Showing 168001 words to 171000 words out of 287659 words
Chapter 57 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
ɗan waresu ta ƙara buɗesu kafin ta zarosu tana ƙarewa tukunyar fulawar kallo, abun mamaki abun al'ajabi, yauƙanannun fulawowin dake acikinta waɗanda sun jima da bushewa duk sun yagalgale sun lafe cikin ƙasar dake acikinta, ɗaya daga Cikinsu tagani ta miƙe ta bubbuɗe ganyayyakin jikinta sun wawware tayi matuƙar ɗaukar hankalinta, musamman launin Jikinta Ja da ya ciza, tsabar mamaki ya hana ta rufe bakinta, Idan ta kalli furan sai kuma ta kalli fuskar Danish,
Har dai tagaza jurewa tace"taya akai kayi hakan? Kamar a mafarki,"
"Ba shi yakamata ki tambayeni ba, wannan furen da kika gani ki ɗauka cewa ran mutun ne mai numfashi a jikin shi " Ya ƙarasa maganar tare dakai hannu ya shafa ganyen shi tare da cewa"Batool ɗinki ce, Our lovely sister, idan kika kalli furan da kyau, zaki ga yana da cikakkiyar lafiya ajikinshi, Launin shi ya ciza, hakan na nufin batul aduk inda take a yanzu tana acikin ƙoshin lafiya, Idan kuma ki gaka ganyen jikin furan Yana fitar da ruwa kamar zufa batare da an yayyafa mashi ruwa ba, that mean batool kuka take yi tana kewan ƴan uwanta, idan kuma ganyen ya kwanta jikin ƙasar dake acikin fulawar, to batool bacci take yi........" tunda ya soma kora bata jawabi, take kallonshi babu wasa a fuskarshi, Yadda kasan irin malamin duban nan, sai da yakai ƙarshen maganarshi tukunna tace"to idan furan ya mutu fa me hakan yake nufi? Maimakon ya bata amsa sai ya sadda kanshi ƙasa, tuni ta gane me hakan ke nufi wato mamallakin furan ya mutu kenan,
"Baka amsa mini tambayata ba," ɗagowa yai da kanshi ya ɗaura idanuwanshi akan fuskarta yace"idan ganyen dake ajikin furan Ya bushe ƙamas Ya tsotse ko ya fiffige, Hakan yana nufin mamallakinsa yana acikin mawuyacin hali, Idan kuma ganyen furan ya mutu, ko ansa mishi ruwa bazai tashi ba, ma'anar hakan mamallakinsa ya mutu baya araye" duk da bata gasgata maganarshi ba, amma sai da taji gabanta ya faɗi ras, muryarta na ɗan rawa tace"Shi...shi fa daddyna? Ina nashi furan yake? Taya za'ae in iya gane cewa yana a raye ko ya mutu?" aruɗe take jera mashi tambayoyin,
Kwantar mata da hankali yayi, "Ki natsu yanzu xan duba maki na daddyn ki amma kafin nan Kiyi mini alƙawarin cewa komai ki ka gani ba zaki yi kuka ba, idan kuma muka yi nasarar ganin furan daddynki Cikin ƙoshin lafiya, zaki bani abinci abaki. Nima in baki, a karo na ƙarshe kafin mu ƙauracewa juna,"
da yake a ƙagare take da son gani, da sauri tace mashi eh ta amince, yace to ta rufe idanuwanta, Bayan ta rufe su, Na ɗan wani lokaci, Yace ta buɗesu a hankali, Kamar wata sakarya haka take bin umarninshi, tunkafin ta ƙarasa buɗe idanuwanta ta soma hango fure Launin Kore, a gaggauce ta zare eyes ɗinta akan furan har zata fara Farin ciki sai kuma ta lura da naƙasar dake a ƙasan furen ya ɗan lanƙwashe alamar ba lafiya atattare da shi.
Wasu irin zafafan hawayene suka wanke fuskarta, Har wani zazza6i taji ajikinta, muryarta adabarbarce take faɗin" Danish Ya mutu ko? Naga ganyen kamar ya karye, Dan Allah ka faɗa mini, zuciyata zata Iya bugawa...." tsananin tausayinta ne ya kama shi ganin yadda tabi ta ruɗe, bakomai yake tunani ba face Iyayen shi, Shi da bai rayu dasu ba, kuma ba shi da tabbacin Suna araye ko sun mutu, shin dagaske sune suka sadaukar dashi? Anya kuwa shima yana da iyaye kamar kowa? A lokacin baya kafin zuwan angel bai ta6a tunanin wasu iyaye ba, gani suke Yi kamar tsohuwa itace komai na rayuwarsu, zuwan angel ne yasa suka fara tunanin suma ina iyayen su suke? Idan tana basu labarin irin ƙaunar da daddynta yake yi mata sai suji inama ace suma sunyi rayuwa da nasu Iyayen........."
Sautin kukan angel daya ƙaru ne yasa shi Barin yin zancen zucin nashi ya ɗago ya kalleta, ta wage baki sai kuka take Yi, baisan time daya saki murmushi ba, bai ta6a ganin ƙuruciyarta ba sai yau, da ta gasgata abunda shi kanshi baida tabbaci akanshi, kawai yana nuna mata ne don ya samu ya kwantar mata da hankalinta,
Ahankali ya sanya hannayenshi biyu Ya tallabo fuskarta, Yana ƙare mata kallo, hawaye ta ko'ina, Cikin sanyin murya yace"kin manta bayanin da nayi maki? Idan har furan bai bushe ba ko ya fiffige ya mutu, to mamallakinsa yana araye," Cikin shessheƙar kuka tace"Am...amma ae ya naƙasa, kai ba ka ga Ciwo a jikin iccen shi ba" Da lumsassun idanuwanshi ya ɗan kalli furan kafin yace"na gani, sai dai ba hakan yana nufin mamallakinsa ya mutu ba, sai dai ko karyewa ƙafarshi tayi sakamakon wani rauni daya ji, ko kuma wani ciwonne na daban ya same shi a ƙafar shi, kinji ma'anar raunin dake ajikin furen" hannu tasa tana share hawayenta hankalinta har ya ɗan kwanta,
"Kuma Allah idan har na gane cewa ƙarya kake Yi mini, to ka sani har bada babu ni babu kai, kuma kullum xan dinga zuwa ina duba furennin ina basu ruwa akai akai. Kodan kada su mutu, hakan kuma ba yana nufin na yarda da maganganun ka bane kawai dai zanyi amfani dasu ne" ƙiris ya rage ya saki dariya, jin wautarta, Ta wani 6angaren kuma yaji daɗi sosai, koba komai yasanyata farin Ciki, ya kuma bata aikin yi, duk da shima yana jin fargabar ranar da zata gane cewa ƙarya yake yi mata,
Taso ta tambaye shi furan aunty aneelerh kodan tasan awani hali take aciki, amma sai ta fasa don ta gaji da zama Acikin toilet ɗin, Gashi tana buƙatar Yin wanka sai dai tasan bazata Iya ba saboda ga6o6in jikinta dake yi mata ciwo,
"Muje mu ci abinci, Ko xaki yi wanka in taimaka maki"? Sakin baki tayi tana kallon shi jin abunda yace,
"Yanzu idan nace ka taimaka min inyi wanka? Kuma saika amince"? Fuskarta a ɗaure tayi mishi maganar, baisan sadda ya furta"ae naga komai jiya so ba wani abu bane, nima ae kin ta6a gani na naked, bai kamata ki damu ba, har wankan ma sai mu yi atare,"
ras taji gabanta Ya faɗi, Ta zazzare gray eyes dinta tana kallonshi, Da sauri ya sanya tafin hannayenshi biyu ya toshe kunnuwanshi, saboda gudun tsiwar da zatayi mashi, shi kanshi baisan Ya furta maganar ba, su6ul da baka yai,
sosai ta runtse idanuwanta, tana ƙoƙarin tariyo abunda ya faru jiya, saboda lokacin data dura tagar nan, batasan cewa Ya zame wandon jikinta ba, Ita dai kawai tasan ta dura ta miƙi hanya, sai yanzu da ya yi wannan maganar ya tuna mata da komai, aikuwa ta daddage ta fasa wata irin gigitacciyar ƙara, Jikinshi ya kama rawa, saboda sautin daya fita hatta masu bacci na Cikin ɗaki saida suka farka, Kusan atare suka yaye bargunansu, agaggauce suka dudduro daga saman gadajensu, da gudun gaske suka nufi sashen toilets dinsu hada masu Yin tuntu6e garin sauri, Haris ne agaba su Hanna na abiye dashi, kamar wasu sabbin mahaukata haka suka faɗo Cikin toilet ɗin, Gaba ɗayansu ne suka shugo ciki, Sai faman haki suke yi, a matuƙar ruɗe suke kallon angel da danish, ta runtse idanuwanta jikinta har wani jijjiga yake yi kamar mai iskokai, muryarsu da alamun baccin bai ishe su ba, suka shiga tambayarsu lafiya, azeeza tuni ta nufi angel ita da parveen suka zukunna suna shafa fuskarta tare da tambayarta lafiya meya faru da ita? Meyasa take kuka, Hanna dasu rubina suka karasa suma suka zuƙunna agabanta, Mazan da suka rage a tsaye sai aika mishi da harara suke Yi, gani suke kamar wani mugun abun yayi mata, dama tun Juya suke zargin shine yayi mata bugun tsiya da har ta raunata,
Haris yana huci yace"wato saboda kaga muna bacci shine ka ɗaukota daga saman gadonta ka kawo ta cikin toilet ka naɗe hannun rigarka ka nannausheta saboda bugun da ka yi mata jiya bai ishe ka ba, Wai danish me kake so ka zama ne? Slowly Ya xame hands dinshi daga saman ears ɗin shi daya toshe, hawaye ne kwance acikin fararen idanuwanshi, Tsawar angel tayi matuƙar ta6a kanshi ta tsokano mishi da lalurarshi, shiyasa jikinshi ya kama kakarwa,
Javed yace"Ae bazai ta6a buɗe baki ya bamu amsa ba, mugu kawai, yanzu xamu ji komai abakinta tunda ta farfaɗo, serious idan har tace kaine ka dake ta, zaka ji a jikinka ne,"
Mubeen dai bai ce komai ba, Ya jingina bayanshi Jikin bango yana kallonsu, Gaba ɗayansu babu wanda Ya lura da sabbin kayan da aka sanya musu acikin toilet ɗinsu, saboda hankalin su ba a kwance yake ba,
Su Deeja sai faman lallashinta suke Yi, Ganin yadda take ta kuka, Tana faɗin Wlh ka cuce ni, Na tsane ka Danish, ashe kai ɗan iska ne ban sani ba, Allah ya isa bazan ta6a yafe maka ba, tun da ka gane min budurci na....." muryarta ashaƙe ta ƙarasa maganar, ita kanta batasan menene ma'anar budurci ba, tadai san kalmar acikin kanta, azeeza ta janyota ajikinta ta rungumeta tare da zagayo da hannayenta saman bayanta, tana ɗan bubbugashi, Hankalinsu Haris yai matukar tashi jin abunda tace har suna haɗa baki wurin maimaita kalmar budurci, basu ta6a ji ba sai abakinta, Amma sai suka ɗauka cewa wurin bugunta ne Ya ta6a wani organ na jikinta, Shi take kira da budurci, nan fa suka harzuƙu, Naufal Ya shaƙo wuyan rigar Danish Ya ɗago dashi Yana huci yace"ka faɗa mana uban me kayi mata? Taya akai ka gane mata budurcinta? Saboda baƙin hali irin naka"! bawan Allah ya rasa ya zaiyi, hayaniyar su ba ƙaramin tafasa zuciyarshi take yi ba, Ga wani irin zafi da jikinshi ya ɗauka, haris ne ya lura da yadda yake lumshe idanuwanshi, Da sauri ya ƙarasa gabansu Ya ruƙo hannun naufal ya janye shi daga jikinshi, wani irin jiri ne ya kwashi danish Ya tafi xai faɗi ƙasa sai dai bai kaiga ƙarasawa ba, haris Ya tallaboshi da hannu biyu, ya ruƙo shi zuwa saman jikinshi, Ya rungume shi sosai, yana ambaton sunanshi, duk da ƙarnin Jinin da ke a jikinshi hakan baisa haris Ya guji ta6a shi ba, kallonsu mubben yai tare da cewa"Pls ku taimaka mini, mu kai shi daki" Turo baki Javed, Naufal kuma ya juya mishi ƙeya, mubeen Ya ɗaga kai ya kalli ceilling ɗin toilet, alamar bazasu ta6a shi ba,
"Ka bani mamaki haris, Kafi kowa nuna 6acin rai akan abunda Danish yayi mana, amma sai gashi yanzu nema ka ke yi ka taimake shi" Rai a6ace naufal yai maganar,
Fuskar haris ɗauke da matsananciyar damuwa yace"bazan iya jure ganin shi acikin mawuyacin hali ba, Shi ɗan uwanmu ne, tabbas yayi mana kuskure amma abunda nake so ku fahimta, koda ace danish Bai miƙa ma giant batool ba, to xasu ɗaukota ne da kansu, don su tafi da ita, baida za6ine,"
Sunyi mamakin canzawar da haris yai lokaci ɗaya, duk dan sunsan irin ƙaunar dake a tsakanin shi da Danish, dole yaji tausayin shi a halin dayake ciki,
Ganin sunƙi taimaka shi yasa shi yin fushi, Yaja danish shi kaɗai ya shiga dashi cikin ɗaki ya kwantar dashi saman gadon shi, idonshi biyu sai dai jikin nashi ne ba ƙwari,
Shigowa cikin ɗakin Hanna da deeja su kayi angel tana a goye bayan hannah, Ta rurruƙeta da hannu biyu. A saman gadonta hanna ta kwantar da ita, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, a can ƙasan zuciyarta wani irin ƙunci ne ya cunkushe mata, danish yaga tsiraicinta, Babu sauran kwanciyar hankali, yanzu shikenan zai dinga ganinta tsirara koda ace da kaya ajikinta, tuna wannan yasa ta ƙara fashewa da wani sabon kukan, gaba ɗaya hankalinsu Ya dawo kanta, baiwar Allah bakinta duk ciwo amma ahaka take riskar kuka,
"Dan Allah angel ki daina kuka, Kiyi haƙuri, Ki faɗa mana me danish yayi maki? Hibbe ce tai mata magana, duk sun shiga damuwa, Azeeza tace"ina matuƙar jin tausayin angel, taji jiki ba kaɗan ba, danish bai kyauta mana ba Allah," Kowa yana tofa albarkacin bakinsa, danish dai duk yana sauraronsu ya lumshe idanuwanshi yayin da hannayen shi biyu ya rungume pillow dasu,
sai da Angel ta gama shan kukanta mai isarta, tukunna tace musu ita fa bashi bane Yayi silar halin da tashiga ba, hasalima taimakon ta yayi a jiyan nan, a dole ta ƙirƙiro ƙarya ta fada musu cewa, Ta fita hayyacinta ne Saboda ɗauke batool da akayi shine ta fada toilet ta ɗauki bokitin nan na ƙarfe ta bubbuge jikinta dashi, da ta galabaita shine ta faɗi ta sume cikin toilet ɗin, ta faɗa musu hakan ne badan tana so ta kare shi ba, face don ta kwantar musu da hankalinsu,
Gaba ɗaya sunyi amanna da abunda ta fada musu, har suka ɗanyi danasanin maganganun da suka gaya mishi duk da haushin sa da suke ji, Duk wannan abunda dake faruwa babu wanda ya ankara da sabbin gadajen da aka sanya musu acikin dakinsu, Har sai da suka fara Jin yunwa, Parveen tana hamma tare da kai hannu ta shafa cikinta ta soma ambaton Yunwa take ji,
Tana rufe baki Danish yace "An kawo mana breakfast tun ɗazu da safe, time da kuna bacci," batare daya buɗe idanuwanshi ba, yayi maganar,
Atare suka Juya baya don suka ga In dagaske ne an kawo musu abinci, duk da sun cewa danish baya ƙarya.....
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Kaitsaye idanuwansu suka sauka akan sabbin gadajen da aka jera a cikin ɗakin nasu, gaba ɗaya suka zazzare idanuwansu saboda tsabar mamaki duk suka bi suka ruɗe, Sun saki baki suna kallon Ikon Allah saboda ba su yi tsammanin zasu yi arba da wani baƙon abu a cikin ɗakin su ba, da mamaki akan fuskar parveen Tace"Kuna ganin abunda nake gani kuwa? ko dai idanuwana ne suke nuna min ba dai dai ba"? Azeeza tace"Ae duk mun gani sabbin gadaje ne har kusan goma sha biyar tare da Akwatuna Biyu, ko a ina aka same su"? Danish ne ya basu amsa da cewa Ɗazu da safe kuna bacci giants suka kawo su, akwai ma kayan amfani da aka sanya mana a toilets" deeja tace"hakan na nufin zamu kar6i baƙuncin wasu prisoners ɗin"? Tai tambayar fuskarta babu walwala, domin kuwa ba abun farin ciki bane agare su, da duk wani mai hankali ba zai so wani bawa ya ɗanɗani irin rayuwar ƙuncin da suke yi ba.
"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Ni dai har ga Allah bana farin ciki da zuwan waɗannan Sabbin prisoners ɗin, Saboda bana so suma su ɗanɗani irin rayuwar da muke Yi acikin kurkukun nan" Deeja ce tai maganar, Haris yace"ni kaina bana son mu ƙara yawa, muna fama da kanmu xa'a ƙaro mana wani ciwon kan" hibba tace" ni babban baƙin ciki na, Mu da muke fatan wata rana mubar kurkukun nan, sai gashi ana ƙoƙarin kawo mana wasu har mutum goma sha biyar zamu ƙara cunkushewa, tashin hankali kuma zai ƙaru" hannah tace mu je mu duba gadajen ni sunyi mini kyau, Dama mu ma a canza mana sababbin," wani kallon harara deeja tai mata "Wato ke ta gado kike yi, to Allah yasa acanza miki gadon kiyi ta zama cikin prison ɗin, mu kuma Allah ya bamu sa'ar fita daga cikinsa" hanna tana ƴar dariya tace ba amin ba, Aniyarki tabi ki,"
Agaban gadajen suka tsaitsaya cirko cirko suna ƙare musu kallo, Sabbi gal dasu sunyi matuƙar yin kyau, Azeeza da parveen hada ƙoƙarin hawa saman wasu daga Cikinsu suna faɗin Bari su ɗana kafin baƙi su ƙaraso, azeeza tace ita yau ma asaman sabon gado xata kwana, suma sauran su ka ce duk anan zasu kwana su sha lagwada,
sai da suka gama kallon gadajen kafin suka koma kan akwatunan suna kallonsu tare da Floor laps ɗin da aka ajiye musu, ba ƙaramin daɗi suka ji ba, dama fitilun dake gare su sunyi kaɗan, Idan dare yayi sai dai mutun yai ta yawo da fitila zuwa toilet, amma yanzu sun yanke shawarar zasu ɗauki ƙananun fitilun guda uku, su ajiye su a kowani toilet, don su sawwaƙawa kansu.
a cikinsu an rasa wanda zai buɗe boxes ɗin nan, duk sunyi tsammanin Ba mallakin su bane, na sabbin prisoners ne da za'a kawo shiyasa basu ta6a su ba, saima suka kawar dasu zuwa bakin gadajen, bayan sun gama da ɗaki, eve tace"su je su duba toilets suga sabbin kayan da aka sanya musu, Parveen ta bubbuga ƙafa tare da cewa"Mu fara Cin abinci tukunna idan ku ba ku jin yunwa ni ina ji" sai da ta yi maganar suka tuna da cikinsu, hankalinsu gaba ɗaya yana akan Kayan da aka kawo musu,
Atare suka nufi dining carpet ɗinsu suka zazzauna, Kowa ya natsu zasu fara Cin abinci,
Duk wannan abun dake faruwa angel da danish suna kishingiɗe saman gadajensu, sun Juyawa juna baya babu mai fuskantar wani, kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarshi, ita dai damuwarta batool ɗinta, ko awani hali take ciki? Fatanta Allah yasa maganar da danish ya faɗa mata akan furen nan ta zama gaskiya,
Bayan su parveeen sun kammala Cin abinci. Sauran da suka rage ma angel da danish, Haris yace su je su ɗauko kwandon batool a kwashe musu nasu aciki, Nan fa duk jikinsu yae sanyi tunawa da batool ɗinsu, duk da dama tana acikin ransu ba yadda za su yi ne, tsakaninsu da ita addu'a ce kawai.
Hanna ce taje ta ɗauko kwandon batool dake a kusa da gadon danish Kifin da suka ajiye mishi tun jiya duk ya bushe jikinshi, hada ƴar rabin gwandar da baici ba, nuna musu kwandon tai tare da cewa"Fried fish din ma ya lalace bari naje na zubar dashi, in wanko basket din sai asanya musu abincin aciki....." tunkan ta ƙarasa maganar parveen tai wuf ta sanya hannu ta kar6e kwandon tana faɗin"Inji wa yace maki ya lalace, bani nan ki gani, yanzu nan zan sanya shi a hanya..." Murmushi suka saki gaba ɗayan su yayin da suke kallonta, A ƙasa ta zuƙunna ta ajiye kwandon tare da kai hannu Ciki tana tatta6a Jikin kifin, azeeza tace"amma parveen baki da hankali, tun jiya fa yake a buɗe cututtuka duk sun hau jikin shi a haka zaki ce? Salon Cikin ki ya 6aci," Harara parveen