Header Ads
Showing 213001 words to 216000 words out of 287659 words

Chapter 72 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1816

Ads at the middle of Article

addu'o'e angel ta karanto mata ta tottofa mata saman fuskarta da jikinta.

Hankalin Gabriel gaba ɗaya yana akan angel, yayin da shi kuma Danish nashi hankalin ke akan Gabriel, Ya kafe shi da ido ba tare da ƙyaftawa ba, sarai gabriel ya lura da kallon tuhumar da Danish ke yi mishi, amma sai ya basar.

Saukowa yai daga saman gadon shi ya nufi angel, da sauri Danish Ya miƙa shima Ya nufi gadon Unaiza, atare suka tsaya bakin gadon, har suna haɗa kafaɗa, Kallon mamaki Gabriel yai ma Danish, fuskar angel a yamutse ta kalle su, harara ta watsa ma Danish, muryarta ƙasa ƙasa tace"Shi ne ku na ganin bata da lafiya amma an rasa wanda zai taimaka mata acikin ku sai Azeeza"? Gabriel ne yace"Bansan time da ta farka daga bacci ba, hankalina baya akanta,"Danish yace"saboda ke yasa ban je wurin ta ba" ta6e baki ta ɗanyi, tare da juyar da kanta, Ta kalli su Hanna tunkafin ta yi magana parveen tace"ae kin hana mu zuwa wurinta saboda mayyace zata shanye mana jini, shiyasa mu ka ƙi taimakon ta"

Numfasawa tayi yayin da take kallonsu, Acan cikin zuciyarta tana tunanin taya zata fahimtar dasu cewa ba mayya ba ce? Kada su ɗauke ta maƙaryaciya, tun da ita ta faɗa mu su hakan da bakinta.

"Ae bance kada ku taimaka mata ba, idan bata da lafiya, a bun dana hana ku shi ne ku daina bari tana ta6a jikin ku, saboda babu kyau, wani ya kalli tsiraicin ka koya ta6a shi, Itama don batasan babu kyau ba ne shiyasa take yi, amma in muka ja ta ajikin mu mu ka fahimtar da ita zata daina ne....." tun kan ta rufe baki, Rubina tace"Hada jinin zata daina sha"? Ɗaga mata kai angel tai alamar eh, su ka ce toh zamu dinga taimakonta daga yanzu, amma itama kija mata kunne ta daina rashin jin magana, kuma ta daina yi mana gorin ƙirji," angel tace musu toh, zata ja mata kunne.

Mayar da idanuwanta ta yi akan su Danish dake atsaye, kowannan su ita ya ke kallo, ta rasa gane dililin yin tsayuwar na su akanta.

"Lafiya"? Tai tambayar tana jiran jin amsar su, kusan atare suka haɗa baki wurin cewa ba komai," juyawa gabriel yai tare da komawa gefen gadon shi ya zauna, shi ma danish ya koma nashi gadon ya zauna.

Duk wani motsin Gabriel Akan idon Danish, Ya hana shi sakat, Abu kamar wasa, Ko toilet Angel zata shiga sai Danish yabi bayanta, lamarin ya ɗaure mata kai, a bakin ƙopar toilet ɗin zai tsaya har saita fito sannan yaja hannunta su koma ɗaki, hakan ba ƙaramin 6ata ma Gabriel rai yai ba, shi burin shi su zauna da ita su tsara yarda zasu ɗauko ƴan uwansu, da kuma yarda zasu gudu daga Cikin kurkukun tun da yaji cewa itama tana da wannan ƙudirin aranta, Sai dai ga dukkan alamu, akwai mutun ɗaya da baison hakan ta faruwa, shiyasa ya hana shi sukuni, dama can bai yarda da Danish ba, tun zuwanshi, daga gani yana da wayau, akwai abunda yake 6oye musu, kuma yasan komai akan gidan kurkukun kallon su kawai ya ke yi.

Lokacin da dare ya yi kowannansu yai shirin kwanciya, mutun biyu ne babu alamun zasu runtsa.

Jikin Unaiza ya ɗan lafa, da taimakon su azeeza taci abinci kaɗan, tun ɗazu bacci yayi awon gaba da ita.

A tsakiyar ɗakin Gabriel ya dinga sintiri yana jiran bacci ya ɗauki Danish, Ko ya samu yaje su yi magana da Angel, amma ɗan tahalikin nan Yaƙi kwanciya, ƙarshe ma daya ga dagaske Gabriel ba bacci zaiyi ba, sai ya ɗauki pillow ɗinshi, Ya koma saman gadon Angel da ke kwance tana yin bacci, Ya ɗaura pillow ɗinsa saman mattress ɗinta, ya hau ya zauna tare da jingina bayan shi jikin pillow ɗin,' mamaki ƙarara akan fuskar gabriel, Ganin wani iko na Allah, a dole ya haƙura ya koma kan nashi gadon ya kwanta zuciyarshi acunkushe da tunani kala kala,.


Dare Ya nutsa sosai, Sunyi nisan kiwo acikin baccin su, har time ɗin Danish na zaune saman gadon angel, ahaka bacci yai awon gaba dashi, Ba zato ba tsammani, Unaiza tafarka tana ihu tana daddafe cikinta, wata irin kururuwa kamar ana zare ranta, a matuƙar firgice masu bacci suka soma farkawa Kowa Yana faman zazzare idanuwanshi, Haƙiƙa sunyi matuƙar firgita, ɗaya bayan ɗaya suka soma saukowa daga saman gadonsu suna tunkarar gadonta, mutun biyu ne basu farka ba, Jamima da majnun, kamar matattu sai sharar baccin su su ke yi, A kewaye da gadon unaiza suka tsaitsaya curko curko suna kallonta hankalin su yai matuƙar tashi, suka dinga tambayarta lafiya meke damunta, amma ta kasa buɗe baki ta basu amsa, Sai cizon la6en ta take yi, yayi suntum dashi, Angel tafi kowa shiga damuwa tsoranta, har ga Allah bata son wani abu ya samu unaiza duk da baƙin halinta tana ƙaunarta.

"Yanzu ya zamuyi da ita? Danish ba wani taimako da zaka iya yi mata? Angel ce tai maganar tana kallon shi, yae shiru bai ce mata komai ba,

Haris yace"ni fa inaga kamar kalar ciwon da su Hanna suka ta6a yi ne" gabansu ne yai wani irin mugun bugu jin abunda Haris yace, muryar deeja na arude tace"In sha Allah ba shi bane," Azeeza tuni ta fashe musu da kuka, tana zaune saman gadonta, ta kasa saukowa gudun kada ta faɗi ƙasa saboda lalurarta, tana jiyo muryoyinsu acikin kunnuwanta

Suna Cikin yin maganar nan, sautin motsin buɗe ƙopa ya karaɗe kunnuwasu, hankalin su ya ƙara tashi, nan take ransu ya basu cewa Anzo atafi da ita ne' jikin su duk yai sanyi, lokacin da su ka yi arba da Giant ɗin dake saukowa saman benan, basamudan ƙato, Mai ɗauke da star 1 agaban rigarshi, tunkan ya ƙaraso ciki, suka bashi hanya, Ya sanya hannu biyu ya ɗauki unaiza saman kafaɗarshi ya juya ya fuce da ita daga Cikin ɗakin, kamar wasu sakarkaru haka suka bi bayan shi da kallo har ya 6ace ma ganin su, Suna jiyo datse ƙopar ɗakin nasu da akayi, shi kenan an tafi da Ƴar gidan daddy, Gabriel yaso ya tambaye su ina za'a kai ta? Sai kuma ranshi ya bashi cewar wata'ƙil zasu kaita inda zasu duba lafiyarta ne, hakan yasa shi dakatawa da yin tambayar tashi, dama bai shirya yinta ba agaban Danish, don zai ƙara sa mashi ido ne.

Ba su ta6a tunanin zasu zubar mata da ƙwalla ba, saboda babu shaƙuwa atsakanin su da ita, Amma sai gashi yau saboda ita sun gaza runtsawa, a gefe da gefen gadonta matan su ka zauna shiru babu mai magana, Babu yadda haris baiyi dasu ba akan su koma su kwanta saman gadajen su, amma suka ƙiya, A ƙarshe nan suka kwana.

A washe garin ranar da safe, suna ta sharar bacci, wasu sun jingina bayansu jikin bango wasu kuma sun ɗaura kawunansu saman cinyoyin ƴan uwansu, Waɗan da suka kwana asaman gadonsu, mazan ne duka sai Jamima da azeeza, Cikin sa'a Gabriel ya riga Danish farkawa daga bacci, Ae yana buɗe ido ya hango Danish baje saman gadon shi, yai wuff ya duro daga nashi gadon Cikin sanɗa ya nufi bakin gadon unaiza inda suke zazzaune suna bacci, A hankali ya zuƙunna inda angel ta jingina bayanta jikin bango, hanna ta ɗaura kanta saman laps ɗinta, haka su kai bacci jiya, saitin kunnanta yakai bakin shi cikin raɗa ya shiga kwala mata kira "Angel! Angel" har cikin dodon kunnanta, ganin tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta yasa shi yin sauyin ɗaura tafin hannun shi saman bakin ta, gudun kada ta razana ta saki ƙara Danish ya farka, tsantsar mamaki ne ya kamata ganin Gabriel, Zuƙunne agabanta, hada ƙoƙarin toshe mata baki, zazzare mishi idanuwanta ta soma yi, tare da kai hannu zata ka6e mishi nashi hannun daya toshe mata baki.

Da sauri yace"ina son magana dake, tun jiya, bana so kowa ya sani, pls ki bani haɗin kai, ki taso mu shiga sashen toilet ɗin mu" yana ƙare maganar ya zame hannun shi daga saman bakinta, Ya miƙe cikin sanɗa ya nufi 6angaren toilet ɗinsu, yana tafiya yana waiwayon shimfiɗar Danish, wata irin kasalace ta baibaye Jikinta, A hankali takai hannu ta ɗauke kan Hanna daga saman laps ɗinta ta kwantar da ita ƙasa, kafin ta miƙe ta bi bayan Gabriel, tana shiga sashen toilet ɗin ta same shi atsaye ya jingina bayan shi jikin bango.

Yana ganinta yai saurin ruƙo hannayenta biyu acikin nashi, kamar wani mara gaskiya, yana magana yana kallon bakin ƙopar shigowa sashen toilet ɗin, Nan take ta fahimci cewa akwai wanda baya son yaji abunda zai faɗa mata.

"Tun jiya nake son na yi magana dake amma ɗan uwanki ya hanani sakat, na rasa gane dalilin dayasa baya son na tunkare ki"

"You mean Danish"? Ɗaga mata kai yai alamar eh"

Tace mai ka ke son faɗa min ne"? Har ya buɗe ba ki zai yi magana ya ji ta yi saurin katse shi da cewa"Oh wai kana magana akan Unaiza da aka tafi da ita jiya? Nasan ka tsorata da ganin an ɗauke ta, bawani abu zasu yi mata ba, za'a kai ta treatment room ne aduba lafiyar jikinta" tun da angel tai wannan maganar nan take Gabriel ya fahimci cewa DANISH yazo wurin, shiyasa tai saurin tarar numfashi shi, Saboda ita ta hango shi, kamar walkiya, ko yaushe ya tashi daga bacci.

ta wutsiyar ido Ya hango shi tsaye bakin ƙopar shigowa wurin ya goya hannayen shi saman ƙirjin shi, ya kafe su da ido.

Yatsina fuska Gabriel ye ba tare daya kalli fuskar Danish ɗin ba, yaji takaicin bayyanar shi, ɗan hana ruwa gudu, sauƙin ma Angel ta gan shi da baisan me zai biyo baya ba, idan ya faɗa mata ya shiga cikin kurkukun.

"Zan shiga toilet in yi wanka, yakamata kaima ka shiga ka yi" tana magana kamar batasan da zaman Danish a wurin ba, Ta juya ta nufi toilet ta buɗe ta shiga, duk akan idon Danish, Shima Gabriel ya nufi ɗayan toilet ɗin ya shiga Ciki, Ya datse ƙopa.

Sun so ace ya koma cikin ɗaki amma yaƙi tafiya, kowannan su sai da yae wanka time da suka fito daga cikin toilet ɗin, Yadda suka barshi haka suka same shi, Gabriel bai tanka mishi ba ya wuce ɗaki, Angel ce ta tsaya tana kallon shi fuskarta ɗauke da murmushi tace"ya ka ke? Fatan ka tashi lafiya"?

Wani irin kallo taga yanayi mata, kamar ba zai amsa mata ba, muryarshi da alamun kasala ya amabaci sunanta

"Angel, na tashi lafiya, ina fata kema haka" matsawa tai kusa dashi, jikinta da lemar ruwan wankan da tayi, Tace"jiya nashiga damuwa da aka tafi da unaiza, banma san time da bacci ya ɗauke ni ba, zuciyata ba daɗi" ta ƙarasa maganar kamar zata fashe da kuka, Ruƙo hannunta yae acikin nashi, ya ɗan janyota kusa dashi,

"Fuskarki harta kumbura, yakamata ki koma kiyi bacci, ko kin samu relief," girgiza mishi kai ta yi "a'a, baccin ya ishe ni, zan jira abinci ne, ka shiga toilet ka yi wanka zan jira ka anan"

(Angel sarkin wayau, tana so ne ya shiga don ta samu damar yin magana da Gabriel, ta ƙagara amatse take da taji me zai faɗa mata)

Maƙe mata kafaɗa Danish yai tare da cewa"Bana buƙatar yin wankan, mu koma ɗaki mu zauna, mu jira abinci nima yunwa nake ji," kallon shi kawai ta ke yi, wato ta fahimci wani abu agame da Danish, shegen wayau ne dashi, mutun sai yana da kaifin basira zai iya gane hakan.

"Dan Allah ka shiga ka yi wanka, inaso ne kaima ka ji irin daɗin da naji ajikina, idan ka kammala sai mu koma ɗaki,"

kamar maroƙiya haka tadinga yi mishi magiya akan yaje yae wanka, hada bubbuga mishi ƙafa da shagwa6a, sai taga ya saki ƙayataccen murmushi akan fuskar shi, ta yi tsammanin zai amince ne hakan yasata sakin murmushi tace"Ka amince zaka shiga ka yi wankan"? Ɗaga mata gira yai tare da cewa"Eh amma atare zamu shiga, sai kiyi min, idan har baki amince mun shiga atare ba, to ki daina roƙona akan yin wanka don ba inda zanje INA ATARE DA KE!" takaici ne ya isheta

A ƙule tace "ai ni nayi wanka akan me zan bi ka mu koma toilet"? Tai maganar tana gatsina mishi hanci, yace"nasan kinyi ae, ni zaki yi mawa yanzu" tsoki taja tare da bi ta gefen shi ta wuce cikin dakin, Ya juya yabi bayanta, Suna shiga Ciki suka sami Gabriel zaune gefen gadonshi ya zabga uban tagumi, Takaicin Danish ne ya ishe shi, sam baya son aja tsawon lokaci ba tare da yayi gaggawar sanar da angel game da yarinyar nan ba, zata iya rasa ranta.

Saman gado Danish ya zauna, angel kuma ta nufi akwatin kayansu, ta ɗauko red vest ɗinta, tare da dogon wandonta baki, Ta nufi sashen toilet dinsu ta shiga, acan ta canza kayan jikinta, ta cire tsaffin ta maida sabon, Vest ɗin tabi jikinta ba ƙaramin kyau ta yi mata ba, duƙunƙune tsohon uniform din ta yi a hannunta.

Bata fito ba, sai ta tsaya tana leƙen Cikin ɗakin su daga cikin sashen toilet ɗin, bakowa take kallo ba face Gabriel, ranshi ne ya bashi cewar ana kallon shi, hakan yasa shi juyowa don ya tabbatar, Cikin sa'a su ka haɗa ido da ita, Da hannu ta dinga yi mishi alamar ya iya rubutu? Ta kwatanta mishi biro ta hanyar yin amfani da hannunta na dama kamar tana rubutu, nan take ya gane me take nufi, bai amsa mata ba saboda Danish daya tsare shi da ido, shiyasa ya kawar da kanshi gefe ɗaya, Fitowa angel ta yi daga cikin toilet din ta shiga ɗakin ta zauna gefen gadonta, ta daura idonta akan Gabriel, so take ya bata amsar tambayarta idan ya iya rubutu, tana so ta sanar dashi akan ya buɗe backpack ɗin Unaiza ya ɗauko jotter dinta da biro yae mata rubutu, Ya jiye mata, ta hakanne kaɗai zasu iya magana da juna, if not Danish bazai ta6a bari su ke6e ba, sai dai batasan koya iya rubutun ba, zaiyi wuya ma ace bai iya ba, tun da a hasashenta ba rainon kurkukun ƙaddara ba, Akwai wayewa atattare da shi.

Yaso ya bata amsa amma Danish Ya kafe su da lumsassun idanuwanshi, Su uku ne idonsu biyu acikin ɗakin, Sauran har yanzu basu farka ba, Sai daga bisani ne Ɗaya bayan ɗaya su azeeza suka soma tashi daga bacci, da tunanin unaiza suka farka, suna ta jimamin halin da aka tafi da ita jiya, abun ya ta6a zuciyoyinsu, Angel tace dasu suje suyi brush suyi wanka, idan suka fito zasu motsa jiki yau, hakan yasa suka miƙe atare suka nufi sashen toilet ɗinsu, kafin wani lokaci duk su kayi wanka, kowa ya sanya red vest din shi da dogon wandon shi na sabon kaya ba ƙaramin kyau, su ka yi musu ba.

Ba su kai ga fara motsa jikin nasu ba, Giants suka kawo musu abinci, Dama da yunwa suka farka, Kowa ya samu wuri ya zauna, tsiren nama ne aka kawo musu da kayan marmari, hada robobin lemu dana ruwa, suna cin abinci idon Gabriel akan fuskar angel, yana so ya bata amsar tambayar da ta yi mishi ɗazu shiyasa ma ya zauna yadda zasu fuskanci juna, ko da ta ɗago suka haɗa ido dashi, saboda rashin gaskiya atare suka saci kallon Danish, shi da yafi su iyawa, ashe tun ɗazu ya ajiye cin tsiren naman don kada ya janye mishi hankali daga kansu har su samu damar yin wani abu ba tare daya gani ba, kyawawan idanuwanshi na akan faces ɗin su.

Danish bai ta6a bata mamaki ba irin na yau, ashe dama yana da wayau? Yake nuna kamar sakarai ne shi? yau dai ta shaida hakan, har tambayarshi ta yi meyasa bazai ci Abincin shi ba? ya ce mata kada ta damu, zai ci ne zuwa anjima.

tasa naci akan saiyaci, yace idan har tana so yaci, to ta dawo saitin inda yake zaune, don yaji daɗin ganinta da kyau, ba tare da ta yi mishi musu ba, ta miƙe tabar saitin Gabriel ta koma saitin inda ya ke ta zauna, Sai gashi ya sanya hannu yana ci yana kallonta, a haka har suka kammala Cin abincin, Giants suka tattara farantan kayan abincin suka bar ɗakin, fitarsu ke da wuya, Angel ta nufi toilet, Da sauri Danish yabi bayanta, tana shiga ya fado ciki, murmushi ta sakar mashi tare da cewa"My bodyguard, wankan zaka yi ne"? yace mata a'a, ita ya biyo tace mashi toh, su shiga dama tazo duba furenni ne taga awani hali suke ciki, ta kuma basu ruwa, Atare su ka shiga, da kanshi ya ɗabo mata ruwa a bucket yazo da shi gaban tukunyar fulawar, har yanzu dai furen batul Yana nan yadda yake, ya bushe Ganyan sun tsamure, suna a tsaye ta kalle shi tare da cewa"furen batul ya nuna alamun bata da ƙoshin lafiya, amma banji ka ce komai ba"? Ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba, ya bata amsa da cewa"bani da masaniya akan yanayin ganyan jikin shi, zai iya yiwuwa ruwa furen ke buƙata" ya ƙarasa maganar tare da kwarara ruwan da ya ɗabo saman furennin, bayan ya kammala ya sauke bucket ɗin,

Kallon juna su ka yi ita da shi, ba tare da ƙyaftawar ido ba,

"Irin wannan kallo haka, me kake gani akan fuskata"? Tae tambayar tana dan harararshi,

Bai bata amsar maganarta ba, sai ce mata yai
"Pls angel, bana so in gan ki tare da yaron can, ni ban yarda da shi ba, kuma na lura kamar yana son shisshige miki ne......" dariyar da tayi ne ya sa shi dakatawa da yin maganar, sai da tayi mai isarta tukunna ta dai dai ta natsuwarta.

"Ka faɗi min dalili ɗaya da zaisa in janye jiki da shi, in banda abun ka ni menene alaƙa ta dashi? Ko ka ga wani abu ne"? Shaking head ɗinsa yai "just ni bai kwanta min araina ba" fuskarshi ayamutse ya bata amsa, ta6e baki ta ɗan yi, tana ƙoƙarin motsa lips ɗinta da niyar ta yi magana, ɗan juyi da zatayi keda wuya ta hango wani sabon tsiron fure kyakkyawan gaske a gefen na daddynta, waro

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads