Showing 183001 words to 186000 words out of 287659 words
Chapter 62 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
mawuyacin hali, Nagaza zuwa in taimake ta, nasan Ta jira zuwana taji ni shiru, dole taji ba daɗi duk irin ƙaunar dake a tsakanina da ita," A gefenta haris Ya zuƙunna Ya soma lallashinta kamar yadda yayi ma deeja, A ƙarshe Ya ruƙo hannunta yace"Ki taso mu koma ɗaki" Maƙe mashi kafaɗa tayi"a'a Kabarni anan, Inaso zanyi ma furennin addu'a" gyaɗa kai yai tare da miƙe wa, da niyar yabar toilet ɗin, har ya juya zai fita sai kuma ya ɗan dakata tare da kallonta yace"Angel, badan halina ba, badan na isa dake ba, pls Ki karya alƙawarin dake a tsakaninki da Danish! Idanuwanta jawur ta juyo tana kallon haris, yaci gaba da cewa"Ki tausaya mashi, dama ba cikakkar lafiya ce dashi ba, yanzu kuma kin ƙara jefa shi cikin wani hali, duk fa saboda ke ya gaza sakewa acikin mu, yaƙi cin abinci yaƙi canza uniform ɗin jikin shi, ni bansan ya akai kika sa ya ɗaukar maki alƙawari fa" fuskarshi a yamutse yayi maganar, Hannu tasa ta matse tsinin hancin ta, yayin da take kallon shi, muryar ta ƙasa ƙasa tace"haris, Nasan ban kyauta ba, nima nayi regretting da na sanya shi ya ɗaukar min alƙawari, raina ne yake a6ace, Amma har ga Allah ni bana fushi dashi ayanzu, sai da nace mashi nafasa promise ɗin, Mu shirya amma yace min shi bai fasa ba......" kaf angel ta kwashe duk yadda su ka yi atsakaninta da Danish ta sanar mashi,
Dafe goshi haris yae da hannun shi na dama kafin ya zame shi ya ruƙe qugu yana faɗin"Oh my God, Danish matsala, kin san shi da ruƙe alƙawari, idan har mu ka ce zamu biye mashi bamu san har tsawon wasu kwanaki za'a ɗauka ba, Yana Cutar da kanshi, Tun da ba mu san ranar da za'a dawo da Batool ba, kuma bamu da tabbacin cewa idan an dawo da ita zata yafe mishi," Dakatawa yae da yin maganar yana kallonta, itama shi take kallo,
"Yanzu ya zamu yi kenan? Alƙawarin Ya karye" Haris ne yai tambayar, shiru angel tayi na wani lokaci tana yanke shawara daga cikin zuciyarta,
"Kin yi shiru" a ƙagare yae mata maganar, har ya fara gajiya da tsayuwa,
"Kada ka damu haris, Ni nasan yadda zanyi dashi, In sha Allah a daren yau ɗin nan zan karya alƙawarin, " ajiyar zuciya haris ya sauke fuskarshi asake yace"Dama nasani zaki Iya!" ya ambaci hakan tare da juyawa da sauri ya fuce daga Cikin toilet ɗin,
Lokacin daya shiga Room ɗinsu, Su parveen duk sun farka daga bacci, sai surutu suke yi. Kamar ba waɗanda suka sha bacci ba, Kowacce Tana daga zaune saman gadonta, Hannah tana hamma tace"Wai ina angel ɗinmu take ne? Naga banganta ba" hibba tace"yanzu haka tana acikin toilet, wani uzirin ne ya kamata," saukowa daga saman gado azeeza tayi tare da cewa"Nima toilet ɗin xan shiga" takarasa maganar tare da wuce wa ta nufi sashen toilet, tuni haris ya jima da komawa saman gadon shi, ya zauna yana yi musu sannu da farkawa bacci, sarakan ɗumi yanzu xa'afara, gaba ɗaya suka kama dariya, Parveen na miƙa tace"Motsa Jiki zamuyi, Jiki na duk ya ruƙe, " Haris yace'ae dole, An cika ciki yayi haiƙam ta ko'ina babu space ai dole ki nemi motsa Jiki, ko kin samu Cikin ya kwance Aje toilet kamar yadda aka saba," Wani irin kallon harara take jefa mashi, Eve tace"Haris ka sanya ma sis parveen ido Allah, bansan me tayi maka ba" Ta6e baki yai"ae tunda tace ban da kyau saita gane kuren ta," Deeja dake kwance tana jin muryoyinsu Acikin kunnanta, taƙi motsawa ne don kada suga halin da take ciki na damuwa,
"Yakamata Baƙin prisoners ɗin nan su ƙaraso tunkafin Ku 6alla musu gadajensu" javed ne yai maganar idanuwanshi rufe, yana kwance saman nashi gadon,
"Idan ma akwai wanda zai 6alla musu gado to bai wuci ku ɗin nan ba, saboda kune ƙattai da kai da haris da mubeen da naufal, gadon ma yayi maku ƙanƙanta" parveen ce tai maganar tana gatsina mashi hanci,
Wani irin kallo haris da javed suke jefa mata jin abunda tace, Naufal dai bai tanka musu ba, tun da ya farka bai mike zaune ba, mubeen dai ne ya tada kanshi saman pillow,
"Kina wuce gona da iri parveen, da alama yau kinci kin ƙoshi, shiyasa kike gaya mana magana" kafin parveen ta mayar mashi da martanin maganar da yayi, muryar naufal ta katse su da cew "wai ba dai har yanzu, maji daɗin gadon can Bai sanya uniform ɗinshi ba? Nagan su ajiye gefen shi," yai maganar yana kallon gadon Danish Bawan Allah ya baje sai sharar baccin shi yake yi, haris yace"ae kasan halin shi, ba yadda banyi dashi ba, akan ya sanya kayan amma yaƙiya, abincin shi ma yaƙi ci, narasa ya zanyi da Danish yafi ƙarfina...." Haris na ƙarasa maganar, parveen tace"ae wlh indai cinyar kazar shi takai anjima tsakar dare bai ci ba, Sai na cinye ta, in haɗa da fruit ɗin, Ni natsani inga ana wulaƙanta abinci, " Tana magana tana hura hanci,
Harara Naufal Ya jefa mata Daga kan gadon shi, Yace"Sannu MAJI DAƊIN ABINCI, uwar haɗamammu, ke da ba ki gajiya da abinci, Ga shi ni ko ajiki banga kina ƙiba ba, " murguɗa mashi ƙaramin bakinta ta yi, batare da ta bashi amsa ba,"
A6angaren Angel dake a tsugunne gaban tukunyar fulawa, ta ƙurawa furennin idanuwanta, Hankalinta ya ɗan kwanta ganin furen batool Lafiyar shi ƙalau, jikin shi yai kyau launin shi ya ciza, haka zalika furen daddynta Yayi kore shar dashi, Addu'o'i ta shiga jerowa tana tottafa ma furennin, bayan ta kammala bata miƙe ba, Zurfin tunani ta shiga akan yarda za'ae ta karya alƙawarin da ke tsakaninta da Danish, Dole ta yi mishi dabara.
"Angel!" firgigit tayi Jin an ambaci sunanta, da sauri ta sanya tafin hannayenta ta share hawayen dake akan fuskarta kafin ta juya ta kalli ƙopar shigowa cikin toilet ɗin, bakowa bace face Azeeza, fitowarta kenan daga cikin ɗaya daga Cikin makewayin nasu, sai faman sakin murmushi take yi,
"Azeeza, haka na koya maki yadda ake shiga toilet? Batare da neman izni ba"? Fuskarta aɗan ɗaure tayi mata magana, ɗaure fuska azeeza tayi tana tur6una fuska, kamar zatayi mata kuka tace"Ae Naji muryoyinku keda haris kuna magana, duk da bana jin ku sosai, naga ya shigo, shiyasa nima na shigo"
zuba mata ido angel tayi ganin yadda take magana tana wani farfari da idanuwanta, miƙewa tsaye angel tayi tare da juyowa ta nufi bakin door ɗin inda azeeza take a tsaye, Ruƙo hannunta ta yi acikin nata, taja ta suka dawo Cikin ɗakin, a tsakiyar ɗakin suka samu su Hannah, Sun ɗauko madubin nan suna kallon fuskokinsu, Yadda kasan sun ruƙe Waya a hannunsu Suna ɗaukar Selfy, gayun ne bai ƙare ba, dama ɗazu gajiya suka yi shiyasa suka ɗan kwanta, Yanxu sun wartsake, mutun Uku ne basu sauko daga kan gadon su ba, Danish da Haris sai deeja, amma su mubeen duk sun sauko, suma suna kallon madubin, ba ƙaramin burgeta su ka yi ba, tana fata wata rana Idan Allah yasa suna da rabon tsira su ɗauki pics tare da ƴan uwanta.
kafin su ƙarasa inda su hanna suke, Tana jiyo muryar Rubina tana faɗin"Allah yasa baƙin da za'a kawo musu basu kaisu kyau ba" Yasmin tace"ke damuwarki kenan, Ni fatana Allah yasa akawo mana masu hankali da natsuwa," parveen tace'Ni kuma bana son masu shegen cin abinci, Allah yasa akawo mana Irin Danish, marasa son cin abinci, sai mu dinga yi musu wayau idan sun rage abinci mu kwashe mu cinye" tana magana tana kwatanta yadda zasu dinga kwashe abincin da hannunta, gaba ɗaya suka saki dariya, "Allah ya shirye ki parveen, baki da burin daya wuce abinci abinci, " mubeen ne yai maganar, Naufal yace"ae shiyasa na sanya mata maji daɗin abinci, sabon sunan parveen kenan, ita kuma azeeza maji daɗin shagwa6a" Yana rufe baki, Hanna tace"ita fa angel"? hannu yasa ya toshe bakin sa tare da cewa"Rufa min asiri, kunfi kusa da ita, ku bata sunan daya dace da ita," murmushi angel tasaki yayin da take kallonsu tace"Ae basai wani ya faɗi ba, Ni da kaina zan bama kaina sunan daya dace ni,"
Hayaniyarsu ce ta farkar da Danish, gaba ɗaya sun cika mashi kunnan shi sun hana shi sakat, bakomai ya faɗo mashi aranshi ba, face maganar da haris ya faɗa mashi akan sabbin uniform da kuma cin abinci, baya so haris ya daina Kula shi, ko dan saboda haka zaisa kayan, a hankali Ya miƙe zaune yakai hannu ya ɗauki uniform din ba wanda ya lura dashi acikinsu, saukowa yae daga saman gadon cikin kasala Ya nufi sashen toilet dinsu Ya shige,
Bayan wasu ƴan mintuna, Suna Cikin yin firarsu da raha, Kwatsam Suka ji parveen ta fasa ihu, Mai matuƙar razanarwa a gigice suka kalle ta, Ta zazzare idanuwanta, Yayin da take kallon bakin ƙopar shiga sashen toilet ɗinsu, Da sauri Suka kai idanuwansu kan ƙopar, Wa'iya zubillah, Tabarakallahu ahsanun kaliqin, Kusan atare suka waro idanuwansu waje tamkar eye balls ɗinsu zasu faɗo ƙasa saboda tsabar yadda suka zazzare idanuwan, Sun saki baki Galala suna kallon shi yayin da yake shigowa cikin ɗakin,
Tsarki ya tabbata ga wanda Ya halicci wannan bawa, Maƙerin wannan kyakkyawar Halittar, mai matuƙar jan hankali da ɗaukar ido, Hatta haris da deeja dake kwance saman shimfiɗarsu, sai da su ka miƙe zaune sakamon Ƙarar da parveen ta saki, A wani irin yanayi suke bin shi da kallo from head to toe, black trouser ɗin Ya xauna mashi sosai, A bunka ga dogon namiji, daga sama Ya sanya red vest ɗin shi, tayi tighting ɗinsa, tayi mashi kyau ta fito da ainihin Farar fatarshi, Daga saman Jar vest ɗin ya ɗaura wrap Coat ɗinsa black colour, Abunda ya ƙara ƙawata kyanta, bai ɗaure igiyoyinta ba, hakan zai baka damar ganin ƴar ta cikin,
saman dogon wuyanshi ya rataya Cotton scarves ɗinshi red colour, Ya ɗaure yalwatacciyar sumar kanshi ta baya Ta zubo mashi, Wohoho, A fagen kyau Danish Yana a mataki na farko, don da ace zai shiga gasar kyau to kuwa yana ɗaya daga Cikin waɗanda zasu lashe gasar babu tantama, Kayan sun dace dashi, yadda kasan don shi akayi su, tausasan red lips ɗinsa launin su yayi Ja sosai sunyi matching da Cotton scarves dinsa da kuma Red vest ɗinsa, Launin ƙwayar idanuwanshi, russet brown sai ɗaukar ido suke yi, ga eye lashes ɗin nan nashi masu tsayi da cukowa sun ƙawata zagayen idanuwanshi,
Wallah An rasa me magana acikinsu gaba ɗaya Danish Ya shammace su, Mamaki ne da al'ajabin kyawunsa sunyi matuƙar gigitasu, sun rasa gane a tsakanin shi da Angel waya fi wani kyau, ita irin zazzafan kyau ne da ita, wanda farat ɗaya ka kalle ta sai gabanka ya faɗi, shi kuma nashi wani irin sanyi ne dashi, mai narkar da zuciya,
Ganin yadda suka zuba mashi na mazurinsu suna kallon shi nan take yabi ya rikice, a ruɗe ya juya ya koma sashen toilet ɗinsu, Ya jingina bayan shi jikin bango yana faman sauke ajiyar zuciya,
"Allah yasa bani kaɗai nake gani ba" parveen ce tai maganar, azeeza tace"Ae duk mun gani, wlh Danish Yayi min kyau, kamar in sace shi, muryar parveen kamar zatai kuka tace"Yafi abinci kyau da kyan gani," gaba ɗaya suka saki dariya, Hanna tace"Speechless bansan da wasu words zanyi amfani wurin Bayyana irin kyan da danish yayi mini ba" naufal dai sai jinjina kai yake yi, da alama shima ya rasa tace wa, Inaga uwar gayya wato Angel, babu wanda ya lura da ita, tuni ta zuƙunna ƙasa, zuciyarta kamar zata buga, Bakomai take tunani ba face Hamshaƙin Kyan Fuskar Danish, Mamaki take wai a ina ya gado wannan kyan nashi? Su wanene Iyayen shi? Tama rasa da wani jinsi zata kwatanta shi, Larawa ba ne indiyawa ne, turawa ne, South korean ne, Ko kuma Nigerian ne!! A ƙarshe dai Zuciyarta ta bata amsa da cewa"Yafi kama da jinsin aljanu, kiyi tunani xaiyi wuya ya kasance mutun ne" murmushi taɗan saki, ƙuruciya ta motsa, nan take ta yadda da abunda zuciyarta ke raya mata, Muryar haris ce ta dawo da ita daga zurfin tunanin da ta shiga
"Ina takalmanshi suke, " yai tambayar Yayin da yake saukowa daga saman gadon shi, Jiki na rawa parveen ta nufi akwatinsu, Ta buɗe ta curo takalman Danish Ta miƙa ma haris Ya sanya hannu biyu ya kar6a, ya juya ya nufi sashen toilet ɗin nasu, yana fadin"kada wanda ya kuskura ya biyoni, Duk kunbi kun ruɗamin ɗan uwa," da zolaya yai musu maganar,
Yana shiga ya samu Danish Ya lumshe idanuwanshi, A gaban ƙafafuwan shi, haris Ya zuƙunna, Ya ajiye takalman tare da kai hannu Ya damƙo ƙafar shi,
a firgice Danish Ya ware fararen idanuwanshi akan fuskar Haris, ya ɗan tsorata saboda bai yi tsammanin zaiga mutun ba, Fuskar haris dauke da murmushi yace"Allah ya taimake ka, da ace yau ba ka sanya kayan nan ba, da babu ni babu kai, amma tun da ka sanya to muna atare," murmushi ne ya bayyana akan fuskar Danish, A tsanake Ya sanya mashi takalman, Bayan ya kammala ya ɗago, suna fuskantar juna, Ya ruƙo igiyar Coat ɗin, Ya ɗaure mashi ita, Kafin ya sanya hannayenshi biyu Ya tallabo fuskarshi wani irin murmushi suke sakar ma juna,
"Dole na ƙaunace ka ɗan uwana, kai ɗin na daban ne," haris ne yai maganar, tare da janyo shi jikin shi, yae hugging dinshi, zagayo da hannayenshi yayi abayan haris yaɗan ƙanƙame shi, Muryarshi asanyaye yace"Nima ina ƙaunarka haris, ina jinka kamar yadda kake ji na acikin zuciyarka, am so proud of u, kai tamkar kyauta ne agare ni, bana tunanin zan samu madadin ka a duniyar nan......." tsabar farin Ciki yasa haris sakin dariya yana bubbuga bayanshi da hannun shi, haƙika yaji daɗin kalaman danish agare shi, cos this is the first time daya ta6a furta mashi hakan,
"Mu kuma fa"? kamar daga saman suka jiyo muryoyinsu Naufal, da sauri suka raba jikinsu daga Na juna, Su ukun nan ne, Mubeen da Javed, sai kallon su suke yi, ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskar Danish Ware masu hannuwanshi yae alamar suzo suma ya rungumesu, aiko da sauri suka ƙarasa Ya haɗasu duka ajikinshi, Lamarin yayi matuƙar burgesu, Gwanin ban sha'awa, musamman yadda Danish Ya sake dasu Yana faɗa masu da ɗaɗan kalamai akan irin ƙaunar da yake yi masu abunda bai ta6a yi ba," Suna Cikin hakan suka Jiyo muryar azeeza da shagwa6a tana fadin"To mu fa? Baza a rungume mu ba," atare suka ɗago suna kallonta, ta ruƙe qugu abakin ƙopa, Haris yace"sarkin rigima, ki koma ciki, gamu nan zuwa, ɗaya bayan ɗaya sai Danish yabi ku ya rungume ku," Fuskarta ɗauke da murmushi ta watsa da gudu ta koma cikin ɗakin, tana faɗa masu parveen cewa Ga Danish nan xai zo ya rungumesu ajikin shi, Parvee tace har na ƙosa in shaƙi ƙamshin Jikin shi," kamar wata mayya,
Kusan atare suka shigo Cikin ɗakin, Haris yana a ruƙe da hannun Danish, ya zama tauraro Acikin taurari, A tsakiyar ɗakin suka tsaya, A lokacin angel ta koma gefen gadonta, har ta cire wrap coat dinta, ta ɗaurata saman mattress, ta ɗaure fuska babu walwala,
"Ka faɗa musu irin mahimmancin da suke dashi awurinka kamar yadda ka faɗa mana" acewar haris,
Natsuwa Danish yayi, A yayin da yake bin su da kallo sun jera layi kamar mabuƙatan dake jiran abasu sadaka, duk sun ƙagara su ji mai zaice, Bakowa yake son gani ba face ANGEL, ta wutsiyar idon shi ya hangota, saman gado sai hura hanci take yi, kamar Zakaran daya sha sigari,
"A yau inaso na faɗa maku, irin mahimmancin da kuke dashi awurina, You are more than just a friends saboda kun xarce hakan, Na ɗauke ku tamkar iskar da nake shaƙa, wurin yin numfashi domin in tsira, baku da banbanci da bugun zuciyata, Ina matuƙar ƙaunar ku, I luv you more than words can say bani da tamkarku a duniyar nan, i can even sacrifice my life for u guys" tunda ya soma jawabin nan, angel take ta satar kallon la66ansa, wani irin yanayi take ji mara misaltuwa, duk ta rasa sukuni,
"We're not only prisoners, we're life partners, bonded together by fate.
We were meant to be under the same roof, sharing a common destiny.
My hope is that one day we can be proud of each other, and Proud of the journey we've taken and the challenges we've overcome, we are more than just cellmates, we are family."
saboda tsabar daɗin kalaman shi da suke ji, har wani lumshe ido sukeyi, muryar tashi ce kamar ana busa sarewa gashi ya iya jawabi kamar jinin sarakai,
"Abubuwa da dama sun faru atsakaninmu, masu daɗi da marasa daɗi, dama shi haka zaman tare yake, sai ana haƙuri da juna, ni mai laifine amma still ina da damar da zan gyara kuskure na, duk da nasan akwai waɗanda suke yi min kallon mara amfani, inaso suyi mini uziri, nima bana so na dawwama ahaka, kodan saboda farin cikin ku, Zanyi ƙoƙari na gyara alaƙar dake atsakanina da kowannanku......." wannan magnar da Danish yayi tayi matuƙar karya musu zuciyoyinsu, musamman deeja da Angel, sunji wani irin acikin zuciyoyinsu,
"Aduk lokacin dana aikata ba dai dai ba, ku yi min uziri kada kuce zaku ƙaurace min, cos that's not the solution, kamata yae ku ja ni, ajikinku kamar yadda haris yake yi min shi kaɗai ne acikin ku yake faɗa min cewa nayi kuskure in gyara, kuma ina jin dadin hakan, Bayan shi mutun ɗaya ce nasan zata Sanya ni ahanyar dai dai, ko ban fada ba kunsan kowacece......." daƙyar ya ƙarasa maganar, saboda raunin da zuciyarshi tayi mashi, tunawa da ƴar uwarsu Batool, mai kyakkyawar zuciya,
"Duk da abunda nayi ma batool, Ni shaida ne akanta, idan yau ta dawo Cikin mu, bazata ta6a gudu na ba, zata fahimce ni, but why wasu suke ganin laifi na"? da sauri angel ta kifa kansa saman pillow, wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke mata fuskarta, sosai ta ƙanƙame pillow ɗin, kalaman shi sun kashe mata jiki, yanayin yadda