Header Ads
Showing 246001 words to 249000 words out of 287659 words

Chapter 83 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1777

Ads at the middle of Article

data uwa da ɗanta, ji take kamar ciki ɗaya suka fito da batul.

Sarah da ke a tsaye tun ɗazu tana kallonsu, bata furta komai ba, sai dai da alama itama ta tayasu kukan don hada hawaye kan fuskarta, bakomai ne ya ta6a zuciyarta ba, face yarda taga sunata kuka, da kuma yarda Angel ta ƙanƙame ƴar uwar ta su a jikinta, hakan ya tabbatar mata da irin son da su ke yi mata, duk da batasan wacece batul ba, amma tana yawan jin suna ambaton sunanta, ta shaida irin ƙaunar da suke yi mata, ba ƙaramin burgeta su ka yi ba.

"Angel har yanzu bata farka ba? Ya za'ae muna so musan awani hali take ciki, A ƙagare muke da mu rungumi ƴar uwar mu, muji ɗuminta a jikin mu, tsawon lokaci bama a tare" Deeja ce tai magnar, fuskarta a yamutse don hankalinta ba'a kwance yake ba.

Dare ya koma masu tamkar da rana, babu mai jin bacci a cikin su, dama sun sha bacci yau.

"Bari na ɗebo ruwa a yayyafa mata ko mun samu ta farka" acewar rubina, kafin tayi yunƙurin mikewa Yasmin ta dakatar da ita ta hanyar yi mata magana"ai ba suma tayi ba, bacci ta ke yi, bana so mu takura mata, tunda tana nunfashi mu jira har zuwa time da zata farka"! Fasa zuwa ɗebo ruwan rubina tayi,
Cikin sanyin murya parveen tace"Allah yasa kada ta farka tana jin yunwa, wlh da ace mun san yau za'a dawo mana da ita, ai da mun ajiye mata abinci dayawa," ta yi maganar tana matse ƙwallar idonta, ɗakin yai tsit masu yin shessheƙar kukan duk sun dakata.

Sun yi zugudum kamar masu zaman makoki, kowa da abunda yake saƙawa a cikin ranshi dangane da tsintar batul da su ka yi a cikin su, Damuwace ƙarara akan fuskokinsu, fatansu Allah yasa ba acutar masu da ita ba, duba da irin baccin da take yi mai nauyin gaske, deeja ce tai tunanin yi magana akan suje su kwanta.
"Yakamata kuje ku kwanta ku yi bacci, dare ne sosai, nasan kafin gobe da safe in sha Allah zata farka......" tun kan ta kai ƙarshen maganar, su ka haɗa baki wurin cewa"ai bazamu iya runtsawa ba, idan har ƴar uwar mu bata farka ba, kusan wata uku bamu atare da ita, till today aka dawo mana da ita, Ta yaya kike tunanin zamu iya yin bacci? Ba tare da mun gana da juna ba"

Ita kanta Deeja ta yi masu maganar ne kawai, don tasan ba kwanciyar za su yi ba, duk wannan maganganun da suke yi Angel bata fahimtar su, domin kuwa hankalinta na akan batul ɗinta, dake kwance saman ƙirjinta, ta natsu tana sauraron bugun zuciyarta, sai faman lumshe idanuwanta ta ke yi, waɗanda suka canza launi saboda kukan da tasha, har yanzu hawayen basu daina gangarowa ta cikin idanuwanta ba.

"pls Angel ki kwantar mana da ita, yadda zamu samu damar ganin fuskarta da kyau, munyi kewarta sosai" Acewar eve, shiru Angel bata motsa ba, babu alamun zata kwantar da ita, hannu Deeja ta kai saman bayan Angel ta ɗan bubbugata don ta dawo hayyacinta.

"Angel muna son ganin fuskarta, ki kwantar mana da ita" deeja ce tai maganar, still bata tanka masu ba.

"Ko dai ta yi bacci ne"? Hibba ce tai tambayar, Sarah dake a tsaye ta matso kusa da gadon, ta sanya hannayenta biyu da niyar ta raba jikin batul daga na Angel, amma ta kasa, Lamarin ya ɗaure masu kai, suka dinga kiran sunanta taƙi amsa masu, kuma ba bacci ta ke yi ba.

Parveen da Deeja ne suka haɗa hannu wurin ƙoƙarin 6an6are batul daga jikinta, abun ya ɗaure masu kai, yadda taƙi sakinta, kamar su fashe da kuka saboda yadda suka ƙagara da son ganin fuskarta.

"Bani na ruƙe ta ba, itace ta ruƙe ni"

Muryar Angel ce ta yi masu magana, abunda basu sani ba, tun lokacin da Angel ta rungumo batul a jikinta ta farka daga baccin, koda taji jikin ƴar uwarta ne, ta ƙanƙameta sosai, hannayen batul na abayan Angel ta zagayo da su, sumar kan Angel ce ta rufe su shiyasa basu lura da cewar itace ta matse ta a jikinta ba, tun da farko da su ka buƙaci ganin fuskarta, Angel tai ƙoƙarin sakinta, sai dai ita batul ɗin taƙi bari ta raba jikinta daga nata, that mean batul ta farka daga bacci tuntuni.

Sun yi mamakin jin abunda Angel tace masu, na cewa itace ta ruƙeta, muryar Deeja a sanyaye tace"Batul, idan kina jin mu ki juyo ki fuskance mu, mu ma minyi missing ɗin ki sosai, muna buƙatar mu yi hugging ɗin ki a jikin mu......."

Kafin Deeja ta rufe bakinta, batul ta zame hannayenta daga ruƙon da ta yi ma Angel, kamar bata son raba jikinta daga nata, slowly ta zame kanta daga saman kafaɗar Angel, ta ɗago da kanta, yayin da ta ke ƙoƙarin buɗe idanuwanta kamar sunyi mata nauyi.

Angel sai kallonta ta ke yi, hatta su parveen sun zagayo ta inda zasu dinga ganinta da kyau, a wani irin yanayi ta buɗe kyawawan idanuwanta akan fuskar Angel da ke kallonta kamar zasu haɗiye juna, tun daga kan kallon da ta ke yi mata zai tabbatar maka da cewa ta yi matuƙar yin kewarta, ta yi kukan rashinta atare da ita, A hankali ta ɗauke idanuwanta daga kan fuskar Angel ta mayar dasu kan fuskokin su Deeja, Ɗaya bayan ɗaya take ƙare masu kallo kamar yau ta fara ganin su, haka suma su ke ta kallonta kamar sun samu tv, tambayoyi suka shiga jera mata kamar ƴan jarida


"Batul kina lafiya? Babu abunda ke damunki? Kin gane mu kuwa? Meyasa kike ta kallon mu! Ba zaki iya magana ba? Ko akwai inda ke yi maki ciwo? Dan Allah ki yi mana magana, mun damu dake sosai, munyi kewarki, munyi kuka rashinki kamar mu zauce........" suna magana hawaye na bin fuskokin su, basu yi tsammanin zata tanka masu ba.

Tausasan la66anta ta soma motsawa muryarta a sanyaye ta soma ambaton sunayensu ɗaya bayan ɗaya

Angel, Hannah, Hibba, Deeja, Parveen, Eve, Yasmin, Rubina," tsabar farin ciki yasa suka fasa ihu Jin ta kira sunayen su hakan na nufin Tana acikin hayyacinta, wani irin farin ciki ne ya lullu6e Su, kamar waɗanda akayiwa albishir da mukullin fita daga cikin kurkukun ƙaddara.

Tana so ta bayyana masu irin kewarsu da tayi sai dai takasa magana, saboda hawayen da suka ciko idanuwanta, daƙyar ta iya buɗe masu hannayen ta tare da yi masu alamar su matso kusa da ita, da sauri suka matsa ta haɗa azeeza da parveen da deeja ta rungumesu, sai lokacin ta samu damar fitar da kukan da take 6oyewa, sosai ta fashe masu sa ku ka, suma kukan suke yi an rasa me lallashin wani acikin su, ta ɗauki tsawon lokacin kafin ta saki su deeja, ta miƙa masu Hibba hannu suka matso suma ta rungume su a ƙirjinta, dukkan su saida suka ji ɗumin jikinta, da hannayensu suka dinga share mata hawayen dake akan fuskarta, itama ta sanya hannunta tana share ma kowannansu na kan fuskarshi.

Cikin sanyin murya ta furta"ashe da rabon mu sake ganin juna nida ƴan uwana! ashe mafarkina zai zama gaskiya na sake yin rayuwa a cikin ku? Jan numfashi tai kafin taci gaba da cewa"duk yadda zan faɗa maku irin kewarku da nayi ba zaku fahimta ba, haukane kawai banyi ba, amma naji jiki na rashin ku atare dani, na zubar da hawayena kamar bazan rayu ba, Allah ne kaɗai yasan irin raɗaɗi da ƙuncin da na shiga........" kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan daya ciyota, da sauri Angel ta sanya hannayenta biyu ta dafa shoulders ɗinta tana lallashinta.

"Batul ki daina kuka dan Allah, kuma ku daina zubar da hawayen ku, godiya yakamata mu yi ma Allah daya dawo mana dake lafiya, duk da naga sauyi atattare dake, bamu san ina aka kaiki ba! Me a ka yi maki na tsawon watannin nan! Na yi maki tambayoyin nan ne saboda su ne damuwar mu, amma bamu buƙatar amsar su ayanzu, saboda kwanciyar hankalin ki mu ke so, ashirye mu ke da mu sanyaki farin ciki, wanda zaisa ki manta da duk wata damu da kika shiga na rashin mu atare dake,"

Kalaman Angel ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, atare suka ɗaga hannayensu sama suna yiwa Allah godiya haɗi da yi ma ƴar uwarsu batul addu'a, duk tana sauraronsu, wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, bayan sun kammala yi mata addu'ar ne, ta ɗago da kanta daga jikin Angel, Ganin tana kallon gadajensu Danish yasa duk suka sha jinin jikin su, aruɗe take ƙare masu kallo, abun da basu ta6a tsammanin zata tambayesu ba, sai ji su ka yi tace"Ina Danish!" shine mutun na farko da ta fara tambayarsu, sun yi mamakin hakan duk irin abunda yayi mata, cigaba da tambayarsu ta yi cikin ruɗu.

"Meyasa bangan su asaman gadajen su ba? Ina Haris ina Javed da Mubeen da Naufal? Ina su ka je ne? Ko sun shiga toilet ne"?

Angel ce ta yi mata magana"ki yi haƙuri batul, zuwa gobe da safe zamu faɗa maki komai, yanzu dare yayi sosai, ki kwanta ki huta ," ta yi maganar tare da ruƙota, ta kwantar da ita tare da janyo bargo ta lullu6a mata shi saman jikinta zuwa ƙirjin ta.

Ta yi mata hakan ne duk don ta kawar mata da tunaninta, na tambayarsu agame da su Haris.

Mayar da dubanta ta yi gasu Deeja"Ku je ku kwanta, Zuwa gobe za mu yi magana da ita" Ba don sunso ba suka miƙe kowa ya nufi tsohon gadon shi, duk don saboda ita suka kwanta saman su yau, itama sarah ta nufi shimfiɗarta ta kwanta, zuciyarta cike da saƙe saƙe dangane da ƴar uwarsu batul da ta gani yau, da alama akwai wani abu daya ɗan sha mata kai.

Mutun biyu ne ya rage Azeeza dake zaune saman gadon batul, sai jamimah dake zaune gefen gadon sai gyangyaɗi ta ke yi kamar zata faɗo ƙasa.

"Azeeza taso muje in raka ki ki kwanta," maƙe kafaɗa Azeeza tayi tare da cewa"Inaso na kwana a gefen batul" shiru Angel ta ɗanyi tana kallon fuskarta, taci burin ta kwana tare da batul dinta, ga Azeeza ta nuna tanaso.

Ita kanta batul ɗin, bata son Angel tabar gadon nata, sai satar kallon juna su ke yi, da alama akwai wani abu daya ɗaure masu kai agame da canjin da kowan nan su ya yi, Sai da Angel ta ruƙo azeeza ta kwantar da ita gefen batul, tukunna ta sauko daga saman gadon, still idon batul akan fuskarta.

"Zanje na kwanta, ki kulamin da kanki, gobe zamu yi magana" ta ƙarasa maganar tana sakar mata murmushi. lumshe ido batul ta yi tare da ɗan jinjina mata kai, hawaye ne masu ɗumi suka soma gangarowa ta cikin idanuwan nata, nan take Angel taji gabanta ya faɗi, sai dai bata tambayeta hawayen menene ba, ta bari sai zuwa gobe su yi magana.

kasa tafiya tayi, komawa tayi daga gefen gadon ta ɗan zauna tare da duƙar da kanta saitin fuskar batul, ta manna mata kiss saman forehead ɗinta da cheek nata, a hankali batul ta ɗan ware idanuwanta tana duban Angel wadda tuni ta miƙe daga gefen gadon, sai da ta fara ɗaukar jamimah, kafin ta juya ta kwantar da ita saman gadon Danish itama ta kwanta daga gefenta tare da rungume jamimah a jikinta, sai kallon juna suke yi ita da batul da ke akwance saman gadonta, Da yake suna fuskantar juna.

Tsawon lokaci sunata ta kallon juna, ɗakin yai tsit baka jin sautin komai, sun ƙi bari bacci ya ɗauke su, gani su ke yi kamar in suka runtsa za'a ƙara zuwa a ɗauke masu ita, zuciyoyinsu a cike suke da tambayoyi iri iri da suke son su yi mata, idan gari ya ware, sun kwana da wadataccen farin ciki acikin zukatansu saboda dawowar ƴar uwarsu batul, kaɗan daga cikinsu ne suka samu damar tuntsawa.

❤PRISONERS💖

A washe garin ranar tun da sassafe, ta soma jin hayaniyarsu a cikin kunnanta, muryoyinsu da alamun farin ciki atattare da su, a hankali ta ɗan buɗe idanuwanta, biji biji ta fara ganinsu a kewaye da gadonta, har saida ta ɗan firgita, daga bisani ne idanuwanta suka dawo normal taga fuskokinsu a washe sai murmushi suke sakar mata, azeeza da ke a gefenta kwance, ta ɗan tada kanta saman gwiwar hannunta, ta ƙura mata ido sai kallonta ta ke kamar zata lashe ta.

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah! Allah mun gode maka daka dawo mana da ƴar uwar mu batul, Nifa jiya da daddare dana kwanta, gabana ya dinga faɗuwa gani nake kamar in na runtse idanuwana zan farka inga babu batul ɗin mu" Deeja ce ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushin farin ciki.

Parveen tace"wlh nima haka naji araina, shiyasa yau da safe ina farkawa nai wuff nazo gaban gadonki don in duba in ga ko kina nan" ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskar batul, ta rasa akan wa zata tsayar da idanuwanta, sai faman jujjuya eye balls ɗinta ta ke yi akan faces ɗin su.

"Ni kaina da mafarkin ki na kwana, ƴar uwata rabin raina" da sauri ta wurga eye balls ɗinta kan fuskar Angel wadda zuwanta kenan, Tana agefen Hibba, wani murmushin ne ya ƙara bayyana akan fuskarta, wanda ke nuni da irin farin cikin da take a ciki.

"Fatan ba mu takura maki ba, mun tada ki daga bacci, wlh mun yi kewarki ne kamar mu zauce" acewar hibba, calmy ta soma magana"Nafi so ku takura min hibba, aini abunso ne a wurina, in gan ku atare dani, ko na minti ɗaya bana son wani a cikin ku ya nisanta dani, ba dan ƙaddara ta rabani da ku ba, ku kan ku kun sani, da ƙafafuwana bazan ta6a yin nesa da ku ba" muryarta na ɗan rawa ta ƙarasa maganar, tuni idanuwanta suka cicciko da ƙwalla, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyarta.

"Batul pls don't cry, idan har ba so kike zuciyoyin mu su raunata ba, mun fi buƙatar farin cikin ki ayanzu, ki daure pls," Deeja ce tai maganar, lumshe idanuwanta ta ɗanyi yayin da take binsu da kallo, su kansu sun fahimci akwai wani abu dake damunta.

"Azeeza irin wannan kallo haka, " daƙyar ta furta maganar, tana kallon azeeza, murmushi ta sakar mata tare da cewa"Ƙaunarki nake yi batul, dole in kalle ki don baki san irin kewarki da nayi ba. Kamar in haɗiye ki" tayi maganar tana wage bakinta, Hakan da ta yi ba ƙaramin dariya ta basu ba.

Ita kanta batul ɗin saida ta ɗan murmusa, a hankali ta yunƙura ta miƙe, itama azeeza ta miƙe zaune saman mattress ɗin, Saukowa ta yi daga saman gadon taci gaba da tafiya tana bin ɗakin nasu da kallo, ganin irin sauye sauyen da a ka yi mashi, gaba ɗaya suka bi bayanta suna tafiya atare da ita, dakatawa tayi da yin tafiyar tare da juyowa ta kallesu tace"Jiya na tambaye ku amma ba ku bani amsa ba, ina Danish dasu haris su ke ne"? Deeja ce tai ƙarfin halin faɗa mata cewa anzo an tafi dasu almost one week, An riga tafiya da Danish," iya abunda ta sanar da ita kenan, bata faɗa mata awani hali aka tafi da shi ba, jinjina kanta ta yi ba tare da tace komai ba, sai dai fuskarta ta nuna alamun damuwa, kuma idanuwanta hawaye ne acike dasu.

"An kawo mana sabbin prisoners ne? Jiya kamar naso inga wata ƙaramar yarinya," tai tambayar tana kallonsu "naga kuma sabbin gadaje, kusan goma sha biyar" yasmin ce ta bata amsa dacewa"Eh, bayan tafiyarki aka kawo su, Amma mutun biyar ne prisoners ɗin, sai dai daga cikinsu Giants sun tafi da mutun uku, yanzu biyune atare damu. jamimah itace ƙaramar sai Sarah," ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa"ku bani labari mana, dame dame ya faru bayan bana nan"? A taƙaice Angel ta sanar da ita duk wani abu da ya faru bayan bata nan sai dai bata faɗa mata wanda zai sanyata damuwa ba.

"Mu koma mu zauna batul," yasmin ce tai mata maganar, ganin sai yawo su ke yi cikin ɗakin, ga shi daga gani jikin nata babu ƙwari, ga ƴar guntuwar rigar dake a jikinta sai ɗagewa ta ke yi.

"Kina jin yunwa" parveen ce tai mata tambayar, ɗaga mata kai ta yi alamar eh, langwa6e kai parveen"wayyo Allah, ga shi babu abinci sai giants sun kawo mana" ƴar dariya Batul ta saki kafin tace"Ki kwantar da hankalin ki, kallon ku da na ke yasa naji na ƙoshi, babu wani yunwa atare dani,"

"Batul baki bamu labarin ina aka kai ki ba tsawon wata uku? Sannan waye ya dawo mana dake ko giant ne, mun ga kin canza mana sosai, kin rame kamar babu ƙoshin lafiya atare da ke" rubina ce tayi maganar,

Shiru ta ɗanyi kamar bazata amsa mata tambayoyin ta ba, duk su ka tsareta da ido suna kallonta, tun kafin ta fara magana Angel ta raya aranta cewa batul baza ta faɗa masu gaskiyar abunda ya faru da ita ba, ko dan kada ta sanya su damuwa.

A tsanake ta soma magana"bakomai ne zan iya tunawa ba, tun time da aka tafi dani, na dai san ba a cutar dani ba, ramar da ku ka gani a jikina bata komai bace face rashin ku atare dani, na tsinci kaina acikin wani ɗaki ina rayuwa ni kaɗai, ban rasa ci da sha ba, ana kawo min lafiyayyen abinci, ina yin wanka har ma in kwanta in yi bacci, mafi yawancin lokutta, ina yawan yin kukan rashin ku, in dinga ihu ina ambaton sunayen ku don kuzo ku ɗauke ni sai dai shiru babu mai jina........." iya abinda ta faɗa masu kenan, kuma sun yarda da maganarta, banda Angel, don koda tana basu labarin idonta akan Angel don tasan bazata yarda da ita ba, abunda yasa su deeja suka yarda da labarin da ta basu, saboda an dawo masu da ita ba kamar yarda aka saba dawowa dasu ba, Cikin mawuyacin hali, wasu ma basa a cikin hayyacin su.

"Batul yakamata kije ki yi wanka, akwai sabbin kaya da muka fada maki

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads