Header Ads
Showing 282001 words to 285000 words out of 287659 words

Chapter 95 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1826

Ads at the middle of Article

Malamai na duniya masu zagaye ƙasashe domin yin da'awa, Allah yayi mashi baiwar ilimi, ɗan ƙasar Nigeria ne, Tun da ya ke bai ta6a yin aure ba, a zamanin shi baida burin daya wuce Yayi koyi da manzo SAW wurin karkato da hankulan waɗanda basuyi imani da Allah ba don Ya Musuluntar dasu, Ita kuma mahaifiyata tsohuwa Tamira Ƴar Ƙasar America ce ba musulma bace bata da addini, Farkon haɗuwar su da mahaifiya ta yaje ƙasar Dubai domin gudanar da gasar Musabaƙa ta karatun alƙur'ani ta duniya da aka gayyace su tare da manyan malamai na sauran ƙasashen duniya A babban birnin Dubai wato Abu dhabi, A can Allah ya haɗasu itama lokacin taje ƙasar Gudanar da harkokin kasuwancin ta, kamar yarda ya bani labari tun da yake bai taba sanyawa ran shi zai so wata ƴa' mace har takai su ga yin aure ba, sai gashi ƙaddara ta haɗa shi da auran Baturiya ƴar ƙasar america, bakomai ne yasa shi amincewa da tayin soyayyar da tayi mashi ba, face don ta nuna tana so ta musulunta in har ya amince zai aureta, kinji dalilin daya sa har ya aureta ba tare da sun samu matsala ba, kinsan su turawa da zarar yaro ya haura 18 years Yana da ƴancin da zai yi komi yake so, Iyayenta basu son auran sai dai ba yadda zasu yi dole suka haƙura tabi za6in ranta, Bayan sun dawo ƙasar Nigeria ne ta musulunta, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma dangin shi ba, tun da iyaye na suka yi aure basu ta6a haihuwa ba, Har saida auran su yakai shekara goma tukunna Allah ya ƙaddara samuwata, A lokacin sun manyan ta mahaifina Ya tsufa, Ita kuma Mahaifiya ta tana da shekara arba'in a duniya.." dakatawa ya ɗanyi da yin Maganar, Angel ta zuba mashi ido tana jiran yaci gaba da bata labari.

"Akwai wata baiwa da Allah yayiwa mahaifina, duk idan ya haɗu da mutun mai sihiri a jikin shi sai ya gane, To haka ce ta faru a tsakanin shi da ɗaya daga cikin shuwagabannin dake ruƙe da kurkukun ƙaddara, a lokacin an gayyace shi wani taro jihar Kano state za'a yaye ɗalibai da suka Haddace alƙur'ani mai girma, A filin taron Allah ya haɗa su dashi, tun da sukayi tozali da idon junansu hankalin shi yaƙi kwanciya, Saboda matsafa suna jin shakkar habibullah, tun bayan da aka kammala taron Mahaifina ya dawo gida yana ta tunanin wannan mutumin da su ka haɗu a wurin taro, Abun da ya ɗaure mashi kai Duk wurin shine babban Mutun da aka gayyata, basu ta6a haɗuwa dashi ba sai ranar, shigar mutuncin da ke a jikin shi ta bashi mamaki matuƙa, kuma sananne ne a idon jama'a, Bibiyar rayuwar shi mahafina yaci gaba da yi don ya gano me suke aikatawa saboda ya gane bakin sihiri yake da shi, duk inda yasan za'ayi taro na manyan mutane sai yaje don ya haɗu da wannan mutumin kuma cikin sa'a suke haɗuwa dashi harma su gaisa, A wata rana ne Bayan an yi wani taro na manyan mutane, mahaifina yabi bayan su a 6oye basu sani ba har yaga kaɗan daga cikin abunda suke aikatawa, Hankalin shi ya tashi matuƙa a daren ranar bai kwana a garin da akayi taron ba, Tsakar dare ya dawo Kaduna, babu wanda yasan da dawowar shi a wannan ranar sai dai muka gan shi ya shigo gida, ashe tun lokacin da yake yi masu leƙen asiri sun gan shi suka ƙyale shi don suga iya gudun ruwan shi, a lokacin da ba muyi tsammani ba Matsafan nan suka kawo mana hari, tsakar dare su ka yi mana zuwan bazata a cikin gidan mu, Gaba ɗaya suka tattara mu da mahaifiyata dani kaina da mahaifina, kinji silar kasancewar mu agidan kurkukun ƙaddara! Ɗakin da kuke rayuwa acikin shi anan suka kulle mu, mu duka ukun, tun kafin a sabunta ginin tun yana tsoho, Mahaifina yayi ƙoƙari wurin ganin ya nema mana hanyar da zamu ku6uta amma abun ya faskara saboda babu ƙopa a cikin ɗakin a datse yake tako Ina, Akan idon shi mugayen matsafan nan suka yi amfani da mahaifiyata da kuma ni kaina duk don su ƙuntata mashi, tsabar baƙin Cikin wannan abun yasa shi kamuwa da ciwon zuciya, mun fuskanci tashin hankali a hannun Giants dake tsaron kurkukun nan, Kamar yadda ake baku abinci sau ɗaya a rana haka suke bamu, Mahaifina bai cin Abincin shi ni yake ajiye mawa don kada inji yunwa, yana matuƙar sona, Nima ina ƙaunar shi, har roƙon mu yayi akan mu yafe mashi saboda shine silar jefa mu cikin halin da muka tsinci kan mu, da ace baiyi masu leƙen asiri ba da duk hakan bata faru ba, Ire iren waɗannan maganganun da yake yi mana ba ƙaramin karya mana zuciya yake yi ba, da kanshi ya faɗa mana cewa zaiyi mana hanyar da zamu gudu daga Cikin kurkukun Amma baya jin zai rayu, Yayi ƙoƙarin sama mana hanya koda ta bango ne mu bi mu wuce Sai dai hakan ya faskara, gashi komai muke yi idon su akan mu suna kallon mu, da zarar sunga ya fara ƙoƙarin yin ibada sai su shigo su kamamu suna azabtar damu nida mahaifiyata duk don ya dakata, Da zarar sun fara yake dainawa saboda baison su halakar damu, Bayan mun ɗan samu sassauci daga wurinsu ne yaci gaba da neman hanya a cikin ɗakin, Har Allah yasa ya gano wata tsohuwar Hanya da ruwa ke bi ya wuce ta cikin ta, Girman ƙofar mutun zai Iya bi da rarrafe ya wuce ta cikinta, koda ya gano hanyar bai bari sun fahimci hakan ba, Ya dinga bi a sannu wurin ganin ya tono ta saboda A garƙame take sun rufe ta da dakakken ƙarfe wanda Idan har ba Sihiri Mutun ke gare shi a jikin shi ba bazai Iya buɗe ta ba, Taya zai Iya buɗe murfin ƙarfen dake a jikinta bayan komai muke yi suna kallon mu? Zasu gane ne Asirin shi ya tonu, Silar hakan kuma zamu iya rasa rayukan mu, Abunda mahafina yayi a wurin da ya zauna yayi amfani da Baiwar ilimin addini da Allah ya bashi, addu'o'i ya dinga yi yana tottofe cikin ɗakin, Tsawon kwana biyu ya ɗauka bai motsa daga wurin ba, babu ci babu sha haka ya zauna yana kai kukan shi ga Ubangijin mu Allah subhanahu wata'ala, Silar wannan addu'o'in da mahaifina yayima wannan wurin yasa garkuwar sihirin da ke a zagaye da sashen ta karye, har yau har gobe matsafan basu Iya sanin meke wakana a ciki ba, Muddin Mutun ya shiga wurin baza su iya ganin shi a allon tsafin su ba, Mu kan mu sai daga baya muka fahimci cewa garkuwar sihirin da ke a wurin ta karye, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mana ba, sai dai kash muna shirin 6alle ƙofar don mu gudu ciwo ya turniƙe mahaifina ya faɗi ƙasa Yana ambaton kalmatusshahada, Dama yace mana da wuya ya rayu saboda cuwon zuciyar da matsafan suka dasa mashi ga ba magani, Munyi kuka tamkar ran mu zai fita, Yana a cikin mawuyacin hali yake roƙon mu akan mu tafi kada mu tsaya jiran shi, kada suzo su kamamu.

Bamu ji maganar shi ba, Muka ƙi tafiya saboda mun sanyawa ranmu cewa dole sai dashi zamu gudu, Muna tsaka da ƙoƙarin dawo dashi hayyacin shi don ya tashi mu tafi, Giants ɗin dake kawo mana abinci suka ritsa damu, Nan take kuma mahaifinmu Ya cika, Mu kuma suka tasa ƙeyar mu zuwa can cikin kurkukun, nasan dole an neme mu an kuma yi Addu'oi sosae saidae bawa baya wuce ƙadddarar sa, tun daga wannan lokacin Suka maida Mahaifiyata ma'aikaciyar su ni kuma suka bani horon zama Giant, horo mafi wuya a duniyar nan, Miƙa wuyan da mu ka yi gare su muka zama masu biyayya shiyasa suka yarda damu sosai musamman mahaifiyata tsohuwa tamira, Tabbas mun aikata babban kuskure na bin umarnin matsafa saboda son ɗaukar fansa duk da da farko da suka yi mana tayin aikin ko su kashe mu kin yarda mukai sai daga baya ita Mahaifiyar tawa ta amince saboda a tsarin su ba su yi ma mutun sihiri don ya amince zai yi masu aiki sun fi so da kan ka Amince kana a hayyacin ka, sai daga baya ne ake baka sihirin a koya ma abubuwa, lokacin ba irin ƙoƙarin da ban yi ba wurin nusar da ita kan illar hakan don kuwa sai mun yi ridda amman ta kafe dama kuma tubabba ce, ina ji ina gani mahaifiyata tabar addinin musulunci ta shiga Cikin matsafa sosai saboda taci galaba akan su, a lokacin ta roƙe su kan kar su wulaƙanta gawar Mahaifina su maida ta gida a samu ai masa sutura suka amince don dama ba zatai masu Amfani ba sai ma taja masu matsala, Amma ni an sha daga dani kan in amince naki, k'arshe dai soyayyar uwa ta kwashe ni da kuma nuna man da tayi in muka kawo k'arshen su hakan kaman jahadi ne mukai daga baya sai mu tuba mu rok'i Allah ya yafe mana, da haka na amince saidae ni har yanzu musulmi ne don zuciyata tak'i yarda in bar musulunci sai dai kuma bana sallah gaskiya, Saboda a gidan kurkukun ƙaddara ba'ayin sallah shine abu mafi muni da suka tsana shiyasa a duk lokacin da mutun yai niyyar yin sallah suke burkita mashi lissafin ƙwaƙwalwar shi, Ba don mun so muka kasance Ma'aikatan gidan kurkukun nan ba, kafin mutuwar mahaifina yayi mana addu'a mai ƙarfi akan Allah Kada ya basu nasara akan mu, Ya roƙi Allah da ya bamu ikon Tarwatsa matsafan da ke ruƙe da kurkukun ƙaddarar nan, Inaji araina cewa Addu'ar mahafina ce take bibiyar Rayuwata shiyasa har yau har gobe hankalina bai ta6a gushewa ba, ina sane da komai, duk wani zalunci da ake aikatawa bana ɗaya daga Cikin masu yi, ban ta6a kisa ba tun bayan da aka horar dani nazama Giant, silar hakan yasa har yau basu bani matsayi mai girma ba amman suna d'aga man sosae sakamakon mahaifiyata da tay mubaya'a gaba daya, Ina matuƙar tausayin rayuwar Danish! ni na fara rayuwa a gidan kurkukun nan na mallaki hankali na, shi kuma tun yana jinjirin shi bana tunanin ko cibi an yanke mashi a haka aka kawo shi nannaɗe cikin Towel, Matsafa sun girgiza da ganin irin kyan da Allah yayi mashi, wlh banji daɗin yadda suke sarrafa rayuwar shi ba, Yaron yana da kaifin basira fiye da tunanin ki, Allah yayi mashi baiwar da zaiyi wuya asamu mai irinta, Yana da saurin haddace abu, he's a gifted sannan Yana da ƙarfi tunkafin su sanya mashi sihiri ajikin shi Danish Yaro ne mai ƙarfin gaske, ko ni nasha jaraba yin dambe dashi a gidan kurkukun nan tun yana da shekara sha biyar yake bamu wahala, Da biyu suke haɗa mu Faɗa dashi, don su jaraba ƙarfin shi, Abun da zai baki mamaki mu tsafi ne ajikin mu, shi kuma babu sihiri a haka yake cin uban mu......" Sosai Angel ta fashe da matsanancin kuka tausayin danish ya kamata, ashe tun yana jariri aka sadaukar dashi agidan kurkukun ƙaddara, maganar da Salsabeel ya gaya mata ta ƙara Sanya mata ƙaunar Danish acikin zuciyar ta, son shi ya ƙara ninkuwa, Ji take kamar tayi fiffike taje inda zata ganshi don ta rungume shi a jikin ta.

"Sauran tambayoyin da kikayi mini bazan iya amsa maki ba saboda babu isasshen lokaci, zasu iya riskar mu, Abu ɗaya da nake so kiyi mini alƙawari shine kiyi ƙoƙarin ganin kinbi duk wasu sharuɗɗa da zan faɗa maki don ku tsira daga Cikin kurkukun nan, Mun ɗaura buri akan ki Unaiserh, saboda ta hanyarki ne kaɗai zaki iya tona asirin matsafan da ke ruƙe da kurkukun ƙaddara! Muna so duniya tasan da zaman su, A san me ake aikatawa a gidan kurkukun, yin hakan da zakiyi shi zai janyo hankalin mutanan duniya daga nan za'a samu waɗanda zasu Iya kawo masu farmaki, Inaso ki ɗaurawa kan ki nauyin yin hakan ko dan saboda rayukan dake rayuwa acikin kurkukun nan cikin mawuyacin hali! Akwai ire iren ku da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba, An kulle su an hanasu sakat, Kullum ne sai an rasa rayuka agidan kurkukun nan, kashe mutane suke yi tamkar kyankyasai, Idan har bamu kawo ƙarshen kurkukun nan ba to kuwa zasu cigaba da aikata 6arnar da babu ranar dainawa, Muna matuƙar jin tausayin yaran da ke rayuwa a kurkukun nan, Dan Allah Unaiserh ki taimaki rayuwar su! Ki daure ki jure wurin ganin kun tona asirin abun da ake aikata......" hannayenta Ya ruƙo a cikin nashi ya dinga yi mata magiya sautin muryar shi kamar zai fashe da kuka, Ga dukkan alamu sun gaji da ganin Zaluncin da ake aikatawa agidan kurkukun ƙaddara

Tun tana yin kuka har muryarta ta disashe da ƙyar ta samu ta tsagaita tana kallon shi tace "NAYI MAKA ALƘAWARI Idan Allah ya bani damar fita daga kurkukun nan zan tona asirin su harma mu bada gudunmawa wurin ganin an kawo ƙarshen su, Bi'iznillahi,

Ajiyar zuciya ya shiga saukewa kafin ya daidaita natsuwar shi yaci gaba da cewa "Silar sabunta ginin da aka yi ƙofar ta 6ace mana, amma muna hasashen tana a cikin ɗaya daga cikin waɗannan makewayin naku guda uku, akwai wata tukunyar fulawa da ke ajiye Cikin toilet ɗinku Mahafiyata ce ta ajiyeta saboda bayan an sabunta ginin shafen dake a ƙasan wurin bai zauna da kyau ba, kuma bakomai ya jawo hakan ba face silar zaman da mahaifina yayi awurin na tsawon kwana biyu yana ibada, to duk wani abu da ke da sihiri idan ya ta6a wurin bazai zauna ba sai ya nuna alama, gudun kada ta manta da ƙofar yasa ta ajiye wannan tukunyar fulawar, Idan kuna so shafen dake akan ƙopar Ya 6a66ako batare da kun sha wahala ba, Ku yi amfani da ruwan zafin da ake kawo maku a matsayin ruwan shan ku, da zarar kun yayyafa shi asaman wurin zai tsastsage daga nan ƙofar zata bayyana, amma fa sai kun yi takatsantsan, kada farin cikin ganin ƙopar yasa ku fasa ihu wanda zai janyo hankalin su........."

Wani irin Farin ciki ne ya lullu6e Angel, Bakinta yaƙi rufuwa

"Kada ku sanyawa ranku cewa dukkan ku zaku tsira, ba abune mai sauƙi ba, dole ku fuskanci tarin ƙalubale wurin ku6uta, musamman Makullin nan ɗaya da baya a cikin ku wato Danish dole ku dawo da shi saboda shi kaɗai ne zai Iya Cire murfin ƙarfen da ke a jikin ƙofar cikin sauƙi ba tare da kun sha wahala ba.

Cikin shessheƙar kuka tace"Taya zamu iya gano Danish har mu iya dawo dashi Cikin hayyacin shi"? bai amsa mata tambayar ta ba, ganin ya miƙe tsaye yasa itama ta miƙe tana kallon shi,

"Akwai ruwan zam zam da mahaifina yake yawo dashi cikin aljihun rigar shi, ya mallake shine a wurin wani hamshaƙin malamin addini wanda ake kira da Shaykh al-ikhlass ɗan ƙasar Madina, shi ya yi mashi kyautar jarkar ruwan zam zam ɗin duk mutumin da ya kur6i ruwan abakin shi ya haɗiya to zaiyi wuya Sihiri yayi tasiri a jikin shi, sannan waraka ne ga kowace irin lalura da izinin ubangiji, Dubarar da mahaifina yayi sai ya dinga ɗibar ruwan xam xam din yana ɗura shi cikin ƙananun robobi, duk in zai fita a cikin aljihun shi yake ɗauka ya tura, saboda tsaro baisan ko Allah zai haɗa shi da mai buƙatar taimakon wata lalura dake damun shi, shiyasa Yake yawo da robobin ruwan cikin aljihun shi, to aranar da matsafa suka farmake mu tsakar dare suka kawo mu kurkukun nan akwai kingin roba ɗaya da ta rage a cikin aljihun jallabiyar shi, Kafin ya rasu ya damƙa ma mahaifiyata ita mun 6oyeta wurin da babu wanda ya sani daga ita sai ni, Robar ruwan zam zam ɗin tana a cikin ɗakinta inda ku ke rayuwa, da zarar kun dafa jikin bangon ƙofar zata buɗe da kanta, Sai ku shiga ku ɗauko ta.

Ke za ki nemo Danish a gidan kurkukun nan saboda ke kaɗaice zaki iya sarrafa tunanin shi amma fa sai kinci baƙar wahala domin kuwa baisan wacece ke ba a yanzu, Har kashe ki zai Iya yi, komai zai iya aikata maki, duk runtsi duk wuya karki bari tsoron shi yasa ki kasa watsa mashi ruwan a cikin bakin shi, ki tabbatar ya haɗiye shi.

Sannan Giant basa jin Bugu, Wuƙa bata iya tsaga jikinsu, haka zalika harsashin bindiga bai iya tsaga fatar su, Mutane ne masu hatsarin gaske, ƙarfin shaiɗanun aljanun da ke a jikin su ya rinjayi halittar su ta ɗan adam, Giant's heart ba irin zuciyar mutun bace, ta shaiɗanin aljani ce, Ko da ace kinyi nasarar sanya mashi ruwan abakin shi zai dawo hayyacin shi na ɗan lokaci ƙanƙani amma duk lokacin da Giant's heart ɗin shi ta motsa zaku ci baƙar wahala, Shiyasa ni ke so ki dage dayi mashi addu'a saboda ku samu ya fitar daku daga Cikin kurkukun nan, In yaso daga baya idan kuka faɗa cikin mutane zan baki Address ɗin gidan mu da mahaifiyata ta rubutamin don in baki, idan ku ka duba zaku iya samun sauran robobin ruwan zamzam na mahaifina daya ajiye a ƙarƙashin gadon shi, da shi zaku dinga yin amfani wurin shawo kan Danish a duk lokacin da Giant's heart ɗinshi ta motsa. Ki kula da rayuwar shi Angel Ki ɗauka cewa amanar Danish na baki, ki ruƙe mini shi hannu bibbiyu, kada ki kuskura ki bari yayi nesa dake, ku kasance atare domin mu samu muyi nasara agidan kurkukun nan, Danish yasan komai fiye da tunanin ki, mun riga shi zuwa kurkukun nan amma yafi mu sanin komai, shi kaɗai yasan hanyar da za'a iya ruguza su, Matsalar shi ɗaya mugun miskili ne kuma yana da taurin kai, zaku ci wahala kafin ku samu Ya baku haɗin kai.........." Yana kai ƙarshen maganar shi da sauri ya zura hannu cikin ajihun baƙin wandon dake ajikin shi ya zaro takardar dake a ninke ya miƙa mata, Address din gidanmu ne dake a Kaduna state,

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads