coat ɗinta, Bakomai ne ya faɗar mata da gaba ba, face Ƙirjin Unaiza, Musamman da ta ƙarasa Cire rigar Hankalin Kowa Ya koma kansu, Kamar babu riga ajikinta saboda Yadda surar su ta bayyana ajikin vest din, Manya manya dasu kamar balan balan, shatun nipples ɗin sun fito sosai, kamar zasu huda ta, gata yarinya amma tubarkalla, Allah yayita da boobs, "
Kwanciyar hankali ya ƙarewa angel, Kishi ne ya addabi zuciyarta, kodan hada ƙarin ita bata da su ne, Oho dai,
Bayan Unaiza ta ɗebe Coat ɗin Ta miƙa ma Danish tace Ya ruƙe mata, Hannun shi na kerma ya ruƙeta, wani irin ƙamshi ne ke fita jikin coat ɗinta," hannayenta ta ɗaura saman gajeran skirt ɗinta, Waro ido angel tae baki a sake take kallon ikon Allah, Cire shi tae ya rage daga ita sai Short na mata, "
duk su naufal suna a tsaye suna kallon ikon Allah, Miƙe ma Danish Skirt ɗin ta yi"Ka ajiye min su" Kafin yai yunƙurin kar6ar skirt ɗin angel tai saurin komawa wurinsu ta sanya hannu ta kar6i skirt din ta kuma ƙwaci coat ɗin dake a hannun Danish, Fuskarta a ɗaure ta nufi akwatinsu ta sanya mata su a ciki, Kafin ta dawo ta tsaya agefen Danish,
"Muje ka raka ni toile ɗin" ta yi maganar tana ƙoƙarin ruƙo hannunshi, Angel tae saurin ka6e mata hannun"Ni zan raka ki," Bata jira amsar da unaiza zata bata ba, Taja hannunta, ta wuce da ita zuwa sashen toilet ɗinsu, sai bayan da suka shige, azeeza da parveen suka kalli juna, Alamar mamaki, sufa sunga abunda basu ta6a ganin irin shi ba, tun da ko tsohuwa nata azube suke kamar silifas, Cikinsu kuwa ba wadda ta ke da su irin na ƴar gidan daddy, har ƙwara waɗan da suka fara manyanta, Sune ya fara fito mawa, amma ita ko wannan ƴar shilan ƙirjinta sunfi ƙarfin jikinta da shekarunta.
"Gabriel, banji kace komai ba"? Danish ne yae mishi magana ganin yayi tsaye bai motsa ba shi da sauran ƴan uwan nashi, Cikin sanyin murya yace"Inaso na kwanta, saboda kaina ciwo yake yi min" Nuna mashi gadonshi danish yae da hannu, Yace mashi thanks kafin Ya nufi gadon, Sai da ya fara cire coat ɗinsa, Ya ɗaura ta gefe, Sannan ya haye gadon ya kwanta,
Kallon Jamima su kayi ƴar ƙaramar yarinyar nan, parveen ta raya aranta cewa"Wannan dai rainonta zamuyi da alama" Haris ne yace da ita"Kefa? Zaki kwanta ko xaki ci abinci" Ta6e baki ta ɗanyi kafin tace"Yunwa nake ji," Deeja tace"amma ke kike yin wanka da kanki"? Ɗaga mata kai tayi"Eh, inayi yanzu, amma sai ana cuta min bayana saboda hannu na bai kai wa" Murmushine ya bayyana akan fuskokinsu, don ba ƙaramin burgesu tayi ba, gata ƴar kyakkyawa da ita, Hibba tace"idan ma kinaso har wankan sai muyi maki," dariya tasaki tare da sanya tafin hannayenta ta rufe fuskarta, alamar taji kunya.
Ruƙo hannunta Haris yae acikin nashi yace"muje muci abinci ko"? Tace mishi eh, " mubeen yace"to itafa Wannan bamu ji ra'ayinta ba, " yae maganar yana nuna Sarah dake atsaye Ta ruƙe qugu, Yatsina fuska Ta ɗanyi can kuma saita ƙaƙaro murmushi tace"Nima bana Jin yunwa, zan kwanta na huta ne" tae maganar tare da juya ta nufi gadajensu, Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, a sukwane Ta juyo ta kalle su Deeja tace"wai a ina zata kwanta ne"?
Nan take su ka fahimci cewa Ta raino gadon ne, Wato yayi mata ƙanƙanta, Hannah tace"Acan inda kuka Baro, a saman Ina ki ke kwana ne"? ta6e baki Sarah ta yi Ba tare da ta bata amsa ba, Ta maida idonta kan gadon, Ta curo bargon saman shi, Ta shimfiɗashi a ƙasa, ta ɗauko pillow ta jefa, Kafin ta cire coat ɗin Jikinta ta ɗaura a ƙasa, Ta faɗa sama gadon ta kwanta.
A bunda ya faru bayan Angel ta raka ƴar gidan daddy toilet, suna shiga ciki taja burki ta tsaya Tana faman zazzare blue eyes ɗinta haɗi da yatsina fuska, Angel tace"Ni xan Koma, ayi wanka lafiya" har zata juya muryar Unaiza ta dakatar da ita
"Nifa ban fahimta ba, Ina bathtub yake ne? tana nufin (kwamin wanka) Wannan wani irin toilet ne kamar na Marasa galihu" Tsabar mamaki yasa angel sakin baki kamar sakarya tana kallonta, Daƙyar ta iya buɗe baki tace"ba mu da bathtub, Iya a bunda idonki suka gane maki acikin toilet din su muke dasu, Ga Shower nan, Sai kuma bokiti, can kuma Soso ne da sabulu," aruɗe unaiza tace"that's Impossible, ae ni bana sharing soson wanka, Kuma bana wanka in ba a cikin bathtub ba, I can't stay here i wanna go home, cos daddy ba haka Ya kwatanta min school ɗin ba, Yace min fa komai irin na Gidan mu ne, but why naga banbanci"? tamkar zata fashe da kuka tayi maganar, har saida gaban angel ya faɗi jin abunda tace, Wato ita duk a tunaninta School ce aka kawota batasan cewa Prison bane, To me hakan ke nufi? Kodai mahaifinta ne ya yi mata ƙarya kan cewa za'a kawo ta makaranta! Tashin hankali Sai lokacin angel ta tuna da irin uniform ɗinta na gayu, dama ta yi mamakin ganinta da haɗaɗɗun takalma ƴan ƙwaras ƙwaras, Ga gajeran skirt na gayu, Ga kuma ƙatuwar School bag Ta goyo, Tabɗijancan, In dai a bunda take hasashe ya tabbata to kuwa Iyayenta sun Cuce ta, Mamaki Ya hana angel cewa komai, taya akai basu gusar mata da hankalinta ba? Kamar yarda aka yi ma Gabriel? Ko kuwa sihirin ne bai kama Jikinta ba?
ta yi zurfi acikin tunaninta muryar unaiza ta katse ta"Pls talk to me! Ni ban fahimci komai ba, game da school din nan," tashin hankali ne Ya bayyana ƙarara akan fuskar angel, miryarta na ɗan rawa tace da unaiza"wacece ke? Dama ke ba rainon Kurkuku bace"? Waro ido tae tare da maimaita sunan prison da angel ta faɗi, Ba don ta fahimci me hakan ke nufi ba,
"Ban fahimce ki ba, Naji kince prison, Nifa daddyna yace dani xai sanya ni a high school Na south korea, saboda inason kallon drama ɗin su komai nasu yana ƙayatar dani, Daddyna yana yi min komai nake so, shi ne Da kanshi, Ya sama min admission a school ɗin nan, a gida aka kawo min uniform na sanya ajiki na......" unaiza bata ƙarasa maganarta ba, Angel ta ɗaura hannunta akai,! Irin ta shiga ukun nan, fito wa ta yi daga Cikin toilet ɗin Ta tsaya daga waje tana ambaton"Innallahi wa'inna ilaihirraji'un"! da sauri ƴar gidan daddy ta biyo bayan angel, baiwar Allah duk ta ruɗe ta rasa gane me angel ke nufi,
"Pls tell me the truth Ko ba school bane nan ɗin? I ave to know" wani irin kallon tausayi angel ke binta dashi, muryarta kamar ta mashayin giya tace"Zaki iya tuna Ta ina aka kawo ki Nan" girgiza kai tayi"I can't remember, Ni dai nasan time da masu aikin gidan mu, suka taimaka min nayi wanka na sanya uniform da daddyna ya bani, so bayan nan sun rakoni zuwa wurin da motocin bodyguards ɗina su ke, sun buɗe min mota, Na shiga Ciki na zauna, ina ta farin ciki, duk na qagara mu ƙarasa Airport sai bacci ya ɗauke ni, daga nan ban ƙara tuna komai ba, sai dai na ganni Acikin School ɗin nan tare da sauran students din da muka zo da su" Tana magana tana yatsina fuska daga gani ɗabi'arta ce yin hakan,
Jinjina kai angel tae yayin da take kallonta, haƙika ta yi mamakin da basu canza mata tunaninta ba, tun da har ta iya faɗin yadda aka kawota Cikinsu, tabbas kowanene Ubanta ba ƙaramin Mugu bane, Azzalumi, Wato shi wayau yayi mata ya fake da cewa za'a kaita Sk don ta yi karatu batasan cewa Sadaukar da ita ya yi ba zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara, don biyan wata buƙata tashi, Rayuwarta abun tausayi baiwar Allah, Sai da aka gama sangartata, Daga gani an gama jiyar da ita duk wani daɗi na duniyar nan kafin aka tsamota daga aljannar duniya aka kawota gidan kurkukun ƙaddara,
Ganin irin kallon da angel take binta dashi ne yasa tace"Pls Ke nake jira ki bani amsa," A ƙagare tayi maganar,
"Ya sunan mahaifinki? Kuma wanene shi"? Muryarta A disashe tace"Ae ni bansan real name nashi ba, na dai san ana kiran shi Jan wuya..." bata ƙarasa maganar ba angel ta katse ta da cewa"Ba ki ta6a zuwa school bane? Da wani suna kike amfani"? Ta bata amsa da cewa"ni tunda na taso ban ta6a zuwa school ba, daddyna bayaso ina shan wahala, A gida ake koya min karatu, yanzu ma don na kwallafa raine akan inason zuwa south korea karatu shine yace zai sani...."
Jinjina kai angel tae kafin tace"Amma awace ƙasa ku ke zaune duk da naji kina magana da yare biyu, hausa da turanci so na kasa gane wani jinsi kike"
Wannan karan tamkar zata fashe mata da kuka ta yi maganar don ta gaji da tsayuwa,
"My dad is from Nigeria and my mom is from England. I've never been to Nigeria, and I don't know my dad's hometown or his job, Ni da Mommyna ne kawai muke rayuwa a england sai ƴan Aikin gidan mu, amma yana yawan zuwa kawo min ziyara daga Nigeria"
Hankalin angel ya ƙara tashi, daƙyar tace mata yanzu kiyi haƙuri kiyi wankan idan kin kammala zanyi maki bayanin komai" Girgiza kai tayi"ae bazan iya wanka awannan toilet din ba, saboda ba irin na gidanmu bane, ni nasaba acikin bathtub nake yi, kuma masu aikin gidan mu ne suke taimaka min wurin yin wankan"
Kallon ta kawai angel ke yi, Iya cutuwa dai an Cuci yarinyar nan, tama rasa taya zata fahimtar da ita cewa Nan kurkuku ne, ba high school ta ƙasar korea ba? Zaiyi wuya ta fahimce ta, babbar matsalar irinsu Suna da ƙarancin imani, sannan basu da tawakkali, Tana iya ta faɗa mata azo asamu matsala, Ya za tayi da ita?
Yayin da su Angel suke a sashen toilet dinsu ita da ƴar gidan daddy, Su kuma can ɗaki suna fama da wannan mahaukacin Yaron, abunda ya faru Suna ƙoƙarin zuwa suci abinci, Eve tace dasu,
"Wai nikam Ina Yaron nan yake ne"? Kafin wani ya buɗe baki ya bata amsa suka Ji ƙarar karyewar wani abu acikin kunnuwansu, Agigice suka kai idanuwansu wurin da suka Jiyo sautin ƙarar, ransu yae mutuƙar 6aci ganin Irin uwar 6arnar da Yaron yayi musu, Gaba ɗaya Ya kado da cake ɗinsu ƙasa, Table ɗin Ya 6alle, Cake ɗin ya ƙundumo kasa Ya tarwatse, hakan bai ishe shi ba, sai da ya hau saman Cake ɗin Ya dinga duma hannuwanshi aciki Yana Kwaso shi Yana turawa abakinsa, duk ya 6ata uniform ɗin jikin shi da cake ɗin, A ƙarshe ma sai ya hau saman Cake ɗin ya dinga burgima yana dariya, a fusace parveen ta nufi inda yake, Haris da Danish suna ta ƙoƙarin dakatar da ita akan kada ta buge shi, amma ina ko waiwayon su bata yi ba, wata irin damƙa takai ma wuyan rigar shi, ta ɗago dashi ta daddage ta buga kanshi a ƙasa, azabar zafi yasa shi fashewa da kuka mai tsiwar gaske, tana huci tace"Shege ashe kana jin bugu, ae nayi tunanin kurma ne kai" Sautin kukan yaron ne ya karaɗe kunnuwansu angel dake a sashen toilet ɗinsu, da gudu suka nufi ɗakin suna shugowa suka ci burki suna kallon Yaron dake ta kuka, Hatta gabriel dake kwance yana bacci shi da Sarah sai da suka farka saboda sautin kukan fitinannan Yaron, An rasa me lallashin shi acikin su, haushin shi suke Ji, Ya baƙanta musu rai, duk irin yadda suka ƙwalla fa ransu ga son cin cake ɗin nan ya tarwatsa komai, Farin Cikinsu Ya gushe, Har ga Allah basu Ji daɗin zuwan prisoners ɗin nan ba, Saboda mutun biyun nan dake acikinsu, Mahaukacin yaron nan da Angel ta sanyawa suna Majnun saboda Yaƙi faɗa musu sunanshi, Sai kuma Unaiza ƴar gidan daddy, A ranar Bayan Danish ya lallashi Yaron Yaje dashi toilet ya wanke mishi Jikin shi Da uniform ɗinshi da ya 6ata da cake, Ya shanya su saman igiyar toilet ɗinsu, ya ɗauko bargo Ya ƙudundune shi ajiki yakai shi Daki ya kwantar dashi saman gadon shi, Cikin ƙanƙani lokaci bacci yayi awon gaba dashi, Hankalinsu har ya kwanta, ashe ƙura bata lafa ba, Sun gama shan wahalar gyara ɗakin nasu da ya 6ata musu ya hargitsa komai, Suna ƙoƙarin zama su huta, Unaiza tace musu Yunwa take ji, Suka ce mata Ga abinci can saman dining carpet ɗinsu taje taci, Saboda damuwa ma yasa babu wanda ya waiwayi abinci acikin su, Sai wannan ƙaramar yarinyar jamimah ita kaɗai ta zauna tana ci.
Ita ko Unaiza ƴar gidan daddy ta ce musu ba zata ci ba saboda a gidansu saman dining table ake jera mata abinci kala goma sha biyar, sai ta za6a ta darje, hatta abincin ma abaki masu aikin gidansu suke bata tana ci" gaba ɗaya ta rikita su da maganganunta, sun gaza gane inda ta dosa,
Duk yadda suka so su lallasheta akan taci abinci taƙi ci, tace musu dole a kira kukun da suke girƙa abinci a makarantar ta, don ta faɗa musu kalar wanda ake girka mata agidan daddynta, idan har suna son zaman lafiya, idan ba haka ba zata yi magana da shugaban makarantar yayi musu magana, " Su angel sun sha dariya kamar zautattu jin wani sokiburutsi na Unaiza, Sun maida ta mahaukaciya, ta zamar musu tamkar Comedy, kuma ita har ga Allah dagaske take basu Umarni, Rashin sani yafi dare duhu.
Lokacin da dare Ya tsala, Babu wanda Ya runtsa acikinsu daga su har sabbin prisoners ɗin saboda rigimar Mahaukacin yaron nan MAJNUN! ya addabi rayuwarsu tun da ya farka daga bacci, Ya dinga Tsalle tsalle har saman gadajen su, Ya hanasu sakat, Su azeeza sun sha kuka saboda ƙululun baƙin cikin daya dasa musu, Har bugunshi suka so suyi amma Danish ya hana su, ya basu haƙuri akan kada su ta6a shi yaro ne, ba dan sun so ba suka Haƙura suka ƙyale shi, Taimakon da Allah yayi musu yaron baison duhu, Sun gane hakan ne lokacin da Danish Ya sauko daga saman gadonshi yaje ya kashe floor lamps ɗin ɗakin, Duhu ya gauraye ko'ina, ai kuwa ya birkice musu ya dinga kuka yana fadin su taimaka mashi, dodo zai cinye shi, angel tace munafuki ai kaine dodon daka addabi rayuwarmu ashe kana magana, nayi tunanin kurma ne kai.
Daƙyar Danish Ya ruƙo hannun shi Cikin duhu Ya kai shi saman gadonshi ya haye Yana faman sauke ajiyar zuciya, ganin ya samu natsuwa ne, ya tambaye shi ya sunanshi, Muryarshi adisashe ya ce"CHINONSO" jinjina kai Danish yai kafin ya miƙe ya rufa mishi bargo saman Jikin shi.
A washe garin ranar da aka kawo musu sabbin prisoners, lokacin Da Giants suka zo kawo musu Abinci, Sun ga haukan da basu ta6a gani ba, wato unaiza ce ta tsare giants tana zazzaga musu masifa akan su bi tsarinta, na gidan daddynta, hada ƙoƙarin ɗauko jotter acikin school bag ɗinta tare da biro ta rubuta musu list na abunda take so adinga girka mata tana ci, bayan ta gama ta je gaban su ta miƙa musu paper ɗin data yago cikin jotter din, tace dasu su kar6a, Kamar gumaka babu wanda ya motsa a cikin su,
Su haris suna ta ƙoƙarin fahimtar da ita akan ta matsa daga gabansu basa magana, amma taƙi sauraransu, ba don Allah yasa Naufal Yaje ya janyeta ba, da ranar ta yabawa aya zaƙinta, don wlh mazga zata sha awurin su, don basa ɗaukar raini.
A taƙaice Cikin kwana uku sai da suka fita hayyacinsu, Akan mutun biyun nan Unaiza ƴar gidan daddy da kuma Majnun Chinonso,
Wata sabuwar rigima ta unaiza, ta faɗa musu cewa ita fa Ta saba agidansu masu aiki suna yi mata tausa, don haka suma dole suyi mata, Kuma idan zata kwanta bacci, Da pillow uku take kwana saman gadonta, ta saba duk in zata kwanta, tana ɗaura kanta saman pillow, ɗaya kuma A tsakankanin ƙafafuwanta, Cikon na Ukun A ƙirji take rungume shi, Ba tare da sun yi mata musu ba, Su Parveen su ka yi mata tausa, Lokacin da dare ya yi Danish da Mubeen suka bata pillows ɗin su don ta kwanta kamar yadda ta saba yi agidansu, Idan fa tace su yi mata abu su ka ƙi yi mata, Kamar ƙaramar yarinya haka zata zauna tana raira musu kuka, waya ga shagwa6a66a
Haris yace"Su ƙyaleta Ai wadda tafita iya masifa tazo kuma ta miƙa wuya sun yi rayuwa da daɗi da ba daɗi balle kuma ita, " Wato yana magana akan angel, sai dai fa akwai banbanci sosai tsakanin Angel