Showing 138001 words to 141000 words out of 287659 words
Chapter 47 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
tace yayi ma kanshi ƙiyamul laili, dama Bata son ya faɗi ne don kada ajinta ya zube, su ji cewa itace ta biyo shi don ta ba shi haƙuri,
Bata fito daga Cikin toilet ɗin ba, sai da ta yi wanka, A waje ta samu Su haris suna Jiran Na cikin toilets ɗin su fito su ma su shiga ko sun samu su yi wanka, Wuce su ta yi zuwa Cikin ɗakin, Babu kowa duk suna a can sai ita kaɗai, daga gefen gadonta ta zauna, bakomai ya faɗo mata acikin ranta ba face Deeja, Ko awani hali take ciki yanzu Allah wa'alamu, ɗaga hannayenta sama tayi cikin harshen labarabci ta soma jero addu'o'i tana karanto da niyar Allah ya tsare musu ƴar uwarsu, tana Cikin Yin addu'ar taji yo motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, da sauri takarasa shafa addu'ar, Ta juya tana kallon ƙopar, tsohuwa ta fito daga cikin ɗakin, hannunta ruƙe da sanda, fuskarta a harmutse baka Iya gane awani yanayi take, haɗa ido su ka yi da angel, da buɗar bakinta sai cewa ta yi"Ba zaki zo ki gaishe ni ba"? Murguɗa mata baki angel ta yi tare da cewa"Mutanan kirki nake gaisarwa, ba masu matattar zuciya ba" bazawarin murmushi tsohuwa tasaki, haɗi da girgixa kai tace"kin tsane ni kamar mutuwarki" angel tace"fiye da haka" dariya tsohuwa tayi,
"Idan ba ki son ganina to ki kwantar da hankalinki, nan badajimwa ba, Zaku daina gani na," babu yabo ba fallasa angel tace"Da munji daɗi wlh, kwara mu daina ganinki, tun da dama babu amfanin da kike yi mana, sai sai kawai kullum ki leƙo da ƴar sanda a hannu," wannan maganar ta angel ba ƙaramar dariya ta bata ba, Musamman data kwatanta yadda tsohuwa ke leƙo wa da kanta,
"Ba zaki yi kewata ba"? Ta jefa mata tambaya, angel tace"Kin ta6a ganin anyi kewar maƙiyi? To idan ma ana yi ni bansani ba, Ni dai burina shine ki fita arayuwar mu, saboda baki da amfani, " hannu takai ta ɗauki pillow Ta ɗago dashi tana nuna ma tsohuwa tace"Kinga wannan matashin kan na hannu na? wlh yafi ki amfani yafi ki daraja da ƙima a wurin mu, ai ke dake da waccan tukunyar fulawar ta Cikin toilet ɗin mu baku da banbanci,"
Tuntsirewa tsohuwa ta yi da wata irin mahaukaciyar dariya hhhhhhhh, da gudu su Hannah suka shigo cikin ɗakin sakamon Jin sautin dariyar tsohuwa wanda yajawo hankalinsu, A tsakiyar ɗakin suka tsaitsaya suna Kallonta, Ɗauke ido tsohuwa tayi daga kan angel ta mayar dasu kansu Batool tace"Kuma bazaku gaishe ni ba"? Maimakon su gaishe ta, Sai suka juya suna kallon angel, Tsohuwa tace"ba shakka, Uwarku kuke Jira ta baku Umarni kenan"? Shiru suka Yi basu ce mata komai ba, Still idonsu na akan angel data maƙe musu kafaɗa alamar kada su gaishe da ta ita, Shigowa cikin ɗakin mazan su ka yi gaba ɗayansu duk sun yi wanka, Suna ƙarasowa inda tsohuwa take, cikin girmamawa Danish Ya ɗan russuna tare da gaishe da ita, hakan ba ƙaramin fusata Angel yayi ba, har saida taja dogon tsoki,
Dogara sanda tsohuwa ta yi zuwa inda danish yake a tsaye, Ta miƙa hannunta ɗaya ta shafa sumar kanshi tace"Albarka zata tabbata akanka, Yarona, ina matuƙar alfahari dakai, Saboda kai na musamman ne, Zan yi kewarka sosai" Cikin sanyin murya danish yace"meyasa kika ce haka"? gajeran murmushi tsohuwa tasaki kafin tace"Bakomai," ta ambaci hakan tare da kallon su Batool dake a tsaitsaye cirko cirko tace"Ko kaɗan banji haushi ba da kuka ƙi gaishe ni, Saboda bancancanci hakan ba, Naji daɗi da ku ka nuna min cewa Kun girma kun mallaki hankalin ku, zaku iya tafiyar da rayuwarki even without me," tana kai karshen maganarta, A sukwane ta juya tana dogara sanda ta nufi ɗakinta, Har ta kusa shiga sai kuma taci burki, kamar an dakatar da ita, a hankali ta waiwayo baya ta kalli angel dake zaune tana hura hanci, tace"me ma ki kace? Dani da tukunyar fulawar dake acikin makewayin ku bamu da banbanci"? Ɗaga mata gira angel tayi alamar eh, dariya tasaki tana girgiza kai tace"Tukunya fulawar dake a makewayinku tafi ni mahimmanci Angel, Ku dage da bata ruwa akai akai, Furannin dake Acikinta zasu Yi tsuro su girma, gwanin ban sha'awa," tana faɗin hakan ta juya ta karasa shigewa cikin ɗakinta, taja ƙopa ta rufe,
Ta6e baki angel ta yi tare da watsa hannayenta tace"Abanza" batool tace"bansan meyasa naji jiki na yayi sanyi ba, sai naga kamar bamu kyauta ba da muka ƙi gaishe da tsohuwa" Harara angel ta watsa mata"Ae sai ki bita cikin ɗakin ki gaishe da ita, Ni ko me matar can zata yi wlh bazan ta6a girmamata ba, muguwa azzaluma macuciya kawai da ita," Cikin sanyin murya danish yace"Ki daina angel badai dai bane, ita tamkar mahaifiya ce agare mu, koda ace kuwa muguwace ita, saboda tafi iyayen mu, idan har dagaske suna araye kuma su ne suka yi silar zuwan mu nan" daƙyar ya kai ƙarshen maganar, ganin tana nuna shi da yatsan hannunta"Kai ka kiyaye ni! Wato raini ya fara shiga tsakanina dakai saboda jiya mun kwana a shimfiɗa ɗaya ko"? yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya taba su batool ba, Haris yace"Da alama Jiya kunji daɗin baccin nan, shiyasa muka taras daku a manne da juna, Yadda kasan ANTA da JINI,' dariya su hanna suka saki, Angel kuwa tasha mur, tana jifar danish da harara, murmushi ne ya bayyana akan fuskar danish, tana ƙunƙuni tace"zamu haɗu" juya mata ƙeya ya yi, batare da ya tanka mata ba,
Azeeza tace"Ni dai bari naje toilet, In zuba ma fulawar nan ruwa, Saboda tsohuwa tace mana tana da amfani" ruƙo wuyan rigar azeeza haris Yayi"Zo nan Sullu6iyo, Ke har kin yarda da maganar ta? Bayan irin ƙarairakin da take gaya mana? Shin idan kin bama fulawar ruwa ta girma, wani amfani zata yi mana? Ko ɗibarta zamu dinga yi muna ci ne"? Yayi tambayar yana Leƙen fuskarta, Gatsina mashi hanci ta yi, tare da cewa"Oho, Nima bansani ba," ta faɗi hakan tare da buge hannunshi, Ya zame daga ruƙon da yayi mata, Hanna tace"Dama ita mashiririciya ce narasa me ke damun azeeza, Kwakwalwarta gaba ɗaya shirme ne acikinta, saboda rashin aikin yi flower zaki je ki zuba ma ruwa? bubbuga ƙafa azeeza tayi rai a6ace tace"To wai ina ruwanku dani ne? Bani naji zan iya ba, Sai ku ƙyale ni," Da ɗan tsoki ta ƙarasa maganar,
Parveen dake ta faman Yin hammar yunwa tace"Dan Allah ku yi shiru, Surutunku Yana ƙara Harzuƙa Yunwar Ciki na,"
Rubina tace"damuwarki kenan, abinci abinci, Kowa dai da abunda ya ishe shi," Haris yace"Ni kuma damuwata deeja, " Yana faɗin hakan gaba ɗaya walwalar dake akan fuskar kowannan su ta canza zuwa damuwa,
"Ba kai kaɗai ba haris, Gaba ɗayan mu mun damu da deeja, tana acikin ran mu, Mun yi shiru ne saboda bamu da yarda zamu yi, damuwa ko yin kuka bazasu ta6a dawo mana da ita ba, Haƙuri Shi ne yakamata mu yi, Sai kuma mu bi ta da addu'a, Allah Ya tsare mana ita aduk in da take" Angel ce tayi maganar a yayin da ta miƙe daga saman gadonta, walking Slowly Ta nufi inda suke a tsaitsaye itama ta tsaya, Jikin kowannan su Ya yi sanyi, shessheƙar kuka azeeza ta fara, aikuwa haris ya daka mata tsawa tare da cewa"Zaki yi shiru ko saina buge maki baki? Ƴar rainin wayau, yanzu kika gama zancen bama flower ruwa amma daga jin anyi maganar Deeja kin wani 6are baki zaki ma mutane kuka ke da kika fi kowa ƙaton baki acikin mu" idamuwanta cike tab da kwalla take kallon haris, sai kuma ta duƙa ƙasa ta ɗaura kanta saman guiwowinta ta fashe da kuka, girgiza kai danish yai idonshi akan na haris, Shi ma haris din kallon nashi yake yi, don yasan dole ya tanka mashi, Saboda sanin halin shi na rashin son ana 6ata musu rai, musamman azeeza kodan yana ganinta ƴar ƙarama ne acikinsu,
Tunkafin danish yace wani abu haris ya riga shi cewa"Its ok Bazan ƙara ba, amma itama ta daina Yi mana kuka" Azeeza dake a tsugunne tana kuka ta ɗago da kai Cikin shessheƙa tace"Bazan daina ba, In ka tashi ka kashe ni, Kuka yanzu na fara" yanayin yadda ta yi maganar taso basu dariya,
Matsawa angel tayi kusa da azeeza, Ta sanya hannayenta biyu ta ɗago da ita, tare da rungumeta ajikinta, tana lallashinta, Cikin ƙanƙanin lokaci azeeza ta yi shiru, kamar wadda ta samu jikin mahaifiyarta, ta lafe ma angel, hada zagayo da hannayenta biyu abayan angel ta ƙanƙame, Batool dake kallonsu ta saki murmushi, tare da cewa"gwanin ban sha'awa," angel tace"kema idan kinaso kizo in rungumeki" kafin batool ta bata amsa, Hanna tace"Ni baki ta6a rungume ni ba ajikin ki" Tun da hanna tace haka gaba ɗaya sauran Ƴan matan suka ce suma bata ta6a yin hugging ɗinsu ba, Lokaci ɗaya ta ji gabanta ya faɗi rass! Da sauri ta sanya hannayenta Biyu ta janye azeeza daga Jikinta, Hannunta na dama ta ɗaura saman ƙirjinta a saitin zuciyarta, Yayin da la66anta suke kerma, Hankalin su Hanna ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin irin canzawar da angel ta yi, Ji su ka yi ta fara ambaton"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un"! har suna haɗa baki wurin tambayarta lafiya, Girgiza kai ta ɗanyi tare da cewa"Bakomai kawai bana Jin daɗi," Tana kai karshen maganarta, Jiki na kerma ta koma gefen gadonta, duk sunata kallonta,
Haris yace"Yakamata Mu je mu zauna, kafin giants su kawo mana abinci," hibba tace"Yau bazamu motsa jiki ba"? Parveen tace"Sai mun ci abinci tukunna," Basu kai ga zuwa sun zauna ba, Sai ga Giants sun shigo kawo musu abinci, Bayan sun sauke abincin Jiki na rawa kowannansu Ya samu wuri ya zauna saman dining carpet, Suna tsaka da cin abincin Angel ta miƙe suka tambayeta Harta ƙoshi sun ga bata Ci dayawa ba, tace masu ta ƙoshi, gaba ɗaya sun lura da yanayinta, kamar bata Jin daɗi, ko bayan da suka kammala Cin abincin giants suka tafi, Agaban Gadon angel suka je suka tsaitsaya Suna kallonta, Ta kwanta idanuwanta na fuskantar ceilling, cikin nuna damuwa suka tambayeta ko lafiya tace musu babu komai su kwantar da hankalinsu, Badan sun yarda da maganarta ba suka ƙyaleta kowa ya koma saman gadon shi ya zauna, Yau ko motsa jikin basu samu sun yi ba, saboda canzawar da angel ta yi musu, tana daga kwance ta kasa kunne tana jin muryoyinsu suna fira, parveen tace"idan angel ta gudu damu, zuwa gidansu, Shikenan mun huta da ganin giants, Zamu sakata mu wahala, Kuma zamu dinga fita yawo, Wlh ni duk na ƙosa inga ya wajen kurkukun nan yake, Nasan zaiyi kyau sosai, kuma zaifi daɗi," Azeeza tace"kuma ta faɗa mana cewa daddynta zaiso mu kamar ya'yanshi, hada sauran ƴan uwanta ma, mu ma zamuyi rayuwa kamar kowa, " can kuma tajiyo muryar javed yana cewa"dama kun daina wannan mafarkin da bazai ta6a zama gaskiya ba, In banda abunku taya za'ai ku fita daga Cikin kurkukun nan? kuna tunanin Giants zasu Barku? haris yace"faɗa musu dai, Nima jinsu nake kawai, Ni bana so ma suna ƙwallafa rai akan son Yin rayuwa awaje, saboda suna wahalar da zuciyoyinsu ne, ita kanta angel ɗin da take Sanya musu rai, bata da hanyar da zata Iya ku6utar dasu" Hanna tace"Amma ae ta faɗa mana cewa, Idan muka dage da addu'a, muna kai kukan mu wurin Allah, Zai ji ƙanmu ya taimake mu, Mu fita cikin kurkukun" koda tayi wannan maganar sai haris Ya tuntsire da dariya tare da cewa"Taya kenan hakan zata Iya faruwa? Wannan fa ba gaskiya bane....." Bai ƙarasa maganar ba, sakamakon Tsawar da angel ta daka mashi, a yayin da take ƙoƙarin miƙewa daga saman gadonta, Hankalinsu duk ya dawo kanta, Harara ta wurga mashi tamkar ƙwayar idanuwanta zasu faɗo ƙasa, Muryarta da rauni tace"Ya isa haka haris! Bana so kana shiga hurumina, kuma Ka daina ƙaryata magana ta! Idan kai baka Yi imani da Allah ba, Su sunyi, Kuma in sha Allahu zamu samu mafita ne bi'iznillahi, ka zuba ido ka gani" Jinjina kai haris yae fuskarshi ɗauke da murmushin rainin wayau, yaso ya mayar mata da martani, Amma danish ya dakatar dashi ta hanyar yi mashi magana, gyaɗa kai ya yi tare da jan baki Ya yi shiru,
Ɗakin Ya yi tsit babu mai magana, wuraren marece, Duk sun kwanta saman gadajensu, wasu sun fara bacci, yayin da wasu kuma sun lumshe idanuwansu ne badan suna jin bacci ba,
Damuwar duniya ta ishi angel, Ga wani irin faɗuwar gaba da take ji, tarasa gane dalilin hakan, addu'o'i kawai take janyowa Acikin zuciyarta, Tana ji aranta kamar wani abune zai faru, wasa wasa suna kwancen nan har dare Ya ratsa hasken ɗakin Ya yi duhu, tun tana iya jiyo hirarsu suna faɗin har yanzu ba'a dawo da deeja ba, har tadaina Jin surutunsu alamun sunyi bacci, Aranta tace"ita kuma wannan Makauniyar rayuwar haka zata ƙare? Kullum muna ƙunshe a ɗaki Ɗaya tsawon shekara da shekaru, Gaskiya bazai yiyu ba, Nifa ina da burikan da nake son Cimmawa don haka bazan zauna in zuba ido ba, dole in nema ma kaina mafita, tana karasa zancen zucin nata, ta yunƙura ta sauko daga saman gadonta, Cikin duhu ta shiga laluban Fitilun ɗakin su, ko da ta ɗauko fitilar bata kunnata ba, saboda gudun kada Danish ya farka daga bacci Ya bi bayanta, Cikin sanɗa taci gaba da tafiya ko sautin tafiyarta baka Iya ji, tana shiga sashen toilet ɗin Abakin door ta kunna fitilar, Ta buɗe toilet ta shiga ta zura jamlock, A ƙasa ta sauke fitilar, Ta ɗauko bokitin ƙarfen nan, ta Ajiye shi jikin bangon da tagar Nan take, saboda ta sa mu tsawonta yakai, Daddagewa ta yi tare da haye saman bokitin, tana yunƙurin kai hannu ta zame glass ɗin muryar danish Ta ratsa kunnata
"Angel!" ras taji gabanta Ya faɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau kerma, tsantsar 6acin rai ne ya bayyana akan fuskarta, a tsiyace ta juya saitin Da yake tana kallonshi, A tsakiyar toilet ɗin taganshi A tsaye, tun kafin yai magana ta riga shi cewa"kai nifa nagaji, Don me zaka dinga faɗo mini cikin toilet? Bayan ka yi mini alƙawarin cewa bazaka ƙara shigowa ba?
Cikin sanyin murya yace"Ina Bibiyarki ne saboda sanin ƙudirin da kike dashi na son shiga Cikin prison, wanda yin hakan zai iya haddasa mana shiga mummunan haɗari, " Har saida taji gabanta Ya faɗi, jin abunda yace, Da mamaki tace"Oh dama kasan abunda nake son yi kenan? Taya akai ka sani?
"kawai naji araina ne, kina son ki dura ta tagar, ko last time dana Sauke maki glass, Ban yarda da abunda kika faɗa mini ba, na cewa bakya son kallon glass yana affecting ɗinki, da ace dagaske ki ke, to da tun lokacin kin kawar da shi daga Cikin toilet ɗin amma sai baki yi hakan ba, " Ya ƙarasa maganar a yayin da yake tunkararta, Runtse ido ta ɗanyi tare da cizon lips ɗinta, Rai a6ace tace"wlh duk bala'in ka baka isa ka hana Ni yin abunda nayi niya ba, kada ka kuskura kace zaka ma dakatar dani, idan har ba so kake In yi maka Illa ba"
"Angel Na roƙe ki kada ki je, Zaki jefa rayuwarki da tamu Cikin hatsari, Ba'ayi musu leƙen asiri, Ki fahimce, yafi muyi rayuwarmu Cikin duhu akan musan ainihin abunda ke faruwa acikin prison, amma daga ranar da kika haura tagar nan, xaki ja mana ne gaba ɗayan mu ne"... Tamkar zai fashe da kuka Yake yi mata magiya akan karta dura, A ƙarshe daya ga ta kafe tasa naci akan saita dura, ai kuwa da ƙarfi Ya sanya hannu ya janye bokitin da tahau sama, Gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa da sauri ya sanya hannayenshi biyu Ya tarbo ta, ta faɗo saman jikin shi, Suka rubza ƙasa atare, kanshi ba ƙaramar buguwa yai ba, ita kuwa kamar jira take yi su faɗo aikuwa ta daddage ta dunƙule hannayenta, Ta shiga kai mashi bugu a ƙirjinshi, Ya yi shiru batare daya dakatar da ita ba, zuciya ce ta fusgeta, a karshe ta kifa kanta saman ƙirjinshi tana kuka tana faɗin"Ya rabu da ita taje, Ita ta gaji da rayuwar kulle, Bazata Iya jure azabtar da ƴan uwansu da ake Yi ba, " Haƙiƙa Danish yaji tausayinta, Sai dai bazai Iya barinta taje yin leƙen asirin ba, saboda shi ya fita wayau da hankali, Ya kuma san Abunda sai biyo baya, Idan har ta dura ta tagar nan,
Tuntana yin kukan har tagaji tadaina muryarta ta disashe, Sai lokacin ya samu damar yunƙurawa Ya ɗago da ita a jikinshi, A saman kafaɗarshi ya kwanto da ita, ranƙwafa yayi tare dakai hannu ya ɗauki fitilar da tazo da ita, Ya juya ya fuce daga cikin toilet ɗin, Yana shiga ɗakinsu Ya kwantar da ita saman gadonta, Daga ƙasa ya ajiye fitilar hannun shi, Ya zauna daga gefenta yana kallon fuskarta, Wadda ta yi jaga jaga da hawaye, hannayenta ya ruƙo acikin nashi, ya soma lallashinta, ya ɗauki tsawon lokaci Amma ko kallo bai isheta ba, Sai da ya gaji don kanshi tukunna Ya ƙyaleta, Ya koma nashi gadon Ya kwanta, A daren ranar daƙyar bacci ya ɗauki angel,
Ranar da Deeja ta Cika 4 days da aka ɗauketa, A daren Ranar Giant Ya dawo da ita, Babu wanda ya sani duk sunyi nisa a cikin baccin su, A tsakiyar ɗakinsu Giant Ya sauke ta, Baiwar Allah duk ta fita hayyacinta ta rame ta fige, kamar wadda aka ɗibi naman jikinta, kasancewar sun kunna fitilun ɗakin su, Hakan ya bata damar bin Cikin ɗakin, Bata nufi ko'ina ba sai bakin gadon angel, a gefe gadon ta zauna, fuskarta sharkaf da hawaye, hannu takai saman shimfiɗar angel ta ɗan bubbuga kafadarta, Ƙasa kasa da murya take ambaton sunanta don kada ta takura ma masu yin bacci, koda angel taji muryar deeja acikin baccinta, a matuƙar ruɗe ta yaye bargonta, muryarta na kerma tace"deeja! Dagaske kece? Ko dai mafarki nake yi," jinjina kai deeja tayi