Showing 258001 words to 261000 words out of 287659 words
Chapter 87 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
irin wannan rayuwar, unaiza just 16 years mahaifinta ya wulaƙanta rayuwarta, ya barta acikin duhun jahilci, saboda mugunta da son zuciya na wasu mutanan masu hali irin na dabbobi, masu neman duniya ido arufe wai ace yau ɗanka na cikin ka zaka sadaukar don ka biya buƙatar kanka wadda a gidan duniya zaka bar koma me ka mallaka.
Ya hana ta mori duniya sannan lahirar ma ya hana ta nemeta, da ya ke Allah ba azzalumin bawan shi bane sai ya haɗa ta da Angel agidan kurkukun ƙaddara, Abunda yake baƙin cikin ta sani game da addinin Shi, Angel ta fahimtar da ita, finally Unaiza ta koma ga mahaliccin ta amatsayin musulma, ta tafi atsarkaken ta, tamkar a ranar aka haife ta, don haka unaiza ba ita bace abun tausayi, mugun ubanta shi ne zai ji tausayin kan shi, domin kuwa ire iren su tun a gidan duniya zasu fara gir6ar abun da su ka shuka, ya yi asarar rayuwar shi, saura ya jira haɗuwar shi da mahaliccin shi, Ya Allah duk masu Hali irin na Uban unaiza Jan wuya, ka hanasu jin daɗin rayuwarsu Allah ka toni asirinsu ka kawo mana ƙarshensu, saboda basu da amfani acikin rayuwar mu, Idan muka koma 6angaren majnoon, Yaron baisan komai ba, just 12 years ahaka aka sadaukar dashi! Shin su wanene iyayenshi? Dabbobine ko makafi ne ko kurame ne? yaron da bashi da ƙoshin lafiya, ga ta6in hankali ga ƙuruciya, a haka aka samu wani mara imanin mai zuciya irinta kafuran farko ya sadaukar dashi, Tsakanin iyayen shi ko danginshi, tabbas zasu ɗanɗani kuɗarsu, wannan alwashine alƙalamina ya ɗauka, kowa sai yaji a jikin shi! Ɗaya daga cikin su bazai sha ba! Muddin ina numfashi! In sha Allahu.
Kusan kwana uku da rasuwar Majnoon da Unaiza, Ko ruwa bai gifta maƙoshin su ba, waɗanda suka suma har yau basu farfaɗo ba, tamkar ba zasu rayu ba, Jamimah kaɗai ce ta ke rayuwa acikin ɗakin nasu, ta yi kukan har ta gaji ta gode ma Allah, babu mai jinta balle a samu wanda zai lallashe ta, Yadda suka ga rana haka su ke ganin dare, yadda ake kawo masu abinci haka ake ɗaukar shi ba tare da sunci shi ba, Jamimah kaɗaice wani lokacin ta ke kwasar shi a kwando ta 6oye, ko ta yi niyar cin abincin bata jin daɗin shi, kayan marmari kaɗai take iya sha, sai ruwa, Haka zata dinga bin su tana ambaton sunayen su haɗi da yayyafa masu ruwa don su farfarɗo su dawo cikin hayyacin su amma babu mai motsi, hatta su batul ga dukkan alamu suman su ka yi su ma.
A cikon kwana na huɗu ne, Batul ta motsa, da matsanancin ciwon kai da zazza6i, idanuwanta biji biji take kallonsu kamar matattu, daƙyar ta iya buɗe baki ta soma ambaton sunayen su ɗaya bayan ɗaya.
"Sarah! Hibba! Hannah! Parveen! Pls ku tashi, ku tashi mu rungumi junan mu, bana so na ƙara rasa wani a cikin ku.........." numfashi taja tare da ɗaura hannunta saman sumar kan eve tana ɗan bubbuga shi"Eve ki tashi, wai ba ku ji ina kiran sunayen ku," ta yi maganar a wahalce sautin ke fita, A hankali ta janye kan eve daga saman laps ɗinta ta kwantar da shi bisa floor, ta yunƙura ta matsa kusa dasu Parveen ta sanya hannu tana bubbuga jikinsu, Haka ta dinga binsu tana tatta6a su tare da ambaton sunayen su, Jin muryar Batul yasa Jamimah ɗago da kanta daga jikin Angel, don anan take wuni, rungume da ita, duk da bata motsi, jikinta na rawa ta sauko daga saman gadon da gudu ta nufi sashen toilet ɗin, tana shiga ta tura ƙopar makewayin da su ke a ciki ta shiga, a zuƙunne ta samu batul tana yin shessheƙar kuka, sanyi ne ya ratsa zuciyar Jamimah.
Ta ji daɗi sosai ganin sun fara farkawa, idanuwanta a cike tab da ƙwalla ta ambaci sunanta"Sister BATOOL" jin muryar Jamimah Yasa ta yi saurin juyar da kanta don ganin me magana, suna haɗa ido da Jamimah, a hanzarce ta miƙe jiki ba ƙwari ta nufi bakin ƙopar, ta zuƙunna tare da janyota a jikinta ta rungumeta sosai tana cigaba da matse ƙwallar dake acikin idanuwanta.
Cikin muryar kuka jamimah take faɗin"Sun tafin min da majnoon ɗina, bazan sake ganin shi ba, ko zai dawo ne? Ta yi tambayar tare da ɗago da kanta daga saman ƙirjin batul, sam takasa amsa mata tambayarta, saboda bata fahimci me take nufi ba, tun da su basu san cewa hada Majnoon ya mutu ba, su na acikin toilet, ko lokacin da giant ya shigo ya ɗauki corpse ɗin Unaiza basu fargaba.
"Majnoon ɗina jikin shi duk jini, inata kuka ina kiran sunan shi, babu mai jina, pls sister batul ki faɗi min gaskiya, mai ya faru da majnoon ɗina zasu dawo min dashi, ko in fidda rai," Tana magana hawaye na bin cheek ɗinta, fuskarta ta yi jawur da ita, har rama ta yi, tsananin tausayinta ne Ya kama batul, ta sanya tafin hannayenta biyu tana share mata mata su.
"Sister batul, baki bani amsa ba, yau 3 days kenan, Ni kaɗai nake motsi a cikin ɗakin mu...." bata ƙarasa maganar ba, ganin yadda batul ta zazzare idanuwanta tsananin mamaki ne akan fuskarta, jin abunda tace A ruɗe ta maimaita 3 days! Ras gabanta ya faɗi don bata fahimci cewa sun ɗauki tsawon kwana uku basa a cikin hayyacin su ba, sai da Jamimah ta furta mata.
"Ina ta kiran sunayen ku babu mai amsa min, gashi bani da lafiya zazza6i da ciwon kai, Har ruwa nake watsa maku a jikin ku don ku farka amma babu wanda ya motsa, itama Genie ɗita taƙi farkawa inata kiran sunanta......."
Tun kan jamimah ta ƙarasa maganar batul ta zabura ta miƙe Jiki ba ƙwari ta soma ƙwala masu kira na fitar hayyaci, tamkar maƙoshin ta zai 6allo, babban abunda take ji ma tsoro kada ace zuciyoyin su ne suka buga, da sauri ta tsallake su ta nufi bucket ta ɗebo ruwa a fanfo, kusan rabi ta cika, daga inda ta ke a tsaye ta ɗaga bokitin ta daddage ta watsa masu Sarah saman jikin su, Cikin sa'a suka soma jan numfashi, da sauri ta juyar da bokitin saitin jikin su Parveen ta watsa masu ruwan a jikinsu, nan take suka soma Jan numfashi da ƙarfi, Ganin ruwan ya qare ne yasa ta sake ɗebo wani abakin fanfo, ta sungumi bokitin zuwa cikin room ɗin su, tana shiga tsakiyar ɗakin inda su Deeja su ke a kwance, ta ɗaga bokitin ta daddage ta watsa masu ruwan a jikinsu A figice Azeeza da Deeja su ka farka suna faman sauke ajiyar zuciya, ragowar ruwan daya rage a bokitin ta watsa ma Angel da ke kwance saman gadon Majnoon, koda ruwan ya sauka a jikinta, bata buɗe idanuwanta ba, sakamakon nauyin da su ka yi mata, sai dai ga dukkan alamu ta farfaɗo, duba da yadda take motsa la66anta kamar tana ambaton sunan Allah.
Sanyayyiyar Ajiyar zuciya batul ta sauke, a yayin da ta ke bin su da kallon, A galabaice su ka miƙe zaune saman floor suna ambaton ruwa zasu sha, maƙoshin su zafi, ƙishi su ke ji, ' ajiye bokitin hannunta ta yi a ƙasa da sauri ta nufi ƙarƙashin gadonta tana laluban robobin ruwan da Jamimah tace mata ta ajiye masu, kusan guda shida ne, ta rungumo huɗu A ƙirjinta, taje ta miƙa ma Deeja da azeeza yatsun hannayen su na kerma suka kar6a tare da cire murfin, Yanayin yadda su ke shan ruwan ne ya bata tausayi, Kamar ta fashe masu da ku ka.
Motsin da Angel za ta yi ke da wuya ta ƙundumo daga saman gadon ta faɗo saman floor, kanta ba ƙaramin buguwa yayi ba, Da sauri Batul ta nufe ta tare da zuƙunna agabanta, sai da ta fara A jiye bottle waters dake a hannunta a ƙasa kafin ta sanya hannayenta biyu wurin tallabo da kanta ta ɗaura shi saman laps ɗinta, muryarta a sanyaye ta soma yi mata magana.
"ƴar uwarta rabin raina, Pls ki tashi, nasan kina jina, ki yi haƙuri ki jure, komai ya wuce, bana son abunda ya faru ya yi silar tarwatsewar farin cikin mu" a hankali Angel ta buɗe idanuwanta waɗanda suka canza launi sun ƙanƙance, biji biji ta ke ganin fuskar batul.
Hannu batul ta miƙa ta ɗauko ɗaya daga cikin robobin ruwan da ta ajiye gefenta, bayan ta cire murfin, ta ɗago da kan Angel zuwa saman ƙirjinta,
"Nasan kina jin ƙishin ruwa, Ki buɗe baki kisha" ganin taƙi motsa lips ɗinta ne yasa ta cusa mata bakin robar abakinta, don dole tasha ruwan, sosai ta kur6e shi, kusan rabin robar ruwan ta shanye, yunƙurin amai ne yazo mata gaba ɗaya ta sheƙar da ruwan data sha saman jikin batul, a ruɗe batul ta ajiye robar ruwan da ke a hannunta, ta rungume Angel ajikinta, tamkar zata mayar da ita cikin cikinta, ita kanta ba lafiyar ce da ita ba, a haka ta dinga lallashinta, Azeeza da Deeja sun yi zugudum babu mai iya magana a cikin su, Bayin Allah sunyi fatan ace mafarkine abunda ya faru ba gaske ba, Sai da kash ƙaddara ta riga fata, idanuwansu akan gadon majnoon, jinin shi ne daskare akan zanin gadon, Allah sarki rayuwa kenan babu wanda yafi ƙarfin mutuwa, idan ajali yazo dole ka miƙa wuya.
"Deeja Yakamata Mu daina zubar da hawayen mu, mu lallashi ƴan uwan mu tunda mune masu juriya a cikin mu, idan har bamu fi ƙarfin zuciyoyin mu ba, zamu rasa ƙwarin gwiwar da mu ke dashi, dama su abunda su ke so kenan, saboda basu san ciwon kan mu ba, da biyu suka dawo mana da Ƴan uwan mu bayan sun san cewa mutuwa za su yi, meyasa basu ruƙe su a wurin su ba? Suna so ne kawai su kashe mu da ran mu shiyasa su ka dawo mana da su a wulaƙance don muga irin mutuwar da za su yi, Allah ya isa tsakanin mu da su!" daƙyar ta ƙarasa maganar cikin ƙunar rai.
Shigowa Cikin ɗakin su parveen su ka yi, Hannun su ɗaya dafe da goshin su, Tafiya su ke yi tamkar zasu kife ƙasa, saboda jirin da suke gani acikin idanuwansu, ga ciwon kai da yunwa da ke addabarsu, ga damuwar da ke ƙunshe cikin zuciyoyin su.
Gaba ɗayan su ne na cikin toilet ɗin suka fito a jere, a saman floor su ka zazzauna, Parveen na ƙoƙarin zama idanuwanta su ka hango mata gadon majnoon.
A gigice ta furta "Innalillahi...." ba tare da ta ƙarasa maganar ba, tsananin tsoro ne da firgice su ka bayyana a cikin akan fuskokin su, Hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, musamman parveen a ruɗe ta nufi gadon majnoon ganin daskararren jini asaman shimfiɗarsh, hannayenta biyu ta ɗaura saman bargon shi, yayin da zuciyarta ke tafarfasa.
Muryar Hannah na rawa ta furta"INA MAJNOON YA KE? JININ MENENE MU KE GANI A SAMAN SHIMFIƊAR SHI, DAN ALLAH KADA KU CE MANA YA MUTU SHI MA"!
Babu wanda ya iya buɗe baki ya basu amsa, hakan yasa su ka fahimci cewa Majnoon ya mutu babu shi, hawaye ne masu ɗumi su ka wanke fuskokinsu, A saman shimfiɗarshi Parveen ta kifa kanta da ke sara mata da ciwo, ta dinga kuka tamkar ranta zai fita, bakomai take tunawa ba face Irin rayuwar da su ka yi dashi, ta yi matuƙar tsaya mata arai, ta yi danasanin duk wani bugu da ta yi mashi, tun ranar farko daya fara kasancewa a cikinsu, Ya 6arar masu da Cake, Tana matuƙar son yaron tsanar da ta yi mashi a lokacin saboda 6arnar da ya ke yi masu ce, ɗago da hannayenta tayi tare da ɗaga su sama tana kallon fingers ɗin ta da ke kerma, Hawaye jaga jaga akan fuskarta, sautin kukanta ya cika ɗakin nasu, Muryarta da wani irin sauti ta ke faɗin"YA ALLAH KA ƊAUKI RAINA IN HUTA! BAZAN IYA JURAR TASHIN HANKALIN NAN BA! Bana fatan na sake yin tozali da gawar wani a cikin ƴan uwana, So nake na mutu in huta, Narasa Majnoon abokin Faɗa na ga Unaiza ma ta tafi tabar mu da kewarta, wayyo Allah nah! ' sosai ta rushe masu da kuka, kamar mahaukaciya haka ta cusa hannayenta cikin sumar kanta, ta dinga hargitsa gashin cikin ƙunar rai, kafin ta mayar da kanta saman mattress ɗin Majnoon.
Duk suna jin sautin kukanta, Jikin su duk ya yi sanyi, mutuwar mutun biyun nan ta raunata zukatan su, ta sagar masu da gwiwarsu, komai ya fita aran su, babu mai sauran walwala acikinsu, ba don zuciyar Imani ba da tuni wasu daga cikin su sun zauce, musamman Azeeza ta shiga halin ha'ula'u, tsoro da firgici sun hana ta sak, har zufa ke tsastsafo Mata saman goshinta, tun da ta farfaɗo daga suma ta zauna ko motsi ta gaza yi sai dai tabi su da ido.
Miƙewa tsaye Sarah Ta yi jikinta kamar zai 6alle, saboda rashin kuzari, fuskarta a bushe muryarta asanyaye ta soma magana"Idan har mu ka cigaba da zama ba tare da mun ɗauki mataki ba, za'a cigaba da yi mana ɗauki ɗai ɗai ne ana kashe mana rayuwa, Yakamata musan abun yi, wlh na tsorota Na firgita da ganin irin mutuwar da Unaiza ta yi, Tare da ita fa aka kawo mu cikin ku, bazan ta6a manta farkon gani na da ita ba, ban ta6a tunanin cewa zan shaida mutuwar ta ba, na girgiza sosai, please na roƙe ku, idan zaku iya ku kashe ni zaifi min kwanciyar hankali akan aƙara zuwa a ɗauki wani acikin mu, saboda na fahimci cewa rayuwar mu bata da amfani awurin su, mutuwa ta zamar mana dole yanzu ma aka fara yinta, bansan wanene next zai mutu ba, bana so na gani shiyasa nake so in mutu................" daƙyar ta ƙarasa maganar, saboda raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyarta, miƙewa tsaye Hannah ta yi, idanuwanta jawur dasu ta soma magana tana fuskantar sauran ƴan uwan nasu da ke a zazzaune ƙasa
"Meyasa har yau Allah bai dube mu ba? Mu ma fa bayinsa ne kamar kowa, Angel ke da kan ki kika faɗa mana cewa wanda ya halicce mu yana sane damu, but why mu ke fuskantar irin wannan tashin hankalin? bawani mai taimakon mu, sau nawa muna hana idon mu bacci don mu kai kukan mu agare shi, amma shiru...!
Hankalin Angel ba ƙaramin tashi yai ba, jin maganganun da Hanna ke yi, duk da matsanancin halin da ta ke a ciki sai da ta girgiza, ganin sun soma ƙoƙarin kauce hanya, dama ba wadataccen ilmin addini gare su ba, ba lallai bane a yanzu da suka fara fuskantar tashin hankalin nan su iya jurewa ba, saboda suna da raunin imani da tawakkali, a haka ma sunyi ƙoƙari saboda basu ta6a ƙaryata maganar ba, sai dai awannan karan tana tsoron Su juye mata su canza ra'ayinsu.
Runtse idanuwanta ta yi sosai tare da cusa kanta a ƙirjin batul, ba ta yi tsammanin zata samu sauran hawaye a cikin idanuwanta ba, sai gasu sun soma tsastsafowa saman kuncin ta masu ɗumi.
zuciyar batul ba ƙaramin karaya tayi ba, Jin yadda Jikin Angel ya yi zafi sosai, tasan dole taji raɗaɗin a cikin zuciyarta,' ƙara ƙanƙameta ta yi a jikinta, hannayenta asaman sumar kanta, A hankali take shafa sumar Angel tana lallashinta, zuciyarta tamkar ta fashe saboda ƙunar da ta ke yi mata, gudun kada ta zauce ta rasa madafa, yasa ta soma furta duk wasu addu'o'i da tasan zasu kwantar mata da hankalinta.
A yayin da ta ke yin addu'o'in idanuwanta suna arufe, sosai ta matse su, tana jiyo muryar Yasmin tana faɗin
"Angel Kin yi shiru baki bamu amsa ba, har yaushe ne zamu tsara Jiran taimako daga wurin Allah! Kina ganin mun fara mutuwa, tsoro da firgici kaɗai kaɗai sun isa su sa mu zauce, Mun yi tunanin cewa idan muka kar6i addinin ki, Mu ka yi Imani da Allah, komai zaizo mana da sauƙi, Amma shiru sai ma ƙara shiga tashin hankali da mu ke yi, lokacin da kika zo cikin rayuwar mu Ba ki ji daɗin da mu ka ji ba, saboda alƙawarurrukan da kika ɗaukar mana na cewa Zaki taimaka mana wurin ganin mun ku6uta daga cikin kurkukun ƙaddarar nan, Ki ka sanya mana kwaɗayin son yin rayuwar ƴan ci kalar wadda ki ka yi awaje, Meyasa angel muke ganin ba dai dai ba? Idan da ace kinsan ba zaki iya taimakon mu ba, meyasa kika sanar damu hakan? Kuma kika bamu labarin rayuwarki har muka sanya rai da yin irinta........"
Yasmin bata ƙarasa maganar ba, ta rushe da kuka, Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi, Dama fa dole ta fuskanci wannan matsalar, cos itace mutun ta farko data fara sanar dasu komai agame da mahaliccin su, Nauyin komai ya rataya akan wuyanta! Duk idan su ka ji ba daɗi dole ita zasu tunkara, to ayanzu dai mutuwar Unaiza da Majnoon ta kwance notikan kawunansu, sun fara tsorota shiyasa su ke waɗannan maganganun.
"Angel idan har akwai abunda ya rage mana wanda ba mu yi ba dangane da addinin ki, to ki faɗa mana shi don muyi wata'ƙil Allah zai ji ƙanmu ya tausaya mana, ya dube mu da idon rahama ko mun samu mu tsira da ranmu!" Eve ce ta yi maganar, Duk sun mimmiƙe tsaitsaye Agaban Batul da ke a rungume da ita, sai ƙara tighting ɗinta ta ke yi a jikinta, ita kanta batul ɗin hawaye ne sharkaf akan fuskarta, cigaba da ambaton sunan Allah ta yi acikin zuciyarta, tana roƙonshi akan ya basu bafita kada yasa su ga gazawarta.
"Angel Mun san kina sauraron mu, kin yi shiru ba ki ce komai ba, kada ki sanya mana kokwanto A cikin zukatan mu, Mun yarda dake, Munsan kina ƙaunarmu, kuma kina son Farin Cikin mu, don haka Muna jiran amsar ki me ya rage mana wanda ba muyi ba a cikin addininmu wanda zaisa Allah ya jiƙan mu......" Cikin rauni na murya Hibba ta yi maganar, daga ganin fuskokin su a matuƙar tsorace suke.
Angel tana a cikin tsaka mai wuya, ta kasa ɗago da idonta ta dube su, saboda bata da ƙwarin gwiwar yi masu