Header Ads
Showing 75001 words to 78000 words out of 287659 words

Chapter 26 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1794

Ads at the middle of Article

tana karanto addu'ar ta shi daga bacci, tunawa da danish yasa tayi hanzarin buɗe idanuwanta A hanzarce ta yi wuff ta miƙe zaune tana kallon shimfiɗarshi, babu kowa asaman mattaress ɗin sai Bargonsa da pillow dinsa, hankalin ta ya yi matuƙar tashi, ta shiga tambayar kanta Ina danish ya shiga? Meyasa kowa yana a kwance saman gadon shi, sai shi kaɗai ke babu? Ko dai ya shiga toilet ne?

Ta ƙarasa zancen zucin a lokacin da take sauko daga saman gadonta, cikin takun sauri ta nufi ƙofar shige toilets ɗinsu, hannu tasa ta tura ƙofar ta shiga daga Ciki, sai da tabi kowani toilet ta bincika amma babu danish,

Dawowa tayi da sauri taje gaban gadon batool,

Bubbuga ƙafarta tayi tare da Kiran sunanta"Batool! Sister!" saboda tsiwar muryar angel hatta su Azeeza sai da su ka farka,

"Meya faru sister" muryar batool a disasashe tayi mata maganar, tashin ta kenan daga bacci, idanuwanta sun ɗanyi ja saboda bacci,

"Na duba ko'ina banga danish ba, Jiya ya kwana da zazza6i yanzu kuma na farka ban same shi ba,"

"What? Danish bai da lafiya"? Haris ne ya yi maganar tashin shi kenan shima daga bacci, Fuskarshi da alamun ruɗi don ba ƙaramin Jin danish yake ba acikin zuciyarshi,

Jinjina kai angel tayi alamar eh kafin tace"Bansan inda ya shiga ba, tun ɗazu nake neman shi" Ta shi xaune batool ta yi, idonta akan angel tace"meya faru da danish ɗin mu"? Ina ya shiga"? Ta yi tambayar tana faman yin hamma,

Javed yace"Ni dama tun jiya na lura bai da ƙoshin lafiya, kunsan halin shi idan baya da lafiya yana da juriya baya bari mu sani kodan kada mu tashi hankalin mu akanshi, Amma nasan yanzu duk inda yake yana a tare da GIANTS, zai iya yiyuwa sune suka so su ka ɗauke shi"

Batool tace"taya zamu iya tabbatar da hakan"?

Hibba tace"Idan mu ka tambayi tsohuwa zata faɗa mana inda ɗan uwan mu yake, Bari naje na sanar mata," Ta karasa maganar tare da saukowa daga saman gadon nata, da azama ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa,

Kowa yayi zugudum yana jiran tsammani, Knocking ƙopar Hibba ta yi, Almost 3 times, suka soma jin mutsu mutsun buɗe ƙopa ta cikin ɗakin,

Fitowa tsohuwa ta yi hannunta ruƙe da sanda kamar kullum dai Cikin shigar nan tata, ta gado, wato doguwar riga launin Ja,

Haɗa ido su ka yi da hibba, Cikin girmamawa hibba ta gaishe da ita, ta amsa mata gaisuwar ta ta, tare da cewa"Zan iya sanin meke faru"?

"Dama danish ne, Angel tace jiya taji zazza6i a jikin shi, yanzu kuma mun farka bamu ga ɗan uwan mu acikin mu ba, bamu san inda ya tafi ba" Hibba ce ke magana amma idon tsohuwa yana akan angel dake daga can cikin ɗakin tsaye ta ruƙe qugu a bakin gadon batool, wani irin kallo take yi mata, murguɗa mata baki angel tayi tare da galla mata harara,

Ƙayataccen murmushi tsohuwa ta saki wanda bai kai zuci ba, ta ɗauke idonta daga kan angel ta mayar dasu kan Hibba,

"Giant ne yazo ya ɗauke shi, yanzu haka danish yana a treatment room, da zarar yaji sauƙi za'a dawo maku da ɗan uwanku," tana kai ƙarshen maganarta, ta juyawa ta koma cikin ɗakin nata, taja ƙopa ta rufe,

Kowa ya ji Amsar da tsohuwa ta ba hibba, hankalin su duk bai kwanta ba, Mamaki ƙarara akan fuskar angel tace"dama har treatment room ke akwai a Cikin prison ɗin nan"

Batool ce ta bata amsa da cewa"Eh, amma bakowa ne idan baida lafiya, ake kai shi can ba, Tsohuwa ce take duba lafiyar jikin mu,'

Yau tsawon shekara ɗaya da rabi, bata ta6a jin Zancan wani treatment room ba, sai yau, kuma tun da take da su, da wuya wani acikin su ya yi koda Ciwon kai ne, wani iko na Allah, Lafiyarsu ta banbanta dana sauran Jinsin bil'adaman da ta sani, ita dai hankalin bai kwanta da Treatment room ɗin nan ba, saboda me za'a ɗauke shi daga Cikin su, maimakon tsohuwa ta bincika lafiyar jikin, Shi ne sai an wani ɗauke shi daga cikin su,

Zuciyarta duk ta karaya, Batasan a wani hali yake ciki ba, juyawa tayi tare da nufar toilet ɗinsu, Tana ƙoƙarin shiga ta jiyo muryar haris yana cewa"Ke ce silar Ciwon Danish, saboda jahilin bugun da ki kayi ma shi jiya, idan har muka rasa ɗan uwanmu, kema ki fidda rai da rayuwa" Kasa buɗe ƙopar toilet ɗin tayi Kamar wadda aka dasa ma aya

Muryar batool ta kuma ji tana cewa"Haris dan Allah kadaina wannan maganar, Angel ba ita bace silar rashin lafiyar shi ba, lafiya lou muka wuni da danish, daga baya ne Ciwon ya same shi"

Tsawa haris ya daka mata"Shut up! Dama ae kina bayanta, wa kika fara sani acikinsu? Danish tun kafin ki mallaki hankalin ki kike a tare da shi, amma saboda wata can wadda bamusan da zamanta ba, gaba ɗaya kin kwaye mana baya," yana huci yakai ƙarshen maganar,

"Dama ba ƙaunarsa take yi ba, shiyasa take son raunata shi," acewar deeja,

Ta yi niyar ta juya taje ta nakaɗa masu bugu, amma saita fasa, saboda a halin yanzu ita kanta zuciyarta ta karaya,
Buɗe ƙopar ta yi tare da shigewa Ciki, Ta jingina bayanta Jikin bango, siraran hawaye masu ɗumi suka soma gangarowa saman kuncinta,

Ta ɗauki tsawon lokaci bata motsa ba, har saida Taji motsin shigowar mutun a toilet area ɗin, Firgit ta ɗanyi tare da kai idonta kan wanda ya shiga, Batool ce a tsaye tana kallonta,

"Angel meyasa kike kuka? Ko dan saboda abunda suka ce? Bafa laifin ki bane,"

Cikin sanyin murya tace"Ba saboda su nake zubar da hawaye na ba, idan naso zanje in bubbuge su ne, Kawai ina jin ba daɗi, saboda bugun da nayi ma danish jiya, baki ji jikin shi ba jiya yayi zafi sosai, yana a cikin wani hali, kuma nasan Nice silah,"

Dafa kafadarta batool tayi"Dan Allah ki kwantar da hankalin, ki daina zubar da hawayenki, danish fa zai dawo cikin ƙoshin lafiya, tsautsayi ne kuma ya riga da ya faru,'

Murmushin takaici angel ta yi withouth sayin anything,

Saukar tafin hannun batool taji a saman fuskarta, tears ɗin da take zubarwa ta shiga goge mata,

"Ina da saurin kuka, abu kaɗan yake harzuƙa ni," angel ce ta yi maganar cikin ƙunar rai,

"Koda ace kowa zai juya maki baya, Ki sani Ina atare dake, a koda yaushe zan kasance a hannun damanki," da ƙwarin gwiwa batool tayi maganar,

Wani irin kallo angel ta ke yi mata mai nuna tsantsar so da ƙauna,

"Da ace mu tagwaye ne Iyaye na suka haifa da sai ince ke ce twin sister ɗina, saboda yadda kika damu dani, kika mayar da damuwarki tawa, Idan ina farin ciki kema kina farin Ciki, haka zalika idan ina baƙin ciki kema kina baƙin ciki, Batool you're so special, Ina roƙon Allah ya bani damar taimaka ma rayuwarku,'

Ƙayataccen murmushi batool ta ɗan saki,

Kafin tace"Muje muyi wanka, idan muka fito, zan gyara maki gashin kanki, naga duk ya hargitse," tayi maganar tana ruƙo doguwar sumar kanta, Gashin yayi tsayi sosai har ya zarce waist ɗinta ga uban yawa, yayi datti babu gyara har tashi yake yi, ita fa mantawa take yi da wani gashi akanta, Tun zuwanta kurkukun sau biyar ta ta6a wanke shi,

Cikin shessheƙar kuka tace "Na saba daddyna yake wanke mun kaina, shiyasa nake jin wahalar wanke shi da kaina, ya saba mun da komai, yanzu gashi bamu atare da shi," zuƙunnawa ƙasa tayi tare da fashewa da matsanancin kuka, da sauri batool ta zuƙunna agabanta, tana lallashinta

"Ashe dama haka rayuwar duniyar take? ni ban ta6a tunanin akwai wani lokaci da zaizo ba, wanda zanyi rayuwa ni kaɗai batare da daddy na ba, kuma ba'a cikin gidan mu ba, sai gashi yau na tsinci kaina a wata sabuwar rayuwa Cikin mutanan da banta6a yin tozali ba, duk yadda naso in jure nakasa, ina kewarka daddyna, inason naganka, nasan bada son ranka ka jefa ni cikin ruwa ba, kayi hakan ne donka ceci rayuwata, meyasa baka bini cikin ruwan ba? Ka tsaya har saida suka kashe ka'?

Natsuwa batool ta yi tana sauraron sambatun da angel take yi, da alama tafara fita hayyacinta,

Mahaifina shine sanyin idaniyata, shine komai nawa, ya gatanta ni tamkar sarauniya, Ya Allah duk wanda yayi silar tarwatsa ƙaunar dake a tsakanin zuciyoyin nan guda biyu, Ya Allah ka ƙasƙantar da rayuwarshi, ka haɗa shi da bala'e da masifa, wanda zasu hana shi runtsawa,'

Duk da batool batasan kan zancen ba, hakan bai hana zuciyarta yin sanyi ba, hawaye suka soma sintiri saman fuskarta,

Girgixa kai ta shiga yi, idanuwanta cike tab da kwalla, fuskarta tayi jawur da ita,

Kallon batool tayi Jin shessheƙar kukanta, ƙaƙaro murmushi angel tayi"meyasa kike kuka"?

Cikin muryar kuka batool tace"Saboda ke angel, ina tausayin rayuwarki"

Itama Cikin muryar kuka tace"Bani bace abun tausayi ba, kune abun tausayi, Nifa na taso ta tare da iyaye na, nasan dangina, Naje makaranta, kuma nayi rayuwar ƴan ci, Ina sanya sutura mai tsada, Inci abinci fiye da sau uku arana, Daddyna yana ɗaukata a cikin motarsa yakaini duk inda nake so, Amma kufa?....daƙyar takai ƙarshen maganar saboda kukan daya ciyota,

"Ba...tool, An cuci rayuwarku, An ƙuntata ku, an hana ku duk wani jin daɗi na duniyar nan, tun kuna yara kuka tsinci kanku acikin gidan kurkukun nan, Bakusan komai game da rayuwar duniyar nan ba, bakusan su wanene Iyayen ku ba, ku kanku bakusan suwaye ku ba, rayuwar kawai kuke yi a kurmance, mutumin da baisan mahaliccinshi ba, idan ya faɗi ya mutu yau, ya farka ya same shi acikin ƙabari Ya zaiyi? A lokacin da yasan gaskiya bayan lokaci ya qure masa, Wlh an cuci rayuwarku, ni kuma indai ina araye duk runtsu duk wuya bazan ta6a bari rayuwarku ta qare ahaka ba, koda kuwa zan rasa raina ne wurin ceton rayuwarku, xan roƙi Allah ya bani tsawon rai saboda ku............'

tana kai ƙarshen maganarta, ta kifa kanta saman gwiwowin ta, taci gaba da yin kuka kamar ranta xai fita, itama batool ɗin kukan take yi har yanzu hawayenta basu daina zuba ba
Ƙara matsawa tayi tare da ɗaura kanta saman bayan angel, su ka cigaba da yin kukan atare, sun ɗauki tsawon lokaci, kafin batool ta ɗago da kanta daga saman bayan angel,

Calmy ta furta Sunanta"Angel" a hankali ta ɗago tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta da suka raunata sosai saboda kukan da ta sha,_

"Batool kinsan komai game da gidan kurkukun nan saboda acikin shi aka raine ki, meyasa ba zaki iya yi mun bayani yadda zan fahimta ba"? Muryarta a sanyaye tayi maganar,
Girgiza kai Batool tayi tare da cewa"Angel bansan komai ba, da ace na sani, bazan iya 6oye maki ba, Ni dai tunda na taso acikinsa, a killace nake bama zuwa ko'ina, bamu san komai ba"

Jinjina kai angel ta ɗanyi tana faman matse hancinta da ya yi jawur,
"Yanzu duk acikin ku, babu wanda yasan wani abu dangane da prison ɗin nan duk irin tsawon shekarun da ku kayi acikin shi"?
Zurfin tunani batool ta shiga, ƙasa ƙasa da murya ta furta sunan"DANISH"

A ruɗe angel ta maimaita sunan"Danish? Ya san wani abu? Ki yi mun bayani pls......'

Cigaba da magana batool ta yi" Idan ma akwai wanda yasan wani abu, To shi ne, danish ne, duk da bani da tabbaci, " a matuƙar ruɗe angel ke kallonta,
"Sai dai danish bazai ta6a baki haɗin kai ba, saboda yana da wuyar sha'ani fiye da tunaninki, baida yarda, tun fil'azal balle kuma yanzu daya samu lalurar rashin son hayaniya, sai ya ƙara burkicewa,'

"Kina nufin lokacin baya Danish ba haka yake ba'?

Jinjina kai batool ta yi"Eh, daga baya ne ya koma haka, lokaci ɗaya muka rasa gane kan shi, ko bacci yake yi ya dinga furgita kenan yana sambatu, yanzu ne abun ma ya ɗanyi sauƙi,

Dafe kai angel tayi"Ni nasan koda me nake yawo danish bazai ta6a sakewa dani ba saboda ya tsane ni,"

"yana da sauƙin kai angel, sai dai yarda ce baida ita, bai yarda da kowa ba a cikin mu, tsohuwace kaɗai ya yarda da ita,"

Wani wahalallan Murmushi angel ta saki wanda bai kai zuci ba, dafa kafadar batool ta yi"ngde ssai batool, muje mu shiga wankan, idan muka fito sai ki gyara mun gashin kaina," amsa mata tayi da toh, Atare suka miƙe kowa ya shige cikin toilet,'

Bayan wasu ƴan mintuna kusan atare suka fito daga Cikin toilet ɗin lemar ruwa kwance saman sumar kansu da suka wanke, Lokacin da suka shigo cikin ɗakin a zaune suka samu kowannan su Saman Red Carpet ga kayan breakfast ɗinsu nan an kawo masu,
Giants Suna a tsaye Sun goya hannayensu saman ƙirjinsu,

Yau fa ta 6aci saboda rashin danish, Sun gaza sakin Jiki su ci abinci, Ji su ke kamar ɗan uwansu bazai dawo Cikin su ba, sanin cewa a lokacin baya duk wanda aka ɗauka zaiyi wuya adawo da shi,

babu irin lallashin da Batool batayi masu ba akan suci abinci amma sunƙi Ci, kowa sai dai ya tsakuri kaɗan kamar anyi ma su dole, ganin zasu wulaƙanta abincin yasa ta ɗauko kwandon da take ajiye abinci a cikin shi, ta kwashe rabi da kwata aciki, Ta ajiye masu shi tasan da anjima dole su 6uƙaci cin abinci, idan yunwa ta addabe su,

Bayan tafiyar su Giants, Batool ta ɗauko Comb, ta zauna saman gadonta daga gefe, tace ma angel ta zo ta zauna ta gyara mata gashin kanta,

Angel kaɗai tayi niyar gyarawa gashi, sai gasu rubina dasu Hanna, Sun jera layi suna jira ta kammala gyara mata ga shi, Suma ta gyara masu nasu gashin,

Baƙamar wahala batool tasha ba, Wurin taje masu sumar kawunan su, kowa cikinsu tubarkallah Yawan gashi gare su ga tsayi, In ka cire deeja ita kaɗaice keda gajeran gashi, amma yana da yawa cike da kanta,

Mutum biyar ta yi mawa, ta miƙa ma angel comb ɗin tace Ta gyara ma sauran Huɗun gashi idan ta kammala itama ta gyara mata nata gashin, yinin ranar abunda su ka yi ta yi kenan, hada mazan suma duk saida suka sharce sumar kawunansu, su kansu ba ƙaramin daɗi su kaji ba, da su ka gyara Sumar kawunansu.

*Boss Bature🌷✍️*

Wasa wasa Har dare ya yi ba'a dawo da danish ba, duk sun damu, kowa yana zaune saman gadon shi, ita kanta angel da bata shiri da shi saida ta damu da son sanin a wani hali ya ke ciki, kallon kowannan su ta yi"me zai hana ku kwanta ku yi bacci nasan cikin dare zasu dawo maku da ɗan uwanku,"

Batool tace"angel bazamu iya runtsawa ba, mun saba kwana atare idan har danish bai dawo ba, a zaune zamu kwana"

Ba haka angel taso taji daga gare su ba, taso ace sun kwanta bacci ya ɗauke su, ko dan ta samu damar Bincikar inda danish ya 6oye wuƙar shi,

Takun tafiya suka jiyo da sauri suka kai idanuwansu kan mutumin dake fitowa, tsohuwace ta shigo cikin ɗakin hannunta ruƙe da sanda, ta tsaya tana binsu da kallo,

Da sauri haris dasu Hannah suka sauko daga saman gadajensu su ka nufi wurinta har suna haɗa baki wurin gaishe ta, ta amsa masu fuskarta asake, kafin tace"me ya hana ku yin bacci ne"?
Atare suka haɗa baki wurin furta sunanshi" Danish, har yanzu ba'a dawo mana da shi ba, muna ta jira" ta lura da irin halin da suka shiga,

"Kamar yadda kuke kewarshi shima haka yake kewarku, kuna aranshi,"

"Amma jikin na shi da sauƙi"? Haris ne ya yi tambayar a ƙagare,

Kafin tsohuwa ta basu amsa angel ta sauko daga saman gadonta, ta nufi inda suke a tsaye ido cikin ido suke kallon kallo tsakaninta da tsohuwa,

"Muna so mu gan shi, mu kuma yi mashi ya jiki," Acewar angel

"Kada ku damu kanku, zuwa gobe danish zai dawo cikin ku," acewar tsohuwa

"Me zai hana akai mu treatment room ɗin mu duba lafiyar jikin shi"? cike da tuhuma angel ta kuma yi mata tambayar,

"Ba'a bada iznin zuwa inda danish yake ba, saboda ciwon nashi baya son hayaniya"

"Idan muka je ba zamu yi surutu ba, kawai muna so mu ganshi ne" angel ta kuma tambayarta, Hannah tace"pls tsohuwa kibari muje mu duba shi, we really missed our brother"

Girgixa kai ta kuma yi"dare yayi yanzu zuwa gobe zai dawo"

"A yanzu muke son ganin shi, kibar mu muje mana ko akwai wani dalili dayasa baki so muje ne"

"Ke da baki jituwa da shi, meyasa kika damu dashi ne"? Tsohuwace ta jefa mata tambayar, fuskarta ɗauke da wani shu'umin murmushi,

Tur6une fuska angel tayi tare da haɗe rai tace"wannan bai shafe ki ba, wai taya ma akai kikasan cewa bana jituwa da danish? Bayan wannan taya akai kikasan Halin da danish yake ciki, ta wace ƙopa kike bi ki fita daga Cikin ɗakin nan ne? Don ni bana ganin gifcinki, bansani ba ko bangon ɗakinki, kike ratsawa ki wuce, ko kuma layar zane kike yi ki 6ace,

Matashin murmushi tsohuwa ta saki, Yayin da idonta ke akan angel tace"duk yadda kika ɗauka haka ne," ta6e baki angel ta yi, su haris duk suna sauraronsu batare da wani ya sanya baki ba,

"Danish zai dawo zuwa gobe, iya amsar da zan iya baku kenan, kowa yaje ya kwanta" tana kar ƙarshen maganarta, ta juya tana dogara sanda ta shige ɗakinta tare da jan ƙopa ta datse,
"Wannan munafukin ɗakin ko menene acikinsa, wata rana saina san yadda nayi na kutsa kai

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads