Header Ads
Showing 180001 words to 183000 words out of 287659 words

Chapter 61 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1781

Ads at the middle of Article

toilet ɗin, sai gasu sun shigo kusan su Shida hada su javed da naufal, wai sun zo wanke mata kai, ashe bayan da hannah ta fita daga cikin toilet ɗin, ɗakinsu ta shiga taje ta kira su, donsu taimaka mata, mamaki Ya kama angel, ganin sun shigo suna nannaɗe hannuwan rigunansu, Kusan dambe akayi acikin toilet din, tana faɗin ita bata so su barshi ta haƙura da wanke gashin, Su kuma suka ce bata isa ba, Yadda aka wanke ma kowa gashi, Itama sai sun wanke mata nata, ko tana ko bata so, A lokacin Danish Yana la6e bakin ƙopar toilet din yana kallonsu, don ba ƙaramin nishaɗi ya samu ba, ganin yadda suke ta yawo acikin toilet din sai zagaye shi suke yi, Ita tana gudu su kuma suna bin bayanta hannayensu ruƙe da shower gel da comb, da sauran abubuwan da zasu yi amfani dasu wurin wanke mata gashin su gyara mata shi, Sai da kowannansu Ya gama galabaita, tukunna suka samu ta basu haɗin kai, Su shida suka wanke mata gashin kanta, tadaici azaba, har wani jiri take gani acikin idanuwanta, saboda yadda suke ja mata gashin, Bayan sun kammala wanke mata shi, waɗanda ke ruƙe da combs, suka soma sharce mata shi, daga bisani suka bi da mayukan gyaran gashi suka shasshafa mata, ' Lokacin da suka kammala, Sunyi mamaki Ganin irin yadda gashin kanta ke ta ɗaukar ido, yayi dark brown dashi ya warware tamkar hijabi yayi mata abayanta, ta yi farin Ciki sosai da suka taimaka mata wurin gyara mata gashin kanta, ta ƙara jin ƙaunarsu acikin zuciyarta,

Kafin marece ya doso, ɗaya bayan ɗaya suka soma shiga toilet suna Yin wanka, saboda yau sun shirya canza Uniform dinsu, sai ɗauki suke Yi zasu sanya sabbin kaya, Bayan sun kammala Yin wankan, Ya rage saura Danish Yaƙi zuwa yai wanka, Hatta mazan sun wanke sumar kansu, amma shi duk ya takure kanshi, Ya hana kanshi sukuni acikinsu, duk da ayanzu babu wanda yake nuna mishi wariya, tun ranar da tsohuwa tayi musu faɗa akan su daina ware shi acikinsu, tun daga ranar suka daina gaba da shi, Shi ɗin ne dai kamar baison suna kusanto shi, Kuma bakowa yaja hakan ba face Angel, ita ɗin dai ce da baya son ya karya mata alƙawari.

Ganin baida niyar tsohuwa ya wanke sumar kanshi Yasa haris zuwa har saman gadonshi, Ya damƙo hannun shi ya janyoshi, Har saida ya sauko daga saman gadonshi suka nufi toilet, Yana fadin Allah idan bakai wanka ba, Ni zanyi maka da kaina, kowa yana nishaɗi sai kai kaɗai duk kabi ka takura rayuwarka sai kace wani bare, Idanma don abunda ya faru ne ae mun yafe maka komai ya wuce mana, tun da ya riga daya faru," Kamar wani ubanshi haka haris ya dage yana tayi mishi faɗa, har suka shiga cikin toilet din, bawan Allah yai shiru bai tanka mishi ba, haris bai fito daga cikin toilet din ba sai da ya taimaka mashi ya wanke sumar kanshi, Kafin Ya fito yabarshi aciki, don yayi wankan,

Kafin wani lokaci, duk suka hallara acikin ɗakinsu, Angel ta janyo musu akwatin kayansu Ta bude shi, a hankali take zaro uniforms ɗin tana miƙa musu, da yake tasan numbers ɗinsu, shiyasa ba ta sha wahala wurin banbanta na kowa ba, Bayan kowa ya kar6i nashi, nan fa suka soma sanya su ajikinsu, Cikin dabara, Idan suka cire tsohon wandon, sai su zura sabon a jikinsu ta yadda tsiraicinsu bazai fita ba, kafin ma su sanya kayan ajikinsu saida angel ta biya musu addu'ar sanya sabbin tufafi, duk suka yi banda Danish, Ya ruƙe kayan a hannunshi yana zaune gefen gadonshi, babu alamun zai zurasu ajikinshi,

Uniform din sunyi bala'in yi musu kyau, yadda kasan ɗaliban high school na ƙasar Korea, Tabarakallahu ahsanul khalikin, Kyau ne ya haɗu da kyau, abunka ga farare kayan sun fiddo da hasken fatarsu, Sun bi shape din jikinsu sun zauna musu cuf cuf, Especially angel, Wow abun ba'a magana, Yarinyar dama can kalar kyau ce, Ƙarshe ce afagen kyau, Hatta ƴan uwanta su azeeza sai santin kyanta suke Yi, duk da irin kyan da su kayi don itama azeeza ba daga baya ba, jajayen kayanta sun mayar da ita tamkar fure awurin kyau, musamman in tayi dariya fararen hakoran nan suka bayyana ajere kamar gonar auduga, tubarkalla,

Danish fa sai satar kallon angel yake yi da zarar Ta juyo zata fuskanci inda yake sai yae saurin kawar da kanshi gefe, baisan cewa ta lura da irin satar kallon da yake yi mata ba, hakan ba ƙaramin dadi ya yi mata ba,

bakomai Yafi ƙawata kyan uniform ɗinsu ba face Cotton scarves din da suka daura awuyansu, da kuma igiyar wrap coat dinsu da suka daure, Sai takalmansu, da kuma ribbom da matan suka ɗaure Sumar kansu dashi, Banda angel saboda sanin yawan gashinta shiyasa bata yi gigin sanya ribbon ta daure shi ba, don zai iya tsinkewa, hatta giants da suka zo kawo musu abinci, sai da suka yi musu wani abu daya basu mamaki, da hannu suka yi musu thumbs up, wato alamar jinjina, wannan abun dai ya gigitasu, basu ta6a yi musu hakan ba sai yau da suka ga sun ɗauki wanka, angel dai bataji dadi ba, saboda tasan ƙarshe duk wannan gayun da suke Yi, abanza zai tashi, tun da ba fasa daukarsu za'ayi ba, sai daga baya tadinga danasanin Gyaran gashin da su kayi da sabbin uniform ɗin da suka sanya ajikinsu, don ba ƙaramin fiddo da kyawun surar jikinsu kayan su kayi ba, hakan zai ƙara ma ƴan iskan ƙaimi wurin biyan buƙatarsu da su, zasu ji daɗin gur6ata musu rayuwa, in ba haka ba taya akai giants da basu magana Yau kawai don sunga sunyi kyau shine suka yi musu alamar jinjina wato sun burgesu da suka yi gayu, aiko dai akwai matsala babba!!



*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*





Lokacin da marece ya nutsa, duk sun gaji an gama shan gayu, Anci an ƙoshi, wata irin gajiya ce ta rufar musu, ba arziƙi suka lalla6a kowa Ya nufi Sabon gadon daya mallaka suka kwanta, tun suna yin fira ƙasa ƙasa har bacci yai awon gaba dasu, Ya rage saura Danish Kaɗai zaune gefen gadonshi, don shi bai canza gado ba, har time ɗin hannayen shi na aruƙe da uniform ɗinsa Ya ƙanƙame su, Daga bisani ne Ya ɗaura su saman mattress ɗin shi.

A hankali ya sauko daga saman bed din nashi, Cikin sanɗa yake tafiya yana tunkarar gadon da angel take a kwance, Yana ƙarasawa bakin gadon ya zagayo ta left side Ya ɗan zuƙunna, yayin da kyawawan idanuwanshi ke akan fuskarta, ta natsu sai sharar bacci take yi, numfashinta yana fita cikin kwanciyar hankali da natsuwa, lumshe idanuwan shi yai tare da buɗe su kan fuskarta, wata irin natsuwa yaji acikin zuciyar shi, Angel ta yi mishi kyau, fiye da ko yaushe, zuciyarshi ce ta dinga tunzura shi akan ya ta6a sumar kanta, dama itace ta tsole mishi ido, Yatsun hannun shi na kerma ya ɗan ɗago dasu Ya ɗaura su samar doguwar yalwatacciyar sumar kanta, tun da ya soma shafa gashin, ya gaza janye hannayenshi, da zarar yaga tafara mutsu mutsu kamar zata farka, sai kaga yai wuf Ya zuƙunne gefen gadon yana faman sauke ajiyar zuciya, a hankali Yake sake ɗagowa Yana kallonta, Wannan karan Hada Tausasan la66anta Ya shafa da yatsan hannun shi, ya shagala Yana kallonta, Kamar daga sama Yaji an damƙi wuyan rigarshi ta baya, a matuƙar firgice Ya ɗago don ya ga wanene, Ajiyar zuciya ya sauke ganin haris Ne, har wani numfashi yake fitarwa kamar wanda yasha gudu.

"Bro, Me kake Yi anan? And why are u looking at her"? Yai tambayar yana kallon fuskar Danish da alamun tuhuma, a yayin da yake ƙoƙarin zame hannunsa daga ruƙon da ya yi ma wuyan rigar shi.

Cikin sanyin murya yace"Bakomai" Iya abunda ya furta kenan, Ya miƙe daga bakin bed ɗin nata, Ya nufi gadonshi Ya zauna daga gefe, Girgiza kai haris Ya yi, tare da bin bayan shi ya zauna a kusa dashi.

"Ka faɗa mini menene damuwar? May be ina da hanyar da zan Iya taimaka maka, Ka canza sosai Danish, Mun rasa gane kan ka, Kowa yana walwala amma banda kai, hatta sabbin uniform ɗinka dana baka, baka sanya ba, why Danish? Idan ma saboda abunda ya faru ne, ae mun yafe maka ko? Komai ya wuce" Cikin Kulawa Yake yi mishi maganar, daƙyar ya samu Danish Ya buɗe baki ya furta "Ita ce"

Aɗan ruɗe haris ya furta"Wa kenan"?

"Angel mana, tasa na ɗaukar mata alƙawari akan cewa zan nisanta kaina da ita, ko kallo kar in bari ya haɗa ni da ita, haris na shiga damuwa sosai, "

Shiru haris ya ɗanyi Na wani lokaci, Yana kallonshi, shi kanshi Ya lura da irin damuwar dake atattare dashi, Duk ya rasa sukuni, ashe duk akan angel ne,

Murmushi haris ya saki tare da cewa"ka kwantar da hankalin ka, Mutumina, indai angel ce zata nemi hanyar da zaku shirya, ae itama ta damu dakai, So bana so kana tada hankalin ka, gashi ko abincin ka baka ci ba,

"Ae bana jin yunwa...." tunkan ya rufe baki Haris Ya katse shi da cewa"ƙarya kake yi, look at ur stomach, A shafe kamar Bangon ɗakin mu, " yatsina fuska Ya ɗanyi ba tare da ya kuma cewa komai ba.

"Yanzu dai, bari na ɗauko maka chicken leg ɗinka da fruit kasha, after ka gama Sai in taimaka maka ka canza uniform ɗinka" kafin haris yai yunƙurin miƙewa tsaye Danish Ya ruƙo hannun shi, Yana faɗin"Bana Jin yunwa, zan ci da anjima, Yanzu so nake in kwanta" ɗaure fuska haris yai"meyasa kake yi min haka? Ko dan saboda na damu dakai ne"? Girgixa kai yai
'Ba haka bane, just bana jin yunwa, Nayi maka alƙawarin da anjima zanci" gyaɗa kai haris yai, tare da cewa"Uniform ɗin Fa? Yakamata Ka canza na jikin ka," Yatsina fuska yai don ba ƙaramin takura shi haris yake yi ba.

rai a6ace haris yace"Na lura ba ka damu da kan ka ba, Kamar yadda na damu dakai, shiyasa ka ke ta yi min wulaƙanci, Shikenan, Zan tafi nabarka, wlh idan har baka canza kayan nan ba, ka ci abinci, kada ka ƙara tunanin zan tanka maka" yana kai ƙarshen maganar, Yaja tsoki tare da miƙewa Ya juya ya nufi gadon shi, Ya haye ya kwanta, zuciyarshi duk ba daɗi, yana matuƙar jin haushin abunda Danish ke yi mishi, Gashi Allah ya jarabce shi da ƙaunar ɗan uwansa, Shi dai yana son Danish, baya son 6acin ran shi, tun suna yara, haka yake fama da shi, Baison Cin abincin baisan hayaniya, baisan yin magana, ga nuna halin ko in kula, da yake yi musu, wani lokacin ka rasa gane kan shi kamar ba cikakken mutun ba, shi dai yafi gane ma hawa saman gadon Ya rungume pillow a ƙirjin shi.

"Haris meya faru ne naga fuskarka ta canza"? Muryar deeja ce ta katse mishi zancen zucin da yake yi, kasancewar suna fuskantar juna, Gadon da yake kwance Yana facing ɗin nata, Farkawarta kenan daga bacci, Ta yi arba dashi kwance saman gadon shi ya ƙurawa ceilling ido, sai tsoki yake bugawa,

"Haris ka yi shiru baka bani amsa ba" ta6e baki ya ɗan yi kafin yace mata"Nida mutumin ne, ina ta fama dashi ya tashi yaci abinci, ya canza uniform ɗinshi, amma yaƙiya, narasa meke damun Danish, Yafiye taurin kai da kafiya"

Mirmushin takaici deeja ta saki,"Kaine ka damu dashi ae, shiyasa yake yi maka abunda yaga dama, Tunda baya cin abincin ka ƙyale shi mana, ba cikin shi bane, idan yunwar ta addabe shi zai nema ne" girgiza kai haris yayi

"Bazaki fahimta bane, ni bazan Iya ƙyale shi ba, saboda ina zargin wani abu atattare dashi, gani nake wani abun kamar ba yin kanshi ba, Danish fa ya canza sosai, Sa6anin lokacin baya da muka sanshi, shiyasa nake yi mishi uziri, kuma gaskiya ni, Ina matuƙar son ɗan uwana, bana jin zan iya share shi, idan shi bai son ciwon kanshi ba, Ni nasani,"

Murmushin dake akan fuskarta bai washe ba tace"Haris you're so special, fiye da tunaninka, ni shaida ce akan irin ƙaunar da kake yi mishi, bama shi kaɗai ba, kowama acikin mu, kana son mu, kana bamu kulawa, kai tamkar jagora ne acikin rayuwarmu....." Tun da Deeja ta soma magana cikin sanyin murya mai daɗi, haris Ya tsare ta da idanuwanshi batare da ƙiftawa ba, saboda wani irin daɗin da yake ji, sai da takai karshen maganarta, sannan yace"Haka nake fata wata rana Danish Ya ɗauki ragamar kula da ku kamar yadda nake yi, shiyasa kika ga ina ƙoƙari don ganin na gyara mashi tunaninsa,"

"Ka yi tunani mai kyau, nima ina fata Wata rana Danish Ya canza ya zama kamar kai, tabbas zamu Ji daɗi," shiru suka yi na wani lokaci suna kallon juna. Kafin Haris yace"bakomai yafi damuna ba, face rashin batool, Deeja ya zamu yi? Sun ɗauke ta almost one month babu alamar zasu dawo mana da ita, na damu sosai, duk in na tuna da batool baki ji yadda nake ji ba, gaskiya bai kamata ace mun yi shiru ba, mutanan nan fa mugayene azzulamai, zasu iya cutar da ita, kamar yadda suka yi maku," hawaye ne kwance acikin idanuwanshi, yayin da yake yin maganar.

Cikin karyayyiyar murya deeja tace"Ae batool sai addu'a, Har ƙwara mu da aka ɗauke mu an dawo damu within weeks, amma ita fa har One month! Wlh ji nake kamar sun kashe mana ita....." bata ƙarasa maganar ba, saboda kukan da ya tari numfashinta, da sauri ta kifa Kanta saman pillow taci gaba kuka. Hankalin haris duk yabi ya tashi, muryar shi araunace yake lallashinta, yana bata haƙuri, akan tayi shiru tadaina kuka kodan saboda ƴan uwan su dake bacci kada su farka, suji suma su shiga damuwa.

Abunda basu sani ba, tunda suka fara magana angel ta farka, ba tare da ta buɗe idanuwanta ba, duk da akwai tazara atsakanin gadajensu amma tana iya jiyo maganganun da suke tattaunawa, wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke mata fuskarta, zuciyarta sai tafarfasa take yi, Tamkar zata 6allo ƙirjinta, aduk lokacin da ta tuna da batool, saita dinga jin kamar ana tunzurata akan ta ƙara dura tagar nan akaro na biyo taje ta nemo ta, ko Allah yasa ta dace, Dama fa ba haƙura ta yi ba, akwai dalilin dayasa ta dakata da kudurin nata, saboda ta lura shiga cikin prison ba abune mai sauƙi ba, dole saita yi mishi kyakkyawan shiri na musamman, kafin ta aiwatar da aikinta, can ƙasan zuciyarta kalaman tsohuwa tamira ne suka shiga yi mata yawo acikinta kanta, tarasa gane dalilin dayasa Suka tsaya mata aranta, tabbas akwai abunda take nufi game da makullan farin cikin nan, kuma tace Idan suka Cigaba da nuna ma danish wariya to wata rana zasu rasa madafar su, ko dan saboda haka dole ta nemi hanyar da zata karya alƙawarin dake a tsakaninta dashi,

numfasawa ta yi tare da ƙoƙarin miƙewa zaune hannunta ruƙe da pillow, ta ɗan juya 6angaren hagu ta kalli su Deeja, har lokacin bata daina kukan ba, haris sai aikin lallashinta yake yi, tun yana akan gadon shi har ya kai ga dawowa gefen gadonta ya zauna, tare da kai hannu yana shafa sumar kanta, daƙyar ya samu Deeja ta yi shiru, ya kwantar da kanshi gefen ta, yana leƙen fuskarta da ta yi sharkaf da hawaye, Angel tana jiyo shi yana faɗi"Hakan ma bazata ta6a faruwa ba, ki daina zancen mutuwa, inaji araina ƴar uwarmu tana araye, zasu dawo mana da ita ne" Cikin shessheƙar kuka deeja tace"bayan sun gama amfani da ita ko? Sai sunyi mata kamar yadda su ka yi mana, ko ka manta yadda aka dawo dani ne? Tae tambayar tana kallonshi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa Jawur dasu, Zuciyarshi ta karaya sam ya kasa magana

Ta ci gaba da cewa"A wulaƙance, aka dawo dani, ji lokacin da aka dawo dasu Hanna, Hada yakushin akaifa akan wuyansu, le6e duk ya bushe ya faffashe jini yana tsastsafowa, idanuwa sun jagwale da ruwan hawaye.....haris duk da bamusan me akeyi mana ba, amma munji raɗaɗin azaba ajikin mu, mun yi jinya, mun yi kuka tamkar rayukanmu zasu fita daga gangar jikin mu, Iya cuta dai ancuci rayuwarmu," tana faman jan majina ta ɗaura da cewa"Ina tsoron Awani hali za'a dawo mana da BATOOL! ita da ta ɗauki tsawon lokaci ahannun su, mugaye azzalumai Allah kaɗai yasan me su ke ƙunsa mata a yanzu haka......"

Deeja bata kai ƙarshen maganar ta ba. Sakamakon jin sautin kukan angel, A matuƙar ruɗe su ka ɗago daga saman mattress ɗin suna kallon shimfidarta, A lokacin harta duro daga saman gadonta, da gudun gaske ta nufi sashen toilet ɗinsu ta shige, damuwa ce ta bayyana akan fuskokinsu.

"Tun yaushe ta farka? da ace na sani da ban yi maganar ba, bari naje in lallashe ta, nasan dole taji raɗadi acikin zuciyarta," Deeja na yunƙurin miƙewa haris yae saurin katse ta, ta hanyar yi mata magana,

"kada kije, Ayanzu bata buƙatar kowa a kusa da ita, ganinki zai ƙara karya zuciyarta saboda kece kika yi maganar..."

"Amma tana buƙatar wanda xai lallashe ta, kana ji fa tana kuka"

"Nasani, kema yanzu kika gama kukan inata aikin lallashi, Ki koma ki kwanta, Zanji da ita" sai da ya samu ya kwantar ma deeja da hankali, kafin ya miƙe ya nufi sashen toilet ɗinsu, Har satar kallon shimfiɗar danish yai ta wutsiyar idanuwanshi ya hange shi kwance saman gadonshi, aranshi yace"Kaji haushin rayuwarka, wato baka ci abincin ba, sabbin uniform ɗin ma ba za ka sanya ba, saboda Taurin kai irin naka," Guntun tsoki yaja yayin da yake shigewa cikin toilet, tunkafin ya ƙarasa ciki ya same ta zuƙunne agaban tukunyar fulawar nan, Ta tasa ta gaba sai kuka take yi kamar ranta zai fita,

"Why angel? Wannan kukan fa da ku ke yi bazai kare ku da komai ba, Ina fama da deeja, kema kuma kin kama kuka, nasan saboda kinji maganganun da muke tattaunawa ne," a bayanta ya tsaya hannayenshi rungume saman ƙirjinshi,

Cikin shessheƙar kuka tace"Bazan Iya jurewa bane, Batool tana can Hannun fasiƙan mutanan can, Cikin

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads