Showing 234001 words to 237000 words out of 287659 words
Chapter 79 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
su nata kerma muryar su a tsananin tsorace suke roƙonta suna faɗin Dan Allah Angel kada ki kashe mu, ki tausaya mana halin da mu ke a ciki, laifin me muka yi maki? Yau ke da kanki kike neman halaka mu! Magana suke yi amma sam babu alamun tana jinsu, abunda basu sani na, A halin yanzu Angel ba ita ɗaya bace.
Ganin maƙiya ta ke yi musu, Burinta kawai ta kashe su har Lahira, shin ina labarin azeeza da jamima dake a la6e ƙarƙashin gado, kowannan su yasha jinin jikinshi, tsabar tsoro yahana su motsa, Sai da suka ji kukan su Hannah ya cika ɗakin, tukunna suka soma ƙoƙarin fitowa, cikin tashin Hankali yasmin da ta hango kan azeeza dana jamima dake shirin fitowa ta ƙarƙashin gado, ta dinga girgiza musu kai alamar karsu fito su koma, da hannu ta dinga yi masu alamar su koma ƙarƙashin gadon.
Ƙwaƙƙwarar damƙa Angel ta kai ma wuyan Eve da Yasmin, ta juyar dasu su ka fuskanci bango, ta daddage ta buga kansu jikin sa, tuni jininsu ya wanke jikin bangon a ƙasa suka sulale kowannan su ba numfashi, Mayar da idanuwanta ta yi akan Sarah da Hanna da suka rage, Sai faman zazzare idanuwansu suke yi, Zufa ta ko'ina ta shiga tsastsafo musu, sai kuka su ke yi haɗi da yi mata magiya, Sai kewaye cikin ɗakin su ke yi, Ganin da gaske fa ba ƙyale su zata yi ba, hakan yasa Sarah ta watsa da gudu zata shige sashen toilet ɗinsu, sai dai kafin ta ƙarasa, Taji an damƙi ƙafafuwanta ruƙo bana wasa ba, Gaba ɗaya ta kife saman floor Kanta ya daku, ƙugun ta ya bada wani irin sauti ruƙuƙus.
Hanna ce ta yi saura a tsakiyar ɗakin, tsautsayi ya fiddo da jamimah, Karaf akan idon Hanna tana ƙoƙarin buɗe baki tace mata ta koma ƙarƙashin gadon, kwatsam Angel ta nufo wurin Jamima, tana tafiya tamkar damusa har wani gyara wuyanta take yi, tana lashe baki, da gudun gaske Hanna ta ɗauke jamima ajikinta ta ƙanƙame ta tana faɗin
"Dan Allah kada ki yi mata komai, Kin ga ita ƙarama ce na roƙe ki, idan ma bugun ne ki haɗa da nata ki yi mini, amma ki ƙyale jamima, zata iya rasa ranta....." kafin ta ƙarasa maganar, Angel ta ware hannayenta biyu ta yi masu ƙwaƙƙwaran ruƙo, da hannar da jamimar da ta rungume a jikinta, Dukkan su ta haɗa, ta cuccu6esu ta daddage ta maka su ga saman floor, nan hake haƙorin jamima ɗaya ya 6allo daga bakinta jaga jaga da jini, har saman kumatunta, kuka tamkar ranta zai fita, tuni ta saki fitsari ta cikin wandonta saboda tsabar raɗaɗin da ta ji.
Hannah da ke ruƙe da ita tuni ta sume, kunnuwanta ne suka dinga motsi suna jiyo mata shessheƙar kukan mutun, nan fa ta shiga neman wanene, Gadajen ta dinga bi tana ɗaɗɗaga su har Allah Ya kawo ta kan gadon da azeeza ta 6oye, Tana ɗaga gadon idanuwanta suka sauka akan azeeza da ke ta yin kerma ta ƙanƙame jikinta, sam ta kasa ɗagowa ta yi tozali da fuskar Angel.
Gyara wuyan ta ta yi kamar yana yi mata ƙaiƙayi har wani sauti ya bada muƙus, A tsananin tsorace Azeeza ta soma yin rarrafe don ta gudu daga wurin, aiko ta daddage ta ɗaura ƙafarta ɗaya saman yatsun hannun azeeza ta ta ke su ta murje duk suka faffashe, jini ya soma tsastsafowa, a nan ƙasa ta baje a sume, wata irin mahaukaciyar dariya Angel ta fashe da ita.
Sautin kukan jamimah daya karaɗe cikin ɗakin nasu ne ya janyo hankalin Angel kanta, ita kaɗai ce bata kai ga suma ba, Lashe baki ta yi tare da Nufar inda jamima take a kwance ƙasa cikin mawuyacin hali, Kafin ta ƙarasa gare ta ta ji an damƙi ƙafafuwanta, Sai dai wanda ya ruƙe ƙafafuwan nata, ya gaza Kifar da ita ƙasa saboda tsabar ƙarfinta.
A sukwane ta jiyo da kanta don taga wani isasshen ne Wannan mai ƙarfin halin, Karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar Deeja wadda hawaye suka wanke ta, muryarta cikin shessheƙar kuka ta ke faɗin Angel kin bamu mamaki yau ke da kan ki ki ke neman kashe mu, ashe dama ba ƙaunar mu ki ke yi ba, ban ta6a tunanin zaki iya raunata wani a cikin mu ba....."
Ɗaga ƙafarta ɗaya ta yi da niyar ta murje kan deeja da ƙarfi deeja ta ambaci"La'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! " shi kaɗai ne abunda ta iya furtawa la66anta na kerma.
tamkar an daki kanta da guduma, haka ta sanya hannayenta biyu ta daddafe kanta, wani irin jiri ta soma gani acikin idanuwanta, muryarta na rawa ta shiga ambaton
"La Hawla Wala Quwwata Illa Billah" Jikinta ne ya soma jijjiga, ta runtse idanuwanta saboda wata irin sarawa da kanta ke yi mata, Deeja nata kallonta, tangal tangal ta soma yi zata faɗi ƙasa.
Allah sarki duk da irin abunda ta yi musu hakan bai hana Deeja yunƙurawa ta miƙe tare da yin saurin tallabo Angel don kada ta faɗi ƙasa ta bugu, A hankali ta zaunar da ita, tare da zuƙunnawa gefenta, tana ambaton sunanta cikin sanyin murya ta wanda ya karaya"Angel, Allah yasa kin dawo hayyacin ki, Ni nasan ba yin kan ki bane" Tana magana hawaye nabin fuskarta, hannayenta tallabe da Angel, tsawon lokacin tun sautin kukan jamima na fita da ƙarfin shi har yakai ga disashewa, a ƙarshe ma ta sume, yanzu su biyu ne su ka rage a cikin ɗakin masu numfashi.
Muryarta ƙasa ƙasa ta soma magana"idan har dagaske ne abunda ya faru ba mafarki ba, Deeja ki kashe ni, kawai in mutu, meyasa na aikata ma ku hakan? Da hannayena nabi kowannanku da jahilin bugu, duk da irin haƙurin da ku ke bani amma naƙi sauraron ku, saboda rashin imani........'
girgiza kai deeja ta shiga yi tana faɗin
"ba laifin ki bane Angel, Ba yin kan ki bane, ko a mafarki bana tunanin zaki iya yi mana hakan balle kuma a zahiri......"
raba jikin ta ta yi daga na Deeja ta yunƙura ta miƙe jiki ba ƙwari take bin kowani 6angare na ɗakin su da kallo, bakomai ta ke gani acikin idanuwanta ba face jinin su, gasu nan a kwankwance kamar gawawwaki,
Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Lamarin ya yi matuƙar girgizata, kamar mahaukaciya haka ta shiga bin hannayenta da kallo, Acikin zuciyarta kuwa tsantsar tashin hankali ne da fargaba, lokaci ɗaya ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, da gudun gaske ta nufi bangon ɗakin su, Deeja ta miƙe da hanzari tabi bayanta, Daddagewa ta yi ta dinga buga kanta jikin bango da niyar ta kashe kanta, bugu bana wasa ba, Goshinta da hancinta dukansu sai da suka faffashe, Zallar jininta jawur dashi ya dinga gangarowa ta saman goshinta yana wanke fuskarta, hatta la66anta bata bari ba, cizonsu ta dinga yi da haƙoranta duk ta gurgujesu, jini ya dinga tsargowa, duk yadda Deeja taso ta janye Angel daga jikin bangon abun ya faskara, Saboda bata acikin hayyacinta, takai maƙura, idanuwanta sun makance kunnuwanta basu ji, mutuwa kawai take son ta yi awannan lokacin, ta tsani kanta, tsana mara misaltuwa, zuciyarta tagama hasala.
Cikin muryar kuka Deeja ke roƙonta tana faɗin ta yi hakuri tadaina cutar da kanta, saboda ba yin kanta bane abunda ya faru, tace Angel ki tsaya in yi maki bayanin abunda ya faru, kada ki kashe kan ki don Allah, idan ki ka mutu kika barni ya ki ke so inyi da raina, mu kaɗai fa muka rage da zamu iya taimakon ƴan uwan mu da su ke acikin mawuyacin hali, Ki tausayamin Angel, wayyo Allahna, Ya Allah ka kawo mana ɗauki, wannan wata irin masiface! Zubewa ta yi a saman gwiwowinta, ta ci gaba da kuka hannunta dafe da goshinta.
Angel kuwa bayan tagama Wanke fuskarta da jikin jikinta, Jiri ne ya ɗebe ta, ta sulale ƙasa babu numfashi, kafin wani lokaci ɗakin nasu yai tsit, baka jin sautin hayaniyar komai, Ko'ina ka kalla a cikin ɗakin, Jinin su ne, ita kanta Deeja da ta rage idonta biyu, A gefen Angel ta kwanta idonta arufe, busassun hawaye ta ko'ina akan fuskarta, kukan zuciya take yi mai raɗaɗin haske, batasan ya za ta yi ba, ita kaɗai ta rage taya zata iya ceton rayuwar ƴan uwansu? Ita kanta ba ƙoshin lafiya gare ta ba, don ba ƙaramin dakuwa kanta yai ba, lokacin da Angel ta bugata ga ƙasa har ta sume, Allah ne ya farfaɗo da ita harta tashi.
Cikin zuciyarta ta soma magana
_Ya Allah bamu da kowa face kai da ka halicce mu, Angel itace silar da muka san komai agame da mahaliccin mu, ta faɗa mana cewa kana ƙaunarmu kamar yadda ka ke son sauran bayin ka, kana ganin mu kuma kafi kowa sanin halin da muke aciki, mun yi imani da kai, duk da bamu da wadataccen ilmi akan ka, Ya Allah ta tausaya mana kaji ƙan mu, ka kawo mana ƙarshen wahalar nan, rayuwar mu a ƙuntace ta ke, bamu ta6a cutar da wani ba amma mu ana azabtar da rayuwar mu, babu mai taimakon mu, babu wanda yasan da zaman mu balle a kawo mana ɗauki, muna ji muna gani ana neman halaka mu saboda rayuwar mu bata da amfani awurin su, Bafa sune silar zuwan mu duniya ba! Mu ba bayin su bane, bayin ka ne Ya Allah! Baka halicce mu don a azabtar da rayuwarmu ba face don mu bauta maka, amma meyasa waɗannan mutanan suke ƙoƙarin mayar damu dabbobin su, Ya Allah idan har dagaske kai maji roƙon bayin ka ne, Ya Allah kajiƙanmu kaji koken mu, ka kawo mana ɗauki, koda ranmu ne ka ɗauka mu koma gare ka, zaifi mana sauƙi akan wannan wulaƙantacciyar rayuwar da muke yi mara ƴan ci, Ya Allah badan halinmu, mu ci albarkacin Annabin mu Annabi muhammand (SAW) mafi soyuwa agare ka_.........."
sosai ta runtse idanuwanta, ta yi zurfi acikin zancen zucin nata, ta soma jin motsin buɗe ƙopar ɗakin su acikin kunnuwanta, wani irin tsoro da firgici ne ya lullu6e ta, hakan yasa taƙi buɗe idanuwanta don taga wanene
Takun tafiyar mutun ta soma ji a cikin ɗakin nasu, kamar ana kewaye ɗakin, ji take kamar ta buɗe idanuwan nata sai dai tsoro ya hana tayi hakan, tana cikin wannan Halin taji wani irin matsiyacin bacci yana fisgarta, na ban mamaki, duk yadda taso ta tsayar da kanta don kada ta runtsa hakan ya faskara don tuni yai awon gaba da ita anan inda ta ke a kwance, Tsawon lokaci Deeja tana sharar baccinta, Har dare ya nutsa, hasken saman ɗakinsu ya ɗauke Na floor lamps ɗinsu Ya kunna kanshi, Haskensu ya gauraye ko'ina tamkar da rana.
A matuƙar firgice ta farka tare da ware manyan idanuwanta kan ceilling ɗin ɗakin, Zuciyarta na harbawa sama sama cike da fargaba, tunawa da ƴan uwanta ne yasa tai wuf ta miƙe a zaune, wani iko na Allah Kaf ɗinsu babu wanda ke kwance a ƙasa sai ita, duk suna asaman gadajen su, tamkar wani abu bai ta6a faruwa ba, babu ɗigon jinin mutun ɗaya daya kasance a cikin ɗakin, an goge komai babu shi, ɗakin ya koma fes ɗin shi, tsabar mamaki ne Yasa ta miƙe Jiki na kerma ta ke bin kowani gado da kallo, bacci su ke yi Hankali kwance, Jikinsu lullu6e da bargunan su, da sauri ta kalli gadon jamimah, tana a kwance Ga azeeza itama kwance saman nata gadon, Haka zalika parveen da rubina, eve and yasmin, suna kwance saman nasu gadajen Hada Sarah da hibba, uwa uba, Angel itama tana naɗe cikin bargonta tana bacci, kaɗan daga cikin ikon Allah kenan, wannan bakomai bane,
Jikinta na kerma ta nufi gadon Angel ta sanya hannu tare da yaye bargon jikinta, don taga idon raunin goshinta na nan, babu jini akan fatar fuskarta, sai dai akwai alamun fashewar goshinta dana tsinin hancinta, sai la66anta, yanayinta ya nuna alamar cewa babu raɗaɗin ciwo atattare da ita, kamar an kwashe mata shi,'
sakin bargon Angel ta yi tare da juyawa da sauri ta nufi gadon jamima, hannu tasa tana duba fuskarta itama babu jini, tunawa ta yi da haƙorinta data gani ɗazu a ƙasan ɗakin su, koda ta buɗe bakin ta, tabbas haƙorin ta ɗaya ya cire, sai dai babu kumburi abakinta, lamarin ya ɗaure mata kai, mamaki ne ƙarara akan fuskarta.
matsawa ta yi zuwa gadon Azeeza ta yaye bargonta tare da leƙa fuskarta, ko hawaye babu, yatsun hannayenta dai ne da suka faffashe, amma babu jinin daya tsastsafo akansu, idan ka kalli ciwon kamar ya kwan biyu.
Ɗaya bayan ɗaya saida Deeja tabi kowannan su ta duba shi, lafiyar su ƙalau, Babu ko zazza6i a jikin su.
Deeja ta ruɗe sosai ta rasa tunanin me za ta yi game da wannan iko na Allah, har aranta ta aminta da cewa Allah ne ya ji ƙansu ya kawo musu ɗauki, sai dai ba ta san takun tafiyar wanene taji ɗazu ba, a cikin ɗakinsu, tabbas akwai wanda ya shigo.
"Ruwa zan sha, maƙoshi na zafi"! Muryar Angel ce ta fargar da ta, a hanzarce ta mayar da dubanta gare ta, farkawarta Kenan daga bacci, Ko idonta bata buɗe ba, a gaggauce Deeja ta nufi ƙarƙashin gadon Batul ta ɗauko ɗaya daga ciwon bottle waters ɗin da Su Jamima suka 6oye musu ɗazu, ta nufi gadon Angel ta haye sama tare da taimaka mata ta miƙe zaune, bayan ta buɗe murfin ta kafa mata abaki, ta dinga kur6ar ruwan,'
Hankalin Deeja ba ƙaramin kwanciya yai ba, bayan ta kammala ta maida murfin robar ruwan ta ajiyeta daga ƙasan gadon, kafin ta ɗago idonta akan fuskar Angel dake ƙoƙarin buɗe nata idanuwan.
Ido cikin Ido suke kallon Juna ita da Deeja, muryarta na ɗan rawa ta furta"Ina Danish ya ke"! Abunda ya fito daga bakinta kenan, fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa ta amsa mata da cewa"Har yanzu ba a dawo dashi ba" girgiza kai Angel ta yi"ba'a dawo dashi ba, meyasa naji a jikina cewa danish ya ta6a ni!" A ruɗe Deeje ke kallonta, Jin abunda tace, tunani ta shiga yi anya Angel bata samu ta6in hankali ba?
Da alama ta manta abubuwan da su ka faru, ta manta jahilin bugun da tayi musu, kamar wadda tayi loosing memory ɗinta.
Ganin yadda Deeja ta tsareta da ido yasa tace"meyasa kike kallo na? Wani abu ya faru ne? Nayi ma ki tambaya baki bani amsar da zata gamsar dani ba, nifa naji Danish Ya ta6a jikina, taya zaki ce min ba a dawo dashi ba'? A ruɗe ta yi mata maganar.
Deeja bata amsa mata tambayarta ba, saima ta sanya tafin hannayenta biyu ta tallabo fuskar Angel, murmushin yaƙe ne ya bayyana akan fuskarta wanda bai kai zuci ba, a hankali ta furta Alhamdulillah, Allah na gode maka, daka kawo min mafita, da yanzu bansan ya zan yi ba, Naji daɗi dana ga ƴan uwana suna bacci cikin kwanciyar hankali, na ƙara yarda cewa addinin musulunci gaskiya ne, Kuma ubangijin mu Allah maji roƙon bayinsa ne, idan su ka yi imani dashi, babu tantanma zai agaza musu a lokacin da suke cikin buƙatar taimakon shi.
da alama taji daɗi sosai, da irin taimakon da Allah ya yi musu, daba don haka ba, da yanzu batasan awani awani hali zasu tsinci kan su ba, domin kuwa ba ƙaramin jiki zasu ji ba, Jinya ce zasu yi bata wasa ba, sai kowa yaji a jikin shi, musamman Jamima da haƙorinta ya 6alle, da kuma Sarah wadda aka buga ta da ƙasa qugunta ya daku, da sauran waɗanda aka buga kansu jikin bango.
"Deeeja na kasa fahimtar komai, dan Allah ki yi min bayani, inaso inji meya faru ne, naji araina kamar wani abu ya faru, sai dai na kasa tunawa......" da sauri Deeja tace"in sha Allah ba za ki tuna ba"
Maganar Deeja ta ɗaure mata kai, yunƙurin saukowa tai daga saman gadonta, da sauri Deeja ta ruƙo hannunta"Ina zaki je? Dare ne fa! Ki koma ki kwanta" ba tare data juyo ta kalle ta ba, tace"Toilet zan shiga" Jin haka yasa Deeja sakin hannunta, Hankalinta bai kwanta da kalaman deeja ba, shiyasa tace mata za ta shiga toilet ne don ta samu damar ƙarewa ɗakin nasu kallo, duk don ta samu ta tuna abunda ya faru, don ta fahimci cewa akwai wani abu da take 6oye mata.
Tana ƙarasa saukowa daga saman gadon, kaitsaye idanuwanta suka sauka akan shimfiɗar su Haris, nan take taji gabanta yai wani irin bugu na tashin hankali, ganin babu kowa asaman gadajen su, sai bargunansu da matashin kansu, babu haris babu naufal babu javed da mubeen.
A fujajen ta waiwayo tana fuskantar gadajensu Sarah, Tsayar da idanuwanta ta yi akan shimfiɗar Gabriel wayam babu kowa saman gadon shi, zuciyarta a hautsine ta wurga eye balls ɗinta kan gadon Majnoon, babu kowa, tsabar ruɗanin da ta shiga ya hana ta furta komai, Tuni deeja ta lura da yanayin da ta shiga.
saukowa ta yi daga saman gadon, ta nufi Inda Angel ta ke atsaye ta ɗaura hannunta ɗaya saman kafaɗarta, idanuwan ta acike tab da ƙwalla ta soma magana
"Ko ban faɗa maki ba, nasan kin riga da kin fahimci komai, abunda zuciyarki take faɗa maki gaskiya ne ba ƙarya ba, sai dai inaso mu rungumi ƙaddarar mu, mu yi haƙuri mu daure, tun da ko munyi kukan ba abunda zai haddasa mana face ciwon kai, damuwa bazata ta6a sanyawa adawo mana da ƴan uwan mu ba, haƙurin nan dai shine magani, Gaba ɗaya maganganun dana faɗa maki ayanzu, a wurinki na saba jinsu, don haka ina roƙonki, kada kice zaki sanya damuwa aranki, dama ba ƙoshin lafiya gare ki ba, kuma kinga ƴan uwan mu suma suna acikin mawuyacin hali, mune kaɗai muka rage waɗanda za su iya kwantar musu da hankali, idan ba haka ba, dukkan mu zamu fuskanci matsala ne........." tun kan ta ƙarasa maganar, Angel ta daddafe kanta saboda wani irin jiri da ta ke gani, ba arziƙi ta zunna ƙasa ta yi zaman cin tuwo, yayin da hawaye masu ɗumi ke bin fuskarta.
"Deeja ki faɗamin! Meya faru dasu Haris? Tafiya aka yi dasu ne? Inaso na sani"! Daƙyar take magana cikin raunin na murya.
Ita kanta Deeja