Header Ads
Showing 132001 words to 135000 words out of 287659 words

Chapter 45 - KURKUKUN ƘADDARA! (TAKUN FARKO) BY By Boss Bature [www.aihausanovels.com.ng].txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jul 2024

1802

Ads at the middle of Article

sauke ajiyar zuciya atunaninshi ta yafe mashi ne, ashe masifa ta tashi ta zazzage mashi,

Cakumar wuyan rigarshi tayi da hannayenta biyu, ta zazzare mashi manyan gray eyes ɗinta Ta jijjiga wuyan rigar tashi, Saboda masu bayyaci yasa ta sassauta muryarta,

"Wai menene alaƙata dakai ne? Ka addabi rayuwata ka hanani sakat, kai nifa bansan ganin wannan mummunar fuskar taka, na tsani ragon namiji irin ka, pls na roƙe ka ka tashi kabar gefen gadona ko na samu inyi bacci" Takai karshen maganar tare da ture shi gefe, ko motsi baiyi ba, kallonta kawai yake yi da lumsassun idanuwanshi,

A hasale tace"idan har bazaka sauko daga saman gadon ba, Ni zan tashi in baka wuri," ganin tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon yasa shi yin saurin damƙar hannunta, wani irin mugun kallo ta jefa mashi"sakar mini hannu na," ba musu ya saki hannun. ta sauko daga saman gadon, Ta dauƙi bargonta da pillow, Ta juya ta nufi tsakiyar ɗakinsu Ta shimfiɗa bargon ta jefa pillown saman shi, Ta haye ta kwanta, duk yana a zaune gefen gadonta yana kallonta,

Lumshe idanuwanta ta yi da niyar bacci ya ɗauketa, kamar daga sama taji an sanya hannu an ɗauketa da ita da bargon da pillown duka ya tattare su ya ɗaga sama Ya nufi gadonta, Yana zuwa ya jefe ta saman gadonta, aɗan tsorace ta ware idanuwanta tare da wurgasu kan fuskarshi Yana atsaye ya kafe ta da ido, Tsabar mamaki ya hana ta furta komai, kamar walƙiya haka Yaje ya daukota,

Cikin nuna jin takaici tace"Nashiga uku! Wai ina ruwanka dani ne? idan na kwana a ƙasa matsalarka ce ko tawa"? Ya bata amsa da cewa"tamu" guntun tsoki taja, bata ƙara furta mashi komai ba, tana jin motsin shi abayanta, haukanshi na matuƙar ɗaure mata kai, Lokacin da bacci yayi awon gaba da ita, A zaune ya fara gyangyaɗi, A ƙarshe da baccin yafi ƙarfinshi a bayanta ya kwanta saman gadonta, lallai ya taro march,

*ANEELAH*

Wuraren ƙarfe 12 na safe, Tana a ƙudundune Cikin bargonta, Tun bayan sallar asuba data kwanta bacci bata farka ba, wani irin nauyin bacci ne ya ɗauketa, Hada ƙarin maganin muran da tasha a daren Jiya,

Baby junaid ne ya shigo cikin ɗakin yana azaune Cikin motar shi ta wasan yara, Da hannu Yake juya streering wheel ɗin motar, Ba ƙaramin kyau yayi ba, jump suit ne a jikinshi launinsu ɗaya da ƴar motar wasan shi, Army green, da alama ba ƙaramin daɗin motar yake ji ba, daga ya juya steering saita tafi da gudu, agaban gadon Mommynshi Ya tsaya, tare da kai hannu ya danna wani maddani A jikin motar, nan take motar ta soma yin Jiniya, Afirgice aneelerh Ta farka tare da yaye bargon data lullu6a dashi hannunta dafe da ƙirjinta, jallabiya ce a jikinta, Muryarta na kerma take ambaton" Innallahi wa'inna ilaihirraji'un"

tayi matuƙar tsorata, Duk a tunanin ta ƴan sanda ne suka zo gidan ashe motar wasan junaid ce, Fuskarta a yamutse take kallon shi, ya wage baki yana dariya fararen hakoranshi tar dasu, Dimples ɗinshi biyu sun lotsa sosai, a fusace ta miƙa hannu ta ɗauki pillow ta wurga mashi saman fuskarshi, nan take ya kwa6e fuska zai yi kuka,

Cikin nuna 6acin ranta ta soma Yi mashi magana"Karka kuskura kace zaka yi mini kuka stupid, Wlh nayi regretting dana fidda kuɗina na siya maka motar nan ashe kaina abun zai ƙare!, bazaiyiyu ba ka hanani kwanciyar hankali, zan 6a66alla motar In jefata cikin bola kowa ya huta" Jin wannan maganar yasa shi ƙara sautin kukan nashi, Ganin tana yunƙurin saukowa daga saman gadon yasa jin tsoro, gudun kada ta 6alla mashi motarshi kamar yadda tace, aikuwa da sauri yaja streering Ya juya motar da gudu yajata ya nufu ƙopa, Murmushi ta saki tana bin bayanshi da kallo, aranta tace"Allah kaɗai yasan irin ƙalin sharrin da zaije yayi mini a wurin mami, yau nifa na shiga uku, Wata'ƙil ma yaja a hanani Yin breakfast, " takai karshen maganar tare da saukowa daga saman gadon takai hannu ta ɗauko filon data jefa mashi a ƙasa ta wurgo shi saman gadon, miƙa tayi tare da yin hamma ta wuce toilet, after some minutes ta fito tana tafiya a slow ta nufi gaban mirror ta zauna, wata irin yunwa take ji kamar taci ƴan hanjin cikinta, wayarta ta ɗauka dake ajiye gaban mirror, ta danna power hasken screen ɗin ya kawo, hoton angel ne a matsayin wallpaper ɗinta, ta yi mata hoton ne saman gado tana bacci ta saki baki, Tana matuƙar son angel, Tayi missing ɗinta sosai, duk rana ta Allah idan tafarka daga bacci ta ɗauki wayarta saita sumbaci hoton, Yanzu ma kiss ta manna mashi, aranta tace"I really missed u angel, kamar in yi hauka, Allah ya kare mini ke aduk inda kike, Inaji araina cewa Kina araye kuma kina tunani na, I luv u so much" tuni hawaye sun Cika idonta,

Tana yunƙurin miƙewa daga saman mirror chair ɗin, Sai ga Ana Mai aikin gidansu ta faɗo Cikin ɗakin tana Haki hannunta ruƙe da wayarta, Jikinta sanye da Riga da skirt, Sun matseta, Hankalin aneelerh ba ƙaramin tashi yae ba, Ta cikin mirror ta hangota, da sauri ta ƙarasa Juyawa Baya tana kallonta tace"Ana lafiyarki kuwa? Babu neman excuse kin faɗo mini ɗaki? Kamar wadda tasha ƙwaya"? Tayi maganar tana tunkararta, Duƙar dakai ƙasa ana tayi Muryarta na ɗan rawa tace"Am sorry madam, Wani abune na gani daya bani mamaki, shi ne nazo in nuna maki,"

Matsawa aneelerh tayi kusa da ita, Tare da miƙa hannu ta kar6i wayar Ana, tana ɗaura idanuwanta kan screen ɗin, Ras taji gabanta ya faɗi waro ido waje tayi tana kallonta, mamaki ƙarara akan fuskarta tace"Abun mamaki! ana a ina kika samu hoton nan? Kuma daga gani sabuwar ɗauka ce!" murmushi ana ta ɗan saki kafin tace"Yanzun nan Na ganshi A instagram, shafin twins Na Family ɗin Obinna, Zayn da zaid pravin Obinna, Su ne su ka yi posting ɗin a page ɗinsu na insta, madam i was shocked da naga pic ɗin nan nace ashe matar nan tana araye da ranta da lafiyarta! " jinjina kai aneelerh tayi da alama tayi matuƙar girgiza tace"Wonders shall neva end" kallon Ana tayi tare da cewa"Ki jira ni ina zuwa, dole mami taga hoton nan, amma dai matar nan ta bani mamaki matuƙa" Jiki na rawa aneeleh ta fuce daga Cikin ɗakin, gudu gudu sauri sauri ta nufi bedroom ɗin mami, bayan tafiyarta ana ta fito ta tsaya a falo tana jiran dawowarta,

Aneelerh Na yunƙurin yin sallama a ƙopar ɗakin Mami, sai ga mamin ta fito Jikinta sanye da riga da zani na atampa, Ƙiris Ya rage su bangaji juna ita da aneelerh, Sakin baki mami tayi tana kallonta,

Da sauri aneelerh tace"Am sorry mami, a ruɗe nake ne, wani abun mamaki ne Ana ta gwada mini acikin wayarta, Shi ne na kawo maki kema ki gani" tana inda inda tayi maganar, tare da miƙa ma mami wayar hannunta, tasa hannu ta kar6a, koda mami ta kalli hoton saita ruƙe ha6arta da hannu ɗaya, ta ɗan zaro ido da mamaki akan fuskarta tace"Kai! Wa nake gani kamar BENAZIR"! aneelerh tace"Mami itace, Kalli dakyau ki gani, ba'a jima da yin posting ɗin ba, " Mami tasha ruwan mamaki, Sai ƙarewa hoton kallo take yi, dagaske ɗin dai benazir ce, Daga gani hoton batasan an yi mata shi ba, tana a tsaye, hannunta ɗaya ta dafa murfin danƙareriyar motarta, tsadaddiyar gaske, jikinta na sanye da business suit black colour sunbi shape ɗinta sun zauna mata cuf cuf, kamar don ita aka ƙera kayan, hips ɗinta sun fito sosai, hannunta ruƙe da wayarta ƙirar i phone 15 pro, kanta babu hula ko ɗan kwali, Zallar gashin kanta ne daya sha gyara Har midback dinta, idanuwanta na manne da glass, idan ka ganta a hoton ba zaka ta6a yarda cewa ta ta6a aure ba, Ko tana da ƴa, saboda tsabar haɗuwarta, Jikinta Badai kyau ba, agogon diamond ɗin dake sanye a hannunta, a ƙalla Price ɗinta yakai 100m,

Kallon Juna mami da aneelerh su ka yi kowa Fuskarshi ɗauke da al'ajabi, mami tace"Abun mamaki baya ta6a ƙarewa, Wai dama ƴar nan tana nan da ranta da lafiyarta? Hankalinta kwance tsawon shekara da shekaru bata ta6a waiwayar ƴarta da mijinta ba, Anya kuwa benazir ce aneelerh? Kodai watace me kama da ita? to ae abunne da ɗaure kai wlh, '

Murmushin takaici aneelerh ta saki tare da cewa"wlh mami itace! Babu shakka benazir ce, ae ina ganin hoton ko doubting ban yi ba, na shaida itace, Kinsan dama ita tun fil'azal wayayyiyar macace akwai son gayu, Kuma tafi sha'awar rayuwar ƴanci, " mami tace"Haka fa take, Oh Ni ƴarsu, duniya da abun tsoro take, Anya kuwa Benazir tasan ciwon kanta"? aneelerh tace"Ina fa, ae babu alama, Yanzu haka ko Iyayenta basu da masaniya akan inda take rayuwa, Duk da Naga kamar Ƙasar waje ne, idan kika ƙura ido a jikin Ginin dake a bayan hoton an rubuta Rbc (Royal bank of canada) dake acikin toronto, Kuma ga dukkan alamu mami hoton bada saninta aka ɗauke shi ba, don da ace ta sani da bata bari an ɗauke shi ba, kodan kada asirinta ya tonu agane inda take, tun da ko Iyayenta basu son awace nahiya take zaune ba suma nemanta suke Yi ruwa ajallo,"

Mami tace"Nama rasa me xance, kawai dai Allah ya shiryeta in me shiryuwace, amma dai wannan rayuwar da ta ɗaukarwa kanta bamai 6ullewa bace, Wlh zata yi danasanin mara amfani, kwata kwata benazir bata yi wayau ba, Allah kanta tayi mawa, Ace da ranka da lafiyarka, Ka gudu kabar Jinjira acikin kwamin wanka, da mijinka batare da ka waiwaye su ba almost 4 years, Saboda shafewar basira da rashin hankali, tana can tana yawon biɗiɗi," takarasa maganar tare da jan dogon tsoki Ranta ya 6aci ta miƙe ma aneelerh wayar"kar6i nan nagaji da ganin kayan takaici," kar6ar wayar aneelerh Tayi, Har ta juya zata Bar ƙopar ɗakin mami sai kuma ta ɗan dawo baya tace"mami Baby junaid fa"?

"Yana aciki kwance saman gado yana bacci, Yazo yana kuka ya faɗa min wai kin ce zaki 6alla mashi mota, Daƙyar na samu na lallashe ya daina kuka ya kwanta," dariya aneelerh tasaki tare da cewa"Ya takura mun ne mami, ina tsaka da yin bacci na ya daddage ya danna jiniyar motar, baki ga yarda na zabura ba, Ni nayi tunanin ƴan sanda ne suka zo ashe shine" Dariya mami tayi tana girgiza kai tace"Allah ya shirya min jikana, " aneelerh ta amsa da amin, kafin Ta juya ta nufi falo, Agaban dining ta hango ana tana jera kayan breakfast ɗinsu, Ƙarasawa tayi inda take atsaye ta miƙa mata wayar tare da yi mata godiya, don ba ƙaramin daɗi taji ba, atlease tasan benazir tana araye, Idan Allah yasa suna da tsawaicin kwana wata rana Allah zai haɗa su ne, ta wani 6angaren kuma Abun ya tsaya mata acikin zuciyarta, Irin yadda taga benazir a hoton hankalinta kwance babu wata damuwa akan fuskarta,

Yinin ranar da tunanin benazir tayi shi, Da rana ne Abie Ya dawo daga wurin aikinshi, Yazo musu da babban albishir Na ƙara mashi matsayi da akayi zasu koma Abuja da zama, mami tayi farin ciki, aneelerh kuwa sam bataso haka ba, Ita fa duk wani abu da zai rabata da jos ba son shi take Yi ba, gani take kamar idan ta ɗaga ƙafa tabar garin shikenan ba zata ƙara ganin mutanan nan ukun da ta rasa ba, waɗanda a koda yaushe take Addu'ar Allah ya Bayyanar mata dasu, babu yarda ta iya yanzu dole tabi iyayenta don bata son rabuwa dasu, tafi so duk Inda zasu je ƙafarta ƙafarsu,

*Back To prison*

Ƙwaƙƙwaran Juyi angel tayi da niyar ta gyara kwanciyarta, sai ji tayi an tokare bayanta, A matuƙar ruɗe ta juyo tana kallonshi, waro ido waje tayi ganin danish saman gadonta, Aikuwa rai a6ace ta sanya ƙafarta da ƙarfi ta ture shi gaba ɗaya ya gangara ƙasa Kanshi Ya bugu sosai har saida yafirta"ash!!" saboda zafin da ya ji, Zazzaga mashi masifa ta soma Yi ta inda ta shiga bata nan take fita ba, sautin muryarta ya karaɗe Kunnuwan masu bacci ɗaya bayan ɗaya su batool suka dinga farkawa Suna tambayar lafiya me ya faru?

Nuna danish ta yi da yatsan Hannunta tace"wlh kaɗan ka gani, Idan har baka fita sabgata ba, Ina mace kana namiji Ka kwana a gadona, Salon kawai kaja mini zunibi," Tun da ta fara Yi mashi faɗa, bai motsa daga kwancen da yake a ƙasa ba, ya dafe gefen goshin shi da hannu, Yaji zafin buguwar da kanshi yayi,

Saukowa su batool su Ka yi daga saman beds ɗinsu, fuskokinsu duk A yamutse idanuwansu sun kumbura sakamakon kukan da suka sha Jiya da za'a tafi da deeja,

Abakin gadon angel suka tsaya suna kallonsu ita da danish, Ta rufe ido sai faɗa take mashi hada pillow ta jefe mashi saman fuska, Ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, shouting ɗin da take yi mashi ba ƙaramin gigita shi yake yi, daurewa kawai yake yi,

"Pls angel, Ki yi haƙuri Ki ƙyale shi hakanan, kodan saboda lallurarshi ta rashin son hayaniya zai iya rikicewa, Hanna ce tayi maganar, angel ta watsa hannu tare da cewa"Idan ya tashi ya haukace ƙarewa ma, wlh ko ajikina, tun farko saida naja mashi kunne akan ya ni santa kanshi dani amma yaƙiya, saboda head fish ne dashi"

Girgiza kai batool ta ɗanyi idonta akan angel tace"Sister badan halina ba, Pls Ki bar maganar nan, Ki barshi yaji da kanshi, Nasan kina fushi dashi ne saboda abunda ya faru jiya, Ki yi haƙuri ki manta komai, kuma ki daina fushi dashi saboda Baya ƙaunar yaga ana share shi, Yana shiga damuwa" daƙyar batool takarasa maganar ganin irin kallon da angel ke jefa mata,

Gyaɗa kai tayi tare da jinjina kai tace"Shikenan zan ƙyale shi amma babu ruwanshi dani! Ni kawai bana son Yana kallona ko Yana yi mini magana, " Tana kammala maganar ta sauko daga saman gadonta ta bi ta gefensu Ta shige toilet,

Zuƙunnawa batool tayi agaban Danish Ta ruƙo hannunshi acikin nata, Ba ƙaramin tausayin shi taji ba, ganin sahun marin da angel tayi mashi asaman fuskarshi har yau bai disashe ba,

Cikin sanyin murya tace"Am sorry danish, Kamar yarda tace ka ƙyale ta, to ka rabu da ita har zuwa time da zata huce, if not zata cigaba da Ƙyararka ne, Nasan zata dawo da kanta ne ta nemi yi maka magana," sai lokacin ya samu ya miƙe zaune, ya jingina bayanshi jikin bango, ɗaya bayan ɗaya ya shiga binsu azeeza dake atsaye da kallo, matan ne gaba ɗayansu, Sai daga bisani Haris da su naufal Suka Sauko daga saman gadajensu, A inda yake zaune suka tsaya cirko cirko suna kallon shi,

"Kuma fushi ku ke yi da ni? Kamar yadda take fushi dani"? Yayi masu tambayar idonshi akansu, atare suka haɗa baki wurin cewa a'a, Kallon haris yayi tunkafin yayi mashi magana haris yai saurin cewa"am not angry with u, kaima ka sani bazan iya fushi dakai ba, just banji daɗin abunda ya faru ba jiya, amma komai ya riga daya wuce" jinjina kai danish yayi kafin ya kuma cewa"komi nake yi ina yi ne saboda ku, amma nasan zaiyi wuya ku fahimci hakan, sai nan gaba"

Naufal yace"Pls danish, mu komai ya wuce awurinmu, abunda ya faru ya riga daya faru ba wanda ya isa ya dawo dashi baya, so pls mu manta kawai, baida amfani tuna baya," Danish yace"idan ku kun fahimce ni, ita taƙi ta fahimce ni, tun daren jiya nake bata hakuri amma taƙi ta saurare ni," sai lokacin suka gane inda damuwarshi ta dosa, dama shi haka yake sam baya son wani yana fushi dashi tun fil azal, gaba ɗaya yake rasa sukuni,

"Danish kada ka damu kanka, In dai angel ce Zata kula ka, Ae bata iya fushi ba, tana da saurin hawa da kuma saurin sauka," acewar javed,

Ta6e baki yai tare da cewa"Its okey, ngde da kulawarku agare ni, " daga haka Ya miƙe jiki ba ƙwari Ya Nufi toilet, domin yin wanka,

Kafin Giants su kawo musu Breakfast ɗinsu, Sai da kowannan su Ya yi wanka, Basu jima da hallara A cikin ɗakin nasu ba, Sai ga Giants ɗin sun shigo ɗauke da kayan abincinsu, bayan sun ajiye musu saman dining carpet, duk suka zazzauna kewaye da farantan, Yau farfesun naman kaza aka kawo musu da zafinshi hada tiriri Yaji kayan ƙamshi, ga kuma dambun nama da aka haɗo musu dashi, sai Kayan marmari kamar kullum da kuma soft drinks, Abun na ɗaurewa angel kai, ganin irin badagon da ake yi da nama agidan kurkukun, sam bata yarda da irin wannan Lafiyayyar cimar da ake kawo musu ba, kullum basu da abinci sai nama kala kala! Na kaza na shanu na rago, wani naman ma batasan na wace dabbar bane, tana yawan tambayar kanta ko su wanene ke girka abincin kurkukun daga gani ƙwararru ne a 6angaren catering, sun iya sarrafa abinci, wani naman saboda tsabar dahuwar shi kana jefa shi abaki tunkafin ka taune da haƙori zai dagargaje da kanshi, ita dai fargabarta kada ace abincin da ake basu su naci, da ransu za'a fanshe, duk in zuciyarta ta saƙa mata hakan sai taji gabanta ya faɗi rasss! Don kuwa ko gwamnati bata aikin banza, balle kuma mutanan da Ba Allah ne aransu ba, Sunsan dalilin dayasa suke basu lafiyayyan abinci wata'ƙil kodan suna amfani dasu ne, Allah wa'alamu


kafin su fara Shan farfesun saida ta tunasar dasu akan su yi bismilla, Kullum ne sai ta tuna musu, hatta haris yau da tace su yi bismillah sai da yayi duk da bai musulunta ba, danish ne kawai baiyi ba, Ta lura dashi duk wani abu daya ƙunshi sunan Allah aciki bai furta shi, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba, Har suka kammala cin abinci, da zarar sun haɗa ido dashi sai ta dinga jefa mashi harara, duk yabi ya tsargu ya hana zuciyarshi sakat, farfesun ma ba'a cikin kwanciyar hankali yasha shi

Ads At the End of Article
Sidebar Ads

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads