Showing 240001 words to 243000 words out of 287659 words
Chapter 81 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
da Angel ɗaki ɗaya don ta samu damar ƙarasa 6alle mata sauran haƙoranta da suka rage abakinta.
Maganganun Jamimah sun yi matuƙar basu dariya, ita abunda yafi 6ata mata rai, Haƙorinta ɗaya da Angel ta cire mata, Angel har ce mata ta yi ta kwantar da hankalinta, ita yarinya ce ba ta gama fanfara ba, wani haƙorin zai fito mata, amma taƙi yarda da zancenta, Ko kusa da ita taƙi bari Angel ta je, Tsabar yarda take zabgawa Angel harara kamar idonta zai faɗo ƙasa.
Har tambayar Angel su ka yi ya akai Jiya suka dawo saman gadajen su? Sannan ya a kai basu ga jinin su da ya yi bleeding ba, a jikin bango da ƙasan ɗakin, sannan kuma ya akai Basu tashi da raɗaɗin ciwon su ba, Deeja ce ta basu amsa da cewa"Allah ne ya kawo mana ɗauki, narasa ya zanyi a lokacin saina roƙe shi, akan ya bani mafita, kuma cikin ikon Allah Sai gashi kowannan mu ya tashi babu ciwo a jikin mu,"
Mamaki ne ya kama su jin abunda tace, jamimah uwar masu hankali hada cewa Meyasa ita ba a dawo mata da haƙorinta ɗaya ba? Angel tace idan kika kwantar da hankalin ki, kema zanyi maki addu'a akan Allah yasa haƙorin ki daya fita ya dawo, Wani kallon rainin wayau ta yi ma Angel hada gatsina mata hanci, ƙiri ƙiri itafa ta tsangwami Angel, ganin aljana ta ke yi mata.
Yunwa ce ta fara addabar su, dama dole suji yunwa wannan jijjigar da Angel ta yi masu a jiya, Kamar an kwashe abincin da suka ci, dama jiyan basu ƙarasa cinye abincin su ba, Sakamakon sumewar da Angel ta yi, hakan yasa suka ƙi ƙarasa cin abincin.
Tunawa da abincin da su Majnoon suka ajiye musu a jiya ne yasa Parveen ta sauko daga saman gadonta, ta nufi ƙarƙashin gadon Batul, Ta janyo kwandon, Hibba tace"Anya bai lalace ba? Kada fa mu ci abunda cikin mu zai 6aci" Parveen ta bata amsa da cewa"Ai wlh ko ya lalace sai na ci shi, idan ma cikin ya 6aci iya kaci in ta yin zaryar shiga toilet ne, dama na saba"
A saman Dining carpet ɗinsu ta ajiye musu kwandon tace musu Mai jin yunwa ya sauko suci, Jiki duk ba ƙwari kowan nan su ya sauko daga saman gadon shi duk da babu raɗaɗin ciwo a jikin su, sun rasa kuzarin jikin su, idan ka kalli fuskokinsu gaba ɗaya babu wanda bai faɗa ba.
Sai da suka fara zuwa toilet su ka wanko bakunan su da fuskokin su tukunna su ka dawo ɗakin, kowa ya samu wuri saman dining carpet dinsu, su ka zazzauna, Jamima sarkin rigima, ba yadda ba su yi da ita ba akan tazo ta zauna su ci abinci tace musu taya zata iya cin abinci, bayan babu haƙori ɗaya a bakin ta.
Ganin zata 6ata masu lokaci yasa Deeja ɗaukarta, ta nufi toilet da ita, ta wanke mata bakinta da fuskarta, ta fito da ita rungume a jikinta.
Sai da Angel ta fara dudduba abincin don taga idan akwai wanda ya lalace, lafiyar shi qalau, ya dai yi sanyi, kayan marmari ne sai flat bread wraps, da snack Hada ragowar meat balls, "
Bismilla su ka yi, suna cin abincin hawaye na bin fuskokin su, tunawa da ƴan uwan su, carpet ɗin yayi musu faɗi saboda waɗanda babu acikin su, rayuwa kenan, da ta ko'ina gefe da gefen carpet ɗin zaka gan su zazzaune sun kewaye shi.
basu ta6a tunanin za'a kwashe su haris ba, sun yi matuƙar yin kewarsu, Sun damu dasu sosai, Parveen ba kowa take tunawa ba face MAJNOON, duk in ta tuna yadda ya zo saman gadonta ya haye tare da ɗaura kanshi saman kafaɗarta, Sai taji hawaye sun cika idonta, haka da zai tafi ya dinga waiwayonta, duk da irin bugun da take yi mashi kamar ta samu jaki, yaron ba ƙaramin ƙaunarta ya ke yi ba, ta yi danasanin muguntar da ta ke yi mashi, da tasan haka zata faru da ko dungurin shi ba zata yi ba, Allah sarki majnoon.
Idan muka koma 6angaren Deeja tunaninta akan HARIS ne, zuciyarta kamar zata fashe saboda kewar shi da ta ke yi, Allah sarki haris masoyi, a duk lokacin da ta shiga wani hali yafi kowa damuwa da ita, bashi da magana saita Deeja, Yana matuƙar kyautata mata tare da sauran ƴan uwan shi, haƙiƙa sun yi babban rashi na ɗaya daga cikin jagoransu, wanda suka fi damuwa dasu, wato Haris, a zuciyar Angel waɗanda suka fi tsaya mata arai duba da irin halin da aka tafi dasu, mutun na farko BATUL ce! ba zata ta6a mantawa da irin yanayin da aka tafi da ita ba, Allah sarki batul, itama tana ɗaya daga cikin jagoran su, masu ƙarfafa musu gwiwa masu nuna damuwa akan ƴan uwan su, Bayan ita sai mutun na gaba Maji daɗin gado wato DANISH, dole ne kowa yaji jiki na rashin shi, saboda shi a raunace aka tafi dashi, babu ido ɗaya fuskarshi a wanke da jinin shi, Allah kaɗai yasan awani hali ya ke ciki a yanzu.
Anyi masu babban gi6i, ɗaya bayan ɗaya haka suka zauna suna tariyo irin muhimmancin da suke da shi awurin su, bayan Danish mutun na gaba JAVED ne! yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙaunaci Angel farkon kasancewarta a gidan kurkukun ƙaddara, kyawawan halayansa abunso ne, kowa nashi ne, yana matuƙar ƙaunar ƴan uwan shi, bayan javed mutun na gaba bakowa bane face NAUFAL, Tazarar halayan shi dana haris kaɗan ne, Yana da zafin zuciya idan aka ta6a ƴan uwan shi yana ɗaya daga cikin masu tada jijiyoyin wuya, shima ba daga baya ba, in dai akan ƴan uwan shine a shirye ya ke daya zare takobi don ayi yaƙi.
Bayan Naufal Sai MUBEEN yana ɗaya daga cikin masu faranta musu rai, ya iya jan ƴan uwan shi a jiki, mutun na ƙarshe a cikin jerin waɗannan bakowa bane face GABRIEL! duk da shi daga baya ya tsinci kanshi agidan kurkukun, Amma tabbas da ace yai rayuwa dasu ba ƙaramar gudummuwa zai bada ba! Saboda yana da zuciya, ga tausayi kowace mace yana ganinta kamar ƴar uwarshi ne, sannan yana da burin su ku6uta daga cikin kurkukun ƙaddara!
Tabbas sun yi babban rashi na zaratan samarin dake acikin su, hatta ɗakin su ya yi musu girma saboda rashin su.
duk yadda suka so su hana kansu damuwa saida abun yaci tura, Sun sha kuka tamkar ba gobe, Deeja da Angel sai aikin lallashin su su ke yi, a ƙarshe suma suka koma suna taya su kukan, sautin kukansu ya karaɗe cikin ɗakin, Dama ba ƙoshin lafiyace da su ba, Sai da su ka yi mai isarsu tukunna suka haƙura kowa ya lallashi zuciyarshi, A saman floor ɗin ɗakin kowan nan su ya kwanta kamar matattu tsabar baƙin ci ne kawai da raɗaɗin da su ke ji a cikin zuciyarsu.
Yinin ranar babu wanda ya yi wanka a cikin su, Jikinsu sai tsami yake yi, koda giants su ka zo kawo musu abinci babu wanda ya motsa a cikin su, dama ba yunwa su ke ji ba sun ɗan samu sun ci ragowar na jiya, babu yunwa atare dasu, Jamimah ce tai ƙoƙarin ɗauko kwandonsu tunawa da yadda su ka yi jiya ita da majnoon, itama fa hada ƴar ƙwallarta, saboda an tafin mata da abokin wasan ta, duka abincin ta dinga kwasa da hannu biyu tana turawa cikin kwandon, sai da ta kammala ta kasa ɗaukar kwandon saboda yai mata nauyi, hakan yasa ta barshi asaman dining carpet ɗin, Giants na ganin ta kammala tattara abincin, su ka kwashe trays din tare da barin ɗakin, Zama jamima ta yi ta dinga ɗaukar abincin tana ci tana kallon su Hanna dake kwance ƙasa hawaye na bin fuskokin su, Sai da ta cika cikinta ta yi kulu wash rabu hani'an tukunna ta miƙe tare da komawa cikin su itama ta kwanta kamar yadda su ka yi, ta ci gaba da matsar ƙwalla tana ambaton sunan Majnoon.
A cikin waɗannan kwanakin babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, kamar za su yi hauka, idan Giants suka zo kawo masu abinci haka zasu dinga zazzaga musu masifa akan su dawo musu da ƴan uwan su, sun gaji da jira, a ƙarshe da su ka fahimci cewa Giants ba sauraron su su ke yi ba, don dole su ka haƙura.
yanzu ta kai ga da zarar sun ji motsin buɗe ƙopa da gudu suke zuwa bakin benan don suga idan ƴan uwan su ne aka adawo musu da su, ashe kunnuwan su ne, su ke jiyo musu hakan saboda tsabar yarda suka sanya damuwa aran su.
Bayin Allah duk sun rame sun fige sun fita hayyacin su, kamar ana ɗibar naman jikin su, ƙasusuwan wuyan su duk shatunsu ya fito saman fatarsu, idanuwansu sun faɗa, ganin zasu zauce saboda rashin ƴan uwansu ne yasa Angel ta tattarasu tana yi musu nasiha akan su yi haƙuri subarma Allah komai, shi zai kawo musu mafita, ta dage sosai wurin cigaba da koya musu addu'o'in da zasu dinga yi don su samu maslaha acikin zukatan su, har tsakar dare ta ke tada su daga bacci, su zauna su na addu'a suna kai kukan su wurin Allah, kullum suna zama cikin jimami, kafin Allah ya kawo musu sauƙin damuwar da ke damun su, Sun haƙura suna zama harma su ɗan ta6a fira a tsakanin su, su yi murmushi su yi dariya.
*💔PRISONERS💔*
*After one week (bayan sati ɗaya)*
Tun bayan da aka tafi dasu Haris, babu wanda yai wanka a cikin su, sun zama ƙazaman ƙarfi da yaji, Saboda rashin sukuni da walwahala, hatta gashin kansu Ya fita hayyacin shi saboda rashin gyaran da bai samu akai akai, sai yau da Angel ta lalla6a su tace su je su yi wanka zata gyara musu kansu, tukunna suka amince za su yi, Ita kanta Angel ɗin ba wankan ta ke yi ba, yau dai ne ta ke son su ɗan gyara jikin nasu.
Gaba ɗayan su suna a sashen toilet ɗin su, banda Jamimah ita kaɗai ta rage a ɗakin zaune saman gadonta, Hannunta ruƙe da madubi, ta wage baki tana kallon gi6inta, kullum ne saita ɗauki madubi ta duba bakinta don taga idon wani haƙorin ya fito, har yanzu babu jituwa a tsakaninta da Angel.
Su hanna da ke a sashen toilet ɗinsu, kowanansu Ya zuƙunna suna fuskantar juna, kusan su bakwai ne suna jira na cikin toilets ɗin su fito don suma su samu shiga su yi wankan, Waɗanda ke acikin Makewayin Angel ce da Sarah sai Azeeza.
Angel da ke acikin toilet, tun da ta shiga, ba wanka ta ke yi ba, tana a zuƙunne gaban tukunyar fulawan nan tsawon lokaci basu ba furennin ciki ruwa ba, saboda rashin kwanciyar hankali.
Furennin duk sun bushe sun fita hayyacin su, hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, da sauri ta miƙe taje bakin fanfo ta cuko bokiti da ruwa ta dawo ta kwarara shi acikin tukunyar, bayan ta kammala ta juya ta kai bucket ɗin gefen fanfon ta ajiye shi, kamar ance ta waiwayo ta kalli furennin, unexpected idanuwanta suka sauka akan Sabbin tsiron furennin da suka cika tukunyar fulawar, A matuƙar ruɗe ta ke kallonsu, launuka daban daban daga cikin su akwai wani dogon fure wanda tsayin shi ya kere sauran, Lafiyayyan gaske, Ganyayyakinsa sun bubbuɗe launin punch pink ya ciza sosai.
Zazzare idanuwanta waje ta yi, Hannunta dafe da saitin ƙirjinta, don ba ƙaramin faɗuwa gabanta yai ba, walking slowly ta nufi tukunyar fulawar kamar wadda taga wani abun tsoro, duƙawa ta ɗanyi tana ƙare musu kallo, kusan guda takwas ne sabbin furennin, bakwai daga cikin su, ganyayyakin jikinsu sun ɗan bubbushe, akwai wani ɗan ƙarami fari fat irin na jikin aunty Aneelerh, sai dai wannan ganyayyakinsa kamar sun mutu, duk sun tsomare.
Tarasa tunanin me zata yi agame da waɗanann sabbin furennin da su ka yi tsiro, ta gaza fahimtar na wanene su? tunawa tai da maganar Danish, a inda yake faɗa mata cewa kowani fure yana ɗauke da ran mutun, idan har dagaske ne, taya za'ae tasan ran wanene akansu? Ga biyu ma daga cikin furennin sunfi jigata.
Wani irin faɗuwar gaba taji, ba tare da sanin dalilin hakan ba, sai ta dinga ji aranta kamar Danish yana atare da ita cikin toilet ɗin, da sauri ta juya tana ƙarewa makewayin kallo, babu kowa a wuri.
Muryarta na ɗan rawa ta furta sunanshi "DANISH"! cike da sa ran zai amsa mata, shiru ba'a amsa mata kiran nata ba, kusan sau uku tana ambaton sunanshi,
"Danish, are you here with me? Please answer my call. I really miss you my Man," she said, her voice on the verge of tears.
Sai faman wurwuga idanuwanta take yi acikin toilet ɗin, duk da taga babu kowa amma ita ranta ya bata cewar Yana atare da ita.
"Danish Even if you can't speak, please make some kind of sound to let me know that you're here. I need to know if my suspicions are true, saboda a duk lokacin sa ka zo kusa dani, Inaji a jikina kuma na yarda da hakan,"
kamar mahaukaciya sai sambatu ta ke yi a cikin toilet.
Da ƙarfi ta ƙara furta sunan shi"Danish ka amsa min" karaf akan kunnuwansu Deeja dake zuƙunne cikin sashen, su azeeza har sun fito daga wankan, hibba da parveen sun shiga, ita kaɗaice bata fito ba,
"Kamar muryar Angel nake ji acikin toilet!" yasmin ce tai maganar, Deeja tace"kin riga ni faɗi, nima naji maganarta tana ambaton sunan Danish" hanna tace"Anya lafiyarta kuwa? Yakamata muje mu duba,"
Kusan atare suka miƙe, zuwa bakin ƙopar toilet ɗin, knocking deeja tayi mata tare da ɗaga murya tace"Angel! Lafiya mu ka ji kina kiran sunan Danish"?
Jin muryoyin su Yasa ta dakata da yin sambatun, idanuwanta acike tab da ƙwalla, ta nufi ƙopar, bata buɗe ba, magana tayi masu cikin sanyin murya
"Babu komai, banma san na ambaci sunanshi ba, nayi missing din shi ne"
"Shiyasa kike ta ƙwala mashi kira a cikin toilet, gaskiya Angel ba ƙaramin ƙaunar ɗan uwan nan namu ki ke yi ba, muna nan munata jiran ki ki fito, ashe kina nan kina ta sambatu halan ko wankan ba ki yi ba"?
Fuskarta a yamutse ta basu amsa da cewa"ban kai ga yi ba, na tsaya bama furenni ruwa ne, idan na fito zan nuna maku wani abun mamaki, amma yanzu ku koma ku zauna kunsa inata magana acikin toilet bayan babu kyau,' a ƙagare take da su tafi, jin shiru yasa ta fahimci cewa sun tafi, ajiyar zuciya ta ɗan sauke, ba tare da 6ata lokaci ba, ta yi wankan, suna a zaune sai gata ta fito, adai dai time ɗin da su parveen da hibba suma su ka fito daga wankan.
Kallon su ta yi gaba ɗaya idanuwansu akanta, jira suke suji me zata faɗa musu
"Kunsan me ya faru"? Girgiza mata kai su ka yi alamar a'a tace"dana shiga toilet na ɗebo ruwa na zuba ma tukunyar fulawar nan, naje in ajiye bucket ɗin, Juyowar da zan yi idanuwana su ka yi tozali da sabbin furenni masu kyan gaske, dayawa fa nayi mamakin fitowar......." bata kai ga ƙarasa maganar ba, da gudu su deeja suka shige cikin toilet ɗin, a bakin tukunyar flower ɗin suka tsaitsaya cirko cirko suna kallon furennin, gwanin ban sha'awa, sunyi matuƙar burgesu, sai dai abun da ya ruɗarsu sun kasa gane furennin wanene, sun 6ata lokaci wurin kallonsu, kamar su cinye su, daga bisani ne suka bar wurin, sauran da basu yi wanka ba a cikinsu suka shige toilets.
Lokacin da Angel ta shiga ɗakinsu, Jamima na nan yadda suka barta, zaune tana duba madubi, azeeza tana azaune saman shimfiɗar sarah, tana sharce mata gashi, sai santin shi ta ke yi, saboda ita tsayin gashinta bai kai nasu ba,
"Sumar kan ki sak irin na Unaiza ne ƴar gidan daddy, banbancin kaɗan ne ita nata tsawo ne da shi ba yawa ke kuma naki yana da yawa kamar roba jikin shi"
"Allah sarki har kin tuna min da ita, ko yanzu tana awani hali, oho, " acewar parveen, ta yi maganar ne a yayin da ta ke ƙarasa shiga cikin ɗakin.
Angel tuni ta wuce gefen gadonta, parveen ce ta ɗauko mata comb donta gyara masu gashin kan su, atare da Sarah suka zauna zaman gyara masu sumar kan nasu, ɗaya bayan ɗaya suka yi ma kowan nan su bayan sun fito daga wankan, mutun ɗaya ta rage bata yi wanka ba, har magana azeeza ta yi mata akan tazo ta yi mata wanka tace ita bataso, Su ƙyale ta, haƙorinta ke ciwo, alhalin ƙarya ta ke yi babu wani ciwon haƙori da ta ke yi, wankan ne bata so, Dama angel neman hanyar da zasu shirya da ita take yi, aiko tana zaune saman gadonta, ba zato ba tsammani taji an ɗauketa, ta dinga kuka tana wuntsila ƴan ƙafafuwanta tana faɗin bata so ta sauke ta, hada ƙwala masu deeja kira tana faɗin bazasu zo su cece ta ba, suna ganin genie zata cutar da ita, dariya suka dinga yi mata babu wanda ya motsa.
A cikin toilet ta sauketa, da gudu ta nufi ƙopa zata fuce Angel tai saurin rigata isa ta datse ƙopar da jamlock, kallon kallo su ka shiga yi a tsakaninsu,
Nuna jamimah tai da yatsan hannunta tare da cewa"dama daga ganin ki ba ƙaramar fitinanniya bace, amma duk masifarki baki kai ni ba lokacin da ina ƙarama, kawai daga tsautsayi yasa na 6alle maki haƙori, shine zaki ɗaura min karan tsana, nifa ce Angel ɗin ki,' ta yi maganar tana marairaice mata fuska.
Murguɗa mata baki jamima tayi tare da juya mata ƙeya, Dariya angel ta saki tana kallon bayanta, Kamar kasanya ƙafa ka take ta saboda ƙarantarta, komai nata gwanin burgewa irin na azeeza, tana matuƙar jin tausayin su.
Jin shiru Angel din bata motsa ba yasa ta ɗan waigo ta saci kallonta, suna haɗa ido ta wurga mata harara.
Dafe ƙirji Angel ta yi da hannu ɗaya
"Genie ɗin kika harara, aiko yanzun nan zan ƙarasa 6a66ake sauran haƙoran na bakin ki ki koma wawulo, " jin wannan maganar yasa Jamimah fashewa da wani sabon kukan.
matsawa Angel