Showing 231001 words to 234000 words out of 287659 words
Chapter 78 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
mata ba, haris ma yai magana amma shiru taƙi tasowa, naufal yace su ƙyale ta, inyaso sun ajiye mata nata acikin kwando,
Har sun yi nisa da fara cin abincin, kowa ya natsu yana ci, Majnun sai cusawa ya ke yi abankinshi Parveen nata jifar shi da harara ganin yadda yake yin cin mugunta.
Babu wanda ya lura da ita, Saukowa tai daga saman gadonta fuskarnan sharkaf da hawaye ta yi jawur da ita, tafiya take yi kamar zata kife ƙasa saboda rashin kuzarinta, bata nufi ko'ina ba sai wurin Giants dake a tsaye kamar dakarun Yaƙi.
Dab dasu ta tsaya kamar zata faɗa musu, fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin, zuciyarta a bushe take, muryarta a sanyaye ta soma yi musu magana
"Bawani abu ya kawo ni wurinku ba, so nake ku faɗamin, yaushe zaku dawo mana da ƴan uwanmu? Batool shiru har yau, Danish kuma bansan awani hali yake ciki ba, ni dai don Allah na roƙe ku, ku taimaka ku faɗamin awani hali suke ciki, shin suna raye ko sun mutu ne, idan naji sai in haƙuri in fidda rai......" tun da Angel ta soma yi musu magana Hawaye nabin fuskarta, gaba ɗaya muryarta ta janyo hankalin su Mubeen akanta, tuni sun dakata da cin abincin suna kallonta, an rasa me buɗe baki ya dakatar da ita.
Girgiza kai ta yi tare da lashe hawayen daya gangaro saman la66anta da harshenta, kafin taci gaba da cewa"wai ku ba zaku ta6a aikata abun kirkiki ba arayuwarku? Haka zaku ƙare wurin aikata zalunci......." muryar Haris ce ta katse mata maganarta
"Angel, pls ki matsa daga wurinsu! Kodan saboda mu, idan wani abu ya same ki mu zata shafa, mun rasa mutun uku acikin mu yanzu idan kema wani abu ya faru da ke ya kike tunanin rayuwarmu zata kasance'? Fashewa tayi da matsanancin kuka, azeeza tuni ta kama yin kukan itama.
Cikin shessheƙar kuka Angel tace mashi"don bakasan yadda nake ji acikin zuciyata bane, ni ƙwara ma su kashe shi in huta, da irin wannan rayuwar mara amfani....." daƙyar ta ƙarasa maganar saboda wani irin jiri da ta soma gani acikin idanuwanta, ƙirjinta yai mata nauyi tamkar zai dare biyu, hannu ɗaya tasa ta dafe kanta, ganin yadda jikinta ke rawa yasa Gabriel saurin miƙewa shi da yake a zaune ƙarshen carpet din dab da inda suke hannu biyu yasa wurin tarbeta, Ya ɗauke ta Ya nufi Gadonta, a sama ya kwantar da ita, hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, abincin ma ya fita aransu, duk suka miƙe da sauri suka nufi Gadonta don ganin meke faruwa da ita, Mutun biyu suka rage kan abincin, majnun da Jamima, kallon juna su ka yi kowannansu ya cunkusa abinci abakinshi, Suna tauna suna magana
"Ki ɗauko kwandon batul mu ɗibar masu abincin kada waɗannan dodonnin su tafi dashi," Majnun ne yai mata magana, harara ta wurga mashi"Kai bazaka je ka ɗauko ba, saini," ƙarasa cinye abincin bakinsa yai tare da yunƙurawa ya miƙe ya nufi gadon batul hada ɗan gudunsa, Ya zuƙunna a gaban ƙarƙashin gadon ya zaro kwandon da sauri ya dawo ya zuƙunna kamar mutumin kirki, Ya dinga kwasar abincin Yana zubawa ciki komai Ya haɗe musu kusan Duka ya kwasar musu har saida kwandon yai soro, ya ɗago ya kalli Jamima dake ta tura plaintain chips abakinta.
"Tun da ni na ɗauko kwandon, Ke zaki maida yanzu" ta6e baki tayi"ae bani da ƙarfin iya ɗaukarshi, faɗuwa zanyi ƙasa, kai ka ɗauka mana" Girgiza kai majnun yai kamar babban mutun Yasa hannu ya ɗauki kwandon, Ya nufi ƙarƙashin gadon Ya tura shi ciki, yana ƙoƙarin miƙewa Yaji muryarta abayanshi"Gashi na ɗauko" kallonta yai, Robobin ruwa ne ta rungumo guda uku a ƙirjinta, sai yatsina fuska take yi, Hannu yasa ya kar6a Ya tura a ƙarƙashin gadon, yace mata ta kwaso sauran, Ta koma ta daukosu, Ta miƙa mashi ya kar6a ya ajiye musu, babu wanda Ya tuna da abinci ba su san ma sun ajiye musu ba, Hankalinsu gaba ɗaya yana akan Angel sun kewaye gadonta damuwa ce danƙare akan fuskokinsu, sai kiran sunanta suke yi tare da jijjiga jikinta don ta farka amma taƙi motsawa, hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankalin yai ba,
"Angel! Pls ki tashi! Dan Allah ki farka!' azeeza ce keta magana tana matsar kwalla, Deeja tace"Allah yasa ba waɗancan mugayen bane su ka yi mata wani abu ba," haris yace"nima abunda na ke hasashe kenan"
muryar Gabriel ce ta janyo hankalinsu akan shi" Ba abunda ya same ta, Yunwa ce take ji, ku miƙo min ruwa" yatsina fuska Naufal yai"kawai saboda tana jin yunwa saita yanke jiki ta faɗi? A ina ka sami wannan ilmin" Banza Gabriel yae dashi bai tanka mashi ba, Haris yace"Shisshigi ne kawai," Dogon tsoki Gabriel yaja tare da kallon Azeeza da ke ta yin kuka yace ta ɗabo mashi ruwa, Kafin tayi yunƙurin zuwa ɗebowa Sai ga majnun bakin gadon hannun shi ruƙe da bottle water yaji suna nema shine ya kawo musu, karo nafarko kenan da majnun ya ta6a yi musu abun kirki.
Ba tare da 6ata lokaci ba, Gabriel ya kar6i robar ruwan, ya samu wuri daga gefen gadonta ya zauna tare da sanya hannun shi ɗaya ya ɗago da kanta ya ɗaura shi gefen chest dinshi, azeeza ce ta buɗe mashi murfin robar hannun shi ta ruƙe a hannunta, Ya kanga ma Angel robar abakin ta, Duk suka baza ido suna jiran ganin in zata motsawa, aiko kamar jira take taji an daura mata robar ruwan abakinta, ta dinga kur6arshi kamar zata shaƙe maƙoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat!
Saboda tsabar kunyar da ta kama su haris da Naufal Sai gashi sun sadda kansu Ƙasa, Kusan rabin ruwan ta shanye, wani irin yunƙurin amai ne yazo mata, saboda rashin ƙwarin jikinta bazata iya miƙewa taje toilet ba, asaman rigar Gabriel ta shiga kwara aman, tsananin tausayinta duk ya kamasu sai sannu suke yi mata, kamar zasu ɗauke mata ciwon haka su ke ji, duk da irin aman da ta ke yi ajikinshi bai ji komai ba, ko irin ƙyanƙyamin nan, saima ƙara ruƙe ta da ya ke yi da hannayenbshi don tuni ya miƙa ma Azeeza robar ruwan, bakomai ke fita acikin bakin nata ba face kayan marmarin data sha tun jiya da zallar ruwa, Sai nishi take yi tana faman lumshe idanuwanta.
"Sannu sister, Allah ya baki lafiya" acewar javed, Suma saura suka ƙara yi mata ya jiki, sam ta kasa motsa la66anta donta amsa musu, daƙyar tafara magana kamar ma sambatu ta ke yi musu tana ambaton sunan Danish da batul, miryar deeja ce tasa ta ƙoƙarin buɗe idanuwanta
"Angel ki daure kidaina sanya damuwa aranki, Idan kina yin hakan ba ƙaramin raunata mata zuciyoyin mu kike yi ba, ke da kika saba ƙarfafa mana gwiwa, amma yau kece kike neman zaucewa saboda rashin su, kowa ya jure amma kin gaza, Ya ki ke so muyi"? Idanuwanta acike tab da ƙwalla tayi mata maganar.
Cizon la66a ta ta yi ba tare data iya furta mata komai ba, ruwan hannun Azeeza ya kuma kar6a Ya kuskure mata bakinta dashi, tare da wanke mata fuskarta, Kafin ya miƙa ma Azeeza robar tasa hannu ta kar6a,
"Akwai sauran abinci"? Yai tambayar yana kallon su, har suna hada baki wurin rabka salati suna faɗin"Mun manta Bamu ɗebi abincin ba, gashi giants sun tafi dashi" Kamar zasu fashe da kuka.
Chinonsu dake sauraronsu shida jamima, jin suna neman abinci yasa Suka nufi ƙarƙashin gadon Batul atare suka ruƙo hannun kwandon, suka nufo wurinsu, tunkan su ƙaraso Ƴan uwan nasu suka ga uban tulun abincin da suka ajiye musu, Wani irin farin Cikine ya lullu6e su, Ba ƙaramin daɗi su ka ji ba, Bakin parveen washe da annuri tace"Kai ba dai kune ku ka ɗebi abincin nan ba"? Har suna haɗa baki wurin furta"Mune nan muka ajiye shi" with proud su kai maganar, suna ƙarasowa parveen ta kar6i kwandon daga hannunsu ta ruƙe shi, tace da Azeeza ta ɗauko Mayafi da zasu goge aman da Angel tay, ta masa mata da toh, ta juya ta nufi akwatin kayansu kafin ta dawo Gabriel yace ta miƙo ma shi abunda zai fara bata ta ci.
Zura hannu tayi cikin kwandon ta ɗauko meat balls ta miƙa mashi, ya kar6a ya soma bata abaki tana ci, ba ƙaramin daɗin shi su ka ji ba ganin yadda ta zaƙe tana ci.
Dawowa Azeeza tai hannunta ruƙe da ɗan mayafi ta shiga goge mashi aman da Angel ta yi a jikin vest dinsa, da saman laps ɗinsa, bayan ta kammala tace mashi ya curo mata taje ta wanke mashi, murmushi yaɗan saki tare da kallon ta yace"bakya gajiya da yi min wanki Azeeza, kibar shi zan wanke da da kaina" maƙe mashi kafaɗa tai alamar bazata bari ba, yace toh bari na ƙarasa bata abincin, sai na baki rigar,
sai da ya kammala bata ya kwantar da Angel kamar me bacci ta lumshe idanuwanta, hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yai ba, Kowa ya nufi gadon shi ya zauna, parveen ta ɗauki kwandon taje ta ajiye musu a ƙarƙashin gado, miƙewa Gabriel yai daga gefen gadonta, Ya tu6e rigar jikin shi ya miƙa ma azeeza tasa hannu ta kar6a, ta nufi toilet shima yabi bayanta don ya watsa ruwa ma jikinsa.
Bacci mai daɗi ya ɗauki Angel, Su majnun dake shirin yin wasa atsakar ɗakinsu, parveen ta lalla6asu akan su yi shiru kada su tada Angel tunda sun ga bata da lafiya, suka amsa mata da toh, Kafin marece yai kowannansu na zaune, wasu sun ɗan kishingiɗa da niyar bacci ya ɗauke su, rabi da kwatansu idanuwansu arufe yake, duk don saboda Angel sunyi tsif babu mai magana, gudun kada su katse mata baccin ta.
💔PRISONERS💔
Kunnuwansu ne suka soma jiyo musu motsin buɗe ɗakin su, Ras gabansu Ya faɗi ba tare da sanin dalilin hakan ba, kusan atare kowannansu Ya buɗe idanuwanshi Hankalinsu gaba ɗaya ya koma Kan staircases ɗin, Jira suke suga waye zai shigo ko wani ne za'a dawo musu dashi tunda an riga an kawo musu abinci, Yadda suke zazzare idanuwansu akan ƙafafuwan masu shigowa tamkar ƙwayar idanuwansu zasu faɗo ƙasa,
Bakowa bace face tsohuwa Zafreen Hannunta ruƙe da sanda cikin shigarta ta jajayen kaya, Rabin fuskarta rufe yake, Iya idanuwanta ne awaje, Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, Abayanta Wasu Gabza gabzan Giants ne Su biyu garada masu ɗauke da Star 2 agaban baƙar rigar jikinsu, Takun tafiyarsu yadda kasan na wani namun dawa.
Wahalallan yawu kowannansu Ya haɗiya, hakanan suka dinga jin bugun zuciyarsu na hauhawa, Chinonso dake ta tsalle tsalle ganinsu yasa shi yin saurin nufar gadon parveen ya haye ya zauna gefenta hada ɗaura kanshi saman kafaɗar ta, Azeeza kuwa cikin sanɗa ta duro daga saman gadon ta faɗa ƙarƙashinsa ta la6e jikinta nata kerma, ganin ta 6oye yasa jamima lalla6awa itama ta sauko daga saman gadonta, ta shige ƙarƙashi. sauran kuwa ba wanda ya motsa kowa yasha jinin jikinsa.
Lokacin da mai girma tsohuwa Zafreen ta ƙaraso Tsakiyar ɗakin nasu, Sai kowannansu ya sadda kanshi ƙasa ba tare da sun furta komai ba, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, duk sun kame kansu.
"Fatan na same ku lafiya" tai tambayar tana kallon fuskokinsu, wasu daga cikinsu ne suka samu damar amsa mata da cewa"Muna lafiya" tace"tsawon lokaci banzo na duba jikokina ba, saboda uzurirrika da suka yi min yawa, sai yau na samu damar leƙo wa, hope you're happy to see me"
kamar waɗanda aka ma dole haka suka furta mata"eh" Jinjina kai ta ɗanyi yayin da take cigaba da binsu da kallo kafin ta tsayar da idanuwanta akan fuskar haris Ya ɗaure fuskarshi sosai, Idonshi na kallon ƙas
"Zuwan nawa ba lallai bane yayi maku daɗi ba, domin kuwa nazo ne na raba ku da zaratan samarin dake a cikin ku" a firgice suka ɗago suna kallonta la66ansu na kerma ba tare da wani ya iya furta wani abu.
"Haris, Mubeen, Naufal, Javed, and Gabriel, A kan ku nake magana, Ba'a ta6a zuwa an ɗauke ku ba, wannan karan kurkukun ƙaddara ya buƙace ku, Don haka ba tare da 6ata lokaci ba, kowannan ku ya sauko daga saman gadon shi, A jere zaku tafi," A matuƙar ruɗe su parveen ke kallonsu, wani iko na Allah babu wanda ya musa acikinsu, Kamar yadda ta basu umarni haka suka sauko a jere suka nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, Sai waiwayon ƴan uwansu suke yi, idanuwan kowannansu cike tab da kwalla kai daga gani bada son ransu suke yin tafiyar ba, Sarrafa su aka yi, Hankalin Deeja idan ya yi duba toh ya tashi, Ba ita kaɗai ba hatta sauran matan da ke acikin su, Gashi sun gaza ɗaga koda yatsan su, Sai hawayen da ke gangarowa ta cikin idanuwansu.
"Albino, Follow their back" tai maganar ba tare da ta juya ta kalli inda chinonso yake zaune gefen parveen, Jikinshi nata kerma ya sauko daga saman gadon idon parveen akanshi, Yana tafiya yana waiwayonta kamar zaiyi tuntu6e, ahaka harya haura saman starcases ɗin Yabi bayansu Haris, Tashin hankalin da ba'a sama shi date! Kaf an kwashe mazansu, Cikin su 20 yanzu saura mutun goma sha ɗaya, Shin Ina za'a kai su haris?
Tsayar da idanuwanta ta yi akan gadon Angel dake ta sharar bacci, babu alamun zata farka,
"Ba'a san ƙaddarar kurkuku da rauni ba, tana bacci gwanin ban sha'awa, nan badajimawa ba, zamu buƙace ki" Tayi maganar tare da matsawa dab da gadon Angel Ta ɗaura sandarta asaman ƙafarta, Nan take angel tayi wani irin juyi ta fuskanci ceilling ba tare data farka daga baccin ba, A saman ƙirjinta zafreen ta ɗaura sandar hannunta Saitin zuciyarta, Wani irin numfashi Angel ta shiga fitarwa ahargitse, Su Deeja dake kallon abunda ke faruwa kamar su ɗaura hannu aka su fasa ihu, Sai dai kash babu mai iya motsawa a cikinsu, Sai da Angel tagama banƙarewa kamar zata koma zombie, tukunna tsohuwa zafreen ta sauke sandar daga saman ƙirjinta.
💋PRISONERS💋
A hankali ta ɗauke idanuwanta daga kan fuskarta Angel, ta mayar dasu kan fuskokinsu Parveen da suka jiƙe sharkaf da hawaye, La66ansu sai kerma suke yi kamar waɗanda sanyi ya kama.
"Tun da ku ka taso a gidan kurkukun nan ba ku ta6a gabza faɗa a tsakanin ku ba, kullum kuna a cikin farin ciki, ba'a ta6a samun prisoners masu ƴanci irin ku ba, Prison ta gatanta ku, Sai dai kash a dokar gidan kurkukun ƙaddara prisoners basu da ƴan cin kansu, bamu amince ma wani daga cikin ku ya ji daɗin rayuwar shi ba, yakamata ace a yanzu kun yi bankwana da farin ciki, fatan an fahimce ni" tai maganar tana binsu da shu'umin kallo.
kamar ta yi magana da duwatsu, babu wanda ya tanka mata, Wata ƴar iskar dariya zafreen ta saki tare da cewa"Dama na sani ba za ku Iya magana ba, saboda ban baku iznin yin ta ba," Ta ƙarasa maganar tare da juyawa Giants ɗin da ke abayanta suka take mata baya, Tana tafiya Cikin ƙasaita, sai da ta kai bakin matakalar benan ta ɗan dakata da yin tafiyar suma Giants ɗin suka tsaya da yin tafiyar, magana ta soma yi masu ba tare da ta juyo ta kalle su ba.
"Idan ƴar uwar ku ta farka, ku isar min da saƙon gaisuwata agare ta, nabarku lafiya" tana ƙarasa yin maganar tasa kai ta fuce daga cikin ɗakin tare da masu take mata baya.
Fitar su keda Wuya! Sautin rufe ƙopar ya fargar dasu, a firgice su ke kallon kallo a tsakanin su, fuskokin su ɗauke da matsananciyar damuwa, kukan ma yaƙi zuwa masu sai hawayen da ke ta wanke fuskokin su, tsananin tausayin kansu ne ya kama su, wannan wata irin rayuwace suna ji suna gani anyi masu yankar ƙauna An rabasu da ƴan uwansu, babu mai iya magana acikinsu, saboda tsabar takaici da baƙin cikin da su ke ji,
Azeeza da ke la6e ƙarƙashin gado, tasha kuka kamar ranta zai fita, ta ƙanƙame jikinta da ke ta kerma tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, itama jamima tana nan ƙarƙashin gadonta bata motsa ba, ta dai ji duk maganganun da tsohuwa zafreen tayi acikin ɗakin su, sai faman zare idanuwanta ta ke yi.
Yunƙurin buɗe baki deeja ta yi, sai dai bata kai ga furta abunda take son faɗi ba, idanuwan su, su ka sauka akan Angel da ta soma motsi tana banƙarewa, yatsun hannayenta nata kerma, wani irin gurnani take fitarwa da huci, Nan take maganar tsohuwa zafreen ta faɗo musu aransu, wani irin mugun tsoro ne Ya kamasu, la66an Deeja na kerma tace dasu"ku tashi mu 6oye in ba haka ba, Angel zata iya cutar damu......"
kafin wani daga cikin su ya kuma furta wata kalma, Angel ta duro daga saman gadonta Yadda kasan gardin ƙato, facial muscles ɗinta har kerma su ke yi, launin ƙwayar idanuwanta sun 6ace 6at sai farin, Har wani gyara wuyanta ta ke yi, tana banƙare ƙirjinta da bayanta, gadan gadan ta nufo gadajen su, aiko jiki na 6ari Suka soma ƙoƙarin saukowa don su nemi wurin 6uya, Kamar walƙiya deeja taga Angel agabanta, Damƙar wuyanta tai tare da wujijjiga ta, kafin ta ɗaga ta da hannu ɗaya ta buga ta ga ƙasa, nan take deeja ta suma, ganin hakan yasa hankalin sauran yai matuƙar tashi, da gudu Parveen ta nufi sashen toilet ita da Hibba da Rubina da niyar su 6oye, kafin su kai ga ƙarasawa jikin ƙopar ta riga su isa, sai dai suka ganta agabansu, Hannu biyu tasa ta shaƙi wuyan Parveen dana hibba, Ta ɗaga su sama, suna ta kuka kamar ransu zai fita, Rubina na ƙoƙarin bi ta gefe ta shige, aiko ta sanya ƙafarta ɗaya ta taɗiyeta, kanta ya bugu da ƙasa jini harta hanci, Innallahi wa'inna ilaihirraji'un.
Basu ta6a ganin tashin hankali makamancin na yau ba, Angel bata ji bata gani, bugun mutuwa take nakaɗa musu, ko da ta ɗaga su pareen da hannayenta, A saman floor ta maka su, babu wanda hancinsa baiyi bleeding ba a cikinsu, saboda wani irin ƙarfine irin na dawakai, idan ta daki mutun dukkan sassan jikin shi ke amsawa.
Waro ido waje Hanna da sauran su ka yi, kowannan su Ya shiga ja da baya suna a jere tsakiyar ɗakin Jikin