Showing 276001 words to 279000 words out of 287659 words
Chapter 93 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
ruƙo hannun shi ta yi a cikin nata tare da jan shi don su shiga ciki ko motsi wannan baiyi ba, hakan yasa ta fashe da kuka tare da ɗaga murya tana yi ma su batul magana "Wai bazaku zo ku taimaka mashi ba? Kun barshi shi kaɗai a tsaye" babu wanda Ya juyo ya kalle ta Hankalin su ba akanta ya ke ba, Tsagaitawa tayi da yin kukan tare da kallon fuskar shi wata irin zufa ce ke tsastsafo mashi, Ya galabaita sosai, Cikin shessheƙar kuka ta ambaci sunan shi, bai amsa mata kiran da ta yi mashi ba, Sai dai taga Ya zuƙunna saman matakalar benan Yana faman Fitar da numfashi mai ɗumi.
"Ka tashi mu shiga ciki, Inaso na taimaka maka" A hankali yake bin ta da kallo fararen idanuwan shi sun canza launi zuwa ja, daga gani ba ƙaramin jin jiki ya ke yi ba, azeeza sarkin tausayi hada sanya Ƙasar rigarta saman fuskar shi tana share mashi gumin da ke tsastsafowa, acikin zuciyarta ba ta ji dadin yarda su Batul suka manta da zancen shi ba, Shi kaɗai suka ware, marairaice mashi fuska tayi "Pls ka tashi mu je ka kwanta, baka da lafiya fa, Nasan baka jin dadin Jikin ka,......" tunkan ta ƙarasa maganar Gabriel ya yunƙura ya miƙe, Daurewa kawai ya ke yi don ba ƙaramin jiri yake gani acikin idanuwan shi, ƙoƙarin Yin tafiya yayi Ƙafarshi ta Hagu taƙi bashi haɗin kai, Gaba ɗaya Ya tafi zai kife ƙasa, Azeeza ta fasa uwar ƙara haɗi da ambaton sunan shi, hakan ne ya jawo hankalin su Parveen ga kallonta A lokacin har sun taimakama su Haris sun kwanta saman gadan su, Da gudun gaske suka nufi Gabriel dake ƙoƙarin faɗuwa, Da ya ke Namiji ne Allah yayi shi da ƙarfi bai bari Ya faɗi ƙasa ba, Handrail ɗin benan Ya dafe da hannun shi, Sai faman Huci ya ke fitarwa, Nannaɗaɗar sumar gaban goshin sa duk ta rufe idon shi, Koda su parveen suka ƙaraso ganin ya dafe Hannun benan yasa suka sauke ajiyar zuciya, Azeeza kamar jira ta ke yi su ƙaraso ta dinga surfa masu bala'e akan sun tafi sun bar ta da shi, bayan sun san ita ƙarama ce, da ace ya faɗi kasa kanshi ya bugu me suke tunanin zai biyo baya, Faɗa sosai ta rufe su dashi, ta inda take shiga bata nan take fita ba, sai faman tada jijiyoyin wuyanta take yi duk akan Gabriel.
"Allah ya huci zuciyarki Azeeza bada son ranmu muka ƙyale shi ba, Hankalin mu ba a kwance Ya ke ba, Amma yanzu kiyi haƙuri, zamu shiga dashi Ciki" Fuskar Yasmin a hautsine tayi mata maganar, ɗaure fuska azeeza tayi hada ruƙe qugu tana binsu da kallo.
Parveen da Yasmin ne suka taimaka wurin ruƙo Gabriel Suka nufi Cikin ɗakin dashi, agaban gadon shi suka sake shi ya hau ya kwanta, Daga gefen shi Azeeza ta hau ta kwanta tana ƙare mashi kallo mai nuni da tsantsar ƙaunar shi kewar shi da Tausayin shi.
a 6angaren Haris Deeja ce zaune saman gadon shi, Eve da yasmin suna zazzaune gefen gadon shi, Sai sannu su ke yi mashi, Sam ya kasa amsa masu, Sai dai yabi su da ido,
Javed Yana a kwance saman gadon shi, Batul da Sarah ne Zaune gefe da gefen mattress ɗinshi, Ji su ke kamar su ɗauke masu ciwon Jikin su saboda tsabar tausayinsu da su ke Ji,
Idan muka koma 6angaren Naufal Shima Yana kwance Ya lumshe idanuwan shi, Parveen da Hibba suna a zaune saman gadon nashi, suna yi mashi sannu.
A yayin da Hannah da Rubina suke akan gadon Mubeen, hakan ba ƙaramin sanyaya zuciyoyin ƴan uwan nasu yayi ba, Ganin yadda suka nuna damuwa akan su,
"Yanzu ya zamuyi? Ko abinci babu da zamu Iya basu nasan dole suna jin yunwa," parveen ce ta yi maganar,
"Ko ruwa ne mu fara basu Mu ga idan zasu sha" a cewar Batul, Jin suna maganar ruwa yasa Jamimah ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta lalubo robobin ruwa taje ta miƙa ma Deeja, Bayan ta kar6a taje ta miƙa ma parveen kafin ta nufi Batul ta bata ɗaya" da sauri ta koma ta ɗauko sauran robobin ruwan guda biyu Ta kaima Hanna ɗaya, sannan ta nufi gadon Gabriel Ta miƙa ma Azeeza, Hannu tasa ta kar6i robar ruwan tare da miƙewa zaune ta cire murfin kallon shi tayi, Still idanuwan shi Na akan fuskarta,
"Ruwa ne ka tashi ka sha" tayi maganar tana nuna mashi robar ruwan, Da ƙyar ya yunƙura Ya tada kanshi saman pillow, Yatsun hannun shi sai kerma suke Yi ya gaza iya ruƙe robar, hakan yasa ta kafa mashi ita saitin bakin shi ya soma kur6ar ruwan Yana bi ta makoshinsa, A tsanake Azeeza ta ke kallon fuskarshi Ya canza sosai, kamar ba Gabriel ɗin da ta sani ba.
Bayan kowannan su Yasha ruwan, Jamimah ta tattara robobin ta maida su ƙarƙashin gado ta killace su,
Har yanzu babu wanda Ya tuna da Angel a cikin su, bacci ne ya fara ɗaukar su Javed, cikin ƙanƙanin lokaci baccin yai awon gaba dasu, ganin sun samu bacci yasa hankalin su Batul ya ƙara kwanciya. Kamar sun samu tv haka suka tasa su agaba suna kallon su yayin da su ke yin bacci,
Farin Cikin su ragagge ne, Abu Biyu ya tsaya masu aransu, Na farko Meyasa ba a dawo da Danish ba, Bayan An riga tafiya dashi? Na biyu me aka yi masu na tsawon watannin nan? basu da amsar tambayoyinsu.
"Allah sarki Danish ɗinmu shi ba'a dawo mana dashi ba, Na yi tsammanin dukan su zamu gansu" Batul ce tayi maganar, Deeja tace"saboda mugun nufin su akan shi sunƙi dawo mana da ɗan uwanmu, Nafi damuwa dashi saboda halin da aka tafi dashi, "
Da alama ransu ya 6aci sosai na rashin dawo masu da Danish, tsawon Awanni Sunyi zugudum babu mai Magana a cikinsu, Wuraren marece Mubeen Ya farka daga bacci, A matuƙar firgice ya zabura ya miƙe zaune Yana haki Gaba ɗaya idanuwan su akan fuskar shi, Kafin su yi yunƙurin tunkarar shi Ya duro daga saman gadon shi kafar shi kamar zata 6alle A haka ya dinga janta ya nufi Sashen toilet ɗinsu, Da gudu Hannah dasu Yasmin suka bi bayan shi, A cikin toilet suka tarar dashi Ya zuƙunna gaban fanfo Yana kwara amai, Wani irin Farin abu mai yauƙi yauƙi ya ke fitowa daga bakin shi har ta hancin shi ya dinga gangarowa, Wa'iya zubillahi! Zuciyoyin su sun karaya da ganin yadda Mubeen ke kwara aman fargabar su kada ya mutu kamar yadda unaiza ta tafi tabarsu, Tuna wannan yasa hawaye wanke fuskokinsu, A gaban shi suka zuƙunna suna kallon fuskar shi, Sai nishi yake yi Yana jan numfashi a wahalce,
"Mubeen dan Allah ka jure, bamu so wani abu ya same ka, Kaga Muna ƙaunar ka sosai" a hankali ya ɗago da idon shi kan fuskar Parveen da tayi maganar, Girgiza kanshi ya yi yana faman cizon la66an shi ya soma magana "Kada ku tada hankalin ku akaina, lafiyata qalou," tun daga kan yarda yai maganar zai ƙara tabbatar maka da Babu lafiya a jikin shi, ya faɗi hakan ne kawai don ya kwantar masu hankalin su,
"Wlh baka da lafiya Mubeen, Kalli yadda idanuwan ka suka canza launi, kamar ba mubeen ɗin mu ba", murmushi ya ƙakalo akan fuskar shi Yayin da ya ke kallon Hanna da ta yi maganar,
"Nifa lafiyata qalou, Nagode da kulawar ku agare ni, nayi missing ɗinku sosai," Cikin sanyin murya ya furta hakan, A hanzarce Batul ta miƙa hannu ta kunna fanfo ruwa ya soma zubowa, tarba tafin hannayen ta tayi Ruwa ya taru a cikinsu ta wanke mashi fuskar shi tare da zuba mashi ruwan a bakin shi Ya kuskure shi, Bayan ta kammala ta ruƙo hannun shi "Mu koma ɗaki Mubeen" Sai da suka taimaka mashi tukunna Ya iya miƙewa, fitowa su ka yi daga Cikin toilet zuwa ɗaki, A saman gadon Shi Ya kwanta Yana faman sauke ajiyar zuciya, kewaye da gadon shi suka tsaya suna tottafa mashi addu'o'i, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mashi ba, bayan sun samu komai ya lafa suna shirin komawa su zauna Kwatsam Gabriel Ya farka Hananyen shi biyu daddafe da kanshi Ya fasa wata irin gigitacciyar ƙara da ta janyo hankulan su Gare shi, Jikin shi sai kerma yake yi musamman la66ansa, Sambatu ya ke yi na fitar hayyaci, A hankali Su ka soma tafiya suna tunkarar gadon shi, A kewaye da gadon shi suka ja burki suna ambaton sunan shi Muryoyin su a tsorace
"Gabriel! Meke damun ka? Faɗa mana ina ke yi maka ciwo," Shiru bai tanka masu ba, Hankalin Azeeza duk yafi tashi don tuni tafara sharar ƙwalla, tsananin tausayin shi ne ya kama su, musamman da ya daddafe kanshi sai ya tuna masu da Danish, duk idan ciwon shi ya tashi haka ya ke yi masu ya dinga fasa ƙara,
"Gabriel are u okey? Kan ka yana maka ciwo ne"? Azeeza ce ta ke tambayar shi, Deeja tace "Ku ɗan jira in jaraba yi mashi Karatu kamar yarda Angel ta ta6a Yima Danish wata'ƙil shima yaji sauƙi, ta ƙarasa maganar tare da hawa saman gadon ta matsa kusa dashi ta tallabo kanshi da yatsun hannayenta tare da ɗago dashi, Saitin kunnan shi na dama ta kai bakinta, Kafin a tsanake ta soma Yi mashi karatun qur'ani, surorin da ta haddace akanta, fatiha, iklas, Falak da nasi, da wasu ayoyi irinsu Ayatul kursiyyu, Amanar rasulu da sauransu, A nutse Deeja take karanta mashi su cikin kunnan shi, su Parveen duk suna a tsaye bakin gadon suna kallon shi azeeza tana zaune daga gefen shi, ga dukkan alamu natsuwa ta fara shigar shi, don tun da ta fara Jikin shi ya daina kakarwa, natsuwa ta fara shigar shi, A hankali ta zame Hannayenta daga saman kanshi,
"Da sauƙi jikin naka"? Tayi maganar tana kallon fuskar shi, sai faman lumshe idanuwan shi ya ke yi, daƙyar ya iya buɗe baki Ya amsa mata da cewa "Am ok, Ina fata mun same ku lafiya," har suna haɗa baki wurin furta mashi "Muna Lafiya" parveen tace "faɗa mana su wanene mu, don ni ban yarda ka dawo dai dai ba," A hankali ya ke kallon fuskokin su ɗaya bayan ɗaya Ya soma faɗa masu sunayen su
Hannah Hibba Deeja, Parveen, Eve, Yasmin, Batool, Rubina, Aziza, Sarah, Jamima......." tunkan ya rufe baki yaga suna ta murna ganin ya dawo dai dai, haƙiƙa Yaji daɗin kulawar su gare shi, Sai dai abu ɗaya daya faɗar mashi da gaba rashin mutun ɗaya acikin su, Yarinyar da ya ƙwallafa rai akan son ganinta, don su dasa daga inda su ka tsaya
"Where's ANGEL"? Ras gabansu Ya faɗi Jin tambayar da ya yi masu, Nan fa suka fara kallon kallon a tsakanin su fuskokinsu ɗauke da matsananciyar damuwa
"Inna lillahi..! Mun manta da Angel! Tun ɗazu da safe ta shiga toilet ta datse, Ba irin bugun da bamuyi ma ƙofar ba amma ta ƙi buɗewa, bamusan me ta ke yi a ciki ba"
Muryar Haris ce ya janyo hankalin su ga kallon shi, Farkawar shi kenan daga bacci Yana ji suna zancen Babu Angel, Jikin shi A raunane Ya yunƙura Ya miƙe zaune, Da sauri Deeja ta nufi gadon shi ta haye sama ta zauna tana kallon shi,
"Haris Sannu Ya jikin Naka? Ina fata ba inda ke yi maka ciwo" murmushi ya sakar mata yayin da ya ke bin ta da kallo, daga gani ba ƙaramar kewar ta yayi ba,
"Deeja lafiyata qalou, Jiki na da sauƙi, Naji ana zancen babu Angel me ya faru da ita? Ko sun zo sun ɗauke ta ne"?
Girgiza mashi kai tayi alamar a'a "Ɗazu da safe ta shiga toilet yin wanka, bamusan meya faru da ita ba, mun jira ta buɗe mana ƙofa amma shiru, mun yi iyakar bakin ƙoƙarin mu wurin ganin mun 6alle ƙofar amma taƙi buɗuwa,' deeja na kai ƙarshen maganar ta, Batul ta jefa masu tambaya "Haris Ina Danish ɗinmu"! Ɗago wa yai da idon shi tare da kallonta, Mamaki ne ya bayyana akan fuskar shi
"Kamar batul nake gani! Yaushe aka dawo da ke?" Murmushi ta sakar mashi tare da cewa "Tuntuni na dawo, Na yi kewar ku sosai," Jinjina kan shi ya yi kafin yaci gaba da magana "Bansan inda Danish ya ke ba, saboda ba'a tare mu ke dashi ba, tsawon lokacin nan bamu ta6a Yin tozali da shi ba," Idon Gabriel akan Batul Sai yanzu da ya dawo hayyacin shi ya gane ta, Yasan cewa ƴar uwar su ce da suke ta nema, kuma itace Yarinyar da ya gani a kwanakin baya saman Third floor Tana gudun ceton Rai! Baisan ya akai ta dawo ba, Sai dai yaji daɗin ganin ta da ranta da lafiyarta.
"Ƴar uwar mu ce Batul, nasan baka santa ba" Azeeza ce tayi mashi magana ganin yana kallonta, Numfasawa ya yi tare da saukowa daga saman gadon kamar zai kife kasa saboda rashin ƙwarin Jikin shi
"Ina zaka je"? Atare su Hibba su ka haɗa baki wurin yi mashi magana
"Inason ganin Angel, ku nuna mini ƙopar toilet ɗin da ta shiga, zan yi ƙoƙari in 6alle ta"
"Kana fama da kanka Gabriel taya zaka iya 6alle ƙofa, tafiyar ma daƙyar ka ke yinta, Pls Ka koma ka zauna bazamu bari ka Ƙara raunata kan ka ba, " Hannah ce tayi maganar tare da ruƙo hannun shi, ba don ya so ba ya koma ya zauna daga gefen gadon shi.
Hankalinsu Ba ƙaramin tashi yai ba, sun gama murnar dawowar su Haris damuwar rashin Angel ta hana su sakat ga dare har ya gabato amma babu ita, Jamimah sai kuka take yi masu akan Su Je su buɗe ƙofa su ɗauko Mata Genie ɗinta Idan suna son zaman Lafiya, Sun saba atare su ke kwaciya bacci, kwanakin nan ita ke yi masu shimfiɗa a saman floor.
Komawa Cikin sashen toilet ɗin su ka yi, Don su ƙara jaraba ƙarfi ko sun samu ƙofar ta buɗe masu, Gabriel da haris sun so su taimaka masu Wurin buɗe ƙofar sai dai sun hanasu yin hakan saboda babu ƙoshin lafiya a jikin su.
Kukan Jamimah Ya karaɗe Cikin ɗakin su, Hatta Javed da Naufal sai da su ka farka daga bacci saboda sautin kukanta daya cika kunnuwan su, Taƙi samun wuri ta zauna, Ga uban bargon data zumbula a jikinta, Angel ta rufe mata uniform a cikin toilet shiyasa take ta yin zarya da bargo, Kanta har ya fara sara mata, Gabriel ne ya miƙa mata hannu tare da ambaton sunanta, Kamar jira ta ke yi da gudu ta nufi gadon shi ya ɗauketa saman jikin shi yana lallashinta, cikin shesshesƙar kuka take ce mashi "Dan Allah kaje ka ɗauko mini Genie ɗita, tun ɗazu tana a cikin toilet, ƙofa ta rufe da ita sunƙi su taimaka mata, Uniform ɗina ma suna a ciki itace ta yi mini wanka tace zata Wanke mani su, in sun bushe sai in saka su a jiki na...." duk ta cika shi da surutun ta, shi kanshi hankalin shi ba a kwance ya ke ba, Kowa da abunda yake saƙawa a ranshi dangane da rashin Angel gani su ke kamar fa an ɗauke ta shiyasa taƙi buɗe ƙofar, saboda babu alamun mutun acikin toilet ɗin, Ko motsi wannan baka Ji.
Ina Angel ta shiga meya faru da ita?
abunda ya faru Lokacin da Angel ta zuƙunna a gaban tukunyar fulawar nan, Hankalinta ba'a kwance ya ke ba, tun da ta fahimci Furen Danish, Azalzalar da zuciyarta ke yi mata akan taje ta nemo shi taga a wani hali ya ke ciki shi yaja hankalinta, miƙewa tayi a fujajen ta nufi glass window ɗin nan ta sanya Hannu ta sauke glass ɗin ta dire shi ƙasa Jikin bango, duk da irin tsoron da take ji hakan baisa ta fasa ƙudirinta ba, Bayan ta janyo bokiti ta haye sama sai da ta fara Ambaton Bismillahi da kyakkyawar niyya tare da wasu addu'o'in neman tsari masu ƙarfi Kafin ta daddage ta haura tagar ta duro ta bayanta, tsananin tsoro ne ya kamata da firgici Amma a haka ta daure ta cije saboda idanuwan ta a makance suke bata ji bata gani burinta Kawai ta gano inda Danish ɗinta Ya ke, Cike da ƙwarin gwiwa ta miƙi doguwar hanyar nan wadda zata sada ta da ground floor ɗin Gidan kurkukun, Tana tafiya tana ambaton sunan Allah, Duk addu'ar da tazo mata a cikin bakin ta karanta ta take yi, hada ɗan gudu gudun ta wurin yin tafiyar, lokacin da ta kawo ƙarshen hanyar ta faɗo ta cikin babban Filin dake a kewaye da waɗannan Dogayen benayen, Ras taji gabanta ya faɗi tunawa da abunda ya faru da ita a rana ta farko da ta fara zuwa wurin, ba zata ta6a manta irin baƙar wahalar da tasha ba, A tsananin tsoroce take ƙare ma benayen kallo don ta ga ko zasu motsa kamar yarda su ka yi mata aranar farko, ganin sunƙi Motsawa yasa ta soma tafiya Cikin sanɗa tana tunkarar su, shiru baka jin hayaniyar komai, ita kaɗai kwallin ƙwal kamar ba mutane A gidan Kurkukun.
Har ta kai bakin benan ta soma Jin sautin Wata shaƙaƙƙiyar murya tana ambaton sunanta, A gigice ta juya tana kallon bayanta don taga wanene Sai dai bata ga komai ba, Sautin dariya mai kama da haniniyar Doki ta dinga Ji a cikin kunnuwan ta, Tuni zufa ta wanke fuskarta sharkaf, Can kuma ta dinga jin kukan jarirai Enyaaa enyeeh, Da sauri ta toshe kunnuwan ta da tafin hannuwan ta, bugun zuciyar ta na ci gaba da hauhawa, Jikin ta ya hau rawa, Saboda taurin kai irin nata a haka ta soma hawa benen la66anta na kerma wurin ambaton sunan Allah, ba zato ba tsammani taji Matattakalar Benan ta soma Motsawa, hakan ya sa ta daddage ta watsa da gudu tana haura matattakalar Yayin da benan ke mayar da ita baya har tuntu6e take yi ta kife Ƙasa, Staircases ɗin suka dinga janyeta suna mayar da ita baya kamar zasu saukar da ita daga saman gadon, Cikin zafin nama ta ɗago da kanta tare