Header Ads
Showing 99001 words to 102000 words out of 287659 words

Chapter 34 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1808

Ads at the middle of Article

Angel Amadadin danish, muna matuƙar yi maki godiya, bamu ta6a tsammanin zaki iya taimakon shi ba, a lokacin da kika nemi alfarmar mu baki dama, Sai gashi kin bamu mamaki, Ta silarki danish ya fara wartsakewa, tabbas ke ɗin alkhairi ce agare mu, Kuma yakamata Gaba ɗayanmu mu fahimci cewa angel masoyiyarmu ce ba maƙiyiyar mu ba" ya ɗan dakata da yin maganar yana kallon fuskokin sauran ƴan uwan nashi, kafin yaci gaba da cewa"Idan har muka yi ma angel biyayya zamu koyi abubuwa da dama awurinta wanda bamu Iya ba, zata wayar mana da kanmu, kuma zata ɗaura mu akan hanyar dai dai, Amma fa shawara ce nake bamu muyi tunani," yakai ƙarshen maganar yana jira yaji amsar da zasu ba shi,

Deeja ce tace"Amma ae tsohuwa tace mana kada mu yarda da ita, mu daina sakewa da ita, zata gur6ata mana tarbiyarmu ne, kuma tana yi mana ƙarya nidai gaskiya bazan yarda da angel ba, " tayi maganar tana maƙe kafaɗarta, maimakon angel taji haushin maganar deeja, Saima ta saki murmushi saboda ta lura hada quruciya ke ɗawainiya da ita,

"maganar da Javed ya faɗa gaskiya ne, Angel masoyiyarmu ce, kuma komai take yi mana tana ƙoƙarine don taga mun dawo akan hanyar dai dai, Ina roƙon duk wani dake ƙyararta acikinmu ya ajiye makaman yaƙin shi, yazo mu rungumi juna, faɗa ba namu bane," a tsanake batool takai karshen maganarta,

"Silar angel, danish ya samu sauƙi, bashi kaɗai ba, Tun jiya da angel ta raira mana waƙar nan mai daɗi da sanyaya zuciya, gaba ɗaya jikin kowannanmu yayi sanyi,......" dariya angel tayi jin abunda azeeza tace,

"Ba waƙa bace, Karatun al'qur'ni ne mai girma, " cike da mamaki suka maimaita kalmar"Karatun al'qur'ani mai girma" Hanna tace"menene ma'anar hakan? Ko zaki iya fahimtar damu"? Tayi maganar a ƙagare da son Jin amsar da angel zata basu,

Ƙoƙarin buɗe baki tayi da niyar ta ba Hanna amsar tambayarta, Sai dai kafin tayi yunƙurin yin hakan, Suka Jiyo Motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, Nan fa hankalinsu gaba ɗaya ya koma akan ƙopar ɗakin,

Fitowa tayi daga Cikin ɗakin tana dogara sanda, Fuskarnan a tur6une babu walwala acikinta, da sauri Su hanna suka Nufe ta, Cikin girmamawa suka gaishe da ita, babu yabo babu fallasa ta amsa masu,

Parveen tace"tsohuwa Yunwa muke ji, Giants sun kawo mana abinci, A lokacin bamu farka daga bacci ba, har suka tafi da shi"

Jinjina kai tsohuwa ta ɗanyi tana bin fuskokinsu da kallo, Su kansu sun lura da canjin dake atattare da ita, kamar wani abu na damunta, Hanna tace"tsohuwa Baki da lafiya ne? Naga kamar bakya Acikin walwala," sai lokacin tsohuwa ta buɗe baki tace" kunyi kuskure da ku ka bari giants suka juya da abincin nan, ai kunsan basa wasa da lokaci, meyasa baku farka daga bacci ba har suka tafi? Bayan kunsan cewa Ba dawowa zasuyi ba, idan har suka tafi dashi"!

Muryar Parveen tamkar zata fashe da kuka tace"yanzu shikenan bazamu samu abinci ba yau"? Idanuwanta suka cicciko da ƙwalla,

angel dake acan tsaye ruƙe da qugu, ta tunkari inda suke, agaban tsohuwa ta tsaya tare dacewa"Irin ƙaunar da kike masu kenan? ashe uwa zata Iya barin ƴa'ƴanta da yunwa? Alhalin ita tacika cikinta ta ƙoshi! Waye bai kuskure rayuwa? Yin bacci ya zama laifi kenan? Inbanda rashin lissafi taya mutumin dake bacci zai zama mai laifi? Meyasa su giants ɗin da suka zo basu ajiye mana farantan abincin ba, su sai su tafi idan yaso aduk lokacin da muka farka sai mu ci, Amma saboda tsabar zalunci shine suka tattara kayan abincin suka tafi dashi, Anya kuwa tsohuwa? Cike da tuhuma takai ƙarshen maganar tana kallon fuskar tsohuwa, ta tsareta da waɗannan Jagwalallun idanuwan nata,

Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Haka dokar Aikin Giants suke! Lokaci gare su, basa wasa da aikinsu, idan suka kawo abinci suka ga babu wanda yazo yaci zasu kwashe ne su tafi dashi," wannan itace amsar da tsohuwa taba angel,

Mamaki akan fuskar angel tace"Wannan wata irin dokace mara kan gado mara tsari? Wannan ae horo da yunwa ne! Abincin ma da sau ɗaya ake bamu shi a rana, mun ƙoshi bamu koshi ba wannan ba damuwarku bace, Shine kuma harda wata dokar in an kawo abinci bamu hallara ba, za'a juya dashi? Me hakan ke nufi? Wai mu me kuka ɗauke mu dabbobi ko me? A harzuƙe angel tayi maganar,

Wata irin gigitacciyar tsawa Batool ta daka ma angel, gaba ɗaya saida kowa ya razana hatta danish dake a kishingiɗe saman gadonshi saida ya firgita ya nemi zaucewa,

A matuƙar ruɗe Angel ke kallon batool, ta ɗaure fuska tamkar ba ita ba, Cikin fushi ta soma magana
"Yakamata ki kiyaye harshenki aduk lokacin da zakiyi magana da tsohuwa, don me zaki dinga yi mata magana a gadarance? Babu tausasa harshe? Idan ma kina son shiga tsakaninmu da ita ne, Inaso ki sani bazaki ta6a yin nasara ba, ita ɗin uwace agare mu kuma bazata ta6a iya cutar damu ba......" ba angel ba, hatta su haris sai da suka sha Jinin jikinsu, Jin yadda Batool ke magana a faɗace abunda bata ta6a yi ba,

Muryar angel adisashe tace"Batool! Yau keda kanki kike Yi mini tsawa! Saboda kawai ina son ƙwato maku haƙƙinku da aka tauye....." kafin takai ƙarshen maganarta, Javed ya dakatar da angel ta hanyar ɗaga mata hannunshi"Is enough! Kawai kiyi mana shiru, Kina so ne, Ki shiga tsakaninmu da ita, babu ruwanki da rayuwarmu, Ki barmu a yadda kika ganmu, haka muka saba rayuwa, bin dokar kurkuku wajibi ne agare mu prisoners" wani irin shu'umin murmushi tsohuwa ta shiga saki Nan da nan walwalar fuskarta ta dawo Jin yadda Suke Goyan bayanta, ashe har yanzu Hayaƙin sihirinta na aiki yadda ya dace, ta ambaci hakan acikin zuciyarta,

Tuni idanuwan angel sun Ciko tab da kwalla, tsabar baƙin Ciki Ya hana ta ƙara cewa komai, Juyawa tayi a fusace ta koma saman gadonta, Ta zauna tare da ruƙo pillow ta rungume a kirjinta,


Kallonsu tsohuwa tayi da alamun farin Ciki akan fuskarta tace"Ku cigaba da yi mun biyayya ƴa'ƴana, albarka zata tabbata akanku, " muryar parveen a ƙule tace"Abincin fa"?

Tsohuwa ta bata amsa da cewa"Ku jira ni, Ina zuwa" ta ambaci hakan tare da juyawa ta shige Cikin ɗakinta, baka iya hangen komai ko ka leƙa sai duhu,

Badajimawa, Sai ga tsohuwa ta fito hannunta ɗaya a ruƙe da Kwandon kayan marmari, Miƙa ma Su tayi" Ku je kusha, Kafin zuwa gobe zaku samu abinci" Hannunsu har kerma yake yi wurin kar6ar Kwandon daga hannunta,' Juyawa tayi tana dogara sanda ta koma Cikin ɗakinta, tare da jan kopa ta datse,

Ita dai angel sam bata yarda da kayan marmarin da tsohuwa ta basu ba, Cike fa da kwando, manyan apples ne tare da damin ayaba," a kalla kowa zai samu apples uku, da Ayaba Uku, Batool ce ta rarraba masu kayan marmarin kowa ya kar6a yana sha, koda ta miƙa ma angel hannu tasa takar6a amma bata sha ba, A ƙarƙashin pillow ɗinta ta 6oye su, tana jira taga idan sun kammala sha batare da wani abu ya faru dasu ba, itama sai tasha, Har batool sai da tayi mata magana akan bazata sha ba, tace mata ba yanzu zata sha ba, Sai zuwa anjima,

Tun da suka kammala Cin apples ɗinnan da ayaba, wani irin matsiyacin bacci ne yazo masu, lamarin ya ɗaurewa angel kai, Ganin su kwakkwance A ƙasa suna bacci, kamar waɗanda suka Sha kayan maye, Juyawa tayi da sauri tana kallon gadon danish, cike da fargabar kada ace shima baccin ya ɗauke shi, idonshi biyu ta same shi, ya kwantar da kanshi saman pillow, babu alamun bacci attare dashi, Su biyu suka rage idonsu biyu,

Tabbas tafara zargin Kayan marmarin da tsohuwa ta basu ne ya sanya su yin bacci, da yake ita da danish basu sha ba, shiyasa bacci bai ɗauke su ba, ko meyasa tayi masu haka? Kodan kada su ji yunwa ne"?

"Meyasa ba zaka sha ba"? Tayi tambayar tana kallon danish, ganin ya ajiye nashi apples ɗin a gefenshi,

Cikin sanyin murya ya amsa mata da cewa"bana ra'ayi, zuwa anjima xansha" ya ƙarasa maganar, tare da miƙewa zaune, ya zuro da dogayen ƙafafuwanshi ƙasan gadon kafin ya yunƙura ya miƙe tsaye, Har yanzu jikin nashi babu ƙwari, shiyasa tun ɗazu ya gaza saukowa daga saman gadon,

Daƙyar yake ɗaga ƙafar yana tafiya, Ji take kamar taje ta taimaka mashi sai dai batasan tana kusanta kanta dashi,

Tafiya yake yi yana waiwayon su Haris dake baje a ƙasa suna sharar bacci, sam bai kawo komai aranshi ba, Shigewa Ƙopar toilet ɗinsu yayi, Sai da ya 6ace ma ganinta tukunna ta ɗauke idonta daga kanshi, Cike da fargabar kada ya raunata kanshi, tun da ba ƙoshin lafiya gare shi ba,

Tsawon lokaci da shigarshi cikin toilet ɗin, ta Lumshe idanuwanta tare da kishingiɗawa, da niyar ta ɗan runtsa itama, Takun tafiyar mutun tajiyo acikin kunnata, tana buɗe ido ta fasa wata irin gigitaciyar ƙara tare da sanya hannu ta rufe idanuwanta, Jikinta na kerma, A matuƙar ruɗe Ya koma Cikin 6angaren toilet ɗin nasu, Ya la6e abakin ƙopa yana leƙen ta,

Abunda ya faru Lokacin data buɗe ido, Karaf idanuwanta suka sauka akan Surar danish, Ya fito naked babu sutura ajikinshi, Wannan ne yasa tayi matuƙar firgita, Jikinta ya hau kerma, dole ta ruɗe saboda halittar dake gare shi, Dogone sosai komai Na jikinshi ba ƙarami bane, shi kuma tsawar da tayi ne yasa shi gigicewa ya juya aruɗe ya koma sashen toilet ɗin, Yana leƙenta,

Ƙanƙame jikinta tayi ta gaza motsawa, tayi matuƙar tsorata, ranta ya 6aci sosai batare data buɗe idanuwanta ba, taci gaba da surfa mashi masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba, sai da ta gaji da zazzaga mashi masifa tukunna ta yi shiru tana faman huci har lokacin bata buɗe idanuwanta ba,

Jin yayi shiru bai ce mata komai ba, yasa ta sassauta muryarta tare da cewa"Go back, I don't wanna see you naked, if you need something, you should ask me to give it to you"

a ƙule tayi maganar, don ba ƙaramin haushin sa taji ba, ƙato da shi zai fito babu kaya ajikinshi, yanzu da ace idonsu Batool biyu ba bacci suke yi ba, duk haka zasu ganshi, tarasa gane wani irin mutunne shi, duk da tana yi mashi uziri na halin da yake Ciki na rashin lafiyar da take tunanin ɗaura mashi ita akayi, shiyasa ya zama wani sauna dashi,

Kasa kunne tayi sosai don ta samu damar jin me yake ce mata, magana yake yi mata akan ta miƙo mashi bargonshi, yana so zai lullu6e jikinshi,


Sai lokacin ta fahimci cewa, Ya wanke kayanshi, dama haka suke Yi idan suka wanke kayansu, sai su sanya bargo su lullu6e jikinsu, maimakon tunkafin ya shiga cikin toilet ɗin ya tafi da bargon shine bai tsaya ya ɗauka ba, yanzu gashi yasata kallon haramun, ta ambaci hakan acikin zuciyarta,

"wait, I will hand it to you ka koma toilet" amsa mata yayi da toh, bayan wasu daƙiƙai, ta ɗan zame tafin hannunta daga kan fuskarta, ta saci kallon Hanyar toilet ɗin, Ganin babu shi yasa ta yi saurin saukowa daga saman gadonta, takai hannu saman nashi gadon ta ɗauko bargonshi, Ta nufi bakin door ɗin farko ta tsaya tare da ɗaga murya tace"Ga bargon" zuro mata da hannun shi yayi, maimakon ta miƙa mashi bargon saita tsaya tana kallon kyawawan yatsun hannunshi, sai kace bana ɗan bil'adama ba, saboda tsabar kyau, matsalarsu ɗaya basu yanke akaifa, yadda kasan hannun shaiɗanu, Ƙumba zaƙo zaƙo,

"Bring me am waiting" figigit tayi jin muryarshi, harya gaji da miƙa hannu, da sauri ta damƙa mashi bargon, ya kar6a,

Abakin ƙofar ta tsaya tana jiran ya kammala sanya bargon ya fito itama ta samu ta shiga wankan,

Tana Cikin tsawuwar nan, Taji takun tafiyarshi, bin ƙopar tayi da kallo, Fitowa yayi, Jikinshi ɗaure da bargon daya sanya, har zuwa chest ɗinshi,

Bata bari sun haɗa ido ba, Ya wuce ya nufi gefen gadonshi Ya zauna, tare da jingina bayanshi a jikin bango,

Tunani tayi kodai itama ta wanke kayanta ne ? Domin kuwa tajima bata wanke su ba, har tsami suke Yi mata,

Komawa tayi ta dauko bargonta dake yashe saman gadonta, da sauri ta nufi toilet ta shige, tsawon lokaci tana aciki, sai da ta kammala wanke kayan ta ta shanyasu, bayan tayi wanka ta ɗaura bargon a ƙirjinta, A bakin ƙofar fitowa daga sashen makewayin nasu ta la6e tana satar kallon danish, Sam bata so ya ganta in zata wuce,

Ganin ya lumshe idanuwanshi ne, yasa ta yi tunanin yin sauri ta wuce, Cikin sanɗa take tafiya, har ta samu takai bakin gadonta ta haye ta kwanta, yinin ranar su biyu suka yi shi, ita da danish, lokacin da kayansu suka bushe ita taje ta dauko masu uniform ɗinsu, ganin ya fara bacci yasa tayi saurin warware bargon dake ajikinta, ta xura uniform ɗinta, sai daga bisani taje bakin gadon danish ta tada shi daga bacci, ta miƙa mashi nashi unifom ɗin yasa hannu ya kar6a,

Ta juya ta koma gadonta, ta zauna daga gefe, idonta akansu batool dake ta sharar bacci, koda taga yana kokarin zame bargonsa don ya zura kayanshi da sauri ta kifa kanta saman pillow, ba ita ta ɗago ba har saida ya kammala sanya kayan ajikin shi, tukunna ta ɗago da kanta,

Abu kamar wasa har dare yayi su batool basu farka daga bacci ba, Hankalin angel yaƙi kwanciya shi kanshi danish jikin shi duk yayi sanyi, har sauko yayi daga saman gadonshi yaje ya duƙa agabansu yana tatta6a su, wannan wani irin dogon bacci ne da mutun zai kwashe yini guda tun safe har dare? Anya kuwa tsohuwa abunda tayi ta kyauta masu? Sai kace wasu matattu,


*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*


"Danish Ko dai inzo in kama maka, Mu mayar dasu saman beds ɗinsu? Ta yi tambayar tana kallon danish dake zuƙunne agaban Haris dake ta bacci, batare daya juyo ya kalle ta ba, yace mata eh, saukowa tayi daga saman gadon ta ƙarasa inda danish yake, yasa hannu ya ruƙe ƙafafuwan Haris ita kuma ta ruƙe hannayenshi Suka ɗaga shi zuwa saman gadonshi suka kwantar da shi, Haka suka bi kowannansu ɗaya bayan ɗaya suka ɗauko shi daga ƙasa suka mayar dashi saman gadonshi, suna ajiye batool saman gadonta, gaba ɗaya hasken ɗakin ya ɗauke duhu ya mamaye idanuwansu, basa iya ganin juna,

"Bari naje na kunna fitilun ɗakin, kada ka motsa" ta faɗa mashi hakanne don tasa halin shi da ruɗu, yanzu ya rikice mata, tafiya take yi cikin ɗakin tana laluban hanya har Allah yasa taci karo da table ɗin da fitilun suke, takai hannu ta kukkuna su, ɗakin yayi haske sosai, ta ɗauko ɗaya daga Cikin fitilun ta juyo tana hasko inda danish yake a tsaye, Ya goya hannayenshi saman chest ɗinshi ya ɗan jingina bayanshi jikin bango, tunkararshi tayi adai dai inda yake ta tsaya, Da sauri ya rufe idanuwanshi saboda hasken fitilar dake a hannunta, ba ƙaramin cika mashi ido yayi ba, ganin haka yasa ta kawar da fitilar gefe,
"Muje mu kwanta ko"? tayi tambayar tana kallonshi, babu musu ya amsa mata da toh, juyawa tayi gaba ta wuce nata gadon shima Ya wuce gadonshi, a tsakankanin beds ɗinsu ta ajiye fitilar, kusan atare suka haura saman gadonsu suka kwanta suna fuskantar juna, ya tsareta da sexy eyes ɗinshi yana kallonta without blinking, ganin kallon yayi yawane yasa tace"ba zaka yi bacci ba"? Wit low voice ya amsa mata da cewa"bana jin bacci," yatsina fuska tayi sam ba haka taso ba, saboda ta shirya yin amfani da wannan damar da take da ita,

"Danish Baka jin yunwa? Naga jiya baka ci komai ba, yau ma kuma babu abinci, why bazaka Ci apples ɗinka ba? Sai in haɗa maka da nawa ka ci"? Angel sarkin wayau, so take yaci don shima yayi bacci mai nauyi irin nasu batool, ko ta samu ta shige toilet ɗin can ta fara gudanar da aikinta na fasa Glass window ɗin nan domin Shiga Cikin gidan Kurkukun ƙaddara,

"Bana jin yunwa" shine amsar da yabata, tunani ta shiga yi ta wace hanya zata yi mashi wayau don ya yi bacci,

"Tunda ba zaka yi bacci ba, to ka daina kallona mana, Ni inaso nayi bacci bana iya bacci idan ana kallona" jin abunda tace ne yasa shi yin saurin rufe idanuwanshi,

Tsawon mintuna angel tana kallon shi, tunanin kiranshi tayi don taji idan yayi bacci" Danish" amsa mata yayi"yeah" wai bazaka runtsa ba, da buɗar bakin sa sai cewa yayi"If you don't sleep, nima bazanyi ba." serious yae maganar, rufe idanuwanta tayi"its okey, ga shi nan zanyi baccin kaima kayi" Ya amsa mata da toh, daga haka kowa yayi tsit acikinsu,

A lokacin da tayi tunanin ya nutsa cikin Baccin shi, ta sauko daga saman gadonta, takai hannu ta ɗauki fitilar da ta ajiye a tsakankanin beds ɗinsu, cikin sanɗa take tafiya tana tunkarar sashen toilet ɗinsu, duk taku ɗaya saita waiwo ta saci kallon Shimfiɗar danish,

Tana kawowa bakin ƙopar shiga sashen ta afka ciki, ta buɗe toilet ɗin ta shige taja ƙopa ta garƙame ta,

A ƙasa ta sauke fitilar, ta taka zuwa gaban bokitin ƙarfen nan ta ɗauke shi, tsayinta bazai kai ga tagar ba, dole sai ta ƙara da tsalle, cike da ƙwarin gwiwa ta daddage ta daka uban tsalle ta ɗaga Bukitin ta bugashi jikin glass ɗin da iya ƙarfinta na ƙarshe, sai dai wani abun mamaki glass ɗin Ko zagewa baiyi ba, Kamar ta daki ƙarfe ashe abun bana wasan yara bane, Tsalle taci gaba dayi tana kwaɗa bokitin jikin glass ɗin a ƙalla tayi kusan sau Talatin amma glass ɗin Ko yaƙi tsagewa, jikinta duk ya saki ga uwar zufa dake tsastsafo mata, sai faman haki take yi kamar wadda tasha uban gudu, ta galabaita sosai, sauke bokitin tayi ƙasa, ta zukunna tana mayar da numfashi, hatta idanuwanta sai da suka Canza launi,

Idan tahuta ta dawo normal saita kuma mikewa ta ɗauki bokitin Ta cigaba da buga shi jikin Windon, Har saita galabaita tukunna saita koma ta zukunna tana haki,

A wannan Karan Da azama ta miƙe ta ɗauki Bokitin ta daddage ta ɗaga shi da niyar ta kwaɗa shi jikin glass ɗin, kwatsam Taji motsin

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads