Showing 42001 words to 45000 words out of 287659 words
Chapter 15 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
zasu ɗauke shi bazan bari su rabaki da shi ba, idan suna son ɗa su haifi wani mana, wannan dai naki ne ke kaɗai........"
Jin kalaman mami yasa aneelerh ta tsagaita da yin kukan, ba ƙaramin daɗi taji ba, ɗagowa tayi daga kan pillow ta kwantar da kanta saman kafaɗar mami,
"Mami karki bari araba ni da baby junaid ɗina, wlh zuciyata zata iya bugawa" shafa sumar kanta mami tayi"ae me raba ki da shi sai ya shirya, Idan ma suka matsa number zanyi wa lawyer na magana," murmushi aneelerh ta saki saboda jin daɗin maganar, tasan mami tana son farin cikin ta, bazata so a bunda zai6a ta mata ranta ba
"Kada mu makara, ta shi kije kiyi sallah, shime babyn naki ki tada shi yaje ya yi sallah," dariya aneelerh tayi tare da saukowa daga saman gadon ta nufi toilet, mami nata kallonta har ta shige ta rufe ƙofar, ajiyar zuciya taɗan sauke dama ta faɗi hakan ne donta kwantar mata da hankalinta,
Juyawa ta yi tana kallon Junaid dake kwance sai sharar baccinsa yake yi, hannu takai ta shafa sumar kanshi" Grandson, Allah yabar mana kai," bargo taja ta lullu6e mashi jikin shi, yaron ba ruwanshi sam baida damuwa, ga nauyin bacci da Allah ya yi mashi, shifa ba ƙaramin abu ke tada shi daga bacci ba,
Saukowa mami ta yi daga saman gadon ta fuce daga ɗakin zuwa nata ɗakin domin tayi sallah,
Fitarta keda wuya aneelerh ta fito daga toilet, shaf shaf ta canza rigar baccin jikinta zuwa Jallabiya, ta ɗauko hijabi ta zura a jikinta, ta koma saman darduma ta kabbara sallah a tsanake ta shiga yin ibadarta,
Bayan ta kammala yin sallar saman darduma ta zauna tana yin tasbihi, hannunta ɗaya ruƙe da cazbaha, bayan ta kammala tayi azkhar, kafin ta ɗaga hannayenta sama ta soma yi masu Angel addu'a, Yayin da hawaye ke bin fuskarta,
"Ya Allah kafi kowa sanin a wani hali waɗannan bayin naka suke ciki, ya Allah ka tsare su da tsarewarka, Ya Allah ka kare su daga sharrin mutun sharrin aljan da sharrin duk wani abin cutarwa, Ya Allah idan har suna araye ya Allah ka bayyanar mana da su, idan kuma......kasa ƙarasa addu'ar ta yi, sam bata so ta ambaci mutuwa, tuni idanuwanta sun cicciko tab da kwalla, lumshe idanuwa ta ɗanyi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata fuskokinsu, Uzair taj da kuma Angel,
Ta yi nisa acikin tunaninta, Sautin kukan Junaid ya farkar da ita, ajiye cazbahar tayi saman dardumar ta miƙe da sauri ta nufi saman gadon, yana ganinta ya dakata da yin kukan ya tsareta da manyan idanuwanshi, murmushi tasakar mashi sai gashi shima ya sakar mata murmushi,
Cire hijabin jikinta tayi tare da ninketa ta ɗaura saman mattress ɗin, hawa saman gadon tayi tare da kai hannu ta ɗauke shi jan hancin shi tayi"i know u are not hungry rigima ce kawai ko"? ta6e tausasa la66ansa yayi alamar zaiyi kuka, dariya tasaki tare da cewa"stop crying my baby boy, shagwa6a66an yaro na" a gefen gado ta zauna tana shayar da shi, bayan ta kammala ta zaunar da shi, takai hannu ta ɗauko hoton su angel dake ajiye saman drawer,
Su haɗu ne a haton ranar birthday ɗin Angel a kayi masu hoton, sunyi matuƙar yin kukan, kowannansu fuskar shi ɗauke da dariya ga cake duk ya 6ata fuskarsu, yatsun hannunta ta ɗaura saman hoton tana shafa fuskokin su, tun daga face ɗin Uzair zuwa ta taj, kafin ta tsayar da hannunta a kan hoton Angel, murmushin takaici ta ɗan saki, ta ɗago ta kalli junaid, ya tsareta da ido yana kallonta ko ƙyaftawa baiyi, gefen shi ta matsa ta zauna, ta saita hoton saitin fuskarshi, magana ta soma yi mashi saitin kunnanshi,
"Ka ga wannan shi ne daddyn ka, sunanshi Uzair, wannan kuma Taj, shi aminine kuma ɗan uwa ga mahaifinka, ita kuma wannan she's ur elder sister Sunanta ANGEL" tana rufe baki taji ya maimaita sunan Angel, murmushi tasaki dama wani lokacin duk in tayi magana saiya maimaita,
"Da ace tana nan, da yanzu ita zata dinga goya mun kai abayanta, Allah sarki Angel tayi jiran zuwanka na tsawon lokaci kullum tana tambaya aunty aneelerh wai ke bazaki haifa mun ƙani ba, ni na ƙosa naga ɗan yaron ki, sai ga shi na same ka a lokacin da angel bata nan, tana a raye kota mutu bani da masaniya akan hakan," duk wannan surutun da Aneelerh ke yi, Ya natsu yana sauraronta kamar yana fahimtar me take cewa"
"KANA NAKA ALLAH NA NA SHI wa ya yi tunanin ma za'a wayi gari babu su a lokaci ɗaya? Ban ta6a kawo hakan araina ba, kaima kuma ban sanya ran zan same ka ba, sai gashi Allah ya bani kai, ina matuƙar sonka my baby boy," takai ƙarshen maganar tare da manna mashi kiss saman forehead ɗinsa, kafin ta ɗaura hoton saman side drawer,
Rungumoshi ta yi a jikinta, wani baccin ne ya kuma ɗaukarsu,
Wuraren ƙarfe tara na safe, Mami ta shigo ɗakin nata, har ta kimtsa kanta Cikin Atampa,
Ganinsu rungume da juna ita da junaid, yasa ta saki murmushi, baƙaramin ƙaunar yaron take ji ba, ita kanta mamin saboda sunan yaron yaci Sunan marigayi mahaifinta Alhaji Junaid Shuwa, tun lokacin da mami ta auri Mahaifin Aneelerh Alhaji Muhammad falgore ta ƙwallafa rai akan ta samu ɗa namiji don ta sanya ma shi sunan mahaifinta, Allah bai nufa ba, ƴa ta samu mace kuma daga ita bata ƙara haihuwa ba, Aneelerh tasan da wannan burin na mahaifiyarta, shiyasa ta sanyawa yaron Suna Junaid, kuma aka amince mata da sunan, ko lokacin da su Uncle abdallah suka zo Nigeria don su ga jikan su, basu yi gaddama ba da aka faɗa masu sunan yaron, saima farin Ciki da su kayi An haifa masu ɗan kyakkyawan Saurayi.
Ƙarasawa gaban gadon tayi ta kira sunanta"Aneelerh wake up, lokacin yin breakfast ya yi, abie na son magana dake,"
Buɗe ido aneelerh tayi akan mami, biji biji take ganinta kafin idon ya washe,
"Mami," ta ambaci sunanta muryarta da alamun bacci,
"Muna jiran ki a dining area," mami ce ta yi maganar, tare da juyawa ta fuce daga ɗakin,
A lalace Aneelerh ta miƙe ta sauko daga saman gadon, toilet ta nufe ta shige, bayan ta fito daga wankan, bata canza jallabiyar jikinta ba, mayafi kaɗai ta dauko cikin closet, tayi rolling ɗin shi a saman kanta,
Fitowa daga ɗakin tayi ta nufi dining area, A saman dining chairs ta iske su zaune su biyu, sai Ana mai aikin gidan Aneelerh dake tsaye tana yin serving ɗinsu,
Tana ƙarasowa Ana ta soma gaishe da ita cikin girmamawa"good morning madam, how was ur night" murmushi Aneelerh ta sakar mata"Alhamdulillah, ina fata kema haka," jinjina mata kai ta yi alamar eh,
Mayar da idanuwanta tayi kan iyayen nata, gaba ɗaya ita suke kallo, da sauri ta gaishe da su, su ka amsa mata fuskokin su a sake,
Kujera taja ta zauna, Ana tace" me zan zuba maki"?
"Cup of tea, ki haɗa mun da noodles," amsa mata tayi da toh, ta ɗauki serving spoon da plate ta soma zuba mata noodles ɗin, bayan ta gama haɗa mata ta tura mata gabanta, tare da kofin tea,
Har ta ɗauki fork zata fara cin abincin ta ɗago ta saci kallon iyayen nata, da yake suna fuskantar juna,
Ganin suna kallonta yasa ta sunnar dakai ƙasa, murmushi su ka sakar mata, mami tace" Ina kika baro mana baby junaid ɗin mu"?
"Bacci yake yi,"
"Ya cika bacci anya kuwa lafiya"?
Abie yace"lafiyar ce ta kawo haka ae, yaron fa ɗan hutu ne, " da zolaya ya yi maganar, murmushin gefen fuska aneelerh tasaki"mami ae ya farka ɗazu, daga baya ne ya koma bacci" mami tace"Okey, ki ci abincin ki, yana huce wa" kallon abie ta yi tare da cewa"abie da gaske ne uncel abdallah ya kira akan zasu kar6i baby junaid"? yanayin yadda tayi maganar a ɗan tsorace take da jin amsar da zai bata,
"Dagaske na, Amma ki kwantar da
hankalin ki, bawan da zai raba ki da babynki, mutu ka raba takalmin kaza" dariyar farin ciki ta saki, hatta Ana dake a tsaye saida ta murmusa,
"Ci ki ƙoshi daughter, farin cikinki ae shi ne namu," yakai karshen maganar tare da kallon Ana dake a tsaye"Nayi magana da drivern da zai kai ki garin ku, ki kasance a cikin shiri a kowani lokaci zai iya zuwa ku tafi" jin wannan maganar yasa yanayin fuskarta ya canza ta shiga yarfa hannu, cike da mamaki suke kallonta, tattara skirt ɗin jikinta tayi tare da zuƙunnawa saman guiwowinta, tana faɗin
"Allaji ayi haƙuri abarni anan tunda har nakai wannan lokacin, wlh kona koma ƙauyanmu wahala zanci, Noman doya za'a sanya ni, dan Allah Alaji a taimaka, ƴan uwana duk suna a cikin garin nan suna aiki, dama mu uku ne marayu iyayen mu sun rasu," tuni hawaye sun wanke fuskarta, kallon aneelerh tayi a marairaice tace"madan ki taimaka, abarni anan wlh noman doya da wahala", duk wannan ƙibar da nayi idan har na kuskura na koma ƙauyan mu, Cikin kwana uku zan sace," mami dai dariya ce ke son kufce mata, amma ta gumtse ta cikin baki, shi kanshi abie taso ta ba shi dariya, musamman hausarta da bata fita sosai,
"Abie, tunda tana taimaka ma Inna hauwa wurin yin girki, da aikace aikacen gida ni ina ganin barta kawai,"
Mami ma tace"Nima na goyi bayan haka, saboda ta nuna bata son noman doya....."takai ƙarshen maganar tana ƴar dariya,
"Yanzu ina ƴan uwan naki"? Abie ne yae mata tambatar,
Hannu tasa tana matse ƙwallar dake akan fuskarta,
"Esther tana aiki a restaurant itace take aiki gidan Iyayen Sir uzair, Tun bayan barin su ƙasar ta koma restaurant da aiki, ita kuma janet, tun lokacin da madam Benazir ta koreta, ta samu aiki a hotel,"
Ajiyar zuciya abie ya sauke, kafin yace"Shikenan zaki zauna anan, amma fa zan sa maki ido, duk ranar da kika aikata badaidai ba, zan turo ki ƙauyan ku, aje can ayi noman doya,"
Gaba ɗaya suka saki dariya, miƙewa tayi muryar na rawa ta shiga faɗin"thank u sir, thank u madam ngde ngde," tsantsar farin ciki ne akan fuskarta,
"Ki koma wurin Inna hauwa, ku yi breakfast ɗin ku," mami ce ta yi mata maganar, da sauri ta juya ta nufi part ɗinsu,
A tsanake suka cigaba da yin breakfast ɗinsu, sai da suka kusa kammalawa, aneelerh ta mike mami tace ina zuwa,
"Inaji araina kamar Junaid ya farka, bari naje na duba shi," da sauri ta wuce ɗakinta,
Kallon Juna abie da mami su kayi,
"Namanta ban faɗa maki ba, Munyi waya da ɗan Iya, wai yana so Aneelerh ta koma hannun shi da zama, Zai sama mata aiki a Asibitin *CHIEF OBINNA* " rass Mami taji gabanta ya faɗi, can kuma ta ɗan saki murmushi,
"Ka daina yarda da maganar ɗan Iya, kasan halin shi, Ya iya shirga ƙarya in banda abunka taya za'ae ya iya sama mata aiki A wannan katafaren asibitin wanda ma'aikatan cikinsa ma fa, ɗai ɗai ku ne ƴan ƙasar nan, amma fa in ta samu aiki acan zan fi kowa mafarin ciki, don naji ance ƙaramin ma'aikaci na asibitin just cleaner kawai albashin shi yakai Dubu ɗari da hamsin,
Abie yace"nima nayi mamaki da yace haka amma kuma kinsan shi, mutunne na jama'a, duk wani politician daya shahara yasan shi, to ba abun mamaki bane don yace zai iya sama mata aiki acan, Ni abunda yasa ma na yi mata sha'awarar zama can abujan, zata fi samun kwanciya hankali akan nan, yau fa tsawon shekara biyu da watanni, rabon aneelerh da taje aiki, badan Dr Aisha ta kar6i ragamar kula da asibitin ba, da yanzu komai ya durƙushe"
Shiru mami tayi na wani lokaci, aranta ta ayyana cewa in kuwa har Aneelerh ta samu aiki a asibitin *CHIEF OBINNA* tabbas cikin ƙankanin Lokaci zata zama hamshaƙiyar mai kuɗi, kuma zata ji daɗin rayuwa agidan ɗan Iya, saboda barkwancin shi dana matar shi, ƴan sharholiya ne ana shan drama a gidansu, sai dai kafin Ashawo kan Aneeelerh ta zauna acan ɗin shine abu mai wuya, kuma suma kansu baza su so tayi nesa da su ba, duk da shima abie Suna hasashen zai samu ƙarin matsayi a wurin aikin shi, nan badajimawa ba za'ayi mashi transfer zuwa Ministry of finance dake abuja,
Sun jima suna tattaunawa da abie kafin Yayi mata sallama, Ya tafi zuwa wurin aikin shi, ita kuma Mami ta koma falo, a lokacin aneelerh ta dawo falon hannunta ɗauke da juanid, fira suka zauna sunayi yayin da plasma tv ke a kunne suna kallon tashar arewa 24,
*To fa😳Su Angel An yi gudun gara An faɗo gidan zago, ko ina ne Wurin nan? Lamarin ya ɗaure mun kaina, To dai mu haɗu a next page gobe in Allah yakainu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya, kada ku manta friday da weekend ba posting, Amma zanyi ƙoƙari in dinga yi maku Long pages, Ga waɗan da suka shirya yin payment ƙopa a buɗe take su yi mun magana (08103884440)**💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
*Boss Bature ✍️*
dedicated to Aunty kubra❤
*E10*
_Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba.✍️_
Gargarɗi
_Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube don already na siyar da littafin, Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_
*South Korea*
Seoul City-Gangnam-Gu
Hamshaƙiyar Unguwace ta Attajiran masu kuɗi dake zaune a Seoul, Babban birnin korea ta kudu, babban birni ne mai manyan-manyan gine-ginen gargajiya dana zama ni masu matuƙar ƙayatarwa, ga manyan hanyoyin jiragen karkashin kasa da kuma Wuraren shaƙatawa, masu matuƙar jan hankali, A ɗaya daga Cikin jerin Modern apartments din dake a Gangnam-Gu Haɗaɗɗen masaukin Uncle abdallah ya ke, inda suke sauka duk in suka zo ƙasar.
tafi ƙarfin awa ɗaya a tsaye Tana Kallon hotonsu dake a manne Jikin bangon bedroom ɗinsu, Idanuwanta Sun Cicciko tab da ƙwalla, Har yau she ne wannan baƙin Cikin zai gushe acikin zuciyarta? taya zata Iya sakin jiki tayi rayuwa acikin duniyar nan batare da Ya'yanta ba? tabbas ta yi babban rashin, A kullum ta kali hoton su, sai ta zubar masu da hawaye, Almost 2 years kenan babu su babu labarin su, itace kullum Cikin zullumi da zarar wayarta tayi ringing, jikinta har 6ari ya ke yi don ta ɗauka taga ko Jami'an dake bincike kan case ɗin su tajuddeen ne suka kirata don su sanar da ita ko an gano inda suke,
Tun lokacin da suka dawo Seoul hajiya adama Bata ƙara samun kwanciyar hankali ba, Gangar jikinta gaba ɗaya tana a nigeria, Sunan tana zaune a korea ne, duk irin Sabon da tayi da ƙasar hakan baisa ta gundure ta ba, duk don saboda Abunda ya faru na 6acewarsu tajudden, Ita fa a ayanzu Tafi sha'awar su koma nigeria, Hankalinta sai yafi kwanciya koba komai Zata dinga ganin ƴan uwanta,
Tsadadden leshi ne a jikinta, launin silver yabi shape ɗin jikinta, Ta kashe ɗaurin ɗan kwali, Yayin da ta goya hannayenta a saman ƙirjinta,
Sam ta kasa janye idanuwanta daga Kallon hoton nasu da take yi, bakowa tafi ji ba, face Angle ƙaramar yarinyar da bata mallaki hankalinta ba, taso ace tuntuni rainon yarinyar ya dawo hanninta da yanzu suna atare, Sai dai kash Ƙaddara ta riga fata,
Ziraran hawaye ne suka soma saukowa kan kuncinta,
Muryar me aikinta ce Ajumma ta katse mata Tunanin nata
Cikin harshen su na korea take sanar da ita cewa Saƙon ta ya iso, Share hawayen fuskarta ta yi, kafin tace"A shigo mun da su ciki," itama da harshen nasu take magana, don tana ji ba laifi,
Turo ƙopar ɗakin ajumma tayi, Babbar macace ta kwana biyu aduniya tsufa ya fara kamata, fara ce sol gashin kanta iya kafaɗarta ya tsaya, Jikinta na sanye da ƴar riga da gajeran skirt, Faffaɗan tray ne a hannunta, Saman shi kwalaban Soju ne (Giya) sun kusa Uku, tare da glass cup guda ɗaya,
A saman Round table ɗin dake a kusa da gadon hajiya adama, ta ɗaura tray ɗin, Ta juya zata fita, har ta kusa kaiwa bakin ƙopar fita muryar hajiya adama ta katse ta"Idan mutun yana so ya bugu sosai, har ya manta wanene shi, kamar yaya ya kamata yasha" shiru ajumma tayi tana tuna gargaɗin da Abdallah ya yi mata akan karta kuskura ta ƙara ba matar shi soju tasha, idan ba haka sai ya kore ta daga aiki, Yau ɗunma don Abdalla baya a gari ne, Shiyasa ta kawo mata soju ɗin,
"Kin yi shiru baki amsa mun ba"? Muryar na kerma tace"Kwalba ɗaya, Amma ran ki shidaɗe ina jin tsoro, kada yalla6ai ya ritsa ki a lokacin da kika sha kika bugu, Zai iya korata daga aiki"
"Kada ki