Showing 123001 words to 126000 words out of 287659 words
Chapter 42 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt
farka sakamakon Kukan nasu daya karaɗe Cikin ɗakin,
Jiki na 6ari suka sassauko daga saman gadajensu, Banda Danish Yana kishingiɗe saman gadonshi, Ya farka amma bai buɗe idanuwanshi ba, da alama baccin bai ishe shi ba, ko kuma tsiwar tasu ce ta addabe shi,
Agaban Gadon deeja Haris da Batool, da hibba hada hanna Suka tsaitsaya suna kallonta Fuskokinsu ɗauke da damuwa,
Su javed da sauran ƴan uwan nasu suna a zuƙunne gaban gadon Rubina,
Duk sun ƙanƙame Jikinsu Dake ta kerma, Sun rasa gane masu, gaba ɗaya sun canza, xama batool tayi daga gefen gadon Deeja, muryarta a sanyaye tace"Deeja, Meya ke faru dake ne? Jikin ki Yana yi maki ciwo ne? Ɗaga mata kai ta yi alamar eh, Haris yace"Ni narasa gane wannan ciwon naku, ance Ana baku treatment amma ya akaiba wani sauƙi atattare daku? Kun wani fige kun fita hayyacin ku," aruɗe yakai karshen maganar, Hanna tace"Deeja zaki Iya faɗa mana inda aka kai ku? Da kuma abunda aka Yi maku? Girgiza kai deeja tayi har lokacin hawaye basu daina zuba kan fuskarta ba,
"Bazan Iya tuna komai ba, tun lokacin da aka ɗauke Ni daga Cikin ku, sai Jiya da aka dawo dani Tukunna Na Iya tuna wacece Ni!" Kaitsaye maganar deeja taje kunnan Angel dake Kokarin Fitowa daga sashen toilet ɗinsu, Bayanta ɗauke da parveen data goyo, ta taimaka mata tayi wanka hada sumar kanta ta wanke mata, Kasa Cigaba da tafiya tayi, ta kasa kunne tana sauraronsu
Hibba tace"Abun da ɗaure kai, Ni fa gani nake kamar an ƙara musu Ciwon ma, To inba haka ba Kallarsu fa ku gani, sati biyu da suka wuce kafin azo a ɗauke su daga Cikin mu, Da ƙibarsu jikinsu da auki amma Yanzu Kamar an ɗibi naman jikinsu," Kowa fa ya fara Kokwanton wani abu aranshi, Hakan ba ƙaramin daɗi Yayi ma angel ba, saboda sun fara tunani na hankali,
Jin muryoyinsu javed dake a zuƙunne gaban Gadon Rubina. yasa takai idonta kansu, Ta kasa kunne don taji su me suke tattaunawa
"Rubina Acan inda aka kai ku suna baku abinci? Naga duk kun rame kamar akwai Yunwa attatare daku, Sa'an nan Ya akai la66anku suka faffashe wani Ya cije ku ne? Eve ce tayi mata tambayar. idanuwan rubina cike tab da kwalla tace"A'a ni bazan Iya tuna komai ba, ku daina Yi mini tambayoyi dangane da inda aka kaini saboda bansani ba ni kaina" Mamaki ne ya kamasu, Jin tace batasan komai ba, yasmin tace"Nayi matuƙar damuwa da hankalin da kuke Ciki, bamu yi tsammanin Zamu ganku haka ba a wulaƙance, kwata kwata Jikinku babu alamun sauƙi, saima abunda yayi gaba, Gaskiya nidai ban yarda da wannan treatment room ɗin ba, Yakamata mu yi ma tsohuwa magana, idan wani bai da lafiya acikinmu kada a ɗaukar mana shi, abar mana shi acikinmu muyi jinyarshi"
Naufal yace"Wai Ina parveen ne? Naga babu ita asaman gadonta"? A hanzarce suka juya suna kallon Gadon Parveen,
Muryar angel ce ta janyo hankalinsu zura gareta,
"Gata nan abayana, Ta farka tana buƙatar Yin wanka shine na taimaka mata Tayi, Yakamata suma su deejan su yi wanka, Ko sunji daɗin Jikinsu" Ajiyar zuciya kowannan su ya sauke, Wuce wa angel tayi zuwa cikin ɗakin Abakin Gadon parveen Ta ɗan rankwafa tare da kwantar da ita saman mattress ɗin, Da gudu Azeeza ta nufo gadon parveen ta haye gefenta, fuskarta ɗauke da murmushi tace"Ƴar uwa ya Jikin naki? Daƙyar parveen ta ƙaƙalo murmushi tare da cewa"Da sauƙi sister, Nayi missing dinku sosai Ƴan uwana, Ina abincin da nace ku ajiye mini"? Fuskarta aɗaure tayi maganar tana kallonsu,
Azeeza tace"Ki tambayi angel kiji, tun ranar da aka ɗauke Ku daga Cikin mu, Kullum sai mun ajiye maku abinci yana lalacewa, Har mun fidda rai da za'a dawo mana da ku ashe da rabon Mu sake sanya ku acikin idanuwanmu," tana kai karshen maganar ta kifa kanta saman mattress tana kukan karya, murmushi parveen tasaki, tare da miƙa hannunta saman kan azeeza ta ruƙo kalabar da akayi mata,
"Azeeza wa yayi maki wannan"? ɗagowa azeeza tayi tare da kallon kalabarta da parveen ta ruƙe a hannunta tace"Angel ce tayi mini, kema in kina so sai tayi maki idan kika ji sauƙi"
"Batool da Hannah, Ku taimaka masu deeja suyi wanka, " Angel ce tayi musu magana,
Batare da 6ata Lokaci ba, Batool Da Hanna suka Goya su deeja da rubina asaman bayansu, suka nufi toilet da su,
Ataƙaice Yau dai kusan Sati ɗaya da aka dawo dasu parveen, Jikinsu Yaƙi sauƙi Lafiya ta yi ƙaranci A jikinsu, basu Iya tafiya sai an taimaka musu, ko sunyi yunƙurin miƙewa da niyar su taka ƙafafuwansu Sai kaga ƙafar ta gurɗe, ko daga baya da suka fara Jin sauƙin jikinsu, sai tafiyarsu ta koma irin ta gwami, basu Iyayin tafiya lafiya lou batare da ƙafarsu ta gwame ba, Hankalinsu Batool Yaki kwanciya, Har zuwa bakin kopar ɗakin tsohuwa su kayi domin Su sanar da ita halin da ƴan uwansu suke aciki, Koda suka kwankwasa ƙopar ɗakin tsohuwa ta fito, Suka sanar da ita abunda ke faruwa dasu Parveen Na rashin Iya tafiyarsu, Sai cewa tayi su cigaba da basu kulawa, Zasu dawo dai dai, tana faɗi musu haka Ta juya ta koma ɗakinta tare da jan ƙopa ta rufe, Babu yadda suka Iya haka suka Cigaba da kulawa dasu, Idan zasu Yi wanka Dole sai An taimaka musu, Batool da angel sune ke ɗawainiya dasu, Hatta wankin Uniform ɗinsu sune suke Yi musu, Hakan ba ƙaramin daɗi yake yi musu ba, Hankalinsu Ya kwanta ganin irin soyayyar da ƴan uwansu ke nuna masu,
Da taimakon Allah, jikinsu Yayi sauƙi sosai suka koma yadda suke ada, Tafiyarsu ta dawo dai, Ranar Har wasa su batool suka yi saboda murnar samun sauƙin su deeja, Yanzu babu faɗa a tsakanin Deeja da angel sun daina ƙin junansu, Tun lokacin da aka dawo dasu, angel ta lura da irin canzawar da deeja ta yi, Bata jan kowa faɗa, babu ruwanta da kowa, Sai In ana wasa ne zaka ga ta sanya baki itama ayi da ita, hatta haris Yanzu sun samu jituwa atsakaninshi Da angel, Suna yin rayuwarsu Cikin so da ƙaunar juna, Tsawon kwanaki, Sun samu kwanciyar hankali,
A daren Wata rane ne, Angel Ta kawo masu shawarar su yi wasan Ƴar 6urun 6urun, ta gabatar musu da yarda zasuyi wasan, Gaba ɗayansu suka hallara atsakiyar ɗakinsu, mubeen Ne ya cire rigarshi Ya miƙa ma angel, ta kar6a ta ɗaurewa batool idanuwanta da rigar, Da gudu kowanansu Ya ruga zuwa ma6oyarsa, Wasu suka shige ƙarƙashin gado, wasu suka Nufi Cikin toilet suka 6oye, Hada wanda ya 6oye Ƙarkashin table ɗin da suke ɗaura fitilinsu, Batool taci gaba da bin hanya tana lalubensu tana fadin"6urun 6urun ku 6oye ku 6oye da nisa, Garin gudu ku faɗi ku gurje abanza, Kun 6oye" suka ce a'a, Kusan sau uku Tana tambayarsu sun 6oye sai suce a'a, Ana huɗun ne suka ce mata Eh sun 6oye, nemansu ta dinga Yi acikin dakin, Tarasa ina suka 6oye, ga shi sun ɗaure mata idanuwanta sosai bata Iya gani,
Angel da azeeza Suna a rungume da juna ƙarƙashin Gadon Batool ɗin, Sai tiƙar dariya suke Yi, Danish kuma Yana a karkashin gadonshi tare da parveen, Haris da deeja suna a Karkashin gadon angel, Naufal da Mubeen Sun 6oye kasan table, hanna da hibba hada javed suna a la6e Cikin toilet, kamar aljanu ko tsoro basa Ji, Su rubina da yasmin hada Eve, A jikin bango suka la6e, Don sunsan bazata iya gano su ba, tunda an kulle mata idanuwanta, Sai wahala take sha sunƙi bari ta kamasu, na cikin toilet ne Suka Ji motsi aikuwa gaba ɗaya suka watso da gudu waje cikin sa'a ta cafki wuyan rigar Javed, Ta dinga tsalle tana faɗin ta kama ta kama, Jin haka yasa sauran ƴan uwan nasu suka firfito daga ma6oyarsu, angel ta warware mata ɗaurin dake akan fuskarta, ta ɗaure ma Javed idanuwanshi, Da gudu kowa Ya rugo Zuwa wurin 6oyenshi, wannan karan Azeeza ta tona musu asiri, fitsari ya matse ta, tace ma angel ta rakata suje toilet tayi, angel tace mata ta jira akama wani acikinsu sai su fita, Aikuwa ta fashe mata da kuka tana faɗin ta taso su tafi ya matseta kada tayi shi awando , Maganar azeeza tayi matuƙar basu dariya, Javed najin muryoyinsu ya dinga laluban hanya Cikin sa'a Ya kamo rigar azeeza a lokacin ta fito daga karkashin gadon, ta buge mashi hannu tana fadin Ita fitsari take Ji, fitowa daga karkashin gadon angel tayi Tace da danish"Ya jira ta rakata tayo fitsarin, Idan suka dawo ita zata Yi wasan amadadin Azeeza" Yace mata toh , Bayan sunje toilet ɗin sun dawo, Sauran ƴan wasan duk suka fito daga wurin 6oyansu, Batool ta kar6i rigar hannun javed ta ɗaure ma angel idanuwanta sosai, wannan karan basu 6oye ba, Raina mata wayau suka dinga Yi suna zagayeta, daga ta miƙa hannu za ta cafkosu sai suyi sauri suja da baya, baƙaramar wahala tasha ba, Daƙyar ta samu ta ruƙo wandon Hibba, Ta dinga murna tana faɗin ta kama,
Daren Ranar Ba ƙaramin nishaɗi suka yi ba, Sai da dare ya ratsa tukunna suka kwanta domin Yin bacci,
A washe garin da su ka yi wasan ne ta farka fuskarta dauke da murmushi, ta miƙe zaune saman gadonta, Babu wanda ya tashi daga bacci sai ita, Saukowa tayi daga saman gadonta, da sauri ta nufi toilet, da niyar yin wanka, Tana shiga Ciki, taja kopa ta datse, Tsayawa tayi atsaye tana kallon glass din jikin tagar, abunda yasa har yau bata dura ta cikin windown ba, Saboda fargabar maganar da tsohuwa ta faɗa mata na cewa Zata ja musu bala'e, A yanzu bata son duk wani abu da zai tashi hankalinsu, tafi son su kasance Cikin farin Ciki, har zuwa lokacin da Allah Zai Taƙaita zamansu agidan kurkukun idan suna da rabon fita, idan kuma Anan ƙaddarar rayuwasa ta tsaya tana yi musu fatan da cewa,
Hannayenta ta sanya tare da kamo ƙasan rigarta, tana yunƙurin tu6e rigar, Hancinta ya shaƙo mata ƙarnin Jini, Nan take gabanta Yayi wani irin mugun bugu, A matuƙar ruɗe ta saki rigar ta fasa cireta, ta soma bin ko'ina na jikinta tana shinshinawa a ƙoƙarinta nata gano Inda ƙarnin jikin ke fitowa, Hatta wandonta saida ta ɗaga ta leƙe ciki don taga idan itama tafara Period ɗin, amma koda ta bincika bata ga Jinin ba, Sai da ta gama shan wahalar duba Jikinta a karshe idanuwanta suka sauka akan busasshen jinin dake a saman tafin hannunta, waro ido waje tayi tana kallon Jinin, tarasa a ina ta same shi, tun da ta duba ko'ina na jikinta bata ga ciwo ba, a kalla ta kwashe fiye da awa acikin toilet din Cikin yanayi na jin fargaba, Ta shiga ruɗani sosai,
Da gudun gaske ta fito daga Cikin toilet ɗin, bata nufi ko'ina ba sai bakin gadon azeeza, Saboda itace Jiya suka 6oye a karkashin gadon batool atare, Tabbas kuwa tana hasashen Jinin daga Jikinta yake, bubbuga ƙafar azeeza tayi da hannunta tare da ambaton sunanta"Azeeza"! Har cikin kunnan ta tajiyo kiran da angel ke yi mata, rai a6ace ta farka tana faman mutsustuke idanuwanta, muryarta adisashe tace"Wai lafiya? Wanene ke kirana, Hakanan mutun na yin baccin shi an wani katse mishi" angel na yunƙurin buɗe baki tayi mata magana tajiyo muryar hanna tana fadin"Nashiga Uku, Jini A jikina! Wanene Ya goga mini jini" afirgice angel ta juya tana kallon hannah dake zaune saman gadonta, Bata gama ruɗewa ba, Suka juyo muryar Eve tana fadin itama Jini ajikinta, hankalin fa angel yayi mugun tashi ganin kusan mutun huɗu acikinsu sun fara Jinin al'ada, da ace tana da halin da zata dakatar da jinin da tayi hakan saboda ta fuskanci ba ƙaramin barazana bane Yin Jinin Agidan kurkukun ƙaddara
Sai kuka suke ta Yi sunga Jini Ajikinsu, Da yake basu da ilmi akan Jinin, Ita kuma angel ɗin Tagaza buɗe baki tayi musu bayani saboda ruɗun da kwakwalwarta ta shiga, koke koken da suke Yi ne ya farkar da Batool daga bacci, aruɗe ta sauko daga saman gadonta tana tambayarsu lafiya koda itama tayi tozali da jinin daya 6ata wandonsu a firgice ta ɗaura hannayenta asaman kanta tana faɗin mun shiga uku, hibba Hanna yasmin Jinin menene ajikin ku? kodai Ciwo kukaji wurin Wasan Ƴar 6oyen da mukayi Jiya"? har suna haɗa baki wurin bata amsa da cewa"Suma basu sani ba, kawai sun farka sun ganshi ajikinsu ne," Lamarin ya ɗaga musu hankali ba matan kaɗai ba, hatta mazan da suka farka daga bacci suka ga abunda ke faruwa da ƴan uwansu jikinsu duk Yayi sanyi, don sun san cewa huɗun ɗin nan duka xa'a zo akwashe su da sunan za'a bincika lafiyar jikinsu daga nan kuma su da ganinsu sai In Allah Ya nufa za'a dawo dasu Cikinsu, kafin su yanke shawarar zuwa su faɗa ma tsohuwa, sai ga giants sun shigo Cikin ɗakin wannan karan ba Su uku suka zo ba, wani iko na Allah Su huɗu suka shigo giants ɗin, Iya adadin marasa Lafiyan dake akwai, Abun ya basu mamaki matuƙa, ka rasa wake sanar dasu game da duk wani abu dake faru atsakaninsu,
Babu irin haukan da angel batayi musu ba akan bazasu Ɗaukar musu ƴan uwansu ba, Amma duk abanza, Ba ita kadai ba wannan karan hada su deeja suna kuka suna faɗin Kada su bari a ɗauki ƴan uwansu, Ba duba lafiyarsu xa'ayi ba ƙara musu Ciwon za'ayi, Wani abun ban tausayin ma. lokacin da giants suka ɗauki su Hanna, Suka nufi kopa zasu fita dasu, Da gudu Azeexa da batool da su deeja suka bi bayan giants abunda basu ta6a yunƙurin Yi ba, Aikuwa sunyi danasanin Binsu da sukayi da niyar su ƙwaci ƴan uwansu domin kuwa, Wurgi giants su kayi dasu, gaba ɗaya suka kife saman benan kansu Ya bugu sosai, Kuka hada majina, danish bai ta6a sanya kokwanto akan Giants ba, Sai yau da suka jefar da su Angel yaga rashin Imani tsantsa atattare dasu, kuma ranshi yayi mugun 6aci, zuciyarshi ta hasala, bashi kaɗai ba Hatta haris da naufal da mubeen Sun fusata sosai,
*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*
Saboda tsabar buguwar da su ka yi, ga6o6in jikinsu sun jigata sosai, Angel tana yashe saman last step na benan, Azeeza da batool sun yi gefen dama atare aka wurgar dasu kamar kayan wanki, Deeja da Parveen da rubina suna ata 6angaren hagu, kowa Ya tarwatse, Sun yi kuka har sun gaji ga takaicin ƴan uwansu da aka tafi dasu ta ƙarfi da yaji, ga kuma takaicin wurgin da akayi dasu kamar wasu dabbobi marasa Ƴanci, ita angel ma hancinta har ya fara bleeding sakamakon bugun ƙasan da yayi, hakan ba ƙaramin tayar masu danish da hankali Ya yi ba, haris Yana zuƙunne gabansu azeeza dake a kwance ƙasa sunata kuka Yana lallashin su, Mubeen da naufal suna a 6angaren da aka wurgar dasu deeja, suna ta aikin lallashi,
Danish ke a zuƙunne Inda angel take kwance ƙasa, ya rasa ya zaiyi da ita saboda sautin kukanta dake neman hargitsa mishi lissafi, yana so ya lallashe Amma ya kasa, Yanke shawarar ɗaukarta yayi zuwa toilet don ya samu ya wanke mata fuskarta ko jinin ya daina zuba, Hannayenshi Ya sanya duka biyun Ya ruƙo waist ɗinta Ya ɗago da ita zuwa saman kafaɗarshi, Ya yunƙura ya miƙe ɗauke da ita Ya nufi sashen toilet ɗinsu,
A bakin fanfo Ya sauketa, Ta zuƙunna saman ƙafafuwanta, idanuwanta sunyi jawur launinsu Ya ciza sun koma kamar na zombie, hawaye duk sun wanke fuskarta sharkaf, Jikinta har kerma Yake yi, Giants bala'e ne, duk yadda suka ta6a mutun sai yaji jiki,
"Am sorry angel" ya furta hakan Yayin da idanuwanshi ke akan fuskarta, a raunace ta ɗago tana kallon shi without saying anything, ita kaɗai tasan Azabar da take ji ajikinta, Zuciyarta ta hasala, har wani tafarfasa take yi,
Janye idanuwanshi yayi daga kan fuskarta, Yakai hannu saman tap ɗin ya kunna shi, Ruwa ya soma kwararowa, Da tafin hannayenshi Ya dinga tarbo ruwan yana wanke mata fuskarta, Ba ƙaramin sanyi taji ba lokacin daya watsa mata ruwan a fuskarta, har saida ta lumshe idanuwanta, Bayan ya kammala Ya kashe tap ɗin, Ya ɗan juyo yana kallonta,
Cikin sanyin murya yace"zaki sha ruwa? Girgiza mashi kai tayi dakyar ta iya buɗe baki tace"bana jin ƙishi, wanka nake so In yi, U can wait for me out side," amsa mata Yae da okey, kafin ya miƙe Ya fito daga Cikin toilet ɗin Ya tsaya Abakin ƙopar Yana jira ta kammala, lalla6awa tayi ta miƙe taje bakin ƙopar toilet ɗin ta datse ƙopar ta koma ciki, tsawon mintuna bata fara wankan ba, takaicin duniya ya isheta, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, yanzu shikenan an ɗauke su hanna? Suma za'aje a cutar da rayuwarsu kamar yarda aka cutar da su parveen, Ya salam, fashewa tayi da wani sabon kukan mai cin rai, Tana jiyo cool voice ɗin danish daga bakin door ɗin yana yi mata magana,
"Angel stop crying, its hurting me, idan ba haka zan shigo daga ciki," tana Jin yace haka da sauri ta taja baki tayi shiru don tasa halin shi, Yanzu ya faɗo mata Cikin toilet, Miƙewa Tayi jiki duk ba ƙwari ta zame kayan jikinta ta ɗaura su saman igiya, Ta cika ruwa abokiti Ta soma Yin wankan,
Yana a tsaye Bakin door ɗin ya jingina bayanshi, fararen idanuwanshi na fuskantar ceilling, Yayin da zuciyar shi ta yi nisan kiwo Cikin tunanin Abunda Ya faru ɗazu Zuwansu Giants, tambayoyi ya shiga jefa ma kan shi wata irin lalura ce ke damunsu Hannah? Jinin menene Yake fita ajikinsu? And why tsohuwa bata nuna damuwa a kansu ba? Bakomai yafi ɗaure mashi kai ba, face yarda giants suka nuna rashin tausayi wurin yin wurgi dasu azeeza, don kawai suna ƙoƙarin hana atafi da ƴan uwansu,
Yayi zurfi acikin tunaninshi, kunnuwanshi suka soma Jiyo mashi muryar haris a kausashe yana magana daga Can Cikin ɗakinsu, Da sauri Ya bar ƙopar toilet ɗin Ya shigo ɗakin nasu, kaitsaye Eyes ɗinshi suka sauka akan