Header Ads
Showing 177001 words to 180000 words out of 287659 words

Chapter 60 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1823

Ads at the middle of Article

matuƙar ruɗe suke kallonta, Wasu har sun fara matse ƙwaalla, ashe basu ji komai ba,

"Zanje naci gaba da rainon ƙannanku masu taso wa, Ku kuma Za'a canza muku sabuwar da zata cigaba da jagorantar rayuwarku, sai dai fa zaku ga banbancin domin kuwa, Ni ba komai bace akanta, bansani ba kota kawo muku ziyara....." Cikin sanyin murya danish ya bata amsa da cewa"tazo, namanta ban fada musu bane"

Tsohuwa tace"Bakowa bace face TSOHUWA ZAFREEN! Ita ɗin takasance ɗaya daga Cikin shuwagabannin dake ruƙe da gidan kurkukun ƙaddara! Kaifi ɗaya ce, zuciyarta bata da banbanci da dutse, a rashin tausayi Cikin kaso ɗari tana da casa'in da tara....." tashin hankalin da ba'a sama shi date!! Tuni gwiwowinsu sun jima da sagewa, Zuciyarsu ta tsorata sosai, tunkafin ma suyi toxali da tsohuwa zafreen, Kusan atare ƴan matan suka zube saman gwiwowinsu, banda angel da mazan,

Sai kuka suke yi suna rokonta akan karta bari akawo musu tsohuwa zafreen, Idan ma yazama dole ta rabu dasu to ta taimaka ta hana akawo musu ita, abarsu suyi rayuwarsu batare da kowa ba, zasu Iya kula da kansu,"


Cikin raunin murya tsohuwa tace"Ae ni bani da ikon da zan hana tsohuwa zafreen zuwa wurinku, Saboda A matsayi ko ƙafarta ban kama ba, wani abun ɗaure kai ma, Ita da kanta ta nemi da abata sashen ku don taci gaba da kula daku, saboda ita ba cikin ma'aikata take ba, Shugaba ce Ra'ayin kanta ne zuwa wurinku, kai Danish ae ka ganta, Tana da babban muƙami, agaban rigarta taurari uku ne, idan baku san ma'anarsu ba, bari in sanar maku, duk wanda kuka gani da Star uku agaban rigarshi To shugabane na gidan kurkuku, A mataki na ma'aikatan prison daga star ɗaya yake farawa zuwa star biyu kafin ka samu taurari ukun nan, Idan kuka duba Jikin rigata babu star ko ɗaya saboda bani da wani matsayi agidan kurkukun ƙaddara, Raino kawai nake yi"

Cikin shesshekar kuka su parveen suke faɗin wayyo Allah mun shiga uku mun bani mun lalace, tsohuwa dan Allah kada ki rabu damu wlh zamuyi biyayya, zamu biki sau da ƙafa, Tun yanzu mun gane kuskuranmu....."

haƙiƙa sunyi matuƙar bata tausayi sai dai ba yadda zatayi, haka Allah ya riga daya ƙaddara musu rayuwarsu, amma fa zasu ci baƙar wahalar da ba lallai bane su Iya rayuwa, Angel duk tafi su shiga damuwa, ita gani take hada ƙarin donta ƙetare Iyakar data faɗa mata na cewa duk ranar da ta kuskura ta yi leƙan asiri to bazasu sake ganinta ba, amma kuma ae koda ta dura tagar bata ga komai ba, sai ma wahalar da tasha, sai dai idan ko dama ƙarya tayi mata data faɗi hakan tun da ta saba canza magana," numfasawa tayi tare da kallon tsohuwa tace.

"Idan ma saboda sa'in sar da muke Yi atsakanina dake ne yasa zaki tafi ki barmu, ina mai baki haƙuri, zan ma iya zuƙunnawa saman gwiwowina akan in roke ki, dan Allah badan halin mu ba, kiyi haƙuri ki cigaba da zama damu....." da sauri tsohuwa ta ɗaura idanuwanta kan wadda tayi maganar, tayi mamaki ganin angel ce, idanuwanta sun Cicciko tab da kwalla duk da basu zuba ba,

Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta tuntsire da ita, Jikinta har jijjiga yake yi saboda tsabar yadda take yin dariya kamar zata kife ƙasa, Duk suka ƙura mata luhu luhun idanuwansu da suka canza launi saboda kukan da suka sha,

Daga bisani tsohuwa ta dakata da yin dariyar tana kallon angel tace"Unaisa kenan, Ban ta6a tunanin zaki Iya furta hakan da kanki ba, lallai kun tsorata da tsohuwa zafreen tunkafin zuwanta, to agaskiya dai ba taimakon da zan Iya yi maku, shawarar da zan baku shine, koda gigin wasa kada ku kuskura tana magana kuna kallon cikin idanuwanta, na farko kenan, sa'an nan, ba'a sa'insa da ita, musamman ke unaisa, Kina da gangancin ya6awa mutun magana, ina mai gargaɗin ki da ki kiyayi harshenki, wurin Yi mata magana, abu na ƙarshe da zan fada maku, idan tana awuri ba'a tsegumi, ko ƙyafcen ido, da yafu ce, Har kisa tana iya yi, idan har akai hakan agabanta, idan har kuna son ku ci ribar zaba da zafreen, to kuyi mata biyayya tamkar zaku bauta mata, idan ta bada Umarni, Jiki na rawa kuyi gaggawar yi mata shi, babu musu, idan har baku kiyayi abunda na fada muku ba, tabbas zaku yiwa mutuwar ku kutse tunkafin lokacinku yayi, " wani irin wahalallan yawu kowannan su Ya haɗiya, wasu har sun fara jin zazza6i ajikinsu, sun tsorata da tsohuwar nan da za'a kawo musu,

"Ba lallai bane, kullum ku dinga ganinta, kamar yadda kuka saba ganina jefi jefi, saboda ita ɗaya ce daga Cikin shuwagabannin kurkukun, zaima yi wuya a sati ku ganta, Zata iya ɗaukar tsawon kwanaki bata leƙo ku ba, Ta inda zaku samu sauki kenan, domin kuwa baiyanarta ba alkhairi bane......"

Muryar su azeeza ce ta katse mata hanzarinta,

"Tsohuwa yanzu shikenan tafiya zakiyi kibarmu? Fuskokinsu sharkaf da hawaye hada majina,

Daƙyar ta ƙaƙalo murmushi akan fuskarta tace"ƙwarai kuwa tafiya zan yi in barku, babu tabbacin zamu ƙara haɗuwa, ni dai shawarata agare ku shine, Ku daina gaba da junanku, ku hada kanku, kuma ku kawar da idon ku ga duk wani abu da ɗan uwanku Danish zaiyi, ku daina fushi dashi, hakan zai iya haddasa mashi matsala acikin zuciyarshi," ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin ta ɗago suka haɗa ido da angel,

"Jikata unaisa, Baki ya mutu, tsohuwa zata tafi ki huta da ganin mummunar fuskarta, meyasa banga kina farin Ciki ba"? Tai tambayar tana sakin ƴar dariya, angel kuwa fuskarta aɗaure take, ta tsuke baki, baiwar Allah damuwa ce danƙare akan fuskarta, " a hankali tsohuwa take buga sandar hannunta, wanda ke nuni da cewa akwai wani abu da hakan ke nufi, sai dai basu fahimci dalilin dayasa take bubbuga sandar ba, dakatawa ta ɗanyi still idonta na akan angel taci gaba da cewa

"Ƙaramarsu babbarsu, ki cigaba da taimakon su kamar yadda kika saba, Inajin daɗin hakan sosai, haƙika zuwanki cikin rayuwarsu tamkar bayyanar haske ne acikin duhu, ki haɗa ka ƴan uwanki, kada ki bari wani abu ƙalilan ya shiga tsakaninki da waninsu, kuso junanku, ku sama ma kanku farin ciki, duk runtsi duk wuya kada kuyi kuskuren da zaisa ku raba kawunanku, idan har kuna son cimma burinku, Inaso ku ɗauka cewa ku kamar

*MUKULLAI NE NA MABUƊIN WATA ƘOFA GUDA ƊAYA WADDA ZATA SAMA MAKU FARIN CIKI ACIKIN RAYUWARKU, TABBAS KUNA DA DAMA*

Amma fa dole sai kun yarda da kanku, kun haɗa hannu, domin kuwa Ƙofar farin cikin nan tana atare daku, Sa'annan

*KU NE MAKULLAN DA ZAKU BUƊE TA*

Nasan a yanzu bazaku ta6a fahimtar kalamaina ba, sai nan da wani lokaci, Aranar da kuka fita hayyacinku, wasu ma basa araye, To awannan lokacin ne zaku gane me nake nufi............"

Tunkafin ta ƙarasa maganarta, Da ƙarfi Ta buga sandar hannunta, wata irin ƙura ta mamaye idanuwansu, Kafin wani lokaci hayaƙin ya washe, Sai dai koda suka buɗe idanuwansu, ba su yi nasarar samun TSOHUWA TAMIRA ba, Ta riga da ta tafi, ta barsu da kewarta, sun shiga ruɗanin maganganun data faɗa musu, ga fargabar da suke aciki na baƙuncin TSOHUWA ZAFREEN, Lamarin yayi matuƙar gigitasu, yinin ranar da jimamin rashinta suka Yi shi, babu wanda bai matse kwalla ba acikinsu, Sunyi kuka tamkar ransu zai fita, sunyi danasanin duk wani abu da ya shiga atsakaninsu da ita, dama ance sabo turken wawa, hatta angel da tafi kowa tsanar tsohuwa a yau Saman gado ta haye ta rungume pillow tana matsar kwalla, fuskokinsu sunyi jawur gwanin ban tausayi, babu wanda yai kwakkwaran motsi acikinsu, kowa yana tuna irin rayuwar da suka yi da tsohuwa Tamira, Har giants suka kawo musu abinci basu motsa ba, badan Allah yasa parveen tayi tunanin kwashe musu abincin Cikin kwando ta ajiye musu shi ba, da sun yi asarar shi, duk irin zumuɗin da suke yi na sabbin kayan da aka kawo musu babu wanda Ya ta6a su, Kai hatta akwati nan basu ishe su kallo ba.

Sai da yunwa ta fara kai musu karo tukunna suka fara neman abinci, A lokacin dare ya nutsa Haka suka zazzauna saman dining carpet dinsu, parveen ta ɗauko musu abincinsu, Yadda kasan waɗanda akayiwa dole, Suna cin abincin suna matsar kwalla, Musamman parveen idan ta cunkusa Naman abaki, tana tauna Tana ambaton sunan tsohuwa, shikenan ta tafi tabarsu, Yanzu ya zasuyi, Bayan sun kammala cin abincin, babu wanda yai tunanin yin wanka, ga jikinsu sai tsami yake yi, ahaka suka haura saman sabbin gadajen nan kowa ya kwanta, zuciyoyinsu cike fal da jimamin rashin tsohuwa Tamira, da kuma fargabar irin rayuwar da za su yi da tsohuwa Zafreen, ɗaya daga Cikin shuwagabannin kurkukun ƙaddara, suna daga kwance suke Yin fira, Haris yace daga Jin sunanta babu imani atattare da ita, Ni inaga toilet zan koma da kwana, zaifi mini kwanciyar Hankali, ashagwa6e azeeza tace Ni dai Allah ƙarƙashin gado zan dinga 6oyewa duk idan naji takun tafiyarta"

parveen tace nidai in har bazata hanani cin abinci ba, babu ruwana da shiga huruminta, zanyi mata biyayya kodan in tsira da Ciki na," deeja kuma tace"Allah ya jiƙanmu badan mun mutu ba," rubina tace"Ai kawai mu ɗauki shawarar tsohuwa mu bita sau da ƙafa, Har Allah ya kawo lokacin da zamu Rabu da ita," dogon tsoki javed yaja mai sautin gaske kafin yace"Kunga surutun ya isa haka, pls kowa ya lallashi zuciyarshi, Ku rungumi pillows dinku, aja bargo a lullu6e jiki, kowa Yae bacci, zuwan tsohuwa Zafreen ba fashi," Sai da duk suka gama surutansu, tukunna Angel ta soma magana muryarta adisashe tace"In sha Allah, babu abunda zai faru, koda tazo bazata Iya cutar damu ba, Ni babu bawan da nake jin tsoronshi aduniyar nan, In ba mahalicci na ba, saboda nasan babu wanda ya isa ya cutar dani face da izninsa, Allah shine maganin duk wani mugu mai kafirar zuciya, kafin ayi azzaluman kurkukun kaddara Anyi waɗanda suka fisu, irinsu fir'auna yanzu duk babu su a doron duniyar nan sai dai kajisu a tarihi,' Tunda angel ta ambaci sunan fir'auna, nan fa suka addabeta akan ta basu tarihinshi suna son Sanin wanene shi, tace musu su yi haƙuri yanzu kanta ke yi mata ciwo, amma ta yi musu alƙawarin idan taji sauƙi zata basu tarihin Annabi musa (AS), bayan haka saida ta kwantar musu da hankulan su, kafin ta samu bacci ya ɗauke su,


Lokacin da dare Ya ratsa, Angel ta sauko daga saman gadonta, zuciyarta duk ba daɗi, ahaka ta lalla6a ta nufi toilet ɗinsu, ba don komai ba, sai don ta duba awani hali furen batool yake aciki, Tana sanya ƙafarta Cikin toilet din ta hango furen batool da alamun lemar ruwa ajikinshi, kamar zufa haka ya tsastsafo ajikin ganyen shi, nan fa hankalinta ya ɗan tashi, da sauri ta ƙarasa inda tukunyar fulawar take, Ta zuƙunna tare dakai hannu tana shafa Jikin ganyen shi, sosai ruwan ke tsastsafowa, Duk saita rasa sukuni, ta shiga damuwa, muryarta na ɗan rawa ta soma faɗin"dan Allah batool ki daina kuka, Ina atare dake, ban manta dake ba, kina araina, kullum ina yi maki addu'a, Duk da nagaza zuwa in taimake ki amma nasan cewa Allah yana atare dake kuma zai kare ki ne,"

cikin shessheƙar kuka angel take lallashin Furen, Batasan cewa Danish Yana tsaye bakin ƙopar toilet ɗin ya la6e yana kallonta, tsananin tausayinta ne ya kama shi, sai dai baijin zai iya zuwa ya lallashe ta, saboda alƙawarin daya ɗaukar mata, abunda baisani ba ita kanta, A halin yanzu a matuƙar ƙagare take da son su shirya da juna don ba ƙaramin azabtuwa take yi ba,

Shiru ta ɗanyi tana ƙarewa furen kallon, ganin Ya daina tsastsafo da ruwa ajikinshi, wani iko na Allah sai taga furen ya kwanta cikin ƙasar tukunyar, alamar mamallakin shi bacci yake yi, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, aranta ta raya cewa Batool taji lallashin da take yi mata shiyasa tayi shiru ta kwanta tana bacci, A hankali ta mayar da idanuwanta kan furen daddynta, tafi yarda dana batool akan nashi, saboda shi bata da tabbacin yana raye koya mutu, Jikin furen yayi kore shar dashi, kuma iccen yaɗan miƙe ba kamar lokacin farko da ya fito a lanƙwashe ba, Ziraran yatsun hannunta ta ɗaura asaman furen daddynta tare da shafa ganyen shi, a fili ta furta I wish kana araye daddyna, har yanzun kana nan acikin zuciyata, ba abinda ya sauya daga ƙaunar da nake yi maka, I luv u so much, zan cigaba dayi maka addu'a kaida batool ɗina da kuma ƴan uwana prisoners, Alƙawarine na ɗaukarwa kaina,"

murmushi tasaki tana faɗin"Har na tuna lokacin da na ƙala maka sharrin cewa kai ba mahaifina bane, ɗan yankar kaine, aranar kasha bugu wurin ƴan ƙato da gora, kuma duk da abunda nayi maka hakan baisa ka guje ni ba, saima ka ƙara ƙaunata, ashe babu rabon xamu ƙare rayuwarmu atare.....haka na dinga burin in zama house wife, ashe da rabon in zama prison wife, Gidan hutun da nake burin inyi aure, har ina faɗa ma aunty aneelerh zan auri hamshaƙin mai kuɗi saboda masu aiki su dinga yi mini hidima ina daga kwance, sai gashi na ƙare agidan kurkukun ƙaddara, wayyo Allah na, babu daddyna babu aunty aneelerh da uncle uzair, babu mommy adamana da uncle abdallah, babu makaranta, babu house wife, duk waɗannan burinkan sun tashi a tutar babu....."

daƙyar ta ƙarasa yin maganar saboda kukan da yafi karfinta, ta kifa kanta saman gwiwowinta taci gaba da kuka, tana fadin nayi danasani daddyna ka yafe mini, wlh ina matuƙar ƙaunarka, dama saida ka fada mini cewa bani da tamkarka a duniyar nan yanzu na shida hakan.....'

Duk wannan suratan da take yi akan kunnan Danish, Ya ɗan jingina kanshi jikin ƙopar toilet ɗin, Ya natsu yana sauraronta, Hakanan taji aranta kamar akwai mutun abayan ta, a hankali ta ɗan dago da kanta, tana ƙoƙarin juyawa ta kalli bayanta danish yai saurin fita daga Cikin toilet din ya tsaya daga waje, Yana faman sauke ajiyar zuciya,

Baiyi tsammanin ta biyo shi ba, Sai dai yaji ta ambaci sunan shi,

"Danish"! Kasa juyawa baya yae don ya kalleta, duk yabi ya kama kanshi,

"Shine kana ji inata kuka ko kazo ka lallashe ni" Yayi mamakin jin abunda ta ce, cije lips ɗinsa yae kafin yace"Saboda me zanzo in lallashe ki? Ko kin manta alƙawarin dana ɗaukar miki? Batare daya juyo ya kalleta ba, yayi maganar,

"Meyasa kake bibiyata? Nasan saboda ni kazo bakin ƙopar toilet din nan ka tsaya, Allah kaɗai yasan tun lokacin da kake kallona, kaga kuwa Alƙawarin Ya jima da karyewa,"

girgiza kanshi ya ɗan yi tare da cewa"bana sa6a alƙawari, idan kin manta bari in tuna maki, kin ce kada na kurkura na ƙara hada ido dake kinaso in nisanta kaina agare ki, Tabbas nazo bakin ƙopar toilet din kuma na kalle ki amma ban bari mun hada ido ba. Hope kin fahimta yanzu ban karya miki alƙawarinki ba, Tun da bamu haɗa ido da juna ba kuma banzo kusa dake ba,"

Harara ta shiga jefa ma bayan shi, kamar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, wani irin kewarshi take ji kamar tae hauka, tayi danasanin sanya shi ya ɗaukar mata alƙawarin nan, ta manta cewa Prisoners basu Iya karya alƙawari ba, ta inda suka banbanta da mutanan dake rayuwa awaje kenan, majority dinsu basa ƙarya kuma basu Iya gulma ba, musamman DANISH!

Takaici ne ya isheta, Can dai tace"Idan nace na fasa alƙawarin fa"? Danish ya bata amsa da cewa"Idan kin fasa Ni bansa fa, bazai ta6a yiyuwa ba" yana faɗin hakan Ya wuce cikin dakinsu yabarta a tsaye tana faman cizon le6enta,

Daga bisani ta gyaɗa kai tare da wuce wa ta nufi cikin dakin, a kwance ta same shi saman gadon shi ya rungume pillow, ta6e baki tayi kafi ta nufi nata gadon ta haye ta zauna daga tsakiyarshi ta ɗaga hannayenta sama tana jera addu'o'i, Cikin harshen larabci,

ta ɗauki tsawon lokaci daga bisani ta shafa hannayenta saman fuskarta, kafin ta gyara kwanciyarta, Sai da ta lumshe idanuwanta, Zuciyarta ta soma tariyo mata maganganun da tsohuwa ta faɗa musu kafin tafiyarta, tabbas akwai wasu kalamai da tayi aciki waɗanda suka ɗaure mata kanta, ta kasa fahimtar inda suka dosa, Duk irin kaifin basirarta, ta gaza gano menene tsohuwa take nufi, da tace musu su dauka cewa su makullaine da zasu Iya buɗewa kansu ƙopar farin ciki, tayaya kenan? daƙyar ta samu bacci ya ɗauketa a daren ranar,!

Ko a washe garin ranar babu wanda ya sanya sabon uniform ɗinshi acikinsu, damuwar rashin tsohuwa ta hanasu sukuni, ga fargabar zuwan tsohuwa Zafreen, da kuma new prisoners, daga Sunji motsin ƙopa a firgice suke kallon ƙopar, don suga wanane, a ƙarshe sai su ga bakowa, Kunnuwansu ne kawai suke Jiyo musu hakan, sakamakon sanya rai da suka yi, wasa wasa yau har tsawon 2 weeks da tafiyar tsohuwa babu wani sabon Labari, ta ko'ina shiru kake ji, su kaɗai suke rayuwarsu, hankalinsu har ya ɗan kwanta don a tunaninsu, An ƙyalesu ne su yi rayuwarsu su kaɗai, Bakomai yafi ɗaga musu hankali ba, face rashin batool don a lissafinsu yau Wata ɗaya kenan babu Ƴar uwarsu acikinsu, Ba'a dawo musu da ita, har sun fara fidda rai da sake ganinta 🥺

*PRISONERS💔*

Yau tun da sassafe Angel da hanna suka taimaka ma ƴan uwansu mata wurin gyara sumar kansu, gwanin ban sha'awa kowa saida suka wanke mashi sumar kanshi, suka gyara musu ita, su kansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba, ganin yadda sumar kansu tayi kyau ga laushi da kyan gani a ido, ga wani irin ƙamshi da gashin nasu yake fitarwa mai daɗin shaƙa, Bayan Sun kammala gyara ma su azeeza, Hanna da angel suke koma toilet, saboda su wanke nasu gashin kan, sai da angel ta kammala wanke ma hanna, ya rage saura ita, duk yadda hanna taso ta wanke mata gashin kanta, hakan ya faskara, saboda uban yawan dake gare shi, Gashi ya nannaɗe yadda kasan taliyar indomi, Tun tana nish tana ƙoƙarin tattaro gashin kan Angel, kamar hannunta zasu 6alle, a ƙarshe data ga abun yafi ƙarfinta, sai ta fita tabar angel acikin

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads